You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Shafi na 18*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*







suna zaune suna kallo itada Sayid suna rigima akan remote wayar Mama tafara ƙara, sakar masa tayi tana cewa, "maza ka cinye idan ka tashi, ni bari na kaiwa Mama waya Allah yasa ma muji ance Anti Zulaihat ce ta haihu"

Kafin taƙarasa ya rigata saurin ɗauke wayar yana dariya yace, "da yardar Allah sai satin aurenki zata haihu ni kuma ni zan kai mata wayar kinga anfi ƙarfinki kenan dole ki zauna ki kalli Arewa"

Kansa tayi da nufin ƙwatar wayar sai yatashi da gudu yayi waje itama ta taka masa baya, sai da ya riga ya miƙawa Mama sannan ta ƙaraso tana numfarfashi, harara kawai ta zuba masa sannan ta maida hankalinta kan Mama, jin ta zuba salati ne yasa ta zaro ido tana kallonta, tana sauke wayar ta jefa mata tambayar "me yake faruwa?"

Mama tace, "oo ikon Allah kenan, kana taka Allah na tashi Yusuf Jose ne yayi haɗari yanzu ma haka suna asibiti abun kamar almara"

rarassss zuciyarta ta buga firgitar da tayi tasa ta sarƙe da yawunta ta ƙware aikuwa tafara tari me tsananin zafi takawa tayi da nufin barin gurin amma takasa saboda wani irin tangaɗi da take can ta tsinci kanta a jikin bango lokacin har tafara ganin duhu gashi tarin ba dena shi tayi ba, dishi dishi take iya ji da ganin Sayid da Mama da suka taru akanta ruwa ma Mama ke miƙo mata amma azaba ta hana ta amsa, lokaci ɗaya ta jigata matuƙa ta fita daga hayyacinta idanunta sunyi jajir sun ƙara firfitowa indai kana da zuciyar imani kayi mata kallo ɗaya sai ka tausaya mata, su Mama duk sun ruɗe sun rasa yadda zasuyi gashi da alamu duk maganar ma da sukeyi bata jinsu, ta ɓata lokaci cikin wannan yanayin kafin ta fashe da wani azababben kuka me matuƙar zafi da raɗaɗi"

cikin sanyi Mama tace, "Aisha sannu maza kisha ruwa ki dena kukan kinji ko??"

Girgiza kai tayi alamar "aa" ƙoƙarin tashi tafarayi Mama ta temaka mata da bi bango ta isa ɗaki wayarta ta ɗauka tafara neman lambarsa amma taji a kashe, wani sabon kukan taƙara buɗewa tashin hankalin ta yaƙara ninkuwa a yanzu bata da buri ko muradin da ya wuce tayi tozali dashi taga halin da yake ciki hankalinta ze fi kwanciya, iya rarrashin duniya anyi amma taƙi dena kuka dan dole suka rabu da ita ta cigaba da yin kayanta har zuwa lokacin da ta gaji ta dena sai sauke huci da ajiyar zuciya, Bata dena kiran lambarsa ba amma duk da hakan taƙi tafiya.

Khaalif yana shigowa Mama ta sanar masa zataje asibiti da daddare duba Jose.
tinda Aisha taji haka ta fitar da rai da samun nutsuwa koda sunje da ita, daren kuwa yanayi Khaalif yace babu amfanin zuwa da yara asibiti dan haka ta zauna ta kula da gida ita kuwa Mama ta yarda, baƙin ciki kamar ya kasheta ji take inama zata iya ta rufeshi da duka sai dai hakan baze amfana mata komai ba dan abun takaici kuma yace baza a je da ita ba kuma an tafi da Sayid sai kace shi ba yaron bane,

duk mutanen da suke wajen ba ta tasu yake ba ido kawai yake
bazawa ko ze ganta amma ko me kama da ita be gani ba wata sabuwar damuwar ce taƙara harba masa mashi dandanan yayi ƙasa da ido magana ma ya dena yiwa kowa sai dai alama da kai"

Sayid ne ya matso kusa dashi ya miƙa masa takarda tareda cewa, "saƙon Anti Aisha bata samu zuwa ba"

cikin sauri ya Karɓa ya warware ta yafara karantawa, " kasancewar Mama baza ta zo da Shahid ba yasa ta barni a gida domin kula dashi amma karka damu gobe zan zo ko ta wane hali ne, idan ban ganka ba bazan iya shan iska me daɗi ba, ina fatan dai jikinka da sauƙi ba kamar yadda nake tunani ba na shiga firgici sosai gashi an hanani ganinka"

murmushi ya saki tareda shafar kansa sai a lokacin yaji ɗan sanyi sanyi, "waye ze hanaki ganina ma idan Ba Khaalif ba??" ya jefawa kansa tambaya, wayar Mu'Allim dake kusa dashi ya ɗauka ya tura mata saƙo kamar haka, "tinda kin ɗorawa Mama laifin ba komai Allah ya kaimu goben ina fatan dai kar wani abu ya dameki ina lafiya naji sauƙi sosai koma nace komai yazo da sauƙi kar hakan yasa ki shiga damuwar da zata jawo min matsala kisa a ranki lafiyata ƙalau kuma zaki tabbatar da hakan idan kinzo gobe idan kinga na faɗa ba daidai ba to ina jiran ki hukuntani"

Murmushi ta saki da taga saƙon ta mayar masa da amsa da cewa, "duk da ban tabbata ba amma naji daɗin jin hakan ko ba komai nasan saƙo na ya iso gareka Allah ya ƙara maka lafiya"

a daren ranar da zazzaɓi ta kwana amma da gari ya waye sai tayi kamar ba ita ba saboda tana son fita kuma idan tabari Mama ta gane bata da lafiya babu yadda za ayi ta barta ta fita"

Cikin baƙar doguwar riga ta shirya ta yafa baƙin mayafi batayi kwalliya ba dan dama ba damunta tayi ba kanta a ƙasa tace, "Mama zan tafi aiki Maman Nabia tace nazo"

Ido Mama ta zuba mata tana nazartar yanayinta kafin tace, "kuma shine baki faɗa min da wuri ba??"

Ƙara yin ƙasa tayi da kai kafin tace, "Mama ai yau ta sanar dani hakan kuma yana da kyau naje dan tace akwai aiki da yawa"

Jinjina kai Mama tayi tace, "Allah ya tsare ki kula sosai fa"

Ta amsa da "amin" ta fice cikin sauri sauri, tayi babbar sa'a batayi gamo da kowa ba,
Lambar Mu'Allim ta nema dan ya sanar da ita inda zataje kai tsaye,
ya sanar da ita sun koma gida ma ya rigime musu dole aka taitayeshi akai gida dashi,
Ita hakan daɗi yayi mata dan haka ta nufi gidan nasu.

cikin sakin fuska Umma ta tare ta bayan sun gaisa ta rakata ɗakin da yake, yana kishingiɗe bakin gado Kiarat tana zaune a ƙasa ƙoƙarin lallaɓa shi take yaci abinci amma yayi banza da ita ko kallonta ma yaƙi yi bare tasa ran ze saurari abincin.

Da sallama ta shiga ɗakin kanta a ƙasa Kiyarat ta amsa cikin fara'a tace, "ga Anti ga Anti zo kisa baki ko ze ci abincin nan yanzu Yaya Jose yafi yara murɗewa wallahi yanzu baya son cin abinci"

Fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Kiyarat sannu da ƙoƙari ai kinyi ma idan da nice ni zan cinye abincin na cewa Umma yacinye tinda ba yaro bane"

Kiarat tayi dariya tareda cewa, "ai kuwa wallahi kin kawo shawara da alamu sai yasha duka ma ze dawo dai-dai"

Ido Aisha ta zaro tana cewa, "laa ila Kiarat nifa da wasa nake haba ke kam yanzu ai kamar jariri haka yake sai da rarrashi amma me yakawo zancen duka?? har kinsa ma na tsorata"

Kiarat ta kwashe da dariya tayi hanyar waje tana cewa, "Anti Aisha kece fa kika fara kawo aidiyar"

fitar da tayi ne ya bata damar ƙarasawa kusa dashi ido ta zuba masa cikin tausayawa tace, "Jose?? ya jikinka"


Tattausan murmushi ya sakar mata tareda cewa, "naji sauƙi sosai ki zauna mana"

Zaman tayi a gefensa tana ƙara binsa da ido zatayi magana yayi saurin katse ta da cewa, "ina tunanin ki sai ga ki kinzo da wuri ma ba kamar yadda nayi tunani ba yanzu Kiarat yar raini take cewa na ma dena tunanin ki ba zaki zo yanzu ba"

Ƴar dariya tayi kafin tace, "ai Kiarat akwai ta da son wasa ooh kenan? abunda ta faɗa maka ne yasa ka ƙi cin abinci??"

murmushi yayi yace, "ba ni kaɗai ne nake buƙatar abincin ba ai kema kina buƙatan dan nasan baki ci komai ba tinda kika tashi"

Cikin zaro ido tace, "kaii? ya akai ka sani"

Shiru ya ɗanyi yana kallonta sannan yace, "nasan hakan ƙaramin aiki ne gareki to yanzu bismillah zauna ki ci ko nayi miki ɗura"

Turo baki tayi gaba kafin tace, "aa gaskiya nifa dubiya nazo kuma sai na ɓuge da cin abincin mara lafiya to ba dani ba, ka zauna ka ci naka kawai"

Girgiza kai yayi yace, " nima kuwa bazanci ba"

Miƙewa tayi ta zubo masa abincin ta dawo ta zauna ta wani haɗe fuska kamar gaske a dake tace, "idan bazaka iya ci da kanka ba buɗe bakin"

"iyee?? zarra zaki min??"

Tace, "eh ai naga alamun hakan"

Murmusawa yayi gami da lumshe ido sannan yace, "tinda na ganki ma sai naji na ƙoshi"

Zare masa ido tayi tareda cewa, "wai wasa nake maka?? maza ka karɓa ka ci ko kuma na tashi nai tafiyata"

Da sauri yace, "aa zanci"

Miƙa masa tayi ya karɓa yafara ci yana ɓata rai kamar me cin magani, ba wani da yawa ya ci ba ya ajiye ya janyo ruwa ya ɗan kurɓa sannan yayi wurgi da robar.
Kallonsa tayi baki a sake ta buɗe baki zatayi magana yayi sauri ɗora hannunsa kan nata cikin wani irin salo me ɗauke wutar kai, hakan yasa ta haɗiye maganar ta ƙara warara masa ido, kallon ido cikin ido suka shiga yiwa juna har na tsawon lokaci be gaji ba sai da tafara neman nutsuwarta ta rasa sannan tayi saurin sauke kallonta ƙasa gami da lumshe ido ta sauke ƴar ajiyar zuciya"

Cikin wata sanyayyar murya yace, "Ashshah nayi miki laifi fa, ba tareda na sanar dake ba na barwa amini na soyayyarki, kinsan alfarmar da nake so kiyi min??"

Girgiza kai tayi cikin sanyin da jikinta yayi. ɗan cije leɓensa yayi saboda wani irin zugi da yaji zuciyarsa tanayi, dannewa yayi ta yadda bazata gane ba yace, "dani da ABU duk abu ɗaya ne ina so ki ninka masa son da kike masa ki haɗa da nawa hakan ne kawai ze sani farin ciki a koda yaushe, kar kiji babu daɗi ko kuma ki fahimci hakan abai-bai Abubakar ya fini buƙatar ki Ashshah yana sonki so me tsanani wannan ne karo na farko da yake son wani abu kuma yake sa ran samu ina son ganin farin cikinsa kuma kece wannan farin cikin nasa dan Allah kar kice min aa"


Tinda yafara maganar take kallonsa har ya kai ƙarshe, murmushin da takasa gane na farin ciki ne ko baƙin ciki ya suɓuce mata, tace, "nayi farin ciki kasancewar ka jajirtaccen aboki kuma na ƙwarai, naji daɗi da kayi hakan domin farin cikin abokin ka bazan taɓa so matsala ta shiga tsakanin ku saboda ni ba ka tseratar dani daga wannan tafarkin ina maka godiya Jose, amma abunda yake damuna shine aurena da Saif lokaci koda yaushe ƙara zuwa yake kasan me ya rage yanzu? be wuce sati biyu ba ina cikin matuƙar damuwa Jo amma babu yadda na iya dole na na aureshi"

Taƙarasa maganar tana kuka kashirɓan.
Duk yadda yake daurewa yana cijewa sai da hawayensa suka samu damar zubowa, ya rasa ma ta ina ze fara rarrashinta gashi kukan take da gaske sai yaji zuciyarsa tana ƙara ƙonuwa dan kuwa ya tabbatar kukan nata yana da alaƙa da abubuwa da yawa ba iya maganar ce ta kawo shi ba tausayinta yaƙara ɗarsuwa a ransa zuciyarsa taƙara yin rauni, janyo ta yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana ɗan bubbugar bayanta alamun rarrashi.

Cikin sanyi yace, "kiyi shiru Ashsha dan Allah kiyi haƙuri akan kuskuren da nayi miki bada son raina nayi hakan ba ba kuma dan bana sonki bane bazan iya so wa kaina abunda bazan iya so wa ɗan uwa na ba ni me haƙura da komai ne na barwa ABU koda hakan ze jawo silar mutuwata dan shi wani tsagi ne na rayuwata, kukan nan naki yana ƙona zuciyata sosai dan Allah ki dena"

Tana so ta dena ɗin amma takasa saboda ya riga ya gama cin ƙarfinta sai da kyar ta samu ta rage ƙarfinsa amma duk da haka bata dena ba.

share nasa hawayen yayi yana ƙoƙarin yin magana muryar Abi ta katse shi "wacece wannan kuma Jose??"

Sunkuyar da kai yayi yana ɗan murmushi a shagwaɓe yace, "Abi harna ɗanji kunya"

Abi yace, "na shigo ne da nufin ganinka amma na ganka tareda wata dole na dasa alamar tambaya amma kai komai sai ka saka shi da wasa da alama sunan kakannin ka gareni ko??"

ƴar dariya yayi yace, "Aisha ce ƴar gidan Ɗan Gaske"


Jinjina kai yayi yace, " to meye alaƙarka da ita kuma??"

Yace, "ƙanwata ce fa Abi"


zeyi magana Umma ta katse shi da cewa, "ƴar ƙanwata ce Aisha kenan bayan alaƙa ta jini ma akwai alaƙar soyayya tsakanin su"

Da mamaki Abi yace, "amma meyesa baku sanar dani ba?? da kun faɗa min ai da abun bazeyi girma haka ba ma zanje na samu Ɗan Gasken muyi magana"











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 19*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*








Umma tace, "baka nan ne shiyasa baka sani ba amma ai yanzu komai ya wuce dan ya riga ya haƙura saboda ɗan uwansa yana sonta"

Da kallo Abi ya bishi cikin mamaki da kuma tausayawa, ƙasa yayi da kai cikin dauriya yace, "Abi kasan waye Abubakar a wajen Yusuf, nayi hakan kawai dan samuwar farin cikinsa ni ɗan gata ne wanda ya taso tareda iyayensa shi kuwa ABU be san daɗin su ba ni me yin ƙoƙari ne dan samar masa da nutsuwa Abi zan ɗauki ko wace irin kasada ce akansa"

Jinjina kai Abi yayi kafin yace, "barakallah Jose Allah yayi muku albarka baki ɗaya Allah ya ɗorar da kai akan kyakkyawar zuciyar nan taka"

Umma ta amsa da "amin"

Abi yace, "kukan me takeyi ne ko laifi kayi mata??"

Girgiza kai yayi yana murmushi yace, "aa Abi kukan ne kamar wasa ta ɗauke shi ko Ashshah??"
ya faɗa yana kallonta, cigaba yayi da cewa, "Ashshah ga mahaifina ku gaisa"

Sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar da kukan da kyar ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a da sakin fuska.

Umma tace, "ka ci abincin kuwa??"

Yace, "eh Umma naci da yawa ma kuwa ta zuba min"

Murmusawa tayi tareda cewa, "bari na baku guri ko?"

Kai kawai ya gyaɗa lokacin ma tini tayi nisa a hanyar fita daga ɗakin dama Abi suna gama gaisawa ya fice.

Kallonta yayi kafin yace, "kuka fa baya maganin komai sai kawo ciwon kai bazanji daɗi ba idan hakan ta kasance"

Murmushin ƙarfin hali tayi tace, "na dena karka damu"

Miƙewa tayi tana cewa, "Jo zan tafi Allah ya ƙara lafiya"

Ya "amsa da amin yana ƙoƙarin tashi"

Mukullin mota ya bawa Mu'Allim yace ya kaita inda zataje ba musu ya karɓa yayi gaba su kuma suka jera tare har ya rakata ta shiga mota sai da suka tafi sannan ya koma cikin gida kai tsaye ɗaki ya nufa a ɗakin ma sai da ya rufe ƙofa sannan ya koma ya zauna, tafukan hannun sa duka biyun yasa ya rufe fuskarsa, nanfa damuwa tace gani nan wani irin raɗaɗi zuciyarsa takeyi wanda yakejin inama yayi kuka ko ze ji sauƙi amma kukan ya gagara ya rasa yadda zeyi yaji sanyi"

Sai yamma sannan ta koma gida bata wani daɗe da dawowa ba wayarta tafara tsuwwa tana ɗauka taga kiran Saif ɗagawa tayi gami da yin sallama.

ya amsa Cikin fara'a sai bayan sun gaisa yace, "ina kikaje ne yau??"

Tace, "aiki mana"

Yace, "ok da kyau me da me kika Ɗinka mana yau??"

a ƙagauce tace, "aikin zanin gado ne dani amma ko abu ɗaya kasa Ɗinkawa nayi saboda banajin daɗi Sosai"

yace, "kai haba to meyesa?"

Tace, "da alamun an taɓa wani sashi na rayuwata ne"

Ƴar dariya yayi kafin yace, "gaskiya ne dole kiji a jikinki wani sashi naka ai abu ne me girma, a adai-daita sahu kikaje??"

Ɗan murmusawa tayi dan kuwa tasan kwanan zancen tambaya ɗaya ce amma ya tsaya kwalo kwalo, a gatsale tace, "kasan dai na iya tuƙa mota ai"

dariya yayi yace, "ba fa cewa nayi ki gaya min magana ba, nasan baki iya ba ai amma kin biya ta wani gurin ko?"

Kafin ya gama rufe baki tace, "ƙwarai kuwa Ya Jo ɗina ne ba lafiya shine naje duba shi akwai damuwa ne??"

Yace, "oh wanda yayi haɗari ko?? Allah sarki be mutu ba?"

Tace, "tukunna kwanakin basu ƙare ba lokacin shan iska beyi ba"

Ganin kamar ta tsargu da wani abun yasa yace, "ai naga motar ta mammole ne da yawa idan mutum ya ganta ze zata na ciki baze rayuwa ba shiyasa"

Ƙwafa tayi iya cikin bakinta sannan tace, "Allah yayi dai da sauran kwanansa Allah sarki dama wani zubin yadda muka so ba haka muke samu ba ai yama ji sauƙi dangargar abunsa"

Takaici kamar ya kashe shi ganin zata ƙara ɗora masa wata jarfar yasa yayi saurin cewa sai anjima yayi maza ya kashe wayar.

Ƙwafa tayi tareda cewa, "baƙin azzalumi ai Allah ya fika"


ABU Kamar da wasa yarafara jin bacci sun gama waya kenan da Jose ya ajiyeta gefe ya kwanta, be daɗe yana baccin ba ya farka yana buɗe idonsa abun mamakin sai yaga baya ganin komai sai duhu, mutsika idon yayi sosai sannan yaƙara waro su dan ya tabbatar ya buɗe sun ko kuwa dama basu buɗu bane har yanzu dai duhun yake gani kuma ba duhun dare ba duhu na gaske tinda lokacin ma ba dare bane rana ce, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" itace kalmar da ya furta tareda dafe ƙirjinsa saboda yadda gudun zuciyarsa ya ninku, Abul'Abbas ya fara ƙwalawa kira ya shigo da sauri yana amsawa tareda cewa, "yaya gani nan waye ya taba ka"

Cikin lalube irin na makaho yafara neman inda Abul Abbas yake, ganin haka yasa Abul Abbas ya matso a fitgice yana cewa, "meke faruwa yaya??"

ABU yace, "ba komai Abul kawai na dena gani ne bana ganinka"

Wata kyakkyawar razana Abul Abbas yayi cikin tsananin firgici ya zuba masa ido a warwaje sai da yayi ƴan sakanni a haka kafin ya iya magana cikin kuka yace, "yaya Umman mu ce ko?? ta makanta ka taji daɗi yaya wallahi bazan yafe mata ba nasan ba kowa bane itace yaya"

Fashewa yayi da kuka me zafi tareda kifa kansa akan kafaɗar ɗan uwan nasa.

hannu ABU ya ɗora akansa yana hawaye cikin sigar rarrashi yace, "ba Umma bace ƙanina kar kayi saurin zarge ta ka dinga kyautata mata zato a koda yaushe"

Cikin kuka yace, "me kayi musu?? baka shiga haƙƙin kowa ba yaya me ka tare musu da zasu nakasta ka??"

cikin daurewa yace, "Abbas kowa ƙaddarar sa tana zane a tafin hannun sa da ita yake cin abinci yake shan ruwa yake komai ma duk da ita be zama lallai sai ka tarewa wani abu ba sannan Allah ze jarrabe ka karka yarda da cewar wani ne ya aika hakan gareni Allah ne ya ɗoramin ana jarabtar mumini ko dan a gwada imaninsa Abbas karka damu komai ze shuɗe kamar ba'a yi ba"

Shiru Abul Abbas yayi yana sharar ƙwalla yakasa cewa komai.

ABU yace, "bana son tayarwa Jose hankali Abul Abbas kar ka bari ya tsinkayi labarin a yanzu kabari sai nan gaba"

Gyaɗa kai kawai ya iyayi dan kuwa bakinsa ma yayi nauyin da baze iya magana ba har yanzu be yarda ba Umman su ce ta mayar masa da ɗan uwa makaho ba"


Jose duk yadda yake son yayewa kansa damuwa yakasa kullum ƙara ninkuwa take ga wani irin zafi da zuciyarsa takeyi koda yaushe a ƙuntace yake gaba ɗaya ya fita daga hayyacin sa, baze iya jurar zaman gidan su ba dan haka ya tattara ya koma gidan sa wanda shi kaɗai ne babu wanda ze dameshi dan yanzu gaba ɗaya baya sauraron kowa, Umma ce dama take ƙoƙarin sa shi magana ko tace zata tilasta masa ya ci abinci shi kuma duk wannan baya gabansa, haka ya tare shi kaɗai sai dai yayi ta ƴan make maken sa babu wanda yasan halin da yake ciki.


Khaalif ne ya shigo cikin sanyin jiki ya zauna bayan sun gaisa da Mama yake gaya mata abunda ya faru da ABU Umma ta sa salati. Aisha kuwa zumbur tayi ta miƙe tafara baya baya tana kokawa da numfashin ta gaba ɗaya hankalinta yabar jikinta lokaci ɗaya kafin su farga ta zube a wajen a sume.

Mama ta nufi kanta da gudu tana faɗin "Hasbunallahu wani imalwakil"

Khaalif kuwa mamakin suman da tayi yasa shima ya daskare yakasa motsawa sai ido da ya zuba musu jikinsa har rawa yake ba gaira ba dalili.

Mama tace, "Sayid kawo min ruwa da sauri"

Ruwan ya ɗebo ya kawo mata ta karɓa ta yayyafa mata, fizgar numfashi tayi gami da firgita lokaci ɗaya jikinta ya hau kakkarwa tafara rawar sanyi, da kyar ta iya cewa, "Mama ki kaini ɗaki dan Allah"

Mama da mamaki ya gama mamayarta da kyar ta miƙewa ta temaka mata ta kaita ɗakin, bayan ta zauna ta dafe kai ta zuba tagumi hannu bibbiyu Mama ta kalle ta cikin sanyi tace, "Aisha meke damun ki ne, Jose yayi haɗari kin ƙware ABU kuma ya makance kin sume nakasa gane alaƙar da ke tsakanin ku amma firgicin yayi yawa na daɗe ina ganin damuwa iri iri a tattare dake amma idan anyi magana sai kice ba komai to duk wannan me yake nufi"

Ba tareda ta kalle ta ba tace, "Mama zazzaɓi nakeji"

Rausayar da kai Mama tayi gami da cewa, "toh Allah ya baki lafiya ya kuma kawo ƙarshen abun, shi kuma ABU Allah ya kawo masa ɗauki"


Bata ce komai dan kuwa bata san abunda zata furta ba...










*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM]

Please Login or Register in order to submit comment