You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta
hanaki ganewa tun can kin damu da Mukhy, kin damu da duk wani takun sa a rayuwa ta
hanyar yawan yin maganar sa with utmost hatred, and too much hatred so ne yake kawo
shi. Haka yawan yin zancen mutum.
Don haka yar uwa bamu makara ba zamu samo kan Yaya Mukhy din mu, ke dai ki
tabbatar kin canza din da gaske kuma da zuciya daya, ki kuma tabbatar masa da
canjin naki ta hanyar nagartattun halaye sababbi da zaki yafa yanzo, ki koyi
bayyana soyayyar dake zuciyar ki a gaban sa da ladabi da biyayya, Sahibah ki nuna
kulawa koda zai miki wata fassarar, to na dan lokaci ne, don na tabbata Mukhtar na
son ki.
Da sauri Amani ta damke wayar ta sosai a kunnen ta, hawayen farin cikin kalaman
Balewa ya tsirgo mata ta ce da gaske kike Hamida Mukhtar yana so na? Kuma zai
cigaba da son nawa bayan duk abubuwan batanci da tozarci da na yi masa? Zai cigaba
da son nawa bayan ya dawo cikin gatan sa, ba zai fassara ni da wata fassarar ta
daban ba? Hamida har ce masa na yi yana kama da.. Astagfirullah bana so in maimaita
don na koyi sakawa harshe na linzami.
Maganar ta yi wa Hamida gingiringin, amma ta san Amani neman wanda zai kwantar
mata da hankali ta a ke yanzu, shi yasa har ta neme ta, tana neman mai bata support
da assurance na cewa in ta gyara kurakuran ta zaa yafe mata, tunda ta ce ta koyi
sarrafa harshen ta ta hanyar yin furuci mai kyau ga kowa, ance matar na tuba bata
rasa miji.
Hamida tayi ajiyar zuciya. Sun tattauna extensively kuma heart to heart yadda
ya kamata aminai na kwarai su magantu, a kan wata masala data sha kan dayan su.
Hamida ta gaya mata cewa har abada Mukhtar ba zai guje ta ba, ta gaya mata dalilan
ta; inda tace bayan soyayya ta jini akwai soyayya gangariya a zuciyar sa a kan ta.
Sannan ta gaya mata wasu maganganu na sirri na yadda zata nunawa Mukhtar cewa da
gaske ta canza da zarar sun tare a gidan su.
Amani da Hamida yau sun raba dare suna tattaunawa kuma Hamida ta taya ta murnar
duk abubuwan da suka faru din. Kuma ta ce zata zo har dakin ta a Diffa watarana
idan Allah ya nufa.
Tun daga ranar dokin ta ga son dawowar Mukhy ya karu, har practicing/rehersing
yadda zata yi masa sannu da dawowa take yi, da irin kallon da zata ke masa mai nuna
kunya da ladabi ba irin na baya ba da take ware idanuwa ta zuba masa harara, yadda
dai Hamida ta gaya mata, ya zama duk dare da tunanin Mukhtar ta ke iya barci, ta
kuma gan shi cikin mafarkin ta, a yanayin da take kwadayin ganin nasu.
Ummami bata san hakan ba ita, domin ta koma fara yi wa dan ta yakin neman
soyayya, a fakaice (kamfen). Daga ranar data fara koyar da Amani karatu, in suka yi
karatun addini suka gaji don ko wajen Mai bata zuwa sosai yanzu kullum tana like da
Amani, don ta fahimci itama irin Mukhy ce ba soyayyar uwa ta tashi, gara ita ta
samu ta uban shi kuwa fa?
A kokarin ta na son kara cusa soyayyar tilon dan ta a zuciyar yar uwar sa kuma
matar sa, tunda ta ji yaa ce bata son sa duk da ta musanta hakan, sai ta ga bari
tayi amfani da damar wajen fayyacewa Aman tarihin Mukhy wataila hakan yasa ta
tausaya masa a matsayin ta na yar uwar sa, tausayi da fahimta ta sani suna tasiri
sosai wajen kimsa SO. Don haka rannan bayan sun gama karatu na addini da Karin
Alqurani da take mata kullum sai Ummami ta sako zancen Mukhtar.

Tace Aminatu kin san labarin mijin ki Maina?
Cikin jin yar kunyar gaske da ta fara samun muhalli a tare da Amani yanzu, ko
da yake in bata kunyar kowa tana kunyar Ummami, ta sunkuyar da kai, a lokacin tana
taje ma Ummami dogon gashin kan ta da furfura ta soma samun muhalli, Ummami ta ce
ta raba shi gida biyu ta yi mata tufka biyu ta gaji da shi a tsefe, mai kitson ta
ta yi tafiya. Amani ta ce.
Aah Ummami, ni dai kawai na tashi na gan shi karkashin kulawar Alhaji na, ban
san inda ya samo shi ba kuma ban taba tambayar Daddy ba don bama jituwa ni da Yaya
Mukhy ko kankani, shi baya son hali na nima bana son nasa, shi yasa kika ji yana
cewa wai bana son sa!.
Ta karasa fadi cikin karamar murya mai nuna kunyar idon uwa, amma gara ta gaya
mata gaskiya a kan ta ci gaba da rikon ta a ran ta a kan bata son Mukhy, ba uwar da
zata so a ce dan ta na auren macen da bata son sa sai dai ta yi kawaici, idan mai
kawaicin ce irin Ummami kenan.
Ummami ta gyada kai ta ce wato Amani, a duniyar Subhana ina tsananin tausayin
Mukhtar Amani, shi yasa nake so kema ki tausaya masa, ki bashi soyayya wadda ban
bashi ba, ki jiyar da shi dadin da mata hudu zasu jiyar da shi a lokaci daya, ki
kuma kula da shi da rayuwar sa yadda nake kokari akan mahaifin sa ba don bai da
wasu matan ba.
Ummami ta nisa, sannan ta cigaba da cewa kin ga yadda ya bar gida duk gatan shi
a shekarun balaga, a shekarun da ya dace a ce yana kusa da mahaifin sa a fadar sa
yana koyar da shi shaanin mulki, amma ya zabi ya tafi uwa duniya sabida rashin
samun kulawar iyaye. A hakan ma don baki san irin rayuwar da yayi tare da yayan
bayi, a kuma sassan bayi ba.
Idanun ta ya ciko da hawaye ta ce shi da ni sai dai leke daga nesa, ban taba
goya shi a baya na ba, duk hakan bai isa ba aka zo aka bi shi da mugun asiri wai
kurciya ya kara yin nesa da gida, kuma Baban sa bai damu ba ya cigaba da gudanar da
harkokin mulkin sa rai kwance hankali kwance.
A kan idanuna babu irin gatan da bai yi wa yan uwan sa mata Sayluba da Saadiyya
ba. Tun ba lokacin auren su ba. ya zaba musu mazaje na fita tsara ya kuma yi musu
auren gata.
Kema kin san kafin uwa ta jure wannan kin san akwai wuya, meye laifin Maina don
kawai ya zo a namiji? Amma haka na jure don farantawa miji na bisa raayin sa, ban
taba kalubalantar sa ba tunda aka ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba
zai hango ba.
Kullum jakadiya ta kawo min shi don in shayar da shi, nuna mata nake bana so,
in ta isheni da roko sai in karbe shi, amma kuryar daki nake tafiya da shi ina
shayar da shi ina kallon shi ina kuka. Ya kan kura min ido kamar yana tambaya ta
dalilin mu na yi masa haka.???
Ummami ta share hawayen da suka kawo a idon ta, itama Amani zuwa lokacin nata
idon ya ciko da kwallah, ta cigaba da cewa na san yana leken mu a shigifar sarki ko
wajen hutawar sa da yamma a yawancin lokuta, wanda ba komai ke kawo shi ba sai bond
din nan na soyayyar iyaye, wannan yasa na ke yawan zuwa wajen da Mai yake hutawar
yammaci, dan mu yi sallar laasar tare, in mun idar in yanke masa akaifa ko in taya
shi hira yana daga zaune bida karagar sa ina daga kasan kafafun sa cikin ladabi mai
yawa, ba don komai ba sai don in ya zo leken namu nima ina samun damar ganin sa a
sace.
Ranar da aka ce min ya gudu ni na san dalilin sa, na kuma yarda da hujjar sa,
tunda bamu taba zama da shi mun masa bayani, wanda zai gamsu da hujjar mu ba, don
haka duk abinda zuciyar sa ta gaya masa ko ta fassara masa a kan mu a wancan
lokacin a wurin sa shine dai dai. Suma na dinga yi ba tare da kowa ya san dalili
ba, ana zuba min ruwa ina farfadowa. Daga ranar kuma ban kara sallah na tashi ban
yi masa doguwar addua ba, kan cewa duk inda ya shiga Allah ya zama gatan sa, ya
kare mun shi da karewar sa da kiyayewar sa, ya kuma kula da shi. Domin na yarda
kulawar Ubangiji tafi tamu ta iyaye, kuma itace ta kawo Mukhtar yau inda yake.
Ya yi rashin duk wata soyayya ta iyaye a kuruciyar sa, ina jin damuwa idan na
tuna hakan. Da wannan nake rokon ki, a kan ki dubi girman Allah ki kula min da
Mukhtar kin ji AMINA! Ko da a kasan ran ki babu soyayyar.
Amani sai ta saka kukan data ke rikewa tun dazu a bakin ta, kuka mai sauti
sosai, ta rasa abinda zata ce da Ummami wanda zai sa ta gamsu ba ta kin Mukhy
yanzu, its true Mukhy had a traumatic childhood, and he deserve happiness a yanzu.
Matsalar ta da shi riko. Ya ki sakin ran sa da ita su mori auren da kuruciyar su
sai tsananin rikon ta da laifukan na baya da ya bari suka yiwa ran sa kaka-gida. Ko
yayi kokarin sakin ran sa da jikin sa da ita wani time din, rikon dake zuciyar sa
sai ya hana shi. Bayan rayuwar bakidayan ta sai ana ma juna afuwa, saboda rashin
tsayin ta da rashin tabbas din ta. Life is very short and transient. Amma ai Allah
ya san ta yi nadama, wadda ba lallai wanda ya santa a baya ya karba ba, zaa ce ne
don ta gan shi da gata ne a yanzu.
Don haka ta hadiye duk wani tunani a ran ta, nadamar ta da damuwar ta a kan
Mukhy bata iya ta cewa Ummami komai ba, sai sheshshekar kuka take tana hadawa da
ajiyar zuciya.
Ummami ta ce to yanzu meye abin kuka daga magana? Ni labara kawai na baki don
ki tausaya masa. Ba don in saka ki kuka ba. Koda yake Jalan ma haka take da saurin
kuka, da abinda ya isa a yiwa kuka da wanda bai isa ba duk abin kuka ne a wurin ta
tana karama, kin yi gado. Ni dai na baki amanar Mukhtar don dai gashi ya dawo gare
mu ne, amma rayuwar sa zata fi yawa tare da ke, ke ce silar duk wani farin ciki da
zai iya samu ko akasin sa, domin sai kin faranta masa daga gida ne zai fito cikin
jamaar sa cikin annashuwa, ya ji dadin tafiyar da alummar sa da mulkin gidan su da
tarin responsibilities din talakawa da ke kan sa, tun da dai kin ga shi Maina ne
wato (Mai jiran gado).
Da zata iya da ta gayawa Ummami cewa ta daina bata amanar MUKHY don Allah, don
ita Uwar sa ce kuma bata san halin sa ba, amma shi ma ai takadarin kan sa ne na
gani kashe ni, wanda baya bari ko da wasa a taka shi, ko a danne hakkin sa da ya
rataya a wuyan mutane. Sai ya kwaci abinsa ko ta karfi ne.
Kamar misali in tayi masa kwauron gaisuwa kasancewar shi mutum ne mai so a
bashi girman da ya cancanta, da son kowacce mace ta kasance da halaye da dabiu na
kwarai na girmama miji kwatankwacin irin na Ummamin sa, to fa ba zai hakura ba sai
ya nemi gaisuwar nan ko ta karfin tsiya ne da bakin sa, haka in tayi masa rashin
kunyar nata mai lasisi, Mukhy ramawa yake yi babu jinkiri babu bata lokaci, wani
lokacin da mai zafin da yafi nata zafi, wanda sai ta kwana tana hadidiye bakar
maganar sa.
Amma tayi relating da labarin da Ummami ta bata na kuruciyar Mukhy, sai ta ga
cewa ita kam, duk da babu Jalan, kuruciya ta gata da yanci kuma mai dadi ta yi, har
ma da jin dadin tafi kowa gatan uba, he really deserves happiness ko yaya ne a
rayuwar girman sa ta yanzu, kamar yadda mahaifiyar sa ta ce. Kuma ba daga kowa
wannan farin cikin zai fara samuwa gare shi ba sai daga cikin gidan sa, wato daga
hannun ita matar sa.
Can cikin kanta ta jiyo sassanyar muryar Ummami, kasancewar ta yi nisa a
tunani.
Kin min alkawarin kula da Mukhtar da bashi soyayya da farin ciki a rayuwar
girman sa AMINA? Ni kuma in kika yi min hakan, na yi miki alkawarin ba dai kiyi
kuka akan Da namiji ba, zan tabbatar na zame miki garkuwa a wurin sa, daga duk mai
son shiga gaban ki. Fata na kawai shine Mukhtar ya samu kwanciyar hankali a rayuwar
girman sa, wadda bai samu ko kadan a kuruciyar sa ba.
Ni da ke, babu hijabin surukuta ko yaya a tsakanin mu, sakamakon cewa ke din ya
ta ce ta halali, wadda ko babu Mukhy a tsakanin mu zamu kashe mu rufe tare, ba tare
da ko Jalan data yi nakudar ki ta ji ba. Hakika Allah Subhana na so na da kwanciyar
hankali a tsufa na, wanda ban samu a kuruciya ta ba cikin gidannan, shiyassa ya
bani ke wato ya sallado min ke a matsayin suruka ba tare da dabara ta ba, ke da
kika kasance ya ta halali a gare ni, bai yi min suruka da wata daga waje ba, wadda
zata sa Mukhtar ya sha wuya a hannun ta, don kawai yana son ta, shi yassa na bude
miki ciki na yau mu fahimci juna mu tallafawa juna ta hanyar bashi kulawa a farin
ciki ni da ke, ki sa a ran ki ni na haife ki ba Jalan ba.
Amani ta share yan kananan hawayen da suke ta tsatstsafo mata a kowanne furuci
na Ummami, wadanda ta san ba na komai bane na tausayin Mukhy da Mahaifiyar sa ne,
duk Ummami ta gama kasha mata jiki da kuzari. A hankali ta gyadawa Ummami kai, wato
ta yi wannan alkawarin, na kula da Mukhtar, da sanya shi farin ciki da bashi
soyayya.
Kuma har cikin ranta ta yi din, domin jikin ta yayi wani irin sanyi, ta yi
lakwas kamar jikaakken tsumma, jijiyoyin rashin kunya, na girman kai, na alfahari
dana dolonci suka shiga tssitstsinkewa suna farkewa da kan su, hankali da nutsuwa
har ma da tsoron Allah ya soma ratsa Amani a kusufa-kusufa daban-daban na
kwakwalwar ta.
Ta gamawa Ummami kitson cikin matsanancin mutuwar jiki, kuma dare ya yi, don
haka ta ce mata zata je ta kwanta, kan ta na sarawa sabida kukan data yi mai
tsanani.
Kuyangin ta da aka bata su suka raka ta har dakin barcin ta, don har zuwa
lokacin suna can suna jiran ta a inda suka saba zama su jira ta in ta zo gun
Ummami, da suka dawo bangaren ta daya daga cikinsu ta hada mata tea mai kamshin
nanaa bisa umarnin ta, ta sha a gefen gadon ta, sannan ta kawo mata Panadol ta
hadiya, suka yi mata duk abubuwan da suke yi mata kafin ta kwanta kamar kashe kayan
wuta, kunna A/C da kunna mata karatun Alqurani a radion bakin gadon ta cikin kiraar
Mahmoud Khalil bisa umarnin Ummami, na kullum su kunna mata in zata kwanta daga
kanan surori don ta kara iyawa da gyara karatun sallahr ta. Tahira da Sugra kenan,
wadanda su tafi sanyawa aiki da ja a jikin ta cikin hadiman nata guda biyar da
Sarki yasa aka bata tun zuwan ta, sauran biyun suna kula da girki da kitchen din ta
ne, daya kuma sharar bangaren ta da goge-goge da wankin toilets, ta zabi Sugra
daTahira su dinga zama a jikin ta ne don su ba yara bane kamar sauran ukun, suna da
hankali da nutsuwa, kuma suna da aure har da yara. Koina zata shiga cikin gidan
suna tare da ita.
Tahira da Sugra suna bada baya, bayan sun mata light off da sai da safe, sun
bar mata dim light shudiya, kukan ta cigaba da yi, mara sauti, da alama dai Amani
Faskari, most at times, finds pleasure and comfort in crying, tana yi tana yin
wannan kukan ne don tausayin Mukhy tana comparing rayuwar sa da nata. Sai ta ga
cewa, ratar gatan da ta samu da wanda ya samu mai tsananin girma da fadi ne. bama
zaa kwatanta ba. Da gaske kamar yadda Ummami tace ne Mukhtar yana bukatar kulawar
su su duka yanzu, amma ta yaya? Ta ina zata fara tata kulawar? Ko ta yi kokarin
hakan ba zai bata dama ba, saboda ya rike ta da yawa a ran sa.
Wata zuciyar ta ce da Amani Ai kema Amani mace ce, ko da ake cewa kin rako
mata! Ki yi tunanin hanyoyin dadadawa mutum, musamman mijin auren ka, ta yadda zai
ji dadi, ya manta da laifukan ka komai girman su, ya sakar maka fuska da zuciyar sa
gabadaya koda baya so, albarkacin kulawar ka gare shi. Tunda an ce zuciya na son
mai kyautata mata.
Sai ki hada da abubuwan da Balewa ta koyar da ke na kissa mai kyau ta waya, da
kuma naki yan dabarun da bazaki rasa ba, da wadanda Ummami ma ta koyar da ke na
tafiyar da Saraki.
Daddyn ta ya fado mata a rai shima zai iya taimakawa wajen sayo mata yardarm
Mukhy a yanzu, ta tuna tun tafiyar Daddy basu yi way aba sai ta dauko wayar ta, ta
kuwa same shi online a kan whtsp. Sai ta yi masa kira ta cikin whtsp call.
Yana dagawa ya ce Tafisu! Me kike yi har yanzu baki yi barci ba?
Amani ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce yanzu nake shiri ai Daddy, so nake
in tambaye ka yaya jikin ka? Kuma Yaya Mukhy yana lafiya?
Dadi mai yawa ya kama Alhaji, y ace na samu lafiya sosai Uwata, kuma ina iya
mikewa ma yanzu, Mukhtar sai dai in ce Allah ya saka shi a aljannah y araba shi da
iyayen shi lafiya, ko ke da na Haifa iyakar abinda zaki yi min kenan a rayuwa.
Uwa in har baki bi Mukhtar sau da kafa ba wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni
da ke, na hore ki da ki bi shi ki nemi aljannar ki babu ruwa na dake duk ranar da
Mukhtar ya kawo min karar ki.
Amani ta saki kukan da ke cin ran ta, ta ce Daddy! Kuna ta dora min abinda yafi
karfi na, bayan ba daga gareni bane matsalar yanzu, na riga na gane kuskure na,
shine dai ya ki ya yarda da ni ya kuma saki zuciyar sa da ni. Hakika na yi kuskure,
ina so na gyara in zai bani dama, ka roke shi ya karbi tuba na ya kuma bani damar
gyarawa. Na yi alkawarin canzawa daga yadda kowa ya sanni dinnan, amma hakan ba zai
yiwu ba sai ya yarda da ni.
Yardar miji kuma yardar Allah ba! In sha Allahu Mukhtar zai karbi tuban ki
musamman in kin ajiye girman kai. Nima kuma zan taimaka wajen ganar da shi halayen
ki ba laifin ki bane, nawa ne. Musamman a yanzu da muke da lokaci ni da shi kullum
muna tare barci kadai ke raba mu.
Ina rokon Allah yayi wa rayuwar ku albarka bakidayan ku, ya kuma albarkaci
auren ku da zuriar da zamu yi alfahari da ita mai yawa mai albarka.
Ta tambayi Maman ta yace ta yi barci tun dazu.
Sun dade suna hira irin tasu ta Tafisu da Daddyn ta.

Washegarin ranar, a darussan su na yau, ita da Ummami, har yadda uwargida ke
zama a gaban Sarki sai da Ummami ta koyawa Amani, da yanayin yin magana da Sarakuna
cikin kankan da harshe da tausasa furuci, da hadawa da kirari na kambamawa da nuna
soyayya.
Wani abun har sai Amani ta rufe ido don kunya. Da gaske Ummami ta janye hijabin
surukuta bakidayan sa. Tasaka na malunta.

***** ***** *****

BAKIN BURKINA FASO
R
anar da su Mukhy suka dawo Diffa daga Burkina Faso ana zabga wani irin ruwan sama
kamar da bakin kwarya har da kankara. Labari ya isko su cewa Maina ya dawo lafiya
tare da jamaar sa, suna fada wajen Mai Diffa.
Tsakanin Mukhtar da Alhaji bata san wa tafi dokin gani ba, don an ce da su
Alhaji na tafiya yanzu a kan kafafun sa. Wannan ya kusa saka ta shekawa da gudu don
ta cimma Daddy har fadar sarki.
Don haka ta roki Ummami Allah Annabi tana son zuwa masaukin su Alhaji. Ummami
tasa kuyangin ta wato Sugra da Tahira suka raka ta har inda aka sauki su Alhajin,
da gudu ta karasa shiga dakin tana kwarara kiran sunan Alhaji Daddy, Daddy na!
Alhajin kuwa ta fara yin tozali da shi yana tsaye a kan kafafun sa yana waya da
Matawalle da ke Katsina, da gudu Amani ta karasa ta rungume shi, tana kukan farin
ciki, da godiyar Allah. Mamma ce ta hau ta da fada tana cewa ta yi masa a hankali,
bashi da kwari, jiya ba yau bace, kuma da da yanzu ba daya bane a gareta ita kan
ta, ta daina wannan haukan da take yi a jikin Alhaji. Ita matar gida ce yanzu
Ta dube su duk sun murje sun yi gwanin kyau, tsufa duk ya bace, Alhaji yayi
kiba yayi haske, ta hau dariya ta ce ai kawai Mamma ki ce honeymoon kika tafi kai
Alhaji Burkina Faso ba jinya ba, wannan irin murjewa haka?
Jalan uwar saurin hannu nan da nan ta kai mata duka. Amani ta goce tana tana ta
dariya, Jalan na fadin na ga alama kin maida ni saar wasan ki, ni kike cewa na je
honeymoon? Alhaji ya kammala wayar da yake yi ya rufe yasa a aljihu, yace Ya ki nan
Uwa ta, kyale ta, sannan ya hau Jalan da fada, ni tunda nake ban taba ganin Uwa mai
saurin dukan Da irin ki ba, to in bata yi wasa da ke ba da wa zata yi? Yar guda
daya ita kenan Allah ya bani bazaki taya ni tattalin ta ba don ke kina da wasu ko?
Amani tayi dariya ta ce aah Daddy, daina mata fada haka, kada ta yi zuciya taki
yi min wasu kannen, biyu sun min kadan. Duk suka fashe da dariya har Mamman. Alhaji
ya ce ta tashi ta koma cikin gida haka, don mai Martaba ya ce masa an gama ginin
su, an saka komai, yau zaa kai ta bangaren ta kafin wucewar su gida Katsina. Su
kuma in sha Allahu gobe zasu wuce Nigeria.
Tuni jikin Amani ya mutu, yar farar data shigo da ita ta koma ciki, aure da
rabuwa da iyaye ba wasa bane ba kuma sauki gare shi ba, damuwa da kewa suka bayyana
a fuskar ta tun ma yanzu kenan, ta soma tunanin irin kewar su da zata yi tun basu
tafin ba, musammamn Alhaji.
Zata soma kukan tun kafin gobe ta yi, Ummami ta aiko jakadiya tayi kiran ta,
don haka ta rike hannun Daddy tana hawaye ta rufa tafukan sa a kan fuskar ta, ta ce
to yanzu Daddy ni da ku sai yaushe? Kai tsaye Alh. Usman yace sai kin haihu zamu
zo, in kin min aboki ko sabuwar amarya, ki sa himma shekara mai zuwa sai ki gan mu
gabadaya mun dawo radin suna, har Balewa zamu dauko miki da su Laure, da Kamilu.
Kunyar da bai san Amanin shi da ita ba ya gani ta zo ta lullube ta, harda kare
fuska da hannayen ta cikin jin kunyar Daddy yau.
Jakadiya da kuyangin ta suka maida Amani wajen Ummami, aka soma shirya ta don
wucewa nata bangaren, wanda ke can gefen dama na masarautar Diffa. Da ka wuce
sassan Sultan Issouffou Massaoudou.
An kawata ginin a zamanance, hakanan ya tafi da zubin sarautar Al Imaraat Al-
Diffa duk da haka. Daga ciki ne aka zuba abubuwa na zamani.
Bangaren Maina Mukhtar Bn

Please Login or Register in order to submit comment