You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya jima a kanta tsaye yana kallonta da mamaki, har zuciyarsa na masa tambayar wai kuwa anya A'isha na sonsa? To dole yace hakan, yasha jin tarihin matan abokansa idan zasu ƙara aure akan kishi, amma ita ko da wasa babu abinda ta nuna masa mara daɗi, kuma dai ance kishi nan na mata shike nuna tsantsar soyayyarsu gareka. Haka dai yayta saƙawa da kwancewarsa, daga ƙarshe yay musu addu'a ita da Haysam ɗin ya kashe mata fitila ya fito tare da karo ɗakin ya nufi ɗakin amarya.
         Washe gari ma Abdul-rasheed yata zuba ido yaga canji ga A'isha ko'a fuska amma shiru, sai ma wani annuri data tashi da shi da farin ciki. Wanda ya sashi kasa gane daga ina ta samosa. (Bai san daga sallar dare bane. Dan cikin dare ta farka tai alwalarta a cikin ɗaki a botiki, ta shiga kaima UBANGIJI buƙatunta da addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da amarya da shi, Alhamdullahi kuma ta tashi ranta fes babu wani damuwa balle nauyin zuciya da take fama da shi a kwana biyun nan). Haka yay ta binta da kallo, musamman da zasuyi kari yaga ita da Yakura nata shan hirarsu hankali kwance kamar ma wasu ƙawaye. Kai daga ƙarshe ma sai bar musu gidan yayi, koda ya dawo samunsu yay suna aiki a tsakar gida suna hirarsu cike da nishaɗi da dariya. Ga Haysam a bayan Yakura a goye tana ƙulla aya da gyaɗar saidawa da A'isha keyi. Ita kuma tana girki. Harga ALLAH sai ya sake jin nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, harma da son A'isha yana sake nunkuwa a ransa. Dan haka da daddare ya sake haɗasu yay musu nasiha da roƙon su ɗore a yanda suka fara, su toshe kunnensu daga munafukai, su kauda idonsu daga azzalumai masu haddasa fitina a bayan fage. Sun tabbatar masa zai samesu fiye da yanda yake fata, suma kuma sun roƙeshi ya kasance adali a tsakaninsu mai tsayar da gaskiya. Shima ya amsa da tabbatarwa...
       Tabbas Alhamdullah, babu abinda Abdul-rasheed da Ai'sha da Yakura zasu ce a wannan gaɓar sai tarin godiyar ALLAH. Dan kuwa gidan aurensu ya zama gidan farin ciki da ni'imarsu da kwanciyar hankali. Bawai basa kishin bane, sunayi, sai dai kowacce tana yin kishi mai amfani wajen ganin ta ƙyautata ma mijinta a ɓoye batare data sosa zuciyar ƴar uwarta ba. Haka shima mijin na ƙoƙarin yin adalci, wadda yafi so kuwa ya barma ransa ne.........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 20_

__________________


_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM
👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
👇🏻👇🏻
wa.me/2349030398006

TIKTOK
👇🏻
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun rikiɗe zuwa kwanaki, kwanaki sun haɗu sun zama sati, satittika sun dunƙule zuwa wata, wattani suka haɗa shekara. Shekaru sun cigaba da shuɗawa. Har amarya Yakura ta cika shekara uku a gidan Abdul-rasheed. Bata samu ciki ba har yanzu, hakama A'isha tunda ta yaye Haysam shekara biyu kenan bata samu wani cikin ba. Abdul-rasheed kuwa nata sake samun ɗaukaka a wajen aiki da kasuwancinsa na ɗinki, dan zuwa yanzu ya koyar da yara da yawa aikin tela, kuma Alhamdullah suma suna cin gashin kansu, ga shagon saida kayan ɗinki ya buɗe duk sati Nasiru na aiko masa da kaya daga kano. Wani lokacin kuma yaje da kansa yayo daga nan yayo zumunci ya siyama Inna kayan abinci ya dawo. Zuwa yanzu kusan duk ɗawainiyar zuri'arsa ta dawo kansa ne. Yayima su Baba yayima yayunsa da ƙannensa, yayi ma dangin mahaifiyarsa, yayima dangin matansa. Sannan ya sauke hakkin gidansa. Haysam yaro ɗan shekaru huɗu a duniya, ya tasa abinsa masha ALLAH, kyakkyawa mai lafiyar jiki ga gatan iyaye dana kakanni, ya tashi yaro mai shiru, mai son karatu da tambaya. Wayonsa ya girmi shekarunsa, damma baida surutu ne. Yana da shekara biyar a duniya kwatsam a ɗan tsakanin sai ga A'isha da ciki, ya salam zo kaga murna wajen Abdul-rasheed da Yakura dama su Baba, cikin A'isha nada wata biyu itama Yakura ta fara nata laulayin, ya rabbi, rasa ina Abdul-rasheed zai saka kansa yayi dan farin ciki, dan harga ALLAH yana matuƙar son yara. Kamar yanda A'isha ta fara samun ciki itace ta fara haihuwa, santalelen yaro namiji a wannan karon ma, mai kammani da Abdul-rasheed shima. Ansha shagali yaro yaci suna Ja'afar. Ja'afar nada wata biyu da kwanaki itama Yakura ta sauka, itama dai ta santalo nata namijin mai kama da Abdul-rasheed, shima dai yaci suna Ma'aruff. Haysam cike yake da farin cikin samun ƙanne da suka tashi tamkar tagwaye, dan kuwa ma tagwayen ake kiransu. Su Ja'afar nada shekara ɗaɗɗaya aka saka Haysam makaranta, dan kuwa ya cika shekaru shida a duniya cif.
      Duk da kuwa kafin ma sakashi makarantar tuni ya fara ɗaukar karatu a wajen mahaifinsa da ma A'isha da Yakura. Dan Abdul-rasheed tsaye yake akan tarbiyyar Haysam, sannan akwai shaƙuwa a tsakaninsu mai girman gaske. Akoda yaushe zaka sameshi  zaune a gefen mahaifinsa yana sauraron karatun Alƙur’ani ko labaran tarihi na Annabawa da jarumai. Hakama sauran litattafai dai-dai fahimtar yaro mai irin shekarunsa. Duk lokacin da mahaifinsa ya karanta masa tarihin jarumtar Annabawa data sahabban MANZON ALLAH (S.A.W) irinsu Abubakar As-Siddiq (RA). Abokin ANNABI mafi kusa kuma khalifa na farko, mai haƙuri da sanyin hali Umar Ibn Khattab (RA). Khalifa na biyu, adalin shugaba jarumi kaifi ɗaya. Usman ibn Affan (RA). Khalifa na uku, ya tattara Al-Qur’ani cikin littafi, mai yawan ƙyauta kuma mai sadaukarwa ga bayin ALLAH mabuƙata. Aliyu ibn Abi Talib (RA). Khalifa na huɗu, kuma ɗan’uwan ANNABI, jarumi da baya tsoro sai dai kafirai suji tsoronsa, dan ya basu wuta iya wuta a filin daga, Mijin Nana Fateema ƴar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga su Abdulr-rahaman ibn Awf (RA). Irinsu Sa'ad ibn Abi Waqqas (RA). Talha ibn Ubaidullah (RA). Zubair ibn Al-Awwam (RA) ɗan uwan Ummul Muminin Khadija. Bilal ibn Rabah (RA), mai kiran salla na farko jarumi na gaske. Salmanul-farisi (RA) da ire-iren su da yawa da in lissafosu zamuyi da irin rawar da suka taka a musulunci da tsayawa kusa da MANZON ALLAH mu kammu mun san jarumai ne abin koyi da ba Haysam kawai ba ƴaƴanmu ma ya kamata ace muna basu tarihinsu domin su tashi da burin koyi da su ba zindiƙan wannan zamanin ba da yaranmu ke koyi da su koyi mara amfani da amfanarwa. A ɓangaren hikayoyi yana bashi irin nasu Iliya ɗan Mai Ƙarfi, Jatau Ɗan Mariya, Sarkin Zamani, da makamantansu. Dan a wancan lokacin, ana yaɗasu a gidajen  rediyo kamar su rediyo Nigeria da jaridu irinsu Gaskiya tafi Kwabo da sauransu.
      Irin waɗan nan tarihi da hikayoyi sunyi tasiri matuƙa a zuciyar Haysam, dan har yana ji a ransa yana son yayi koyi da su wajen hidimtawa addini. Sai dai abinda ke saka lissafinsa ruɗewa shine zamanin da yake saɓanin nasu ne, tunda shi bai zo zamanin yaƙe-yaƙe ba. Dan haka sai yayta jerama Babansa tambaya. Abdul-rasheed kuwa baya gajiya da bashi amsa, tare da kawo masa misalai akan idan su anyi yaƙe-yaƙe a zamaninsu shi kuma zai iya zama Ɗan sanda, ko SOJA ko wani dai aikin kaki domin bama ƙasarsa gudummawa. Ba wani fahimta Haysam yake da ƙyau ba, amma hakan na sashi jin eh lallai zai iya hakan. A haka ya fara makaranta sai abubuwansa suka sake faɗaɗa. Bayan yaye ƙannensa Ja'afar da Ma'aruff iyayensa sun sake samun ciki kusan a tare, amma Yakura ma ta riga A'isha a wannan karon, dan haka ta rigata haihuwar ɗa namiji mai kama da ƴan uwansa. Shima dai yaci suna Bilal, bayan wata uku da kwanaki itama A'isha ta haihu mace. A karo na farko Abdul-rasheed ya samu mace, dan haka taci suna Halimatu mahaifiyarsa Iya kenan suna mata alkunya da (Ummie). Itama dai akasha shagalin sunanta. A wannan lokacin ma Yakura ta sa sake yin gwanne kuma, dan Bilal nada shekara ɗaya ta sake samun ciki, dole A'isha ta cigaba da shayar da Bilal da Ummie a tare, aka bar Yakura da laulayin sabon cikinta har ALLAH ya kaishi haihuwa ta haifi mace itama da taci sunan Inna wato Karimatu suna mata alkunya da (Mommy).
          Bayan haihuwar Mommy babu jimawa UBANGIJI ya amshi ran Baba, jiyyar kwanaki biyu rak. Wannan rasuwa ta girgiza wannan zuri'a, barema Inna data koma kamar ta ruɗe. Haka dai akasha kuka da kai-kawo kowa ya haƙura a ƙarshe. Ashe wata na tafe, dan Inna na cikin takaba itama dai ciwo yay mata tsanani, ta matuƙar sakama kanta damuwar rashin baba, ashe itama ciwo ne na tafiya, itama dai a cikar wata na shida da rasa baba tabi bayansa. Su Abdul-rasheed suka sake gigicewa da ƴaƴanta. Nan ma akasha kuka kowa kuma ya haƙura, shike nan gida ya faɗi, an bar su Abdul-rasheed daga su sai dangi. A lokacin Haysam nada shekara goma sha ɗaya a duniya. Yana primary 5, yana shirin gamawa kenan ma, tunda aji 5 ce a lokacin 1983. An gama kukan rasuwar su Baba da Inna babu jimawa itama mahaifiyar Yakura ta rasu, haka suka kwasa sai Maiduguri. Satinsu guda suka dawo ko muce A'isha da Abdul-rasheed suka dawo tare da yara. Yakura sai data ƙara kusan sati biyu ma sannan ya dawo. A lokacin A'isha ta sake samun ciki, cikin daya dinga bata matuƙar wahala, daga ƙarshe ma ta haifeshi a bakwaini, har sai da aka sakashi cikin kwalba na wasu watanni, ita kuma tasha jiyya tamkar bazata rayu ba, mafi yawan mutane idan suka je dubata gani suke kafin su ƙaraso gida za'ace A'isha ta rasu. Abin birgewa kuma Yakura ke jiyyarta kai bakace kishi bace ba sam. Haka dai tasha fama tsahon watanni kafin ALLAH ya bata lafiya ta miƙe tamkar ba'ayi ba, dan kafin cikar wata biyu jikinta ya murje sarai harta fara dawo da ƙibarta. Kamar jira sai ita kuma Yakura ta shiga nata sabon laulayin cikin.
         A yanzu dai Abdul-rasheed nada ƴaƴa bakwai a duniya. Haysam, Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ummie, Mommy, sai autan A'isha Ammar. Family ya haɗu sai dai Alhamdullah. Ga kuɗaɗe Abdul-rasheed na samu na ban mamaki, sai dai baya tarawa kullum cikin hidimar ƴan uwa yake da ƴaƴansu, kai hatta maƙwafta da abokai cin arziƙinsa suke yi, dan mutum ne mai ƙyauta da hidima. Ga dai kuɗi ana wasa da su, amma idan ka cire gidan da yake rayuwa bai ajiye kaddarar komai ba. Hakan kuma bai taɓa damunsa ba bai taɓa kuma damun matansa ba. Ba shi kawai ba su kansu sun koya daga alkairinsa, ko baya kusa sukan yi a madadinsa da ɗan abinda yake basu da sana'o'in su duk da kuwa ƙananu ne. Abdul-rasheed bai taɓa sayen kaddara koda ta fili ya ajiye ba balle gona idan ka cire ta mahaifinsu da yake nomawa, bayan rasuwarsa kuma aka raba musu gado, daya tashi sai ya barma ƙannensa da suke ɗaki ɗaya ma kason sa. Dan a lokacin ne autan ɗakinsu ke shirin yin aure, shima dai ya gado Abdul-rasheed duk tsawon lokacin nan yana yawon karatu ne, daga ƙarshe dai zaiyi aure a yanzu cikin wannan satin. Auren daya taka rawar gani mai ban tsoro da razanin zuciya a zukatan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi dama al'ummar anguwa, kai harma duk wanda yasan wannan sunan wannan aure ya kawo masa tarihin da bazai manta da shi ba.........✍🏼

       Shin miya faru ne a wannan aure daya zame ma wannan zuri'a tambari da bazasu manta ba? Wane ajiyayyen tarihi wannan aure zai bari haka?🥲. Kudai kumuje zuwa dan har yanzu a shinfiɗa muke. Cakwakiyar da shagulgula na gaba🏃🏼‍♀️.


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 21_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Tabbas an ɗauro auren Umaru lafiya a garin Barno, dan kuwa shi a can ya ɗakko tashi matar da suka haɗu a wajen karatu a Zaria. Su Abdul-rasheed sunyi gangami sun halarci wannan aure a sabbin motocin daya saya musu shi da yayunsa biyu, akan suma sauran zuwa ƙarshen shekara in sha ALLAHU zai saya musu nasu, sannan ya biya hajji zasuje shi da Babban yayansu. Amma rayuwa bata da tabbas, a yayin dawowarsu Bauchi motar Abdul-rasheed tayi haɗari, a ciki kuma shine da yayansa na uku a ciki, sai abokansa biyu da Haysam.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, haɗari ne mai gigitarwa da tada hankalin wanda ya gani, dan kuwa babbar mota ce ta hayesu tsaf. A take ɗaya a abokan Abdul-rasheed da Yayansa suka rasu, dan kuwa sune a gaban motar, abokinsa driver, yayansa a gefensa. Sai Abdul-rasheed da ɗayan abokin da Haysam dake tsakkiyarsu a baya. Wani hikima ta UBANGIJI sai akai kamar anyi wurgi da Haysam ta tagar motar, dan can waje gefe aka tsuntoshi babu rai, yayinda nan su Abdul-rasheed mota ya danne su, shi rabin jikinsa a waje ƙafafunsa zuwa ƙugu na ciki ƙarfen mota ya rabasu kaɗan ya rage ƙugunsa ya rabu da gangar jikin. Yana kuka da kiran sunan ALLAH yana kuma ambatar sunan Haysam da roƙon mutane su taimkesa su duba masa yaronsa karya mutu. (ALLAH sarki ɗa da mahaifi kenan😭, yana cikin azabtuwa amma bata kansa yake ba. Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭 🙏🏼, ka yafe musu laifukansu ya rabbi😭😭).
         Da ƙyar aka iya zaro su Abdul-rasheed a wannan mota, akai asibiti da su. Kafin ma a isa ɗayan abokinsa shima ya cika. Shi ko sai da yay kusan awa guda ma likitoci nata kai-kawo a kansa kafin ALLAH ya amshi abinsa. Wannan rana dole ya zama ranar ruɗani da ahalin Abdul-rasheed bazasu manta da ita ba a rayuwarsu. Ranar da ta raba su Haysam da mahaifinsu, ta zo cikin rashin shiri. (Wato mutuwa! Mutuwa! Mutuwa nada tashin hankali ƴan uwana, mutuwa nada gigita ƙwarai da gaske, wlhy bazamu gane wacece mutuwa ba sai randa tazo kammu. Wane shiri kai mata, wane shiri kake mata? Ka kammala baka kammala ba ko bakama fara ba wlhy sai tazo, zuwan da babu ɗaga ƙafa balle jiranka koda na sakan ɗaya danka kammala abinda ka fara😭😭).
       
         Mata ƴan biki nata kai-kawo anan Bauchi, sai dai jikin A'isha dana Yakura duk a sanyaye kamar marasa lafiya. Ga yawan faɗuwar gaba da suke samu da nauyin zuciya. Ita Yakura sai kowa ke ɗauka ciki ne. Itako A'isha ganin tasha jiyya bata ko jima da miƙewa ba sai kowa ke mata uzirin da sauran nauyin jiki. Sai dai ba haka bane ba, mutane kuma basu gane ba haka bane sai lokacin da labari ya iso cikin Bauchi, tun anayi ƙasa-ƙasa kada su A'isha su fahimta lokacin ma da ran Abdul-rasheed har dai ta fasu bayan rasuwarsa. Dan dole aka kwaso gawarwakinsu huɗu reras idan ka cire Haysam ɗan shekara goma sha ɗaya dake gadon asibiti likitoci na ƙoƙarin ganin sun ceto tashi rayuwar. Hakama matar Ayuba Yayan Abdul-rasheed dake fama da tsohon ciki duk tayi sukuku.
         A lokacin da aka shigo da gawar Abdul-rasheed data Ayuba rawa jikin A'isha da ƙus-ƙus ɗin mutane ya fara shiga kunnenta ya fara. Cikin ɗimuwa ta fito daga ɗakinta batare data fahimci inama take ajiye ƙafa da ɗaukewa ba ta durƙushe a gaban gawar mijinta da aka shimfiɗar a ƙofar ɗakin nata, hawaye na zuba kamar ruwan sama da ba ya ƙarewa. Hannunta na karkarwa ta kaishi kan babbar rigarsa da aka rufa masa dake jiƙe da jini ta yaye a hankali, fuskarsa dake da ƴan ƙananun raunuka ce ta bayyana, sai kawai ta tafi luuuu ta kife akan fuskar tashi ta sume musu. Dai-dai faɗuwar Yakura itama data fito daga ɗakinta a guje, ita kam jini ne ya ɓalle mata abinka da mai ciki. Ga matar Ayuba can ma ƙudar dole ta sameta. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ya rabbi ya rabbi mun tuba, mun tuba ya ALLAH 😭😭.
           Gida ya ɗauki koke-koke da ƙyar ake tsawatama mutane. Yayinda aka zubama A'isha ruwa a jiki ta farfaɗo, Yakura kam dole Inna Salame ce a kanta ana ƙoƙarin tsaida jinin daya ɓalle mata. Haka aka shigar da Abdul-rasheed ɗakin A'isha da Ayuba cikin jini babban Yayansu da mai bi masa sukai musu wanka aka shiryasu a tufafinsu na gaskiya. Tufafin da kai da ni suke jiran mu ma. Duk yawan kaya masu tsadar man da kika tara bango guda na drawer da wanda ka tara duk nan za'a barsu dama anan muka samesu. A naɗemu a wannan yankin farin ƙyalle tal kamar yanda a yau akama Abdul-rasheed da Ayuba. Haka ma sauran abokansa biyu an kaisu nasu gidajen ana musu nasu shirin suma...

            ALLAH sarki rayuwa kenan, taron biki ya koma taron makoki, da ƙyar aka samu A'isha ta iya sallama da gawar Abdul-rasheed. Yakura kam ma anata ƙoƙarin ceto rayuwar ta ne da abinda ke cikinta. Hakama matar Ayuba. Sauran ƴan uwansu makusanta sunyi sallama da gawar Ayuba da Abdul-rasheed kafin a fita da su ƙofar gida inda aka haɗe da sauran abokansa akai musu salla, sannan aka wuce da su makwancinsu na gaskiya. Makwancin da yake jiranmu ni dake, yanzu ko anjima ko gobe, koma yaushe ne dai sai tazo😭.
        Babu wanda hankalinsa ya koma kan batun Haysam sai washe gari. A'isha ta ɗan dawo hankalinta duk da a jiyan ma ba wani kukan shirme take ba. Yaran suna zagaye da su ita da Yakura da aka samu nasarar tsaida jinin daya ɓalle mata tun a jiya da dare. Sai Yakura ta ce, “Yaya ni naga kowa amma banga ɗan albarka na ba tunda gari ya waye”.
    A karo na farko A'isha tabi yaran da kallo itama. Su duka biyar suna nan, wanda take goye yana bayan Alawiyya. Cikin girgiza kai ta ce, Mama (dan haka take kiranta kamar yanda yaran ke faɗi) bana jin tun jiya ma ni naga ɗan nan naki ai”.
        A ɗan rikice Yakura ta tashi a zaune jikinta na rawa, idonta cike da hawaye ta ce, “Yaya tun jiya fa? Mun shiga uku ni Yakura, dan ALLAH ku nemo min cikin kawun nan ku, Haysam fa tare suke da Babansu Yaya. Kai Ma'aruff tashi maza kira min Kawu Nuhu”.
        Ba Yakura dake magana jikinta na rawa ba, itama A'isha rawar jikinta keyi, sai dai kamar wadda aka dokema ƙafafu ta gagara koda tashi balle cewa komai daga inda take. Har ita Yakuran ma tai ƙoƙarin daddafawa ta sauka a gadon tasa Ummi ta taimaka mata. Dai-dai nan Khadijah ta shigo, itama ido luhu-luhu alamar ansha kukan rasa ƴan uwa. Ganin halin da Yakura take ya sata saurin ajiye kwanon fura dake hannunta, dan ganin A'isha bataci komai ba tun jiya gashi yanzu har an kusa sallar azhar shine ta nema fura ta damo ta kawo mata nan ɗakin Yakura da taga ta shigo tare da yara duba ta.
         “Yi a hankali Maman Haysam (da yake haka suke ma Yakura alkunya, ita kuma A'isha suce Maman Ma'aruff) kin san da halin da kike ciki, inama zaki ke da akace ba'a son kina dogon motsi”.
     Muryar Fauziyya na rawa tace, “Yaya Khadijah Haysam, kin san fa tare suka tafi da Babansu, amma babu wanda yay batunsa tun jiya”.
       Sosai gaban Khadijah ya faɗi itama, dai-dai nan Ma'aruff ya shigo tare da kawunsu Nuhu, shima yana jin batun da suke tattaunawar hankalinsa ya tashi, sai lokacin ya tuna cewa lallai tare da Haysam aka wuce da Babansa asibiti, duk da shima babu wani alamu daya nuna yana a raye, amma yaji sanda ake sakashi a ambulance likitan na faɗin zuciyarsa na harbawa kaɗan-kaɗan, shiyasa ma ba'a sakashi cikin gawar su Ayuba ba. Ai babu zama ya fita da gaggawa, kai tsaye asibiti suka wuce shi da su Nasiru. Cikin amincin ALLAH suka samu Haysam ya farfaɗo tun da safe, likitoci nata cigiyar ƴan uwansa an duba kaf sun wuce tun juya kasancewar a rikice kowa yake. Tunda suka shiga ɗakin da Haysam yake kalma ta farko daya fara jeho musu shine “Kawu ina Babana?”.
      Babu wanda a cikinsu gabansa bai faɗi ba, amma suka dake cike da mazantaka suka zagaye shi suna lallashi da tambayar jikinsa. Shi ko yaro ne mai wayo, duk da shekarun nashi duka 11 ne a duniya ALLAH ya bashi basira sosai, sai ya ƙi amsa musu ya zuba musu ido kawai. Tausayinsa mai tsanani ya kama Nasiru, dama ga alhinin rasa aboki, kuma amini zagaye da ruhinsa. Sai hawaye sharr suka shiga rige-rigen zubo masa. Kafin ya kauda fuska Haysam ya ganshi.
      Kawai sai ji sukai ya ce, “Baban Kano kuka kake yi?”.
      Da sauri Nasiru ya shiga girgiza masa kai yana share hawaye. Amma sai Haysam ɗin ya ƙara faɗin, “Babanmu ya rasu

Please Login or Register in order to submit comment