You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,
sai faman hade giran sama dana kasa yake yi yana Harare-harare. Ummami ta ce cikin
kwantar da murya.
Sadaka yana nufin kwarkwara (concubines).
A dan rikice Amani ta ce kwarkwara kuma Ummami? Me yasa aka bashi? Kwarkwara a
wannan zamanin? Shi din ne ya ce a bashi ko shi ya ce yana son su?
Amani ta jero tambayoyin cikin rudewa, rikicewa da da karkarwar murya, ba tare
da ta san lokacin da ta jero su din ba, tsakanin Mukhy da Ummami, sai ka rasa wa ta
jefawa tambayoyin, sai zare ido take a tsakanin su su biyun, tana jiran dayan su ya
bata amsa. Amma duk suka yi mata shiru. Tsabar rudewa ta ma manta da wacece Ummami
a gare ta. Haka ta kafawa Mukhtar ido cikin tuhuma da tashin hankali. Mukhtar sai
ya tashi zai fice daga dakin, yana mamakin dalilin gigicewar ta da rikicewar ta
haka don kawai an ce an bashi kwarkwara, ba dai zai ce Amani kishi take ba, saboda
ya sha jin ana cewa sai da SO mata ke kishin mazajen su. Shi kuwa ai baida wannan
gatan da wannan alfarmar a wajen Amina-Amani.
Ta soma harzuka, tana kokarin komawa Amani Faskarin ta da kowa ya sani wadda
bata barin ko ta kwana, ganin ta rasa mai bata amsa a cikin su. Gashi yana kokarin
ficewa daga dakin ba tare da ya bata amsa ba.
Ya Mukhy! Magana nake yi. Yaya zaka fita baka bani amsa ba? Kai kace a baka
sadakan, me na yi maka? Am I not enough?
Mukhy har ya kai bakin kofa zai fita, sai ya juyo ya dube ta da warning look a
idanun sa, wato ta san a gaban wa take, da irin maganar da zata furta, da alama ta
manta Ummami na wajen, ya ce cikin fushi.
Are questioning or accusing me? Na yi kama da saan wasan ki da zaki jefa min
query? To ban sani ba din, sai kin matse baki na zaki ji amsar tambayar taki.
Yayi tsaki ya fice ya bar musu dakin.

Rudewar da take ciki ya sa ta mancewa ko wacece Ummami gare ta, ta ce don Allah
Ummami shi ya roka? Ko shi ya ce muku yana son sadaka?
Ummami sai ta fito mata a mutum sak! Itama, ta dube ta ido cikin ido ta ce,
Amani! Kin ga na lura tun zuwan ku kallon juna kuke kamar ba aure ne a tsakanin ku
ba, alamu kuma sun nuna min tun a Nigeria ma haka kuke zaune, Mukhtar in ya je fada
Baban sa ya lura baya iya komai sai damuwa, in an yi Magana sai yace naam wato sai
an maimaita, shi kuma Mukhtar da kike gani, Yarima ne maana (Maina ne) Sarki mai
jiran gado, shine wanda ake fatan ya gaji mahaifin sa a komai, bazai yiwu a kyale
shi haka babu kulawar mata ba, ko da sadakan ne don samun nutsuwar sa.
Shi yasa muka ga gara a bashi sadakan ko ba yawa kafin ku daidaita kan ku, da
sabanin da ke tsakanin ku, ki sani Mukhtar Sarki ne, halittar su daban da ta sauran
maza da kika sani a kan mata, kusan in ce miki, duk yawancin sarakuna. A shekarun
Mukhtar yayi hakurin da ya zarce kima babu mace, gara kada a kure hakurin a bashi
karin wasu matan na hutawa, su kuma yi muku hidima ke da shi har zuwa ku daidaita.
Ko ita dakikiya ce zuwa yanzu ta fahimci me Ummami ke nufi yanzu, tunda dai ta
shiga aji, ba wai bata taba shiga aji ba.
Gata suke nufin zasu yi wa dan su, don sun gane bata bashi kulawar data dace
mace ta baiwa mijin ta na auratayya.
Kasa magana tayi, tayi kokarin rike hawayen ta bata bari sun zubo a gaban
Ummami ba, don kada a ga rashin juriyar ta da raunin ta, sannan ta mike ta koma
sassan su cikin sanyin jiki, sai Kuyangar ta mai kula da kitchen wato Ramu ce ta
biyo ta da wayar ta, don a can dakin Ummami ta manto ta tsabar ta shiga rudu mai
yawa, kuma Ummami bata sake bi ta kan ta ba, bayan bayanin da ta yi mata. Ta san ta
ahada mata bom yadda take so ya tashi.
Duk da sanyin AC mai karfi da ke aiki a falon ta. Amma Amani zufa take yi in
ta tuno zancen nan. Idanun ta ba abunda suke hararo mata sai kyawawan yammata
abzinawan usli tare da Mukhtar, cikin irin yanayin su da suka kasance jiya shi da
ita, wannan alamari ba karamin daga hankalin Tafisu ya yi ba.
Fisabilillah me yasa baa yi ma Mukhtar aure tun sanda ta tsane shi ba sai yanzu
da ta soma saka shi a ran ta, ta soma tsara musu rayuwa ta soyayya mai tsafta a
cikin zuciyar ta, kiris ya rage mata ta samu dama ta bayyana masa son da take masa?
Mafarkin ta na haifa ma Ummami da Mai Diffa jikoki daga Mukhy ita kadai ran ta, ya
tashi a banza Kenan muddin aka bashi wasu matan suka riga ta shiga jikin sa?
A hankali ta soma sheshekar kuka, bata san cewa Mukhy yana cikin dakin da ta
jingina da kofar sa ba. Sautin kukan ta ya dame shi, yana ci masa rai, don bilhaqqi
take yin sa, hakan ya fiddo Mukhy daga dakin barcin nasa, ya bude kofar saura kadan
ta fadi, don a jikin kofar ta jigina duka jikin ta, tunda ya baro su ita da Ummami
gidan sa ya dawo, ya kwanta a daki ya rufe kan sa yana tunanin karbar tayin
mahaifin sa ne ko aah?
Ita bata ma san yana ciki ba, ya zo kan ta cikin fushi dama kuma ran sa a bace
yake da abinda ta yi masa gaban Ummami mai kama da raini, cikin tsawa ya ce ke
lafiya zaki zo ki daga min hankali da kuka haka ina kokarin samun barci? Me aka yi
miki? Wani aka ce ya mutu? Koko rashin hankalin ki da kika saba?
Amani ta daga jikakkun idanun ta ta galla masa hararar nan tata da ta dade bata
yi masa irin ta ba. Sai yau da ji take gabadaya ta tsane shi bata ko son ganin shi
a idon ta. Sannan ta juya tana share hawayen ta don bata so ya kama ta tana kukan
nan ba, ko don tsira da sauran ajin ta, ta yi masa banza ta cigaba da share hawayen
ta da habar laffayar ta.
Ba gara mutuwa ba ta san kowanne mai rai mamaci ne. Wannan kuwa tashin hankali
ne na har abada ya same ta, in har ta bari ya faru, kishiya daga zuwan ta gidan
miji! Mijin ma Mukhy dan uwan ta da ta soma kallafawa a ran ta bada jimawa ba,
wanda bata kwatantashi da komai a yanzu, son sa take bilhaqqi.
Mukhtar ya sassauta murya ganin cewa fada da daure fuska bazasuyi tasiri a
gare ta ba, har ya samu ta gaya masa kukan me take yi, ya ce pls Amani! Na hadaki
da Allah ki yi shiru, ki gaya min abinda ya yi sanadin wannan kukan babu gaira babu
dalili.
Don sosai ta firgita shi, don kukan nata ba na wasa bane yau, ko na sakarci
irin wanda ta saba a yawancin lokuta, aah wannan kuka ne mai fita daga kasan
zuciyar matar da ke tsananin son mijin ta, kuma dare daya ya zo ba zato ya ce zai
mata kishiyoyi, kuka ne take yi bilhaqqi, baka da zuci, mai nuna tsananin kishin ta
akan abinda take so da zuciya daya.
A matukar fusace Amani ta dago, idanun ta sun yi jawur, hawaye ya hade da
majina ta ce ina rokon ka Allah Annabi ka bace min da gani Ya Mukhy, sabida bana
son ganin fuskar ka, ka tafi gun sadakan da ka je ka roka a baka sabida na gaza, ka
tambaye su kukan me nake yi, tunda kai baka da hakuri, baka da bin komai a sannu.
Son da na samu kaina da fara yi maka, ina rokon Allah ya sa ya koma inda ya fito,
kada Allah ya bar ni da koshin wahala.
Mukhtar ya hadiye mamakin sa da dariyar data zo masa nan take, sai yanzu ya
gane musabbabin kukan, wanda bai taba ganin Amani na yin mai zafi da cin ran sa ba,
ya ce.
Tafisu yau ni kike kira mara hakuri? Shin a duniya akwai miji mai hakuri ma
iri na? Ni da aka kira bawan Alhaji, mara galihu, mara nasaba kai har mai kama da
shegu an ce min kuma na yi hakuri na Manzon Allah, ban taba kallon ki da kalaman
bakin ki ba, sai matsayin diyar ubangida na mai daraja a idanu na. Ni tsintacce a
bola, ke komai ma na batanci da rashin galihu ni ne. To ki gayamin ya kike so in yi
idan ban karbi wadanda zasu so ni a yadda nake ba?
Ke da yake yar Qaruna ce kin ki yarda mu daidaita kan mu har yanzu, sabida baki
son yaron Alhaji, ni kuma iyaye na na na son ganin yaya na da wuri, Maimartaba kuma
na son gani na cikin nutsuwar data dace da kowanne dan gata.
Kullum in naje fada bani da nutsuwa in na ga babu yayan Mai ko daya bayan ni,
ina son samun yara wa iyaye na yara masu yawa, tun da su Allah bai basu yaya masu
yawa ba.
Ki fada min yanzu da lafiya ta da komai, an yi mana aure ya kusa rufa watanni
nawa amma har yanzu ban san irin nawa ba, Tafisu zina kike so in je in yi in ban
karbi kyautar sadakoki ba?
Ko kuma durkusa miki zan yi in roki alfaramr ki so ni, ki kuma bani hakki na?
Ai gara sa-dakan, ko ba su nake wa Son da nake yi miki ba, a kalla zan dinga rage
zafin da kike kunsa min dasu.
Amani ta zuba masa jikakkun idanun ta da ke zuba cikin tashin hankali, bata ko
kyaftawa, bata taba zaton Mukhtar zai iya wadannan maganganun ba, Mukhy mai kawaici
da kamewa. Mukhy ya kalle ta yana murmushin tura haushi, ya kara guma mata da cewa.
Kuma banda abun ki, banda shirme irin naki Sadaka ai ba matan aure bane na
hakika a wurin sarakuna, da zaki yi kishi da su, kada ki damu ababen hutawa ne ga
sarakuna kadai.
Amani na neman zaucewa yanzu ta ce au, bama daya bane har nawa ne ka roko? Yace
na roka ko aka bani kyauta? Su biyu ne kawai aka kawomin daga Sultanate of
Damagaram.
A wannan gabar Amani ta kusa dawowa tsohuwar Amanin ta yanzu, domin jijiyoyin
rashin kunya sun mimmike, tsigar jikin ta har tashi take, manyan idanun ta suka
firfito waje, ta ce.
Mukhtar! To kai din wane irin jarababbe ne da zaa kawo maka mata biyu a lokaci
daya? Plus me, three? Kwatakwata shekarun ka nawa?.
Mukhtar ya buda hannuwa irin na (ba matsalar ki bace) ya ce har goma in ina so
zan hada a lokaci guda, in kika bani dama ko yanzu sai ki ga irin jarabar tawa.
Ya soma tunkaro ta, idanuwan sa na nuna yau ba mai raba shi da Amani sai Allah
yana balle botirin wuya da links din hannun farar shaddar jikin shi, ta ce.
Allah ya suwake in hada miji da wasu, wallahi sai ka maida ni gidan Uba na,
kafin ka karbo su, ai ba kai kadai ne dan gata ba, nima nan da kake gani na TAFISU
ce har yanzu har gobe, bar ganin na yi sanyi, ina nan a Tafisu na da ka sani in aka
tabo ni.
In banda mugunta na taba cewa kada ka kusance ni? Ko kuwa ba kai kake dakatawa
don radin kan ka ba da son saka ni a damuwa Ya Mukhy? Za dai ka karba ne don ka
sanya ni a bacin rai, don ka ga na fara son ka Mukhtar ba don komai ba!
To idan so cuta ne to hakuri magani ne! na barwa sadakoki kai, ka maida ni inda
ka dauko ni gobe goben nan. Ta rushe da kuka, ta ce wallahi Katsina zan koma wajen
iyaye na, sai dai ka zaba ko ni ko sadakoki, ai da aka bar ni a nan ba wai an ce
gata na ya kare bane.
Mukhy, yau ji yayi kamar yayi juyi a gaban ta don dadi, murmushin da ke kan
fuskar sa sai karuwa yake, for the first time ya fahimci Amani ta fara son sa don
radin kan ta, ba abinda yafi dadi ga da namiji irin ya fahimci matar sa na tsananin
kishin sa irin haka, yau ga Tafisu na kukan kishi a kan sa kamar ta shide.
Niyyar sa da farko shine ya rungume ta, ya lallashe ta ya sumbace ta son ran sa
daga nan koma me zai faru ya faru yau, in yaso gobe yace a bar sadakokin baya so,
ya yi amfani da wannan damar ya gaya mata cewa son da yake mata mai yawa ne da ya
isa cike gurbin mata hudu! Ba wata mace da zai iya yi wa irin son da yake mata.
Amma ko me Mukhtar ya tuna? Sai ya fasa rungumeta din da yayi niyya ko ya
lallashe ta, ya sa kai zai wuce ta gaban ta ba tare da ya tsinka mata ba, amma a
ran sa yana mamaki yana karawa, wato duk shakiyanci ne abun nata, Amani ta san SO.
Yau wace irin ranar saa ce a gare shi?
Amani ganin zai tafi ya bar ta a wurin, wato bashi da lokacin sauraron ta, don
bai dauke ta mai cikakken hankali ba, bata san sanda ta sha gaban sa ba. Ba inda
zaka je Mukhy, na rantse sai ka zaba ko ni ko sa-dakoki.
Kai tsaye Mukhtar ya wani irin dago, ya zuba mata fusatattun idanun nan nasa
masu kama da an diga musu zaiba, ya ce bani hanya in wuce kafin in yi huce kan dami
a kan ki, me zaki iya idan na ce na zabi sadakokin, tunda zasu bani abinda Amani-
Tafisu bata bani, zasu so ni su kaunace ni, son da Amani-Tafisu bata yi min, zasu
so ni duk rashin asali na da rashin kowa nawa.
Amma Amani fa? Wadda kyawun Mukhy da ake fadi bai taba bugar da ita ta So shi
ba, saboda Mukhtar bai isa komai ba a idanun ta tunda ni hadimin gidan su ne! Amani
wadda da ta aure ni, ni da bani da asali, kuma ba dan kowa bane gara ta auri tsohon
mai kudi saan Baban ta Alhaji Sadisu Talle?
Ni kuwa me zai hana ni karbar sadaka, idan har ba maza na rako duniya ba kamar
yadda Tafisu ta rako mata? Kamar wani wani wanda bai san gatan iyaye ba irin wanda
Amani ke tutiya da shi a koda yaushe?
Kullum ki saka a ran ki a wurin Alhaji ne kadai kike amsa sunan TAFISU, amma
baa wurin Mukhtar da sauran mutane ba, tun da ni ban yarda Amani ta fi sauran mata
komai ba sai iya sai rashin kunya da rashin daa, duk halin banza shi ta fi su
iyawa!.
Maganganun sa sun ratsa ta, domin ta fahimci ya fidda tsatsar duka maganganun
ta ne dake kwance a ran sa, duk tsayin lokacin data yi masa su, tana fatan tunda ya
furta su yanzu, bayan ta jima da gasa masa su, daga yau ya samu sanyin su daga ran
sa, ko ta samu su bar zuciyar sa gabadaya.

Ta sunkuyar da kai. Guilty conscience na aikin sa ta koina yana nunawa a fuskar
ta. Jikin ta duk yayi dan sanyi musamman da ta ji a jikin ta Mukhy ya kafe ta da
kyawawan idanun sa, yana karantar reactions din nata, amma Amani-Amani ce har gobe,
sai in baka tabo ta ba, masu iya Magana suka ce. A bar hali a ci me? to hakan yake
ga Amani yau ma.
Domin kuwa share tasirin maganganun sa ta yi gefe ko ince ta hadiye tasirin da
suka yi mata ta ce.
Tunda ban fi su ba, shine na hakura na bar musu Mukhtar din, tunda a duniyar
ka mutum ba ya taba yin kuskure ya dawo ya tuba.
Ko mai yasa? Ita kan ta Amani bata sani ba. Amma ta san bata taba jin faduwa da
karaya sun same ta ba irin yau, duk da dai Mukhy yau cikin subutar baki yayi
gangancin gaya mata YANA SON TA, son da baya iya kwatanta shi dana kowacce mace.
Sai hawaye ya kara tsinkewa Amani, ji take gabadaya yau tata ta kare.
Ta samu kanta kawai da kifa kai a kirjin Mukhtar ta shiga sakin kuka wiwi, tana
rera shi cikin zaki muryar ta kamar sarewa.
Ba kasafai kukan Amani ke bashi tausayi ba, saboda ya riga ya san ita zuma ce
sai da wuta, ta hakan ne kawai zai iya rama kadan daga abinda ta dade tana yi masa,
hakika Amani ta dade tana cutar da shi da kalaman fatar bakin ta, yana shanyewa
yana hadiyewa albarkar mahaifin ta. Amma ganin irin karayar data same ta yau, ga ta
kuma kwance akan kirjin sa sai ya ji shima rauni ya shige shi, ya kuma san lallai
dagaske Amani ta canza, ko a ce ta fara canzawa, domin a irin zafin kan ta, babu
karaya ko kadan a tare da ita cikin tsarin ta. A ajandar halayen ta duka babu given
up, ba zai ce saboda sa-daka bane ta fara canzawa, ya dade yana karantar ta, ya san
tun kafin maganar sadaka ta samu canji a kan sa a zuciyar ta, haka ya san baka taba
kishin mijin da baka so har haka.
Zame ta yayi daga jikin sa cikin karfin hali, domin ta saka masa kasala ba yar
kadan ba, ya juya zai fita, cikin mutuwar jiki, ba tare da ya kara cewa komai ba.
Amani ta sake ruko shi da karfi, murya na karkarwa ta ce,
Mukhy! Will you believe me, if I said I LOVE YOU?
Sai ya juyo da dukkan idanun sa yana mata wani kallo, kamar na warning din ta
daina rike shi, amma kuma ya firgita da jin kalaman, domin sun zo masa a bazata, a
cikin idanun sa soyayya da kaunar ta ne tsantsa, haka nata jikakkun idanun abinda
ke kwance cikin su kenan, kallon da sukema juna ya shiga tado wata irin shaawar
juna ta shiga tarnaki a zukatan su, ta shiga ruruwa tun daga kwakwalen su har
yatsar kafafun su, in bai yi kuskure ba kamar yau ya taba jin sunan sa a bakin ta.
A yanayin da fuskar ta ta koma yanzu, kamar ta rasa duk wani gatan ta sai shi
kadai, a irin kallon data ke masa yanzu, kamar shi kadai ya rage mata a fadin
duniya, hawaye na zubar mata wasu na korar wasu ta zame daga jikin sa ta durkusa
masa, ta rike kafafun shi tanaci gaba da kukan sosai, tana rokon sa da murya mai
ban tausayi ya yi hakuri da duka halayen ta, daga yau ta yi alkawari ta daina!
Ya Mukhy, na yarda ka yi min komai don ka huce hali na na banza, na yarda hali
na da yawa mara kyau ne, na yarda zan canza daga Amanin da baka so, zuwa Aminar da
kake so, na yarda zan zama matar Maina Mukhtar daga daren yau, abokiyar rayuwar sa
ta har abada kuma abar hutawar sa karkashin inuwar aure.
Amma ka yi min rai! Banda kishiya ko sadaka, saboda bana son su, zuciyata baza
ta iya dauka ba Ya Mukhy. Saboda bazan iya sharing Mukhy dina da wasu matan ba.
Hakan zai iya manna min ciwon hauka da ciwon damuwa.
Ya Mukhy don Allah ka yi hakuri, ka yi min rai, kada ka karba!
Kaga ni tun fil azal ba Maina na aura ba Mukhtar na aura, ban san da wadannan
traditions din naku ba, na roke ka kada ka bari kokarin tabbatar da culture and
tradition na gidan ku da basu zama dole ba a addidni su rusa kyakkyawar dangantakar
mu, da rayuwar dana yi mana tanadi daga yau.
Amani ta russuna ta sumbaci babban yatsan kafar sa cikin roko, duk hawayen idon
ta ya koma diga akan kafar sa.
Zuwa yanzun kam hes touched, extremely touched! Kuma ya yarda abinda take fada
daga zuciyar ta yake fitowa, ba daga fatar bakin ta ba, mamakin hakan da birbishin
tausayin da so ke kimsa masa, suka taru suka soma rinjayar dakiyar sa da pretending
din sa, suka hana shi magana suka hana shi motsin kirki, ita kuma ta kai sumba
yatsan kafafun shi, Mukhtar yayi mutuwar tsaye, amma dai yana gargadin kan sa a
kan yayi taka-tsa-tsan da nadamar Amani don akwai gaggawa a cikin ta, kuma sadaka
da bata so ne sila, yaushe har Amani ta fara son sa irin haka, da har ta shirya
rayuwa da shi haka?
Komai aka ce masa mace zata iya, in dai a kan kada a yi mata kishiya ne yau
kam zai iya yarda.
Mukhtar ya san tsakanin sa da Ubangiji yana matukar son Amani, halayen ta da
dabiun ta ne dama baya so. Ganin ta tana neman shidewa a gaban sa yau a kan kishin
kada wasu matan su rabe shi ya yi matukar tasiri a tare da shi ba kadan ba, ya kara
masa son ta da jin tausayin ta, ya rage masa kuzarin muzanta mata.
Duk da haka wani devilish bangare na zuciyar sa bai yarda da ingancin nadamar
tata da soyayyar tata ba, ya fi dangana yanayin ta na yau da KISHI. Amma a irin
kukan da take yi rike da kafafun sa harda sumbata, sai ta soma saka masa rauni,
wato ta soma samun weakness din sa, sabida baya son ganin kukan mace balle matar sa
AMANI-AMANAR ALHAJI.
Domin ji yake sumbar da take ma yatsun sa na neman sumar da shi daga tsaye,
duk wasu tsofaffin feelings din sa a kan Amani na sake dawowa sabbi kar, suna sake
sakin sabuwar yabanya ta korran ganyayyaki a fadin zuciyar sa.
Yau Ga TAFISU a kwance a kan kafar sa, tana neman gafara da jin kan sa, daga
soyayyar sa da kin kishiya, a irin yanayin da yau ko me ya nema zai samu har
mafiyin sa, ba tare da ya yi hurting feeling din ta ba.
Amma duk da haka taurine rai irin nasa ya ki bari ya dago ta, yana gayawa kan
sa kada ya yarda ya bada kai yanzu, sai ya tabbatar da ingancin wannan nadamar tata
da canzawar tata, aka ce kowa ya tuba don wuya ba lada, duk da cewa a cikin idanun
ta ya ga nadama da soyayya tsantsa, sai dai ya san wasu mata ko basa son miji suna
kishin sa, tunda aure ne a tsakanin su.
Sai kawai ya janye kafafun sa daga rikon ta a hankali, cikin karfin hali ya
taka ya fice ya bar ta a falon, zuciyar sa kamar ta fashe da son Tafisu, da ke kara
tumbatsa a kowanne sako na cikin ta. Yana gayawa kan sa Amani Zuma ce sai da wuta,
gara ya kara rike shaawar sa a kan ta komai karfin ta, zuwa lokacin da ya dace da
ya amshi nadamar tata, amma ba yanzu da tsoron sadaka ne yafi rinjaye a ran ta ba,
ba soyayyar sa ba (a ganin sa).
**** **** ****



Please Login or Register in order to submit comment