You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanyar
kokarin danne girman kan ta, wanda har zuwa lokacin akwai burbushin sa tare da ita,
bai bar ta gabadaya ba, duk da ta yi wa kan ta alkawarin dainawa,
Ummami ta tai gun Mai ta bashi amsa murya na rawa da irin hausar gidan, bata
gun Mai shima ya bata amsa, to ina jin tana dakin Mammah. Karo na farko a rayuwar
su, da Amani ta yi masa Magana cikin kwanciyar jankali. Hakan yasa ya taso ya kara
matsowa inda ta ke cikin son tabbatar da canjin da aka samu a tare da ita, na gaske
ne ko gizo idon sa ke mata? Ya ce na zo in gay mata ne zamu yi tafiya Burkina-Faso,
zamu kai Alhaji wajen mai magani, ko zamu jima, ban sani ba.
Ga dukkan mamakin Mukhtar tashin hankali da tsantsar damuwa ne suka bayyana a
fuskar ta, ta ce har wata kasa? Amma ai Daddy is doing well a hakan da yake, not
like before, tunda yana motsa komai nasa tafiya ce kawai baya iyawa.
Mukhy, ya kara matsowa jikin Amani yana jin dan sanyi a ransa na canjawar ta,
ya ce,
Wa ya gaya miki tafiya ce kawai baya iyawa? Ai Mamma Jalan bata yi tsufan da
zata yi zaman zuba ruwa a buta da da daga ruwan wanka da kika zabar mata ba, kin
gane?
Kunya mai tsanani ta kama Amani ta harari Mukhy ba tare da ta sani ba, hararar
da ta kara kunna shi dama ba wai ya zama satisfied bane yana so ko yaya ya sumbaci
bakin nan nata na tsiwa kafin ya bar dakin, zuciya da ego da pride din sa na hana
shi, tasa kai zata wuce shi don bata son cigaba da tsayuwa tare da Mukhy, kafafun
ta rawa suke yi sakamakon kallon kurillar da yake bin ta da shi, sai Mukhtar ya
riko hannun ta tana kokarin wucewa ta gaban sa.
Na gaya miki zan yi tafiya, amma ba wani fatan alkhairi ba komai, me ya kamata
kice min ko ki bani? Allah ya kiyaye hanya kawai zan ce. Ni me nake da shi da zan
baka Yaya Mukhy? Ya ce abunda zai mantar da ni kalolin rashin kunyar ki, da kamanni
na da shegu. Ai Amani kamar jira take sai ta saka kuka tana cewa.
Allah ya gani ban san yaushe zaka bar maganar nan tabi ruwa ba Yaya Mukhtar,
wai shi dan adam ba zai taba yin subutar baki ya hadiye ya ce ya mayar da su inda
suka fito, a karbi tuban sa ba?
Yace in dai ke ce baki san tuba ba, tubanki shi ake kira tuban muzuru, baya
taba cika sharuddan tuba na addini, don ko bayan wannan din da kika fada a
Freetown, bayan mun dawo Katsina me kika ce min a dakin ki???
Wane cin mutuncin ne baki yi min ba ana I gobe zamu taho nan?
Ta gane ya koma neman rikici kuma, ya saki layin soyayyar da ke rinjayar sa da
farko, tana kokarin cewa ta tuba tabi alah ta bi shi ego din ta na rinjayar ta,
yana gaya mata kada Mukhtar ya ce don ta gan shi da matsayin sa na yanzu ne ta
bashi hakuri.
Don haka ta hadiye bada hakurin data so yi a cikin zuciyar ta. Amma hakika
Amani tayi nadama mai yawa, just bata san hanyoyin da zata bi ta yi expressing
hakan wa mijin ya gamsu ba, da kuma yadda zata yi repenting kura-kuran ta, amma ai
darasin rayuwa da karatun ta nutsu da duniya ta gama daukar sa ita kam! Da a ce
tana da wayewa a shaanin aure, da tuni ta saukewa Mukhy hadda, musamman da ya
kasance mai rauni wajen yawan son (body contact) da ita. To bata da wannan exposure
din sai na iya rashin kunya.
