You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa sai gashi an zaƙulo yaran Dagger har uku da suka ji rauni suka ɓuya cikin wasu gidaje.
         “You see! Kuna nan zagaye da gawarwaki maƙiyanku na fake a cikin al'ummar da kuke bawa garkuwa. Abin takaici abin a kamaku da duka.
        Ƙasa duk sukai da kawunansu musamman Captains da Major Imran. Yayinda shi kuma ke ƙara hasala, ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya ya goge wannan zuwa gida nashi. Duk da ya san zamansa a jejin bazai hana komai ba matsayinsa na mutum kamarsu, amma yana jin kamar shine sanadin komai, kamar anyi amfani da tafiyar tasa ne aka tsara komai.
          An kwashe sojojin da suka raunata da wasu a mutanen gari da suma suka ji raunuka. Gawarwakin kuwa aka shiga gidaje da su akai musu wanka aka shiryasu cikin likafanin da su Zak-Shadow suka bayar. Haka aka jera su reras abin tashin hankali akai musu salla su arba'in da uku. Harda su Zak-Shadow akai sallar, sannan aka haɗasu a babban rami guda ɗaya da aka haƙa.
       Tuni rahotanni sun fara fita ga jama'ar gari, dan har sallar da sojojin sukama gawarwakin sai da aka nuna. Hankali ya matuƙar tashi, zantuka suka fara kai-kawo barkatai, dana gaskiya dana ƙirƙira. Yayinda anan cikin jeji su Zak-Shadow suke sabon shiri. Dan sun bar ƙauyen Gangare bayan an zuba sojoji tako ina suka shiga ƙauyen marke da shi ma aka kaima harin duk a daren jiya. Anan ɗin ma akwai sojojin, sannan harin baiyi tsamari kamar na Gangare ba, dan ba'a rasa rai ko ɗaya ba. Wanda suka jikata kuwa an kwashe su zuwa asibiti cikin birni kamar na Gangare.
      Suna cikin ƙauyen Marke suka sami rahoton gaggawa daga sojojinsu cewar a ƙauyen Bankaura an rasa yara matasa har guda hamsin da wani abu maza da mata. Cikin tashin hankali Major Imran da Zak-Shadow suka ɗauki hanyar ƙauyen Bankaura tare da wasu sojoji. Suna shigowa ana kiran sallar magriba. Sun sami garin a hargitse, iyayen ƴaƴa nata koke-koke cikin matsanancin tashin hankali. Tun ba'aje da nisa ba Zak-Shadow ya fahimci koma yaya ne ba'akai ga fita da yaran a garin ba sai dai wasu a ciki. Sannan dole-dole akwai bakin wasu a garin, dan wannan tarko ne na da ɗan gari akanci gari.
     Tuni yasa sojoji suka zagaye duka ƙofofin shiga da fita na garin. Tun a daren suka fara bincika wasu gidaje daki-daki. Binciken daya sa aka fara zaƙulo wasu makamai a wani gida an ajiye ƙarƙashin gadon matar gidan. Ta kuma rantse akan bata san wanda ya ajiyesu ba, kuma ko miji bata da shi ALLAH yay masa rasuwa sai yaranta huɗu duk bama masu wani girma ba. Amma babban an haɗa da shi a yaran da aka sace dudu kuma bai wuce shekara sha biyar ba.
     Kasancewar an sake haɗa musu na'urar sadarwa a yammacin yau cike da bada umarni Zak-Shadow yasa a kawo musu wasu na'urorin, dan tabbas akwai magana a cikin wannan ƙauyen na Bankaura ƙwarai da gaske. Sojoji sun cigaba da shiga gidaje, inda bincike ya ƙara tsauri matuƙa hatta inda bakai zato ba a gidan ka sai an bincika kuwa. Wannan kuma umarni ne daga oga kwata-kwata, wato Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu (Zak-Shadow), ba kuma sojojin ne kaɗai keyi ba harda baradan karnukansa da suka samu training mai wahalar gaske dako su sojojin bazasu nuna musu komai ba....

