You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Bismillahir'rahmanir Rahim.
From the writer of KUNCIN ZUCI...And now


MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️

Wannan Littafin qirqirarren labari ne, banyi dan wani ko wata ba, in yazo dai dai da rayuwar ku, kumin afuwa a bisa kuskure ne. Ban kuma yi dan cin zarafin wani ko wata ba, in sabanin hakan ya gifta, shima ayi min afuwa bisa kuskure ne.


A Blurb for you...
KADDARA....Itace sanadin da yasa ta tsinci kanta acikinsu. Daga lokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci banbancin ta da ahalin da ta daukesu jininta.
"Amma menene laifinta dan kaddararta tazo a hakan?"
"Shin me tayi da yasa take fuskantar kalubale daga garesu?"
Wannan sune tunanin FADWA a kullum. Amma kuma duk hakan tana daukansu da sauqi wani lokacin in aka hada da zafin da takeji na yadda kaddara ta hado ta cikin ahali daya da SHI.

Ta aminta da cewar har abada batada babban maqiyi kamarsa. Tana jin har abada zuciyarta bazata taba sauqowa akan abunda ya mata ba.
Saidai abunda bata sani ba shine kaddarar rayuwar ta tana manne da tashi. Ya zatayi Idan ya zamo shine qarshen bangon majinginar ta a lokacin da ta rasa madafa?

Labarin Muradin zuci zai tabo wani bangare ne na sabanin fahimta da ake samu a rayuwa. Kuma zamuga shin har tsawon wane lokaci zuciya take iya danne son wanda take matuqar so? Shin soyayyar da aka rayu da ita acikin zuciya takan iya boyuwa?
Har zuwa yaushe?


Assalamualaikum Everyone, Bintu ta dawo muku da sabuwar tafiya da take muradin ayi tare daku.

Littafin Muradin zuci zaizo muku a paid book ne wannan karon. Akan 500 kadai. ku tuntubeni ta wannan line din 08134692758
Sannan zaku samu sameshi akan manhajar AREWAPEN.

Ga wa'inda mukayi tafiyar KUNCIN ZUCI babu su kuma you're welcome on board in this journey, masu neman Littafin Kuncin zuci kuma zaku iya samunsa a Arewapen ko Wattpad for FREE. ko kuma ku tuntubeni ta numbern dana rubuta a sama dan samun complete document.
Nagode.

Love, Bintu Musa.


https://www.arewapen.com/book?id=6a284ace1fd5770fa0dc53fa

Ina miqa godiyata sosai ga qunguyar mu ta Wow (women of words) Association.

Da kuma godiya ta musamman ga:

Ramlat (Mai Dambu)
Sayyid (Legends pen)
Nusaiba Rimi (Nusy Bee)

Thank you so much for been there for me when i need you, Allah ya bar zumunci.

Fatima Dahiru
Hajara Usaini

Ina matuqar godiya agareku for your support, My sisters from another mother, Allah ya saka da alkhairi da dukkan qwarin gwiwan da kuke bani a koda yaushe.








MURADIN ZUCI📖📚

Bintu Musa ✍️

Chapter 01

Free page


Houston, United States.

25th October.

Daren Talata, 9:00 pm.



Hankali a tashe matashiyar balarabiyar take tuqin motarta qirar Honda prelude, wadda ta kasance daya daga cikin motocin da suke tashe a wannan lokacin. Tafiya take ba tareda itama ta san inda ta nufa ba, idanunta na kan titi tunda ta fara tuqin taqi juyawa ta kalli seat din dake gefenta. Hannunta da suke riqe da steering wheel din ta kalla ganin yanda suke rawa sai ta sake damqe sitayarin tana mai qara gudun motan a yayin da zuciyarta ke kadawa da wani irin yanayi da yasa idonta kawo kwalla. Tafi awa daya tana yawo acikin garin kuma har sannan bata tsaida inda ta nufa ba sai zagaye take acikin wata makekiyar unguwa ta rasa a wane taqamaiman gida zata tsaya, gashi har sannan jikinta sai rawa yake, can kawai ta samu kanta da tsaida motan a gefen hanya ta kifa kanta akan sitiyarin da hannunta duka biyu ke riqe dashi har sannan. Hawaye masu zafi taji suna zuwa mata idanunta ba tareda ta sharesu ba ta dago kanta tana bin gurin da ta faka motan nata da kallo, ganinta tayi gaban wani babban gida mai cike da alatun rayuwa ga haske a ko'ina tar, samun kanta tayi da qurawa compound din gidan ido ganinsa dauke da gajeran gate irin wanda yawancin 'yan qasar suke amafani dashi a gidajensu, nan kuma idonta yakai kan shukokin compound din da take hangowa daga inda take zaune cikin motan. Sai kuma ta kai hannu ta fara share hawayen da ya sauqa a fuskanta, ahankali ta juya ta kalli seat din dake gafenta ganin har sannan babu wani motsi da basket din dake ajiye a gurin yayi, sai ta kai hannunta ahankali ta yaye farin towel din dake lullube akai tana kallon kyakkyawar jinjirar dake baccinta hankali kwance sai tashin qamshin turaren babies take mai dadi, kuka ne yazo wa matashiyar da sauri ta kai hannunta ta rufe bakinta gudin kar ta tada Babyn. Aqalla ta kai minti biyar tana kallonta sannan cike da jarumta ta maida towel din ta rufe yarinyar, da haka ta jawo baqin gyalen kanta ta rufe fuskanta sannan ta juya ta duban street din unguwar, kasancewar kebababbiyar unguwa ce ta masu hannu shuni sosai sai ya zamtoh babu kowa a daidai street din da take, ganin haka yasa ta bude motan ta fice tareda zagayawa daya bangaren domin daukan jinjirar. Ahankali ta dauko basket din ta juya tana waige waige ganin ko ana kallonta sannan ta fara tafiya a sannu ta tura qaramin gate din and to her luck kuma ba'a datse yake ba, da sauri ta nufi gefen shukokin ta duqa ta ajiye basket din hawayenta na diga kan towel din amma haka ta miqe ta fice da gudu gudu tana sake waigawa ko da wani ya ganta har ta qarasa ga motarta ta shige da wuri ta tayar. Sai da ta kai qarshen layin sannan ta faka motan ta juya tana kallon gidan ta madubi sai kuma kuka mai qarfi ya kwace mata, wani irin zafi takeji a zuciyarta kamar wuta a wannan lokacin tana kukan ahankali take ambaton sunan jinjirar. Can kuma ta kasa daurewa tayi saurin bude motan da nufin ta koma ta dauko yarinyar dan ji take duk wani jarumtar da ta fito dashi kuma ya watse, bazata iya ba...bazata iya ba.
Fitan ta ke da wuya ta hango fitowan wani magidancin mutum daga gidan tareda wasu yara guda biyu suna tafe a jere dashi zasu fita daga compound din gidan, da sauri ta sake komawa cikin motan ta tayar tareda figanta ta bar arean da gudunta.
Tasani..Lokaci ya qure mata..Ya qure mata har abada kuma..


A yayin da magidancin ya fito daga gidansa tareda yaransa maza da suka kasance 'yan biyu kuma 'yan kimanin shekaru sha biyu, hankalinsa naga fita kwata kwata bai lura da abunda aka ajiye masa a compound din gidansa ba sai daya daga cikin yaran ne ya riqe masa gefen riga domin jawo hankalinsa yace "Papa look..A basket" sai ya juya shida dayan yaron nasa suka kalli gurin da IMRAN ke nunawa da yatsansa ya sake cewa "Papa menene?" a sannu shi Papan ya fara nufan gurin cikin kaffa kaffa yaran na biye dashi a baya, kafin ya qarasa kawai dayan yaron nasa dake bayansa ya tafi kansa tsaye ya tsugunna zai bude, da sauri Papa yace "Kash. IMAM meyasa bak.." kafin ma ya qarasa maganan Imam ya bude towel din suka kalli cikin basket din a tare, Imran dake boye a bayan mahaifin nasu shima ya leqo kansa, dago kai Imam yayi yace "Papa it's a Baby" daskarewa Baban nasu yayi yana kallon kyakkyawar Babyn dake bacci hankali kwance ga kuma kayan sanyi na yara mata mai kalan ruwan hoda a jikinta dauke da zanen flowers wanda hakan ke nuni da kasancewar babyn 'ya mace, hannu Imam ya kai zai dauketa sai Papa ya janye hannun nasa still yana kallon jinjirar da kana ganinta kasan farinta ba na 'ya'yan mu hausawa bane, Imran ya duqa kusa da dan'uwansa shima yana kallon yarinyar sai ya dago kai yana murmushi yace "Papa let's keep it" shidai Papa har sannan baice komai ba gashi alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarsa sai kuma ya miqe ya fara bin arean wajen gidan nasu da kallo ko da zai hango wanda ya musu wannan ajiyar a daren nan, can kuma ya juyo yace "Ku tashi mu koma ciki akwai sanyi" sai Imran yace "Papa anan zamu bar Babyn?" Imam dai yanata kallonta har sannan bai sake cewa komai ba, sai Papa yace "No, we're taking her with us" da haka ya sunkuya ya dauki jinjirar tareda furta duk addu'an da tazo bakinsa, sai twins suka miqe suma Imam ya dauki empty basket din suka fara tafiya a gaba while mahaifin nasu yana biye dasu a baya riqe da babyn a qirjinsa suka koma cikin gidan nasu.

A lokacin da suka shiga babban falon gidan nasu suka samu Momma zaune a inda suka barta ga jakadiyarta mai suna Habiba na matsa mata kafafunta da suka kumbura dalilin tsohon cikin dake jikinta, dago kai tayi tace "Ha'a, har kun dawo?. Da mota kuka fita ne?" sai Imran ya qaraso gurin ta da saurinsa yace "Momma we found a Baby" sai ta dan hade gira ta juya tana bin mijin nata da kallo ganin yana riqe da nannadadden towel a qirjinsa, qarasowa Papa yayi tareda zama a gefenta atake kuma Habiba ta miqe kanta a duqe cikin ladabi ta matsa gefe, sai ya duqo ya bude wa Matar tasa towel din tana ganin yarinyar kamar idanunta zasu fado, sai ta dago kai tana kallonsa tace "Menene wannan din?" yana kallonta shima yace "Jinjirace Fatima, anan cikin compound dinmu aka ajiyeta" sai ta dafa cikinta ta fara qoqarin miqewa yana kallonta, da sauri Habiba ta matso zata taimaka mata amma ta daga mata hannu da nufin ta barta sannan ta qarasa miqewan da kyar duk suna kallonta ta kalli Imam dake riqe da basket din har sannan, fuska a hade tace "Bani abun nan" sai ya matso ahankali ya bata ta karba tana kallon mijin nata tace "Kawo ta mu fitar da ita daga gidan nan tun kafin ta jawo mana masifa muna zaman zaman mu" da mamaki Papa yake kallonta yace "Meye haka kike cewa ne Fatima, clearly dai kina gani jinjirace alamun bata sha iskan duniya sosai ba, meye nata kuma?" Momma tayi qanqan da ido tace "Shiyasa zamu mayar da ita inda muka ganta sannan mu kira police da social services, we are not keeping a stranger's Baby in this house wallahi" da mamaki Papa yace "Haba Fatima, ki nutsu da Allah. Ta yaya zamu maida baiwar Allahn nan out there in this cold weather kawai dan kina tsoron abunda hukuma zasuyi, kin manta akwai CCTV a street din ne? Anan zasu gani su kuma shaida ajiye mana ita akayi ai" a fusace tace "Ni ba hukuma nake gudu ba, qananun maganan da hakan zai jawo mana acan gida nake gudu, ya muna zaune qalau zaka jawo mana masifa har cikin gida" sai ya dan girgiza kai ya miqe tareda miqa mata yarinyar yace "Dan Allah ki riqeta, ki kula da ita kafin insan ta inda zan bullowa al'amarin, the mother might come back, bakisan yanda nake burin hakan a raina ba, it's too cruel for the baby, social services will just be passing her from one home to another in the name of adoption, she's innocent" tsayawa Momma tayi tana kallon yarinyar yayin da duk wani annurin fuskanta ya gushe, idonsa a kanta ya sake miqo hannunsa "Riqeta mana Fatima" sai lokacin Imam ya matso tareda dan miqa hannu zai karbeta ai da sauri Momma ta tureshi har sai da ya fadi, rai a bace take kallonsa tace "Uban 'yan karfin zuciya, inna gaura ma mari ba" kafin Papa ya dagosa ya riga ya miqe yana kallon mahaifiyar tasa dake harararsa, sai Papan ya juyo gareta yace "Wai me yake damunki ne Fatima, Lafiyan ki kuwa?" tace "Ba lafiya nake ba, ta yaya muna zaune lafiya zaka shigomin gida da jinjira sabon haihuwa har kana fadin in riqeta, wallahi ka koma da ita duk inda ka daukota tun wuri" da haka ta juya tana riqe da cikinta da yayi nauyi sosai ta wuce dakinta dake nan downstairs wanda tun zuwansu gidan take zama acikinsa dalilin bata iya hawa stairs taje asalin dakinta dake can sama, sai duk suka bita da kallo yayin da Habiba tabi bayanta da hanzari gudun kar ta mata masifan da ta saba.



Wannan littafin Paid ne akan Naira dari biyar (500), masu buqatan kasancewa cikin wannan tafiyan zasu iya biya ta wannan layin.

8134692758 Opay
Fatima Musa Maina

Shaidar biyar ta wannan layin. 08134692758



MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️


Chapter 02
Free page.


Papa daskarewa yayi anan tsaye a falon ya gagara zama yana bin matar tasa da kallo, ya sani wannan din ba sabon abu bane sanin masifa da fitinar matar tasa da yake fama dashi tun fil azal wanda kowa ya shaida a kaf danginsa cewa Fatiman fitinanniya ce kuma in bataso zaman lafiya ba toh ba wanda zai zauna lafiya a can gidansu dake Nigeria. Sai ya koma ya zauna kan kujerar a hankali ya duqar da kansa yana kallon Babyn wadda kamar hadin baki itama ta bude idanunta a hankali, dan stiff yayi yana kallon kwayar idanunta da suka kasance grey color, duk da kasancewar ta jinjira hakan bai hana manyan idanunta fitowa fili ba a lokacin da take kallonsa. Duk yanda yake jin nauyin tashin hankalin dake tunkarosa hakan bai hanasa samun kansa da yi mata murmushi ba, sai ya kwantar da murya ahankali yace mata "Assalamualaiki" nan twins suka matso suna kallonta, Imran yace "Papa please let's keep it" sai ya dago kai yace "She's a girl Imran". Imam kuwa sai kallonta yake baice komai ba shima, sai Papa ya sake duqawa ya kalleta yanajin tausayinta na shiga kowane sashi na zuciyarsa, tayaya wannan innocent being din zata zamo masifa bayan in za'a bata zabi itama bazata so abunda ya faru da ita ba ko kadan, har sannan bata dauke idanunta daga kan Papan ba sai can kuma ta fara motsi tana dan bata fuska alamun zatayi kuka nan ya hau jijjigata yana kallon kayan sanyin dake jikinta, mamakinsa daya a wannan lokacin shine ta yanda kayan jikin jinjirar yake fes da kyau ga wani tashin qamshi da takeyi, sai ya dan dago ta yana sake duba kayan dan ko daga texture din mutum zai fahimci ba daga cikin wahala ta fito ba. Idonsa ne yakai kan wani rubutu ajikin farin towel din nata sai ya kai hannu ya yaye kadan yana ganin sunan da akayi engraving kamar saqa ajiki da harafin larabci "FADWA" ya maimaita sunan a fili, sai lokacin Imam yace "Papa sunanta ne?" ya gyada kai "Sunanta Fadwa" Imran yayi murmushi ya duqa kansa gareta yace "Hi Fadwa" sai Papa ya shafa kansa bai bar murmushin qarfin halin ba, yace "Yes.. Her name is Fadwa" ya qarasa fadi yana danne duk wani tashin hankalin da ke kokarin taso masa a zuciya.

Rai a bace Momma ta shiga dakinta Habiba na biye a bayanta, cikin kwantar da hankali tace "Ranki shi dade kiyi hakuri kar hakan ya ja miki matsala ga lafiyarki" ta juyo a fusace tace "Sai an fitar da yarinyar nan daga gidan nan, ke yanzu yarinyar nan bata miki kama da aljana ba?" Habiba ta dan duqar da kanta tace "Ki gafarceni ranki shi dade, amma yarinyar ba lallai ta kasance aljana ba sai dai asalinta ne zai iya zama da tangarda" Momma tayi saurin cewa "Dama batun shegiya kam shegiya ce, kuma wallahi ba zan raini 'yar cikin shege tareda 'ya'yana ba" kafin Habiba tayi magana suka jiyo tashin kukan yarinyar Momman 'yar kimanin shekara biyar dake kwance akan gadon tana bacci, sai Momman ta juya gareta da sauri tace "Jidda na kin tashi" yarinyar ta gyada kai tana murza idanunta sai uwar ta miqa mata hannu da nufin ta iso gareta. Tana shafa bayan Jiddan ta juya zata fadi magana a Habiban aka turo kofan dakin Imran ya shigo a daddare, qin qarasowa yayi cikin dakin yayi sai ya tsaya anan bakin kofar yace "Mama Habiba kije Papa na kiranki" da sauri tace da Momma "Ranki shi dade bari naje" gyada kai kawai Momma tayi batace komai ba tana kallon Imran din dake tsaye a bakin kofan yaqi shigowa, dan hararansa tayi sannan tace "Meye na tsayawa a bakin kofan toh?" sai yayi murmushi ya juya while Habiba na biye dashi suke fice tana kallonsu, sai can kuma tayi tsuka ta cigaba da shafa bayan Jidda dake shirin komawa wani baccin.
Fitan Habiba falon ta samu Papa na tsaye yana jijjiga Fadwa dake kuka a hannunsa, cikin ladabi ta duqar da kanta tace "Ranka shi dade akwai abunda kake buqata ayi ne?" sai ya juyo yace "Kuka take bansan me takeso ba ko zaki gwada lallabata" nan ta miqa hannu ya bata ita ta cigaba da lallabatan, amma har zuwa karfe goma na dare Fadwa bata bar kukan ba duk da ruwan dumin da Habiba ta bata tasha, har zuwa sannan kuma Momma bata sake fitowa daga dakinta ba duk da kukan jinjirar da take jiyowa ya karade gidan. Hankalin Papa in yayi dubu ya tashi a wannan lokacin ya rasa me ke masa dadi. Sai bayan Habiba ta danyi dabarunta ta gano ciwon ciki ne ke damunta sannan ta fada masa, aikuwa nan da nan ya dauki car key twins na biye dashi zasu fice siyo mata maganin sai Habiba ta sake tuna masa yarinyar na buqatan madara da kayan sakawa har dasu pampers ya gyada kai tareda ficewan. A daren Papa suka fita zuwa super market don nemo madaran nata, yana tafe a motan yana tunani har sai da Imam dake seat din gefensa ya ankarar da shi isowarsu gurin ganin zasu wuce sannan ya dakata, daga nan kuma suka biya boutique na saida kayan yara amma kuma sai suka samu a kulle, haka ya hakura ya biya dasu pharmacy ya siyo maganin ciwon ciki na daidai jinjiri sabon haihuwa sannan suka koma gida.
Bayan Habiba ta bata maganin cikin sa'a suka samu ta fara bacci sannan Papa ya sake dubasu kasancewan suna cikin daya daga cikin dakunan dake nan downstairs, ganin Fadwan tayi bacci yasa shi ficewa sannan ya nufi dakin matarsa, anutse ya bude kofan sai ya sameta a zaune a bakin gado sanye cikin kayan bacci tana dan dafa cikin ta dake dan mata ciwo kadan, da sauri ya qarasa yana mata sannu amma bata ko dago kanta ba sai ya zauna kusa da ita ya sake cewa "Sannu, ko in taimaka miki ki kwanta?" nan ma ta girgiza kai bata ce komai, shiru sukayi sai can yayi qasa da murya yace "Fatima, yarinyar nan itama batada zabi akan abunda ya faru da ita" sai sannan ta dago kai tana kallonsa tace "Ni bance laifinta bane daman, kawai bazan riqe yarinyar da bansan asalinta bane, ya kawai daga ganin yarinya a yashe zaka dauko ka qaqabamin nima inaji da kaina" sai yayi murmushi tareda kamo hannunta yace "Haba mana Binta na, ai ba lallai sai ke zaki raine ta ba, ga hadimanki dayawa da duk abunda kikace shi zasuyi, Ina laifi in kin taimaki yarinyar da batada gata ayanzu sai na Allah da namu, ki tuna fa muma ba dabarar mu bane ya bar mana namu 'ya'yan cikin gata kuma a gaban mu" sai ta kwace hannunta tana hade fuska tace "Ni ka daina dangantamin yarana da irin wannan maganganun, kuma ai ba mu kadai bane mutanen da zamu iya riqeta, akwai orphanages dayawa ai" Papa na kallonta yace "Then..Menene makomar yarinyar kenan? what if.." kafin ya qarasa ta fara qoqarin gyara kwanciya tace "Ni kawai banaso, nace banaso ana dole ne? naji yau ta kwana a gidan amma zuwa gobe bazan lamunci zamanta a gidan nan ba" da haka ta kwanta ta juya masa baya yana kallonta, can ya sauqe numfashi ya miqe ya fice. Dakin twins ya tafi a upstairs dan tabbatar da ko sunyi bacci sai ya samu Imran nata munsharin bacci abunsa while Imam na zane a takarda anan zaune kan upper bunk dinsa dake saman na Imran din, murmushi Papa yayi yace "Imam bazaka bar zanen nan haka ba kayi bacci?" sai ya dago kansa, ahankali yace "Saura kadan" yace "No son, it's late..ka kwanta haka nan sai gobe ka qarasa" da haka ya qaraso bakin gadon ya fara tattare masa takardun, sai ya dago takarda guda daya yana gani a zuciyarsa yana mamakin baiwar yaron a kullum in yaga abubuwan da yake zanawa kala kala. Sai da ya tabbatar ya kwanta sannan ya nufi switch din dakin zai kashe wutan yaji Imam din yace "Papa, cikin ya daina mata ciwon?" sai ya juyo yace "You mean Fadwa?" ya gyada kai ahankali, sai Papa yayi murmushi yace "Eh ya daina har tayi bacci, now sleep....saida safe" da haka ya kashe wutan sannan ya fice tareda rufo musu kofan..
Tunda ya koma dakin kwanansu Momma bata juyo ta kallesa ba duk da idonta biyu har sannan, har ya gama shirin baccinsa yazo ya zauna a gefen gadon bata motsa ba kuma idanunta a bude tana kallon wall din dakin ta bashi baya, sai ya juyo yana kallonta yace "Kinyi bacci?" shiru tayi bata amsa ba, qasa qasa ya sake cewa "Ya cikin naki?" nan ma tayi shiru, ganin halin nata ne ya motsa yasashi kwanciya shima ya juya bayansa yana jin zafin hali irin na matar aurensa.

Bintu ✍️

Paid Book (500)
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758


MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️



Chapter 03

Free page..

Washegari tun da lokacin sallahn asuba yayi Papa ya kwankwasa dakin su Habiban dan jin lafiyan yanda suka kwana. Bayan ta bude sai ta sunkuya ta fara gaisheshi cikin ladabi sannan ta fito daga dakin domin bashi guri, da ya amsa mata sai ya shiga cikin dakin direct ya nufi gadon inda Babyn ke kwance tareda Jidda, bacci ya samu tanayi kamar ba ita ta tada musu hankali jiya da kuka ba, sai ya maida towel din ya rufe tareda gyarawa Jidda duvet dinda take lullube itama sannan ya juya ya fice daga dakin. A falon ya tadda Habiban tana jiran fitowansa sai yace "Ya cikin nata?" kai a duqe tace "Da sauki, bata sake wani kukan ba ranka shi dade" ya gyada kai sannan ya nufi upstairs gurin 'yan samarin yaran nasu. Tare da twins din yayi sallah anan falon suna biye dashi ya jagoranci sallahn dalilin rashin yawaitan masallatai a kasar a wannan shekarun. Har Habiba ta gama hada breakfast Momma bata fito ba, da Papan ya leqata ya mata magana ma bata kulasa ba sai ya dawo dinning area din suka cigaba da cin abincin da yaransa wanda suma a daddare suka gaisa da mahaifiyar tasu a wannan safiyar.

Habiba dai ita take tsaka mai wuya, fushin Momma uwargijiyar tata take tsoro matuqa gashi tasan ko giyar wake tasha bazata tsallake maganar Papa ba. To wa ya isa ya tsallake magana ko umarnin Yarima mai jiran gado bayan sarki Abdulfatah, sahun giwa ne ya taka na raqumi shiyasa babu yanda ta iya ta amshi kulawan jinjirar ta hada da aikinta na kula da uwargijiyar ta da tazo yi takanas a qasar.

Da Papa ya shirya fita gurin aiki ne Habiban ta sake tuna masa batun tufafin Babyn sannan ya sake shiga dakin dan dubota, nan ma ya samu ta koma wani baccin bayan Habiba ta bata madaran tasha kadan. Duqawa yayi idonsa akanta zuciyarsa na qara karyewa, sai ya kai hannu ya kama qananun fingers dinta duk bata motsa ba, wani irin nauyi yaji zuciyarsa nayi akanta, what a cruel world! This beautiful innocent child didn't deserve this, wane mara imanin ne zai yasar da wannan yarinya?.. Da wannan maganganun zucin ya miqe cikin sanyin jiki sai twins suka shigo dakin Imran na gaba suka qaraso bakin gadon suna kallonta. Sai Imran ya hau gadon ya kai hannu yana taba fuskanta yace "Papa bacci take har yanzu?" ya gyada kai yanajin nauyin yin maganan kar suga gazawarsa, sai ya juya yana kallon Imam ganin ya tsaya dan nesa da gadon idonsa quri akan babyn baice komai ba, dan murmushi Papan yayi sannan yace "Daga nan zaka gaisa da ita kuma Imam?" sai ya girgiza kai ya qaraso bakin gadon amma bai hau ba, cikin nutsuwarsa da ta zame masa jiki dukda yarintarsa yace "Papa ya cikin nata?" sai Papan ya amsa da "Ta samu sauqin, gashi har baccin ta takeyi ma" ya gyada kai bai sake cewa komai ba sai Imran dinne yake wasa da hannunta suna magana da

Please Login or Register in order to submit comment