You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko? Irin rasuwar Baba da Inna da Gwaggon Maiduguri. Dama ranar nayi mafarki ai, dana gaya masa yace nai shiru kada na gayawa kowa mafarki ba gaskiya bane, gashi kuma ya zama gask....”
     Ya kasa ƙarasawa sai haɗiyar zuciya. Sai suka ga ya rufe idanunsa kawai. Gaba ɗayansu hawaye suke sosai, amma abin mamaki Haysam ko ɗigon hawaye babu a idanunsa, tunda ya rufe idanun nan shike nan, bai kuma sake magana ba har suka baro asibitin. Koda suka dawo gida mutane nata hamdala da ganin Haysam ɗin yana lafiya sai ƙananun raunuka. Kowa kuma na ƙara jinjina hukuncin UBANGIJI, dan duk wanda ya kalla motar su Abdul-rasheed da yanda su suka kasance, dan su dukansu likafaninsu sharkaf da jini aka bizne su a kabari amma ga Haysam ko babban ciwo babu a jikinsa. Babu wanda zai tunanin za'a samu wani mai sauran rai a motar nan.
         Rungume Haysam Yakura tayi tana kuka, amma A'isha ido kawai ta zuba musu. Koda Haysam ɗin yazo gabanta ya zauna bata iya ce masa komai ba, shima kuma bai iya yama kowa magana ba har lokacin. Duk wanda yace kuma yaga kukan Haysam a zahiri game da wannan rashi yayi ƙarya. Sai da dare A'isha ta kama shi a wani ɗan lungu cikin ɗakin Abdul-rasheed yana kuka shi kaɗai a cikin duhu. Hakan na nufin yazo ya ɓuya ne anan baya son kowa yaga yana kuka. A karo na farko taje kusa da shi ta zauna, tare da kamoshi jikinta ta kwantar da kansa a saman kafaɗarta, sai ya sake fashewa da kuka shima ya rungumeta. Itama kukan take yi sosai.
       Ranar a ɗakin nan suka kwana ita da shi, tana zaune dangan-gan, shi kuma tun yana a kafaɗarta har tai masa dabara ya zame ya kwanta kansa a cinyarta, a haka gabannin asuba barci ya sacesu su duka. Sai kiran salla ne ya farkar da su........✍🏼

Matan da suka rasa mazajensu ALLAH ya gafarta musu, ALLAH ya baku haƙuri bayin ALLAH, ALLAH ya raya muku zuri'arku ya albarkacesu, yasa su zama masu jinƙai a gareku😭😭🙏🏼.


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 22_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM
👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
👇🏻👇🏻
wa.me/2349030398006

TIKTOK
👇🏻
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Anyi addu'ar uku, ranar addu'a mutane sun cika fal harma da wanda ba'a sani ba abokan aiki dana kasuwanci na Abdul-rasheed daga gari-gari. A washe garin cikon kwana na huɗu mutane suka fara raguwa. Sai ƴan uwa na jiki kawai da danginsu na Maiduguri sai su Innar A'isha ƴan kano. Bayan addu'ar bakwai ma kowa ya wuce sai su A'isha kawai da Innarta da zata zauna da su. Sai wata ana kiranta Gwaggo Laraba ƴar Maiduguri dake matsayin kamar kaka a wajen su Abdul-rasheed ɗin. Zasu zauna da su har su kammala takaba, koda yake A'isha ce mai gama takaban a kusa. Yakura kam sai in ALLAH ya sauketa lafiya kuma. Gashi cikin ƙarami ne zubar jinin da tayi kuma zai iya sakawa ma ya koma baya.
       A yanzu kam Alhamdullah, basu da matsalar abinci da abubuwan buƙatu na rayuwa, dan suna samun ɗauki daga ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman ma Nasiru dake yin iya bakin ƙoƙarinsa. Bai gajiya da yawo tsakanin Kano da Bauchi. A haka A'isha ta kammala takaba, sai Yakura dake jan ciki, tana kuma samun kulawa sosai daga Inna da Gwaggo Laraba har ma da A'isha kanta. A tsakanin Haysam ya kammala primary ɗinsa, sai su Ma'aruff kuma daya kamata ace anyi haramar sakasu, amma a ƴan uwan na Abdul-rasheed babu wanda yayi magana. Sai da Nasiru yazo yaga shirun yayi yawa shi ya ɗaukesu ya sakasu, ya kuma ce saura a jira takardar Haysam ta fito shima ya wuce Secondary, ƙananun kuwa Ummi, Mommy, Bilal. Aka sakasu ta allo kamar yanda Haysam ke zuwa. Daga haka ya juya ya koma Kano.
      Watan Abdul-rasheed bakwai a cikin ƙasa ALLAH ya sauki Yakura lafiya. Sai dai kuma haihuwa tazo da tangarɗa da tashin hankali, dan tunda dama cikin ya tsufa gata nan ne dai babu isashiyar lafiya. Yau kuma data haihu sai jini ya ɓalle mata. Abu kamar wasa Inna Salame anguwar zoma zata iya tsaida shi, ga su Innar A'isha da Gwaggo Laraba na taimaka mata har abu yaci ƙarfi akace a wuce asibiti. Amma mi babu isasshen kuɗin zuwa asibitin, A'isha ta fita hankali a tashe zuwa gidan babban Yayan su Abdul-rasheed sanar masa, amma sai ya nuna shi wlhy baida kuɗi, hasalima yau haka ya tashi baida ko sisi, sai dai taje wajen ƙaninsa mai bi masa. Shima koda ta shiga ma sai matarsa tace baya nan. Hankalinta ya tashi ta dawo gida, bama ta iya sanar ma su Inna yanda akai ba ta sake fitowa, abinka da babu waya balle ta kira Nasiru dake tsaye akan al'amarin su. Wajen makwafcinsu dake saida dabbobi ta nufa, tace ya taimaketa ya bata kuɗi zasu kai Yakura asibiti idan sun dawo yazo ya kama akuyarta da take kiyo. Bai musa ba ya bata kuɗin, cikin farin ciki ta juya zuwa gida, tana isa aka ɗauki Yakura aka nufi asibiti. Likitoci sunyi faɗa sosai, daga ƙarshe dai suka amsheta.
     To ashe wasa farin girki, dan kuwa dai Yakura jiyya ce mai girma a tare da ita. Dan abu tun ana ɗaukarsa na marmari har ya wuce gaban kwatance. Tun ƴan uwa na zarya da bada ɗan taimako har kowa ya naɗe hannunsa ya bar A'isha da Nasiru kawai da Innar A'isha akan al'amarin Yakura. Sai Khadijah da autan su Abdul-rasheed angon da sukai haɗari ran aurensa da suma suke nasu ƙoƙarin duk da ba masu ƙarfi bane, dama dai ƴaƴansu Abdul-rasheed ɗin ne taƙamarsu, yanzu kuma ya tafi abubuwa duk sun tsaya musu. Shima Nasiru ƙarfin hali ne kawai ba wani ƙarfi ne da shi ba, gashi yana shirin tafiya ƙara karatu daya samu scholarship a ƙasar waje. Ana cikin wannan kai-kawo maganar tafiyar tashi kuma ta tashi, da farko yace ya haƙura A'isha taita roƙonsa akan yaje dan ALLAH kada ya fasa. Nan dai su Inna ma suka saka baki haka ya tafi bayan ya ajiye musu ɗan abinda zai iya na iya ƙarfinsa, bayan tafiyarsa matarsa da ƴarsa ɗaya Raihana da bata wuce shekara biyu ba sukabi bayansa.
     Tun ana zaman asibiti da Yakura har rashin kuɗi yasa suka tattaro suka dawo da ita gida, Gwaggo Laraba ma ta sulale ta tafi abinta, sai A'isha kawai da Innarta, ga yara har takwas dan yarinyar da Fauziyya ta haifa ma sai A'isha ke shayar da ita. A wannan halin A'isha ta ƙuƙuta ta saka Abdul-rasheed a Secondary school, ta fara sana'ar masa da safe. Sai kuma ƙananun tsogumin ya fara tashi akan zaman Inna, wai ya kamata ya tattara ta koma Kano, rasuwa shekara ɗaya da rabi amma ta tare a gidan ƴarta. ALLAH sarki Inna uwa mai dattaku, haka ta tattara ta wuce A'isha na kuka Yakura dake kwance komai sai an mata da yara nayi ta wuce. Tafiyar Inna baifi da wata guda ba Babban yayan su Abdul-rasheed ya lallaɓo yazo wa A'isha da batun wai yana son ya aureta, dan su haɗu su riƙe ziri'ar Abdul-rasheed. Takaici ya saka A'isha rufe ido tai masa tass, wannan abu da tayi kuma babu bincike mutane da dangin Abdul-rasheed suka sakata gaba saboda shi ya juya maganar a baibai. Haka aka dinga zuwa har gida ana cin mutuncin A'isha, sai dai su haɗe kai da Yakura da bata ɓoye ma komai ba suyita kuka. Ana tsaka da wannan rikicin jikin Yakuran ya rikice matuƙa, A'isha ta dinga bin dangi tana neman taimakonsu amma kowa ya nuna bazai iya ba bai da shi. Sai kawai ta yanke shawarar saida gidan da suke domin takai Yakura asibiti. Abinda ya bata mamaki sai ga ƴan uwan Abdul-rasheed sunyi uwa sunyi maɗaukiya, ƙarshe ma Yayan nan nashi da suke kira da Yayan gandu daya ce yana son aurenta ne ya sai gidan. Haka ta share bata nuna ta damu ba takai Yakura asibiti, ta biya kuɗi za'a mata aiki da tun farko likitoci suka faɗa rashin kuɗi ya hana. Sai dai UBANGIJI mai hikima bayan yin aikin da kwana biyu ALLAH ya ɗauki ran Yakura😭.
       Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wato gigita da magagin tashin hankalin da A'isha ta shiga da Haysam mai ɗan wayo a cikin ƴaƴan ɓata lokaci ne ma wajen zana shi. Dan Yakura haihuwar Haysam ne kawai batai ba. Amma komai da uwa take ma ɗa ta masa. Haka tsakanin Yakura da A'isha zamane na amana da ba'a batun wani kishi. A ranar da Yakura zata koma ga ALLAH ta kama hannun A'isha dana Haysam ta jaddada musu ta bar musu amanar ƴaƴanta. Bata yarda A'isha ta bama wani su Ma'aruff ba a duniya koda ƴan uwanta ne da suke uwa ɗaya. Tace ta baiwa A'isha har abada, ta kuma bama Haysam dake matsayin Babban yaya ya koma Uba a yanzu. A haka ALLAH ya ɗauki rayuwarta hannayensu riƙe a hannunta.
       A wannan rasuwa A'isha ta sake tabbatar da lallai suna cikin halin shiga uku ita da waɗan nan yara har takwas, dan kuwa Yakura batai wata biyu da rasuwa ba Yayan gandu ya sake zuwama A'isha da batun auren da yay mata a wancan karon, da tace bata yarda ba yace to ta tattara yara ta bar masa gidansa, ya bata sati ɗaya kacal. Hankalinta ya tashi, ta kira Jamilu autan su Abdul-rasheed ta sanar masa komai dake faruwa, harna sharrin farko da Yayan gandu yay mata, shima hankalinsa ya tashi, dan basu taɓa sanin gaskiyar zancen ba sai yanzu, amma sai yace su koma gidansa dan babu yanda zai yi tunda yayansa ne. Dan haka suka shiga tattare kayansu, abinda zai zama kaya A'isha ta saida shi, sai kayan sakawarsu da abubuwa masu muhimmanci kawai suka koma gidan Jamilu da zama. Sai dai ko wata basu cikaba sabon kalubale ya ɓullo daga matar Jamilu, dan ƙiri-ƙiri ta nuna ita bata yarda da wannan zama ba. Taya tana amaryarya haihuwa ɗaya (dan zuwa yanzu itama ta haihu) ace azo a cika mata gida da ƴaƴa. Rikici ita da mijinta A'isha taga aurensu na neman mutuwa ta shiga tsakani da roƙon Jamilu ya barta ta wuce Kano. Zai tada hankalinsa ta lallaɓasa da nuna masa muhimmancin yin hakan. Badan yaso ba haka A'isha ta hau shiri, da taimakonsa da rakiyarsa A'isha da ƴaƴanta takwas tai bankwana da garin Bauchi ta koma garinta na haihuwa Kanon dabo....

        Babu zato babu tsammani Inna ta wayi gari da baƙin Bauchi. Al'amarin ya girgiza mata zuciya, duk da kuwa kullum dama addu'arta ALLAH ya kawo ma A'isha mafita, dan tunda taje rasuwar Yakura ta sake tabbatar da Bauchi bazata zaunu ga ƴar tata ba. ALLAH sarki rayuwa, bayan shekaru goma sha shida A'isha ta dawo gidansu babu Abdul-rasheed a duniya. Tayi aure tana da shekara sha huɗu. Shekararsu goma sha huɗu da Abdul-rasheed, yanzu yana shekara biyu da wasu wattani da rasuwa. Haysam nada shekara goma sha uku da wasu watanni a duniya. Ja'afar da Ma'aruff nada shekara takwas, Bilal nada shida, Ummi nada biyar. Mommy nada huɗu da wata takwas, Ammar nada uku da wata huɗu, sai ƴar da Yakura ta haifa a ƙarshe da taci sunan A'isha suna kiranta MiMi nada ɗaya da rabi. A yanzu A'isha nada shekara talatin da ɗaya ne cif a duniya.
      Inna ma ba mai ƙarfi bace, dama Abdul-rasheed ne ke mata komai a yanzu, hatta da karatun su Bashir, dan tunda ya rasu suma su Bashir ɗin karatun ma ya nema taɓarɓarewa sai da Nasiru ya shiga ya fita ya samar musu wani taimako sannan. Ƴar sana'ar koko Inna keyi da safe yanzu, sai daddawa, da itace take ruƙe su ita da su Tasi'u da yake ba zama suke ba a gida koyaushe suna ma makaranta ne a Zaria, yanzu ga A'isha da iyalanta sun ƙaru. Lissafin ya canja ƙwarai da gaske. Ita kanta A'isha tunda ta shigo gidan take tattauna abubuwa a zuciyarta, da yanda rayuwa zata sake kasancewa. Amma dai tasan zama bashi yiyuwa, babban tashin hankalinta karatun yaran, duk rintsi bata fatan karatun yaran ya tsaya musamman Haysam dake jss 2 zai tafi jss 3 ne nan da ƴan watanni. Haka taita lissafi tun a daren da suka iso Kano ko rintsawa batayi ba. Washe gari karatun ya fara mata maimaicin kansa a cikin ƙwaƙwalwa. Ga Haysam tunda suka zo ya tsangwami kansa sai dai ka gansa zaune gefe shiru. Koda yake tunda Yakura ta rasu rashin maganarsa ta sake girmama fiye da bayan rasa mahaifinsu. Ya sake zama mara fara'a da yawan walwala.........✍🏼

_Rayuwa kenan, akowane motsi bawa baya rabo da jarabawa da sabbin ƙaddariri, ALLAH ya baki wuyan ɗauka A'isha🥲._


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 23_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Zak-Shadow da su Mammah sun wuce Kano, zasuyi hutu na makwanni har shida. Ashe walima Mammah ta shirya masa. Dan haka suka iske gida cike da danginta anata girki. Ƴan Bauchi dai iya kawunsa ne kawai sai Khadijah da Alawiyya suka zo. Bai damu ba, wanda ya gani ɗin ma sun wadatar. Anci ansha an masa addu'oi kala-kala harda mutanen anguwa.
     Bayan kwanaki biyu gida ya koma sai su kaɗai, Zak-Shadow ya sake fahimtar rayuwa ta canja ga mahaifiyarsa, ta tabbata dai bata tare da sabon mijinta. Sai dai yanzun ma bai tambaya ba saboda girmamawa har sai da Mammah ta sanar masa komai a wannan karon da bakinta. Tabbas zuciyarsa ta hasala matuƙa, amma bai ce komai ba dai a zahiri. Itama Mammah data fahimci yanayin nasa sai tai masa nasiha da gargaɗinsa akan kar taji wani abu daga garesa. An riga anyi ya wuce sai a tari gaba. Badan yaso ba yay shiru kamar yanda ta gargaɗe san.
      A cikin wannan hutu ya samu damar bibiyar karatun ƙanensa, har zuciyarsa kuwa ya gamsu da yanda komai ke tafiya Alhamdullah. Musamman ma su Ja'afar ƴan Secondary. Ya ji daɗin kuma ganin yanda kasuwar Mammah tai tasiri a gida. Ya ziyarci Malam Zayyanu da abokinsa Malam Datti. Sun masa addu'a sosai da nuna jin daɗin nasarar da ya samu a NDA.
     Duk da yana cikin hutu bai daina yin motsa jiki da safe da yamma ba, kamar yadda suke yi a NDA. Wani lokacin idan yana fama Mammah har faɗa take masa ya huta. Yakan yi murmurshi ne kawai ya ce, “Mammah idan banyi ba jikina zai yi ciwo ne”.
    Haka dole ta ƙyaleshi har hutunsu ya ƙare, kamar kuma yanda yay alƙawari yaje Bauchi tare da su Ma'aruff cikin weekend. Sun ziyarci kabarin mahaifinsu da Umma har ma da kakaninsu su Malam. Babu wanda yasan yaje a ƴan uwan mahaifinsu sai kawunsu Jamilu kawai, dan basu kwana ba a ranar suka juyo Kano.
       A watan Agusta ya koma Jaji, domin yin Young Officers Course, inda ya sake haɗewa da Imran, a wannan karon ma a ɗaki ɗaya suka zauna, dan sai da sukai duk yanda zasuyi aka haɗasu cikin amincewar UBANGIJI. Alhamdullahi sun kamalla course ɗin su a farkon shekarar 1999, daga nan kowa aka turashi inda zai fara aiki. sai dai an samu matsala dan anyi posting ɗinsu waje daban-daban shi da Imran, amma da yake suna da oganni tuni suka nema oga Adetunji suka sanar masa damuwarsu. Shine yay ta kai kawo har aka haɗasu waje ɗaya yanda suke fata, antura su aiki zuwa 82 Division Enugu, inda suka fara rayuwar soja ta zahiri. A can suka gane cewa aikin soja ba na jarumtaka kaɗai ba ne, aikin zuciya da sadaukarwa ne.

★Su Zak-Shadow na Enugu cikin sabuwar rayuwar aikin soja, anan rayuwar Mammah da marayun ƴaƴanta na neman canja salo da fuskantar sabuwar jarabawar rayuwa. Domin kuwa Zak-Shadow bai wuce watanni uku a Enugu ba Tasi'u ƙanin Mammah ya zo kwatsam. Zuwan daya saka Mammah a farin ciki dan tayi tsammanin har abada ta rasa dukkan ƴan uwa a duniya.
       Da farko dai kamar abin arziƙi tsakaninta da Tasi'u, dan harda zama ya bata labarin rayuwar da yake ciki ta tashin hankali. Yarinyar daya aura basu ko ƙulla shekara ɗaya ba a rayuwar aure suka rabu, ya shiga halin rayuwa mai tsanani a sabuwar ƙasar da bai san kowa ba, haka ya jure saboda karatun da yake yi. To zuwa yanzu ya kammala, acewarsa har ya samu aiki, yanzu ma yazo gida ne domin wani aiki da zai yi na wata uku ya koma. Mammah ta jajanta masa ta kuma tayashi farin ciki.
      Sunyi sati kamar uku a wannan farin cikin kwatsam rana tsaka sai ga Tasi'u da lauyoyi har biyu da wasu mutane, wai yana son a raba gida a bashi nashi kaso. Mamaki ya kama Mammah, ta kalla gida ta sake kallo, tabbas gidansu babba ne, gashi a bakin titi, kusan a yanzu ma gidan yafi duk wani gida na layin ƙyau saboda gyaran da Alhaji Nura yay masa lokacin daya aureta. Da farko ta ɗan so tirzawa tai masa faɗa, ya nuna mata shifa ba yaro bane, sannan gidan nan dai yana da hakki ai kuma dolene a bashi nashi hakki. Ganin yana son su zubar da mutunci a anguwa tace ba damuwa yayi duk yanda yaso, ko ɗaki ɗaya ta samu ALLAH ya amfana zata zauna da yaranta. Haka kuwa akai yayta shiga da fita batare daya bari tasan yaya komai yake tafiya ba. Kwatsam a cikin wata na biyu da zuwansa ta nemeshi ta rasa. Duk inda ya kamata ta bincika kuma tayi amma babu shi. Hankalinta yaso tashi kawunsu yace karta damu kanta, ta barshi duk ma inda yaje zai dawo tunda ba yaro bane. Haka dole ta haƙura ta share. Abin mamaki cikar wata ɗaya saiga wasu mutane wai sunzo gidan nan da take ciki nasu ne an sayar musu, suka nuna mata takardu harma da shaidun gani da ido da akai ciniki da su. Hankalin Mammah ya tashi kwarai da gaske, sai ta rasa inama zata saka kanta dan tashin hankali, kawai ta yanke jiki ta faɗi sai da aka kaita asibiti. Kwananta biyu aka sallamota, abu dai kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba Tasi'u ya saida gida ya gudu. Masu gida kuwa sun bata wata ɗaya kacal suna buƙatar gidan akwai abinda zasuyi da shi.
     Wannan tashin hankali ya saka Ma'aruff da Ja'afar sulalewa suka tafi Enugu suka sanar ma Zak-Shadow. Kwatsam babu zato ya gansu, mamaki ya kama shi ya balbalesu da faɗa domin a ganinsa ai kasada ce zasu kamo hanya batare da sanin gari ba su taho. Su dai haƙuri suke ta bashi, Imran dai ya kwacesu da ƙar, shine ya basu abinci sukaci ya basu wajen kwanciya. Zak-Shadow bai saurarensu ba sai dare, anan ne suka sanar masa abinda ke faruwa da halin da Mammah ke ciki, suka tabbatar masa a yanzu ma sunzo ne bada saninta ba, dan sun tabbatar tana can tana nemansu ƙilama hankali a tashe..   
      Jin wannan zance ya sake ɗaga hankalin Zak-Shadow, haka ya samu da ƙyar da kamun ƙafa aka bashi damar zuwa gida kwana uku kawai. Ya taso ƙanensa gaba suka nufi Kano. Aiko hasashen su ya tabbata, dan sun sami Mammah cikin tashin hankalin rashin sanin ina su Ja'afar ɗin suke, sai kuma gashi ta gansu harda uban gayya Haysam. Kukan dake danƙare da ƙirjinta sai a lokacin ne ta samu ta yi shi. Wannan al'amari ya sosa zuciyar Zak-Shadow matuƙa. Wanda ma bai san fushinsa ba a wannan karon ya gani kwarai da gaske.
     Ɗan kuɗin albashinsa da yake faman ajiyar taro da kwabo a account ya kwashe domin sayen fili, sai dai a karo na farko Kano ta fita masa a rai gaba ɗaya, yana son yin nesa da ita nisa mai yawa ko mahaifiyarsa zata samu salama tamkar yanda ta baro Bauchi, amma kuma bai san ina zai maidasu ba, dan haka ya nema shawarar Imran ta hanyar kiranshi a wayar landline. Babu wani ja'in-ja Imran ya bashi shawarar zuwa Abuja kawai, ya kuma haɗashi da yayansa.
    A ranar Haysam ya bar Kano zuwa Abuja. Inda da taimakon yayan Imran suka samu fili suka saya. Sauran kuɗin daya rage ya sayi siminti da bulo aka fara ginin ɗakuna ƙwara biyu kacal. Kwana uku aka bashi kawai a wajen aiki, dan haka dole ya koma Kano yabar sauran aikin wajen yayan Imran. Yana zuwa Kano ya sanar ma Mammah komai, mamaki ya kamata sai kuma ta shiga yi masa faɗa akan dammi zai yi hakan. Shi dai kansa

Please Login or Register in order to submit comment