Cikin rikici irin nasa kuma ya sake riko ta, wannan karon bakin sa ya hade da
nata yana kissing, da wani irin zafin rai, kamar ta hakan ne zafin sheganta shi din
data yi zai fita daga zuciyar sa, shi kadai ya san irin pleasure din yake samu daga
irin wannan kiss din da yake yi wa bakin ta a karo na biyu kenan bayan wanda ya
faru a Saliyo, wanda yake jin zakin sa ya fi na zuma, gardin sa ya fi na madara.
Watakila kuma hakan ne kadai zai sa ya samu rangwame a zuciyar sa da gangar jikin
sa na tasirin soyayyar ta mai zafi da ke damun sa, da kuma jin zafin maganar ta ta
baya ta da yake yi akan maganar shege, yawan sumbatar ta na sakawa ya manta duk
wannan, wani sako na zuciyar sa ya yarda cewa Amani masifa ce a gare shi.
Eh masifa fa, tunda maganganun ta na Saliyo kadai sun isa su sa ya tsane ta, ya
shata babban layi a tsakanin su amma ina! Kullum sai in bai gan ta ba, yana iya
jurewa rashin ganin ta na wani lokaci amma da zarar ya ganta din shikkenan ya rasa
duk wani control na kan sa.
Ya cigaba da sakin zazzafan kiss din sa idanun sa a rufe, a kasan ran sa yana
rokon Allah ya canza masa Amani, (from evil to good, and from devilish to saint),
cikin wannna halin suka jiyo takun Ummami tana kokarin shigowa don suna jiyo
kirarin da bayin ta ke mata daga waje.
Da sauri Amani ta hankade Mukhy, ya ce ta baya ta rago bayan duk kin gama
tsotse mata Dan ta, na kan manta ke kanwata ce nake wannan aikin zubar da girman da
ke, in sha Allah ta yi kai, daga yau ba zan kara ba. Ya dauki wayar sa a kan sofa
ya nufi kofar fita, ya bar Amani da budadden bakin mamakin sa.
Mutum kamar mai iskokai, ya gama yamutsata yadda yake so har dakin uwar ta,
kuma ya bita da wannan maganar, wai itace ta tsotse shi, ta yi dan murmushi tana
cewa a ran ta Mukhy-Mukhy case ne shi wallahi, ko yaya ne dai, ni di kujera ce,
dole a zo inda nake a zauna a kai na, duk da gorin hali da ake yi min din!.
Yana saka kai zai fita daga dakin Ummami na shigowa, sun kusa karo, ya yi maza
ya ja baya ya bata hanya, ta ce to kai kana nan ashe, ana can ana ta neman ka, duk
sun fito kai suke jira zaku tafi airport Ummami ke na zo nema ni, bamu yi sallama
ba aah ka dai zo yin sallama da matar ka, to gani me zaka bani? Mukhy sai ya riko
hannun Ummami, ya sumbaci saman hannun nata ya ce wannan sallamar zamu yi. Kunya
irin na rashin sabo ya kama Ummami, amma ta yarda Mukhtar yayi rashin wannan
soyayyar tata, bata nadama, amma tana tausayawa faruwar hakan a tare da shi, yau
gashi ai Allah ya raya musu shi, ya zama magidanci cikin koshin lafiya.
Tabbas ka ki naka ne duniya ta so shi, amma mutanen duniyar ma ba kowadanne ne
irin Alhaji Usman Faskari ba. masu maida dan kowa nasu, kodayake shima din saar sa
aka ci don a baya halin mutanen duniya gare shi.
Da wannan tunanin take so itama ta kwatanta, wajen rike masa tilon yar sa da
amana duk da cewa itama yar ta ce. To Amani zata ci tudun alfarma har biyu kenan a
wurin su.
Ta dubi Amani dake ta sunkuye-sunkuyen kai, rashin gaskiya duk ya bayyana a
tare da ita, da kyar in Ummami bata ga abin da ta gani ba, ta ce,
ina fatan kun yi sallama, zasu wuce Burkina-Faso ne. Yace Ummami wace irin
sallama ce tsakanina da ita? Baki san Amani bata so na bane?
A firgice Amani ta dago ta kalle shi a tsorace, ya kuwa tsare ta da kyawawan
idanun sa ya ce ko zaki ce karya nayi miki? Ba auren dole Alhaji yayi miki ba? Ko
in gaya mata me kika ce da ni a Freetown gidan Faytoory?.
