You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai ɗacin gaske, dan haka Imran yay saurin faɗin, “Mammah bara nai muku bayanin komai”.
       “Ai bakai aka tambaya ba”.
   Momyn Nabeeha ta faɗa tana hararar Imran.
    A hasale Uncle Nasiru ya ce, “Shine kuma zai bada amsa, kai Imrana faɗi muna jinka. Kai Imran ya jinjina ma Uncle Nasiru yana gyara zama. Yayin da a jikin Windows su Ja'afar kejin kamar su tsallako falon su daki bakin Momyn Nabeeha, dan zuwa yanzu suma su Aunty Ummi sun iso, tuni kuma su Ma'aruff sun musu bayanin komai dan haka suka nema wajen maƙewa suma ayi komai da su.
       “Wannan yarinya sunanta Naja'atu, amma iyayenta na kiranta Nimrah saboda sunan kakarta taci...........” tsaf Imran ya zayyane musu komai, sai dai banda ainahin halin da mahaifinta ke ciki, hasalima kamar yanda Umma ta roƙa sai ya sanar musu mahaifinta ya rasu a rikicin kamar mahaifiyar tata. Ba ƙaramin daɗin hakan da yayi Zak-Shadow da Mammah sukaji ba. Dan ita Mammah komai sai da Dadan ya sanar mata bai ɓoye ba.
     Cikin damuwa sosai Uncle Nasiru ke jimanta al'amarin, da tsakanin jin tausayin Nimrah a ransa. Amma a mamakin kowa sai ji sukai Nabeeha ta ce, “Wlhy ban yarda ba, Imran kai dama ai munafuki ne nasani, tun ba yau ba nasan ba ƙaunata kake yi ba. Banda ma rainin hankali in har da gaskene abinda ka faɗa ɗin ai ba ita kaɗai bace aka kashewa iyaye, miyasa su sauran yaran kuka barsu can ita kuka taho da ita nan. Ba sai ku barta acan camp ɗin ba kamar sauran. Ni wannan labarin ƙanzon kuregen bazan taɓa yarda da shi ba, dan dama na jima ina zargin ana cin amanata, idan har ana son na yarda ba ƴarsa bace sai dai muje asibiti ai musu gwaji shi da ita.....”
         A matuƙar fusace Zak-Shadow ya miƙe, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa dake fita da kaushi da ɗaci ya nuna Nabeeha, “Baki isa ba, kinyi kaɗan wlhy. Kije labarin ƙaryar aka baki, kuma ana cin amanar taki kiyi duk abinda zakiyi, dan ke baki isa sakani yin abinda banyi niyya ba wawiya kawai”.
      A fusacen itama ta miƙe tana kuka, kai da ka ganta kasan kishi ne da zuga suka rufe idannunta, itama cikin ƙaraji ta ce, “To wlhy kuwa sai dai mu rabu, dan nima baka isa na cigaba da zama da kai ba. Jaka ka ɗauke ni ko dabba?, shekara da shekaru ina fama da kai muje muga likita akan matsalar haihuwa amma kaƙi saboda kasan mi kake shiryawa, kaje ka ajiye wata ƴar iska a jeji kana dadiro da ita ku haihu dan yanzu an kasheta ka ɗakko ƴar ka kawo gida mu shaƙi iska ɗaya da ita, mu kwanta muhalli ɗaya da it.....”
     Tasss! Tasss!!! Kake jin saukar mari har biyu a kan fuskarta irin mai gigitarwar nan, ai ko ƙara ta ƙwalla, dai-dai da miƙewar Momyn ta ta riƙeta tana shiga tsakkaninta da Uncle Nasiru mai marin........✍🏼

Gaskiya ƙawata Nabeeha baki ƙyauta ba, ya zaki mana haka kuma😳😏.
      


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 56_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t


UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta
+201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1F
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........“Miyasa zaka mareta? Naga akan gaskiyata take dai ai? Sai a daki yarinya a hanata kuka. Idan yasan yana da gaskiyar mizai sa yaƙi yarda suje suyi gwajin?”.
     Cikin kuka Nabeeha ta ce, “Momy ki barshi ya kasheni, Abba ka kasheni, dama mun san ai ba son mu kake ba yanzu, shi da yay laifin ka kasa yimasa magana saboda kana tsoronsa sai ni, sai ni da nake da gaskiyata za'a tauye ni......”
