You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

09025576222

💃💃TALLAH TALLAH💃💃

*INA MANYAN MATAN SUKE?*
*Masoyana ina ƙara talalta muku kayan sana,ata kamr su*

*Less, atamfa, laffaya, kamfala, mayafai zannuwan gado, kayan yara, takalma na yara da manya, abayas, huluna na maza, mata, yara frames, sarƙa ɗan kunne zubuna banguls.*

*Akwai kayan maganin mu na kamfanin meera b herbs, maganin sanyi, maganin ƙiba, maganin rage ƙiba maganin rage tumbi, maganin cire tabo ga wanda suk shafa mai ya ɓata musu jiki ko fuska, sannan uwa uba maganin mata.*

*A ƙarshe ina tallata muku FURA dakan mai, wacce muke yi mai garɗi da ƙamshin man shanu, muna yi don biki, ko suna, ko taron naɗin sarauta da dai sauransu muna aikawa ko ina, akwai nono galan galan da bokitai ga masu buƙata, ku nuna min ƙauna ta hanyar siyar abin da nake siyarwa* .

*Mai so ya min magana a number ta 09025576222 idan ba saya za ki yi ba kar ki min mgn.*


https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c


👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal Da sauransu
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*


BOOK1️⃣
PAGE 8

Sanye take da doguwar rigar less wacce ta kama jikinta, ta yi ɗaurin ɗankwali wanda ya zauna daram a kanta sai mayafinta wanda yake kala ɗaya da leshin da ta saka, ƙarami ne mayafin yana rataye a gefen kafaɗarta ɗaya. Ƙaran takalmin ta mai tsine wanda take sakkowa da saman benen shi ne ya janyo hankalin Hajiya da take zaune a kan kujera tana waya.

Tana riƙe da wayarta ta ƙaraso tsakiyar rangameman falon, lokacin ya yi daidai da gama wayar Hajiya. Ɗagowa ta yi ta kalle ta, ta ce

"Inyeee ka ga ƴan matan Daddyn ta, kyakkyawar mace kuma matar manya ƴan boko masu faɗa ji, sanann matar masu kumbar susa" Wani daɗi ne ya mamaye zuciyar Rahma tana jin daɗi jin furucin da Hajiya ta mata, tabbas a duniya ta tsani talaka, ta tsani talauci kuma, tana son saurayi ɗan manya wato ɗan gidan masu kuɗi sannan ɗan gayu ko ma dai yaya yake in har za a iya nunawa sa,a shi to tana son shi sosai. Kai ta langaɓae gefe cikin shagwaɓaɓɓiyar fuskarta ta ce

"Ai ni sai na zaɓa sai wanda ya isa ne zai aure ni Mummy bana son duk wani namiji in har bashi da masu gidan rana" Murmushi Hajiya ta yi ta ce

"Da gaskiyar ki ko ni talauci ya yi gabas na yi yamma, kuma ke da kika tashi a gidan naira ai dole sai ɗan naira" Murmushi ta yi ta ce

"Bari na je baby nah yana jirana" Hajiya ta ce

"Ya zo kenan" Rahma ta ce

"Eh ya zo" Tana faɗa ta kiya cikin takunta na maau aji irin na mata masu ji da kansu.

Yana zaune a wajen da aka tanada don zama a sha iska zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun wajen, hango ta ya yi ta taho tana tafiya tamkar tarwaɗa, tana tafiya tana yanga da wani jan a ji da mata masu aji ne kawai suke yin irin taku. Sulaiman tun da ya hango ta kwacakwam ya mayar da hankalinsa a kanta, dama yana chartin ne da wata budurwarsa, amma ganin Rahma ta taho sai ya yi saurin kashe data ya sauka ma daga kan whatspp ɗin gabaɗaya.

Ma'aruf yana daga can ɗaki ya zo buɗe labulen window saboda ya ji ɗakin ya ɗauki zafi, dama dawowarsa daga makaranta kenan, ya shiga ya yi wanka shi ne zai shirya. Ganin Rahma sai ya ji gabans ya faɗi, musamman da ya hango irin kallon da Sulaiman yake mata mai cike da soyayya. Kishi ne ya tsaya masa a rai. Idanu ya runtse yana jin irin yadda zuciyarsa take bugawa.

Da son samu ne yana so ya samu ko da kwatar matsayin da Sulaiman ne ya samu a wajen Rahma, shi in ba ma jarabawa ba da kuma zuciya da baka tursasa ta, ina shi ina kamauwa da son Rahma bayan ya san ko suma yake yana falkowa ba zai same ta ba.

Cike da jin haushi ya rufe labulen dan sai ya ji gwara ya dawwama a cikin zafin ɗakin, a kan ya bar windown a buɗe yake kallon takaici.

Rahma kuwa ƙarasawa ta yi tana ɗan murmusawa, ta samu kujerar da take kallon ta Sulaiman ta zauna, idanun da ya kafe ta da su, hakan ya sanya ta sakar masa da wani shu'umin murmushi mai bayyana haƙora, yadda hakoranta suke a jere reras kamar masara sai ya ji ya ƙara mutuwa a kanta, ya san za a saka Rahama a sahun farko na kyawawa.

Cike da murya irin ta mayaudarin namiji, irin muryar da dama ta saba da yi digiri a yaudara ya ce

"Sannu da zuwa sarauniyar matan duniya, alkairin Allah yana lulluɓe da ke, ina so ki sani mutuwa ce kawai za ta raba mu, don na san na gama dacen mace ta kece raini ta nunawa sa'" Ya faɗa yana kafe ta da idanunsa wanda har aai da ya sa ta ɗan sunkuyar da kai tanaƴar dariya kaɗan.

Hannunsa ya miƙaya ajiye wayarsa a kan teburin da yake a tsakiyarsu ya ce

"Da a ce zan mallake ki da kuwa na gama dace a duniya, ke ni bana jin zan sake bacci a duniya, don an sallame ni, a baya in jin tamkar wanda na rako maza duniya, in na ga suna da budurwa mai aji kuma ana nuna musu kulawa da soyayya ashe dai ni ɗin ma zan samu rabona"

Sai da ta ɗago fuskarta ta sauke idanunta a cikin nasa sannan ta ce

"Ba kai kaɗai ne ka yi sa'a ba ni ɗin ma har kullum ina alfahri da kai, yanzu daga zuwana ko gaishe da kai ban yi ba amma kana ta zuba mini yabo" Ta faɗa don kaf ta rasa inda za ta saka ranta, tana son ta ji ana yabonta ko ana koɗa kyawunta sai take ji kamar duk duniya babu kyakkyawa kamar ta.

Idanu ya lumshe ya buɗe su tarrr a kan nata idanun yana jifanta da wani kallo na mayaudara wanda duk macen da akw mata sai an sace zuciyarta ya ce

"Ke ɗin ce kin cancanci haka, ke ɗin ce duk kin rikita mini lissafi, bana iya kallon kowace mace sai ke, bana son kowacce mace sai ke, har abada na gama zamar mace sauran duk kallon maza nake musu" Wani mugun daɗi take ji

Tana kallonsa yana kallonta, hannunta da ta ɗora a kan teburin ya miƙa hannunsa ya ɗora a kan hannunta, Ma'aruf da fitowarsa daga ɓangarensa kenan sanye yake da farin yadi ɗinki tazarce yadin marar nauyi, ya yi matukar karɓar jikinsa, Sulaiman ganin Ma'aruf ya fito ya yi saurin janye hannunsa, ita kuma da yake ta ba Ma'aruf baya bata san ya fito ba, kuma ita bata ma ɗauki cewa taɓa hannun nata wani laifi ne da har za ta janye hannunta, tun da tana ganin yanzu dan ma saurayi ya taɓa hannun mace ma wani abun ƙarama bane, tun da yanzu har wajen hoto saurayi da budurwa suke zuwa, kuma a kama hannun juna, har ma da abin da ya fi hakan, kuma a ɗora a status mutane su gani babu mai cewa an aikata haramun sai dai ake cewa sun yi kyau, idan aka samu wanda ya ce hakan bai dace ba, sai a ce ai saurayin da za ta aura ne, ko a wane hadisi ko ayar aka bayyana haka? Kawai dai ƙarshen duniya ne duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba.

Ma'aruf zuciyarsa ce ta fara tafasa shi fa dama ya lura cewa duk mazan nan da suke son Rahma ba wai son aure suke mata ba duk mayaudara ne. Wani mugun kallo yale jefaw Sulaiman daga nesa, Rahma ce ta lura da Sulaiman hankalinsa ba ya kanta baya ta waiwaya ta ga Ma'aruf ta yatsina fuska ta ce

"Baby mene ne" Ta faɗa lokacin da ta mayar da kallonta kan Sulaiman ɗin.

Haushi ne ya kama zuciyar Ma'aruf jin Rahma ta kira Sulaiman da wanann sunan, sunan da ko a mafarki zai ji daɗi ta kira shi da shi, shi ya rasa ma yaushe ya kamu da son Rahma abin nan yana ci masa tuwo a ƙwarya ya san dai ko a tsarinsa babu mace irin Rahma, wacce bata san darajar ɗan adam ba amma gashi so yana neman ya kai shi ya baro.

Idanu Sulaiman ya ɗauke jin Ma'aruf yana masa kwarjini, shi dama ya tsani ya zo gidan su Rahma ya ga wannan baƙauyen da bashi da komai sai gidadanci da rashinw wuyewa. Ma'aruf kuwa ji ya yi da a ce yana da dama da ya je ya kora Rahma cikin gida, sai dai bashi da iko da wannan damar.

Sulaiman ne ya yi ƙasa da murya ya ce

"Baby ki sa wannan baƙauyen yayan naki ya kawo min ruwa" Ta kalli Sulaiman cike da jimanta abin da ya ce ta ce

"Ruwa kake so sha bari na kira Mummy ta sanya ƴar aiki ta kawo" Yana ɗan haɗe rai ya ce

"Ni ba na son wata ƴar aiki wannan nake son ya kawo mini" Murmushi ta saki cike da kulawa ta ce

"Kar ka damu ai yanzu kuwa" Ma'aruf da ya nufi get zai fita so yake ya je masallaci ya karanta qur'ani ko ya samu sauƙi da salama a zuciyarsa, jin ƙaran wayarsa da take aljihu ya fito da ita, ganin sunan Rahma abin ya bashi mamaki har sai da ya tsaya ya juyo don ya tabbatar da cewa ita ɗin ce take kiransa, don ya san saboda wulakanci irin nata kwanaki cewa ta yi ta goge numbersa saboda bata son take jin maganar baƙauye a kunnenta.

Juyawar da ya yi sai ya ga ita ɗin na wajen take kallo, kamar wasa sai ya ga tana ɗaga masa hannu alamar ya zo, bao je ɗin ba kuma bai cigaba da tafiya ba don ya san wannan kiran akwai wani abu a ƙasa kuma shi bashi da wata daraja da zai rama ko ma mai suka masa, saboda tana faɗawa Daddy shikenan ko kuma Mummy wacce a dole son babu yadda za ta yi ne yake zaune a gidan.

Yana mayar da idanunsa kan wayar hakan ya yi daidai da tsinkewar kiran, yana katsewa ya ga wani kira ya shigo, juyawa ya yi yana tafiya ya ɗaga wayar ya kara a kunne yana lumshe ido, a hakan yake tafiya kasancewar gidan babban gida ne, akwai tazara daga harabar gidan zuwa get ɗin.

Yana karawa a kunne sai ji ya yi ta ce

"Na ce ba" Ta daɗa cike da iko da raini.

Cikin nutsuwa ya ce

"Ina jinki"

Ta ce

"Ka dawo ka ɗakkowa Sulaiman ruwa zai sha" Ransa ne kawai ya yi mugun ɓaci kasanceqar ya san al'adar Rahma ce ta tsani a kashe mata waya sai kawai ya kashe domin ita ma ya ƙunsa mata ɓacin ran da ta sa ya shaƙa.

Yana kashewa ya cigaba da tafiya har ya buɗe get ɗin ya fita waje.

Rahma ranta ne ya ɓaci kamar yadda ya yi zato, cike da jin kunya ta ce

"Ya ce sauri yake zai je wajen suturar abokinsa da ya mutu" Ta tsinci kanta da sheƙa ƙarya.

Sulaiman banza ta mata ko da ta ce za ta ɗakko masa da kanta sai ya ce ta bari ma ya daina jin ƙishin. Haka dai ranar hirar tasu ta wakana babu wani armashi. Da zai tafi ya shiga mota ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyar guda biyu ya bata wai ta sha ice cream. Motar ya shiga direbansa da yake ciki zaune yana jiransa ya tada motar, tana tsaye tana ɗaga masa hannu, har mai gadi ya wangale musu get suka fita tare da haurawa titi.

Tana komawa ciki ta kwashe abin da Ma'aruf ya mata ta faɗawz Mummy inda ta ringa faɗa ta inda take ahiga ba ta nan take fita ba, tana faɗin zai dawo ya same ta, tun da ba ubansa Mai Gari bane ya gina gidan, da har yana zaune ba za a amfane shi ba.

Daddy sai bayan magriba ya dawo gidan, ko da aka zo cin abinci Mummy ta kwashe komai ta faɗa masa na tsinka Rahma da Ma'aruf ɗin ya yi a gaban saurayinta, duk da Daddy ya san abin da Rahmar ta yi bata kyauta ba sai dai ba zai iya tsawatar mata ba saboda soyayya da kuma Hajiya ya san ba za ta bari a ga laifin ƴarta ba kasancewar ƴar tata ƴar ido ce. Ma'aruf dama sai dai ya ci abincinsa da ban saboda Hajiya da Rahma wai basa iya cin abincin idan yana waje zuciyarsu tana tashi, wai suna jin yana warin ƙauye, kuma kawai tsabar rainin wayo ne.


Sai da aka yi ishasha'i ya dawo don karatu suke tsakanin magriba da isha'i a masallaci, Daddy ne ya kira shi yana masa faɗan rashin gaskiya, Ma'aruf ya ce

"Haba Daddy ni ne fa gaba da Rahma amma sai ta aike ni kuma a gaban saurayinta, kuma ma saurayin fa zan ɗakkowa ruwa, duk ƴan aikin gidan nan, yanzu fa ko Yayan da ka ce take faɗa min ta daina Ma'aruf take kir...

Daddy ne ya katse shi da cewa

"Haba kai kuwa ana ga yaƙi kana ga ƙura, ana maganar baka je aike ba kai kana maganar bata ce maka Yaya.

Hajiya ce ta katse da cewa

"An ƙi a ce maka Yayan ubanta ne kai da sai ta girmamaka" Kai ya sunkuyar don ya san Daddy kawai yana tsoron Hajiya ne amma ai ya san shi ne da gaskia, haka ya masa faɗan ya tashi ya fita ya koma ɓangarensa.

*BAYAN SATI UKU*

Zaune take a lambu ta ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tana zaune ne bisa kujerar roba sai ta ɗora ƙafafunta a kan wata kujerar, jarida take dubawa sai kayan maƙulashe a kan plate a gabanta tana ci.

Tun da fa shigo lambun yake kallonta da yake idanunta a kan jaridar bata san da tahowarsa ba ma, sanye yake da riga blue mai ƙaramin hannu sai jeans baƙi sai ƙamshin turare yake mai daɗi.

Rahma da ta jiyo ƙamshin iska ta kawo mata ta lumshe idanu, don ƙamshin turaren ya mata, kasancewae sabo ne ya saya ƙamshinsa ya sha bamban da wanda yake shafawa. Sai da ya zo dab da ita ta ji ƙamshin ya ƙaru alamar ma ƙamshin ba iska ce take kawowa ba mai ƙamshin yana dab da ita. Murmushi ta saki, saboda ta san sun yj waya da Sulaiman ya ce zai zo su fita su shaƙata kuma ta faɗa masa tana zaune a lambu, a tunaninta shi ne ya zo zai tsokane ta take son ya rufe mata ido ko dai wani abu makamanci haka.

Cike da shauƙi ta ce

"Barka da zuwa Babynah" Gaban Ma'aruf ne ya faɗi yana tunanin ko dai addu'ar da ya kwana yana yi a kan Allah ɗora shi a kanta ta amince da shi, ita ce ta karɓu.

Ta cigaba da cewa

"Ƙamshin turarenka ne ya sanar da ni ƙarasowarka, zuciyata tana maka marhabin, tana maka tuni cewa da kai kaɗai za ta rayu!" Kaɗan ne numfashin sa bai bar gangar jikinsa ba, tsabar irin yadda maganar ta dake shi, a hankali ya fara taku a dawo gabanta, sai lokacin ta ɗago fuskarta daga kallon jaridar tana murmushi mai ƙara mata kyau da kwarjini.

A kan kyakkyawar ƙafarsa da take cikin baƙin takalmu ta fara yi wa idanunta masauki, ko a mafarki bata taɓa zaton Ma'aruf bane, cikin murya mai taushi, wacce take damfare da nutsuwa ya hau faɗin

"A nawa ɓangaren ma haka ne, da ke kaɗai za ta rayu, kuma zuciyarta ta janyo linzamina ne zuwa wannan wajen, don ta bayyana miki asirin da yake cikinta, tana fata da addu'ar mu rayu a tare har mutuwa...

Waɗannan kalaman sun sauka a kan dodon kunnen Sulaiman da ya nufo wajen, wanda kuma ya ƙara shiga kunnuwan Mummy da ta zo za ta sanar da Rahma cewa za ta fita, saboda ta kira wayar ta ta ji bata shiga ba, shi ne ta tasho don ta faɗa mata sai kuma kunnuwanta suka yi arba da wannan babbar maganar...




*INNA TASALLAH*


Zaune take a tsakar gida da yammacin ranar asabar, tana zaune hannunta riƙe da mangwaro irin mai ƙamshin gawasa, nunanne ne jawur da shi, tana sha tana lunshe ido har wani karkaɗa kai take saboda zaƙin da take ji har tsakar kanta.

Tana a wannan halin Lami ta shigo da sallama, idanu Inna ta buɗe ganin Lami afujajan ta dakata da shan mangwaron ta ce

"Lami lafiya kamar an hakaɗo ki?" Lami cike da jin haushin Inna tana wani ɓata rai ta ce

"Wato ke Inna har kin samu damar sha mangwaro har kina lumshe ido" Galala Inna take kallonta cike da takaici ta ce

"Haba Lami wai ni ku mutane mai ya sa bakwa son ku ga wasu sun ci gaba? Da raina da lafiyata ma ba zan sakata in wala na sai ana sanya min ido, yanzu kayan miyana sun ƙare duka don cikin ribar na ɗauki naira talatin na saya mangwaro in sha a ruwan raina shi ma sai ya zama ana mini baƙinciki, mutane bakwa so ku ga mutum duniya tana gara masa, wato kun fi so ake zaman kashe wando...

Wata harara Lami ta aikawa Inna ta ce

"Inna tsakani da Allah ko ana yi wa wani baƙinciki wa zai miki, ni wallahi a sana'ar kalwa da barkono da kuka ban ga abin baƙinciki ba" Kamar Lami ta yi saɓo haka Inna ta zaro ido ta ce

"Kina wasa da maƙiyi, maƙiyi ai shi ko alawa kake siyarwa sai ya maka baƙinciki, yanzu ni a wajena ai cigaba na samu tun da gashi a cikin ribar har ina shan mangwaro" Ta faɗa tana gutsuro fatar mangwaro,
Lami a zuciyarta ta ce

'Yanzu zan rikita miki lissafi, yanzu za ki kiɗime don na tabbatar baki san da abin da nake tafe' A fili kuma sai ta ce


"Inna saƙon kira ne aka bani wajenki" Sai da ta suɗi mangwaron ta ce

"Kai zaƙu har cikib kaina wallahi, wannan mangwaro da zan samu iri ai da na shuka, to ke waye yake kirana in ka ji kira ai samu ne"

Baki Lami ta damƙe cikin dakewar murya ta ce

",Inna, ina ce dai kina sane yau kwana ukun da Mai Gari ya ɗauka a kan maganar saniyar da Ibra ya tafi da ita" Tari ne ya sarƙe Inna jin wata gagarumar matsala sabod ita kwata-kwatanta manta don maganar ta kwanta mata , sanadin tarin da ta yi mangwaron hannunta ya suɓuce ya faɗi a ƙasa amma ko ta kansa bata bi ba ta ce

"Lami waye ya faɗa miki wannan magana, yanzu haka ma Mai Gari ya manta da zancen nan amma saboda ke ce mai tada zaune tsaye kika je kika tado da maganar ko?"

Lami ta ce

",To ba ni ɗin ba ce, Jummai ce tun da sanyjn safiya ta je faɗawa Mai Gari cewa kwana uku sun cika amma Ibra bai dawo gari ba, to da ta je da safen Mai Gari ba ya nan sun yi asubanci sun je wani ƙauye gaisuwa, shi ne yanzu ta koma da yamma, tana can ma fadar Mai Gari cike maƙil da mutane, yanzu ma daga can aka aiko ni kiranki, saboda kowa ya hallara amma ban da ke" Idanun Inna suka yi rau-rau tana tunanin abin yi sai ta ji hankalin ta ya tashi domin ita ta manta da wannan maganar kwata-kwata ashe dai yau wa'adin kwanakin zai cika.

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce

"Kai jama'a ba dan na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo wallahi da babu abin da zai kai ni fadar Mai Gari, saboda bani da kuɗin saniya, ban ajiye ba "

Lami ta ce

"To Inna ni ina zan gane wannan yaren naki, Mai Gari za ki yi wa bayani" Banza ta yi da Lami ta wanke hannunta, ɗaki ta shiga ta haɗo kan kuɗin kayan miyan da ta sayar, akwatin ƙarfen ta ta buɗe tana zaune a gaban akwatin ta fito da atamfofi guda uku ɗinkakku, wanda a wanke suke tas sun sha linki takaicin ɗakko atamfofin take ji a ranta amma haka ta zuba a ledar Viva ta fito ta ɗakko wata samira irin ta ƴan da mai hawa huɗu duk sun yi lamba a jiki, ta ce Lami ta riƙe mata, ita kuma ta yafa gyalenta ta ɗauki ledar atamfofin ta rufe gidan suka kama hanya a ranta tana cewa

'Ba saniya ba ko giwa ce Ibra ya gudu da ita in na bada kayan nan ba zan ƙara komai ba' Ta faɗa tana kallon setin samirarta da yake kan Lami...


MAMAN AFRAH
09025576222




[7/9, 3:38 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c


👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*



BOOK1️⃣
PAGE 9


*SHEIK*

Jin kamar dai babu alamun wani da zai taho daga ƙofar gidan ya kawo masa ɗauki, wato ya tabbatar muryarsa bata isa waje ba, don haka yanzu kam matar ta cim masa ba zai iya ma bari ta cigaba da azabtar da shi ba, dakyar ya ƙwace kansa ta shiga binsa da gudu suna tsere a ɗakin bai ankara ba sai ya ji ya kama rigarsa daga baya a haka yake gudun tana jansa tana rinjayarsa kasancewarta ƙatuwa ta fishi ƙiba, sai ya zamana dakyar yake iya gudun kasancewar rigarsa jallabiya ce a zuciyarsa ya ce

'Ina ganin ikon Allah, in ban da maluntar nan da na ɗakko ta larabawa ina dalili mutum zai kafa fama kullum da doguwar jallabiya kana tafiya tana taɗe ka' Ya faɗa a daidai lokacin sun zo saitin ruwan da ya ajiye, wanda yake kwalfa yana ba mutane, ruwan ne suka ture ya zube, tsautsayi ya sa suka shiga ciki gabaɗaya Sheik ya yi gaba ya yi baya ji kake tim santsi ya kwashe shi ya faɗi, ya yi

Please Login or Register in order to submit comment