You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sule ya shigo ɗakin, ai kuwa ta ɗan ɗago kai yake mata zancen kurma da hannu yana tambayarta ina adda, da hannu ta nuna masa inda ta ga Jummai ta ajiye, lallaɓawa ya yi ya ɗakko ya tura ƙasan gadon, gaban gadon ya ƙarasa ya juya bayansa Inna da sauri ta tashi ta ɗare bayan Sule ya goya ta, cike da zumuɗi suka baro ɗakin Jummai ransu fari ƙal.


Ashe tun shigowar Sule Jummai ta falka tana kallonsa munsharin ƙarya take, kawai ta bari ta ga gudun ruwansa, suna fita ta sakko daga gadon ta ɗauki addarta, ta fito ta bi bayansu Sule yana shiga ɗakin ya garƙama sakata, sai kuwa ga Jummai ta sake dawowa, amma kasancewar a rufe sai ta kasa shiga, ta window take musu magana tare da cin alwashin muddin Sule ya kusanci Inna sai ta ɓalla ƙofar ta zo ta musu aika -aika.

Tsabar tsoro sai Sule ya kasa komai, tun da tana tsaye ma Jumman tana kallon su, haka ya zauna a ƙasa yana kifa wani uban tagumi, don shi ya ga mace a ɓagas yana ganin ya tsinci dami a kale, babu sadaki babu kuɗin aure ko biyar bai kashe ba.


Inna tana zaune ta miƙe ƙafa tana jin kamar ta shaƙe jummai, a haka suka kwana babu wanda ya runtsa a cikin su.


Da asuba haka Inna ta yi alwala sai da ta ɓata buta guda a wajen tsarki saboda ni'imar da ƙwaƙwalwar raƙumin nan ta sanya mata a zuciyarta ta ce

'Wannan yarinya Jummai an yi ƴar kan uwa, da bata kasa ta tsare ba jiya Allah kaɗai ya san ganimar da za mu kwasa, amma don asara kalli yadda nake wanke ni'imar a banza tana bin makwararar banɗaki'

Haka ta yi sallah ranta duk ba daɗi shi dama tun da ya tafi masallacin ma bata ganshi ba, ita kuma Jummai sai da ya fita sannan ta bar ƙofar ɗakin, amma Inna a ranta ta ci alwashin yau sai ta kai ƙara wajen alwalin ta wato Mai Gari.

Haka kowa ya kama sabgar gabansa, Duduwa kishiyar Jummai ce ta yi ɗumame ta kaiwa Inna,, haka yaran Jummai suka tare a ɗakin Inna suna ta murna Inna mai kayan miya ta zama amaryar babansu, haka ta ɗauki tsiran nan ta raba musu.


Jummai kuwa wata kaza ta kama aka yanka ta gyara ta dafa, ta juye a kwano ta bayar aka kaiwa Mai Gari ba tare sa kowa ya san wanda aka kaiwa ba.


Dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta san dole ta amsa kiran Mai Gari yau, shi ya sa ta yi riga malam masallaci, ta dafa kaza ta aika masa saboda toshiyar baki da kuma cikar burinta.


Wajen ƙarfe goma aka aiko kiran Jummai daga fadar Mai Gari, haka ta tarar da Inna da Sule a can, bayan ta zauna Mai Gari ya kalli Inna ya ce


"Tasallah wai lafiya kike ta tagumi kina cika kina batsewa?" A ƙufule ta ce


"Haba Mai Gari ya kake so in yi to? Ko baka ji a akan abin da muke ƙaran Jummai ba"

Mai Gari ya ce


"Na sani mana"

Inna ta ɗora da faɗin

"To wannan ne dai ai ka ji kan maganar, amarcu dai daren jiya bai ciyu ba" Ta faɗa tana gallawa Jummai harara. Amma buɗar bakin Mai Gari sai ya ce


"To ai Jummai ta fiku gaskiya" Sule da Inna suka kalli juna suka kalli Mai Gari, Jummai ta saki wani murmushi, don ta san tabbas Mai Gari ya ji daɗin dahuwar kalwar da ta yi masa wacce ta sha farin maggi.


Nan ya shiga faɗin dole a bi abin da Jummai ta ce har zuwa dawowar Ibra wannan shi ne adalci. Kowa ya ji ba a kyauta amma amma mai gari in ya tuna dabgen kazar da ya ci da sanyin safiyar nan sai ya ji ba zai iya musawa Jummai ba

An yanke hukunci a kan Inna ta zauna a ɗakin Jummai takaici kamar ya kashe Sule, Inna kuwa ba a magana, haka aka tashi daga fada kowa yana jimami ban da Jummai da ta san amasar tambayar.


Tsawon kwana biyar Inna tana kwana a ɗakin Jummai, saboda yanzu an kasa kwana ma tsakanin Duduwa da Jummai amma ban da Inna Tasallah. Yau da ya kama alhamis tun da yamma Jummai take gyare gyare sannan kuma Inna tana lura da magungunan mata da take sha, sai dai kuma ta san yau bakin Duduwa ne ba na Jummai ba.


Abin da ya ba Inna mamaki yau yaran ba a ɗakin za su kwana ba, tun da wurin ta musu shimfiɗa a wani ɗaki da ake ajiye tarkace ta gyara musu tas.


Tsakanin Inna da Sule sai gani daga nesa Jummai ta kasa ta tsare duk da Inna ta ci wani alwashi da zai rusa duk wani shirin Jummai, saboda tana ta ayyana yadda za ta zamewa Jummai ƙadangaren bakin tulu.

Haka ta ga an gyara ɗakin, gadon ta hau ta kwanta, ita ma Jummai ta hau. Tsakiyar dare Inna tana bacci sai ta ji an dafa mata kafaɗa ranta fari ƙal ta buɗe idanu tunanin ta ko Sule ne, amma abin mamaki sai ta ji Jummai ce, Jummai ta ce


"Inna tashi matata" Idanu Inna ta zaro tana tunanin ko ta yi makuwa ne amma saj ta ji da gaske take, cike da mamaki ta ce


"Mai kike cewa Jummai?"


Jummai ta ce


"Tashi za ki yi ki biya ni sadakina"


Inna ta ce

"Na ce miki sai Ibra ya za a biya ki"


"
Jummai ta ce


"Ai kin san a birni an ce akwai abin da ake yi mace tana auran mace to nima yanzu kin zama matata, don haka dole ki bani haƙƙina" Ta faɗa tana farwar zanin Inna, sai ga zanin Inna an warɓar gefe sai ɗan tofin ta(Skirt ɗin ciki)


A take Inna ta tuna da ana cewa ana lalata mace da mace in bata manta ba an ce hakan yana faruwa a gaske to yaushe Jummai ta zama a haka ba a sami ba, a take Inna ta hau ihu tana cewa


",Ihu kwartuwa, Sule taho ka ga marar imanin nan za ta mini fyaɗe...


*MUMMY*


Babu wanda zai gane ko ya iya fasalta yadda tanji wani abu ya caki ƙahon zuciyarta, jikinta ne ya hau karkarwa a lokacin da ta yi wa idanunta masauki a kan fuskar yarinya, ko daga bacci ta tashi tabbas ba za ta kasa shaida Zainab Zee ba ƙawar ƴarta. Hannu ta saka ta dafe bango ɗaya hannun tana nuna su da yatsa.

Duk rikicewar Hajiya Daddy ya fi ta rikicewa saboda shi ji ya yi wani irin tsoro da fargaba a masa dirar mikiya, bai taɓa zato ko mafarkin wannan rana ba, kenan duk wannan sirrin da yake binnewa ya aka yi Hajiya ta sani.

Mummy kanta ne ya shiga juyawa, a take ta yanke jiki yaraf ta zube a ƙasa, Alhaji ne ya yi kanta yana kiran sunanta, ita kuma Zee ganin yadda duk ya birkice sai take ganin kamar ya fi son matarsa a kanta ita a nata ganin tun da ba zaman dadiro ne suke yi ba, ai ba komai ba ne don Mummyn ta sani, ita a ranta ma daɗi ta ji doin za ta saki jiki ta yi rayuwarta son ranta, duk da ta san dai yanzu tun da Hajiya ta sani da wuya ta ci gaba da samun Daddy a ɓagas kamar a baya da kullum ma yake mallakin ta, babu ranar bakin ta babu na Hajiya.

Haka ya kira mai gadi ya fito da mota shi kuma ya kinkimo Hajiya ya saka a motar Zee kuma ganin yana rawar ƙafa kawai sai ta ce ita banu inda za ta je.

Asibiti ya kai Hajiyar inda aka shiga bata taimakon gaggawa.

Bata farfaɗo ba sai wajen asuba, ta falko da kiran sunan Rahma, Daddy yana riƙe da hannun ta ko da ta kalle shi sai abin da ya wakana jiya ya dawo mata a take ta warce hannunta tana fashewa da kuka.

Misalin ƙarfe bakwai aka sallame su, amma Hajiya ta ƙi shiga motar ta hau napep duk da cewa Daddyn yana tabbayar mata cewa ba fasiƙanci yake yi ba matarsa ce ta sunna.

A ganinta ya ci amanar ta tun da ya yi aure matar har da ciki.

Daddy yana bin bayan napep ɗin da take ciki har suka je gida, ko parking bai gama ba ya kashe motar ya fito shi ya sallami mai napep ɗin ma ta hanyar masa transper tun da bai fita da kuɗi ba.

Yana shiga falon ya haura sama kasancewar bai ganta a ƙasa ba, zaune ya tarar da ita a ɗakinta a bakin gado tana ta faman rasgar kuka Rahma tana bata haƙuri, duk da Mummy ta mata bayani amma ta ji haushin Daddy da kuma Zee da ta auri ubanta.

Daddy yana shigowa Rahma wani takaici ya cika mata zuciyarta, a take ta yi ƙunci, fita ta yi daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka, tunanin ta ɗaya yadda mahaifinta ya auri ƙawarta yanzu abin da ya tsaye mata a rai wai har Zee tana ɗauke da cikin mahaifin nata kenan Zee ta ga Daddyn ta babu kaya a jikin sa har wani abu yana shiga tsakani.

Mummy kuwa ko sauraren sa bata yi ba ta ce ya fita mata a ɗaki, haka ya fita yana tunanin gwara ya bari idan ta huce ya yi aikin lallashin.

Rahma ta kasa jurewa, wajen sha biyun rana da ya fita ta je ta cewa Mummy za ta tafi Ƙundu ta je ta faɗawa Mai Gari halin da ake ciki, don ita abin ya mata ciwo tamkar dai wanda aka ce Daddy babu aure ya yi wa Zee ɗin cikin.

Tana fita Mummy ma ta rufe ƙofar ta kwanta ranta yana ƙuna tana tunanin mafita da kuma yanda za ta yanke shawara.


Rahma mota ta ɗauka ta saka jakarta a ciki, direba ta sa ya tuƙa ta suka doshi garin na Ƙundi wanda rabon ta da ƙauyen har ta manta kuma ta san dai Mai Gari yayan Daddy ne kaɗai yake iya sanya Daddy ya yi ko ya hana shi.


*SHEIK*

Cike da tashin hankali Sheik ya yi cilli da bulalar hannun sa, yana kai hannu biyu ya taɓa ƙirjin yana faɗin

"Innalillahi, na shiga uku ya zan yi?" Ya faɗa a hankali yana kallon amaryar tasa da ta zube a ƙasa kamar wacce ta suma.

Mai Gari da ya ji Sheik yana cewa su maido da nonon da suka ɗauka, kuma dai sai ya ji Sheik ɗin ya yi shiru wannan dalilin ne ya sa murna ta cika Mai Gari don a tunaninsa Sheik ya sa aljannu sun maido da nonon amaryar, baki ya buɗe yana cewa mahaifiyar yarinyar

"Kin ga abin da nake faɗa miki ko? Ai balaraben malami mashayar ɗa ba ko mutum sukutum aka ɗauka sai Sheik ya dawo da shi bare wani nono ai abu mai sauƙi ne fitar da wando ta ka" Ya faɗa yana dariya mai sauti, duk matan tsakar gidan a kunnen su aka yi wannan magana, a take aka fara ƙusƙus kowacce tana cin alwashin ta samu wajen zuwa neman maganin damuwarta.

Mahaifiyar amarya ta washe baki tana jin daɗin sa'ar sirikin da zai zama silar warakar ƴar tata. Duk maganar nan da ake a kunnen Sheik da ya jiƙe jagaf sa gumi ƙirji da tudun breast.

Maganar Mai Gari ce ta katse shi da faɗin

"Ya Sheik sun maido ko?" Sheik yana kallon ƙirjin sa ya buɗe baki dakyar ya ce

"Ina ta fafatawa dai da su suna gab da maidowa" Ya faɗa yana hawaye da jin da na sanin wannan maluntar BOGIN

Ya cigaba da karanta qulhuwallahu wacce ita kaɗai yake iya tunawa zuwa yanzu, yana tofawa amaryar don yanzu bashi da ƙarfin dukanta ma.

Yana yi sai ya ga ƙirinta ya fara tasowa kamar almara sai ga tudun ƙirjinta ya dawo, a rikice ya kalli nasa ƙirjin ganin bai ɓace ba kuma dai natan ya dawo das dashi.

Da sauri ya tsugunna yana yin ƙasa da murya ya ce

"Haba aljannu kar mu yi haka da ku, ni na yafe nonuwan nan domin Allah ku raba ni da shi" Amma atishawar amaryar tasa ce ta tabbatar masa da cewa aljannun sun sake ta.

Ƙuri ta masa da idon ta ɗaya tana washe baki, fuska ya tamke yana ganin duk ita ce silar shigarsa matsalar da yake ciki.

A wayince ya shiga kare ƙirjinsa gudun kar ta gani, ya janyo hiraminsa ya yafa a kafaɗa yana dibara wajen kare ƙirjinsa.

Magana take masa yana amsawa a daƙile, ya buɗe ƙofar ya fito ta biyu bayansa tana tafiya dakyar alamar ƙarfin jikinta bai dawo ba, mahaifiyarta ta rungume ta cike da murna, kowa na wajen ya zo ana kallon yadda Sheik ya sa aljannun suma maido mata da nonon ta, sai dai babu wanda ya lura da ƙirjin Sheik bare a ha ajiyar da aljannun suka masa.

Mahaifiyarta tana ta masa godiya, tana cewa yanzu ai za a kawo masa ita gidan, amma buɗar bakinsa sai ya ce aljannun sun ce ba yau za ta tare ba idan ta tare yau za su haifar da gagarumar matsala a garin.


Jin haka sai Mai Gari ya ce a dakata da tarewar yau, shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda rufuwar asirin sa, don ya san matsawar aka kai amarya to tabbas ita ce za ta fara tona masa asirin ajiyar da aljannu suka masa a ƙirji, bare kuma shi da rayuwarsa gabaɗaya sirri ce yana sana'arsa ta MALAMIN BOGI.


Daga nan masallaci suka wuce ya ja su sallar isha'i basu lura da yadda yake ta kare-karen ƙirji ba. Ana gama sallah ya ce zuwa zai yi ya kwana yana lazumi saboda matsalar garin, amma ya faɗa ne kawai don yanzu tashin hankalinsa bai wuce ƙirjinsa ba, so yake ya ce ya ga ta yadda zai yi da breast ɗin ƙirjinsa.


Bayan ya je gidan ko ta kan abincin da aka kawo bai yi ba, ɗakin ya bankawa sakata, ya yi saurin cire hirami ya jefar ya kama riga ya cire.

A razane yake kallon ƙirjin nasa ganin wani baƙiƙƙirin ɗin breast ne, musamman da suka haɗu da farar fatarsa da ta sha bilicin, sai baƙin su suka ƙaru, kamar a jikinsa suke tun asali haka suka yi, ya rasa ma ya zai yi da su.

Ya fara tunanin mafita cewar yake yafa hiraminsa a wuya yana dabara yadda zai ke ɓoyewa ba tare da kowa ya gani ba, har zuwa lokacin da Allah zai yanke masa wahala, don shi bai taɓa jin an ce namiji yana da breast ba in har ba mata maza ba. Ya san mata maza ne suke da breast sannan suna da HQ da kuma mazantakar namiji a jikin su, amma dai bai taɓa jinw wanda shi ba mata maza ba kuma aljannu su fito masa da breast rana tsaka tashin hankalin ya yi yawa.


Haka ya kwana ranar da zulumi sai bacci ɓarawo ne yake ɗauke shi.

Washe gari aka kawo masa wata mata ƴarnuwar Mai Gari an ce masa bazawara ce sakin wawa, an kawo ta ne a mata magani saboda tun da suka rabu da mijin har yau ta rasa mashinshi ni, shi ne ake tunanin ko mijinta na farko ne ya mata asiri.

Sheik tun da ya ƙyalla idanu a kanta ya ji yawunsa ya tsinke, sannan a ransa yana tunanin ina ma a ce wannan ce aka ɗaura masa aure da ita ba waccan mai ido ɗayan ba, yanzu kuma da kunya matsayinsa na balarabe ya ce ya ga baƙar fata yana so, domin ita ma farar bafulatana ce gashi har kafaɗa ga shi tana da cikar halitta wacce ita ce ta sanya Sheik ya rasa nutsuwarsa don sai ya ji ko fatar jikinta ne yana so ya taɓa.

Saboda wannan dalilin na ba ya son ya daina kallon ta ya ce maganin na kaana uku za a yi, sai wanda suka kawo ta suka koma garinsu ita aka barta a gidan Mai Gari a kan cewa idan an gama maganin ta koma.


Da yamma motar su Rahma ta yi wa garin Ƙundu dirar mikiya, a ƙofar gidan Mai Gari motar ta tsaya, tun kafin ta fito ta hangi Sheik yana tsaye da wasu mutane, gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin wani balarabe fari tasss da shi yana sanye da baƙar jallabiya ga gashin kansa kwance lufff kamar na jarirai. Sajensa da ya ƙara ƙawata fuskarsa shi ne abin da ya ja hankalin ta cikin sauƙi, gemunsa da ya tashi ziyat a habar shi kaɗai ma abin kallo ne.


Ta shagala da kallon Sheik bata san lokacin da ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba. Sheik bai ganta ba saboda hankalinsa ba a wajen motar ma yake ba, dakyar ta samu ƙwarin gwiwar fitowa daga motar.

Abin yana bata mamaki ya aka yi aka samu balarabe a wannan kwaraɓaɓɓan ƙauyen, ko ita da take bahaushiya ba don wannan damuwar da suke ciki ita da Mummyn ta ba, babu abin da za ta shigo ƙauyen nan ta yi.

Direban ne ya bita da akwatin kayanta wanda ta ɗakko kala uku da kuma su madara kwanfiles da sauran abubuwan buƙata saboda ba za ta iya cin cimar garin ba, kuma dai a yadda ta yi fushi da Daddy tana so ta ɗan nesanta kanta da shi, sannan sai ya zo har garin an magance matsalar wannan dalilin ne ya sa ta taho da kaya.

Mai Gari ganin Rahma ya cika da murna, har ya kasa zaune da tsaye ganin ƴar ɗan uwansa da ya fi ƙauna. Mutane suna ta mata sannu amma ko kallo basu ishe ta ba, tana ta waiwayen inda za ta ƙara ganin balaraben nan amma bata ga inda ya yi ba.


Direban komawa ya yi a cewarta za ta masa waya ya zo ya ɗauke ta, in buƙatar hakan ta taso.


Da suka yi sallar isha'i Sheik yake cewa Mai Gari ya fara sha'awar saka kayan hausawa babbar riga da ƴar ciki, Mai Gari ya yi mamaki ganin dai Sheik bai saba da saka kaya in ba na larabawa ba, amma ganin ya ce tana so sai ya ce za a siyo shaddodi da yadika masu tsada a ɗinka masa.

Shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda ya fara ɓoye breast ɗin ƙirjinsa, sannan yana so idan ya je wajen malamin da yake karɓo magunguna ya bashi kuɗi a siyo masa bireziya saboda ya fara suturta ƙirjinsa tun da yana ganin bra ɗin za ta sanya ba za a lura da tudun ba kuma musamman idan ya saka kayan hausawa da babbar riga.


Rahma ta faɗawa Mai Gari gabaɗaya damuwar da ta kawo ta, Mai Gari dama ya san cewa ɗan uwan nasa ya yi aure amma kuma bai san cewa bai sanar da iyalinsa ba, don haka sai ya nunawa Rahma zai kira shi ya masa magana za a san abin yi a hukunta Daddy, ta ji daɗin furucin shi ma kuma ya mata hakan ne don ta fita daga damuwa.


A nan take tambayarsa labarin wani balarabe da ta hanga lokacin da ta iso, Mai Gari ya kwashe komai ya faɗa mata, dangane da Sheik a take ta ji ta kamu da muguwar ƙaunarsa, kuma in dai shi ne ta amince ko a cikin kara ne tw zauna ba wai a ƙauye ba. Ta sa a ranta idan Daddy ya zo garin nan ba za su tafi ba sai ta mallaki Sheik a matsayin miji, dole Daddy ya gina musu gida mai kyau inda za su rayu, ta haifi ƴaƴan larabawa, idan kuma Sheik ɗin yana so sai su tafi Abuja su rayu a can amma dai bata da mijin sai balarabe daga ƙasar Yemen.

Bata faɗawa Mai Gari ba ta dai bar maganar a zuciyarta zuwa safiya. Haka ta kwanta cike da shauƙi da ƙaunar Sheik tana fatan ya zo mata a mafarki.


*DARE*


Darebya tsala, kowa yana bacci sai dai Sheik sa tun da ya ga baƙuwar nan ya kasa sukuni, idanunsa yanzu ma sun hana shi ya runtsa saboda ya sanya tunanin ta a ransa kawai burinsa ya ji matar nan a kusa da shi. Juyi ya yi yana jon tunanin da ya saka a ransa ya hana shi sukuni. A take ya yanke shawara, tsaye ya tashi ya ɗako wani zani da hijabi cikin kayan da yake tsinta idan aka zo aka taru ana karɓar magani, sai a ga hijabi wani lokacin a rasa mai shi ko ɗankwali ko hula ta mata ko zani.

Zanin ya ɗaura ya saka hijabin, yana jin cewa yau ko ta halin ƙaƙa sai ya je ya ji ɗumin jikin baƙuwar nan, shaiɗan yana ta zuga shi yana masa linzami.

A zuciyarsa ya ce


"Ai na lura tana cikin buƙatar kulawa da soyayya, kuma ai ba za ta gane waye ba, buƙatar maje hajji sallah" Ya faɗa yana fitowa waje, yana duba gabas da yamma arewa da kudu ya ga babu kowa sai kukan karnuka kawai.


Katangar Mai Gari ya kama ya ɗare, da yake bata da tsawo ya sauka a hankali, yana lashe baki ya shiga ƙarewa ɗakunan gidan kallo yana so ya gano inda zai samu baƙuwar, ko dogon tunani ba ya yi ya fi so kawai ya ganshi a ɗakin.

Ɗakin matar Mai Gari ya fara leƙawa amma jin ana sakin munshari kamar an shaƙe raƙumi sai ya zaci ɗakin Mai Gari ne a tunaninsa Mai Garin ne yake munsharin.

Wani ɗaki ya shiga yana ji a jikinsa tabbas a nan masoyiyar tasa take, da sanɗa ya ƙarasa ya haye katifar ganin ta lulluɓe ruf da bargo shi na ya bankaɗa ya yi wa kansa masauki a ciki.

A hankali ya lallaɓa ya rungumo na bargon, a zuciyarsa yana cewa


'Alhamdulillahi, ƴar fara zo ki ji lallausar fatar balarabe'


Bai tsaya a nan ba ya kai baki zai kamo bakin, amma cikin rashin sa'a sai ya cafko hancin, ya manta ma da ƙirjinsa da aljannu suka masa ajiya, jin an cafki hancinsa sai hakan ya hana na cikin bargon shaƙar numfashi da kyau, yana riƙe da hancin a bakinsa yana sauke numfashin cin nasara da cikar burin sa.

Fisge-fisge na cikin bargon ya fara, yana son ƙwacewa amma Sheik ya ƙara zage ƙarfinsa ya maƙalƙale.

Cikin hargitsi aka ce


"Kai wai waye a nan ne, wane shegen ne ya shigo mini bargon yana lasar mini hanci kamar tsohon maye?"

Sheik a zuciyarsa ya ce

'La'ilaha ilallahu ba baƙuwa ba ce Mai Gari ne ai!"

Gaban Sheik ne ya doka da ƙarfi ya fara janyo salati a zuciyarsa da fatan Allah kuɓutar da shi, a take ya fara ƙoƙarin ficewa daga cikin bargon, Mai Gari jin haka sai ya kai hannu ya riƙo shi, tunanin Mai Gari rigar mutumin ce ya riƙo ashe hijbin ne ya riƙe saitin fuskar, Sheik ya rasa ta ina zai fito da kan nasa ma domin Mai Gari ya cukwikuye, yana faɗin


"Wane kwarton ne wai, wato an ga na yi baƙuwa daga birni"




Please Login or Register in order to submit comment