You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

AMANI
A
wajen da Mukhy ya bar ta ta ci kukan ta ta koshi, tana gayawa kan ta Mukhtar baya
ta tata yanzu tunda ya zo cikin gatan sa, ko dama can yaya lafiyar Kura? Dubi dai
irin lallashi da roko da bada kan ta data yi amma yayi funfurus! Itama kawai gara
ta koyawa zuciyar ta hakuri da shi ta yi zaman Ummami cikin gidan nan, tunda uwar
ta ce ko ba Mukhtar a tsakani, tunda in tace ta barwa sadakoki Mukhtar din, ita a
maida ta Katsina ba sauraron ta zaayi ba, ba kuma maida ta zaa yin ba, ta san ta
shigo gidannan kenan har abada ba saki ba yaji, sunan auren nan mutuka raba in ji
Ummami, zata koyawa kan ta juriya ta rabu da shi ya auro ko goma ne ta koma gefe ta
yi kallon su.
Tunda shi baya amsar tuban dan adam, baa kuskure a nemi gyarawa ya yarda ya
bada second chance, Allah da kan sa mai afuwa ne, kuma yana son bayin sa masu
afuwa, yana amsar tuban bayin sa idan sun yi repenting, sun tsarkake zukatan su
daga sake aikata wannan kuskure, then why not him?
Wanda shima ba sama yake da aikata kuskure ba, tunda ba maasumi bane ba kuma
Annabi b.
Ai bari kawai ta nuna masa har gobe tana nan a Tafisun ta, ajin ta bai tsinke
ba, halin ta na banza na girman kai da raina mutane da wulakanta su kawai ta bari.
Tana wannan sake-saken tana hadiyar zuciya sabida kukan data ci, daga bisani
ta wuce uwar dakin ta ta kwanta bisa gado, da tunanin Mukhy barcin wahala ya sure
ta a wajen.

Cikin barcin ta, tsabar yadda ta saka Mukhy a ran ta, da son ya lallashe ta
koda da kalaman fatar baki ne, amma ya saka kafa ya fice ya yi banza da kukan ta,
ba tare da ya ce ya fasa amsar sadakokin da aka yi masa tayi ba wadanda tunanin su
kadai neman haukatata yake.
Ta tsinci kan ta a duniyar mafarkin ta tare da MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU
cikin wani nauI na soyayyar auratayya mai shiga jiki da zuciya, tare da dan
Issouffou jikan Massaoudou Balaraben Diffa mai abun mamaki, ta gan su cikin
mafarkin Mukhtar yana sumbatar ta iya sumbata, yana juya ta duk ta yadda yake so,
daga hakan sai kawai ta ji ya dauke ta suna tafiya zuwa turakar sa, yana rada mata
cikin kunnuwan ta cewa.
Tafisu kin fi sauran mata a zuciya ta!.
Irin mafarkin da in dan adam yana yi baya so ko sauro ya cije shi ya farka.
Sai kawai Amani taji muryar Baba Sahura a cikin kwanyar ta.
Uwa Uwa, Uwa, ke wai lafiya kike barci haka a kasa, ko fadowa kika yi daga
gadon, da baki na faman motsi kamar kina cin tsutsa, ga hawaye kina faman yi, kuma
a bakin kofar daki kamar wata wadda uwa ta yi wa baki?
Sai lokacin ta ankara wai ashe duk wannan a mafarki ne, kenan ita tata soyayyar
bata zo da wasa ba, Mukhtar har a cikin mafarki neman zautata yake don ya ga ta
gama mika wuya ga soyayyar sa.
Ta mike zaune, bata san yaushe ta fado daga gadon har ta mirgina kofar daki ba,
ita dai ta gan su suna mirginawa a cikin korran ciyayi ita da Mukkhy, sannan ta
dubi Baba Sahura, ta tabbatar mafarki take hakan bai faru ba, Mukhtar tunda yasa
kafa ya fice bai dawo gidan bama, ta kama Babar ta Sahura ta rungume jikin ta na
kyarma, sai ta fashe da kuka, ta ce Baba Sahura wai kin ji sadaka zaa bashi? Sahura
ta ce,
Au! Shine kike neman haukata kan ki Uwa? Yo in dai a kan zancen sadaka ne Uban
ki ma ya auri mata yana saki sun fi goma, shi a kan me zaki hana shi cika alada?
Gaki ke ban ga alamar kina masa wani amfani ba sai shegen kaudi da rashin kunya da
kika fi kowacce mace iyawa.
**** **** ****

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment