You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kai tana amsar plate
‘din da ya cika mata da abinci. Sai ta samu kanta da cin abincin sosai ko don yana ta janta da hira ne. At
last ta saka hannu zata ‘debi abincin sai taji wayam. Ta yi saurin kallon plate ‘din tana waro ido. Shima
Alwan waro idon ya yi ya ce “Duka kika cinye?” Kunya ta kamata ta yi saurin sunkuyar da kai. Alwan ya yi
dariya yana janyo leda ya tura mata a gabanta. Chocolates ne da Ice cream masu mugun tsada. Farin ciki
ya bayyana a fuskarta sosai don ta yi missing ‘dinsu. Da sauri ta ja robar Icecream ‘din mai flavor ‘din
chocolate ta fara sha. Tana furta “Thank you Uncle…” Alwan ya saki ajiyar zuciya yana mayar da fuskarsa
serious face ya furta “Kina so na cigaba da zuwa?” Ta d’aga Kai. “To ki dinga yin duk abinda aka saki, kin
ji? Bana son musu kuma ko me aka baki ki ci, a yanzu dai ba zasu cutar da ke ba, don ba su d’auko ki don
haka ba, but idan kika musu taurin Kai zasu iya cutar da ke.” Hawaye ne yazo idonta ta yi saurin Kama
hannunsa tana girgiza kai. Don’t live here Uncle, ka zauna please…” ya duba watch d’in hannunsa yana
girgiza kai “I have a meeting, but bari na kunna Miki kallo akwai Korean movies da Indian movies ki kalla
zasu dinga d’auke miki kewa…” ta bi babbar Wall Tv ‘din da kallo ita ta manta ma da wani zancen kallo
saboda tashin hankalin da take ciki. Sai ta ji wani relief ganin Uncle Alwan yasa ta ji ta samu nutsuwa
sosai, a yarda ta ‘d’auke shi kuma a inda yake mu’amalantar su sai taga kamar ba zai cutar da ita ba. Ya
kunna mata kallon sannan ya fita bayan ya ce mata ta yi wanka. Bata yi musu ba kuwa yana fita ta mik’e
ta shiga wankan, don ita da kanta ta san tana buk’atar wankan a yanayin yarda take Jin jikinta. Wanka ta
yi sosai a ha’dadden toilet ‘din. Kuma ta samu Skin routine masu kyau sosai. Ta wanke gashin kanta. A
mirror ta tsaya tana kallon cikinta da ya fara tasawa ka’dan. Sai ta dinga Jin tausayin cikin tana mamakin
dalilin da yasa Alwan ya ce cikin kawai suke so, amma ta San ya yi haka ne don ya taimaketa, don da
kansa ya furta shi yasa aka ‘d’auko ta don baya son a San ta haihu. Hankalinta ya kwanta ta ji bata da
wata damuwa tabbas hakan shine rufin asirinta…..
Duk inda tashin hankali yake to Familyn Lami’do suna cikinsa. Ba inda basu duba Amani ba sai dai ba ita
ba labarinta. Didi kam ciwo ya sake rikicewa, ga Umma D data saka su a gaba da tijara iri iri, tana furta
“Ashe citata aka so a yi, shi yasa aka dinga cusawa ‘dana ita, to yanzu kam Asiri ya tonu, ai na San za’a kai
ga haka, wannan dukiya ta Moddi ai abin a binciki hanyar da ya samu ne, ga abinda sangarcin da kuka
masa ya janyo, sannan ake tunanin na rufa masa asiri bayan Allah ya tona masa….” Didi ta dinga kallonta
tana tuno sanda ta haifeta da kanta a cikin d’aki, bada haka da sai ta ce canja mata Dijatu aka yi. Hawaye
take fitarwa cikin karyayyen harshenta ta furta “Dijatu, kika furta labarin nan ga kowa Allah ya isa ban
yafe Miki ba, d’anki dai Amani ba zata aure shi ba, ba shikkenan ba…” “Bas kuwa.” Fateemah ta furta
zuciyatta cike da jin haushin y’ar uwarta. Dijatu ta watsa mata wani kallo ta furta “Eh Mahmud ba zai
aureta ba, ke ki aura mata wani cikin y’ay’anki, kinibabbiya kawai.” Fateemah ta sauke wani murmushi
tana furta “In dai ni na haifi yara na kuwa kuma na isa da su zaki sha mamaki…” fa’da fa ya kaure a
tsakanin su. Moddi yana ji ya lumshe idonsa kawai ya yi shiru. Sai yamutsa sumar kansa yake zuciyarsa na
fitar da wani irin hucin turiri. Idan har ya ce zai bu’de bakinsa ya yi magana abinda zai fa’da ba zai zama
mai sauk’i ba, zai kuma iya yiwa Dijatu mugun duka idan ya bu’de idonsa ya ganta. Shi yasa ya rufe idon
ruf. Shi duk ba wannan ne a gabansa ba ina Amani ta shiga shine tambayar da yake wa kansa. Ina Alwan
ya kai ta. Furucin Didi shi ya togace Dijatu daga yama’di’di da zancen, sai dai an ce zancen duniya baya
b’uya don labari sai ya fara baza gari da ka’dan ka’dan.




★★★★




Ita ka’dai take juyi a saman gadon. Bayan shigar Dada toilet ya kuma gaya mata ta shirya zasu Paris.
“Duniya sabuwa!” Ta furta cikin wata irin murya mai nuna zallar farin cikin da take ciki. Komai yazo mata
a sauk’i burinta ya cika. Amani ta bi duniya. Dama yarinyar ce take togace ta da komai. Don ba k’aramin
shakkar yarinyar take ba. “Y’ar banza mai kafaffar zuciya, yau kema kin bi Uwarki…” ta furta tana sakin
dariya. Imaam kuma shi da aure har abada. Sai ta sake jin wani relief a zuciyarta. Fitowar Moddi ce yasa
ta ta yi shiru ta dawo cikin hankalinta ta dinga binsa da kallo tana son furta abinda ke k’asan ranta, ta
wani gefen tana shakkarsa. Mik’ewa ta yi ta isa wajensa tana karb’ar lotion ‘din da yake shafawa cikin
yaudara ta dinga Shafa masa. Murya a k’asa ta furta “Amma idan mun je, this time zaka
Amince naga Doctor Akan maganar rashin haihuwar nan…” D’auke kansa ya yi kafin ya furta “No
need…” da sauri ta kalleshi cikin harzik’a ta furta “Wai me yasa Moddi? Me yasa duk sanda na maka
magana akan matsalar rashin haihuwarta sai ka ce wani No need? So kake sai na wuce haihuwar? Ya
‘d’ago ya kalli cikin idanunta. Sai Ya saki murmushi yana furta “Ba zaki tab’a haihuwa ba…” Da sauri ta
saki lotion ‘din a k’asa jikinta na rawa ta furta “Saboda me?” Ya lumshe idonsa yana fusgar lips ‘d’insa ya
furta “Saboda na bada mahaifarki Safna, na bayar da mahaifarki a lokacin da kika umarce ni komai su
Alwan suke so na amince ciki har da ran Uwata, y’an uwana, da yara na, sai abin yazo min da sauk’i don
basu nemi komai ba sai mahaifarki ni kuma take na basu, saboda kince ana yin komai saboda ku’di…..”
Ya fa’da yana ‘dage mata gira guda. Wani irin tashin hankali ta shiga, tashin hankalin da har ganinta ya
‘d’auke na wuncin gadi, ga wani irin zufa da take zubarwa zuciyarta sai fisga take. Bata San sanda ta
cakumo Moddi ba tana furta “Muguntar da ka min kenan?” Ya ‘dan waro ido yana furta “Na miki ko kika
ma kanki? Ku’di kike so kuma kin samu, ina da ku’din da har ki Mutu ba zaki gama cin su ba. Kwanciyar
hankali dai kika saka muka rasa…. Don’t blame, blame yourself…” ya fisge rigarsa ya fice ya bar mata
masifaffen k’amshin turarensa “6;00 pm… jirginmu zai tashi.” Ya furta yana rufo d’akin da k’arfin gaske.
Buguwar k’ofar ya yi daidai da sake buguwar zuciyarta da k’arfin gaske bata San sanda ta dafe zuciyar ba
tana sakin kuka. Me take shirin ji? Abinda Moddi ya yi mata kenan, tana ta sak’ar yarda zata samu
haihuwa sai yazo mata da wannan banzan zancen, har tunani ta fara yi ko cikin k’arya zata k’irk’ira ta siyo
jariri a asibiti, Ashe shi ya Riga ya siyar da mahaifarta ba zata tab’a ganin gudan jininta ba har abada!




★★★




Amani ta samu nutsuwa sosai ta daina fargabar komai, don ba taga alamar cutarwa daga ahalin gidan ba.
Ta sake wani irin kyau saboda komai aka kawo mata tana ci tana gyara jikinta da kayan gyaran jiki da suke
zube a toilet ‘din. Fatarta ta sake fresh kuma Alwan kullum yana tafe wajen ta yana kula da ita sosai. Kyau
fa kam iya kyau ta yi sha ga na ciki ga na zama waje ‘daya. Akwai abubuwa da yawa da idan suka bata
kawai sha take ba tare da ta tambayesu na menene ba. Kyau kuma ta sake yinsa sosai. Boss ce dai bata
tab’a ganinta ba don an sanar da ita bata gari tana Paris. Yau ma tana zaune Sadiya mai kula da ita ta
shigo. Waya a kunnenta tana sakin dariya k’asa-k’asa ta furta “Ma’am ga ajiyarki, tana nan lafiya sai ma
kyau da ta k’ara…” ta sakawa Amani wayar a kunnenta. Sannan ta juya ta fita daga d’akin. Amani ta yi
shiru bata ce komai ba a cikin wayar kamar yarda Boss itama ta yi shirun… sai can Amanin ta ji ta saki
ajiyar zuciya tana furta “Ama… tana kan line?” Aman ta ‘d’an cije bakinta tana jin Voice ‘din matar ya cika
kunnenta muryar y’an gayu sosai. “Kina ji na?” A hankali Amani ta furta “Yes Ma’am.” Matar ta saki dariya
tana furta “Ke ma Ma’am ‘din zaki kira ni? Whatever dai ki shirya gobe za’a kawo ki waje na. Zamu ga juna
gobe, hope Baby na ya lafiya?” Amani ta saka hannu ta Shafa cikinta, sai dai bata ce komai ba. “Ki shirya
Sosai Sadiya zata baki kaya masu kyau ki saka, don gobe zaki San dalilin da yasa nake bibiyar cikin ki, zaki
ha’du da mutane ki yi shiga mai kyau, bana son Gardama…” Amani haka kawai ta ji gabanta ya fa’di kafin
ta yi wani furuci an katse kiran. Tabi wayar da kallo tana kallon rututun Numbers ‘D’in da aka kira da su.
Da alama Boss ba y’ar Nigeria ba ce don muryarta bata mata Kama data y’an Nigeria ba. Karyayyiyar
Hausa take, mai caku’de da wani irin English mai da’din saurare. Sai ta ajiye wayar tana sakin ajiyar
zuciya. Turo k’ofa aka yi Sadiya ta shigo fuskarta still da murmushi ta ce mata “Akwai Wanda suka zo zasu
miki predicare da manicure, zaku ma a Miki gyaran gashi…” Amani kallonta kawai yake kafin ta furta “Ina
son ganin uncle.” Sadiya ta San wa take cewa Uncle don haka ta ce “Baya k’asar, zasu dawo da Ma’am
gobe, saboda suna da taro….” Amani ta bita da kallo kawai har masu gyaran jikin suka shigo. Cikin
babban toilet ‘din akwai komai da suke buk’ata wasu kuma Sun zo da su don haka suka fara aikinsu kawai.
Sai ga Amani ta fito ta sake wani masifaffen kyau. Duk da cikinta watanninsa biyar Amma bai fito ba, ya
dai ‘dan tasa ka’dan. Jikinta ya yi wani irin soft and silk kamar na jarirai. Bin su take kawai da kallo kawai
don Boss zata da ita taro sai an mata wannan irin gyara kamar wacce bata wanka…




Kashegari kuwa da wani irin fa’duwar gaba ta tashi. Don haka har yamma tana na’de a gado. Sai da aka ce
ga mai shirya ta tazo sannan ta mik’e. Ta yi wanka aka kuma shirya ta cikin rantsatstsen Hkg lace. Aka
mata Light make up. Sannan around 5:30 Sadiya ta ce ta fito su je, motocin da zasu kai su airport sun zo.
A airport taga Uncle Alwan Amma bata ga Boss ba. Don haka da sauri ta isa wajenta sai Ya mata alamar
da su tafi cikin jirgi kawai. Haka ta saka k’afa ta bi shi sai a sannan ta San a Abuja suke zasu tafi Kano… ta
dinga Jin dama Alwan ya kaita gidansu sai dai bata da halin tambaya.




Babban hall d’in Event D’in ya cika mak’il da manyan mutane. Haka kawai Amani ta dinga jinta
Uncomfortable don haka ta cafki hannun Sadiya da take kusa da ita ta damk’e. Tana kallon yarda
mutanen wajen suka sha kwalliya, ba Wanda ta sani a wajen, banda Sadiya da Uncle Alwan. Sai ta dinga
Jin fargabarta tana k’aruwa ta yi saurin jan mayafinta rufe fuskarta. Bata San da shigowar Boss ‘d’in ba, ta
dai ji ki’dan Band ‘din ya canja sai kuma Mc ya dinga kwararaton shigowar mai girma shugabar taro. Ta
‘d’an bu’de idonta tana kallon Hamshak’iyar matar mai masifar kyau da ita… suka ha’da ido matar ta
sakar mata murmushi tana zama a wajen da aka tanada don zamanta. Aka cigaba da gudanar da taron
yarda ya kamata kafin Boss ta amshi mic D’in. Cikin muryarta mai bayyana ajinta ta furta “Mak’usidin
wannan taron don ku taya ni murnar ha’duwa da gudan Jini na a yau da nayi bayan d’aukar tsawan
shekaru ina gujewa ha’duwar mu. A yau nake son nunawa jama’a ita tare da sanar da su auren ta da aka
‘d’aura da Uban rik’onta Imaam Moddibo…. Ta fa’da tana nuna Moddi da Safna da suka shigo a lokacin
bayansu y’an Uwan Moddi ne da Didi da Imaan. Boss ta sake furta “Thank you Moddibo come and meet
your Wife Amani Moddibo………




Anan Book 1 ya k’are don samun cigaban book 2 a biya 500 kacal cikin account 2118666253 UBA aji na
musamman 1k.




HADARIN GABAS….. yanzu aka fara zubar ruwansa kuma yana gaba. Shin wani irin zama za’a yi tsakanin
Moddin Didi da Amanin Dada? Wacece Boss shin ko dai y’ar riga ce take raye? Idan kuma y’ar rigar ce da

😀
gaske kenan da cikin su Amani ta je gidan Dada? Wai ya abin yake ne? Don samun amsa ku siyi Book 2
Wanda zai sauka a telegram




JIKAR NASHE ✍🏽


Ina jinjina ga BRIGHT PENS..




Nimcyluv



Ayshacool
Zee kumurya 🙏

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment