You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  Wannan shine saƙon umarni da COAS ya samu a dai-dai wannan lokaci da agogo ke neman buga ƙarfe shida na yammaci a ofishin ministan tsaro bayan fitowarsu daga meeting room.
     Shiru General Yusuf yana kallon ministan tsaro dake bada umarnin bai iya cewa komai ba na ƴan dakiku. Ya kasa ma kallon sauran takardar da ke gabansa. Sai da Ministan ya sake maimaita umarnin da baki cikin ɓacin rai, yana jaddada cewa umarnin daga shugaban ƙasa ne, sannan Janar ya furta,
    “Yes, sir”.
   Ya faɗa yana sauke numfashi mai nauyi tare da miƙewa ya fito. Da sauri aka buɗe masa mota ya shiga, tunda suka baro ofishin minista ya faɗa duniyar tunani. A zuciyarsa kalmomin Minista ne kawai ke maimaituwa a kwalwarsa kamar amsawa kuwwa ne a cikin kunensa. Haysam Abdul-rasheed... to be apprehended.
Hankalinsa a tashe yake matuƙa, zuciyarsa na masa zafi. Duk da cewa aikin soja ya koya masa ya bi umarni ba tare da tambaya ba, wannan karon zuciyarsa ta ƙi yarda. Amma ba shi da zaɓi.
      Suna isowa office shima yay kiran Director of Military Intelligence dake ƙoƙarin barin office. Amma dole shima ya yanke nasa hanzarin ya amsa kira. Tunda ya shigo office ɗin ya fahimci akwai matsala sosai, dan fuskar COAS ta nuna kai tsaye. Yayi gaisuwa cikin girmamawa. Amma COAS bai iya ya amsa da baki ba hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan sakanni biyu ya fara magana muryarsa cike da raɗaɗi, “Issue the arrest directive Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu quietly. No noise.”
        Shima ba ƙaramin faɗuwa gabanshi yayi ba, ya ɗan zaro idanu waje zuciyarsa na girgiza. Sai dai kafin ma yace komai COAS ya miƙe abinsa alamar baya buƙatar wani zance. Rai a dagule ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya tsaya da kowa ba ya bar Headquarters ɗin gaba ɗaya zuwa gidansa, kamar wanda yake guje wa wani abu da zuciyarsa ta kasa jurewa.

       Bayan mintuna talatin, takardar Arrest Directive ta fita da cikakken sa hannun doka. An tura ƙungiyar jami’ai shida daga Military police da zasu kama Zak-Shadow bisa umarni, tare da amsar dukan abinda ya shafi matsayinsa.

        (((*)))(((*)))

     A ɓangaren Zak-Shadow da Imran sam basu sam mike faruwa ba, dan yanzu ma suke isowa gida daga asibiti bayan jam'an sojan nan sun tabbatar musu da komawar kulawar yaron a ƙarƙashinsu bisa umarni daga Headquarter kai tsaye gida suka nufa.. Sun yi ƙoƙarin kauda hankalinsu daga tashin hankali, kowa da tunanin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, duk da shi Imran yaso su cigaba da tattauna maganar da suka fara ɗazun da Zak-Shadow ɗin, amma shi kuma yanata kaucewa sai kawai ya haƙura yay shiru shima har suka iso anguwarsu.
        Zak-Shadow sai da ya kai Imran har gida sannan shima ya shiga. Bilal ne ya buɗe masa gate, dan ya fito zai je massalaci sallar Magriba da aketa kira. Shima sai yana ajiye motar bai shiga ba ya fito domin gabatar da sallar kamar yadda ya saba. Bayan idar da sallar magriba ya fito Bilal tare da shi. Labarin rigimar Nimrah Bilal ke bashi har suka iso ƙofar gate ɗinsu, hakan kuma yay dai-dai da isowar motar data saka Zak-Shadow tsayawa. Shima sai Bilal ya tsaya yana kallon motar kawai........✍️



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 70_

__________________

https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt


https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite

https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt
Assalamu alaikum,
Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝
Kamar
Kayan Yara
Zannuwan Gado
Kayan kitchen
Shoes and bags
Jewellery
Laces, atamfa,shadda
Dadai sauransu.
To nesa tazo kusa,
Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.

Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Cikin nutsuwa jami'an Military Police suka fito a tsare. Babban cikinsu ya matsa kusa da Zak-Shadow cikin girmamawa da risinar da kai yayi gaisuwa.
     Amsa masa Zak-Shadow yayi cikin jinjina kai batare da yace komai ba. Sai kuma ya juya yana kallon Bilal yay masa alamar ya shiga gida. Bilal da bai fahimci komai ba face abokan aikin Dadan ne sukazo maybe zasuyi magana ne akan aiki sai ya shige gida abinsa kawai.
       Sai a lokacin Zak-Shadow daya sake binsu da kallo a taƙaice ya furta, “Akwai matsala ne?”.
      Cikin sake risinar da kai ogan nasu ya ce, “I'm sorry Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed... by the order of the Defence Headquarters, you are under arrest. You’re to come with us quietly.”
       Zak-Shadow yay shiru kawai yana kallonsa na tsawon daƙiƙu, amma bai ce komai ba. Sai kuma a nutse ya koma kallon fuskokin sauran suma da duk suka risinar da kai alamar suna matuƙar jin nauyin kallonsa ma. Sai kawai yay wani ɗan murmushi yana sauke ajiyar zuciya.
      “Understood” ya furta cikin dakakkiyar murya, tare da miƙa musu hannunsa, alamar basu damar yi masa abin da suka zo yi. Wani daga cikin jami’an ya matso domin ɗora masa restraint band amma sai ya kasa. Sai ma cikin rawar murya ya ce, “I'm sorry Sir! wlhy bazan iya ba”.
        Murmurshi Zak-Shadow yayi anan ma, batare da yace komai ba ya amsa da kansa ya saka....

       ★★★★

Motar su Ja'afar ta iso dai-dai Jami'an MP na barin ƙofar gidan. Sukabi motocin biyu da kallo, batare da sun kawo komai a ransu ba su ma Ma'aruff ya fita ya buɗe musu gate suka shiga ciki. Idan har suka shigo gida sukan fara zuwa su gaida Mammah ne kafin su wuce nasu ɗakunan yin wanka. Yau ma kamar kullum can ɗin suka nufa. Tun a farkon shigowa suke jin surutun Nimrah da Mu'azz da Ruƙayya da bata koma gida ba. Sunayin sallama Mu'azz da Ruky sukayo kansu suna musu oyoyo. Nimrah dai babu damar tashi saboda ƙafa.
      Gaishe su Bilal yayi, su ka amsa da kulawa suna tambayarsa ya aiki dan shi kam ma'aikaci ne. Fitowa Biebah dake kitchen itama tayi ta gaishesu, daga haka suka nufi ɗakin Mammah, dan in ta shiga sallar magriba bata sake fitowa sai tayi har isha'i. Har sun je ƙofa Ma'aruff ya juyo yana tambayar, “Dada fa? Ko yana sashensa?”.
         Biebah ta ce, “Yaya tun ɗazun ya fita har yanzu bai dawo ba”.
     Bilal ya ce, “A'a ya dawo Auta, tare ma mukayi sallar magriba. Zamu shigo gida yayi baƙi baku gansu a ƙofar gida ba?”.
        Yanzu kam Ja'afar ne ya ce, “Eh muna isowa wata motar sojoji na barin ƙofar gidan, amma mu bamu ga Dada ba”.
     “Maybe ya riga ya shigo ne”.
  Duk sun gamsu da abinda Bilal ɗin ya faɗa, dan haka suka ƙarasa shiga wajen Mammah....

       ★Bayan idar da sallar isha'i su Ja'afar sun ta baza idon san ganin Dada ya fito a masallaci shima amma shiru. Kuma sun tabbatar idan yana gida jam'i baya wucesa. Sai da kowa ya shashshare suka tabbatar dai babu shi sannan suka koma gida. Kai tsaye sashensa suka nufa, tunda sun san shi kaɗai ne yanzu Nabeeha anyi yaji.
      Da knocking suka fara kafin su shiga. Sai dai ko ina shiru fitilu ma duk a rufe. Ma'aruff ya kunna fitilar falon haske ya gauraye ko ina. Sallama suka ƙara yi amma shiru babu alamar mutum. Sai kawai suka zauna a falon. Abin kamar wasa fin mintuna talatin babu motsin Dada, Bilal yaje yay masa knocking ƙofa amma shiru, dai-dai nan kiran Biebah ke shigowa wayar Bilal ɗin. Ma'aruff ya ɗaga.
            “Yaya Bilal Mammah tace wai ina kuka tsaya?”.
      Miƙewa Ma'aruff yayi da wayar a kunne yana amsa mata da, “Gamu nan zuwa, muna sashen Dada ne kuma da alama baya gidan”. Bai jira amsarta ba ya yanke kiran suka fito suka koma sashen Mammah. Duk sun sakankance Dada yaje wani waje ne har sunyi dinner sun dawo falo suna hira. Sai dai ganin Mammah tayi sukuku da yawa suka zagayeta da tambaya.
     Ajiyar zuciya ta ɗan sauke, batare data amsa musu ba tace, “Biebah kwashe yaran nan su koma ɗaki kinga sun fara barci anan”.
      Biebah ta ce, “To Mammah” tana miƙewa. Sai da ta tada Mu'azz ya wuce ɗakinsa sannan tazo ta ɗauki Nimrah takai ɗakin Mammahn ta ɗauki Ruky ma. Sai a lokacin Mammah ke amsa su Ja'afar.
        “Tun ɗazun nake jin zuciyata na rawa, sannan ina jina tamkar cikin tsoro-tsoro”.
     Duk kallonta suke cikin tashin hankali suma a karo na farko. Jikin Bilal a sanyaye ya ce, “Mammah wani abu ya faru ne kuma?”.
      “Babu abinda ya faru Bilal, kawai dai na fahimci bayan abinda ke faruwa a gidan nan na shirmen Nabeeha kamar Muhammad nada damuwa, sai dai yana ɓoyewa. Yau kuma gashi tunda ya fita har yanzu bai dawo gida ba, bai kira kowa a waya ba, kalla agogo ƙarfe goma saura. Sannan jiya na fahimci kamar Imran bai kwana a gidansa ba shima”.
          “Tabbas Mammah maganarki na kan hanya, dan kinga ɗazun da safe wasu jami'an soja sun kawo ma Dada takarda, amma sai yaƙi ya buɗe a gabanmu yace muzo muyi shirin tafiya kasuwa”.
      “Nima kuma yanzu kaga da yay baƙin nan Yaya Ma'aruff cayay fa na shigo gida, bai bari sunce komai a gabana ba.”
         Shiru falon yay tunanin kowa ya fara dawowa jikinsa. Kamar an saita sai ga kiran Imran na shigowa a wayar Ja'afar. Ɗagawa yay cike da zumuɗi yana gaisheshi, Imran ya amsa da kulawa yana tambayarsa lafiyar kowa, sannan ya ɗora da tambayar Zak-Shadow. Ɗan jimm Ja'afar yayi, sai kuma cikin damuwa ya ce, “Dada baya gida, muma bamu sameshi ba.”
      Da mamaki Imran yace, “Baya gida kuma?”.
      “Eh wlhy Yaya. Mun zata ma kuna tare ai a wajen aiki. Dan Bilal yace bayan fitowarsu a massalaci sallar magriba yayi baƙi kuma kamar jami'anku ne”.
      Imran ya ɗauki sakan biyu shiru kafin yace, “Ina Bilal ɗin?”.
    Wayar Ja'afar ya miƙama Bilal. Koda ya amsa sai da ya fara gaisheshi, Imran ya amsa a taƙaice ya cigaba da jeho masa tambayoyi. Ba ƙaramin rikita Imran amsar Bilal tayi ba, dan yana faɗar motar da suka zo da ita ya gane jami'an MP ne. A dai-dai kuma lokacin yake canja channel daga tv da nufin kallon labarai aka nuna jirgin sojoji ya samu haɗari da yamma a wani ƙauye, kuma jirgin na ɗauke da wasu masu laifi ne da aka kama kwanan nan a rikicin daya auku na yammacin ƙasar. Ai cikin tashin hankali Imran ya yanke kiran batare da cigaba da tambayar Bilal ba, dan kai tsaye ya samu amsar tambayarsa ne.....

<<•>><<•>><<•>>

           Duk da rufa-rufar da ake ta kama Zak-Shadow zuwa safiya dai zance ya gama fita cewar an kama shi ɗin. Abin mamaki kuma wata ɓoyayyar gidan jarida ta fara fidda bayanan kamashi a shafinta na X, tare da hoton lokacin da jami'an MP ke tare da shi, harda hoton dake da handcuffs a hannunsa. Kafin awa guda mutane miliyoyi sun zuba sharhi akan batun, manyan kafafen yaɗa labarai sun bazama binciken gaskiya.
       A gidan soji kuwa wasu hankalinsu a tashe matuƙa. Wasu ko na dariyar ALLAH ya ƙara da farin ciki mara misali. Nan fa wasu sabbin zantuka ma suka fara fita iri-iri masu ban mamaki. Kafin ƙarfe biyun rana ƙasa gaba ɗaya ta gama ɗauka. Babu wani labari dake trending sai batun kama Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu. A ɓangaren al'ummar ƙasa da yawa basu yarda zarge-zargen da akema Zak-Shadow ɗin ba, sun fi gaskata al'amarin da batun siyasa ce kawai ko wani abu daban. Su ko maƙiya na hura hanci da hanƙoron bada tabbacin zai iya fiye da haka....

      ★Ga su Mammah kuwa fassara halin da suke ciki ita da iyalanta ma ɓata lokaci ne. Dan tuni sun taru ƙwansu da kwarkwata a gidan sunata kuka. Sai dai Mammah baiwar ALLAH tana cikin nutsuwarta a zahiri, babu abinda take sai ambaton ALLAH.
      Imran, mahaifinsa, Uncle Nasiru, Ja'afar, Ma'aruff tunda safe da zancen ya fito suka bazama inda akace an ajiye Zak-Shadow, amma anƙi basu damar ganinsa. Dan wani mugun tsaro aka bama wajen ma da duk mai hankali ya gani yasan lallai akwai magana, sannan al'amarin bamai sauƙi bane ba.
      ALLAH sarki COAS da kansa ya gana da su yana mai kwantar musu da hankali akan suyi addu'a in sha ALLAHU babu abinda zai faru, gaskiya zata fito dan yanzu haka shima ya baza jami'ai ana kan binciken number motar da akace wanda sukaje ɗaukar Ojo sun tafi da ita. Sannan a yanzu haka ana kan bincike a ƙauyen da aka samu haɗarin wancan jirgin dan kai tsaye an samu tabbacin an harbo jirgin ne gangan ba haɗarin kai da kai ya samu ba.....
     
      <<•>>

     A can kuwa ƙungiyar duhu na cikin matsanancin farin ciki ne su da duk wasu munafukai dake ƙin Zak-Shadow. Dan kuwa babu wani kace nace aikinsu ya faɗa fiye da yanda suke so da fata batare da sun sami kowace irin tangarɗa ba. Sun sha bikin cin nasara a daren jiya, sun kumayi rabon dukiya ga duk wanda ya taimaka musu aikin ya tafi dai-dai. Ƙungiya kuma ta ɗauki sabbin members da za'a tada sabon jadawalin aiki da yafi na baya muni da zubar da jini. Dan sunyi alwashin duk wanda yace zai tare musu gaba kamar Zak-Shadow sai sun masa kisa irin na wulaƙanci. Shi kansa Zak-Shadow ɗin sunfi buƙatarsa a raye ne dan ya dinga kallon nasarrasu a gaɓar da bazai iya komai ba. Tunda yace shi mai kishin ƙasa ne da baƙin ciki zasu kashe shi. Dan sunyi alƙawarin dasa masa ciwon zuciya.
     A yanzu haka Ojo na hannunsu, dan sune suka saka aka ɗakko musu shi. Haka ma su Dagger na hannunsu, sune suka saka aka harbo jirgin nan, saboda suna buƙatar su Dagger a tafiyarsu, babu wanda zai musu kamar yanda Dagger ke musu su sami natsuwa, dan sun gwada yaransa amma basu sami biyan buƙata ba. Shiyyasa suka sake sabon shirin dawo da shi ta hanyar jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya, kuma sun sami nasara, dan haka yanzu lokaci ne na sake SABON WASA........✍️

     Alhamdullahi 🙏.

  Tabbas yanzu shine lokacin sake SABON WASA kam masu karatu. Dan anan book 1 ɗinmu zai ƙare. Ku muje zuwa book 2 inda ainahin baje kolin cakwakiyar take.

Idan nace daku cakwakiya kawai kaɗan ma kenan, dan book 2 ɗin nan ba'a magana. In sha ALLAHU zai zo muku da fiye da abinda kuke tunanin gani. Dan book 1 tamkar shinfiɗa muka baza, yanzu zamu tsunduma ainahin labarin KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODO...

★Ya zata kasance da Zak-Shadow?.

★Abin zai tsaya kansa ko zai haɗa da Imran?.

★Zasu sake shi da wuri ko kuwa zasu turashi kurkuku?.

★Ina batun Nabeeha da ƴan uwansa da uwarta?.

★Mi uwarta ke shiryawa?

★Nimrah ƴar Amana, yaya girman wannan tsuntsuwa zai kasance a gidan su Zak-Shadow? Ina batun aurenta da Zakinmu? Wane wasa za'a buga ita da Nabeeha ne?.

★Ina mahaifin Nimrah ne? Ya rasu a cikin wanda suka rasu ko kuwa an ɗaukesu tare da su Dagger?.

★Ƴan uwanta da gaske duk sun rasu babu ko ɗaya daga dangin uwa dana uba?.

Kai jama'a kada na cika ku da zance, Amma fa KIƊA A RUWAN kiɗa a ruwan ne fa, dan za'a buga wasa iya wasa, soyayya iya soyayya, cakwakiya iya cakwakiya. Rikita rikita iya rikita-rikita, gumurzu iya gumurzu. Dan ni kaina Bilynku na saka sulken yaƙi😎🏃🏼‍♀️.

     Ku muje zuwa book 2 kawai mutanensa❤️❤️❤️💃🏼.


Bilyn Abdull ce.
((C--2025))

_________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7
Mmn surayya me kayan kamshi
Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa
Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada
Turaran wuta na danal banat
Kajiji
Turaran kaya watau abbasiyya
Kabbasa spray
Humra
Kwallacca
Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu
Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇
08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina

__________________

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*





An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment