You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Issouffou Massaoudou dake ciki Al Imaraat Al Diffa
wato masarautar Diffa, zan iya kwatanta shi da Palace din da babu kamar shi a duk
cikin fadin masarautar, in ka cire sassan Sarkin Diffa.
An shirya musu dakunan barci har shidda, da shigifu (faluka) na alfarma wadanda
aka yi wa design da furnitures kala daban-daban, wasu an yi musu zubin royal
parlors, wasu kuwa English parlors ne, da kuma Francaise.
Jalan na cikin hada kayan ta don gobe da asubah zasu kama hanya, Mai ya basu
driver wanda zai kai su har Katsina sannnan ya dawo, Jalan ta ki yarda su yi
sallama da Amani ta ce da Ummami a wuce da ita gidan ta kawai, ita bata son koke-
koken banza na Amani, sannan duk wani abunda uwa zata fada mata ta san Ummami ta
gama gaya mata, don haka Ummami tayi abunda baa taba yi ba a masarautar Diffa, inda
tace da kan ta zata kai Amani har dakin ta.

A daren Mukhtar yana tare da Mai, suna cin abinci a kwano guda, yana masa hirar
abubuwan da suka faru dasu a Burkina Faso da yadda aka magance lalurar Alhaji Usman
ta suga da shanyewar jiki ta hanyar maganin gargajiya ziryan. Mai cikin gamsuwa da
taimakon da aminin sa sarkin Burkina Faso yayi masa ya ce da Mukhy, ya saka an
warewa Alhaji Usman Rakuma hamsin, a fara yi masa kiwon su anan cikin bargar
Rakuman sa, in kuma yana so a kai masa su Nijeriya ne duk zai iya sawa akai masa
har can, sannan ya bashi sittiru irin nashi na alfarma da rawanin sarautar Diffa
akwati guda, har da zoben azurfa mai matukar daraja.
Mukhy ya taya Alhaji godiya sai ya ce Uwa ta fa? Me aka tanadar mata? I mean
ita me zaa bata? (yana nufin Mamma Jalan).
Mai ya ce ya bada bracelet na zinare a bata, har Baba Idi ma ya samu kyautar
Rakuma goma daga Mai Diffa, Baba Sahura kuma Sarki yace Ummami ta ce a nan shiyyar
Amani zata zauna tare da ita har sai ta saba da gidan da mutanen cikin sa koda zata
koma Katsina. Duk da dai an bata wadatattun kuyangi da masu hidimar ta. amma zaman
Sahura zai mata amfani.
Mukhtar yana can suna wannan tattaunawar da mahaifin sa, ba tare da ya sani ba
Ummami da Baba Sahura suka kai masa Amani dakin ta, bai san hakan ba don tun
dawowar su bai nemi ganin Amani ba, kuma ko a hanya basu hadu ba, tunda yayi
alkawarin daina kebewa da ita sai ta yi hankali ta kuma koyi son shi don radin kan
ta, ya fahimci sai sun kebe ne take warware masa lissafi, da haka yake so ya koyawa
kan sa hakuri daga shiga lamarin ta yanzu, ya fuskanci muhimman alamuran da ke
gaban shi na taimakawa mahaifin sa kan shaanin mulkin sadon sauke nauyin alummah
dake kan su.
Don haka yayi gefe da Amani daga ran sa (for the mean time) na yana so ta koyi
son shi domin Allah ba don wasu material attachements, ko nasabar da take goranta
masa ba.
Daga wajen Mai, sai ya wuce suka yi sallama da su Daddy, yana jin wata irin
kewar Alhajin nasa, Mukhy har da hawaye ya yi, ya fiddo wayar shi ya yi ma Alhaji
hoto, yace Alhaji duk tsayin lokacin nan wai ace bani da hoton ka a waya ta. Dariya
Hon. Ya yi ya ce to gashinan ka samu, sai ka ajiye in ka tuno ni ka dauko ka duba.
Tunda ni da Uwa bama kama balle take tuna maka ni, Jalan da yake ta fini karfin
jini ta kwace wannan. Da kyar suka iya rabuwa don dare ya fara yi, daga wajen su
sai ya wuce sassan Ummami.
Ya same ta tana shirin kwanciya, sai ta ce Maina tun dazu nake jiran shigowar
ka in kwanta don na gaji da yawa, hidima kan hidima yau na sha ta har na gode
Allah. Alhamdulillah tunda komai ya nabbaa yanzu yadda na tsara Mukhtar ya samu
kujerar sofa din ta ya zauna, ya ce ai ga ni yanzu, Sweet Mum, me zaki bani Ummami
na?
Budar bakin Ummami sai cewa tayi.
Amanar diya ta Amina mana!.
Maina ka sani daga yau zaka soma rayuwar manyantaka, ka kasance mai hakuri da
yi wa matar ka adalci da rangwame a kan duk wani ajizancin ta, kai ne babba sama da
ita, don haka babba juji, bayan kasancewar ta matar ka yar uwar ka ce, jinin ka ce,
da ta fi karfin kowanne uzuri a wurin ka.
Haka Ummami ta zaunar da Mukhy wajen awa guda tana masa wata irin nasiha mai
ratsa zuciya, ta gaya masa ta kai masa Amani gidan sa yanzu haka.
Ya dan yi shiru na yan sakanni, ya rasa a yanayin da yake ciki, finally, shi da
Amani yanzu! A gida daya, daki daya, kuma gado daya. Tsakanin farin ciki ko akasin
sa, bai san wane ne yake nukurkusar sa a kasan ran sa ba, a can wani sako na
zuciyar sa yayi kewar ta, a wadannan sati biyun da bai sanya ta a ido ba kuma bai
ji muryar ta ba, duk da yake busy da kula da Alhaji, amma kullum sai Alhaji ya masa
zancen ta, mai nuna yay aye mat aba don halin ta ba, mai nuna tsanannin kaunar da
shimahaifin nata yake yi mata, wanda ke sawa ya kara mannata a zuciyar sa shima ko
ya ki Allah balle yana son ta, albarkar Alhaji sai son yake ninkuwa kullum. Amma ba
don ita ba, ba kuma don halin ta ba, sai don an jarrabce shi da son ta da kaunar ta
tun kafin haka, (no matter how worse her behaviours are).
A haka suka yi sallama shi da Ummami, yana jin kan sa kamar wani sabon mutum
yau da ya mallaki matar aure a cikin gidan sa, kuma yar Alhajin sa, Amani Tafisu da
zuciyar sa ke matukar so fisabilillah, ya shiga ratsa falillukan Ummami ya wuce
zuwa sassan nasu, dogarai na faduwa suna gaida shi a duk kofar da ya wuce.
Tunda Ummami ta ajiye ta a bakin gado bata sauya wajen zama ba, dan irin kukan
nan na amare babu shi a idon Amani Faskari, idanun kemadagas, kamar soyayyar gyada
marau-marau, amma damuwa da taraddadin haduwa da Mukhy yau, ta mayar dasu yan
kanana, data gaji da lullubin ta sauke shi saman kafadun ta, ta daga kai tana
kallon irin wannan dukiya da aka zuba musu a wannan daki don su biyu rak, ta dade a
zaune tana godiya wa sarki Allah akan komai ma, musamman a kan iyayen ta da suka
koma auren su, sai kuma ta tuna bata yi sallahr isha ba, don haka ta tashi da sauri
ta shiga inda take tunanin toilet ne, don yanzu bata wasa da lokacin sallah ko
kadan sabida nasihun Ummami.
Ta idar da sallahr tana addua ta ji motsin shigar sa dakin da ke kallon nata.
Kamar ta je, kamar kada ta je, ta tunawa kan ta cewa ita fa amarya ce no matter
how, Mukhtar shi ya kamata ya zo inda take duk mulkin sa.
Don haka ta daure ta cigaba da zama akan dardumar da tayi sallah, daga baya tun
tana addua a kan Allah ya gyara mata halayen ta da kowa ke kuka da su, har barci ya
dauke ta a kan sallayar.

Mukhtar na nasa dakin har washegari yana barcin gajiya, haka kawai zuciyar sa
bata amince ya je ga Amani ba, ko ya so hakan zuciyar ta ki amincewa, haka kawai ya
koyi juriya daga shiga alamarin ta.
Basu suka hadu cikin gida ba sai da safe a falon sa na farko, ta fito cikin
sassaukar shiga ta atamfa Holland, ta yi daurin kai dai-dai misali ba irin daurin
ta na baya da ta saba yi ba wato Ture ka ga Tsiya yau daurin Amani kan sa ya
russuna, kamar yadda zuciyar ta ta russuna, musamman da ta ga sun kwana gida daya
da Mukhy amma ko da wasa bai neme ta ba. Jikin ta duk ya yi laasar ya jikakken
tsumma.
Mukhtar na kwance cikin kujerar zaman mutum daya a falon nasa ta shigo ba tare
da ta san yana ciki ba, don ta duba abinda suka shirya musu na Karin kumallo, ya yi
wata irin kwanciya kamar mai barci amma a zahiri ba barcin yake ba, yana tuna
maganar da suka yi da Mai ne, na cewa Mai Diffa yana so ya karbi sarautar Diffa tun
yanzu, sabida shi tsufa ya cimmasa abubuwa da yawa baya iyawa yanzu, sabida rashin
karfin jiki.
Ya tuna amsar da ya baiwa Mai a lokacin.
Allah ya taimaki Mai Diffa, ina rokon a bari zuwa gaba kadan, tunda Allah ya
hore maka lafiya da koshin lafiya da abinda lafiya zata amfana, ina so in kara
samun nutsuwar da zan kara fuskantar yadda shaanin mulkin yake daga gare ka.

Takun sawun Tafisu da kamshin turaren ta ne ya ankarar da shi isowar ta, a
daidai kafafun Mukhy Amani ta zauna, har yanzu gajiyar tafiya bata sake shi ba,
shiyasa yake ta kwanciya tun jiya ya kasa fita yau, ya bita da kallo tana zama a
daidai kafafun nasa, har ta zauna fuskar ta ba yabo ba fallasa sai damuwa da
kulawa, ga dukkan mamakin Mukhtar sai cewa ta yi.
An dawo lafiya Ya Mukhy?
Sai kuma ta tuna zaman da Ummami ta ce irin shi zata dinga yi in tana gaban
Maina, ai kuwa ta gyara zaman nata da irin zaman Ummami din, kamar zata shige cikin
jikin sa russunawa da kulawa kamar baiwa a gaban Sarki, shi dai Mukhy kallon ta
yake daga kwance yana cewa cikin ran sa wannan canjin nata ba na kalau bane, don
ganin abun yake banbarakwai, wai namiji da suna Hajara.
Haka nan dai ya daure ya amsa mata (with straight face), sai kuma ta ce masa
ka ci abinci? I mean breakfast? Ya dan kalle ta da wutsiyar ido yana mamaki, sai ya
biye mata da yadda ta zo, ya ce aah ban ci ba tukunna, wani abu ne ya faru? Tashi
na kenan daga barcin da na koma bayan sallahr asubahi, shine na zo nan nake hutawa,
kafin lokacin fita ta ya yi.
Mukhtar yayi bayani, don ya kasa gane inda ta dosa da sabon canjin, yafi sawa
a ran sa wani abun take so shiyasa, don bai saba da concern din da yake gani yau
daga gareta ba. Amani ta karya kai, Allah ya taimaki Maina to ai ga abincin can sun
shirya shi tun dazu a kan dining-table, Maina ko zaka taso mu je mu karya tare?
Mukhtar ya kasa hadiye mamakin sa har ma da dariyar sa, ya ce Amani ce kuwa?
Don hatta lafuzzan ta da wani irin taushi da rangwada suke fito masa.
Tayi murmushin jan hankalin miji, sannan ta ce ko a kawo maka abincin nan ne
Ya Mukhy? Idan ba ka son tashi daga nan din?. Sai ya ce umh kawai, ya koma yadda ta
zo ta same shi a kwance, ya sake maida hankalin sa kan wayar sa, don ya kasa
gasgata abunda yake gani daga gare ta dinnan. Maiyuwuwa gizo idaun sa ke masa.
Amani sai ta tashi ta tafi ta kawo abincin daya bayan daya, ta shimfida ledar
cin abinci a gaban sa, ta hau hadawa Mukhy black tea mai kamshin kanimfari da
citta, don Ummami ta ce mata lallai su duka su dinga yawan shan kaninfari, tana
cewa ni bana shan tea da madara fa, ban sani ba ko kai ma haka?
Mukhy ya tashi zaune sosai, sannan ya harde hannuwa a kirji, ya kuma harde
kafafun sa, ya zuba mata kyawawan idanun sa, ya sake cewa umh, kawai, yana ta
mamaki dai, don still ya kasa yarda ita ce, sai ta mika masa kofin shayin da ta
kammala juyawa da Zuma maimakon sugar, ta bashi cikin girmamawa.
Mukhtar sai ya karba, ba tare da ya ce komai ba, ya kuma kai bakin sa ya kurba,
kamshin kanimfarin ya masa dadi a makoshi, bai ce aah ba, amma bai yi wata
kwakkwarar magana ba har yanzu.
Amani ta cigaba da zama a yanda take, abin ki da rashin sabo da kyakkyawar
muamalar data ke son assasawa, duk ta kasa sakewa da zaman da tayi din, shi kuma ya
cigaba da sipping shayin sa ko a jikin sa. Ganin ya karba ba tare da ya gwale ta ba
har yana sha, sai ta samu karfin guiwar zuba masa farfesun naman kaza, ta sa spoon
a ciki ta mika masa.
Ya karba again, ya soma shan romon da cokali, yana yi yana daga ido yana kallon
ta, ta kara da zuba masa chips and fried egg wanda ya ji albasa da koren tattasai,
ta sake mika masa, ya karba babu musu, don yana jin yunwar sosai, rabon shi da
abinci tun jiya, amma kuma babu magana a tsakanin su sannan babu nagode.
Ta zauna ta cigaba da latsa wayar hannun ta wanda chatting ne suke yi da
Balewa, ta ce Bestie, Im done with step one, but he seemed careless da kokari na.
Balewa ta turo mata Emoji na jinjina da kwanji, ta ce, dont worry, keep up the good
work, saura kwashe kwanukan da ya gama cin abinci, ki tabbatar rigar ta zazzago
gaba kuma a saitin idanun sa kin masa flashing.
Dariya ce ta kama Amani ta yi yar sheshshekar dariya ba shiri, ta ce Balewa ba
dama! Sai da Mukhtar ya dago daga cin abincin sa ya dube ta, ke da wa Hajjaju? Ya
tambaya cike da tsegumi, don kuwa Amani ba mutum ce mai yawan fara ba balle a je ga
dariya a iya sanin da ya yi mata.
Yau kuwa sai fara take kamar gonar auduga. Yanzu kuma har da kyakyatawa.
Ya Mukhy ni da Balewa ne.
Oh I see! Ki ce Your role model!. Ta yi murmushi, domin bata yarda da abinda
yace din ba, hakika da aboki yana maida abokin sa role model din sa, da tuni Balewa
ta dade da zame mata role model tuntuni ba sai yanzu ba da duniya da kan ta ke koya
mata hankali. Domin iyakar hankali da sanin ya kamata, mutunci da sanin ciwon kai
da rikon addini suna tattare da HAMIDAH HASHIM BALEWA, ita din ce a baya bata yarda
ta yi copying halaye da dabiun Hamida Balewa ba, don a nata tunanin, a sanda take
kan ganiyar ta it ace wayayya Balewa bata waye ba, shi yasa take yin simple life
duk da kasancewar ta yar gata, kuma a nata ganin simplicity din Hamida yayi yawa,
zai sa kowa ya raina ta.
Sai yanzu ne ta san Balewa ce wayayya ba ita ba. Ita shirme da kidifiri da
girman kan banza kawai ta sani, ta kuma kware a kai.
Mukhy ya ci ya koshi, ta tashi don ta kwashe plates da bowl din farfesun, ta yi
yadda Balewa ta ce ta yi, kuma cikin saa Mukhtar dagowar sa kenan idon sa ya fada
kai, ba zato ta ji ya mike shima, zata tafi da kwanukan sai ya dan rungumo ta ta
baya, ya ce.
Na gode da kulawar nan, nagode da dan canjin nan dana gani, honestly I cant
resist it!.
Sannan ya dora karan hancin sa saman gashin kan ta yana rike da ita daga bayan
ta, ya mannota sosai zuwa jikin sa, yana sunsuna gashin ta yana cusa dogon karan
hancin sa a ciki, wanda hakan ya sa dankwalin Amani ya sabule ya fadi kasa ta baya.
Gabadaya gashin da ya shag yara ya zubo bisa kafadun ta. Ya Ilahee! in ji
Mukhy. Yadda Mukhtar ya shiga goga tsinin karan hancin sa cikin gashin kan ta ya
haifar mata da yar rudewa, daburcewa da bakuwar kasala, duk ta san cewa ita ta
tsokano shi, hakan yasa kwanukan dake rike a hannun ta subucewa suka zube a kasa,
da na tangaran ne ba abinda zai hana su fashewa su yanke su sabida yadda suka
subuce daga rikon ta ba zaton ta, amma hakan bai sa Mukhy fasa abinda yake yi ba,
ta fahimci bat un yau ba, babu kamshin da Mukhy yake matukar so a jikin ta irin
kamshin tsakiyar gashin kan ta, wanda ya fahimci turaren gashi na musamman ne take
amfani da shi a cikin gashin ta, wanda iyayen ta Jalan da Aisata dake bata shi
kadai suka san sirrin da ke cikin sa.
Kamshin gashin nan ya tsokano abubuwa da yawa da yake ta kokarin dannewa tun
dazu, kuma dai dama ko ta ina aka je aka dawo Mukhtar ya san yayi kewar Tafisu, ba
ita kadai ba har tsiwar tata, kidifiri da rashin kunyar duk ya yi kewa yadda ba ya
zato, a kwanaki goma sha hudun da ya yi a Burkina Faso.
Sai kawai ya jirkito Amani bakidaya ta fado masa ya soma kissing din ta gently,
wani abu data tabbatar ya matukar kwarewa a kai fiye da komai watau gentle kiss,
duk ta kara daburcewa kafin kisses din Mukkhy ya soma shigar ta yadda ya kamata.
Gangar jikin ta kuma ta soma responding.
Tafiya ta soma yin tafiya, Mukhtar na kara birkita Amani da duk wani nauI na
romancing na miji ga matar da yake matukar so, yana kara sanya mata son amsa kiran
sa ta koina da sumbar nan tasa mai shiga rai, a kowacce gaba mai bukatar hakan a
jikin ta, wannan karon ma kamar wadancan karon, Amani ta gama sakarwa Mukhy komai,
da dukkan zuciyar ta da sahalewar ruhin ta, gabban jikin ta sun gama nuna amincewar
ta, ta shirya welcoming din sa (as a husband), har addua take a ran ta koma meye
zai faru ya faru a yau, kuma a yanzu. Zata jure, in dai hakan zai faranta ran Mukhy
ya daina rikon ta a ran sa ya bari su zauna lafiya.
Lokaci daya Mukhtar ya tuna Amani fa ba wai son shi take yi ba har yanzu, kada
yar canzawar nan da ta yi ya rudar da shi ga sanin ainahin wacece Amanin sa, Tafisu
wadda tafi sauran mata tinkaho, yanzu haka tana da dalilin ta na wannan dan canjin
da ya gani a tare da ita. Maiyuwuwa wani abun take so yayi mata, amma a sanin da
yayi mata, Amani bata da kirki, kuma bata kirki domin Allah. Sai tana neman wata
alfarma a gare ka.
And he will not be selfish anan, duk inda ya kai da son ta, da son kasancewa
tare da ita don bayyana wannan son da tabbatar da shi, yafi karfin yayi auratayya
da macen da baya ran ta kwata-kwata, bata kuma yi masa irin son da yake yi mata,
sai dai ta amince da shi bisa dole don ba yadda zata yi da auren sa, tunda iyaye
suka hada shi bisa karfin ikon su a kanta kuma sun fi karfin ta. A yanzu kam baya
jin akwai abunda ba zai iya hakura da shi ya zauna lafiya ba a rayuwar sa, ya
hakura da iyayen sa ma shekaru sha biyar, kuma ya rayu da numfashin sa balle
soyayyar mace, alhalin yana karkashin gatan sa?
Amani sai gani tayi Mukhtar ya sake ta ya ja da baya cikin mutuwar jiki, yatsun
sa ya saka cikin tarin sumar kan sa, ya ce Im so sorry for that, I know you dont
love me Amani, and I will not force you to love me or to sleep with me, because I
will not be selfish! In na yi hakan na so kai na.
Ya dauki dankwalin ta da ya sabule ya dora mata saman kujera, yana fadin Sorry
for making you to regret this again, I just couldnt resist your changes for today,
I like this new you. Ina ma wannan sabuwar Amani tawa ta dore!
Ya sumbaci goshin ta ya ce by Allah! You will be the death of me Amani, je ki
kada ki sa in kasa controlling kai na kuma, in yi abinda zai zo ya dame ni, kema ya
dame ki, tunda har gobe na kwana da sanin ba kya so na. Dole aka yi miki a kai na.
Na rasa me yasa? Komai na kudurta a raina don tsira da mutunci na daga fitinar
ki, in kika zo gaba na sai kin san yadda kika yi kika rusa min shi. Amani, why? Why
are you playing with my heart? Me yasa bazaki bar ni in zauna lafiya ba? Ko don kin
ga bani da juriya a wannan bangaren Im very fragile? Kullum sai kin san yadda kika
yi kika tsokano ni wato ko? Do you know how Im suffering after touching you? Na
rasa ko ke wace irin mai halin hawainiya ce, yau ki zama fari gobe baki. Kasancewar
kin san ni mutum ne mai son a kyautata min, a kuma yi min ladabi shiyasa kika bullo
min ta nan ba don kina so na ba?
Na bi ladabin ki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta in dai da shi zaki
yaudare ni yau Amani!
Ya sake ta ya kama hanyar ficewa daga falon, ta karfin hali da bin karfin
zuciya da kuma bravity na son kiyaye pride irin nasa domin hakika yanayin da fuskar
ta ya koma yayi tsananin bashi tausayi, ya bar Amani a wani yanayi na rashin jin
dadi da takurar zuciya wanda har a fuskar ta ya nuna nadama, ta cigaba da tsayuwa a
wurin kamar an kafe ta. Kafin kuka mai tsananin karfi na nadama da dana sani ya
kwace mata.
Ta riga ta san it will not be easy for him and for her, ya yarda da ita, ya
amince da tuban ta farat daya, amma bata zaci har haka ya rike abun a ran sa ba.
Duk kuwa da cewa ta san yana da riko.
Haka ta wuni sukuku a cikin gidan ta, cikin rashin jin dadin abinda ya faru
tsakanin su ranar, it made her whole day black! At the same time, ta wuni tana
takaicin dandani haukacin nan da Mukhtar ke yawan yi mata. Sai ta sakankance yau
zata zama matar sa sai kawai ya fasa, yana nufin, this is his punishment a gare ta
ko me? Ko ya fahimci tana son sa ne yanzu, tun kafin ta bayyana hakan da bakin ta
gare shi, shi yasa yake faman yi mata dandani haukaci wanda yafi ramuwar gayya ci
mata rai?
Bayan wannan dan romance din na Mukhy da ya hana Amani barci daren yau
bakidaya, tunda ya fita lokacin bata kara ganin sa ba sai washegari da safe a
sassan Ummami. Don sanda ya dawo gidan ta riga ta yi barci, kuma bai yarda ya kwana
a dakin ta ba. ya dai leko ya gan ganta tana barci ya wuce dakin sa.

Ta shiga kenan domin ta gaishe da Ummami, sai ta samu Uwar da Dan suna magana,
wato suna magana shi da Ummami amma maganar da ta dan ja hankalin ta, don ji tayi
Ummami na gaya masa Sarki ya karba masa kyautar sadakoki wato kwarkwara guda biyu
na yammata daga Sultanate of Damagaram.
Amani ta yi sallama a shigifar Mowar Sarki, saidai kuma cikin rashin saa ta
riga ta ji magana ta karshe da Ummamin ta gama fadi wa Maina yanzun, sai ta samu
wuri gefen kafar Ummami ta zauna, kamar ta ji Ummami tana fadin Sarki ya ce an
baiwa Maina kyautar Sadaka, Ummami din tana tambayar sa ko yana da bukatar amsar
su? Yara ne masu matsakaitan shekaru yanmata, lafiyayyu. Ummami ta kara bayani.
Kamar da gayya don Amani ta ji.
Amani wadda ta ji zancen alhalin tana shigowa, amma bata gane sosai ba, don
haka sai ta tambayi Ummami cikin rashin fahimta bayan ta samu wuri ta zauna a gefen
ta.
Ummami meye kuma Sa-daka?
Ta tambaya ne ganin kamar Mukhy bai so ta ji abinda suke tattaunawa ba, ya
zama kamar mara gaskiya daga shigowar ta, kuma fuskar sa ta ki karantuwa duk ya bi
ya daure fuska. Sannan bai ce komai a kan kyautar da Ummamin ta ce an yi masa

Please Login or Register in order to submit comment