Idanun sa suka kada, suka kuma tsaya a kan ta, kamar yanzu ta fadi maganar,
ita dai ta shiga uku ta lalace da Mukhy a kan wannan maganar, mana daya ya ki yafe
ta. Amani ta hadiyi miyau da kyar, ta girgiza kai, idanun ta fal hawaye, ga mamakin
ta tafiyar da zai yi Burkina-Faso har tsayin sati biyu shi ya fi damun ta da daga
mata hankali a yanzu, ba wannan tone-tonen nasa da neman rigimar tasa ba.
Ummami duk da maganar ta buge ta kuma bata yi mata dadi ba amma ta waske, ta
ce ta yaya zaayi hakan? Dole kanwa ta so Yayan ta yace banda wannan Ummami, ita
bata son kowa daga kan ta sai kan ta da Amani ta ga zai tona mata asiri a gun
Ummamin dake ganin mutuncin ta, sai ta saki kukan da dole zai dakatar da shi, kuka
shiga yi riii-riii sosai, nan kuwa ba na komai bane na damuwar tafiyar sa ne.
Ko har yaushe Mukhy ya soma samun matsuguni irin wannan a ran ta, da har take
jin damuwar tafiyar sa matuka gaya haka a kasan ran ta? ita kan ta bata sani ba!
Ummami ta hau shi da fadan girma, inda take cewa cikin fada-fada kada ya kara gaya
mata wani abu da ya shafe su, tunda ita bai shafe ta ba.
Sannan ta hau lallashin Amani, tace rabu da shi diya ta kin ji, gidan zai bari
ki samu ki huta sosai Amani kamar ta cewa Ummami ita so take ma ta bi shi, babu
wani hutu a nesantar ta shi sai karin damuwa da hakan zai zame mata, hakika yau ta
samu kan ta a sabon yanayi, wato ta samu kan ta da enjoying dan short kiss din da
yayi mata fiercely (a zafafe) fiye da wanda ya faru a gidan Mamma a Kenema, ita
bata san ana soyayya cikin zafin rai ba sai yau.
Memories din hakan, dana sumbatar da ya yiwa kirjin ta, ya like a kasan ran ta,
kamar har zuwa lokacin Mukhy sumbatar nata yake ke cigaba da yi, don har zuwa
lokacin tsigar jikin ta da Mukhtar yayi sanadin tashin ta bai koma normal ba.
Ya saci kallon ta, kamar ya karanci situation din da ya bar ta a ciki, shima
hakan take, ji yayi kamar ya ce da Mamma a tafi da ita su dan zauna tare, amma sai
kawai ya share, yayi wa Ummami sallama sannan ya bar dakin ba tare da ya sake bi ta
kan ta ba, yana so ya koma Mukhtar din sa na baya, mai daurarriyar fuska, rashin
walwala, da cin magani, amma ina! Idan yana gaban Ummami yanzu, sai ya ji kan shi
kamar yaron goye, farin ciki ya cika zuciyar sa, rayuwar sa ta haskaka ta zama
cikakkiya, soyayyar da bai samu a kuruciyar sa ba ita yake samu yanzu wadda take
yawan saka shi a nishadin da yake sawa ya manta previous situation din nasa.
Wannan yanayin nasa na rashin walwala da bacin rai a yanzu ya zama tarihi a
tare da shi.
Ya gane hakan ne da ya ga har ya ga Amani duk da fushi da yake da ita amma kuma
ya kasa ignoring din ta, karshe sai gashi ya bige da sumbatar ta, wanda ya jima da
hana kan sa sake bari wani abu makamancin wannan ya shiga tsakanin su, sabida
abubuwan data faffada masa ana I gobe zasu taho Diffa a dakin ta na gidan su sun
kara kwaba waccan maganar ta farko.
Duk da cewa ya rama da mai zafi har fiye da nata tun a lokacin, daidai da yadda
yake so ya rama din, amma tsatsar maganganun har yanzu bata bar ran sa ba.
Mukhtar, Alhaji, Mamma, Baba Idi da wadanda sarki ya wakilta su raka su har
mutum biyar, sun tashi a jirgin sama zuwa makwabtan su wato Burkina Faso, ya zama
sai ita da Ummami da Sahura da tarin bayi mata da ke shige da fice suna ayyukan su
a bangaren Ummami.
Tunda Mukhy ya kira Ummami yace sun sauka lafiya bai kira Amani ba, hakan yana
cikin sababbin techniques da ya dauka don yana so ya koyawa kan sa tolerance a
kanta, ita kuma ya koya mata sanin darajar sa, har zuwa lokacin da zata koyi son
shi don radin kan ta, irin son da ya samu kan sa yana yi mata, ba wai so na
tursasawa ba ko na cin alfarma, ko don idanun iyayen sa da take tunanin bashi da su
a baya, ko na dangantakar jini da ke tsakanin su.
Ummami tasa aka shirya musu zuwa wajen kishiyar ta wato Hajja Tarha domin Amani
ta gaishe ta, an musu karba ta musamman a sassan Tarha ta kuma kira yar ta Saadiyya
dake Guinea a waya ta hada su suka gaisa da Amani. Ummami ta yi haka ne don samar
da sanayya tsakanin Amani da yayan Sarki guda biyu mata, wato Sayluba da kanwar ta
Saadiya kasancewar su yan uwa biyu kacal da Maina ya mallaka a duniya. Kuma dai
dama tsakanin ta da Tarha babu muguwar gaba ta azo a gani sai kishi, wanda baa iya
kaucemawa, wannan sai Ummu Aymana, wadda Allah ya raba su a yanzu.
Sayluba kuwa sun hadu tun a wajen bikin auren su data zo, har ta koma Tahoa tun
kafin a kammala bikin, halayen yayan Sarki Issouffou mata kwata-kwata bai yi kama
dana iyayen su mata ba. Suna da saukin kai sosai da son mahaifin su, don bai raga
musu komai na soyayyar Uba ba.
Sannan tasa aka kai Amani gun amaryar Sarki ta yanzu wadda ita daga Somaliya ya
auro ta.
A daren Mukhy ya kira Mai Diffa, ya gaya masa in sha Allahu akwai alamun nasara
a maganin da akewa Alhaji, don haka Sarki ya gayawa Ummami, inda ya ce ta gayawa
Amani ta cigaba da yi wa mahaifin ta adduar neman lafiya mai dorewa.
**** **** ****

MALAMA BA SURUKA BA!
W
annan tafiyar da su Alhaji suka yi suka bar Amani tare da Ummami, shi ya haifar da
wata kyakkyawar shakuwa a tsakanin su, kuma Ummami ma kamar kowa ta soma noticing
rashin wadatar ilmin addini da rashin ingancin dabiun Amani, sakalcin ta, doloncin
ta da sauran su. Amma ita ba kamar Jalan ba, bata duka bata hantara, sai tayi
amfani da tafiyar su Mukhy Burkina Faso ta ja Amani a jikin ta, babu tsawa, babu
duka ta soma koyar da ita muhimman abubuwa da ya kamata matar aure ta sani na
addini, Ummami tun daga alwalah, sunnoni da farillan sallah dana alwallah da wankan
janaba ta soma koya mata, domin ta sha mamaki da ta ce ta yi mata bayanin yadda ake
yi ta ga ta hau kame kame, ko kuma kai tsaye ta ce bata sani ba, ko ta ce ta manta.
Sannnan hatta yadda akewa sarakuna magana cikin ladabi da kwantar da murya sai
da Ummami ta soma aikin koya mata, da yadda ake rayuwar aure da masu mulki, wani
abun Amani ta ji kunya, wani abun ta gode har cikin ran ta.
Ummami dai ta zamewa Amani malama ba suruka ba, shakuwar su ta kai ga cewa
Ummami ta fahimci akwai rashin jituwa da rashin kakkarfar soyayya tsakanin Amani da
Mukhtar, kuma auren hadin Alhaji ne ba wai su suka hada kan su ba, amma ta fannin
dan ta Mukhtar dai ta san ko makaho ya shafa zai gane yana matukar son Amani a
cikin idanun sa ma kadai, amma abinda ya fada ranar da zai tafi, ya dan tsaya mata
a rai, da ya ce Amani bata son sa, auren dole Alhaji ya yi mata da shi, ta sunsuni
akwai babbar matsala a kan hakan a tsakanin su.
Ummami bata san cewa daga tafiyar Mukhtar zuwa yanzu an samu positive
improvement wato canji mai yawa ba, a tare da Amina-Amani. Ta kasance cikin kewar
Mukhtar, yadda bata zato, ba tare da ita kan ta ta san cewa tana kewar tasa ke
damun ta ba, gabadaya tayi sanyi, duk ta zama wata irin shiru-shiru ba tsiwa, ba
gayu ba cokala daurin kallabi. Mukhtar ya bar ta da kewar sa mai yawa a ranar da
zai tafi, in ta tuna memories na abinda ya faru ranar da zai tafi kai mahaifin ta
gidan magani, wato (sweet sensation) na lokacin ya ki barin ran ta, taji tana so ma
ya dawo, ko ganin sa ne ta yi daga nesa, koda yake yace ba zai kara kiss ba, umh.
Amma ita yanzu ne ma ta fara so da shaawar kiss din nan nasa, ta samu kan ta da son
yayi maza ya dawo a maimaita sumbar, ko da cikin cokali ne wato wadda bata kai ta
tsayin mintinan na ranar tafiyar sa ba.
A wannan lokacin da wannan tunanin ya zo mata, Amani sai da ta tura kan ta
cikin filo tana jin kunyar kan ta da kan ta, zuciya mai abun mamaki, zuciya tsokar
naman kirjin dan adam mai yawan dawurwura (rashin tsugunawa a wuri guda), wai yau
kuma Mukhtar take kewa, da bege haka, kai har ma da mararin gani, dan adam kenan
mai saurin manta baya. Gaskiya ne da aka ce (no condition is permanent). Gaskiyar
Balewa da ta taba cewa ta taka a sannu akan wannan bawan Allah bata san inda rana
zata fadi ba.
A wannan lokacin Hamida ta fado mata a rai, hakika bata kyauta ba, tun zuwan ta
bata kira Hamida ba, akawari bai ce haka ba, gashi zata so ta bata labarin abubuwa
da yawa da suka faru da ita dinnan a bayan rabuwar su din nan, masu dadi da marassa
dadin, koda yake masu dadin kamar haduwar ta da Maman ta da dawowar Mukhy cikin
nasa iyayen su suka fi yawa cikin labarin da zata baiwa Balewa, to amma wace irin
fassara Balewa kan ta zata yi mata in ta ce mata yau gata dumu-dumu cikin kewar
Dirty Human Being? Cikin mararin ganin Smart Ass da begen sumumu-kasau? In reality,
Hamidah ta fi kowa gaya mata ta taka a hankali a kan Mukhy, ta ji tsoron kaddara,
ta rage kiyayyar ta ga Mukhy, har ce mata ta taba yi bata san inda rana zata fadi
ba, yau ga rana ta fadi da ita a gabas! Inda wanda ya san kin da ta yi wa Mukhtar
da tijarar data zuba masa don wai yana matsayin yaron baban ta babu kamar Hamidah
Balewa, ina ma dai da a ce Hamida zata zo har Diffa, ta ga yadda rayuwa ta yi kuli-
kulin kubra da ita, iyakaci dai tayi mata dariya da shegantakar da bata san karshen
su ba.
Anyway, ya kamata ta kira Balewa, ta labarta mata duk abubuwan da suka faru a
bayan ta, don abokin kuka baa boye masa mutuwa, shakiyanci ne dai ta san zata yi
mata har sai ta gaji ta bari don kan ta.
Amani ta kira wayar Hamida, cikin saa ba jimawa layin ya shiga, duk da ba
koyaushe suke amun network mai kyau na yin kira Nigeria ba, saboda rashin kyawun
network na yankin su. Hamida ta daga da hamzari, tana fadin. Sahibah, ke ce kuwa a
kan layin? In da alkawari ruwa baya dafa kifi ba, kin makale a Saliyo, kin manta da
ni Bestien ki? Anya alkawari ya ce haka?
Amani tayi ajiyar zuciya ta ce da farko dai zan fara da baki hakuri Bestie, ki
yi hakuri Hamdy, na shiga harkalla mai yawan gaske data sa ban samu damar kiran ki
ba, sai yanzu da na samu nutsuwa.
Kawata I have a lot to gist you with, muhimmi a ciki, ina mai farin cikin
shaida miki cewa na hadu da Mama na Haj. Jalan a Saliyo, har an mayar da auren ta
da Mahaifi na mun taho tare da ita, ki taya ni hango irin farin cikin dana ke ciki
a sanadin hakan, amma a halin yanzu bama Katsina muna can yankin Diffa.
Da tsananin mamaki Hamida ta ce Sahibah Diffa kuma? Wajen wa? Inane haka? Amani
ta nisa tana fadin Bestie, wato labarin nan mai yawa ne, mai matukar ban alajabi,
har ma da ban tsoro a cikin sa, na so a ce ga ni ga ki ne, in kwantar da kai a
kafadun ki in yi kukan nadama, in kuma yi dariyar farin ciki as well, amma dai in
takaice miki, na kwashi kashi na a hannun nadama, na kuma nade tabarmar kunya ta na
yi gammo da ita a kai na. Abinda kika dade kina tunasar dani cewa in taka a sannu,
kada watarana in zo ina nadama ya tabbata.
Ashe Mukhtar da nake rainawa dan sarkin Diffa ne, mai jiran gadon sarautar
gidan su, da daya kwal da Sarki Issouffou ya mallaka, wanda inda an bi ta nasabar
da nake masa gori ne, ba zai aure ni ba.
Diffa na daya daga cikin manyan biranen kasar Nijar, sannan kuma ashe dan uwana
ne na jini, dan Yayar mahaifiya ta ne Haj. Aisata, wadda ke aure a can tun da
jimawa.
Hamida ta yi kabbara, ta sake yi, ji ta yi kamar ta shigo cikin wayar ta tadda
Amani sabida zaquwa ga abinda take ji, ta ce ki bari Sahibah, bana so, bana son
irin wannan zolayar kamar ta hikaya Amani ta yi rantsuwa tace babu zancen wasa a
cikin magana ta. Ashe duk jini na na yiwa wannan tijarar, yau gani dumu-dumu cikin
kogin nadama da wani sabon yanayi Sahibah, wanda nake so ki fidda ni a duhun sa.
Ta dan yi shiru, domin ita kan tabtana jin kunyar abinda zata fada, kewar
Mukhtar nake Hamdy, son ganin sa nake, matukar son ya sake kusanta ta na ke, sabida
baya gari yanzu haka, ya kai Alhaji Burkina Faso tun satin da ya wuce ta tusa kanta
cikin filo rike da wayar tana cewa na shiga uku Balewa, don ji nake abinda nake
fada kamar sabo nake, amma gaskiyar abinda ke zuciya ta kenan, mararin ganin sa da
dawowar sa daga Burkina Faso nake yi kamar in yi tsuntsuwa in cimmasa.
Me yasa a da bana jin hakan ban da kiyayyar sa?
Hamida bana so ya kasance sai da ya taka wani matsayi ne hakan ta faru da ni,
don ban san fassarar da shi kan sa da alummar da ke zagaye da mu zasu yi min ba!
Hamida ta yi kabbara ta sake yi, sannan ta fadi ta yi wa Allah sujjadah a dakin
ta, ko babu komai ya karbi adduar da ta dade tana yiwa aminiyar ta, yau matsalolin
ta sun warware ta kowanne bangare, jin abubuwan da take fada mata take kamar almara
ko tatsuniya, tace Amani (sunan da ba kasafai take kiran ta da shi ba), are you
sure duk wadannan abubuwan da kike gayamin daga bakin ki suke fitowa?
Amani sai ta soma share hawaye cikin karaya da tsoron kada ya zamanto Balewa
ce farkon wadda zata karyata ta, ta ce what are friends for? Shi yasa na gaya miki.
Shi ya ce tuba na na karya ne, kada kema ki ce haka don Allah, in na boye miki ai
bazan boyewa Allah ba cewa na yi nadama, Allah ya ga zuciya ta tayi wani irin
damuwa da shi yanzu, ta share hawayen ta sannan ta ce,
amma wa zan gayawa ya yarda da ni in ba ke ba?
Ko cigiyar sa nayi cikin kuskure Baba Sahura mahaukaciya take maida ni, shin
dan adam baya taba iya gyara kuskuren sa ne a karbi tuban sa?
Don na tabbata in kowa zai yarda dani banda shi Mukhtar din, sabida wata bakar
magana dana gaya masa cikin kuskure da ya kasa mantawa, da sauri Hamida ta ce kada
ki gaya min, na san zaki aikata, ni na yarda da ke in kowa bazai yarda da ke cewa
kina son Mukhtar ba Sahibah, ni na yarda kina son sa ba tun yau ba, wauta

Please Login or Register in order to submit comment