You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaji haka a gidanmu ba kuma baza'a fara daga kaina ba kina jina?" "Yarinya kuma gatacan na kawota gidan nan a matsayin 'yata halak malak sai inga abunda zakiyi. Ta zama 'yata da tayi taking sunana a bayan sunanta na matsayin ubanta sai in gani ko ni da ke waye yafi wani sanin abunda ya dace" da haka ya juya tareda ficewa a zafafe ya barta nan zaune bakin gadon a daskare.

Yana kaiwa tsakiyar falon yaji ta jawo hannun rigar sa da qarfi tana huci, ya juyo yana kallonta shima ransa na quna, cikin qwayar idanunsa take kallo tace "Wallahi bazan riqeta ba Abdulaziz, saidai ka zaba koni ko ita, kuma ayau ba gobe ba nakeson komawa gida na fasa haihuwa a qasar nan, ka maidani gida... ko zan haihu a jirgi yau bazan kwana a gidan nan yarinyar nan tana cikinsa ba" ta qarasa maganar qirjinta na hawa da sauqa. Shi mamakin qarfin halin ta ma yake matuqa, ace tana mace amma zuciyarta kamar ta mutanen fari wannan wace irin mace ce ita. A hankali ya zare hannunsa daga riqon da ta masa yace "Ba inda zakije daga gidan nan har sai kin haihu" sai kawai gani yayi ta nufi dakin da Fadwan ke kwance da hanzarinta kamar ba tsohon ciki ne a jikinta ba, ta tura kofar da qarfi tareda shigewa yabi bayanta da saurinsa, Imam ta samu a kusada Fadwan yana rainon ta kafin Habiban ta gama hado madaranta acan kitchen
A zafafe ta qarasa bakin gadon Papan yana qoqarin riqota amma kafin ta duqa ga Fadwan Imam yayi saurin yi mata rumfa akanta da nufin kareta, cikin bacin rai ta hau dukan bayansa Papa na riqeta tana fadin "Wallahi sai an fitar da ita daga gidan nan" bai tsaya sauraronta ba ya matsar da Imam din tareda daukan Fadwan zai fice daga dakin, sai kawai Momman ta fashe da kuka me qarfi tana fadin "Ni ka maidani gidanmu ni da abunda ke cikina tunda ka samu wadda ta fimu a wajenka" bai kulata ba ya fice daga dakin Imam yayi saurin bin bayansa suka nufi upstairs. Dakin boys din ya kaita ya ajiye ta a upper bunk din Imam dan Imran yayi bacci akan nasa, sannan ya juya ga Imam din yace "Ka kula da ita karta fado" ya gyada kai tareda hawa gadon, da haka Papan ya sake ficewa amma kuma sauqansa downstairs din sai bai samu matar tasa a dakin daya barta ba, ya juya zuwa dakinta tareda murda handle din amma yaji a kulle kuma yana jiyo kukanta acikin dakin. Habiba ce ta fito daga kitchen din jiki a sanyaye dan ta jiyo komai sai ya kalleta yace "Kije dakinsu Imam tana can, in kin bata sai ku dawo dakin naku" ahankali ta amsa da Toh sannan ta wuce saman ba kuzari. Har dare Momma taki bude dakinta ga Jidda ma ta tashi daga bacci tana kuka duk Papan na jiyosu amma ba yanda beyi da ita ta bude kofan ba taqi. Habiba ma tayi iya kwankwasawanta amma Momma tayi biris dasu, ganin har karfe takwas na dare bata bude ba yasa Papa dauko landline phone dinsu na gidan dan kiran mutum daya da yasan zata iya tankwara masa ita, duk da yasan tsakiyar dare ne acan gida Nigeria amma haka ya danna kira ga layin da yasan zai samu yayar matar tasa mai suna Aina'u. A bugu na biyu mijinta ya amsa kiran cikin muryarsa dake cike da bacci sai Papan ya bashi hakurin tashinsa da yayi, yace "Ba damuwa Yarima ai kafi haka, mai dakin ta samu sauqa kenan" anutse Papa yace "Har yanzu da sauran lokaci, na kiraka bisa wani uzurin ne daban" sai yace "Ina jinka Yarima" nan Papa ya fara masa bayani a nutse duk da yanda kira yake matuqar tsada a wannan lokacin bai dameshi ba, burinsa daya a wannan lokacin shine yanda zai seta barakar da ta fara kunnowa a gidansa. Sun dauki lokaci me tsaho suna magana wanda iya adadin kudin da suka bata a wannan kiran in aka baiwa wani faqirin zai iya fitar dashi daga talauci na har abada, amma Papa baibi ta kan wannan batun ba har saida ya tabbatar ya isar da duk maganganun da suke bakinsa ga Alhaji Saminu mijin Anty Aina'u, a inda daga qarshe shima ya miqa wayan ga Aina'un ta cigaba da magana dashi Papan.
Jim kadan da gama wayan nasu aka sake kira sai be dauka ba ya tafi daidai kofar dakin Momma yace "Fatima ki bude kofan nan ga Maman Kasim akan waya zakiyi magana da ita" shiru tayi daga farko bata kulasa ba har saida telephone din ta sake yin wani qaran alamun kira sannan ta murda key din kofan tareda miqo hannunta ya dora mata a tafin hannunta sannan ta maida kofan ta rufe.
Momma bata dauki kiran ba sai da ta sake zama a bakin gado, aikuwa tana dauka ta fara cin karo da maganan Anti Aina'u a zafafe "Meye hakan kuma kikeyi kamar wata qaramar yarinya Binta?" tana shirin yin wani hawayen tace "Amma kinsan dai bai kyautamin bako?" Aina'u tace "To dan bai kyauta miki ba shine zaki bi lamarin ta kulle kanki a daki, da kikaje kan yarinyar dukanta zakiyi ko me?" "Kefa bakida hankali wani lokacin wallahi, ai ta nanata miki magana amma yana bi ta bayan kunnenki, banda ma Yarima yana matuqar sonki ai da baku kawo iyar haka ba da wannan banzan halin naki, toh wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki in ba so kike in kira Mama ba a goben nan, ke har Mai Martaba zan kira yasan abunda kikeyi tunda ke baki isa a miki magana kiji ba, ki na abu kamar bakya tuna inda kika fito, meyasa ke kullum sai anyi ta miki bita akan sha'anin zaman duniya ne wai?" nan kuma Momma ta fashe da kukan cin rai, jin wai har iyayenta za'a kira akan abunda aka mata dole tun fari, jin ta kasa magana yasa Aina'un cewa "Ki nutsu ki san me kike yi Binta, dan mijinki ya nemi taimakon marainiyar Allah ba hakan yana nufin ya shiga hakkinki bane, a yanda kika tara hadimai suna miki duk wani bauta ai kula da yarinyar nan bazai zamo abun damuwanki ba. Mijinki babban mutum ne dole ko bai riqe na waje ba zai riqe wasu na cikin gida ma, kuma nasha fada miki ba haka ake zaman duniya ba, da salo ake tafiyar da abubuwa irin haka. Koda bakya sonta ai bazaki nuna masa ba" ta dan dakata da maganan tareda sauqe numfashi sannan ta cigaba "Kin taso gidan mulki gaba da baya amma har yau bakida wayon yin dabarun iya zaman duniya" sai sannan Momman ta share hawayenta tace "Toh Adda me kikeson inyi ?" tace "Ki ajiye komai ki riqe mijinki, wannan yarinyar bata kai ta saka muku matsala a tsakaninku ba sai dai in ke kikaso, kuma wani batun kinason dawowa gida bai taso ba. You will born that child in good condition and come back home safe kina jina?" ahankali tace "Naji" da haka Aina'un tace "Sai gobe da azahar zan kira kafin nan garinku ya waye, banason inji wani batu sabanin wanda muka zanta dake yanzu kinji" ta gyada kai tareda fadin "Toh, saida safe" tace "Amin, kici abinci kuma ki bude kofan yanzu" nan ma ta amsa da Toh sannan sukayi sallama.

Paid book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay

Shaidar biya: 8134692758



MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa


Chapter 06


Free page

Ta bude kofan amma sanin hali irin nata yasa ko shi Papan baya shiga sabgarta in ba dole ba duk da kuwa suna kwana kuma su tashi a daki daya. Every morning in sun tashi zai tambayi yanayin jikinta koda bazata amsa ba wani lokacin, sannan kuma yana lura da duk motsinta dalilin haihuwanta na nan tafe ko yau ko gobe. Wani zubin ma in yaga tana takawa da kyar shida kansa zai riqe ta ya tallafa mata wajen zuwa toilet da sauransu amma har sannan bata kulasa sosai. Ga yaranta ma hakan take saboda sun san halin mahaifiyar tasu a duk lokacin da take cikin irin wannan halin sai suke kaffa kaffa da ita. Banda Jidda da take zama a gurinta su twins zuwa suke gaisheta sannan su koma dakinsu, barin ma Imam da daman maganar bakinsa aiki ta zame masa. A tarin lokuta suma kansu iyayen suna mamakin hali irin na yaron nasu da ya kasance mai nutsuwar da ta kere sa'anninsa, wani irin haiba da nutsuwa Allah ya saka masa mai ban mamaki. Abun qarin burgewa game da lamarinsa shine yanda he's always attentive akan komai. Duk abunda yakeyi indai za'a yi masa magana nan zai maida dukkan hankalinsa yana sauraro kamar wani babba, dadin qarawa ta yanda ya dauki lamarin Fadwa da girma shi ya qara baiwa Papa mamaki game dashi, yayin da gadon sa ya zamo gurin baccin Fadwa a tarin lokuta, ko da Habiba ta tafi yin hidimar Momma shi yakan zamo mai kulawa da Fadwan har ta gama abunda take wanda bazaka taba ganin Imran yana yin hakan ba saboda yanda ya daukaki bacci da muhimmanci a rayuwar sa fiye da komai. A wannan lokutan da Fadwa take yawan yin bacci akan gadon Imam din haka zai tisata a gaba yana zanata a white sheets dinsa kuma ba wanda yake nunawa ko da wasa sai Imran kadai da ya sani kuma bai maida hankali akai ba dalilin sabon da yayi da ire iren zanen da Imam din keyi, dan harshi ma yana zanashi. in kuma Fadwa ta tashi Imam dinne zai kaita gurin Habiba ta bata duk kulawan da take buqata amma kuma yanayin hakan duk bada sanin mahaifiyar tashi ba.
Dan wani irin zaman daki Momma ta koma yi kamar wadda ake kora daga gidanta, bata dai yin wannan mugun fushin amma kuma duk wani fara'anta da ake gani a gidan ta dauke daga fuskarta, kuma duk da hakan Papa bai fasa siyo mata duk abunda yasan tanason din ba, bai fasa kulawa da lamuranta ba, bai fasa zama da yaransa suyi hira ba, bai fasa cin abinci tare da iyalinsa ba, bai kuma fasa kula da Fadwa ba dan itama ya dauketa kamar 'yar cikinsa da kulawanta solely yake qarqashinsa yanzu. Duk wani abunda yasan Baby na buqata yana siyo mata shi harda maji gaba sannan bai fasa rainonta ba, akasarin lokuta Idan ya dawo daga gurin aiki zai dauketa a hannunsa su zauna anan falon suyita hira shida yaran nasa suna kallon wild life a TV, dan Papa mutum ne mai son kallon abunda ya shafi rayuwar dabbobin jeji sosai.
Hakan da sukeyi shima sai ya zamto abunda yake qara tunzura Momma ganin 'ya'yan nata mazan ma basu damu da zuwa gurinta suyi hira ba wanda kuma itace sanadin hakan, mace ce da Idan tana cikin yanayi na bacin rai ko nukra sai ya shafi har 'ya'yan cikinta, abu kadan ta kai bugu, abu kadan tayi hantara ko zagi wanda duk yana daga cikin abunda yasa 'ya'yan nata suke janye jikinsu daga gareta in tana cikin wannan halin...They know better than to go near her.
Bata sake zuwa inda Fadwa take ba tun incident dinda ya farun, ta danne komai aranta tana rayuwarta batareda ta waiwayi inda jinjirar take ba ko sau daya. Bata kuma damu tasan halin da mijin nata suke ciki akan kula da yarinyar ba wanda hakan ke qara ba Papa mamaki akan miskilancinta, amma sai ya danne komai arai shima ya cigaba da sauqe nauyin yarinyar da ya rataya a wuyansa batareda yabi ta kan matar tasa ba.

Bayan sati biyu a wani yammaci Papa ya dawo gidan daga gurin aiki, a gajiye ya shigo falon sai ya samu Momman da yaran nasu duka a falo suna zaune ranan, Habiba na zaune a qasan Momma dake zaune akan kujera tana yanke mata farcen kafafunta, bayan Jidda ta taro shi da murnan ta sai suka qarasa ciki ya zauna a kujeran dake facing din matar tasa, twin suka masa sannu Habiba ma tana qoqarin miqewa tace "Barka da dawowa ranka shi dade" ya amsa da Yauwa sannan ya kalli Momman yace "How are you feeling?" cikin qanqanuwar murya ta amsa "Lafiya" sai ya sake kallon su Imran dake zaune a gefenta yana cin popcorn while Imam na riqe da nashi a hannu, yace dasu "Yau baku dauko qanwar taku ba ne?" dan tun da ya shigo ya lura da dukansu ne zaune a falon banda Fadwa, Imam baice komai ba amma dai Papan ya lura ba cin popcorn din yake ba yana zaune agurin ne kawai, kallon Habiba yayi data kawo masa drinks da bottle water yace "Yau tayi baccin yamma ne?" tace "Yanzu zan qara dubota ranka shi dade" Imran yayi saurin cewa "Batayi bacci ba Papa" sai kuma ya kalli Maman tasu da har sannan bata dago kanta daga gyaran farcen hannunta da takeyi ba, kallonta Papan ya tsaya yi yana ayyanawa aransa yau ma ta hana a kula da yarinyar kenan, sai ya dan girgiza kai tareda miqewa ya nufi dakin da Fadwan take Imam ya bisa da kallo. Bai dade ba ya fito falon hannunsa riqe da Fadwan sannan Habiba na biye dashi a baya cike da sanyin jiki, sai da ya iso gurin Momman ya juya yana kallon yaran nasa yace "Go upstairs" suka miqe Imam ya kama hannun Jidda suka nufi saman, saida ya jira suka shiga dakinsu sannan ya sake kallon Matar tasa da taqi kallonsa, a nutse ya budi baki yace "Fatima, kinsan Allah zai iya miki hisabi da wannan yarinyar?" ta dago kai tana hade fuska tace "Wane irin hisabi? Menene hadina da ita? Ko ka taba ganina a kusa da ita balle wani abun ya hadoni da ita?" bai bar kallonta ba yace "Why are you so cruel ne nikam? She's just a baby, a few weeks baby. Me ta sani a duniyar nan da har zaki rinqa mata irin wannan hukuncin?" rai abace Momma tace "Wai me na mata dan Allah?" Yace "Kin fini sanin me kikayi Fatima, yanzu ki duba fa kiganta, kashi ne a jikinta tun na safe yana wari, sannan ko madaranta baki bari an bata ba, bata samu na mahaifiyarta ba sannan wannan din ma sai an mata katanga dashi?" ya qasara maganar zuciyarsa na karyewa yana qara riqe Fadwan a jikinsa wadda har sannan idonta biyu kuma batayi kuka ba, sai Momman ta fara kokarin miqewa tace "Yaushe na hana a bata madaran?" ta kalli Habiba dake bayansa "Ni na hanaki bata madaranta?" Habiba ta girgiza kai da sauri tana qara sunkuyar da kanta, sai Papan ya sauqe numfashi yace "Fatima, duk wani fushinki da zakiyi ya qare a iya kaina, in kina qaunar Allah da manzonsa ki daina uzzzurawa yarinyar nan, babu ita acikin lamarin nan dan bata zabi hakan ba itama, in laifi ne naji. Ni na miki laifi amma ki cire ta aciki" sai lokacin Momma tayi wani qaramin murmushi tace "Au kasan kamin laifi kenan?" cikin gajiyawa yace "Face me, but don't drag this innocent child into this please" tace "Ka maida ita inda ka daukota, na fada kuma zan qara fada bazan riqeta ba Abdulaziz. Tun ba'a je ko Ina ba ni da yarana ka fara nuna mana banbanci akanta. Tun ba'a je ko Ina ba ka fara fifita ta akanmu" Papa baisan lokacin da ya zauna a kujeran gurin ba yana kallonta, ta cigaba da kallonsa tana fadin "Bazan lamunci ganin bare tana zama abun fifiko a zuciyarka fiye da jininka ba" ba shi kadai ba har Habiba ta girgiza da furucin bakin Momma, amma kafin ya amsa mata ta juya da saurinta ta nufi dakinta tare da bude kofan da karfi sannan ta shiga ta banko kofar duk suna kallonta shida Habiba dake tsaye a gefe har sannan. Sauqe nauyayyen numfashi yayi sannan ya miqa Fadwan ga Habiba yace "Ki mata wankan, amma ki fara bata madaran nata tukunna" ta qaraso ta karbi yarinyar itama zuciyarta na karyewa ganin yanda Fadwan ta fara koyan hakuri ala dole, sai taji ya sake cewa "Please ki rinqa iya kokarinki na ganin kin bata duk abunda take buqata, kuma ki rinqa fahimtar da uwar dakin taki akan gaskiya ko da a fakaice ne, yarinyar nan itada maraya banbancinsu kadan ne. Kema zaki iya fuskantar naki hukuncin a gurin Allah in har kika tauye mata hakkin kulawanta da na rataya miki" a sanyaye tace "Ka gafarceni ranka shi dade, da yardar Allah zan gyara" ya gyada kai kawai tareda daukan ruwan dake kan table din ya fara sha, da haka kuma ya miqe ya nufi dakinsa da ke upstairs dan yanda mai dakin tasa ta banko kofarta yasan ta datse harda makulli kuma.
Amma ga mamakinsa da dare bayan ya gama putting yaran nasu to bed ya dawo dakin nata sai yaji a bude ta cire makullin, kan gado ya hangota ta kwanta as usual ta juya masa baya tana kallon ginin dakin, sai da ya kwanta tareda jan duvet ya juya bayansa shima sannan yaji muryanta qasa qasa tace "Ladan ne ya baka shawaran daukanta?" ya juyo amma bai amsa ba, sai ta miqe zaune itama ta juyo tana kallonsa ta sake cewa "Ladan ne ya saka ka daukota ko?" yace "Meyesa Ladan zai sani yin abu kamar wanda yayi owning dina?" tace "In bashi ba nasan ba ta yanda za'ayi nace maka banason abu kuma kaje ga abun nan, bamu taba haka da kai ba Baban jidda, meyasa zamu fara yanzu?" nan ya miqe zaune shima yace "Tun farkon ganina da yarinyar nan naji tausayinta kuma naji Inason kulawa da ita, da kika nuna bakyaso sai na fara tunanin in bada itan tunda baki aminta da mu riqetan ba, amma sai kikayi defying maganata Fatima. Kika nunamin kinada ikon kiyi abu a karin kanki bada izinina ba" tana share hawaye tace "Wallahi zuciyata bata aminta da yarinyar bane, yara irinsu akasari zakaga ba ta hanya me kyau aka samesu ba, d'an bature ba abun riqewa bane" sai yayi saurin cewa "D'a na kowa ne sannan Fadwa ba baturiya bace, abayyane yake tana da hadin jini da balaraben mutum, ko yau kika fara ganin jinjirin bature ne? And again D'a na kowa ne Fatima, muma bamusan..." tayi saurin katseshi da "Banason kana dangantamin yarana da irin maganganun nan" sai yace "Babu wanda yasan gobe Fatima, kar kiga muna cikin arziqi da daular mulki gaba da baya...Babu wanda yasan gobe" a dan fusace tace "Toh ni kodai 'yarka ce ne yarinyar nan?" ya ware Idanu da kyau yana kallonta yace "What??" ta sake cewa "Ka bani amsa in yarka ce Abdulaziz" sai kawai ya tsaya kallonta kamar wadda kai na biyu ya tsiro mata a wuya, bata bar kallonsa ba tace "Abdulaziz" a nutse ya amsa da " Fatima, are you insane?....kaf zuri'armu kin taba ganin me irin idon yarinyar nan?" tace "Probably ta biyo na uwarta wadda kayi tarayya da ita mana" nan kuma hakurinsa yakai geji, rai a bace ya daga murya yana cewa "Da mutuncina?. Da kimata?. Na fito daga tsatson mutunci irinna gidanmu sannan ki zargeni da bin wasu matan a waje har a haifamin dan gaba da fatiha...Fatima you're insane!" kawai ya miqe daga gadon dan zamansa a dakin zai iya sawa ya fada mata abunda ze iya regretting, ganin haka ta sake hasala itama tace "Toh in ba 'yarka ba ace ka dage lallai sai ka kula da ita, baka damu da mutuncin naka ba balle kimarka" yana tsayen yace "Kinsan me?...kiyi tunanin komai ma, ki yarda da duk abunda zuciyarki zata kitsa miki akanta, ga ki ga yarinyar ki kasheta. Ni kuma zan nuna miki nine ubanta a yanzu dan sai nayi shari'a dake wallahi, Fadwa mazaunin 'yar cikina take yanzu kamar yanda hakkin kulawan Jidda ya rataya a wuyana haka itama" da haka ya juya da sassarfa ya fice daga dakin tana kallonsa with shock.


Paid book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758



From the writer of KUNCIN ZUCI...And now


MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa


Chapter 07


Free page


A wannan daren babu wanda bacci ya yiwa dadi shida itan, and for the first time tunda suka zo qasar kimanin wata na biyu kenan a wannan daren suka raba makwancinsu, wanda hakan ba komai ya qara jawowa ba illa tsanar Fadwa da duk abunda ya shafeta a zuciyar Momma. Tayi kuka kuma tayi tsinuwa mara adadi ga wanda ma ya ajiye musu yarinyar a gidansu in the first place, dan a nata tunaninta gani take babu abunda riqon yarinyar zai jawo musu banda rushewar duk wani farin cikinsu a rayuwa. Da aka wayi gari twins sukazo gaishe ta tun daga bakin kofa Imam ya sha jinin jikinsa ganin yanayin mahaifiyar tasu, sai ya qarasa gareta a sanyaye tana zaune a bakin gado ta sunkuyar da kanta. Ahankali ya zauna kusa da ita sannan Imran ya zauna ta dayan barinta shima duk sukayi shiru, sai ta dago kanta tana kallonsu tace "Meye kun wani sani a tsakiya?" ahankali Imran yace "Kiyi hakuri" ta kalleshi sannan tace "Me kuka min? ba kun samu qanwa har kuna qin zuwa gurina ba, kuna gani banida lafiya amma rainon ta ya fi muku zuwa gurina ko?" nan ma Imran yace "A'a Momma" sai kawai sukaji Imam yace "Momma please let her stay with us" batasan lokacin da tureshi da dan qarfinta ba har saida ya kusa faduwa, a zazafe tace "Ficemin daga dakinnan kafin in saba maka, wanda baisan kishin nasa ba" sai kuma ya sake dawowa gefenta ya zauna bai fitan ba, kamo hannunta yayi ahankali yace "I'm sorry Momma" ta kwace hanun nata "Ka rufemin baki" yayi murmushi tareda sake kamo hannun nata, sai kuma tace "Kunyi breakfast?" ya gyada kai sannan Imran yace "Momma yaushe zamu koma gida? an koma hutun fa kuma Papa baice komai ba" sai ta shafa kansa da dayan hannunta tace "Soon. We'll go back soon".
Papa ne ya leqo dakin ganin yanda suka sa uwar tasu a tsakiya yasa shi yin murmushi, yace "Sirri kuke yi ne?" suka murmusa amma banda Momma data kauda kanta bata kallesa ba, sai ya qaraso ya zauna shima a gefen Imam yana kallonta yace "Ya jikin naki?" ta juyo kadan ta amsa da "Lafiya" Imran yace "Papa yaushe zamu koma gida?" yace "Ka gaji da qasar nan kaima ko?" ya gyada kai sai Papan yace "Zamu koma in Momma ta haihu in sha Allah" nan kuma Imran din ya sake cewa "Allah yasa namiji za'a haifa mana" sai Papa yayi murmushi yana kallonsa kawai, anutse shima Imam yace "Amin" nan kuma Momma tace "Meyasa kuke son namiji?" kafin su amsa Papa yace "Ai haka debate din yake daman, namiji na son a haifa musu namiji, mace na son a haifa musu mace" Imran yace "Munason namiji tunda munada Fadwa yanzu ai" kawai iyayen suka tsaya kallonsa, ganin haka sai ya miqe adan hanzarce zai fice daga dakin sai Imam ya miqe shima, Papa bai bar kallonsu ba yace "Ina zakuje kuma?" Imran ya amsa da "Banyi breakfast ba" da haka ya nufi kofa Imam na biye dashi suka fice, sai sannan Papa ya juyo yana kallonta da kyau, ganin yanda ta dinke fuska yasashi nausar da murya yace "Fatima, abun da ya faru jiya.." bai qarasa ba tace "Banason jin komai daga gareka indai ba akan bayar da yarinyar nan bane Baban jidda, sabanin da muke samu akanta ya nunamin zaman ta a gurinmu ba wani alkhairin da hakan zai haifar" sai ya miqe anutse yace "Bazan bayar da ita ba, you should learn to live with that...abunda na fada miki jiyan shi zan sake fadi, Fadwa 'yata ce yanzu and nothing changes that" da haka ya juya zai fice kawai ta duqar da kanta tareda dafa goshinta tana jin wani zafi na taso mata tun daga qasan zuciyar ta. Atake kuma cikinta yayi wani irin juyawa da qarfi, ta buga wani uban qara tana salatin da yasa Papan juyowa daga bakin kofan da sauri ya sake nufota yana tambayan lafiyanta a rikice, durqushewa tayi bata bar yin salatin ba tana dafa cikin, dakyar ta iya

Please Login or Register in order to submit comment