You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi kwanciyarta. Yau ma kamar kullum hakan ce ta faru, Alhaji da tun da ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa ya hangi wayarsa da take kan bed side drower tana kawo haske wani murmushin gefen baki ya saki yana shafa haɓarsa, wajen wayar ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce ta kasance sunata ya gani kamar yadda ya yi saving my zee bakin gadon ya koma ya zauna ya ɗaga wayar cikin muryarta mai ɗauki da sinadarin shagwaɓa ta ce

"Haba baby ka barni sai tsoron nake ji ina dakon jiran dawowarka" Ta faɗa tana sakin kukan kissa. Wata ajiyar zuciya ya sauke tana jin ta har cikin kunnenta cikin ƙasa da murya ya ce

"Haba amarya ke kin san sai dai in wani abu ne zai riƙe ni amma ina nan zuwa gare ki, kin san dai daga kasuwa ma a nan na yada zango, to yanzu ma ina so ta yi nisan zango a bacci in lallaɓo in taho" Daɗi ne ya rufe Zee ta ce

"Sai ka ƙaraso" Amsa mata ya yi yana lunshe ido tonowa da ya yi da cewa yanzu idan ya je tana nan sanye da kayan baccin nan nata masu taushi da kama jiki.

Sai da ya ɗauki kamar minti talatin ya fito ya nufi ɗakin Mummy yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin, tun kafin ya shiga ɗakin kunnuwansa suka yi arba da munsharin da take sakin tamkar an shaƙewa raƙumi wuya, kasancewar tana da nauyin bacci har ya ɗan tsaya amma ko motsi bata yi ba ta yi shame -shame.

Ƙofar ya jawo mata a hankali, ya rufo, ɗakinsa ya koma ransa fari ƙal, yana zuwa ya ɗauki wayarsa da kuma mukullin ƙofar baya wacce yake bi ya yi ɓadda kama ya tafi gidan Zee.

Zee ƙawar Rahma ce amma ba ƙawa ta jiki sosai ba, sun yi aure da Daddy ba tare da sanin Hajiya ba kasancewar tsananin kishin Hajiya ya saka ta sanya shi ya mata alƙawarin ba zai mata kishiya ba, yanzu kuma da tafiya ta yi tafiya yana son ya yi auren amma babu hali. Don ba za ta bari ba, sun haɗu da Zee ne watarana ta zo wajen Rahma, bayan ta fita shi kuma yana ƙoƙarin shiga get ɗin gidan, hakan ya sa ya ɗauke ta a motarsa ya kaita har gida, daga nan ya karɓi lambar wayarta.


Komai a ɓoye ya yi hatta bikin Zee Rahma bata san an yi ba, saboda lokacin ta je hoto Kaduna gidan wata ƙawar Mummy.

Ya fito cikin dunu da yake gabaɗaya ƙwayayan gidan an kashe su, sannan shi ma ya kashe na ɗakinsa, yana lallaɓawa zai sauka daga matakalae kasancewar a sama suke, kamar daga sama ya ji an buɗe ƙofar ɗaki, da sauri ya ɗauke sawub takalminsa yana saurin ƙarasa sauka daga matakalar. haske ya hango an kunna fitilar harabar wajen, jin ƙaran tafiya ya yi saurin laɓewa, yana nan a laɓe sai ya ga Rahma ta sakko tana sanye sa doguwar rigar bacci hannunta riƙe da waya ta kunna fitilar.


Gabansa ne ya faɗi saboda ya san matsawar ta ganshi sai ta gane shirin fita ne a jikinsa, don bai yi kama da mai bacci ba, kuma ya san idan ta ganshi tamkar a kunnen Hajiya sai ta faɗa mata.

Fitilar falon ta kunna ta nufi frige ta buɗe ta ɗakko ruwan roba ta rufe, fitilar ta kashe ta haura sama, sai da ya ga duhu ya rasa saman alamar ta kashe fitilar kuma ya ji ƙaran buɗe ƙofa da rufewa, alamun ta koma ɗakin ta.


Ƙofar falon ya buɗe ya fita ta ƙofar bayan gidan ya kulle ta, machine ya samu ya tsare ya hau ya nufi gidan amaryarsa. Yana zuwa ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa ya shiga, yana zuwa part ɗinta ya ta buɗe ƙofar ya shiga ta rufe, yana kafe ta da idanunsa sai wani bubbuga ƙafa take wai ya ƙi zuwa tana ta jiransa, a rayuwarsa shagwaɓa da ɓacin da take masa shi yake rikita masa lissafi.


Kimanin wata biyu da yin aure suna cin amarcin su suna cin karensu babu babbaka, yana fitowa daga gidan Hajiya in ya ce zai tafi kasuwa gidan amarya yake zuwa, sai a shelaƙe zai je kasuwar, sai dai yaransa ne a kasuwar, sannan da wuri yake tashi ya koma gidan amarya, a can sai dare zai dawo gida kullum da uzurin da yake ba Hajiya, ko Ma'aruf bai sani ba, abu ɗaya ya sani shi ne Daddyn yana sanya shi ya ajiye shi a gidan amma bai san mai Daddy yake a gidan ba.

Sannan da dare ma sai ya lallaɓa ya je su kwashi soyayya ita Hajoya tana can kwance basho bata san wainar da ake toyawa ba.. Don haka amarya bata san bakin uwar gida ba saboda kullum ita ce take da miji safe rana da dare ma su kwana, sai ya yi asubanci ya koma, don a mota mai gadi yake mayar dashi da yake a gidan akwai motar Zee ɗin.


Ido biyu suka kwana suna bankar amarci tamkar ba za su rabu ba, Daddy ji yake yanzu kaf duniya babu abin da Zee za ta buƙata ya ƙi yi mata saboda yana samun yadda yake so daga wajenta. Tare suka shiga suka yi wankan su, ganin ƙarfe huɗu da wani abu ya ce zai tafi gudun samun matsala, dakyar ya samu Zee ta bar shi ya fito, mai gadi ya ɗauke shi kamar kullum a motar ya nufi gidan da shi a ƙofar bayan ya ajiye shi, ya buɗe ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya shiga ua mayar ya kulle.

A can cikin gidan Daddy kuwa Mummy ce ta tashi zaune, tana murtsuka idanu, tare da sakin doguwar hamma ta rufe bakinta, ta sakko daga gadon ta nufi bayin cikin ɗakin nata domin yin fitsarin da ya tashe ta, da ta fito har za ta koma kan gadon sai kawai ta fasa, ji ta yi kawai tana son jin ɗumin mai gidan nata, ita da ta ma manta rabonta da shi saboda ita a nata hankalin yanzu sai ta shafe tsawon lokaci basu kasance tare ba, tana ganin ai sun girma, bata san cewa shi namiji ba ya girma da buƙatar sunnar aure, haka nan namiji ba ya tsufa da haihuwa. Wayarta ta ɗauka ta kunna fitilar bayan ta kashe fotilar ɗakin nata da ta kunna, duk da ta san ana kiran sallag zai ce masallaci zai tafi amma dai ta san kafin lokacin sun kashe arnan soyayya ya haɗa alwala da wanka, tun da ta ga ƙarfe huɗu ta wuce.

Ɗakin nasa ta dufafa gadan-gadan ta kama hannun ƙofar ta murɗa tare da tura ƙofar ta buɗe...


*SHEIK*

A kiɗime ya ɗago yana kallon Mai Gari ya ce


"Aure kuma Mai Gari ni Sheikul Yemen, balaraben malami daga ƙasar larabawa?" Ya tambaya lokacin yana nuna kansa da yatsa.

Mai Gari ya ce

"Haba Ya Sheik kar ka manta ka sauka a garin nan don ka ceto garinmu daga halakar da shi da aljannu suke yi kuma yanzu wata gagarumar matsala ta taso a ce kana tambaya mai kamar tuhuma?"

Wani yawu Sheik ya haɗiye yana son nuna musu ba haka bane, cike da wayincewa ya ce

"Haba kai kuwa ina ni ina wannan babban al'amari ina so ne in san shin wa kuka samu ya mata ruƙiyya har ya gano wanann baban al'amari na aurena a tare da ita?"

Mai Gari da bai zaci waɗannn tambayoyin ba ya ce

"Sai an mata ruƙiyya za a gane haka, ita da kullum bata cikin hayyacinta ita fa koyaushe aljannunata suna tare da ita, ga shegen leƙen asiri da tone-tone, ai gwara ma da ta zaɓe ka to ai kai ne maganin iskancin nasu idan suka je maka leƙen asiri su ganowa kansu maganin su"

A zuciya Sheik ya ce

"Kun kashe ni, leƙen asiri kuma? Ni da ba gaskiya gareni ba ina ɗan rurrumawa amma yanzu a ce wai za a mini aure, auren ma da mai aljannu, in ƙi auren ku gano lagona' A fili kuma sai ya ce

"Kash aljannun nan basa kyautawa wataran" Ya faɗi hakan a ransa yana cewa sai ya , yanzu ni ai ba zan ke garajen faɗar laifukansu ba kar in je a yi ta kife da shi.

Ɗaya daga cikin dattijan sa suka zo ya ce

"Amma Allah gafarta malam, me ya sa ka ce basa kyautawa wataran ni a nawa tunanin aljannu ai kullum ma basa kyautawa, ka ga fa yadda yanzu suka ce idan baka auri amaryarka ba za a tashi yaƙi a garin nan a kashe rayukan garin rabi da kwata, kenan akwai wani abu ko dai kan tsoron su ne?" Sheik jin za a harbo jirginsa ya ce

"Ashsha Malam Wada ai ni nan aljannu ko wucewa na zo yi suna waje sai sun sara mini, ni ai ba zan ƙi aurenta ba bare ma kun ce ido ɗaya gareta ai mu a ƙasashen larabawa jihadi ne ka auri mace mai nakasa, kamar mai ido ɗaya ma muna kiranta mar'atul mubaraka, wato mace mai albarka"

Gabaɗaya suka ɗauki kabbara " Allahu akbar!"

Don sun jinjina masa, shi kuma a zuci kuka yake yana jin wannan auren kamar dai wata ƙulalliya ce aka shirya masa, tun da in akamce matarka ai dole za a ce za ta san sirrinka, shi kuma da yake da manya sirrika, ya zai yi rayuwar aure da mai ido ɗaya kamar ɓera ya leƙa buta, bayan nasa matan ma masu lafiyar ido ma ya bar su a can.

Haka ya ringa janyo kalmomin larabci wanda bai san ma'anarsu ba yana ta faɗa musu tare da kwaɗaita musu cewa duk wannan larabcin ayoyi ne yake janyowa a kan falalar auren mace mai ido ɗaya, yana yin hakan ne ko Allah zai sa ɗaya daga cikin su ya ce zai auri mai ido ɗaya amma sai ya ga babu niyya ango ya kwana da wando.

Ya amince da buƙarar auren saboda ba ya so ya ƙi su ga gazawarsa, ba ma komai ne ya ɗaga masa hankali ba sai da ya ji Mai Gari yana bayanin cewa asali da idanunta biyu aka haife ta amma daga baya kuma aljannu ne suka cire mata idon guda ɗaya, buɗar bakin Sheik sai ya ce

"Garin yaya?" Ya faɗa gabansa yana tsananta bugu.

Mai Gari ya ce

"Ai wataran aljannunta sun tashi sai aka ɗauke ta zuwa wajen mai magani, to mai maganin ne ya shiga dukanta da dorina, ashe dai aljannun sun ji haushi shi ne suka cirewa mai maganin mafitsara ita kuma suka cire mata ido ɗaya.

Dadammm gabansa ya yi wani irin bugu musamman da ya ji an yi batun mafitsara, tun da ya san dole in ya aure ta a yi sunna to kuwa ina zai yarda ya tuɓe a gabanta ya je a masa mai kankat wato a guntule shi kamar yadda aka bashi labarin an guntule wani malamin mai magani, lallai yana cikin jalala amma dai hakan ba zai sa ya nuna karayarsa ba, a matsayinsa na wanda ake girmamawa.

Haka suka yi ta saka masa albarka a ƙarshe suka ce gobe za a ɗaura auren tun da gudun kar aljannun su fara aika-aika a garin.

Duk da Sheik yana da son mata amma yana ji yana gani, wannan macen ba ya ɗokinta.

Bayan tafiyarsu haka Sheik ya kwana da zulumi bai runtsa ba, saboda ga damuwar aurensa da mai ido ɗaya, ga kuma yadda aka kwana ana taɓa jikin langa-langan da aka binne mai ƙusumbi a gidan.

Washe gari aka ɗaura auren Sheik da mai ido ɗaya, kowa sai kiransa ango yake, amma Sheik ransa ƙuna ma yake da aka ce an ɗaura auren. A ranar ne aka ce za ta tare gudun shaiɗacin aljannun kar su yi abin da suka ce za su yi a garin.

Ranar kaji biyu aka dafawa Sheik saboda sun zama su biyu, kuma dai a gidan da yake za su zauna shi tunaninsa ma buhun kuɗinsa da yake taro, da kuma ya zai yi in zai je wajen Malam karɓar magani, shi dai kawai gani yake wata maƙarƙashiya aka shirya masa don a tona masa asiri. Bayan magriba yana zaune a ɗaki yana tunanin yadda zai ke yi da hular gashin kansa kar amarya ta harbo jirginsa.

Turowar ƙofar gidan da kuma shigowar Mai Gari da mahaifiyar amaryar ta Sheik dukansu a kiɗime suna rafka sallama, shi ya sanya hantar cikin Sheik ɗin kaɗawa ya fito daga ɗakin a ransa yana ambaton Allah sa ma aljannun ne suka ɗauke ta da ya huta.

Mai Gari a rikice ya ce

"Sheik akwai matsala fa, aljannun nan dai sai ka tashi tsaye a kansu, suna son yin fito na fito da kai a gurin amaryarka, yanzun nan muna jiran fitowarka mu yi sallar isha'i sai ga sirikarka a kiɗime wai amarya tana shirin da za a kawo ta gidan miji, tun da ka ce ba sai an kawo ta da komai ba katifar ɗakin ma ta isa, abinku ku malamai mai sauƙi ne kar a yi wahala, to shi ne fa amarya ta kurma ihu mahaifiyar tana zuwa ɗakin ta ga amarya kwance amma abin mamaki abubuwan nan guda biyu sun ɓace ɓat babu su"

Gabansa faɗuwa yake duk sun ruɗa shi, ya kasa ma gane inda maganar ta dosa, uwar amaryar ce ta karɓi maganar da faɗin

"Wallahi sun ɗauke mata mashayar shayar da yara duka biyun(Breast) Babu ko ɗaya wajen ya shafe shafal kamar ƙirjin babe, ko in ce kamar bayan silba"


*MUNA DAB DA GAMA BOOK 1 WANDA PAGES KAƊAN SUKA RAGE MANA, KAMAR KULLUM KUN SANI INA BAKU BOOK 1 FREE BOOK 2 PAID, WANNAN KARON MA ZA A BIYA 500 KACAL DON KARANTA LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA KUN SAN DAI YADDA AKE CAKWAKIYA TO NAN MA BA ZA A BAYAR DA KUNYA BA IN SHA ALLAH.*

*MAI BUƘATA ZAI IYA TURA KUƊIN KARATUNSA TUN YANZU DON WASU TUNI MA SUKA BIYA, ZA A TURA ZUWA FAIZA ABAUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222 IDAN AKA KAMMALA CMPLT DOCMENT 800.*

MAMAN AFRAH
09025576222
[7/15, 8:21 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*


BOOK1️⃣
PAGE 13


IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture

*INNA TASALLAH*

Har aka ɗaura auren Jummai tana sume bata falka ba, Lami tana gefe mamaki ya kashe mata jiki, ta rasa ma ina za ta sanya wannan lamari shin waye mai laifi Jummai da ta kawo a karɓa mata haƙƙinta ko kuwa ita ma da aka cinye mata kuɗin adashe, ko dai Mai Gari ne mai laifi wajen rashin aiwatar da komai bisa adalci.

Inna ta sanya mayafinta ta kare fuskarta sai wani murmushi take dokawa, bayan an shafa fatiha sai Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce

"Sule ga amaryarka nan aure dai sunan ce ta ma'aikin Allah S.A.W ka riƙe ta da amana kar ka ga ta fika shekaru ka ce za ka mata abu na rashin kyautawa ko dai ka bari matanka su mata, ba zan lamunta ba, tun da dai ka ga ta yi hakan ne saboda ta sadaukar da kanta a matsayin kawo masalaha ga wannan tashin tashina da ake yi, ta yi biyan bashi da kanta ka ga hatta ni ta sama mini lafiya a kan wannan shari'a da ban san ranar ƙarewarta ba" Sulen yana wani murmushi sai washe haƙora yake ya ce

"Ai kar ka damu Mai Gari babu abin da zai faru kuma ai amarya ko ta buzuzu ce dole za a so ta a yi ɗokinta" Inna jin wanann lafazin sai ta ƙara jin wani daɗi a ranta.


Abin da basu fahimta ba shi ne Inna ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, ma'ana ta auri mijin Jummai saboda kawo maslaha sannan kuma saboda take samun abinci tun da yanzu ta ga dai idan aka kafa mata ƙahon zuƙa a kan biyan bashin nan hatta abinci ma sai ya gagare ta amma yanzu in ta yi auren dole dai a ciyar da ita, tun da ta lura abincin ta yana dab da ƙarewa kuma yanzu tun da da biyan bashi ba za ta samu sararin siyan abubuwa ba.

Cikin jin kunya ta ce

"Mai Gari a samo ruwa a yayyfawa ƴar uwata ta tashi mana" Kowa sai da ya jinjina lamarin wani ne daga cikin mutane wajen ya ce

"Kai Inna amma dai bakya ma kishi da Jummai"

Inna ta ce

"Haba ina ni ina kishi da ita" A daidai nan aka miƙo ruwa Lami da take cike da al'jabi da jin kunya ganin an ɗaurawa kakar mijinta aure a wajen ta karɓi ruwan ta yayyfawa Jummai, sai ga Jummai wuruf ta tashi tana waiwaye ganin jama'ar wajen da kuma Inna da take kakkare fuska da mayafi hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki take ba a zahiri ne.

Tana tashi tsaye ta kalli Mai Gari ta ce

"Ni ba ni aka yi wa amarya ba tun da ni ce mai bin bashi ni za a biya kuɗina tun da Sule ne ya auri mace"

Mai Gari ya ce

"Jummai Tasallah fa ta ce bata kishi da ke, kin fa zaman nan da za ta yi na ɗan lokaci ne, daga Ibra ya dawo za a bata takardar saki ta bar muku gida... Sule ne ya ce

"Aure ai ba abin wasa ba ne tun da har aka ɗauka babu batun saki, a bar Tasleey ta ƙarasa rayuwarta a gidana" Sunan Tasleey da Sule ya kira a maimakon Tasallah shi ne abin da ya ƙara fusata Jummai, sannan shi ne abin da ya faranta ran Inna ta ji ta dawo tamkar ƙaramar yarinya.

Cikin harzuƙa Jummai ta ce

"Mu zuba mu gani sai na zame muku ciwon ido a gidan nan" Tana faɗar hakan ta juya fuuuu ta bar fadar kamar za ta hantsila.

Mai Gari ya ce ya sallami kowa, ya kalli Inn yana dariyar wasa ya ce.

"Ka ga amarya ran gida, amarya bakya laifi Tasallah amaryar Sule" Wani daɗi Inna ta ji, ta kunce ƙullin hannun zaninta da ta yi ta ɗauko kuɗin kayan miyarta haka ta zaro ɗari biyar ta ce

"Mai Gari ga jaka biyu da rabi (500) Ka ci goro" Sosai ya ji daɗi yana washe baki ya ce

"Yaushe za ki tare?" Ta ce

"Yo tun da aure ya ɗauru ni kuwa tariyar mai zan jira ai a yau ba sai gobe ba"

Sule ya ce

"Dama akwai ɗakina kawai sai ta zauna a ciki".

Lami tsaye ta miƙe ta ce

"Mai Gari ni ina nawa zancen ya kwana tun da ita Jummai an samu mafita?" Kallon sheƙeƙe ya mata ya ce

"Ana batun giwa wa yake maganar ɗan tsako, amma dai ai kin san wanda ya zai je sama ya taka leda ya ci ƙarfin tafiya ko?" ,Takaici ya sa bata sake cewa komai ba, juyawa ta yi sai Inna ta ce

"Yanzu Lami maimakon ki tsaya ki ɗauka mini samirar nan da ledar kayana, ki raka ni gidan in kintsa, amma kya tafi ki barni ai an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo"

Cike da jin haushi Lami ta ce

"Haba Inna tun yanzu ai a tunanina duk gaggawar asara ta jirayi samu" A faɗa ce Inna ta ce

"Ke kika sani ƴar baƙinciki wato kina jin babu daɗi na samu jirgina ya ɗaga na yi aure bayan a gari ga yan mata nan galla-galla da zawarawa masu jini a jika amma ni na tashi na barsu, to ai dama abin rabo ne auren mace da ciki"

Takaicin ta ta danne ta ce

"Haba Inna ai ba batun baƙin ciki ba ne, ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ni ma ba zan so ki ƙarasa rayuwarki babu aure ba, gwara ki yi ko a sama mana ƴan ƙanne"

Kallon kallo aka shiga yi a fadar Lami ta sunkuya ba don ta so ba ta ɗauki samira da ledar Inna ta yi gaba, ita kuma Inna ta tashi tana ta jin kunyar jama'ar wajen Mai Gari ya ce

"Tasallah babu batun kunya ba a aure kuma ai jahadi kika yi" Ya faɗa yana saka ɗari biyar ɗin da ta bashi a aljihu.

Inna ta ce

"Haka ne ai da rashin tayi ake barin araha, kuma da rashin kira karen bebe ya ɓata"

Gabaɗaya ƴan fadar aka amsa mata ana mata jinjina, har ta yi gaba Sule ya tashi yana washe baki ya ɗan bi ta suka keɓe ya ce

"Amarya bakya laifi, yaushe za ki zo"

"Ta ce ahaf dag an yi sallar isha'i mana za a rako ni, kar in je in zauna Jummai ta zo ta min tijara a kan kuɗin saniyar da na fansa da aurenka"

Haka ya tafi yana wani waiwayen Inna, wasu daga fadar suna masa kallon sha-sha-sha.

Tafe suke a hanya Lami tana barin Inna a baya har Inna ta gaji ta ce

"Lami sai wani cin magani kike, wai ke baki san mata tsoffi ƴan da basa tsufa ba, mu fa nan mu ake yi wa laƙabi da mace daki bari" Cike ta haushi Lami ta ce

"Daki bari kamar wata atamfa?" Inn ta ce

"Yo ai atamfa wataran tana yagewa ko ta mutu a jefar da ita, amma mutane da ƙarko garemu kuma shi namiji ba ya ganin tsufan mace waɗannan matan nasa sai ki ga na je na fiye masa su sau miliyan, duk wannan hayagagar da Jummai take wiyarta in tare ai duk wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa rawar, dama alƙawarin Malam na ɗauka na ce ba zan yi aure ba amma yanzu na fasa aurena zan zauna yo malam ɗin ma da shi ne ba lallai ya bari a mini arba'in ɗin mutuwa ba zai gallo wani auren, ita ma Jumman kallon raini take min bata san cewa idan makaho ya ce a yi wasan jifa to tabbas ya take dutse ne, amma dai zan nuna mata gani ya kori ji"

Banza Lami ta mata, har ta fara tunanin ma dama duk rawar kan Ibra da rashin jin nasa wajen Inna ya yi gado.

Suna dab da ƙofar gidan Inna Lami ta ce

"To Inna ga kayan ni zan wuce gida, Inna amarya ta ango" Ta faɗa cike da gatse.

Inna ta kalle ta ta ce

"Kin ga Lami kar ki

Please Login or Register in order to submit comment