      Wani marin ya ƙara kawo mata, dan yama kasa magana saboda abinda ya tsaya masa a maƙoshi. Da sauri Momyn tata dai ta sake tarewa. “Wlhy bazaka sake dukanta ba”.
          Mammah da al'amarin ya girmi kanta ma sai yanzu ta iya ɗaga baki da ƙyar tace ma Uncle Nasiru, “Dan ALLAH Yaya kayi haƙuri ya isa hakan, duka ba shine mafita ba, ku barta ta huta ta huce dan yanzu shaiɗan yayi tasiri a zuciyarta. Sannan kuma tunda gwajin take so ni zan masa magana zaije suyi, ba shike nan sai a zauna lafiya ko”.
     A gatsine Momynta ta ce, “Da dai yafi kam”. Taja hannunta suka nufi ƙofa. Gagara sake yin magana kowa yayi a falon, dama Zak-Shadow tunda ya gama yaɓa mata zancen farko ya koma can dining ya zauna, yaƙi fita ne dan kar ya ɓatama Mammah rai, Uncle Nasiru kuma yaga kamar ya raina shi, dan kallon uba yake masa. Amma ya tabbatar ya cigaba da zama inda Nabeeha take zai iya fara kai mata duka a karo na farko na rayuwarsu, shiyasa ya zaɓi komawa can ya zauna ɗin...
     Salatin da Mammah ta saki ita da Imran a lokaci guda ya sashi buɗe idanunsa ya kallo falon, ai baima San ya miƙe ba da sauri ganin Imran ya taro Uncle Nasiru alamar faɗuwa zai yi. Ganin Uncle Nasirun na neman sumewa ya ƙarɓi ruwan da Mammah ta miƙo da sauri, ɓalle murfin yay kawai ya zuba a hannu yana kaiwa duƙe shima ya shafa a fuskar Uncle Nasiru. Nannauyan numfashi ya kawo mai ƙarfi, sai kuma ga hawaye....
         “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, dan ALLAH Yaya ka kwantar da hankalinka. Wannan fa ba wani abun tashin hankali bane ba. Komai mai sauƙi ne, tunda ma ALLAH ya kawomu zamanin da ake gwaje-gwajen sai a godema UBANGIJI ko. A kuma je ayi dan itama ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali.”
      “A'isha bazai je ba”.
  “A'a dan ALLAH Yaya kada kace haka, ita masalaha a rayuwa babu abinda ya kaita daɗi da sauƙi balle ma a rayuwa irin ta aure, itama yana da ƙyau a bata hakkinta kodan cire zargi, kasan bazan iya bijirema umarninka ba, amma dan ALLAH ko sau ɗaya ne ka bani damar nan na roƙe ka”.
        Yunƙurawa yay zai tashi, Zak-Shadow da Imran suka taimaka masa. A kujera suka maida shi, yay shiru tsawon lokaci, wata irin nadamar auren Momyn Nabeeha yake ji da zama da ita ba tsawon shekaru, wlhy badan ƴar uwarsa bace jininsa mafi kusa da har nadamar haɗa zuri'a yayi da ita. Matar nan itace babban ƙalubalensa na rayuwa, yasha wahala a hannunta a zamansu na turai, dan gaba ɗaya ta fanɗare masa ta saka yaransu fanɗare masa. Shiyasa ma ya yanke shawarar dawowa gida Nigeria. Ko batun saƙo da yake turama su Mammah ɗin da bai zuwa daga baya abokin nashi yazo ya gaya masa gaskiyar itace ta hana, ta dinga amsa tana rabawa uku ta bashi kaso ɗaya ta ɗauki biyu...
      Imran ne ya katse masa tunani da faɗin, “Uncle kayi haƙuri nima ina bayan Mammah, ka bari aje ai gwajin kawai kodan samun zaman lafiya da cire zargi, itama yarinyar kaga zata rayu cikin salama”.
        “Imrana.....”
   “Dan ALLAH Uncle”.
Imran ya sake katsesa. Kallon Zak-Shadow Uncle Nasiru ya ɗanyi, sai tausayinsa ya sake kama shi da kunyarsa mai tsanani, dan tabbas ya cutar da shi da har ya bari aka aura masa Nabeeha bayan yasan bata da isashiyar tarbiyya. Tabbas Haysam magajin Abdul-rasheed ne tako ina, dan ko a halayya da dattako da sanin ya kamata bai bar komai na mahaifinsa ba, kawai dai shi Abdul-rasheed mutum ne mai faranfaran da yawan magana, saɓanin Haysam mai shiru-shiru da ƙarancin fara'a a fuska idan ba shi yaso ba. Amma kowa ya shaida mutum ne mai haƙuri da kawaici.....

••><••><••><••

    Da ƙyar Mammah da Imran suka ci ƙarfin Uncle Nasiru ya yarda da batun gwaji, shi dai gogan bai sake tankawa ba. Yayinda can ƙanensa ke cike tab a waje. Dan sanda Momyn Nabeeha ta fita da ita yanda suka zuba musu idanu a fusace sai da sukaji hantar cikunnansu ta motsa, shiyasa da sauri suka wuce su zuwa sashen su Nabeehan.
       Bayan sallar Magriba da aka kira Mammah tasa Biebah zuwa ta sanar musu su fito za'a asibitin. Koda suka fito a tsakar gida suka iske Mammah ta fito, Uncle Nasiru dama bai shiga ciki ba bayan dawowarsu massalacin. Hakama Imran da Zak-Shadow dake can gefe Imran ɗin na lallashinsa. Cike da gadara Momyn Nabeeha tace kuma sune zasu zaɓi asibitin da za'aje. Nan ma Uncle Nasiru zai yi magana Mammah tai saurin cewa sun amince ayi hakan. Takaici kamar zai kashe Uncle Nasiru da Zak-Shadow, amma dole sukai shiru aka tafi asibiti. Ita da ƴarta motar ta suka shiga. Su ko suka shiga mota ɗaya. Imran ke tuƙi, Uncle Nasiru a gefensa. Mammah da Zak-Shadow suka shiga baya Nimrah da Bilal ya dawo da ita tana barci a cinyarta, dan har yanzu barcin takeyi. Motar ta ce gaba tasu a baya. Cike da kulawa da lallashi Mammah ta kamo hanun Zak-Shadow a cikin nata, dan ta tabbatar zuciyar ƴan mazan na nan na tafasa a ƙirji, saboda umarninta ne kawai zai je gwajin nan.
     Aiko tabbacin a zuciyen yake ko motsi baiyi ba koda ta riƙe hannun nashi. Idanunsa kuma a rufe har suka iso asibitin daya kasance privete ne, babban asibiti ne kuma da akeji da shi a Abuja. Abinka da maganar kuɗi ko zaman mintina goma basuyi ba likitan da zasu gani ta basu izinin shiga. Nimrah da tun zamansu wajen ta farka tana lafe jikin Mammah Imran ya miƙama hannu. Mammah ta kalla, sai ta mata murmushi da faɗin, “Jeki kinji, ai yanzu zaku dawo ina nan ina jiranki”.
     Kai ta jinjina Mammah, sannan ta miƙama Imran ɗin hannu ya sakko da ita. Da ƙafafunta ta taka har ƙofar Office ɗin, sai a lokacin kuma uban gayyar ya miƙe saboda maganar da Mammah tai masa. Nabeeha da itama sai yanzu uwarta ta kamata ta miƙar ta harari bayansa tana murguɗa baki, hakama Momynta da harara ta rakashi. Suna zuwa ƙofar ɗakin inda Imran ke tsaye tsagal Nimrah mai bakin magana da barci ya fara sakinta ta ce, “Baba ɗan sanda kanka ke ciwo ne?”.
     Yanda tai maganar idonta akan Zak-Shadow ya saka Imran yin ƙaramin murmushi, shiko idanu kawai ya zuba mata ya ƙi magana. Yayinda Mammah da Uncle Nasiru ke murmurshin maganar tata, nan kuma Nabeeha da Momynta ji suke kamar su shaƙe shegiyar yarinyar. Nimrah bata haƙura ba ta matso kusa da Zak-Shadow, kamar zatai kuka tana kallon fuskar tasa dai ta kama hannunsa, “Baba ɗan sanda akwai zafi sosai ko? Kada kayi kuka kaj.....”
      “Ke dan ubanki yima mutane shiru!!!”.
    Nabeeha ta daka mata tsawa. A mamakinsu ko irin ma ta tsorata nan sai ma ƙuri datai mata da idanu ba shakka ba girgiza. Aiko ji Nabeeha tai ta sake hasala, ta fige hannunta tayi kan Nimrah zata daka, sai lokacin ta sake matsawa jikin Zak-Shadow sosai ta rungume ƙafafunsa tana ɓoye fuskata. “Wayyo Baba ɗan sanda kace Kada ta dakeni, bana son duka bana so....”
     Jin shiru ba'a daketan ba tai shiru, sai kuma ta ɗan leƙo fuskarta taga miya faru. Nabeeha ta gani tsaye cak tana huci kamar zakanya. Sai dai bata san miya tsaidata ba. Abinda kuwa bata sani ba wani shegen kallo Zak-Shadow kema Nabeeha ɗin daya sakata dakatawar. Imran shi ya katse yanayin da faɗin, “Bismillah ku shiga”.
        Ƙwafa Nabeeha tayi da watsama Nimrah harara, ƙasa-ƙasa ta ce, “Sai na kasheki shegiyar yarinya ƴar zin....”. Bata ƙarasaba Momynta taja hannunta suka shige. Shima cikin lallashi Imran yay masa magana da ido, bai tanka ba ya kama hannun Nimrah suka shiga, Imran biye da su.
      Da Imran kawai doctor ya gaisa, koda ya miƙama Zak-Shadow hannu yi yay kamar bai ma gansa ba. Shima doctor ɗin sai ya sake nutsuwa dan ya fahimci waɗan nan mazan bana wasan yara bane ba. A ɗarare ya juya ga Momyn Nabeeha yana tambayarta mike tafe da su.
     Ganin Momyn Nabeeha zata fara wani ƙalƙale-ƙalƙalen magana da iyayin ƴan bariki Imran ya katseta kai tsaye yay ma likitan bayanin abinda suke buƙata. Doctor yaga ba wajen wasa bane dandanan ya ɗauka waya yay kiran wani. Kafin kace mi an musu dukkan abinda ya dace anan cikin office ɗin nashi batare da sunje lab ba. Dukkan abinda ya kamata anyi musu, duk da dai ansha badaƙala da ihu lokacin yima hajja Nimrah nata gwaje-gwajen. Bayan an kammala komai doctor yace results sai nan da kwana biyu.
        “Bazai yiwu mu sameshi a gobe ba doctor. Abin na gaggawa ne Please”.
  Momyn Nabeeha ce mai maganar, doctor yay ɗan jimm, sai kuma ya jinjina kai. “Okay ba damuwa hajjaju ai kece. Zuwa yamma zan kira ki”.
        “Ai ni da zai yiwu ma zuwa 12 nake so, dan goben zuwa 1 inada meeting da first lady, kuma sai dare zamu fito”.
      Bakin doctor a washe ya ce, “Shike nan yanda kike so haka za'ayi, zan yi ƙoƙarin hakan”.
      “Na gode”.
   Ta faɗa tana kama hannun Nabeeha suka fito, dama Zak-Shadow tuni ya fice da Nimrah. Sai Imran ne kawai aka bari, gama nazartar alaƙar dake tsakanin doctor da Momyn Nabeeha ya sashi tsayawar kuma. Sai da suka fice sannan doctor ya kallesa. “Ranka ya daɗe akwai sauran wani abu ne?”.
        “Mai muhimmanci ma kuwa. Naga akwai alaƙa tsakaninka da su, to ka sani idan ɗigo ya canja a cikin result ɗin da muke buƙatar gani kayi kuka da kanka. Suna Major Imran Abbas.”
     Daga haka Imran yay ficewarsa a office ɗin shima yabar likita da baki buɗe na firgici da mamaki. Dan a kwanakin nan babu sunayen dake amsa kuwwa a kafafen yaɗa labarai dana sada zumunta kamar Major Imran Abbas da Zak-Shadow da sauran Captains ɗin da akasha wancan gumurzun..........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 57_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

...........A inda suka bar su Mammah nan Zak-Shadow daya fara fitowa riƙe da hannun Nimrah suka samesu ita da Uncle Nasiru. Kallonsa kawai Mammah keyi cike da tausayi, dan tasan ransa a matuƙar ɓace yake, yana dannewa ne saboda umarninta. A kujerar kusa da ita ya zauna. Dan wani ɗan jiri-jiri yake ji, haka yake idan ransa yakai ƙololiwar ɓaci, dan mutum ne shi mai haƙuri amma yana da fushi sosai musamman akan gaskiyarsa. Yana kaiwa zaune Nimrah ta sake matsawa kusa da shi ta manne a jikinsa saboda hararar da Nabeeha da Momynta da suka fito ke mata. Hakan kuwa sai ya ƙara ƙona ran Nabeeha, dan babban baƙin cikinta itafa ka raɓar mata miji ne, cikin ƙunƙuni ta ce, “Banda ma ana son raina hankalina Momy, jiba yanda mayar yarinyar nan ke nane masa tabbacin ta masa sani na haƙiƙ....”
           “Malama ya isheki haka”.
    Karon farko Imran da fitowarsa kenan daga office ɗin shima ya faɗa a fusace, dan shi kam ya tsani nacin magana. Haukan Nabeehan ya fara isarsa shima. Ya tabbatar shi kansa Zak-Shadow ɗin darajar Mammah kawai yasa shi ƙyaleta. Hararar Imran tayi cike da jin baƙin ciki da tsanarsa. Tsigit Nimrah ta ce, “Baba ɗan sanda tana harararka” kafin wani yace wani abu ta cigaba da faɗin, “Kuma sai na rama maka, ai ido bai fi ido ba”. Tako ballarama Nabeeha harara harda riƙe ƙugu, dan tagaji da hararar da Nabeehan ke mata tun ɗazun itama. Mi Imran da Uncle Nasiru zasuyi ba dariya ba, Mammah kanta sai da ta murmusa kaɗan. Shi kansa uban gayyar idanu ya zuba mata. Kafin ya kai hannu ya matso da ita kusa da shi, kallonsa tayi a ɗan tsorace, dan ta zata faɗan hararar da taima Nabeehan zai mata, dan haka tai ƙoƙarin son goge laifinta kamar yanda take ma Umma a gida idan tasan tayi ba daidai ba. A bazata kawai yaji saukar ɗan hannunta akan goshinsa. “Baba ɗan sanda har yanzu kanka na ciwo ne?”.
       Yanda sanyin hannun nata da zazzaƙar muryarta suka ratsa kunnensa sai ya sake zuba mata idanunsa kawai, yama kasa mata faɗan da yay niyya ɗin. Itama kallonsa take ƙiri cikin ido kamar ba ita ba. Ji yay bazai iya shareta ba, balle ma shi mutum ne mai son yara sosai, hannun nata kawai ya kamo ya riƙe cikin nashi, tun fitowarsu gida a karo na farko yayi magana yana gyara mata ɗan baby hijjab ɗin jikinta. “Karna ƙara jin bakin nan yayi magana, babu ƙyau rashin kunya.” ya faɗa cikin gargaɗi yana ƙoƙarin miƙewa.
          Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ɗayan hannun nata kuwa na riƙe a cikin nashi. Suma su Mammah miƙewa sukai ita da Uncle Nasiru suna murmushi, dan sun fahimci Nimrah zata fara sakin jikinta da su kenan, da alama kuma yarinyar akwai surutu da tsiwa.....

<<>><<>><<>><<>>

           “Wannan shine gidan Sir!”.
    Matashin ya faɗa cikin karyayyen harshensa fuska cike da murmushi. Shima Dabo murmurshin yayi masa, tare da zaro kuɗi da zasu iya kaiwa dubu biyu ya bashi. “Nagode sosai, amma ko zaka bani number ɗinka, dan in na kammala abinda nake na kiraka ka fita dani koda nayi dare”.
     Ɗan jimm matashin yayi yana gyara zamansa akan mashin ɗinsa, dan haka Dabo yay murmushi a karo na biyu. “Karka ji tsoron komai, ni bamai cutarwa bane ba”.
          “Kayi haƙuri sir, kasan yankin namu ne sai a hankali, ana mana ƙwacen mashina musamman da dare a hanyar tamu shiyasa kaga nayi shiru, amma badan ina tunanin zaka cutar dani ba”.
      “Ayya na fahimta. Shike nan ba damuwa nagode sosai kaje kawai”.
     “A'a bara na baka number ɗin, sai dai idan dare yayi sosai sai dai na baka haƙuri dan ina jin tsoro bazan iya fita da kai ba”.
           “Na gode”.
     Bayan Dabo ya amshi lambar mai okada ya ɗan tsaya a ƙofar gidan yana waige-waigen da ƙarema wajen kallo. Garin ƙauye ne sosai, dan gidaje ma ɗai-ɗai suke. Gidajen duk babu wata katanga irin dai gini ne na yankin. Sai da ya ɗan furzar da iska kafin ya taka steps ɗin barandar ya haye kanta, dai-dai ƙofar dake rufe ya tsaya tare da fara knocking. Yayi fin sau uku sannan akazo aka buɗe. Cikin masa kallon rashin sani tsohuwar data buɗe ƙofar ta ce, “Waye kai? Wa kake nema?”.
       Tsaiwa Dabo ya gyara, cikin girmamawa ya sanar mata shi baƙo ne, kuma ma'aikacin soja, yazo wajensu ne akan wani Ojo”.
            Dan danan yaga fuskarta ta canja, jikinta har rawa ya ke ta kamo hannunsa tana faɗin, “Ojo! Kai soja ne?, kasan inda yarona Ojo yake? Da gaske kaga Ojo na? Shigo-shigo maza shigo ciki”. Ciki ta turashi, ta maida ƙofar ta rufe. Falo ne madaidaici da wasu ruɓaɓɓun kujeru a ciki, sai ƙaramar tv akan katakon tv stand. Sai da ta jawo wani ƙyalle ta saka masa a kujerar sannan ta sake jan hannunsa alamar ya zauna. Baiyi musu ba ya zauna, jikinta har rawa yake ta nufi wata ƙofar tana cigaba da maimaita masa kalmar sannu da zuwa data kasa daina faɗa. Karo na farko yabi falon da kallo, har idanunsa suka sauka akan hotunan dake saman tv ɗin falon manne a bango. Guda kusan huɗu ne, ɗaya mata da miji ne suna da ƙuruciya, kamaninta yasa ya gane itace duk da ta tsufa a yanzu. Sai na biyu mutumin kusa da ita ɗinne dai shi kaɗai da kayan sojoji, sai uku yara biyu matasa masu kammani da juna matuƙa, wanda kai tsaye yaga kamanin Ojo a tare da yaran duk da sanda akai hoton suna ƙananu sosai. Sai na ƙarshe zai iya cewa Ojo ɗin ne da kayan soja....
     Dawowar tsohuwar ya katse masa tunani da nazartar hotunan. Ruwa ta ajiye masa da faɗin, “Fara shan wannan bari naje na kawo maka lemo nan kusa”.
        Hannunta ya kamo da murmushi dan harta yunƙura zata bar wajen. “A'a Mama ruwan ma ya isheni, yi haƙuri ki zauna magana zamuyi ne”.
     Cikin damuwa ta ce, “Ko kaima kana tsoron cin abun hannuna ne? Kaima ance maka ni mayya ce ko....”
     Hawaye suka shiga sakko mata. Da sauri ya shiga bata haƙuri da lallashinta, da ƙyar ta tsagaita kukan bayan ya tabbatar mata shi babu wanda ya sanar masa komai a kanta.
         “Ka tabbatar?”.
     “Yes Mama”.
  “To kasha ruwan”.
Danta samu kwanciyar hankali ya ɗauki ruwan yasha sosai tare da mata godiya. Sannan ya fara magana cike da nutsuwa da kulawa. “Mama kamar yanda na faɗa miki ni soja ne, nazo garin nan ne kuma takanas saboda ke. Sai dai kafin na faɗa miki dalilin zuwana ina son nasan wanene Ojo a wajenki?”.
        Cikin jinjina kai da sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce, “Ojo ɗana ne, shi ɗin twins ne shi da ɗan uwansa, suna kamanni da juna sosai ta yanda koni wani lokacin suna ruɗani bana gane su. Su biyu kawai muka haifa, babansu soja ne, an kashe shi shekaru masu yawa, lokacin su Ojo nada shekara goma-goma. Bayan mutuwarsa nasha wahala akan rainon su Ojo, dan babu mai taimaka min, haka na dinga noman Togo da doya ni kaɗai ina biya musu kuɗin makaranta. Bayan sun gama Secondary Ojo yace yana son zama soja kamar mahaifinsu. Na tsorata sosai da hakan

Please Login or Register in order to submit comment