You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bak’i ciki fiye da Wanda kika sa min a cikin kwanakin nan zan mayar da rayuwarki
miserable…” daga haka ta juya ta fice cikin mutuwar jiki. Imani ta dinga kallon Amani a firgice ganin wata
irin da Amanin take hankalinta kwance kafin ta furta “Before ta yi making life d’ina miserable ni na mayar
da tata, matsafaciya kawai….” Juyota Iman ta yi a fusace tana furta “Ba zaki daina shiga sabgar matar
nan ba ko? Ba zaki fita hanyarta ba ko? Sai ta cutar da rayuwarki?” Amani ta dafa hannunta tana
murmushi ta furta “Wait and See, ba abinda zai faru sai alheri, In sha Allah sai naga bayan matar
nan….na tsaneta Imani, kuma ko yanzu na San burina daf yake da cika.”



Daga haka ta saka kai ta fice daga d’akin. Tana jin zuciyatta fresh kamar ba wata tarin matsala a tare da
ita.




Babban Parlorn Didin taf yake da mutane. Wa’danda suka zo taya ta murna. Yau bakin Didi Sam ya k’i
rufuwa don a yau ne zata saka a kai ku’din auren Moddi. Auren da take ji idan ya yi shi dukkan
matsalolinsa da nasu za su kau. Tana kallon k’aninta Kawu Jauro ta furta “Duka a kai har ku’din har lefen
idan ta kama a basu Har sadakin bana son auren nan ya wuce sati biyu Jauro, ka gaya musu bama
buk’atar komai sai matar kawai.” Jauro ya ‘d’aga kai cike da gamsuwa. Amani kuwa gabanta ne kawai yake
fa’duwa haka kawai jin wai auren Dada za’a je nema. A da kam ta fi kowa son Dada ya yi auren Amma yau
sai taji wani abu ya dunk’ule mata a k’irji jin abinda Didi take cewa. Hakan yasa ta sulale daga cikin
mutane ta shige d’akinsu na sashen Didin tana shiga ta danno k’ofa. Zuciyarta na bugawa ta lumshe ido
tana jan Innalillahi a ranta don idan har ba mafarki take ba, ji take kamar kishin Dadan take, kishi mai
zafin gaske mai dagargaza zuciya da saka zafi a cikin zuciyar…. Ta runtse idonta tana furta “Ya Allah! Me
yasa ne?” Ta fa’da tana kwanciya saman gadon.
Iman kuwa farin ciki ne ya sakata neman idanuwan Amanin don su yi farin cikin tare ko ta hanyar kallon
juna ne, sai dai bata ga Amanin ba. Don haka ta mik’e zuwa cikin gida don neman Amanin a daidai
Sitroom da Dahda yake zama da bak’i. Ta fara juyo sautin muryarsa kamar waya yake, kamar kuma
magana yake da wani a kusa da shi… “Wannan karan fa na shirya da gaske nake zan aikata abinda kuke
so, zan cika muku burinku zan kusanceta……” Nimfashin Iman ne ya kusa d’aukewa tsabar tashin hankali
bata San sanda ta yi baya ba, don idan Har zuciyarta ta fassara abin daidai Furucin Dada yana nufin zai
kusanci Amani don cikar wani burinsa, Wanda ta tabbatar bakomai ba ne, sai SON DUNIYA…….



(wannan littafin book one ne free, book 2 and 3 paid ne. A biya 500 cikin wannan asusun 2118666253
UBA. Don cigaba da jin labarin Moddin Didi, da Amanin da Dahda. Wa ke da nasara tsakanin Amani da
Safna. Book 1 daf yake da k’arewa.)




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS……👌


28.




NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️

08033748387.



BRIGHT PENS SECOND BATCH…
A gigice ta ja da baya da sauri, don bata son Dahdan ya ganta. Sai dai aikin gama ya riga Ya gama, don
tuni idanunsu suka ha’de da juna. Ta Ware ido tana toshe bakinta da k’ok’arin ha’diye kukan da yake son
taho mata. Sai dai ina bata da juriyar rik’e wannan kukan tuni hawayen ya kufce ya dinga zuba daga
idanunta… Mik’ewa Dahdan ya yi don isa wajenta da son ya yi mata bayani, sai dai ko kafin ya kai k’ofa ta
fice da sauri, bata son ganinsa ba kuma ta son jin ko wane kalami daga bakinsa. Ta ji komai ta kuma
amince Dadan matsafi ne, da gaske tsafi yake yi shi yasa duka abubuwan suke faruwa. Ashe hauka take
da take d’orawa Mommy Alhajin komai. Dahdan ne mai laifi shi ya yi silar afkawar Amani cikin wannan
halin. Ta mayar da k’ofar ta rufe Har da murza key sannan ta jingina da k’ofar wani irin kuka da bata tab’a
irinsa ba a rayuwarta ta shiga yi. Da dukkan k’arfinta take buga k’ofar da kanta tana furzar da wani irin
huci mai zafi. Daga k’asan ranta take jin wani irin zafi zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ta da ruwan zafi.
Gangar jikinta idan banda tsiyayar da gumi ba abinda take yi. Duk da tarin sanyin A.cn da yake d’akin jin
ta take kamar tana cikin Oven, tsabar zafin da take ji na tashin hankalin da take ciki. Ta zube a gado
idanunta akan hoton mahaifiyarsu, kallon hoton ta yi kafin ta fisgo shi da k’arfinta ta shiga magana da shi
kamar wacce take cikin hoton tana jinta. “Me yasa? Me yasa Mahmeey kika Mutu kika bar mu? Me yasa
baki tafi da mu ba, kika barmu a wannan duniyar mai cike da maciya Amana da burin duniya? Mun
fuskanci k’alubale da dama kafin mu tashi mu kai yanzu, sai gashi a yanzu muna fuskantar k’alubalen da
yafi Wanda muke ciki, mahaifinmu Mahmeey, Dahdah yana shirin kusantar Amani y’ar cikinsa don Son
Duniya…” Sai ta sakè fashewa da kuka da k’arfin gaske, ta rungume hoton y’ar riga a jikinta. Ta da’de
zube a wajen cikin fitar hayyaci kamar wacce ta zare, burinta mutuwa a loakcin burinta ha’duwa da
mahmeey a can inda ba zata sake ganin Dahda ba, ba zata sake ha’duwa da duk wani k’alubale mai shirin
tarwatsa mata zuciya ba. Tana so ta Mutu sosai kamar yarda Amani take burin mutuwar itama. Bugun
k’ofar da ake yi ne yasa ta dawo cikin hayyacinta, sai kuma tabi k’ofar da kallo tana tunanin waye sai ta ji
muryar Amani tana kiran sunanta. A kasalance ta mik’e ta bu’de mata k’ofar. Idanu suka zubawa juna
gaba d’ayansu kowa yana jin wani irin ciwo a ransa, ganin halin da d’an uwansa yake ciki. Iman ta finciko
Amanin ta mayar da k’ofar ta rufe ta rungume ta da k’arfin gaske, a tare suka saki kuka sautin bugun
zuciyarsu yana k’aruwa. Jikin Amanin zafi zau da alama mugun zazzab’i ne ya kamata. Iman ta ja
hannunta zuwa bakin gadon ta zaunar da ita kafin ta mik’e cikin First aid box da yake gefen gadonsu ta
bu’de ta Ciro pain reliever ta d’auko table water ta dawo inda Amanin take. A baki ta zuba mata maganin
Amanin tana b’ata fuska ta sha maganin. Kafin ta zube a saman gado. Iman D’in ma kwanciya ta yi daf da
ita tana sakin ajiyar zuciya ta furta “Matsalar mu daga yau In sha Allah ta kau Ama.” Amanin ta ‘d’ago
tana kallonta da neman k’arin bayani. Iman ta d’aga mata kai “Dole zamu bar gidan nan a daren yau….”
Amanin ta zaro ido kafin ta lumshe su sai kuma ta ciji leb’enta bata ce komai ba. “Zamu wuce wajen
dangin Mahmeey, Har sai komai ya lafa, ina tsoron afkuwar wani abu da naji shi da kunne na yau, da
wani ne ya gaya min ba zan tab’a yarda ba…” Amanin bata bu’de idonta ba. Zuciyarta ce kawai take
bugawa da wata irin k’aunar Dahda mai zafin gaske… tana kallo Iman ta shiga ha’da musu abinda zasu
buk’ata. Har ta gama bata ce komai ba, tana jin abinda Iman ‘D’in ta yanke shine mai kyau…
Dahda kuwa tun bayan fitar Imani sai kawai ya lumshe ido Ya jingina da kujera yana jin kansa yana matsa
da wani irin ciwo. A hankali yake taune lips d’insa. Daidai lokacin Amanin ta shigo kamar an jehota a
firgice duk ta yi wani irin. Kallonta yake da mamakin yanayin da take kamar wata Mara lafiya. Zama ta yi a
gefen kujerar da yake kawai sai ta samu kanta da saka kuka. Bai ce mata komai ba har ta gama kukan da
ya tabbatar shine zai saka ta samu sauk’in ra’da’din da take ji a zuciyarta. Ta ‘d’ago a fisge ta sauke ganinta
a kansa kafin ta furta “Dahdah da gaske kai ka haife ni?” Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai dai bai janye
idonsa daga kanta ba, ya furta “Kina tantama ne?” Ta cije leb’enta da k’arfin gaske kafin a fusace ta ce
“Ina tantama, idan Uban da ya kawo y’arsa duniya zai aikata abinda ka aikata, idan kuwa kai ka haife ni ka
cuce ni ka cuci kanka Dahda, ka gaya min me yasa ka aikata min haka, kuma waye Uba na don ban yarda

