You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana son Mace
Ma aji wacce idan ka kalleta ma zata zuba maka harara ba irin wannan da take gabansa ba. Shi yasa ko
aure zai yi zai sha wuya wajen neman matar aure don sai ya tantance sosai kada ya auro B’ARAGURBI. Ya
sake gintse fuskarsa Har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana fin cikar leb’ensa al’amari ne da
yake nuna kaiwa k’ololuwa wajen b’acin ransa. Madadin fushi daga Safna dariya ta saki ka’dan irin dariyar
shahararrun y’an bariki ta kuma ja ta tsaya hannayenta a k’irji ta furta “Dole ka yi, kai da kanka ka San ka
ha’du, nice to meet you sunana Safna addu’a ta guda Allah yasa department D’in mu d’aya.” Idan kai da
baka wajen ka yi magana to Moddi ma ya yi magana, shiru ya yi bai amsa mata ba ya sake mayar da P.Cap
d’insa kawai zuciyarsa na gaya masa ya tashi ya falla mata mari. Sai dai kawai ya share yana k’ananan
tsaki ya furta “Bar nan wajen.” Safna ta ware ido tana kallonsa ta ce “In ji ina? Ai ni nan naga wajen
zama….” A zafafe ya mik’e Har yana y’ar da P.Cap d’insa ya saka hannu don d’auka hannunsu ya sauka
tare da na Safna ya bi hannun da kallo da ya sha zak’ala zak’alan farce kamar ba y’ar musulmai. Caraf ta
rik’e P.Cap d’in Har da manna ta a k’irjinta tana furta Alhamdulillah na yi babban kamu wannan hular tafi
min samun 100k yau…..” Moddi cikin b’acin rai ya d’aga mata hannu sai dai ya rasa mai zai ce mata kawai
sai ya danne lips d’insa da harshen sa ya furta “Fuck you…” kansa tsaye yana kallon cikin k’wayar idonta.
Safna ta yi murmushi ta ce “Thank you.” A hassala ya bar wajen yana jin idan ta sake biyo shi wannan
karan sai ya mareta sai Allah yasa bata bi shi ba ta wuce da hular a hannunta, tana shinshina turarensa da
k’amshin sa ya mak’ale a jikin ta. Hararar k’asan ido ya bita da ita kafin ya tauna lips d’insa a hankali yana
furta “Rubbish.”




Daga ranar Ya zama na duk inda Safna ta San zasu ha’du sai ta bi shi. Ya yi mata jan idon amma sam bata
ji. Gashi ajinsu d’aya don department d’insu guda. Tun kowa bai sani ba har jama’a da dama suka targa da
yawan nacin da take masa, shi kuma baya gajiya wajen yarfa ta a gaban kowa. Mata da yawa bayan ita
Sun kawo masa tayin abota ko soyayya, sai dai kallo guda yake musu su bawa wandonsu iska. Don a
idonsa suke hango wani kwarjini da alamun rashin wasa a tattare da shi. Kullum girarsa a tsare idan ka
gan shi yana hira to cikin y’an uwansa maza ne, wannan kuwa zaka tarar da shi yana faffa’dan murmushi.
Bai san abubuwan da suka faru, sai dai lokaci guda ya samu kansa dumu dumu cikin wata irin zazzafiyar
k’aunar Safna, da ko a mafarki bai tab’a zaton zai riski kansa a haka ba. Sha’awarta mai zafi ta kama shi ya
dinga yin wasu irin mafarkai a kanta abin kamar sammu ko sihiri. Tun yana daurewa yana sharewa Har dai
da kansa ya kai kanta wajenta wata ranar Laraba da ba zai tab’a mantawa da ita ba. Address D’in gidansu
ya nema. A shekaru irin nasa Ashirin sai ya dinga ji kamar ya yi k’ank’anta da zuwa wajen budurwa Amma
abinda yake ji a ransa ya hana shi togace kansa daga zuwa wajen Safna. Wanka ya tsala sosai ya shirya
sosai cikin shigar da yake tafiyar da Imanin mata. Jikinsa ya d’au k’amshin masifaffen turarensa na MIYAKI
Wanda a lokacin sai ka kai ka kawo kake fesa shi. Ya fita tsakargidan sai da ya ji gidan shiru sannan ya
tuna basa nan sun tafi biki k’auyen su Didin, sai ya ji missing Didi da addu’ointa. Ya d’an Shafa kansa kawai
yana sakin murmushi da tana nan da ta tuni ta tofe shi da addu’a. Fita ya yi daga gidan bayan ya ja
k’yauren gidan ya datse da mukulli, bai damu da ya yi addu’ar ba ya nufi bakin titi direct don samun abin
hawa. Inda za shi ya sanar da mai abin hawa unguwar Lamid’o crescent. Tabbas Ya san unguwar masu
ku’di ce don haka yake ganin kamar ya yi tsalle Ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba.




Babban gida mai girman gaske nan Mutumin da Ya tambaya ya nuna masa. Nan shine gidan Aliyu
Mak’arfi d’an samari wani ka zo nema a gidan?” Kallo guda ya yiwa gidan ya ji kamar Ya koma sai dai so
da k’aunar Safna tasa ya kasa barinsa komawa. So yake ya bata surprise tunda har yanzu ya san tana son
sa ba abinda zai faru In sha Allah. D’an d’aga kai ya yi yana amsawa Dattijon mutumin. Sai mutumin ya yi
murmushi Ya dafa kafa’darsa yana furta “Ka kula, ka yi takatsantsan don jama’ar gidan basu da mutunci ,
basu San mutuncin d’an Adam ba, gani suke tunda suna da ku’di za su taka Uban kowa bakomai ba ne a
wajensu.” Moddi ya d’aga kai yana yiwa mutumin godiya sannan ya k’arasa bakin gate D’in. Suka gaisa da
mai gadin da yake masa wani gani gani sannan ya gaya masa Safna yake son gani…” Mai gadin Ya bi shi
da wani kallo kafin ya furta “Dama kai ne bak’on da Safna ta ce min ko mu da’de ko mu jima zaka zo, idan
kazo kuma na barka ka shiga. Na zata zan ga wani gwaska sai na ganka a kan sawayenka….” Moddi ya cije
bakinsa yana tattare girarsa waje guda, sai mai gadin ya shiga taitayinsa ganin Alamun Moddi bai zo da
wasa ba ya ce “Bari na kira maka ita, shiga da ciki…” Moddi ya girgiza kai yana mik’ewa ya ce “Batta
kawai.” Da sauri Maigadin Ya ce “Afuwa d’an samari, Ban fa’da fa don wani abu ba. Abin ne Ya bani
mamaki ganin irin manyan mutanen da suke zuwa wajenta su fita a mota yau kuma sai na ga kai dai
matashi ne da baka zarce shekaru ashirin ba, kuma da alama baka da ……” “Ba ni da ku’di.” Moddi ya
fa’da yana zuba birkitattun idanunsa kan na Mai gadin yana jin wani zallar b’acin rai. Me yasa jama’ar
yanzu Sun fi girmama ku’di ne fiye da mutunci? Da sauri Maigadin Ya girgiza kai yana furta “Afuwa ban
san da Soja nake tare ba…” ya furta yana k’ok’arin zubewa a gabansa. Moddi ya saka hannu Ya d’aga shi
yana sakin murmushin da bai shirya ba ya ce “Baba wa ya ce maka ni Soja ne?” Mai gadi Ya girgiza kai
yana furta “Ai ba sai an gaya min ba, kwarjinin idanunka ya isa ya tabbatar da haka, ka godewa Allah
irinku ko ido ba’a iya ha’dawa da ku, irinku k’alilan ne cikin Al’umma. Bari na kira maka Safnan.” Ya shige
ciki ya bar Moddi a tsaye cikin zafi da tafasar zuciya ji yake kamar ya juya Amma kuma ya kasa aikata
hakan kamar Wanda ake controlling d’insa da remote soyayyar Safna ce narke a zuciyarsa….




Ko minti biyar ba’a yi ba, sai ga Safnan ta fito fuskarta fal annuri ya ga ta zuba masa ido. Shima kallon
nata yake yana jin kamar ya rungumota a jikinsa. Tana isa wajensa ta furta “Mu shuga daga ciki, na dad’e
ina jiran wannan ranar sai gashi ta zo yau, gani ga My love.” Bai yi musu ba ya bita. Tana cigaba da sarrafa
jikinta ba don komai ba sai don ta susuta tunaninsa. Ta kuma ci sa’a don gaba d’aya sha’awar Moddi sai
da ta gama tashi. Sitroom ta kai shi. Bayan zamansa ta shiga gida don samar masa abinda zai ci. Jingina ya
yi da kujerar yana jin abinda yake ransa yana sake hauhauwa bai San ta shigo ba don idonsa a lumshe
yake sai da ya ji ta zauna a daf da shi ta kuma rungumoshi kamar jariri. Ya bu’de birkitattun idonsa da
suka canja launi yana k’ok’arin janye jikinsa Safna ta sake shiga jikinsa ta manne k’irjinta da nasa a kunne
ta ra’da masa “Feel Free my dear we are alone.” Sai da ya wani irin runtse idonsa saboda yanayin da ya ji.
Ta saki murmushi ta sake kai harshe tana lasar kunnensa sannan a hankali ta ra’da masa “I love you
Moddi, irin son da ni kaina Ban San ya zan kwatanta maka shi ba, abu guda na sani kullum da kai a cikin
barci na, kullum kuma sai mun shige cikin wani tafki mai da’din gaske fata na yau ka nuna min irin abinda
nake imagining a cikin barci.” Tureta yake k’ok’arin yi sai dai zuciyarsa bata son haka. Ajiyar zuciya yake
saki kawai bai tab’a shiga irin wannan yanayin ba sai yau. Bai tab’a kusantar mace haka ba sai yau shi yasa
ya ji shi a wata irin duniya. Safna ta samu abinda take tuni ta mik’e tsaye ta watsar da abayar da take
jikinta sai ga wata b’ingilar riga da ta bayyana komai nata a jikinta. Moddi bai san sanda ya runtse ido ba.
Yana furta “Ki bari Safna ba kyau.” Bai yi aune ba ya sake jin ta shige jikinsa tana wani irin zuba masa hot
romance gaba d’aya ta gigita shi. A kunne ta ra’da masa “Bakomai Moddi, ka saki jikinka ba sex za mu yi
ba just romance…” ta fa’da tana manna bakinta cikin nasa. Wannan karan duk wata jijiya ta jikinsa ta
mik’e ji yake a halin da yake ciki ko Sex D’in zai iya yi. Sai da ta yi son ranta sannan ta janye jikinta ta kuma
baje a k’asan carpet tana bin Moddi da wani irin kallo da yasa ya rasa nutsuwarsa hannu take mik’a masa
tana nuna masa ya zo su kwanta… sai dai take kwanyarsa ta hango masa Didi da dukkan kashedin da
take masa a kullum tun bayan da ta tabbatar ya balaga. “Ka Guji Zina Moddi, ka guji Zina tana daga cikin
manyan Alkaba’ir. Ina rok’on Ubangiji duk sanda ka aikata zina Allah ya tona min asirinka na sani. Daga
ranar zaka san wacece ni….” Da sauri ya mik’e kamar Wanda da yake zaune a kan wuta ya yi hanyar waje
yana rufe fuskarsa da black glass don son b’oye yanayin idaniyarsa yana Jin muryar Safna tana kiransa da
wani irin nishi bai bi ta kanta ba ya fice da sassarfa yana jan istigfari a ransa.




Yanayinsa da rashin nutsuwa yasa kana ganinsa zaka san akwai abinda yake damunsa. Kullum cikin tunani
ya saka son Safna sosai a ransa. Yana komawa gida ya tarar da Fateema tazo kallo ta masa ta gane yana
da matsala. Hakanan Didi da ta bi shi da nata idanun. Ya zauna yana rik’e kansa da Ya ji yana sarà masa.
Tun bai yi magana ba suka san akwai matsala. Fateema ta k’arasa daf da shi ta zauna kafin ta ‘dora
hannunta a k’irjinta ta furta “Kiddo lafiya?” Cikjn wani yanayi ya kalleta da raunatattun idanunsa sai
kuma ya lumshe su. Cikin wata irin murya Didi ta ce “Muhammad ka yi magana mana, me ya faru?”
Madadin maganar itama kallonta ya yi yana lumshe idon yana cije leb’ensa ya furta “Bakomai fa.”
Fateemah ta gyara zamanta tana furta “A’a da komai fa, ai idanunka Sun bayyana akwai matsala, ka gaya
mana kawai.” Ya sake rik’e kansa yana gurzawa a hankali Ya furta “Mu je d’akina mu yi magana…”
Fateemah da gaban ta yake wani irin tsalle ta mik’e da sauri ta bi bayansa tana fatan koma me ye ya zamo
abinda za su iya maganin matsalar tasa. Zama ta yi a gefen katifarsa shima ya zauna daf da ita, yana sakin
huci ka’dan ba tare da Ya ce komai ba. Tee ta ce “Ina jin ka gaya min Kiddo.” Sai da ya cije leb’ensa sannan
ya furta “Aure nake so na yi….” Da wani irin mamaki take kallonsa ta furta “Aure kuma? Ka San me kake
fa’da Kiddo? Aure at your young age…” lumshe idonsa kawai ya yi don ya lura sam ba zata fahimceshi ba.
Da yana da iko da Ya bu’de mata zuciyarsa taga mai take ciki. Da gaske zafin sha’awa irin na tashe samar
taka yana shirin hallaka shi. Fateemah tab’e baki ta yi tana harararsa ta furta “Idan ma mafarki kake ka
farka, shekarar ka ashirin da d’aya kai ba kowa ba, ba kuma d’an wani ba ka ce zaka gingimowa kanka
maganar Aure wallahi kada ka sake ma Didi ta ji ka tayar mata da hankali a banza.” Daga haka ta saka kai
zata fice daga d’akin ta ji Ya furta “Adda T, duk abinda ya biyo baya ba ruwana, don abinda na gaya Miki
iya gaskiyar kenan har cikin raina…bana son na jawo muku magana zan iya samun y’ar ko waye na sauke
mata abinda nake ji…” Zuciyarta ta ji ta buga amma sai ta cije ta fice da sauri. Bata yi niyyar gayawa Didi
ba, amma ganin kallon Didin take mata yasa ta kasa samun nutsuwar yi mata k’arya. Shigowar Moddi ce
ta saka su d’ago da kai dukkansu. Yana kallon Didi ya furta “Didi kina da lemon tsami, yanzu na tambayi
wani abokina ya sanar da ni shine maganin matsalata…” Didi ta d’ago tana masa kallon k’urilla bai wani
damu ba ya zauna daf da ita yana rik’e k’asan cikinsa ya kwanta rigingine yana cizon leb’e. Takaici da wani
bak’in ciki ne suka saka Fateemah sakin baki tana kallonsa. Bata San rashin kunyar Kiddo har ta kai haka
ba, ta tabbata ko bai fito Ya gayawa Didi abinda yake

Ji ba, Didin da kanta zata fassara abinda yake nufi. Didi wani guntun murmushi ta saki ba tun yanzu ba, ta
San Moddinta ya girma kuma

Lafiyayyen namiji ne. Kitchen ta shige ta ha’da masa Lemon tsamin har da gishiri ka’dan sannan ta fito ta
mik’a masa tana lura da kallon takaici da Fateemah take wurga masa. Hakan yasa ta sakin murmushi tana
furta “Ki bar shi Fateemah, lokaci ne yazo haka girman yake ai, a wajen su Maza.” A zafafe Fateemah ta ce
“Wallahi Didi iskanci ne, da kuma ya raina ni ni da ke, Ya jewa Dijatu da wannan maganar mana idan bata
ci ubansa ba, rashin kunya k’iri-k’iri, shi dole sai ya nunawa mutane ya balaga, a d’aki fa Ya saka ni yana
gaya min wai mu aurar da shi kada ya janyo mana abin kunya….” Didi ta d’an yi dariya tana furta “Allah
y’a hore abin auren, idan Allah ya hore Ai sai a yi auren, Don gwara auren da yaro ya d’ebo maka abin
magana…” Moddi ya turo baki ya yiwa Fateemah gwalo ta kuwa sake hassala hakan yasa ta furta “Ai sai
ka yi auren, idan kana da sana’ar da zaka kula da matar.” Ya mik’e yana ce mata in dai abinci ne ai Didi
zata bata.” Ya fita daga d’akin saboda jin wani yanayi a jikinsa yana buk’atar tsaftace kansa. A zauren
gidan ya juyo siririyar muryarta tana sallama. Ya amsa sallamar yana kallonta da k’waryar nonon da ta
Saba kawo musu talla a kanta. Aa usual yau ma jikinta tas kamar ba wacce tazo daga rigar fulani ba. Ya
bita da kallo tun daga sama har k’asa sai kuma Ya d’auke kansa fuskarsa a d’aure Ya kalleta yana furta
“Zubo fura ki kawo min d’aki na, ke y’ar riga….” Ta yi wal da idonta kafin ta saki murmushi tana bin
bayansa da kallo wani farin ciki na cika zuciyarta a karo na farko Moddi ya mata magana cikin kwantar da
murya ba hantara da kyara, ko dai Allah ya amsa addu’ar da take yawan yi ne? Ko gidan bata shiga ba ta
durk’usa cikin rawar jiki ta fara dama masa furar mai da’din gaske. A bakin k’ofar sa ta tsaya tana furta
“Fillo ga furar…”Cikin wata irin murya ya ce “Shigo Malama…..




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS……👌


24.




NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️


08033748387.



BRIGHT PENS SECOND BATCH.



★★★

Kamar ba zata shiga ba, don zuciuarta wani irin bugu take yi, sai dai ta daure ta shiga ‘din. A zaune a
saman katifarsa mai tudun gaske d’akin sai zabga k’amshi yake don Moddi yana da tsafta baya shiri da
k’azanta kuma sam. Kallo ya bita da shi, kafin ya cije leb’ensa yana tunanin abinda zai aikata D’in daidai
ne, amma abinda yake ji ya shalle tunaninsa, Ya manta DIDI da kashedinta, ya manta da fa’dan da zata
masa ma. Ya dinga bin y’ar riga da kallo kafin ya saki malalacin tsaki ya furta “Zo ki zauna anan…” “Ta
zauna a ina Kiddo?” Fateemah ta fa’da don fitowarta daga gida kenan kawai taga kayan Y’ar riga da
takalmanta, ta San Moddin basa shiri da y’ar riga asalima ya tsani ganinta kullum hantararta yake yi.
Madadin amsa mata wani takaici ne Ya rufe shi ya lumshe idonsa kawai yana taune leb’ensa, banda ma
jaraba irin tasa me zai yi da wannna y’ar abar da baya mata kallon mace? Haushin kansa ya kama shi don
haka Ya cusa yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana fisgar gashin da k’arfin gaske kamar shi ya masa
laifin. Fateemah a hassala ta finciki hannun y’ar riga da take tsaye tana ta rawar jiki da alamun tsoro
mabayyani a saman fuskarta. “Shashasha, me ya kawoki d’akinsa?” Cikin rawar baki ta furta “Shi ya kira
ni….” Wata harara Moddi Ya zuba mata hakan yasa ta ja baki ta yi shiru, jikinta na sake b’ari. Fateemah
ma harara ta zuba mata ta yi k’wafa tana furta “Da ya kira ki baki da wayo da zaki shiga d’akin maza?baki
son ko ya kake da namiji ba a wannan zamanin baka sakin jiki da shi, bare irinsu Kiddo da kunya bata ishe
su ba…” “Kada ki saka ta raina ni, wallahi b’allata zan yi.”

Moddi ya fa’da daga zaunen da yake fuskarsa a d’aure sosai. Sai abin ma ya bawa Fateemah dariya ta
furta “Raini na nawa kuma? Banda Wanda ka siya wa kanka, wallahi zaka zo ka samu Didi ka gaya mata
dalilin da yasa ka ja y’ar mutane d’aki….” K’asa k’asa ya furta “Dalilin ne yasa na ce ku yi mini aure…”
tsabar takaici Fateemah kasa amsa shi ta yi ta finciki hannun y’ar riga suka shiga gida tare wajen Didi.



Didi ta d’ago tana kallonsu kafin ta furta “Ke kuma fa, yaushe kika zo?” Sunkuyar da kai kawai ta yi tana
jan yatsun hannunta. Moddi da yake bayansu ya juya ya shiga parlor yana ji Fateemah na gayawa Didi
abinda ya faru. Didi ta zaro ido tana furta “Lamarin Har ya kai haka? Hasbunallah Wa ni’imal wakeel,
yaushe Moddibo ya koma haka? Ai shikkenan wuce ki tafi gida ni na San maganin abin, auren zan masa
da duk kuma yarinyar da tarbiyyar ta ta kwanta min a rai….” Yana jin haka ya yi saurin fitowa daga d’aki.
Yana muzurai ya ce “Not any girl Didi, ba da kowace mace Imaam zai iya rayuwa ba, na fi son y’ar gayu
mai tsafta wayayyiya y’ar boko.” Ta zuba masa harara tana furta “Shirmen banza da wofi, duk a lissafin
naka kuma Ban ji ka furta mai addini da iliminsa ba, mai kunya da tarbiyya…” Ya girgiza kai “Bagidajiya
kenan? Ai irin wannan yaran ba wayewa a tare da su, nifa nafi son wacce zamu buga Soyayya wacce ba
zata ji kunyarki ba, zata iya rungume ni a gabanki ta min Kiss….” Bu’de baki Fateemah ta yi tana kallonsa
Didi kuwa murmushi ta saki ta San Moddinta Ya kere nan, sam ba ya jin kunyarta sanda ya fara mafarki
ma ita ya fara samu ya gayawa, wai ya ga wani abu mai da’di a cikin barci ashe haka Mata suke da da’di
Didi musamman idan ka rung….” Didi ta yi saurin rufe masa baki tana furta “Wannan sirrinka ne Moddi,
kada na sake jin ka bayyana shi ga wani, alamu ne na ka girma kana kuma da lafiya…” Sai ya d’an yi
dariya yana rik’o hannunta yana furta Didi ko shine Jima’in da ake gaya mana a Islamiyya?” Didi bata ji
kunyarsa ba ta gaya masa shine, amma haramun ne aikata shi sannan Allah yana fushi da mutumin da Ya
aikata zina ma’ana kusantar Mace ba tare da an musu aure ba, don haka ka kiyaye Moddi ka bari ka samu
halaliyarka… haka ta zaunar da shi a matsayinta na Uwa bata b’oye masa komai ba, ta bu’de masa komai
ya sani sannan ta tsorata shi da kusantar koda rik’e hannun mace ne,balle wane sashe na jikinta, da zarar
ka aikata haka Moddi kamar ka shirya jefa kanka cikin zina ne da saninka don haka ka yi matuk’ar kiyaye
wa Allah ya shirya mana. Fateemah ta jijjjiga kai bayan ta sake wurga masa harara shi kuma ya mata
gwalo sai ta gefe shi da biron hannunta sannan ta fice tana furta “Didi siyar da gonar ki ta k’auye Ya
kamaki ko don ki yiwa Kiddo aure, idan ba haka ba kya ji wani labarin…” “Dole kuwa.” Didi ta furta kallon
Fateemahn “Ai dole na yiwa Moddi aure a kusa kusan nan, Allah dai Ya hore mana rai da lafiya.” Haushi
ya kama Fateeman ta fice tana furta “Ko da Uban me zai ciyar da matar?” Moddi da baya shiru ya furta
“Duk abinda Didi ta ci shi za mu ci, balle ma In sha Allah ba zan yi zaman banza zan dinga neman ku’di.”
“Kamar gaske?” Fateemah ta furta tana ficewa da hanzari don idan ta biyewa Didi da Kiddo sai ta kwana
a wajen bata gama kallon dramerrsu ba. Ita dai y’ar riga tana takure jikin Didi duk hankalinta ya tashi jin
za’a yiwa Moddi aure mutumin da take kwana ta tashi da shi a cikin rai… “Tashi daga nan ko na bugeki.”
Moddi Ya fa’da yana zuba mata harara. Da sauri ta tashi sai dai Didi ta ja hannunta ta mayar da ita ta
zauna, haka kawai take son yarinyar don tana da nutsuwa kuma Sam bata da kwarafniya ga Ibada kamar
ba daga riga ta zo ba. Amma bata san dalilin da yasa sam basa shiri da Moddi ba, don kar ya kira sunanta
yake kiranta da y’ar riga, Har sunan Yabi bakin kowa. A hankali ta gyara mata mayafinta tana furta “Uhm
uhm fa Moddi, ka yi fa a hankali don baka san inda rana zata fa’di ba.” Ya yi dariya sosai kafin ya furta ta
fa’di a gabas wallahi Didi, kada ma ki fara ta inama wannan yarinyar da ‘d’an k’ugunta zasu iya d’aukan
hidimata ji ta fa k’waila, ni nafi son mai manyan Abubuwan nan….” Da sauri Didi ta bu’de ido ganin inda
yake nunawa ta kuwa zuba masa dak’iwa tana furta “Fita daga nan Moddibo, Oh ni Mairo Allah ya
taimaki Uban Moddibo baya raye ba zai ga wannna rashin kunyar taka ba.” Ya k’unshe dariyarsa yana
furta “To idan ban fa’da Miki ba wa zan fa’dawa? Ai gaskiya ne ina zan saka wannan k’wailar?” Didi ta jefe
shi da ludayi hakan yasa ya fita yana dariya. Bai san kuma ya suka k’are ba.




Haka Safna ta cigaba da bibiyar rayuwarsa. Duk inda ya saka k’afa tana biye da shi, shima kuma hakan sai
yake masa da’di wata irin haramtacciyar soyayya Safna take koya masa ta inda sam baya iya guje mata.
Hot romance take zuba masa har ya rasa inda zai saka ransa. Ranar da ba zai tab’a mantawa da ita ba,
ranar da Safna ta ja shi wani hotel. Bai so zuwa ba

Amma ganin b’acin ranta k’arara yasa ba shiri Ya amince. Wanka Ya fesa ya fito sai zabga k’amshin turare
yake. A parlor ya tarar da Didi da Fateemah da su Jameela suna ha’da akwatinan Yabi akwatinan da kallo
yana furta “Didi wannan fa? Lefen waye?” “Na wani” Fateeman ta furta fuskarta a d’an d’aure. Tab’e baki
ya yi sai ya saka kai ya fice ganin har Safna ta fara zabga masa kira. Yana jin Didi na k’walla masa kira tana
fa’din Moddi addu’ar fa? Yau ka yafe.” Bai amsa mata ba ya fella da gudu don baya son Ya sake delay balle
ya b’atawa Safna rai. Didi kasancewr ta yi busy sai kawai ta k’yaleshi suka cigaba da abinda suke.




A bakin k’ofar D’akin Hotel D’in ya tsaya yana jin yarda zuciyarsa take harbawa, wai shine yau ya kawo
k’afarsa hotel? Anya bai ci amanar Didi ba. A tsorace yake amma idan ya tuna yarda k’irjin Safna yake a
cike sai yaji baya son barin wannan damar. Shi burinsa ko wasa ya yi da su Ya samu relief daga tarin
abinda yake ji a ransa. Ya d’an fusgi leb’ensa sai kuma Ya saka hannu ya murd’a k’ofar ya shiga. Sai da
numfashinsa yaso d’aukewa ganin Safna a kwanta rigingine ba komai a jikinta. Sai sakar masa murmushi
take tana lasar leb’enta. Ta mik’a masa hannunta Amma ya ja ya tsaya ya kasa matsawa kusa da ita.
Mik’ewa ta yi tana girgiza jikinta ta isa kusa da shi sosai. Sai da Moddi ya runtse ido tsabar yarda yake jin
wani yarrr a jikinsa ganin mace a gabansa ba kaya. Bai san kalar abinda ya ji ba abu guda ya sani ya kasa
controlling kansa a matsayinsa na mutum mai lafiya kuma matashi mai tashe balaga. A wannan daren ya
san Safna

Please Login or Register in order to submit comment