<<<<★><★>>>>

        Duk wanda ya kwana ya tashi a garin bankaura in dai ya kai shekarun banbance rayuwa da mutuwa barci sai dai ɓarawo ya ɗaukesa amma bana zahiri ba. Waɗanda ma aka ɗaukewa yara sun kwana ne suna kukan tashin hankali. Da asubahi sai sojoji ne sukai kiran salla, dan babu wani mai kiran salla daya fita balle liman ko mamu. Kai sallar ma a cikin gidaje wasu basuyita ba sai da rana ta haska.
          Anan kuwa mituniyarku Nimrah sarkin rikici da ire-irenta dama barcinsu suka sha hankali kwance. Tana farkawa ma ta fito tsakar gida abinta wai zata wanke ido, sai da Umma ta kamata da ƙyar ta maida ɗaki. Kuka ta fara da tirje-tirjen ita yunwa take ji, “Umma ki barni naje gidan Iya mai koko na sayo”.
       Baba ne ya kamata ya zaunar kusa da shi, cikin lallashi ya ce, “Uwa kiyi haƙiri, idan yunwa kike ji a saka miki fura kisha da ƙuli, yau iya mai koko bata koko dan garin namu ba lafiya”.
         Cikin rashin fahimta Nimrah tace, “Baba zazzaɓi akeyi?”.
     Kafin ya bata amsa sojoji suka shigo gidan. Dan sai yanzu ne aka iso ta bangaren gidajen su. Gida ne gidan yawa, dole sojojin suka kasu kowane ɓangare.........✍🏼




_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 43_

__________________


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7
Mmn surayya me kayan kamshi
Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa
Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada
Turaran wuta na danal banat
Kajiji
Turaran kaya watau abbasiyya
Kabbasa spray
Humra
Kwallacca
Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu
Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇
08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina.
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Kaf gidan sai da kowa ya fito tsakar gida suka fara bincike a kowane sashe. Nimrah uwar magana sai son sakin zance take yi Umma ta toshe mata baki da hannu. Sojan dake bincike a sashensu ne ya fara fitowa hannunsa ɗauke da botiki, gaban shugaban su ya ƙaraso dake tsaye inda kowa na gidan yake...
        “Mun samu bullets da yawa a nan ɓangaren”.
    Yay maganar dai-dai yana ajiye bitikin gaban ogan ya fiddo jakar dake ciki. Wani irin bugawar zukata Baba da Umma suka samu a tare. Musamman da Captain Musa ya buga tsawa da faɗin, “Suwaye masu wannan sashen?”.
       Rikicewa Umma da Baba suka sake yi, a take suka fara rantsuwar su basu san da jakar bama a sashen nasu. Zaram Nimrah dake kallon jakar ta ce, “Umma kwai ne a ciki fa”. Sai kuma ta zabura gaban sojan tana cigaba da faɗin, “Kai Baba ɗan sanda ƙwan Inna ne a ciki ka ɓoye kada ta gani ta dake ni”.
      Yanda tai maganar ƙasa-ƙasa cikin raɗa tana cacumar jakar ta maida a botikin yasa sojojin zuba mata ido, sai kuma Captain Musa ya kai duƙe gabanta ya riƙo hannunta, jikin ƙafarsa dake tsugunne ya jingina ta, fuskarsa da murmurshi ya ce, “Ƴata miye sunanki?”.
       Kai tsaye ta ce, “Zakanyar Kawu Tanimu”.
Kaɗan ya rage yay dariya, dan yanda tai maganar, amma sai ya danne ya ce, “Bayan Zakanyar Kawu Tanimu sai wane suna kuma?”.
Ta ce, “Naja'atu. Nimrah. Uwa. Sunana da yawa”.
    Murmushi Captain Musa yayi yana jinjina kansa da shafa kanta. “Sunayen kuwa masu daɗi, kamar yanda kike mai ƙyau kema. Kince ƙwayayen Inna ne a cikin wannan jakar? Ya akai ke kika sani?”.
       Inda mutanen gidansu suke ta kalla, ganin duk ita suke kallo ta kauda kanta da kai ɗan bakinta wajen kunnen Captain Musa cikin raɗa ta ce, “Jiya da Umma ta aikeni kai mata tuwo naga ƙwanta a akurkuki shine na ɗauka nasa a botikin, to sai ban ɗaukama Baba ba shima da Kawu ta dawo, shine na ɗakko duka jakar dan karta kamani, kaga ai zata iya zaneni ni kuma bana son duka”.
       Kanta ya ƙara shafawa yana murmurshi, sai kuma ya miƙama sojan dake kusa da shi hannu. Da sauri ya miƙa masa waya. Danne-danne yay ya kai kunnensa yana miƙewa tsaye, hannunsa ɗaya riƙe da nata. Sai da ya ƙame kamar yana a gaban ogan da ya kira sannan ya ce, “Sir mun sake samun harsasai da adadinsu zai kai dubu biyu a wani gida”.
    Banji mi akace masa daga can ba, yanda dai ya ɗan buga ƙafa da sake ƙamewa ya ce, “Yes Sir!”. Zai baka tabbacin umarni aka bashi. Daga haka ya sauke wayar ya miƙama yaran nasa. Idonsa ya maida ga mutanen gidan da sukai tsuru-tsuru cikin matsanancin tashin hankali. “Wacece Inna? Tare da iyayen yarinyar nan?”.
      ALLAH sarki su Umma duk sun ƙara gigicewa, musamman Inna da al'amarin ya haɗa da tsufa, tuni ta jiƙe jikinta da fitsari, jikin sai rawa yake yi sai da Umma ta kamata. Gefe aka maida su, babu jimawa Zak-Shadow ya shigo gidan baradan sojoji kusan huɗu biye da shi. Ƙamewa sojojin sukai a tare, suka sara masa. Hannunsa dake dunƙule kawai ya ɗan miƙar alamar amsa girmamawarsu. Fuskar nan kam ba sauƙi babu sassauci. Dan su kansu mutanen gidan su Nimrah shigowar tasa sake gogitasu tayi, kai da gani kasan BARADAN MAZA ne da kansu ba saƙo ba. Duk rashin tsoron Nimrah tana haɗa ido da shi da sauri ta koma bayan Captain Musa ta ɓuya tana ɗan leƙosa kaɗan da ido ɗaya.
       Zak-Shadow ya bi duk mutanen gidan da kallo irin na nazari, kafin ya ɗauke kansa ya maida ga sojojinsa, a nan ne ya hangi Nimrah dake ɓoye jikin ƙafafun Captain Musa.
       Da sauri Captain Musa ya shiga yima Zak-Shadow bayanin tattaunawar sa da Nimrah cikin harshen turanci. Sai da ya gama tsaf yana saurarensa sannan ya maida dubansa ga Nimrah. Abin mamaki a karo na farko yay mata wani ɗan murmushi, sai kuma ya muƙa mata hannu da muryar lallashi ya ce, “Zo Baby girl”.
       Kalmar Zo ɗin kawai ta fahimta, ta kuma san kiranta yake, dan haka ta maƙe kafaɗa alamar a'a, dan bata taɓa cin karo da mutumin daya bata tsoro da cika mata waje irinsa ba, ko babanta mutum ne mai sanyi hali da rashin hayaniya, bai taɓa dukanta ba, idan yaga Umma ma zata daketa shike cetonta. Haka ma Kawu Tanimu da kowa ke ɗaukarsa masifaffe a gidan, ita sangartata yake ko laifi tai baya dukanta. Risinawa Captain Musa yayi ya gwargwaɗa mata magana a kunne kamar yanda tai masa ɗazun. Karo na farko ta ɗago tana kallon Zak-Shadow. Sai kuma cike da ƙuruciya tace ma Captain Musa, “Da gaske baba ɗan sanda?”.
        Kai Captain Musa ya jinjina mata yana murmurshi. Kallon Zak-Shadow Nimrah ta sake yi, ganin har yanzu yana murmurshi sai ta nufesa da sauri. Hannu ya saka ya ɗauketa gaba ɗayanta, ɗaukar da ta saka Umma kallonsa hankali tashe. Wani mugun waro idanu tayi a kansa, jikinta da bakinta na ɗan rawa cikin suɓucewar harshe ta ce, “Bawan ALLAH kai ne?”.
      Ganin wanda take kallo take maganar yaran sojin suka daka mata tsawa, sai lokacin shi Zak-Shadow ma fahimci da shi take, karo na farko ya dubeta, kai tsaye kuwa ya gane ta, dan dama tunda ya kalla Nimrah zuciyarsa ke yi kamar yasan fuskarta, ashe kamanin mahaifiyarta ne. Hannu ya ɗagama sojan da ke mata tsawa, ita kuma duk ta firgice dan gani take harbeta sojan zaiyi. Zak-Shadow baiyi magana ba sai kallonsa daya maida kan Nimrah Ummanta kamar zatayi kuka. Cikin son kawar mata da hankali ƙasa-ƙasa ya ce, “Muje ki nuna min inda ƙwan Inna yake mu kwaso sauran ma, duka zan baku shi ke da mamanki”.
       Hawayen da take riƙewa na zubo mata ta ce, “To kace Kada Baba ɗan sandan can ya bugar min Umma na”.
         “Bazai bugeta ba ai”.
    Captain Musa ya faɗa cike da lallashinta shima. Sun motsa zasu tafi tace ita sai da Ummanta, babu yanda suka iya da wannan mulkin mallaka na Nimrah dole akabi yanda take so. Umma ce ta kaisu har sashen Inna, Zak-Shadow kam na ɗauke da Nimrah har yanzu. Sai da suka isa sashen ne ya sauketa ya riƙe hannunta, babu ko gargada ta kaisu inda akurkukin Inna suke jere da yawa dan tana kiwon kaji, zabbi sosai har ma da agwagi.
        Cikin bada umarni Captain Musa ya dubi yaransu uku dake biye da su, ai cikin sauri suka shiga bincike akurkayen ɗaya bayan ɗaya. Aiko abin mamaki daban tsoro sai ga abubuwa ana zaƙulowa. Ai tuni an shiga fancake komai dake sashen Inna, itama kuma an taso ƙeyarta. Baiwar ALLAH kuka take tana ƙari da rantsuwar bata san da wannan ajiya ba sam. Hasali ma bata san Nimrah ta ɗauki waccan jakar ba, ta dai ga an ɗiba mata ƙwai biyu, ta kuma san itace ke mata haka, wani lokacin ta kai cikin kajinsu wani lokacin tace zata soya taci.
        Ba ɓangaren Inna kawai ba gidan gaba ɗaya aka shiga masa filla-filla, yayinda aka tattare mazan kaf waje ɗaya, aiko mata da yara nata kuka. Bincike yay bincike har cikin rijiyar gidan da rumbuna ba'a bari ba, an ko samu abubuwa da yawa da sukafi na sauran gidaje da aka samu, kuma abin mamaki an rarrabasu a ɓangarori da dama ta yanda baka isa cewa tunda a sashen wane aka gani ba shine ya ajiyesu. Dole dai aka tattara su Baba da ƙanensa da yayunsa duka su kusan goma sha shida mazan gidan, idan ka cire Tanimu da yay tafiya a jiya da safe kowa yana nan.
      An bar wasu sojoji a gidan dan tabbas suna buƙatar tsaro, dan dole ne akwai mai alaƙa da su Dagger a gidan, idan kuma suka ji an samu kayan da ke gidan zasu biyo sahu na ganin sun ɓadda mai alaƙar da su ko ɗaukar wani mataki...

     
<<•>><<•>>•<<•>>

         Kwanaki biyu kenan su Baban Nimrah na hannun su Zak-Shadow. Hatta Kawu Tanimu daya wuce birni anje an taho da shi. An kuma samu wasu tsirarun yara cikin waɗanda aka kwasa a garin a wani gida, sauran kuwa da alama an riga an fita da su. Har yanzu waɗan nan ƙauyukan suna zagaye ne da sojoji, musamman gidan su Nimrah dake cikin haɗari fiye da kowane gida a ƙauyen Bankaura, sai gidaje huɗu da suma aka samu makamai da yara tara cikin wanda aka sata.
        Tun waccan ranar Zak-Shadow bai sake shigowa ƙauyen ba dan yayi busy sosai, bincike suke babu wasa shi da su Imran da sabbin jami'ai da aka ƙaro musu. Yayinda su Captain Musa da sauran Captains ke aikinsu bisa jajircewarsu da yaran soji tako ina a cikin jejin. Yanzu ma sunzo yin wani sabon bincike ne a nan cikin gidan su Nimrah ɗin ta hanyar zanen hannun kowa, suma mazan gidan dake hannunsu duk an ɗauka acan sansani.
         Sun sami Nimrah na darzar kuka da birgima ita bazataci garin kwaki da Umma ta jiƙa ba shinkafa zataci. Umma kuwa ta zuba mata ido kawai tana kallo dan tashin hankalinta yafi ƙarfin rigimar Nimrah. Ba ita kawai ba duk macen dake gidan tana cikin tashin hankalin tafiya da mazansu da sojoji sukayi, ga yara babu su babu labarinsu dan har yanzu ba'a samo su ba. Imran sarkin son yara da tausayi ne ya zo har inda Nimrah take bori ya ɗagata cak batare daya damu da yanda tai buɗu-buɗu cikin ƙasa ba. Shi dai Zak-Shadow kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, sai da tai wani furuci ma Umma ya juyo a karo na biyu ya ɗan kalleta.
          Cikin kuka Nimrah ta sake maimaita, “Kuma sai naje na kira fatalwoyin bayan gida masu jan ido su saka ki a jakarsu su tafi dake tunda bazaki dafa shinkafa ba”.
      Mutane irin su Zak-Shadow nada wata baiwa ta tsarta da saurin tsarguwa. Sannan inda suna a gaɓar aiki basa raina abu komai ƙanƙantarsa koda ga waye yazo. Imran nama Nimrah murmushi da faɗin, “Yi haƙuri Baby kada ki kira ma Mama fatalwa in dai shinkafa ce ina da ita zan baki....”
       Zak-Shadow daya ƙaraso inda suke idonsa akan Nimrah da tunda ta hango yana tahowa ta ƙanƙame Imran da lafewa a jikinsa dan tsoronsa take ji. Yana isowa ta sake ɓoye fuskarta sosai a jikin Imran ɗin. Kai kawai Zak-Shadow ya ɗan girgiza, kafin ya saka hannu a aljihu ya ciro Dabino da yake yawan ci dan yana matuƙar son shi, zai iya ci miki dabino yasha ruwa matsayin abinci. Ɗan hannunta ya kamo ya saka mata, a karo na farko ta ɗan ɗago cike da shakka ta kallesa tare da hannun nata. Murmushi ya mata kamar ranar, sai ta tashi da ƙyau tana dariya cike da farin ciki.........✍🏼

Tunda aka ba Nimrah dabino aiko za'a sha labarin fatalwoyin bayan gida kenan, yau zamu san mai ɓoye fuska.🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😂
      

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 44_

__________________

*🔥 RASH BEAUTY WORLD 🔥 duniyar kayan mata masu kyau da arha ,Ina masu son kaya na kyan gani, amma basu son tsada? To, *ki daina nema!* Rash Beauty World ta zo miki da komai:

*👗 Abaya masu kyau na zamani Egypt/dubai*
👜 *Bags masu kyau*
*👠 Takalma masu ɗaukar ido*
💍 *Jewelry masu ƙyalli kamar na sarauta*
🍽️ *Kayan Kitchen masu amfani da kyau*

*Koma da Naira kaɗan za ki yi shopping kamar sarauniya!* 👑💃

✅ Farashi mai sauƙi
✅ Kayamasu quality
✅ Fast delivery


*Shiga group dinmu yanzu kiga sabbin kaya ,Kayanmu masu kyau ne kuma farashi mai sauƙi!
Kar ki bari a baki labari don samun kayayyaki masu inganci*
👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/GzcU1TcAem21oJedkisrhj?mode=wwt

*RASH BEAUTY WORLD – Inda kyawu da araha suka haɗu!*
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Hannu ya miƙa mata shima yana cigaba da murmushin nasa dai, babu musu ta tafi wajensa. Cikin wayo da dabara ya tambayeta miye fatalwa? Yaushe ta ganta kuma?. Yo har a gayama Nimrah zance, ba'a tambayeta ba ma faɗa take balle wannan harda cin hanci aka bata. Ai tsaf ta shiga bama Zak-Shadow labarin fatalwoyin bayan gida. Koda yace zata kaishi ya gani? Sai ta bashi amsa da, “Ai sun gudu tun ranar, koda na raka su Fatsima ma da sukace zasu gani babu kowa sai dai mun samo jarkoki harda nama”.
      (Anzo wajen) Cewar Zak-Shadow a zuciya. Dabino ya sake cirowa a aljihu ya bama Nimrah, sannan ya fita da ita su Imran biye da shi ransu fal mamakin al'amarin wannan yarinya. Ranar fa da taimakon ALLAH da wayon nan nata suka gano makamai na ban mamaki a gidan, yau kuma ga wata sabuwar magana da tabbas tunda sukaga oga ya maida hankali akai tana da muhimmanci. Tsaf Nimrah ta dinga nuna musu hanya har cikin gonar nan da taga mutanen ranar da take kira fatalwoyi. A kallon farko kuwa sojojin suka fahimci gaskiyar zancenta. Dan har yanzu akwai alamar mutane sun zauna. Sauran takardun nama da yaran basu ɗauka ba saboda an cinye suna wajen duk da iska ta ɗan ɗaukesu sun matsa, sai kashi a gefe dake nuna alamar na gardawane da kufan fitsari da akayi, ɓawon ƙwai da akaci da sauran sigari da akasha.
      Nimrah na cin dabinonta ta nuna wani waje tana kallon Zak-Shadow. “Baba ɗan sanda, kuma anan naga wani mai irin kayan Babana zaune shima ya rufe fuskarsa saboda tsoron fatalwoyin”.
       “Babanki?”.
   “Eh mana”. ta faɗa cikin shiririta tana cin dabinonta.
          Kallon kallo akai tsakanin Zak-Shadow da Imran. Imran ya maida hankalinsa kan Nimrah, cike da wayo ya ce, “Shine kuma baki masa magana ba?”.
       “Ai tsoro naji na fatalwoyin, kuma ya rufe fuska fa, shima kaga ai tsoron su yake ji ko baba ɗan sanda?”.
      “Miyasa baki faɗama mamanki ba?”.
     “Na faɗa mata ita da Inna sukace na cika surutu, shine na gayawa su Fatsima sukace ƙarya nake, niko na rakosu harnan fatalwoyin kuma har sun gudu”.
      Wani irin cije baki Zak-Shadow yayi, zuciyarsa na hasaso masa tabbas akwai ɓoyayyen al'amari akan mahaifin yarinyar nan. Barin wajen sukai suka koma can gidan su Nimrah. A karo na farko Zak-Shadow ya buƙaci zama da Umma dake cikin tashin hankali tunda suka fita da Nimrah, sai dai ganin sun dawo ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Dan haka ma koda Zak-Shadow ɗin ya nema suyi magana bata musa ba. Tabarma ta ɗakko ta kawo ƙarƙashin inuwar ceɗiya dake a sashen nata. Dan haka kawai take jin girman mutumin nan a ranta tun randa suka fara haɗuwa shekarun baya. Bai musa ba ya zauna shi da Imran. Ita kuma zata zauna ƙasa yace ta ɗakko wata tabarmar. Ɗaki ta koma ta ɗakko tabarma ta shinfiɗa itama ta zauna.
     Shiru wajen ya ɗauka kafin ta motsa baki cike da ƙarfin hali ta ce, “Kayi haƙuri da abinda nayi ranar, ban san kuskure bane ba. Wlhy farin ciki ne kawai ya kamani na ganinka saboda tun wancan shekarun da muka haɗu nai maka alƙawarin baka abinda na haifa sai nake yawaita mafarkinku a barci na. Kullum kuma cikin addu'ar ganin ba haifi namijin da zan baka ba nake, amma har yanzu ALLAH bai cika min burina na ba”.
       Karo na farko Zak-Shadow ya kalleta, kai tsaye ya furta, “Ina abinda kika haifa wancan karon?”.
     Cikin sauke ajiyar zuciya ta kalla Nimrah dake wasa da ƙasa gefensu kaɗan, “Itace waccan da kuka fita da ita ɗazun”.
      Daga shi har Imran kallon Nimrah sukai suma. Imran dake murmushi ya ce, “Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarta. Minene sunanta?”.
      “Naja'atu, amma muna kiranta Nimrah saboda sunan mahaifiyar maigidana ce.”
     Ɗan huci Zak-Shadow yayi kaɗan, ƙasa-ƙasa ya ce, “ALLAH ya rayata”. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Ranar tace miki taga fatalwa a bayan gida, miyasa baki saurareta ba?”.
          “Nimrah nada surutu sosai, shiyasa nakan ƙwaɓeta da irin waɗan nan abubuwan saboda tarbiyyarta matsayinta na mace”.
     “Hakan ba laifi bane, amma yana da ƙyau idan yaranmu sukazo mana da maganar abinda ba kasafai ake zancen sa a cikin al'umma ba mu basu lokacinmu, idan na gyara ne mu gyara musu, ko muyi musu ƙarin bayani ta yanda zasu fahimci abin a yanda yake. Idan ba haka ba zasuje su faɗa a inda bai dace su faɗa ɗin ba, maybe ya cutar da su, ko kuma ya zama na cutarwa ga kowa. Yanzu kamar ita zancen fatalwa data kawo miki mutanen da sukai muku ɓarna da ɗibar yaranku ta gani a wannan ranar, da kin saurareta da kin fahimci abinda take magana akai, koda bazaki iya ɗaukar mataki ba zaki iya faɗawa maigari, kinga kin taimaki garinki da al'ummar garin. Saɓanin haka kuma kinga sakamakon daya kawo.”
        Ba ƙaramin tashi hankalin Umma yay da bayanin Imran ba. Ta zubama Nimrah ido da har yanzu ke wasa hawaye na silalo mata. Imran ya sake katseta da faɗin, “Minene sana'ar mahaifinta?”.
        “Manomi ne kamar sauran mazan garin, sai sana'ar kifi da

Please Login or Register in order to submit comment