You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uwah suka fito din, da hanzari Uwah tace da Laure "Maza jeki daukomin Fadwa ta tashi" da haka ta fasa karban Khadijan duk Momma na kallonta. Kawo Fadwa dakin sai Momma ta rinqa binta da kallo, nan da nan Laraba ta kawo ruwanta da madaranta Uwah ta karba da kanta ta hau bata ruwan a nutse. Daya daga cikin matan ne ta kalli Fadwan tace "Ina abun qi ga d'a irin wannan, yarinya ma mai hakuri. Inajin tun zuwanmu bata budi baki ba sai yanzu" dayar tace "Ko daya, ai irin wa'innan in dai ka riqesu tsakani da Allah kaine da riba, kuma aljanna na nan tana jiranka" daya ta sake cewa "Wallahi kuwa, Allah dai ya kawo mata uwarta ta gari itama" Uwah dai zuwa sannan ta koma bawa Fadwan madara kuma batace uffan ba hankalinta na kanta.
Momma takai qololuwar cika da  maganganunsu da tasan jifanta suke a kaikaice, amma har ta baro sashen itama batace uffan ba. Haka ta kade zaninta ta musu sallama sannan ta fice Laure na biye da ita riqe da Khadijan. Saida suka isa sashenta sannan tace da Laure "Zan nemeki gobe da dare" ta amsa da "Toh ranki shi dade".. Tsabar bacin rai ma koda Papa ya kirata a wannan daren bata dauka ba, ta cika tayi maqil da zancen kishiyar da matan nan suka jefeta dashi.

Washegari da safe ta aika a mata kiran Habiba. Da Fadwan goye a bayanta ta shigo har cikin dakin Momma da tace ta shigo. Sai da Momma ta dauki minti biyar batace komai ba tana feeding Khadija sannan ta dago kai "Bandakin nan zaki shiga ki qara wankemin towels dinnan, sannan ki wankemin shi" ta amsa da Toh tana kokarin miqewa tareda Fadwa a bayanta sai Momma tace "Da itan zaki shiga kenan?" nan da nan ta sauqo da Fadwan, ganin yanda ta riqetan tana kokarin kwantar da ita akan carpet yasa Momma cewa "D'orata kan kujera". Saida ta jira shigan Habiban bandakin sannan ta kwantar da Khadija a tsanake ta miqe tareda nufan gun Fadwan. Sunkuyawa tayi a hankali tana kallonta sosai, tana bin kowanne features na fuskar yarinyar da kallo a tsanake tanajin zuciyar ta na qara bushewa akanta. Har a wannan lokacin batajin nadaman decision dinta akan yarinyar. Ita kuwa Fadwa sai kallonta take da manyan idanunta, hasken dakin na qara fito da color na kwayar idanunta da suka kasance Grey. Baiwar Allah sai wasa take da hannunta a baki tana damalmala yawu kamar yanda jirajirai sukeyi. Momma takai tsahon minti uku a duqen tana kallonta, sai taji ance "Momma". Da wani mugun firgici ta miqe daga duqen abunka da mara gaskiya, idonta wuri wuri ta kalli Imam dake tsaye a bakin kofar yana kallonta shima, a dan zafafe tace "Meye haka? Ba sallama zaka shigo har nan, Meya faru?" a nutse yace "Imran bai shigo nan ba?" tace "Imran din abokin yawo na ne da zaka min tambayar nan, ba tare kuke ko yaushe ba?" sai yayi shiru yana kallonta, can kuma ya maida idanunsa kan Fadwa dake kwance, har sannan idonta na kan Momma tana wasanta da hannunta, sai kuma ya sake kallon mahaifiyar tasa. Ganin yanda yake binsu da kallo yasa Momma cewa "Meye kake kallona?" "Kaje sashen Uwah ka dubosa" a hankali ya juya daga bakin kofar ya tafi. Da sauri ta koma bakin gadonta ta zauna dan har sannan razanar da tayi yasa bugun zuciyarta bai dawo daidai ba. Habiba ce ta fito daga bandakin tace "Ranki shi dade na kammala komai, akwai wani abun da kikeda buqatar ayi?" fuska a hade Momma tace "Dauketa ku tafi" da haka Habiba ta dauki Fadwan suka fita tana binsu da kallo.
Da yammaci ta sake kiran Madina. Sun dauki lokaci mai tsayi tana sake qarfafa mata gwiwa akan alamarin, ta kuma ce zata kirata da daddare kar ma tace zata canja shawara, sai tace "Madina a yanda nakejin zuciyata a yanzu ba sai kin qara bani wani qwarin gwiwa ba, I'm a goner now. na gaba yayi gaba sai dai Abdulaziz ya samo gawarta in yanada halin isowa da wuri kenan" Madina tace "Ai na sanki ne Adda, wani zubin kema komawa kike kamar Adda Aina'u. May be ma a binne ta kafin ya dawo, Kinga ya huta ta baqin ciki" "Zan kiraki dai anjiman duk da haka" Momma ta amsa tareda kashe wayan. Dare nayi kafin ta kira Laure sai gata tazo da kanta. Daki suka shige Momma tayi qasa da murya "Menene shawararki akai? Ta wacce hanya zaki yi batareda an dau lokaci ba?" ahankali Laure tace "A cikin dakin zan gama komai ranki shi dade, ki bar komai a hannuna" ta gyada kai sannan tace "Kiramin Habiban".  Da Habiba tazo sai Momman ta gyara zamanta a bakin gadon kamar ba wani abu, tace "Kin gama kula da yarinyar zan saki aiki ne" a ladabce tace "Nagama ranki shi dade, tana bacci ma" tace "Toh kije babban kitchen, ki dafomin tuwo acan. Miyan kubewa zakimin, na nan din banji dadinsa ba yau" Habiba tace "Toh, yanzu zanje inyi" da haka ta miqe ta fice. Jim kadan Laure ta shigo sai Momma ta miqe tayi qasa da murya "Ta tafin?" tace "Eh ta tafi can sashen, tabar yarinyar a daki" sai Momma tace "Toh ki fadamin ya zakiyi tukun" tace "Jinjira ce fa, da pillow ma bazai dauki lokaci ba" Momma ta gyada kai gumi na hade mata a goshi tace "Toh Ina jiranki" da haka Laure ta fice, sai kuma Momma ta kasa zama ta fara pacing a dakin tana zuwa da dawowa ta harde hannuwanta a qirjin tareda cizan yatsa daya cikin tsumayen abunda zai faru. Batayi pace hudu ba Laure ta dawo dakin ad'an gigice tace "Bata dakin" cak Momma ta tsaya zuciyarta na bugawa tace "Kamar ya..Kamar ya bata dakin?" Laure ta dan qara yin qasa da murya hankali a tashe tace "Wallahi bata dakin kuma banga Habiba ta fita da ita ba"  da hanzari Momma ta fita daga dakin suka nufi can dakin Fadwan, amma sai suka samu babu kowa acikinsa, a firgice tace "Nemomin Habiban?" "Dubomin ita yanzunnan" da haka suka fice tare Laure tayi waje. Da farko tsayuwan jira Momma tayi a falon sai kuma ta nufi dakinta ta samu Madina na kiranta, tana dauka tace "Madina na shiga uku, kar wani ya san abunda muka qulla, an dauke yarinyar" itama adan firgice tace "Kuma kin tabbatar ba Habiba bace ta dauketa" tace "Laure ta tabbatar min ta fita babu yarinyar, ita Habiban da kanta tace min tayi bacci ma" a zafafe Madina tace "Qarya take, ku nemota tun kafin ta muku tonan silili. Inada tabbacin tasan komai" ai a rikice Momma ta jefar da wayar a gado zata fita suka ci karo da Laure da ta shigo tana haki, tace "Wallahi batacan din ma, har sashen  Uwah sai da naje, mun shiga uku. Tasani wallahi, ta gudu da yarinyar" Momma ta dora hannuwanta duka biyu akai tace "Na shiga Uku ni Fatima"  .......

----------------------------

Eighteen Years Later......

--------------------

End of free pages.

Bintu Musa.

Littafin Muradin zuci paid book ne akan 500 kadai, sannan zaku iya samun more chapters a Arewapen App.
Karku bari muyi tafiyar nan babu ku, there's so much to unravel, dan labarin daban yake wannan karon.
Ku biya kudin ku ta wannan account din.
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya
08134692758


Sneak Peak on Chapter 13
https://www.arewapen.com/chapter?id=6a363dedca0887b357abd7c5

Eighteen Years Later.

Kano, Nigeria.

Thursday, 4:pm

Kwance take akan makeken gadon hannunta riqe da wayarta tana dannawa, tayi ruf da ciki akan pillow ta bada hankalinta gaba daya akan abunda takeyi acikin wayan. Laraba ce ta shigo dakin tareda qarasowa bakin gadon ta dan yi tapping kafafunta data miqar, tace "Fadwa" sai ta ajiye wayar ta juyo a hankali tana kallonta "Kije Uwah na kiranki" da haka ta juya tabar dakin. Miqewa zaune tayi tana gyara zaman doguwar rigar atamfar dake jikinta, sannan ta janyo dankwalinta daya ware a gefenta, madadin ta daura saita fara tattare dogon gashinta daya sauqa har gadon bayanta sannan ta miqe tsaye tana neman ribbon din nata akan gadon, amma sai tayi ta lalube bata ganshi ba. A hakan ta fita falon da dankwalin a daure akanta wanda ko rabin gashin nata bai rufe ba. Uwah na zaune akan babban dardumanta tana jan tasbaha ta juyo tana kallonta, sai tace "A kammala gashin nan guri daya Fadwa" cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro tace "Narasa ribbon din ne, Inata nema bangani ba" Uwah tace "Je ki bude closet dina akwai wanda kika bari satincan yananan" Khadijah dake kwance a kujera ta dago kanta daga kallon wayan hannunta tana bin Fadwan da kallo batace komai ba har ta juya ta koma dakin. Bata dade ba ta dawo falon kanta a nannade har da gyalenta hannunta riqe da wayoyinta guda biyu, sai Uwah ta juya ga Khadija tace "Ki tashi ki shirya nasan drivern ku yana hanya yanzu" sai itama ta miqe zaune fuskar nan a dinke ba alamun fara'a. Basu jima a zaune ba daya daga cikin hadiman Uwah ta shigo falon da sallama tana sanar dasu zuwan mai daukan nasu. Ba yabo ba fallasa Khadija tace da Uwah "Mun tafi" sannan ta riga Fadwa fita daga falon. Sai itama Fadwan ta miqe amma ta dan tsaya tace "Inason in kwana anan" Uwah na kallonta tayi murmushi "Kinsan dai Mai martaba na dawowa zai nemeku" tace "Ai bai dawo daga wajen taron ba" Uwah tace "Kije dai yanzu, in yaso sai ki dawo a weekend ki kwana din" sai ta sake cewa "Toh yaushe zaki dawo?" Uwah ta dan tsaya kallonta har sannan fuskarta a sake, tace "Sai na dan qara hutawa tukun, amma bazan dade ba" sai Fadwa ta gyada kai a hankali tanajin ba dadi a ranta, ita ta rasa yaushe Uwah zata fahimci cewar masarautar ba dadi yake mata ba in bata nan, babu ranar da in zata koma batajin zuciyarta na mata qunci. Gurin Mai Martaba kadai takejin sanyi arai indai taje gaishesa, she feel more at home with him each day. Da haka ta fice daga falon cikin sanyin jiki ta nufi parking lot din gidan. Sai ta samu Khadija tsaye a jikin motan ta harde hannu a qirji tana wurga mata wani mugun kallo, tun kafin ma ta qarasa Khadija tace "Ki bari in kika siyi motar ki sai kiyi ikon naki akai, amma ba yanzu da ake miki alfarma ba" ko ci kanki Fadwa batace mata ba ta zagaya ta bude back seat din ta shige, Khadija tayi tsaki itama ta bude back seat din bangarenta ta shiga. Har suka isa ba wadda ta juyo ta kalli 'yar'uwarta balle magana ta hadasu, kowacce tana zaune at far end na motan tana kallon window.......
Ku biya 500 mu tafi tare.
Bintu ✍️ 📖






Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment