You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daddy ya ce ya zauna a ɗakin baƙi kafin ya gama sama masa admission a wata ƙasar inda yake ganin zai dace da cigaba da karatun sa. Ma'aruf ya yi mamakin jin cewa Daddy yana da wata matar bayan ya san babu wanda ya sani kuma ya san akwai matsala ko dai ya ce tashin hankali duk ranar da ƙwan ya fashe za a yi ɗan jijjiɓin yaƙi.

Ya ji daɗin cewa Daddy za fitar da shi ƙasar waje karatu, wannan ya nuna cewa Daddy har yanzu yana riƙe da zumunci kuma, zugar Hajiya da Rahma bata yi tasiri ba kuma dama bashushe ya ce hassada ga mai rabo taki ce.


Zee ta karɓe shi hannu biyu shi kuma yana girmama ta duk da cewa ya girme ta amma kuma, tun da dai matar Daddy ce babu wani batun girmansa tun da idan ana dara fitar da uwa ake.

Daddy ya kammala masa komai na tafiya, inda zai tafi China nan da kwana uku, murna kamar zai yi mai, ashe da rabon ya shiga jirgi. Ana jibi zai tafi ya je Ƙundu ya musu sallama, duk da a tsaitsaye ya yi saboda bai gama shiri ba, har ya je ya dawo basu haɗu da Sheik ba.

Ranar laraba misalin ƙarfe biyu jirgin su ya tashi, Zee da Daddy ne suka raka shi airport yana ta farinciki saboda shi yana son karatu.
*(A page 15 buk 1 zai ƙare mai buƙatar book 2 zai biya ɗari biyar*

Haka rayuwa ta cigana da tafiya, Rahma tana fantamawar ta, sai samari take yi kala-kala ƴaƴan masu faɗa a ji, don ita ta ƙi jinin masu ƙaramin ƙarfi ƴaƴan malam shehu. A ɓangaren Daddy kuwa har yanzu yana ta cin karensa babu babbakaa, domin babu ranar da za ta zo ta faɗa bai kwana a gidan amarya ba, ita kuma Mummy da yake hotiho ce bata taɓa lura ba, saboda idan ta je ta hangame baki sai bacci bata taɓa sanin abin yake wakana ba.

Sannan basu da masaniya a kan tafiyar Ma'aruf karatu su duk tunanin su yana can ƙauye, don Mummy takan ce Ma'aruf ana can ƙauye an kama sana'ar sayar da rake.


Ranar wata juma'a ne Mummy tana kwance bayan ta dawo daga fitsari, bacci bai ɗauke ta ba, sai ta ji kamar alamar hayowa saman benen, shiru ta yi tana son gano cewa ko dai kunnen ta ne amma sai sai bata kawo komai ba tana dai kasa kunne tana jiran ta bambance, kamar daga sama haka ta ji, ƙaran buɗewar ƙofar ɗakin Daddy mamaki ne ya yi masauki a kwanyarta, zaune ta tashi, amma yau kawai sai ta ji tana son sanin mai ya saukar da shi ƙasa, don zuciyarta ma ta fara wasi-wasi wato shaiɗan ya fara mata biyar ko dai ɓangaren masu aiki yake zuwa, ba komai ya sa wanann zargin ya ɗarsu a zuciyarta ba sai furucin wata ƙawarta da ta ce mata ba a gane gaban namiji bare bayansa, haka ta faɗa mata bayan ta bata labarin cewa ba zai msta kishiya ba kuma shi mata ma basu ishe sa kallo ba.

Da sanɗa ta sakko duk da tana masa zato mai kyau amma kuma dai tana son idan ta yi abin da za ta yi ɗin ta tarar da shi a kan gaskiya. Abin da ma ya sa ta fara wannan tunanin sai tunawa da ta yi da wannan ranar ma da kamar wannan lokacin ne ya dawo inda ya ce mata ƙasa ya sauka ya ji motsi, a nata ganin ai ba kunnen maciji ne da shi ba da za a ce wani ƙaramin motsi ya je kunnensa.

Jinginuwa ta yi a window tana ɗan ɗaga labule a zuciyarta tana cewa.

'Idan ka ji ana cewa raka no in yi kashi to tabbas kashin ba gudawa ba ne'

A daidai lokacin da ta ɗaga labule Daddy yana dab da shiga ɗakinsa, abin da ya ɗaure mata kai kuma shi ne yadda yake wani sanɗa yana waige-waige, alamomin rashin gaskiya dai sun bayyana ƙarara a yanayinsa.

Gabanta ne yake faɗuwa, amma haka ta daure tana kallonsa har ya shige ɗakin, kuma a duhu bai kunna fitilar waya ba ko kuma fitilar ɗakin. To in har ba babu gaskiya a tare da shi ba mai ya sa zai yi hakan.

Sai da ta bari ya ɗan jima da shiga sai ta buɗe tata ƙofar ta fito, Daddy da ya shagala da yin waya da Zee bai ma san Hajiya ta buɗe ƙofa ba don ba ya cikin nutsuwar da zai ji ƙaran ƙofar. Sai da ta zo za ta buɗe ƙofar ta ji dirin maganarsa sai dai bata ji mai yake cewa ba, mamaki take da wa za su yi waya a doshin asubar nan.


Ƙofar ta murɗa, Daddy da yake waya ya danne wayar da sauri ta ɗauke, idanu ya rufe kamar mai baccin ƙarya. Fitilar ta kunna abin mamaki har da munshari yake saki, wanann ne dalilin da ya sa ya fara jefa masa ayar tambaya a ranta, tana tunanin wane irin sake ne wannan ta yi a cikin gidanta, sai yanzu ne ma take mamakin yadda Alhajin ba ya ƙulafucin ta zo ɗakin nasa wanda a da can baya ba sa ɗaukan wannan tsawon lokacin ba tare da sun kusanci juna ba, amma sai yanzu ta lura da ita da babu ma duk ɗaya, bata san cewa sabuwar fulawa ya samu yake ban ruwa ba.

Yadda ya mata bariki ita ma barikin ta masa, gaban gadon ta ƙarasa ta ɗan buga ƙafarsa tana kiran sunansa, idanu ya buɗe dakyar yana wani ƙanƙance su irin na mai bacci, sai ta ji wani haushin sa ma tun da ta ga zai munafurce ta.

Ɗan washe fuska ta yi tana masa murmushi take cewa ya tashi lokacin sallah ya yi, ko kunya haka ya tashi yana wani murtsuka idanu, duk da ta san ba a ma fara kiran sallar ba, amma dai dama ta zo ne don ta tababtar da baccin makaho, da a ce yana da gaskiya Daddy da ba zai yi baccin ƙarya ba, sai dai ta ci alwashin sai ta gano abin da yake sauka yi a ƙasa.

Ɗakin ta ta juya ta koma shi kuma ya shiga banɗaki, yana suuke ajiyar zuciyar kuɓuta don shi a nashi tunanin ko ta ji yana waya ne, don bai taɓa kawo cewa ta ga shigowarsa ba, bare har ya yi tunanin ta ji yana waya ya san ma ba zai yiwu ta yi shiru ba.


Bata sauya masa ba ko a fuska bata nuna masa ba, sai dai a ɗauki alƙawarin sai ta ƙurewa motarsa gudu. Sai da dare ya yi ta hau ƙawar ya kwana a ɗakinta amma firrr ya ƙi yana cewa shi katifar ɗakin ce ba ya so, da ta nuna cewa ko ɗakinsa za su je, sai ta ga ya ɗan basa da zancen, ita kuwa bata wani nuna masa ta damu ba ko kuma ta damu, sai kawai ta kwanta a nata ɗakin ya mata sallama ya fita ya rufo ƙofar. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, tana jiran ta ga abin da zai faru. Har ta fara ganin lafin kanta da kanta cewa ta zargi mijinta kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar ɗakinsa, bizigir ta miƙw zaune daga kwanciyar da take ba tare da ta shiryawa hakan ba.

A hankali ta lallaɓo ta zo window sai gashi ya fita, tana nan tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falon ƙasa, shi ma don idanun ta biyu shi ya sa ta ji kuma saboda ta kasa kunne. Gabanta ne ya tsananta bugu tana jin faɗuwar gaba don zuwa yanzu ta tabbatar da cewa wajen ƴan aiki yake zuwa, tun da dai babu abin da zai fitar da shi da dare, windown da ake hango harabar gidan ta zo ta leƙo sai kawai ta hangi Daddy ta cikin hasken farin wata yana ta sauri, kallonsa take hawaye cike a fuskarta don a halin da take yanzu gani take ko rantsuwa za ta yi cewa biyan buƙatarsa ce ta wajen ƴan aiki ta fita da shi.

Sai dai akalar tunaninta ya sauya ne a lokacin da ta ga ya nufi ƙofar fita daga gidan ta baya, a sannan ne ƙirjint a ya shiga bugu da mugun ƙarfi,, ji ta yi hankalinta ya tashi, da sauri ta bar jikin labulen bayan ta ga fitarsa, a kiɗime ta juyo ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ko ina, ƙaramar lokar jikin madubi ta janyo inda take ajiye mukullai, dakyar ta samu mukullin ƙofar fita daga bayan gidan, jikinta yana ta ƙyarma, saboda jikinta ya bata akwai wani gagarumin abin da yake faruwa.

Ko ƙofar ɗakin bata rufe ba, haka ta fito fitilar wayarta a kunne, da matakala bibiyu take sauka daga saman benen, ƙofar falon ma a buɗe ta bari ko takalmi babu a ƙafarta, ita fatan ta ɗaya shi ne Allah sa dai ba wai fira yake da wata macen ba, shi ne ba ya zuwa sai dare ya tsala saboda gudun ɓacin ranta, amma wace mace ce za a ce tana fitowa daga gidansu a wannan daren, sai dai in mutuniyar banza ce, haka take ta saƙawa har ta zo wajen ƙofar, ganin ƙofar a kulle , zargin ta ya zama gaskiya, mukullin ta saka ta buɗe ƙofar sai dai bata da nutsuwar rufe ƙofar, amma sai ta laɓe ta leƙo, daga can ta hange shi tsaye da alama wani yake jira, tana hango shi tana jin tsanarsa a ranta, wato su iyalansa suna nan suna bacci shi kuma lokacin ne safiyarsa ta waye.

Wani machine ne ya tsayar ya hau, suna fara tafiya sai ga wata mata a mota, nan Hajiya ta tsayar da ita ko tsoro ma bata ji, matar kasancewar ta likita kuma sama da gidan su Mummy take, ta fito ne za ta je karɓar haihuwar wata mata, haka ta ɗauki Mummy ganin kamar ba a hayyacinta take ba machine ɗin ta nuna mata a kan cewa ta bi bayansu, ganin sai kuka take tana mata bayanin abin da ya sa ta biyo bayan mijin nata.

Ta tausayawa Mummyn, sun ɗan tsaya daga ɗan nesa ganin machine ɗin ya tsaya a ƙofar wani gida, Mummy ta mata godiya bayan an buɗewa Daddy ya shige ta fita daga motar ta ƙarasa a ƙafa. Ganin katangar bata da wani tsayi a ranta ta ce

'In ka ji kana ba za ka iya ba to bai same ka ba ne, ai ni yau sai na ga ƙwal uwar daka' Ta faɗa a zuciyarta tana komawa daga can bayan gidan ta kama katanga ta ɗare, haka ta ti dabara ta dira amma fargabar abin da za da tarar sai ya sanya bata ji buguwar da mazaunanta suka yi ba.


Tashi ta yi ta yi saurin laɓewa ganin ana hasko fitila, sai da ta dakata mai gadin ne ya zo ya yi ɗan haske haske ya juya bai ganta ba, da alama bai fuskanci cewa gidan aka diro ba.


Ƙofar falon ta lallaɓa ta tura a hankali jin ba a saka mukulli ba zuciyarta tana ta ayyana mata cewa

"Namiji ba ɗan goyo ba ne, tun da ta yarda da mijinta ashe dai saka reshe kama ganye ta yi, sai dai ta ɗaukarwa kanta alƙawarin za a yi kan mai uwa da wabi, domin ta lura tsugunne bata ƙare ba amma sai ta nuna musu tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, tun shi Alhaji ganin hadarin nesa zai sa shi yin wanka da kashi, don ta lura wadatar biki ne tsarki da romo, tun da har ya iya zuwa wajen wata mace za ta nunawa matar cewa abincin wani gubar wani ne, don abin nasu aikin banza ne shafa lalle a ɗuwawu'

Ɗan hasken da ka bari a falon wanda yake kawowa yana ɗaukewa hasken mai kalar blue, ganin falon shiru hakan ya bata tabbacin suna sama, saman ta hau tana jin cewa yau duk sai sun baƙunci lahira, a ɗaki na farko ta fara jin magana ƙasa -ƙasa muryar Zee ta ji tana cewa

"Haba kai kuwa gaskiya yau ka makara baka fito da wuri ba, ka san dai ai bana iya bacci sai da kai, sai ka je ka tare a gidanka ni ka barni da kewa" Mummy ji ta yi kamar ta fasa ihu, Daddy ta ji ya ce

"Haba ƴar lele ai komai nake hankalina yana kanki, kin sha gaban duk matan duniya ke kaɗai idanuna yake iya gani da kuma hange, haba amarya mai capacity, amarya kin fi quality, mu kwanta...

Banko ƙofar da Mummy ta yi shi ya ankarar da su juyo, zumɓur Zee ta miƙe daga cinyar Daddy, a take idanun Mummy suka sauka a kan cikin wata huɗu na Zee wanda ya yi kufkuf a jikinta kamar ƙaramar ƙwarya...


*BOOK 1 free shiga grp na BOOK 2 500, cmplt doc 800*
*Acc no faiza abubakar 9030283375 opya shaidar biya 09025576222 gobe za mu gama book 1*

*Yau ba samu leƙo inna amarya ba da kuma ango Sheik mai breast*
😂😂😂😂😂😂

*Sai gobe in muna raye*

MAMAN AFRAH
09025576222
[7/17, 7:31 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*


BOOK1️⃣
PAGE 15
*END OF BOOK 1 LAST FREE PAGE*

*BOOK 2 500 naira pay in to faiza abubakar 9030283375 opay*

IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_ventureƊ


*INNA TASALLAH*

Cike da tsoro take kallon sabuwar addar hannun Jummai gabanta yana faɗuwa, ta ɗauka Sule jarumin maza ne zai yi iya yainsa don ganin ya dakatar da Jummai daga wannan barazana ta mummunan aikin da take so ta yi amma sai ta ga har lokacin yana dafe da mararsa yana ciccira idanu tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amarya.

Jummai kuwa babu alamar wasa ko kuma yin barazana a kalamanta ko yanayinta kana ganinta ka san iya gaskiyarta take faɗa iya abin da yake cikin ranta ne kuwa alwashin da take ci babu gudu babu ja da baya.

Inna a zuciyarta ta ce

'Tabbas ƴan magana sun ce kifin fadama ba ya gasa da kifin kogi, amma wannan mata tana son kawo min cikas a ɗan amarcin da na ɗora rai zan dangwala, tana son shuka min salalan tsiya' ,A fili kuma sai ta ce

"Haba Sule ka yi wani abu mana, kana dai jin abin da take faɗa tana neman kawo tsaiko a lamarin kasancewarmu tare, kuma sanin kanka ne Mai Gari ya kashe wannan maganar, kuma maganar ta mutu murus"

,Wani yawu Sule ya haɗiye ya lura Inna bata san abubuwan da sukw faruwa a duniya ba, shi da yake ma'abocin sauraren rediyo ne babu abin da bai sani ba saboda yana jin labaran yadda wasu matan suke yankewa maza mafitsara musamman a kan lamarin kishi, bare Jummai da haka nan ma tarar aradu da ka ne da ita bata barin ta kwana.

Yana ɗan sakin murmushin yaƙe ya ce

"Haba Tasleey ai kin san Jummai a kan gaskiyarta take, haƙiƙa saniya ba tawa ba ce ke ma kuma kin sani"

Wani takaici ne ya rufe Jummai jin wai Sule yana kiran Inna da Tasleey wato ta lura maza basu da gaba basu da baya wato sawun keke ne su, amma in ba haka ba ita yake kiranta Jummai amma Inna daga tarewa har ya sauya mata Tasallah zuwa Tasleey.

Inna kuma wani haushin Sule ne ya kamata tana ji kamar ta hau shi da duka, yana ji za a mata sagegeduwar amarcin amma babu wani kataɓus da ya yi, ita ba ma wannan ne tunanin ta ba yadda maƙociyar yarinyar nan ta bata ƙwaƙwalwar raƙumi ta yi amfani da shi gashi yanzu ana neman sakawa ta shiga uku.

Inna ta ce

"Ban gane a kan gaskiyarta ba?" Ido ya shiga ƙiftawa Inna yana mata alama da addar hannun Jummai, ita ma Inna hannunta riƙe da mazaunai ta ce

"To shikenan saboda ta ɗauki adda sai a ƙi faɗar gaskiya, kana ji fa ta ce wai ni za ka bata in koma ɗakinta, ka taɓa jin wannan ɗanyen aiki ni fa tun da an ɗaura mana aure ni ɗin fa na zama mallakinka ita kuma tana a matsayin kishiyata ne, yanzu kawai sai in koma ɗakin kishiya?"

Jummai ce jin har suna shawara, kenan suna ja da maganarta hakan ya sanya ta fara taku ta zo gaban gadon ta zauna ta miƙe ƙafa ranta a ɓace ita kuma adda sai walwali take, wannan ƙallin da addar take shi yake ruɗawa Sule ciki.


Sule ganin haka ya ce

"Tasleey maganin kar a yi kar a soma... A hargitse Jummai ta katse shi da faɗin

"Wane suna ne wannan ɗin?"

Da sauri ya gyara da faɗin

"Tasallah a bar maganar nan Jummai iya gaskiyarta take faɗi"

Inna saroro ta yi tana kallonsa ganin da gaske dai Jummai yake tsoro, duk da ita ma tana tsoron amma tana so ne ta yi yaƙi ta karɓi ƴancin ta.

Inna ta ce

"Jummai kin san dai na yi jika da ke, ni ba na son tashin tashina, tun da Allah ya yi na auri mijinki ki ɗau dangana, duk ranar da Ibra ya dawo da kuɗinki zan sa Sule ya warware igiyar" Kai Jummai ya ɗaga tana wani yatsina ta ce

"Sule ya muke ciki ne? Ka ga yadda na kulle ɗaki daga ni sai ku, sannan ga sabuwar adda"

Sule cike da zuga da kambamawa ya ce

"Jummai ikon Allah, Jummai masallacin kura kike ba a ba kare limanci, ƙarfe duka ƙarfe ne amma a cikin ƙarfe akwai zinare da azurfa" Ya faɗa cike da kirari don ganin ya faranta mata ta janye batun ta, don shi yana tsoron mutuwa saboda bai shirya tafiya ba, kar a je ta guntule shi tsakiyar dare ya shiga uku.


Inna jin ta yi sake reshe kama ganye, wato dai amarcin nan ba ciyuwa zai yi ba, sai kawai ta fashe da kukan takaici" Sule bai lallashe ta ba ko bata baki gudun kar ya yi laifi.

Jummai ta sheƙe da dariya ta ce


"Wato an ga samu an ga rashi, to ai sai ki tashi ki koma ɗakin mijinki, wato ni kenan ɗakin mijin ki Jummai" Cewar Jummai tana ƙara bushewa da dariya

Kai Sule ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, alamar eh, Inna ta kalli Jummai ta kalli sule wanda zuwa yanzu ya fara motsu-motsu da harhaɗa ƙafafu wanda ba komai ba ne ya haifar da hakan sai maganin da ya sha ne yake tambayarsa.

Cike da sanyin murya ya ce

"Tasleey au...

Ya dakatar da maganar tunowa da ya yi Jummai ta yi magana ɗazu.


Yana sauya akalar maganar ya ce

"Tasallah ki tashi ku je ku kwanta" Wani haushinsa ne ya kama Inna tana ganin saboda tsabar shi saunan namiji ne kana da amarya amma ka ba mace saboda namijin hotiho ne shi.


Jummai ta miƙe tsaye tana wata hamma, ta je saitin ƙofar ɗakin ta tsaya, ganin Inna bata taso ba, sai ta saka addae a jikin bango ta karta alamar wasawa ta yi, tsabar ruɗewa a kuɗime Sule ya miƙe bai san ya aka yi ba sai ganinsa ya yi a gaban Jummai, sai da ya ganshi a gabanta ya tuna cewa ashe ba shi ne za a tafi da shi ba.

Inna kuma karta addar a bango sai ya sa ta miƙe tsaye har zani yana neman kwancewa ta gyara, Jummai ce ta ce

"Sule ko har kai za a tafi ne?" Yana wayincewa ya ce


"A haba da girman kujerarki ai da Tasallah ne za ku tafi" Ya faɗa ransa yana ƙuna gabansa kuma yana faɗuwa a lokaci guda, don shi duk abin da za a ce an haɗa da rai to tabbas ba ya son maganar mutuwa.

Inna tana yin yaƙe ta ce

"Eh da ni ce" Dariyar cin nasara Jummai ta saki a ranta tana saka hannu ta buɗe sakatar ta saka Inna a gaba suka nufi ɗakinta suna fita Sule ya yi zaman ƴan bori yana ambatob Lahaula wala quwwata.

Kai ya dafe da hannu biyu a fili yana faɗin

"Kin cuce ni Jummai, sai da na gama ɗora rai zan kwashi garaɓasa kika mini shigar sauri, yanzu a ce sai da na gama bankar magani abokaina suka gama zuzuta maini amarcin zan kwashi ganima amma ki zo ki min haka" Ya faɗa idanunsa suna masa jawur.


Inna kuwa ɗakin Jumman suka shiga, warin fitsarin yaran ne ya ankarar da Inna cewa an shigo ɗakin ƙazama Jummai, don yaran sun isa su daina fitsarin kwance ma.


Cike da umarni ta nunawa Inna gado, haka Inna ta hau gadon tana jin tsinkon da marar ta take mata. Amma babu yadda ta iya haka ta hau ta kwanta, tana tuno tsiren amarcin ta da kuma ruwan ledar da aka kawo mata na amarci. Jummai wuri ta samu ta ajiye addar ta hau gefen Inna ta kwanta, sai yanzu Jummai ta ji sauƙin zafin ranta da yake mata raɗaɗi tun lokacin da aka ɗaurawa Inna auren, ga kishi ga rashin saniya, yanzu kuma tun da Inna ta dawo ƙarƙashin ta sai take ji daidai yake da saniyarta ce a kusa.


Sule a nan tsakar ɗakin ya yada zango, don ko gadon ƙarfen Inna bai samu hawa ba, haka nan tsire ma bai samu shiga ba saboda yanzu amaryarsa kawai yake buƙata amma babu hali, don da alama Jummai da gaske take ba za ta bar Inna a ɗakinsa ta kwana ba, tun daɗewa yake jiran dawowar Inna ya ɗauka Jumman za ta barta ta zo amma dai har har yanzu shiru, kamar maye ya ci shirwa ba amo ba labari, tun da dai babu niyya ango ya kwana da wando.


Har dare ya tsala yana nan tsakar ɗakin yana murƙususu, ganin dai abin ba zai masa ba, tashi ya yi ya lalaɓo ya fito yana sanɗa ya nufi ɗakin Jummai, tun kafin ya ƙaraso yake jin tashin munsharin Jummai, da na yaran da suke kwance a tsakar ɗakin. Da yake akwai fitilar ƙwai irin ta mutanen da, an barta a kunne amma kuma an rage hasken.

Inna wacce ita ma baccin ta kasa tana ta juye-juye, a kan idanunta

Please Login or Register in order to submit comment