You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo yanzu ya karbi Diffa.
A halin yanzu tana can hannun iyayen ta ana mata magani amma tace bazata dawo
gida na ba in dai Mukhtar na cikin sa.
Don haka a jiya na datse igiyar aure na da ita na aikawa mahaifin ta sarkin
Zinder. Diyar da muka haifa nida ita (Sayluba) na dade da aurar da ita a Tahoa,
tana da yaya basu fi uku ba itama ta gado rashin yawan haihuwa ta, sai kanwar ta
yar wajen Tarha (Saadiyya) itama tana aure a kasar Guinea kusa da Liberia ga
Amabasadan Nijar a Guinea.
Bayan Aisata ta haifi Mukhtar shiru shiru babu karin haihuwa a gida na, sai na
kara aure da Balqissa, wadda aka kawo min ita daga kasar Abidjan. Har yau itama
bata haihu ba, Mukhtar mai bakin baya ka hana ni samun ko yaya matan ne sabida
alhakin ka Ubangiji ya hana ni..
Ya karasa fadi cikin zolayar Mukhtar. Sai da kowa a wajen yayi dariya Ummami
ta ce kada ka damu MAI DIFFA! Ba da jimawa ba in sha Allah diyata Aminatu zata cika
maka gida da yaya. Jalan ta ce ni nafi so a kara mishi da sadakoki yadda yaran zasu
fi saurin taruwa dariya kowa yayi, amma banda Amani da Mukhtar, wadanda duk suka bi
suka daddaure fuska, kuma kowanne yaki yarda ya kalli inda dan uwan sa yake. A
zuciyar ta cewa take ta Allah ba taki ba Mamma.
Ga dukkan jin dadin ta sai Ummami tace in har ba ya zama (Mai) din Diffa ba
(Sarkin Diffa) babu mai bashi sa-daka a halin yanzu. Yanzun Maina ne kawai, ku bar
su su mori kurucciyar su don Allah.
Sai Amani ta hau addua a cikin ran ta;

Ya Allah kasa kada a taba baiwa Mukhtar sarautar gidan su, Allah ka kara nisan
kwanan mahaifin sa, yayi ta zama a muhallin sa na Mainan Diffa.
(Ta manta Sarki ya ce tun da ran sa zai baiwa Mukhtar kujerar sa).
Sarki yayi umarni da su Jalan su koma bangaren Ummami da zama har Amani. Gobe-
goben nan zaa saka tubulin ginin bangaren matar Maina.
Ya kuma ce a yau dinnan zai soma aika takardar gayyata zuwa ga sarakunan
jamhuriyyar Nijar, wato gayyatar bikin auren Maina da nadin sarautar sa ta (MAINAN
DIFFA).
**** ****** ******

MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU
(MAINAN DIFFA)
B
aka jin komai sai tashin bushe-bushen algaita da kade kaden ganguna irin na
masautar Diffa, a yau Asabar, wadda ta kasance ranar bikin auren Maina da nadin
sarautar sa.
Cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki har da Yayar shi gimbiya
Sayluba daga Tahoa, mai bi mata da yake tana Guinea, bata samu zuwa ba don tayi
nisa sosai, mahaifin ta ya aika mata kan ta zo ga dan uwan ta Maina ya dawo gida,
ta ce sai ta haihu zata zo daga baya, tana cikin watan aifuwa.
Tunda aka soma shagulgulan bikin nan wanda zaa kwashe kwana bakwai ana yi Amani
bata saka Mukhy a idon ta ba ko daga nesa, rabon ta da shi tun washegarin zuwan su
Diffa, wato ranar da suka gana da iyayen sa, yana can cikin sarakuna abokan Baban
sa da yayayen su saannin sa, wadanda iyayen ke kokarin kulla abota da zumunci mai
karfi tsakanin yayan nasu, kamar yadda nasu iyayen suka yi masu.
Ba iya masarautun Nijar kadai Sarki ya gayyato ba har daga bangarorin
masarautun Songhai, Mali, Gao, da Kanem-Bornu. Haka ya gayyato aminin sa Sarkin
Burkina-Faso, wuri yayi wuri, taro yayi taro sai Rakuma ake kayarwa ana gashewa ana
kyafewa. Abinci kuwa duk iya diban ka haka zaka gaji da diba ka bari.
Umami tasa an yi wa Amani kwalliya irin tasu, da kaya na shudin karen miski da
sarkokin zinare har a hancin ta, an dorata akan kujerar Mowar Diffa, wato kujerar
da Ummami take zama a kai koyaushe, abin gwanin ban shaawa, shagalin sai wanda ya
gani.
Kwana bakwai aka kwashe ana wadannan shagulgulan na ban mamakia Al-Imaraat Al-
Diffa, an nadawa Mukhtar rawanin sarautar jiran gadon mahaifin sa Mainan Diffa,
wato dan sarki mai jiran gado.
**** **** ****

MATAR MAINA

Kuma shikenan don ya zama Maina ganin sa ma ya zama jan aiki? Amani ta tambayi Baba
Sahura babu ko kunya, koda yake dama kunyar ta mata karanci ai, ranar da suka cika
sati biyu a Diffa bata sanya Mukhtar a idanun ta ba. Kai ko daga nesa bata hango
shi ba. Don ko yana son magana da Ummami baya shigowa sassan ta, don ma kada ya
hadu da Amani, can a turakar Mai Diffa suke haduwa da mahaifiyar tasa su yi duk
maganar da zasu yi.
Baba Sahura ta bantari farin goro sal, sannan ta fashe da wata shashashar
dariya, ta dubi Amani tana mamakin rashin kunyar ta, wai yau ta murje ido tana
cigiyar Mukhy a gicciye da idanu, ta ce,
ki na so ki gan shi fa kika ce? To kewar sa kike ko yaya abin yake? A dan
yimin bayani?
Baba Sahura bana son irin wannan rainin hankalin naki, daga magana sai kimin
wata fassara daban, na ga dai mutumin nan tare muka zo, kuma don shi muka zo, ai ya
kamata ya dinga zuwa ganin lafiyar mu, in bai zo don ni da ya raina ba ya zo saboda
ku da yake ganin girman ku
ni kike cewa na raina miki hankali? Wato har yanzu bazaki gyara halshen ki ga
na gaba ba ko? To lafiyar ku ke da wa? Aa Uwa, ki cire mu cikin lissafin ki da
rashin kunyar ki, mu kam ai muna gaisawa da shi a waya, bai banzatar da mu a kasar
sa ba, ko dazun nan ya kira Jalan, yace ko tana son wani abu, ta ce cukui take so
sabon yi, a kawo mata, kuma yasa an kawo shi faranti guda mai laushi.
Haushi ya kara turnike Amani, ita din dai ita kadai Mukhtar ya raina, kuma
baya son ganin ta ko jin yadda take rayuwa a garin su mai shegen zafi, ta tashi ta
bar mata wajen cikin kunan rai. Baba Sahura na kara kyakyatawa kyal-kyal-kyal don
ta gano damuwa sosai a tare da ita.
Tun daga ranar kuwa duk sanda Baba Sahura ta ga Amani ta yi tagumi sai ta fashe
da muguwar dariya.
Ummami kuwa, yanzu ta mayar da hankalin ta ne kacokam! Ga shirin tariyar diyar
ta Amani, shiri na musamman take yi wa Amani, shiri irin wanda ake yi wa yayan
sarakai in zasu dakin miji, masu yi mata gyaran jiki daga Maine-Saroa har su biyu
ta kirawo ta ce daga yau har sati daya su gyara amaryar Maina, gyara na musamman
fiye da wanda suke yi matai ta Ummamin, Sarki kuma ya saka ana ginin bangaren su a
gefen nasa, wani irin kasaitaccen gini shiyasa har zuwa lokacin basu tare ba.
Amani a daya daga dakunan sassan Ummami take zaune, an bata bayi mata masu kula
da komai nata har su biyar, amma in suka nemi yi mata wata hidima ma korar su take
yi saboda haushi, haushin kowa take ji, saboda Mukhy bai neme ta ba ko sau daya,
mai hali dai da baya fasa halin sa.
Sahura da Mamma ma dakin su guda, Sarki ya hana su komawa Katsina yace sai sun
raka Amani ta tare a dakin ta tukunna.
Ginin Maina zai dauki sati biyu ana yi don gini ake ba na wasa ba wanda duk
masarautar Diffa babu ginin da ya zanu, ya kuma zamanantu kamar sa.
Duk da rashin ta idon Amani sosai ta samu kan ta da jin kunyar Ummami, bata
sani ba ko sabida yadda take jan ta a jiki ne, ta ce kuma ita ya take da ita ba
suruka ba, don haka ba karamin tanadi take yi wa tariyar ta ba. Da nata, ya tata,
komai tuwon ta man ta, farin cikin hakan har ya so yayi mata yawa. Shi yasa take
yin komai da karsashi.
To amma yadda Mukhtar ya share Amani tun zuwan su, ko zancen ta bai kara yi ba
ya damu Mamma Jalan a kasan ran ta, bata dai nuna ba, don ta san yayi hakuri iya
hakuri da Amani, yanzun lokacin sa ne, amma bata fatan ya ce zai rama wulakancin
Amani gare shi, don ko babu komi yar uwar sa ce, ta san idan ma Amani ta ce tana
son sa yanzu, ai wata fassara zai yi mata daban, don hankali ba zai kama ba.
Don haka ta shiga rokon Allah a boye a kan ya daidaita tsakanin su ba tare da
sauran mutuncin Amani ya zube daga idanun Mukhtar ba.
Ita kuwa Ummami yawan sabgogin dake kan ta na mijin ta da bayi da tariyar Amani
yasa bata fahimci cewa Maina ko gaisawa baya yi da Amani ba. ba kuma ya zuwa inda
ya san a can take.
Allah kadai ya san me ke zuciyar Mukhy a kan Amani, don har zuciyar sa baya
mararin sake ganin ta, duk da cewa hes absolutey busy kuma busy din da yake ciki da
jamaa da iyaye da yan uwan sa ne ya hana shi zuwa inda suke, amma yana kiran Mamma
Jalan a waya akai akai, har Baba Sahura ma, kuma dai duk da hakan Amani tana nan a
like a ran sa, yana tuna ta a yawancin lokuta in ya kadaice domin kwanciya barci,
amma bai damu ya gan ta ko ya neme ta don ya gan ta ba, duk a kan kalaman ta na
Saliyo, da har zuwa lokacin ya kasa manta su, ya kasa yafe su, ya kasa share effect
din su daga ran sa, kuma in ya tuna suna masa maqaqi a rai, amma ba don wai ya dawo
cikin gatan sa da take masa gori bane ko don halayen ta da ya riga ya sani bane ya
sa bai neme ta ba.
Aka fara yima amarya Hamam Hallawa daga shi aka yi mata Dilka Gomage irin na
matan Diffa, washegari aka yi mata wankan madara da wankan lalle. Sai kunshi, wanda
ya zama shine na karshe a gyaran amarci da aka yi wa Amani a Diffa.
Yau da yamma da aka gama kunshin, aka cire ya kama radau, kamar ka sace kafar
da hannun ka gudu, mai gyaran jiki ta ce ta je ta yi wanka da ruwan turaren data
sirka mata a toilet din Ummami, sun gama gyaran yau kenan sai kuma na gobe in Allah
ya kai mu.
Mukhtar yana son ganin Ummami ya duba inda suka saba haduwa bai gan ta ba, dole
ya shig sassanta har addua yake Allah yasa kada ya hadu da Hajjajun nasa.
Mukhy ya shigo dakin Ummami ne don ya gaya mata zasu tafi Burkina Faso yau,
domin kai Daddy wajen wani mai maganin shanyewar barin jiki na gargajiya da Sarki
ya ce a kai shi. Bisa umarnin abokin sa sarkin Burkina Faso da ya tambaay ko akwai
masu irin wannan maganin na wannan lalurar ta shanyewar barin jiki a kasar shi
bayan na asibiti? Shi kuma yace tabbas akwai, kuma shi zai dauki nauyin maganin, da
duk masu raka Alhaji har sai ya samu lafiya. Don haka suka gama shirya tafiyar
Alhaji Usman da yan rakiyar sa karkashin jagorancin dan sa kuma surukin sa Maina
Mukhtar.
Da sallama ya shiga har kuryar dakin Ummami don bai gan ta a falon data fi zama
ba, sai hadimanta suna ta ayyuka a falon wajen tsaftace shi da turare shi, bayan an
gama kunshin amarya, ya duba duk inda zai gan ta har turakar Mai bata can, kuma
dole yana so yayi mata sallama saboda zasu kai sati biyu a Burkina Faso in sun tafi
gobe ana yi wa Daddy gashin kashi na gargajiya, don har Mamma Jalan zasu tafi, kuma
ya gay mata ta waya cewa ta shirya, don ta dinga kula da Alhajin sosai da daddare.
Bai ga Ummami a dakin ba, sai wani fitinannen kamshi da ya baibaye dakin ta
koina, can kuma sai ya jiyo karar ruwa a shaya, daga toilet din Ummamin, nan ya
gayawa kan sa Ummami tana wanka ne, don haka ya samu kujerar sofa kwalli daya dake
dakin barcin Ummami ya zauna yana jiran fitowar ta, hankalin sa bakidaya a kan
wayar sa da wannan kamshi da yake ji yana fitowa ta toilet ne ko ta falo ne dun sun
bi sun rikita gidan, da wani turare mai tada hankalin yan maza.
Zuwa can Mukhy yaji an bude kofar toilet din, sannan a hankali ta fito daure da
faffadan tawul, gashin ganta ya sha wanki don kitso zaa yarfa mata gobe, dagowar
nan da zai yi sai ga Hajiyar tasa ce tana fitowa daga wankan turare data shiga, ta
zama tamkar hurul-eenin larabawan Diffa. Mukhtar ya samu kan sa da fara tazbihi a
cikin ran sa da sauri da sauri. Gabadaya iskar dakin ta debi kamshin sihirtaccen
turaren da Ummami ta sa aka hada musamman saboda Amani, yau kwana bakwai da shi
take wanka, wanda Ummami tun daga TChad ta aika aka kawo mata shi, daga ita sai dan
faffadan towel wanda ko guiwar ta bai kai ba, tayi wani irin sumul ta yi jazur kai
har wata yar kyakkyawar kiba ya ga ta yi kamar ba Amanin da ya sani kamar a bushe
ta ta fadi ba don rashin kauri. Yo kam ta ci Dawisun Diffa ta koshi.
Da farko ita bata gan shi a dakin ba sam, har rausaya take tana rera wani baiti
cikin wakar mutuniyar ta wato Nancy Agram, da harshen larabci, a haka ta isa ga
mudubi domin ta sharce jikakakken gashin kan ta data wanke, nan ta hango Alhajin
nata zaune yana kare mata kallo, ta cikin mudubin ta hangoshi, sosai ta tsorata duk
ta firgice, don bata san da shi a dakin ba. Mukhy ya dan rikice da kama shi da tayi
yana mata kallon kurillah, duk ya zama wani upset don bai taba ganin real Amani
irin yadda ya gan ta yau ba, ita ma ta diririce don bata san tana da kunya ba sai
yau, tana kokarin komawa bandakin don suturta jikin ta ya daure fuska sosai ya ce
ke da Allah malaam! Tsaya, tambayar ki zan yi, ina Ummami? Ba wajen ki na zo ba
balle ki yi min yanga idon Mukhy na walainiyar da basu san suna yi ba a kan kirjin
ta wanda ya dago sosai kamar an an kara hura mata shi ya zama kamar balloon, sai
zagin idanun sa suke ta cikin kakkauran towel, da zara-zaran hannayen ta da suka
sha jan lalle da hallam hallawa, suka zamar da fatar ta tamkar na jaririya don
taushi, wadannan abubuwan guda biyu, gabadaya sun gama tada nutsuwar Mainan Diffa,
ya kasa dauke ido a kan ta tsayin lokaci, Amani ta juya don komawa toilet ba tare
da ta amsa masa ba. Mukhtar bai san lokacin da ya mike ya soma taku zuwa gaban
Amani ba, ya sha gaban ta yana cewa ba tambayar ki nake ba?
Nan da nan ta fara rawar jiki don dadin ganin sa da ta ji, ga kuma kunyar
yadda ya gan ta, sannan a gaban ta ya tsaya yana fadin, shin sai yaushe zaki yi
hankali ne ke? Ko gaisuwa ga miji har yau baki iya ba, gaida miji ma sai an ce ki
yi? Ni kam anya Alhaji ya san irin shashashar matar da ya bani?
Mukhy yana maganar nan cikin takaici mai yawa, muryar sa na canzawa cikin yar
inina, ta dalilin tasowar wani kwantaccen feelings daga kasan ran sa, duk kuwa da
cewa gashi korafi yake akan halin ta, ya yarda yana son Amani har gobe, duk da
pretending din nasa, amma baya son halayen ta ko kadan, don haka yanzu ma kokawa
yake da kan sa na kada ya sake kai hannun sa gare ta, komai zai faru da shi gara ya
faru amma ba zai kara sake mata ba.
Mukhtar ya kara taku ya tsaya a gaban Amani hannayen sa biyu cikin aljihun
Caftan din jikin sa, ya ce Hajjaju ina fatan zafin kasar mu ta talakawa bai saka ki
ciwo ba? Na san yayan Qaruna basa son zafi da rana da sauro. A yanzun yana maganar
ne fuskar shi dab, da nata, a fakaice yana sunsunar wannan sihirtaccen kamshin ne
dake neman bugar da shit un dazu, wanda yanzu ya gane daga jikin ta ya samo asali,
mai neman bugar da numfashin sa, ya rasa inda suka same shi. In bai manta ba irin
sa ne tayi amfani da shi a Saliyo ya kusa mutuwa a kan ta ba don kwanan sa yana
gaba ba.
Ta rasa me zata ce da shi, don kamar bakar magana ce ya gaya mata, shi kuwa
tsakanin sa da Allah ya san garin akwai zafi, akwai Sauron ma at times, tana rokon
Allah a ran ta yasa kada yau ma Mukhy ya tada zancen Shege! Har yayi abinda zai yi
bar dakin nan.
Zuwa wannan lokacin Mukhy ya kusan hade dan space din da ya saura tsakanin su,
ban da makyarkyata ba abunda Amani take yi daga tsaye. Yace cikin tsananin takaici
wai ashe ke kanwa ta ce duk wanan lokacin ban sani ba, na tsaya kika yi ta yi min
rashin kunya a banza a wofi, kina kunsa min bakin ciki kina cin bulus, kina tada
kai da bulus, to daga yanzu kika kara yi min rashin kunya ko hararar nan taki ta
raini, na rantse da mai samada mai kasa gwabje bakin ki zan yi sai jini ya fito ta
yi wani sunkuye da kai, sannan ta yi kasa da idanun ta bata ce komai ba, jikin
takanwa y agama yin laasar.
Mukhtar ya kara matsowa jikin ta don kamar wani magnet ya ji yana jan sa zuwa
gare ta, abinda bai tsara bane yake neman zuwa da kankanuwar murya ya ce ba zaki
koyi gaisuwa ba? Ya kara nacin fade, wannan karon cikin shakakkiyar murya, Amani
sai ta soma kokarin gocewa kusancin su, ta yi gaba zuwa wardrobe don ta saka kaya a
jikin ta, tana cewa cikin ran ta,
Allah yasa kai ne Sarkin kasar Nijar bakidaya, ba mai jiran gado ba, ba zan
gaishekan ba, tunda ta karfi ake saka gaisuwar, ayi mutum ba maganar arziki
tsakanin sa da wadda yake kira matar sa amma babu lallashi a bakin sa kullum. An yi
sati biyu ma baa hadu ba, yau an hadu tana mararin ganin sa amma ba maganar arziki,
ai kuwa bata isa ga wardrove din ba ta ji Mukhtar ya riko gefen tawul din, sai
ganin tawul din ta tayi a hannun sa ya rataya a wuyan sa, ta bude baki domin yin
ihu, yayi maza ya toshe bakin da hannun sa yana zaro manyan idon sa, ya ce,
baki da hankali zaki yi min ihu ki tara min mutane? Meye haka sai kace yanka
ki nayi? Zaki jawo a zaci wani abun nake miki? Daga kawai na zare tawul?
Amani ta rufe dukkan idanunta kamkam, cikin matsananciyar kunya da gigita,
tana ambaton Allah a ran ta, domin Mukhtar ya damke bakin da kyau da hannun daman
sa yadda bazata iya ihun da ta yi niyyar yi ba don Ummami ta kawo mata agaji. Shi
kuma rufe idon da ta yi sai ya bashi damar karewa kyakkyawar halittar matar ta shi
kallo, yana tazbihi a ran sa har ya fito fili.
Amani bata san yaya aka yi ba daga nan, don idanun ta suna rufe, gara mata
rufe idon da ta hada ido da shi cikin wannan situation din, ta san dai Mukhy ya
tallafe bayan ta ya hanata kai wa kasa daga nauyin jikin ta da da kafafun ta suka
gaza dauka, daga nan kuma sai saukar bakin shi ta ji a kasan dogon wuyan ta yana
sunsunar ta, kafin ya saki wani wahalallen kiss, a asan wuyan nata ba tare da shi
kan sa ya shirya ba, ya gangaro a hankali ya saka fuskar shi saman kirjin ta, bai
san lokacin da yayi hakan ba domin tun dazu yake kokawa da kan sa a kan yin hakan,
amma zuwa yanzu duk wata dauriya da duk wani azanci da ya san ya mallaka ya kwace
masa, jaruntaka da ego da pride din sun subuce masa, wannan yasa ya yarda hakan
wani miracle ne da Amani ke da shi a kan sa.
Wato duk irin fushin da yake da ita baya jin zai kasa kusanta kan shi da ita,
in har sun kebe.
Mukhy ya tafi da yawa, Hajiyar kuwa da ke guilty na damun ta yanzu bata yi wani
hobbasa na hanawa ba, ya manta cewa a dakin Ummami suke sai faman wannan smooth
lallausar fatar da taji wankan madara dana lalle yake yi, yana hadawa da sunsunar
ta kamar ba zai daina ba, sai dai kamar wancan karon, yanzun ma sai da kwakwalwar
sa ta tuna masa AMANI FASKARI ce fa! Sarkin rashin mutuncin duk duniya, har yanzu
bata yi hankalin da zai sake mata ba irin haka, balle yanzu da take matsayin kanwa
a gare, shi tana bukatar ya bar ta ta kara hankali har zuwa lokacin da zata kara
sanin ciwon kan ta afin ya soma irin wannan rayuwar da ita.
Mukhtar ya saki Amani ta hanyar komawa bisa sofa din da ya tashi, ya kama kan
sa da dukkan hannayen sa yana jin haushin kan sa, ya nutsa yatsun sa cikin tarin
sumar kan sa ya runtse idon sa, ya tuna abinda ta gaya masa ana I gobe zasu taho
nan, cewa tana regretting abunda ya shiga tsakanin su a Saliyo, me yasa yake bari
ajin sa ke barewa muddin ya kebanta da Amani? Me yasa yake kasa controlling
emotions din sa a kan ta, a irin wadannan lokutan???
Amsar da baya son samu daga kasan zuciyar sa dole ita ta soma pumping a cikin
kan sa, wato duk da halaye da dabiun Amani Usman Faskari marassa kyau da baya so,
wadanda a yawancin lokuta suke saka masa tsanar ta, ya fahimci duk da hakan still
yana matukar son ta da kaunar ta.
So kuma kwakkwara guda daya, mara algus, wanda ya san daga Allah ne ba don
Alhaji ba.
Shi kawai tun sanin sa da ita a gidan su yake da wani extra feeling a kan ta,
ko ganin ta yayi daga nesa sai gaban sa ya fadi duk da kasancewar ta maras tarbiyya
maras mutunta mutane. Idan kuwa ta matso kusa da shi, to kuwa sai ya ji hakan a
dukkan jikin sa.
Kunya ta sa Amani sanya doguwar rigar Ummami a baibai, wadda ta yayibo daga
wardrove din ta, tana jin wata irin kunyar Mukhy, wadda a baya bata da ita a kan
sa, tana zuwa tana baibaye ta. Da kyar Mukhtar ya samu ya koma daidai, ya mike yana
faman daure fuska kamar yadda ya saba, ya ce,
na tambaye ki kin min banza, nace wai ina Ummami na ta shiga ne?

A kokarin ta na son adopting kyawawan dabiu daga yanzu, wadanda ta fahimci
gaisuwa ga miji na cikin su a gidan sarautar Diffa, kamar yadda suka dauke ta a
matsayin kyakkyawar alada, sai ta yi kasa da murya duk da har zuwa lokacin jikin ta
bari yake yi, ta ce.
Yaya Mukhy ina wuni?
Bai amsa ba, don ko kyau ladabin bai mata ba, da yake bata saba ba, sai ma
cewa da yayi a dan tsawace. Nace ina Ummami?
Amma a kasan ran sa yana mamakin gaisuwar data yi masan, wadda ya ji ta kamar
daga sama, ko kuwa kamar wadda aka tursasa sai tayi, ta yi gaisuwar ne ta

Please Login or Register in order to submit comment