Kai ne ka haife ni ba…” Bai mata magana ba, Ya cigaba da kallonta yana fusgar leb’ensa kafin ya mik’e
tsaye. Wata drawer taga Ya bu’de ya zaro wani enveloped. Ya cilla mata a hankali ya furta “Your
answer…” Ya koma ya zauna yana furta “Komai kika gani jiya ke kika jawowa kan ki, shi yasa idan mutum
ya ce abinsa sirri ne baya son a gani, yana da kyau ka janye hankalinka daga kansa, Saboda baka San me
zaka je ka gani ba, yanzu da kika ga abinda ba a so ki gani ‘d’in ga situation d’in da kika jefa kanki nan, so
are you happy?” Daga haka ya koma ya zauna yana cigaba da kallonta, da kallon yarda hannunta yake
rawa wajen bu’de enveloped D’in. Hoto ne da wasu takardu. Hoton jarirai ne guda biyu rungume a
hannunsa yana nunawa Mahmeeynsu gefe guda kuma Didi ce da Umma T. Fara’ar fuskarsu ta kasa b’uya.
Y’ar riga murmushi kawai take idanunta akan jariran da y’ar k’walla a gefen idon nata. Ta San hoton don
haka ba bak’o bane a wajenta. Takardar ta tsirawa ido tana kallon sunan mahaifiyarsu a jiki da ranar da
aka haifesu. Sai kawai ta lumshe ido hawayenta na cigaba da sauka. Dahdah shiru ya yi yana jin wani
rauni a zuciyarsa, yarda yake jin zafin zubar hawayenta daidai yake da d’igar dalma a jikinsa. “Enough
Ama….” Ya furta cikin wata irin silent voice da take fita da wani irin magana’disu da yasa dole Amani ta
bu’de idanunta ta zube su a kansa… d’aga mata kai ya yi kafin Ya saka handky ‘D’in hannunsa yana share
mata hawaye. Zuciyarta ce ta dinga bugu madadin samun sauk’i a ranta sai ta dinga jin wani irin yanayi. A
firgice ta farka daga mafarkinta ta kuma ture hannun Dadan kafin ta mik’e da sauri, ta yi hanyar fita daga
sashen nasa, sam bata ganin gabanta…




Ya da’de zaune a wajen bayan ya janye idonsa daga kallon Amanin da ta fice a firgice. Ya sauke ajiyar
zuciya yana murzar goshinsa. Yarda yake murza goshin ji yake kamar yana tafiya ne da tarin damuwarsa.
Wani irin sanyi ya dinga bin sassan jikinsa. Nauyin da zuciyarsa ya yi ya dinga sauk’ak’e. A hankali yake
sauke ajiyar zuciya. Da gaske ya samu hanyar warwarar matsalarsa… Amma ta yaya? Ta Yaya zai amsa
tarin tambayoyin da ya hango a idon Imaan da Amani….. a hankali ya mik’e yana zagaye d’akin ya san
Imaan ta ji shi a wayar da yake magana, a idonta ya hango jin firgicin maganarsa, sai dai bata tsaya ba,
bata tsaya ya yi mata bayani ba, duk da shi kansa bai San kalar bayanin da zai mata Har kwanyarta ta
‘dauka ba. Don haka shirun shine yafi gwara ya ja bakinsa ya yi shiru kawai. Ya san shi mai laifi ne a wajen
yaransa, laifin da yake tunanin ba abinda zai goge shi, a idonsu yake hango tsanarsa lokaci guda kuma a
idon nasu dai yake hango tarin k’aunarsa, da tausayinsa. Da gaske shi abin tausayi ne, Safna ta mayar da
rayuwarsa akan irin tafarkin da take so, Ya amince ta yi winning a kansa…..




Cikin sanyin jiki ya koma sashen Didi. Rarraba ido yake a cikin tarin y’an uwansa ko zai hango y’ay’ansa.
Sai dai Babu su ba alamarsu. Ba wanda ya lura da halin da yake ciki. Don murna da zakwa’din aurensa da
suke yi. Ya d’an tab’e baki kafin ya zauna a daf Didin. Da jarumta sosai a muryarsa don son ya kawar da
yanayin damuwar da yake ciki ya yi magana. “Kun cika gidan nan da hayaniya, and kun sani bana son
hayaniya why all the noises don Allah ku tattara ku tafi, I need privacy ina son magana da Didi….”
Dukkansu da suke wajen sai da zuciyarsu ta buga. Basa son komai zai gayawa Didin ya ce Ya fasa auren,
zuciyar Didi ba zata d’auka ba zai raunata mata zuciya. Ba tun yau ake nema

Masa aure yake fasawa ba. Didi ma kallonsa take tata zuciyar tafi ta yaran nata bugawa bata manta wani
lokaci data nema masa auren ba, a ranar auren bayan an d’aura ya gudu bayan ya yiwa matar saki guda.
Don haka ta dinga kallonsa, kallon da Har sai da Ya saka ya yi k’asa da kansa, a hankali ya furta “Ba zan
fasa ba Didi, ba abinda kike tunani bane.” Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin wani murmushi ya bayyana a
fuskarta. Da gaske ta San wannan karan Moddi ba zai watsa mata k’asa a ido ba.. hankalinta ya kwanta, ta
dinga kallon su Fateema da suke tattara kayansu da na yaransu suna mata sallama. Idonsa a lumshe yake,
sam hankalinsa baya kansu yana can wata duniya da Ya yi zurfi a cikin tunaninta… sai da Fateemah ta
dafa shi ta ‘d’an yi magana da k’arfi a kunnensa. “Kiddo mun tafi, saura kuma ka je ka gayawa Safna
k’anwar Didi zaka yi aure..” Bai bu’de idon ba, balle ya bata amsa, alamun y’an miskilancin na kusa, idan
yaso haka yake sai ya cije ya k’i magana musamman idan zuciyarsa bata cikin sukunin yin

Maganar. Shafa gefen kumatunsa ta yi, sai kuma ta

Ja hancinsa tana furta “To Uban miskilanci, saduwar alheri.” Ya d’an murmusa kawai ba tare da ya bu’de
idonsa ba. Ya furta “Akwai sak’o a account d’inki, share it with Your sister’s” Ta k’asan ido yake kallonsu
duk suna ficewa…




Har ta kai k’ofa ta tuna bata yi sallama da su Amani ba. Sai kawai ta dawo zuwa ‘dakinsu na b’angaren
Didin. Jin kamar suna magana k’asa k’asa yasa ta tsaya ta lab’e tana jin su. Iman ta ce “Sha biyu na dare za
mu gudu, idan yaso ko garin su Mahmeey sai mu je.” Fateemah ta waro ido, kafin ta tura k’ofar ta shiga
da sauri suka ‘d’ago suna kallonta sai kuma suka sunkuyar da kai. Akwatin gaban Imaan ta kalla sai kuma
ta kallesu d’aya bayan d’aya gabanta na fa’duwa ta furta “Guduwa za ku yi?” K’asa suka yi da kansu. Jikin
Fateemahn a sanyaye ta zauna daf da su. Nasiha ta dinga musu da alk’awarin ba abinda zai faru In sha
Allah. “Moddi ba mahaukaci bane, na San ko giyar wake ya sha ba zai aikata muku komai ba.” Imaan tana
hawaye ta labarta mata komai. Wani irin waro ido ta yi a gigice ta mik’e ta koma parlorn Didin, da wani
irin duba take kallon Moddi Kfin ta furta “Imaam kana cikin hankalinka kuwa? Didi kin san abinda yake
shirin aikatawa?” Da sauri Ya kalleta a idanunta Ya hango da gaske abinda duk ta sani zata gayawa Didi, Ya
runtse idonsa kawai…..



Free pages Saura few pages fa! Ku hanzarta samba’do ku’dinku. 2118666253 UBA




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…..👌
29.




NAZEEFAH SABO NASHE



08033748387.




BRIGHT PENS SECOND BATCH



Idanu ya sake warewa ganin Fateemah har ta fice daga parlorn ba tare da ya san me suke tattaunawa ba.
Ya sake lumshe idonsa ganin Didin kawai ta zuba masa ido, sai yaga kuma ta mik’e ta nufi d’akin da su
Amanin suke. Tura k’ofar ta yi jikinta a sanyaye ta zuba musu ido. Su ‘‘d’in ma kallonta suke. Ta zauna a
gefen gadon tana kallon akwatinansu sai ta saki murmushi kawai, murmushin da su Amani suka ‘dauka
na mamakin abinda zasu aikata ne. “Za ku gudu saboda Didi ta Gaza a wajen baku kulawa ko? Za ku gudu
saboda k’una tunanin zan iya bari a cutar da ku ko ni na cutar da ku ko?” Sai ta girgiza kai ta furta “In dai
ina raye ku saka a ranku ba abinda zan bari ya cutar da ku, ina son ku ina tausayin maraicinku.. ku k’ara
min lokaci komai yazo k’arshe, na san kuna da matsala Fatima ta gaya min komai, ina kuma kan bincike
akan abin duk Wanda yake da saka hannu a ciki Allah zai yi maganinsa. Komai yazo k’arshe Moddibo zai yi
aure jibi, da matar da nake tunanin ita zata zame masa alheri a rayuwarsa, matar da zata so ku taso mu ta
kuma sake dunk’ule zumuncinku waje ‘daya.” Farin ciki ya cika zuciyarsu gaba d’aya suna jin a ransu
kamar da gaske duk wata matsalarsu ta zo k’arshe. “Kada ku k’ullaci Babanku, bashi da laifi ko ka’dan son
zuciya ne ya shigo cikin lamarin… ku yi hak’uri kun ji.” A wannan gab’ar dai Imaan ta jita kawai ba don ta
yarda da abinda ta ce ba, saboda da kunnuwanta ta ji abinda Dadan yake fa’da a waya. Sai kawai ta ja
ajiyar numfashi ta sauke tana kallon idon Didin da itama ta zuba mata ido, tana son ta gayawa Didin
komai sai dai bata San ta inda zata fara ba, maganar ta girmi kwanyarta. Didi ta shafe kansu ta sake fita.
Iman kallon Amani take da idonta suke lunshe sai kawai ta samu kanta da Shafa gefen fuskarta Amanin ta
Ware ido tana kallonta a hankali ta furta “Menene?” Amanin ta girgiza kai kafin ta furta “Bakomai.” Duk
da akwai komai ‘din wani irin zafi take ji a zuciyarta Wanda ta tabbatar na Kishin Dada ne, sai dai tana
fatan aurensa ya zama silar yayewar matsalarta.




Haka aka dinga shirin biki gadan gadan ba tare da Sun bari Safna ta sani ba. Sai dai a ranar ta fahimci
abinda ake shirin aikatawa don da tashin hankalin da take ciki yasa bata Saka ido a kan mutanen gidan
ba, mafita kawai take nema. Mafitar da zata wargaza kwanciyar hankalin zuri’ar Lami’do ta saka musu
firgici da b’acin ran da ba zasu tab’a mantawa da shi ba. A zaune take gefen gado hannunta rik’e da robar
rubutu ta tsurawa rubutun ido tana d’an murmushi k’asa k’asa. A hankali ta furta “Da gaske komai yazo
k’arshe kamar yarda Malam ya ce..” Sai kawai ta saki wata irin mahaukaciyar dariya… daidai lokacin
wayarta ta dinga ringing ido ta zubawa wayar tana jin wani irin matsananciyar fa’duwar gaba. Hannu na
rawa ta saka ta ‘d’au wayar ganin sunan Alwan da ya bayyana b’aro-b’aro a screen ‘D’in wayar. Tsinkewar
gabar da ta samu kanta a ciki ne yasa bata San wayar ma Upside down ta rik’e ta ba. Sai da ta ji muryar
Alwan yana furta “Kin kasa cika mana aikinmu, ga Mijin da kike so kamar ki Mutu yau ya miki Kishiya, yau
an ‘d’aura auren Mijinki d……” wani irin waro ido ta yi tana jin wani irin zafi tun daga k’asan zuciyarta
Har gangar jikinta. A razane ta ce “What?” Alwan Ya saki murmushi yana furta “Da gaske ya yi aure,
mahaifiyarsa ta masa auren Sirri, idan kina son kuma ya rabu da matar sai kin aikata abinda muke so, ki
saka ya kusanci yarinyar can ko ba ya so, ki yi musu vedio kice idan har bai rabu da matar ba zaki tona
masa asiri zaki saki vedion kowa ya san waye shi?” Murmushi ta saki wata irin nutsuwa tana shigarta.
Tabbas wannan ce shawara dama ko ba’a yi haka ba tayi niyyar ta saka ta tilas ya kusanci Amani don ta
b’ata musu rai kamar yarda suka saka tata zuciyar ciwo. Alwan ya katse wayar ya barta da tata wayar a
hannu. Da k’yar ta zame wayar daga kunnenta. Ta tuna a yau tana da damar da Imaam zai kusanceta sai
ta saki jin da’di a ranta,don a yau ne zata yi amfani da maganin mak’ale mata da Malam ya bata. Ya kuma
tabbatar mata in dai Imam d’in ya kusanceta ba zai sake marmarin wata mace ba da sunan aure… “Zan
yi amfani da maganin amma sai na gama da wannna matsalar.” Ta furta kanta tsaye. Wanka ta shiga tana
jin ba wani b’acin rai tare da ita duk wani shiri ta gama shirya shi a zuciyarta.
Ta gama wankan sannan ta shirya ta shiga kitchen. Favorite dishes d’in Didi ta dafa a gidanta su Mama
Talatu suna tayata cike da mamakin sauyawarta, ko dai bata son abinda ake ba ne a gidan.” Mama Talatu
ta fa’da k’asa k’asa tana kallon Inna Laraba bayan Safnan ta shiga store da yake cikin kitchen ‘din. Suka yi
shiru ganin ta fito still fuskarta cike da walwala tana kallonsu ta umarcesu su kwashi abincin su biyota
parlorn Didi da su. Haka kuwa aka yi Didi sai gani ta yi suna jera abincin a babban Dinning area d’inta da
Yasha adon carpet mai taushin gaske da pillows manya. Don Moddi bai saka mata Dinnig table ba ya san
bata so sai ya saka mata wani table irin na k’asan nan sosai Mara tsaho. Cikin mamaki Didi take bin Safna
data zauna a gabanta da kallo. Murmushi Safnan ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta idonta yana tara
k’wallar da ta k’irk’iro ta k’arya. Murya a k’asa sosai ta shiga bawa Didin hak’uri “Don Allah Didi ki yafe
min, In sha Allah ba zan sake aikata abinda duk na aikata a baya ba, na yi nadama kuma ina neman
afuwarki data yaranki Har ma da Moddi da y’ay’ansa gaba d’aya.” Didi cike da mamaki take dubanta ita ba
yarinya bace ta San wannan tuban na Safna bana gaskiya ba ne, da wani abu a k’asan ranta ba mamaki
yaudara ce ko kuma ta ji labarin auren Moddi take son ruguza shi ta hanyar makirci. Sai kawai ta saki
murmushi itama in dai Makirci ne gidan ta tarar yaushe aka haifi Safnan su da aka haifa zamanin da
makirai ma suka fi yawa, ba yanzu ba da mutane basu da wayon iya makircin ba ma. Hannu ta saka ta
dafa kanta tana sakin murmushi ta furta “Ai haka ake so Safna, tashin hankalin ai bashi da rana, Allah ya
yafe mana gaba d’aya. Wannan abincin dai yau ba zai ciwu ba don duk muna azimin Alhamis.” Safna taji
zuciyarta ta wani irin bugawa duk ku’din da ta kashe cikin abincin na asirin data zuba a cikinsa Sun tashi a
banza kenan? Kai ina wallahi da sake. Sai ta saki murmushi tana furta “Ai ba zai yi komai ba zuwa yamma
sai a yi muku warming ‘d’insa ku sha ruwa da shi, amma shi Moddin ai baya azimi.” “Shima yau ya
‘dauka.” Didi ta furta tana k’ok’arin danne dariyar da take ranta. Ta k’yale Safna a zuwan za’a ci abincin da
daddare.



Daga wajen Didi ta nufi sashen Moddibo, zuciyarta duk ba da’di wani irin zafin Moddibo take ji. Wato ita
zai yaudara ai kuwa zai sha mamaki. A zaune yake laptop a gabansa. Kallo guda ya mata Ya ‘d’auke kai. Ita
kuwa sai da numfashinta yaso d’aukewa tsabar kyau da taga Moddi ya yi cikin black shirt da farin wando.
Gashin kansa ya sha gyara sosai. Ta k’arasa kusa da shi tana nazartar yanayin parlorn da yake a gyare
tsaf-tsaf As usual Moddi baya son k’azanta ta sani don haka komai nasa yake zama very neat. So take ya
kalleta sai dai tun kallo gudan da Ya mata bai sake ba yana ta aikin tapping computer. Sai da ta gyara
muryarta wajen son k’wato tunaninsa da sanyin muryarta ta da take tunanin ta siranta sannan ta furta
“Wajenka na zo Imaan, I need your concentration….” Bai kalleta ba ya furta “All ears….” Ranta ta ji ya
sosu ganin abinda yake mata, Wanda da bai isa ba, bai isa ta yi magana ya shareta ba. Amma sai ta cije ta
daure b’acin ranta ta furta “ka yi hak’uri na amsa duk laifi na ina rok’on yafiyarka please!” D’ago kansa ya
yi yana kallonta sai kawai ya ‘dan saki murmushin gefen lips ya ja bakinsa ya yi shiru. Cak ta mik’e ta isa
gefensa ta shiga jikinsa a hankali ta furta “Da gaske nake, na yi regretting all my wrongs kuma ba zan sake
ba In sha Allah…” cikin idanunta yake kallo yana mamakin jin kalaminta, anya kuwa ta San irin laifin da
yake shirin yi mata. Sai kawai ya kama hannunta ya sumbata ba tare da ya furta komai ba ya mik’e ha’de
da d’age laptops d’insa daga wajen. “Ga abinci a parlorn Didi na kawo muku…” “Azimi” ya furta cikin
husky voice d’insa sannan ya shige d’akinsa. Bakinta ta cije sai kuma ta saki murmushi “Zaka dawo daidai
ne Imaam, zan baka mamaki.” Komawa ta yi parlorn Didi ta zauna ta sake a cikin su har tana jan Imaan a
hirar don kam bata ga fuska wajen Amani ba. Imaan ‘din ta dinga amsa mata a ‘darare don tsoron Safnan
take ji kamar yarda take tsoron ranta. Ban da Allah ya kiyaye tana dagewa da addu’a da tuni ta sakata a
mummunar hanya bata San me yasa a yanzu ma Safnan ta janye makaman yak’inta ba.




K’arfe shidd ta k’irk’iri ciwon cikin k’arya bayan da ta tabbatar ta aikata abinda take so successfully… Ba
wanda ya kawo komai Didi ta ce su tafi asibiti da

Please Login or Register in order to submit comment