You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanann abin kunyar a ce limamin gari guda amma ya yi fitsari a wando, ku taimake ni kar ku kunyata ni' Ya faɗa a zuciyarsa yana wani damƙe idanu tare da haɗe ƙafafunsa waje guda yake fafutukar matse su.

Ɗayan ne ya fisge rigar da ƙarfi ya zungura kansa wanda kan nasa yake a saitin mazaunan Malam Liman, Malam liman ana zungurar mazaunansa ya ji guntun fitsari kaɗan ya kufce masa da sauri ya sake haɗe ƙafafun don ya lura in bai yi da gaske ba sai an saka shi ya saki fitsarin nan duka.

Hannu ya miƙa ya sakarwar kan wannan saurayin wanda yake kusa da mazaunansa, ya sakar masa ranƙwashi a zuciyarsa yana faɗin

'Shegun yara, kamar da ubanku muka haɗa kuɗi muka sayi rigar, sai ja kuke kamar kun samu guga a rijiya' Ya faɗa a zuciyarsa yana jin da a lafiya ƙalaw ake ko iyayensu ba za su yarda su shiga rigarsa ba saboda yadda yake da kima ana girmama shi, a matsayinsa na Limamin garin.

Saurayin nan da Liman ya kaiwa ranƙwashi, zafin ranƙwashin ya saka shi ƙara cukuikuye rigar Liman da gangan, dama shi ne wannan me ƙarfin da aka taho da shi zai buɗe ƙofar gidan, wato ƙaƙƙarfan. Jan rigar da ya yi shi ma ɗaya saurayin yana ta ƙoƙarin ja ya rufe kansa, sai ya zamana gabaɗaya an shaƙewa Liman wuyansa, jin shaƙe wuyan yana barazana ga maƙogwaronsa sai ya lanƙwasa kansa da sauri ya zame kansa daga cikin babbar rigar, hakan ya sa garin ya zame rigar sai kansa ya fita daga cikin bargon da suke tare da Sheik, shi kuma Sheik sai ya ja bargon ya ƙara duƙunƙune kansa, don yana a goho ne duk da yana jin kashin. Samarin nan jin Liman ya sakat musu rigar sai suka cure waje guda suka rufa, tun da yanzu ta ishe su sun rufa tare dama saboda tana jikin Liman ta musu kaɗan.

Malam Liman kasancewar a firgice yake kuma a tsorace kansa yana fitowa daga rufar da yake sai idanunsa suka masa gizo da ganin Kakan Mai Gari wanann marigayin da aka binne a gidan, ya tsago jikin ƙofa yana tahowa sanye da likkafaninsa, ya ɗan duƙa kasancewar yana da ƙusumbi.

A kiɗime Liman ya nayar sa kansa ya cusa a katifa haɗe da cewa

"Wallahi marigayi kakan Mai Gari wato mai ƙusunbi ya tatso ta jikin ƙofa ya shigo ɗakin nan"

Ya faɗa yana miƙa hannu a niyyarsa ya samo bargon da ya fito ya shiga, sai ya cafko towel ɗin jikin Sheik, Sheik kuwa jin furucin Liman na cewa Kakan Mai Gari ya shigo ɗaki, hakan ya tuna masa da jawabin da Audu ya masa a daren jiya na cewa Kakan Mai Gari ƙasa ta ƙi karɓarsa da ya mutu, saboda saɓon da yake yi, sai gida aka dawo aka masa kabari aka binne. Kenan wanda ake zuwa maƙabarta ana samun sa yana gefe kabarin da aka saka shi ma a gefe, to ba abin mamaki bane in aja ce yanzu ya taso da ƙafafunsa, wataƙila fatalwa ya yi. Tsabar ruɗanin da Sheik ya shiga yana jin an iska ta fara shiga jikin mazaunansa alamar mazaunan nasa a buɗe suke tantagarya, amma tsoro ba zai bari ya suturta su ba, don shi tunaninsa towel ɗin zamewa ya yi.

Samarin nan jin furucin Liman sai suka rungume juna kamar sa zama mutum ɗaya, haka kowanne yake jin bugun zuciyar ɗan uwansa alamar dai ana cikin fargaba da tashin hankali, Malam Liman da ya samu towel ɗin Sheik ya rufe yana ta ƙoƙarin son ya ga ya samu ko da addu'a ɗaya ce cikin wanda ya iya don yake karantawa ko a zuciyarsa ce amma ji ya yi gabaɗaya ya manta komai a halin da yake ciki yanzu gani yake sunansa ne kaɗai zai iya tunawa. Yana wannnn halin ne ya ji saukar hannun Mai Gari a bayansa, wanda hakan ya sa ya ɗauka hannun marigayi mai ƙusumbi ne wanda ya masa gizo, duk tunaninsa a zahiri ya gan shi, hakan ya sa gumi ya shiga zarya a gabaɗaya ilahirin jikinsa tare da kufcewar wannan fitsari da yake ta dannewa, saboda yanzu an zo wajen da ba ta girma da martabarsa ta Liman ake yi ba, ana magana ne ta ceton rai tun da har yana ganin gawa ta taɓa shi, gawar ma ta marigayi mai ƙusumbi.


Liman a zuciyarsa yake faɗin

'Allahu akbar! Tamu ta zo (Yana nufin mutuwa) Allah ka bamu ikon amsa tambayar kabari, Allah ni nake jan sallah a garin ƙundu ka bani cikawa da imani' Wannan yake ta maimaitawa a zuciyarsa.


Mai Gari kuwa hannun da ya miƙa shi lalumen bargon Sheik yake yi, so yake ya koma cikin bargon Sheik ko ya samu salama a ransa, tun da yana ganin bargon Sheik za a samu tsari kasancewar malamin balarabe ba za a ce ruɗani ya hana shi addu'a ba.

Jin ya sauke hannun nasa a jikin riga, kuma ya san dai Sheik bashi da riga suka shigo ɗakin, tun da idanun Mai Garin a rufe suke ba ya so ya buɗe bare ya ga fatalwar kakansa mai ƙusumbi, son ya fara tunanin ma kar dai mai ƙusumbin ya ce ya zo ya tafi da shi ne. Hannun da ya fara matsarwa a jikin Liman kasancewar rigar Liman ta shadda ce ta ci uban duniyar ta da tsinke, domin daga baya a yage take kasancewar ya ɗora babbar riga shi ya sa ba a ganin yagar, yanzu kuma da samarin nan suka sa ya cire babar rigar sai yagar ta bayyana a bayansa. Hannun Mai Gari ne ya shige cikin bayan Liman ta wanann yagar, hakan ya sa ya shafo bayan fatar jikin Liman.

Liman mutuwar kwance ya yi don zuwa yanzu ma kawai bakinsa ne yake karkarwa kamar wanda zazzaɓi ya yi wa mugun kamu, haƙoransa suna haɗuwa da juna, saboda ya gama saddaƙarwa cewa fatalwar mai ƙusunbi ce ta dama masa baya take shafa fatarsa, ya san yau babu makawa da shi za ta koma lahira

Mai Gari da sauri ya ɗauke hannunsa, saboda fatar da ya taɓa ya ji wani karsansan, alamar fatarsu ce irin ta baƙaƙen fata, ya san ta Sheik tana da laushi da santsi irin na larabawa, shi zai tabbatar da haka tun da jiya ya kama hannun Sheik mai laushi kamar na jarirai, bai san cewa tsabar amfani da allurai da magunguna da kuma sabulai na garan fata ne ya sa take duk a yanayin da ya ji fatar.

Yana ɗauke hannun ya miƙa wani wajen tun da gabaɗayan su a kan katifar suke, duk sun cushe, tun da su biyar a kan katifa ɗaya, yana ƙara miƙa hannun ya sauke a kan ƙafafun samarin nan shafawa ya yi sai ya ji wani gautsin fata, don har ya shafo kaushi da faso a ransa ya ce

'Kai jama'a har yanzu dai ina ta dawurwuri a jikin ƴan ƙasar nigeri'a Allah ka kaini a kan daidai wato in taɓo fatar balarabe' Ya faɗa yana jin tausayin kansa.


Samarin nan kuwa jin an taɓo musu ƙafafu, kowanne sai numfashinsa ya tsaya cak! Tunanin su fatalwar da Liman ya gani ce za ta yi awon gaba da su. Juna suka ƙara ƙanƙamewa kowanne yana ta ƙoƙarin warto addu'a a zuciyarsa domin ya kuɓuta, sai dai a cikinsu babu wanda ya yi nasarar ambatar kowacce addu'a don ruɗanin ya kai ruɗu.

Gwiwarsa ya ja bargonsa yana ƙamale a kafaɗarsa idanunsa a rufe, ya miƙa hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan mazaunan Ya Sheik, laushi luɓus ya ji, hakan ya sa ya miƙa ɗaya hannun ma ya zamana hannayensa biyu a kan mazaunan don yana son tabbatar da cewa tabbas a kan fatar Ya Sheik ya sauke hannunsa, amma fa duk abin nan da yake bai san cewa a kan mazaunan Sheik ya sauke hannu ba. Sheik kuwa jin an taɓa masa mazaunai a lokacin ya ƙara gane mazaunansa a tantagarya yake babu rufi ba ma wannan ba lalumen da Mai Gari yake yi nema yake ya wuce gona da iri a wajen Sheik domin kuwa hannunsa yana neman taɓo mafitsarar Sheik, Sheik wanda tunaninsa ya fara bashi cewa fatalwa ce take lalumen jikinsa sai ya ƙara tsorata ya shiga ruɗu, da tunanin kar dai fatalwar mai ƙusunbin tana so ta tsinke masa mafitsarar ne gabaɗaya ma, wani sashen na zuciyarsa yana bashi cewa ko dai shayi ake son a masa(Kaciya,sallatu) Idanu ya zaro bai san lokacin da ya buɗe baki ba gabaɗaya ya manta sa ƙalƙalar sa yake yi ta larabci wajen yin magana, wato yadda ko hausa yake sai ka ɗauka ɗan koyo ne.

Wanann karo da hausa sak irin yadda bahaushe yake magana babu gargada ya ce

"Wallahi na rantse da Allah an mini kaciya, don Allah kar a cire mini mafitsara" Ya faɗa a fili ɗakin har yana ɗaukan amsa kuwwa. Don ya fara tunanin kar a je ko dai a tsinke masa mafitsarar ko dai a je garin masa kaciyar a yanke fiye da rabin mafitsarar a bar masa ƴar guntuwa. Yana faɗa wani hawayen tausayin kansa ya cigaba da zubo masa domin ya fara tuno matansa su Lami da ya baro a ƙauyansu ya san duk inda fatalwar kakan Mai Gari ya gabce masa rabin mafitsara, ko ta cire masa gabaɗaya to in har ma bai mutu ba kenan, ya san shikenan sai dai kowacce ta ce ya bata takardar saki, tuno da wannan kuma ya san yana son matansa sai ya ƙara ware murya duk da yana cike da tsoro ya ce

"Wallahi ina son matana, ba zan sake su ba wani ya aura" Mai Gari tun maganar da Sheik ya yi ta farko wato inda ya ji Sheik yana batun kaciya da cire mafitsara, bai san lokacin da ya ɗauke hannuwansa salin alin da sauri ya koma wajensa da ya taso ya kifa kansa yana ambaton

'Lahaula wala ƙuwwata ' A zuciyarsa, don shi ya san dai ya ji an yi magana amma ko za a saka masa wuƙa a maƙoshi ba zai gane ga wanda ya yi maganar ba, sannan ruɗanin da yake ciki bai bari ya gane cewa Sheik ne ya yi maganar hausa sak ba, babu ƴar ƙalƙalar larabcin.

Malam Liman jin ana ambaton kaciya sai ya fara tunanin ko dai fatalwar ta yanke shawarar yayyanke musu mafitsara ne hakan ya sa ya saki towel ɗin da ya rufe kansa da shi, ya mayar wajan matse matsin ƙafafunsa a nufinsa ya yi shirin ko ta kwana, saboda kar a masa sakiyar da ba ruwa.


Gabaɗaya kowa da zaman jiran tsammanin da yake, Sheik ya yi ƙarfin halin jan bargon ya rufe mazaunansa, yana jin da na sanin zuwa garin ma baki ɗaya, sai dai shegen kwaɗayi da son abin duniya ba za su bari ya bar garin ba, ya yi wa kansa alƙawarin zama daram sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi.

Mai Gari ya jiƙe da gudmi sharkaf ga gwiwarsa ta ƙafa da ya tsunduma a fitsarin Liman, amma dai yanzu a matsayinsa na Mai Gari gashi kuma yana tsoron mutuwa dole zai yi ƙoƙarin yin magana don a samu mafita, tun da tana ganin duka manyan garin ne a ɗakin, idan kuwa fatalwar mai ƙusumbi ta musu fata-fata to gari yana cikin garari.

Su kaɗai suka san gari lafiya lau yake, amma shi Sheik har yanzu tunaninsa wani gudun famfalaƙin tsoron ne ya sa suka yi hijira daga cikin gari zuwa gidansa.

Da muryar kuka kuma muryar a shaƙe kai daga ka ji maganar ka san mai yinta ƙarfin hali yake Mai Gari ya ce

"Ya Sheik, muna buƙatar taimako, muna buƙatar addu'a kar fa a mana ɗauki ɗai-ɗai, ka yi addu',a mana, mu baƙaƙen fata muna cikin wani hali kaima babban malami kana...

Tun Mai Gari bai kai aya ba Sheik ya daure ya yi ƙarfin halin saita ƙalƙalar hausar larabcinsa ya fara cewa

"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Tun da ya sanu nasarar yin a'uziyyar nan shikenan yake maimaitawa don shi ita kaɗai ya iya kamowa, don haka bai damu da cewa yana ta maimaitawa za su ce wani abu ba. Mai Gari da yake jiran ya fara jin ana zayyano addu'o'in larabci masu yawa bayan gama a,uziyya da bismillah sai ya ji ba a fara ba ana ta maimaita abu ɗaya. Can ya ce

"Haba Ya Sheik ka fara addu'ar da muke ji ana karantowa a ƙasar makka mana" Ya faɗa yaba ɗan ɗaga muryarsa da take ta zillo tana rawa, tare da saurin gyara fuskarsa daga inda ya nutsa ta a jikin katifa jin ya danne hancinsa numfashi yana neman gagararsa shaƙa, amma fa duk maganar nan da ya yi Sheik bai ce uffan ba kuma bai fasa faɗar abin da yake faɗa ba, saboda shi a ganinsa ya samu makamar ceton kansa.

Liman da samarin nan jin muryar Sheik ta karaɗe ɗakin yana faɗin

"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Cikin muryar larabawa tamkar wanda wani balaraben gaske yake yi, basu san cewa Sheik sai da ya daɗe yana yi wa muryarsa training a kan ƙalƙalar kafin ya zo garin nasu ba.

Liman da samari basa bambance abin da yake faɗa, don yadda yake maganar tamkar wata doguwar sura ce yake karantawa sai suka shiga mishi amshi da faɗin

"Allahu akbar!" Idan ya faɗa sai Liman ya ce

"Attakabir" Sai samari su ce

"Allahu akbar!" Mai Gari ma tuni ya bi yarima yake shan kiɗa, don ya lura shi kaɗai ne muryarsa bata fitowa a cikin ɗakin, yana tsoron abin ya zama shi kaɗai zai samu.

Sun kwashe sama da awa suna a haka, sannan ne Sheik ya ji ƴar nutsuwa, ya buɗe ido ɗaya ya ƙyallara ya ga dai ɗakin babu kowa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tunanin abin da ya faɗa ne ya sanya fatalwar ta fita daga ɗakin.

Daƙyar ya ɗago daga gohon ya zauna, ganinsa babu towel ɗin nasa, sai ya ƙura ido a mafitsararsa yana son ganin ko an masa shayin, amma sai ya ga yadda take haka take, sai dai ta yamushe a waje guda ta tattare saboda wahala. Har lokacin bakinsa bai yi shiru da abin da yake faɗa ba, hannu ya kai ya fisge towel ɗinsa na wajen Liman, Liman da dama bai riƙe towel ba kasancewae hannuwansa suna matse a matse matsinsa, sai ji ya yi an buɗe masa kansa, hakan ya sa ya ƙara runtse ido haɗe da bada ƙaimi wajen ƙara danna hannuwansa don ganin ba a yi kaciyar nan da shi ba, har lokacin yana faɗin

"Attakabir" Da sauri Sheik ya ɗaura towel ɗin ya ɗan muskuta ya koma kan sallayar da take shimfiɗe, tare da miƙa hannu ya ɗakko hirami a jakarsa yana gyra zaman hularsa da gemunsa, sai da ya zauna yana kallon gabas , ya rufa hiramin yana ta cigaba da a'uxiyya.

Dakyar ya samu nasarar warto suratul fatiha a bakinsa, ya shiga karantowa, sai da ya yi sau uku, sannan yana zaunen ba tare da ya juyo ba ya ce

"Alhamdulillahi, na samu nasarar korar fatalwa, komai ya dawo daidai" Ya faɗa cikin muryarsa ta balarabe. A hankali suka fara tashi zaune kowa yana ɗan ƙyallara ido, ganin babu fatalwa a ɗaki, sannan Sheik yana kan sallaya ya rufa hirami sai suka fara hamdala Mai Gari faɗi yake

"Allah mun gode maka da ka kawo mana babban malamin larabawa da yau ya za mu yi?" Ya faɗa yana kallon gwiwar ƙafarsa, da ta jiƙe, shi kuma Sheik bai ma san inda gudawarsa ta yi ba domin yanzu ba ya ma ji.


Malam Lima cewa yake

"Ai ba ƙaramar sa'a muka yi ba" Ya faɗa yana ɗan satar kallon wandonsa da ya jiƙe ya ce

"Wannan yara an yi yaran banza, yanzu a cikin ku aka samu wani marar imanin ya zage wando ya mini fitsari a jikina?" Ya faɗa yana kallon samarin nan da suke sharkaf da gumi. Ɗaya ya buɗe baki zai yi magana Mai Gari ya yi saurin cewa

"Kai ba a son wani tone-tone ku bashi haƙuri" Haka suka bashi haƙuri ba don son so ba, sai don ba yadda za su yi kuma dai ga wandonsa ya fi nasu jiƙewa tun da shi ya yi fitsarin su dai kawai sun shiga lemar ne.

Liman daɗi ya ji a ransa ganin girmansa bai zube ba. Nan suka kalli Sheik da ya juyo daga kallon gabas yana gyara zaman towel ɗin da hiraminsa, gumin da yake yi tamkar ya dawo daga filin tsere.

Mai Gari yana kallonsa ya ce

"Sannu Ya Sheik lallai ka yi artabu" Sheik a zuciyarsa ya ce


'Artabun yau ka gani, da ka ga na jiya da na sha da ina ga wano zancen ake ba wannan ba' Amma a fili sai ya ce

"Kai wannan ai ƙaramin abu ne, ai ina tabbatar muku kuna zuwa cikin gari za ku ga aljannu sun lafa komai ya daidaita" Da mamaki suke kallonsa jin yana batun cikin gari, Malam Liman ne ya ce

"Cikin gari babu lafiya ne dama?" Shiru Sheik ya yi yana tambayar kansa a zuciyarsa cewa

'To da uban me ya taho da ku da gudu idan ba tashin hankali kuka baro a cikin garin ba?' A fili ya ce

"Dama cikin garin lafiya, na ɗauka ai babu lafiya da na ga kun shigo gidan nan a kuɗime" Mai Gari ya ce

"A'a gari lafiya ƙalaw dama zuwa muka yi, mu ga ko lafiya mun zo da asuba kiranka a yi sallah amma aka gaji da bugawa shiru, to shi ne muka samo samarin nan muka ce su ɓalle ƙofar a duba lafiyarka, da aka tura ƙofa kuma sai muka hango ka taho a guje da takalmi ɗaya a ƙafa jiki duk kumfa, wannan dalilin ne ya sa mu ma muka ga tun da har kana gudu to akwai gagarumar matsala gwara mu bika mu tsira ka ji dalili amma gari kowa yama sabgar gabansa lafiya" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wani mugun haushin su, da suka firgita shi, shi a nashi tunanin garin ne a ruɗe suka taho ashe dai shi ya ruɗa su.

Cike da ƙarfin gwiwa ya sheƙo wata sheƙeƙiyar ƙarya don kar a ga gazawarsa ya ce


"Ai nake faɗa musu ina cikin banɗaki ina wanka, nan na ga wani aljani mai ƙaho bakwai ya tsaga bango ya fito, yana fitowa ta sheƙe da dariya yana cewa, wai yanzun nan za su saki manyan aljannun da za su rikita gari, kai har cewa ya yi mai gari ma ɗauke shi, za su yi, wannan dalilin ne ya sa ina nuna shi da yatsa wani hayaƙi ya tashi da shi sama, ya bi iska ya ɓace, to ni kuma tuno halin da garin zai kasance shi ne na fito hankali a tashe domin na kai muku ɗauki cikin gari, ganinku a guje kun shigo ya ƙara sanya hankalina ya tashi, saboda bana son jama'a su shiga damuwa, sai yanzu bayan na gama addu'ar nan na gano ashe dai aljanin nan ne ya shiga jikina ya haifar da tsuma da ruɗu da tsoro, don kar in taimaka muku, shi ne fa muke rige-rige tsakanin ni da ku wajen samun maɓoya" Ya faɗa yana dafe goshi alamar damuwa.


Mai Gari har da ƙwallar farin ciki ganin ba ƙaramar ƙauna Sheik yake yi wa garin nasu na Ƙundu ba, sannan ba ƙaramin taimakon su yake yi ba, bai san cewa Sheik kasuwanci ya zo yi a garin nasu ba, don ba a aikin banza a ko ina.

Cike da girmamawa ya ce

"Allah saka da alkairi Malam ashe kana ta fafutuka ne a kan garinmu, silar haka har aljani ya shiga jikinka ya saka muke tsere, bawan Allah dama na yi mamakin ganin muna ta neman mafaka tare da kai ashe dai ba da kai muke nema ba, da aljani ne" Ya faɗa yana kallon Sheik.

Liman ya ce "Ai ni na yi mamaki dama, malamai ai magada annabawa ne" Sheik ya ce

"Ina ai ƙaryar aljani in ji tsoronsa, su kansu sun sanni" Ya faɗa amma yana ɗan rage murya saboda tuno kunnen jaririn da aka jefo a banɗaki.

Liman ya ce

"Allah mai baiwa, ku dai Allah ya baku" Sheik aka wani gyara zama gudun kar towel ya kunce ya ce

"Ai aljanin ya yi niyyar hanani yin addu'a ma lokacin da fatalwa ma ta shigo hatta bakina sai da suka so riƙe mini, yanzu ma sai da na sha fama na hau sallayar nan, so suka yi kar in yi addu'a" Gabaɗaya suka ce

"Allah ya fi su"

Nan dai aka sa samarin nan su fita da katifa su gyara ɗakin, a nan ne ma Mai Gari ya ƙarewa Sheik kallo ganin idanunsa luhu-luhu alamar ko dai kuka ko rashin bacci ya ce

"Ya Sheik ka ga idanunka kuwa, hatta fuskarka a kumbure take" Sheik tuno artabun da suka sha jiya da jarirai da aljannu har ya hau bishiyar kuka, sai ya ɗan yi gyaran murya ya ce

"Haba Mai Gari wanann tambayar ma ai ɓata baki ake yi, ni da na zo taimako ina ni ina bacci, ai ni nan da na gama cin abinci kawai alwala na yi na hau sallaya, nake salloli ina addu'a ban tashi ba sai da aka fara kiran assalatu, shi ne na sake alwala na yi shirin fita masallaci, sai kuma na tuna ku ne za ku zo mu tafi tare, to dai ni ban ji zuwanku da asubar bama don ni nan na yi sallah da nafiloli, wataƙila aljannu sun saka mini auduga ne a kunne shi ya sa ban ji bugun naku ba" Ya faɗa yana kai hannu ya share zufa a goshin sa.

Sosai suka jinjina masa, daga nan suka ce za su je a kawo masa abin kari, nan ya ce wainar ƙwai da dafaffan ƙwai sai a biredi da shayi me kauri. Mai Gari sai da gabansa ya faɗi, jin abubuwan da ya zana, sai dai har da wasu sunayen abubuwan larabci da shi kansa Sheik bai san mene ne ba, ya zayyana sai da Mai Garin ya ce vasu san abubuwan ba sannan Sheik ya ce a barsu dama abincin su ne na ƙasar larabawa.


Bayan samarin sun gama gyaran suka tafi da su Mai Gari. Lokacin ya saka jallabiya, ya ce zai yi wanka, suna tafiya ya gabansa yana faɗuwa, amma haka ya je ya garƙama sakata ya ɗauki ruwa ya tuɓi ya yi wanka a tsakar gidan, don ba zai iya komawa banɗakin a lokacin ba. Yana gamawa ya buɗe ƙofar gidan saboda masu kawo abincin don an ce masa mutane za su fara zuwa neman magani yanzu gidan zai cika maƙil in ya gama cin abinci.

Juyowar da zai yi ya yi arangama da wani ƙaton hanci yashe a tsakar gidan, amma girman hancin ya yi kan mutum da gudu Sheik ya doshi ɗaki towel a hannu don da ya kunce gani ya yi bashi ma da nutsuwar tsayawa ya ɗaura.


Yana shiga ɗakin ya banke ya jingina da jikin ƙofar yana mayar da numfashi, a fili ya ce

"Ko a ni ko a ku aljannun garin nan, wato kun ga ana girmamani hassada da tsana suke damunku, yadda zan ke shan ganimar girki, da kuɗaɗen magani ana biyana yasin babu inda zan gudu, ba hanci da kunne ba kai ko karo zan ke ci da mafitsara kuna jefowa aradu sai dai na gudu ɗaki amma dai arziƙi sai na dagwala a garin Ƙundu" Ya faɗa yana ƙarasawa ya zauna, ya shiga shafa mayukansa, sai da ya gama tsaf a saka kayansa ya samu turarukansa masu ƙamshi ya shafa saboda su kashe warin mayukan bilicin yake yawan amfani da turaruka.

Yana gamawa ya kabbara sallah, sai lokacin ne ya yi sallar asuba, a lokacin kuma Audu yake rafka sallama, gyaran murya ya yi, sai da ya sallame sanann ya

Please Login or Register in order to submit comment