You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Papan, sai da suka dauki lokaci a dakin sannan suka fice while Papan yayi kiran Habiba dake wajen Momma, bayan ta fito a hanzarce yace mata "Kayan sakawa ne kadai ya saura acikin abubuwan da take da buqatan ko?" tace "Eh ranka shi dade, da dai mayukan yara irin wanda kuka siyo kwanaki da Gimbiya" ya gyada kai sannan ya dauki qaramar jakansa dake dauke da takardun da zai buqata a wajen aikin nasa sannan ya sake leqawa dakin matar tasa suyi sallama. Tana hakimce a bakin gadon hannunta riqe da plate Habiban ta kawo mata nata breakfast din, ganinsa yasa jidda baro gurin mahaifiyarta ta qaraso garesa tana maqalqale kafansa, sai yayi murmushi tareda shafa kanta yace "Where is my little pumpkin?" tana dariya tace "Mee Papa" da haka suka qarasa gurin Momman da idanunta ke kan plate din bata dago ba har sannan, saida ya zauna a kusa da ita ya umarci jidda da taje gurin yayunta sannan ya sake maida hankali gareta yace "How are you feeling?" a nutse tace "Na dauka samun 'yar tsintuwar yasa ka mantawa dani da kuma jininka dake jikina" madadin ya nuna haushin kalaman nata sai ya danne tareda dan yin murmushi yace "Jiya kadai dan ban bi abunda kikeso ba yaci ki zamo me fahimta ta Fatima, i thought ko bance ki kula da ita ba ke me jin tausayin tane, cikin sanyin nan akayi dumping dinta batareda tausayi ba, menene nata aciki, sannan menene laifi na dan na nemi kulawa da ita, ke kanki kin sani babu yanda za'ayi in fitar da yarinyar nan waje a jiya, in kaita Ina? Haba Fatima, Ina imaninki ya tafi?" sai lokacin ta dago kai tana kallonsa, nan hawaye suka fara taruwa mata a Idanu sannan tace "Wato dan na nemi kare mutuncin ka shine rashin imani, yarinyar da kana gani kasan 'yar qazanta ce, wane irin maganganu kake son jawo mana da mutuncin ka, daraja da kuma kimarka?" nan kuma ransa ya fara baci yace "Kina gurin ne da aka sameta ta hanyar qazantar, wai me yake damunki ne Fatima, da kike maganar kima da daraja kina tsammanin mahaifan nawa zasuyi alfahari da cewar na yardar da yarinyar ba tareda na bata shelter bane?" Tayi shiru bata basa amsa ba sai ya sake cewa "Zan zamo jagora bisa mulkin iyayena da kakanni da zan karbi ragama kuma ace tun yanzu bazan iya kwatanta jinqai ba me na zamo kenan? will you be proud of that man?" nan ma tayi shiru batace komai ba, sauqe numfashi yayi sai ya nutsar da muryarsa wannan karon cikin lallashi ya kuma fadin "Ki tayani mu samu ladanta koda na qanqanin lokaci ne Fatima, tunda baki amince da mu riqetan ba zan samo mafita tunda wannan ba qaramin case bane a qasar nan. But before that, please ki ban hadin kai mu kula da baiwar Allahn nan, gidaje dayawa acikin estate dinnan amma sai Allah ya kawota garemu, bamu san me ya boye a cikin lamarin nan ba" ta gyada kai nan ma bata amsa ba sannan ta cigaba da cin abincinta, ganin tayi shiru yasa shi yi mata sallama tareda miqewa ya nufi kofa ta bisa da kallo sannan ta dan tabe baki tana qara hade fuska.

Papa bai dawo gidan ba sai karfe sha daya na safen ya shigo gidan hannunsa niqi niqi da kaya. A dan gigice ya shigo falon sanadin jiyo kukan Fadwa da yayi tun kafin ya bude kofan, sai ya samu su Imam da Imran din tsaye a dan nesa da dakin da Fadwan ke kwance tana ta tsala ihu sun kasa shiga ciki. Da sauri ya ajiye kayan akan table sannan ya nufi dakin ya shiga nan ya sameta har fuskar nan tata tayi jaa abunka da farin fata, cikin hanzari ya dauketa dalilin wani irin tausayi da ta basa ya dorata a kafadansa ya hau jijjaga ta, baiwar Allah sai ta tsaida kukan ta fara ajiyan zuciya jin ta ajikin mutum, sai ya juyo yana kallon twins da suke kallonsa a bakin kofan, idon Imran tsuru tsuru dayake yafi dan'uwansa Imam din tsoro a tarin lokuta, da sauri yayi magana ganin yanda baban nasu ke kallonsu "Momma tace kar mu shiga" ya sake cewa "Imam ya shiga ta dakeshi" sai Papan ya kalli Imam din da ya sunkuyar da kai baice komai ba, da haka ya fito ya wucesu yana kiran Habiban, da saurinta ta fito daga dakin Momman tana sunkuyar da kai jikinta na dan rawa na sanin me tayi, amma kuma ba laifinta bane tunda itama uwar dakin nata ce ta umarceta da tayi mata wasu ayyukan tabar yarinyar, ganin yanda take a tsoracen sai Papa ya fahimci wani abu, ya fara kokarin danne bacin ran nasa yace "Ya kika barta tana kuka, bayan na bar miki kulawanta" da sauri tace "Ka gafarceni yallabai, hakan bazai sake faruwa ba" sai ya gyada kai tareda sauqo da Fadwan daga kafansa yana kallon yanda ta fara kokarin komawa bacci, ya miqota ga Habiban yace "Ki mata wanka, ga kayanta can na kawo, ki tabbatar ta qoshi sosai kafin ta koma baccin, banason abunda ya faru yau ya sake maimaituwa" jiki na bari Habiba ta amsa da "Kayi hakuri yallabai ka gafarceni, bazai sake faruwa ba" sannan ta miqe tareda karban Fadwan ta nufi dakin kwanan su da ita, da dan hanzari Imam ya dauki kayan da Papan ya siyo wa Fadwan yabi bayan Habiban Imran na biye dashi da wasu a hannu suka shige dakin dukansu. Sauke numfashi Papa yayi yanajin bacin ran abunda matar tasa ta aikata bayan ko awanni uku masu kyau ba'ayi ba ya gama neman alfarman tallafinta gurin kula da marainiyar Allah, sai ya girgiza kai kawai ya nufi dakin nata aransa yana tunanin yanda halinta ke sake banbanta a kullum sabanin yanda ya santa baya.
Sai 12 ya shirya tafiya wajen aikinsa bayan ya tabbatar da Fadwan ta samu kulawan da take buqata sannan yayi sallama da iyalinsa ya fice, bayan ya gamo ayyukansa wajen 4 o'clock bai koma gida ba ya nufi gidan Abokinsa me suna Ladan dake living anan Houston din shima da familynsa, dan zuwa sannan duk tunanin da zeyi yayi akan lamarin nan and it's all leading him to one option, shine dole ya bada jinjira nan ga child services, dole yayi reporting ga police, duk yanda yake son yarinyar da kuma son samun ladanta dole haka zai hakura saboda jalala irinta matar da Allah ya hadasa da ita.


Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay

Shaidar biya: 08134692858




From the writer of KUNCIN ZUCI...And now



MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️



Chapter 04

Free page
Papa bai dade ba ya isa gidan Abokin nasa mai suna Ladan, wanda ya kasance citizen din qasar dalilin iyayensa da suka kasance Nigerian immigrants and living in the united states for a long time, a yayinda kuma abota ta hadosa da Papa tun samartakarsu a sanadiyar degree dinsu da suka yi tare a makaranta daya.
Iso Ladan ya masa zuwa dan qaramin garden dinsa dake backyard na gidan suka zauna bisa kujeru na shan iska sannan matarsa mai suna Zulaiha ta kawo musu abun sha ta kuma gaisa da Papan. Sun dau lokaci suna hiran rayuwa da kuma businesses dinsu a inda Ladan din yace dashi "Kargi is high time ka fara tunanin expanding cooperation dinnan naku zuwa Atlanta, there's alot of business potentials there, inda ni nakeda irin privilege dinka na rayuwa da wuya in zauna a guri daya haka sai dai wani ikon Allah. Duniyar matsawa take da gudu yanzu. There will come a time that zuwa America zai zamo abu mafi sauqi ga mutane unlike yanda ake wahalar samun zuwa yanzu" sai Papa ya ajiye cup din hannunsa ya kallesa "Abunda nake ta tunani yanzu haka kenan, in sha Allah zanyi maganan da mai martaba sai muyi shawara, dan kaga yanzu hankalina yafi karkata ga haihuwan mai dakina tukunna, da kuma passport din Babyn, amma zamuyi hakan da yardar Allah" Ladan ya gyada kai cikin gamsuwa sannan yace "Hakane, Allah ya sauketa lafiya" ya amsa da Amin suka danyi shiru while nursing their drinks, can Papa yace "Ladan, nazo neman shawararka akan wani al'amari daya tunkaromu nida iyalina, nayi tunanin iya tunani amma kaina ya kulle akan ta yadda zan bullowa lamarin" nan Ladan ya dan gyara zama yana kallonsa, sai ya hau bashi labarin abubuwan da suka farun daga daren da aka ajiye musu babyn har zuwa wannan ranan, kafin ya gama maganan Ladan yace "Abdulaziz meyesa zaka saka kanka acikin irin wannan matsalan?" sai Papan ya dan hade gira yace "Bakaji me nace bane? Ce maka nayi fa har cikin compound aka ajiye mana ita, ya kakeso inyi? left her in this cold freezing weather?" Ladan ya sauqe numfashi yayi shiru na wasu sakkani tukunna, can yace "Ai lamarin qasar nan dinne, bakayi bama kamar jira suke balle issue irin haka ya faru? But you should've call the police Kargi, nan da Nigeria akwai banbancin mai matuqar yawa" Papa yace "Nasani, shiyasa nazo ka bani shawara ai, raina nason riqe yarinyar nan Ladan, wani irin protectiveness nake ji akanta banason ta fada wani mugun hannun wallahi, Inason riqeta in bata duk wani kulawan rayuwa ta yanda bazata rasa duk wani gatan da ake tunanin yara kamarta suke rashi ba" Ladan yace "Me matarka tace akan haka? ta amince da ku riqetan ne?" ya girgiza kai yace "A'a, as a matter of fact a ganinta na farko da yarinyar ta qi komai dangane da ita, can you believe har hana hadimarta kula da yarinyar tayi, haka na dawo gidan nasamu tanata kuka abun tausayi" sai Ladan yace "Toh kaga matsala ta farko kenan Kargi, dan wannan matsalace babba, the best idea shine ka bada yarinyar nan ga child services, tunda Fatima bataso babu ta yanda zaka taba jin dadin kula da yarinyar nan, Happy wife Happy home" Papa ya girgiza kai "Na dade bama fuskantar same angle nida Fatima, it's always the opposite Ladan, she never understands where I'm heading, yara irin wannan ba qaramin lada ake samu da riqonsu ba. Allah ya gani Ina tausayinta" sai Ladan yayi shiru yana kallonsa baice komai ba, ganin haka sai Papa yace "Amma tunda kaima hakan kace shikenan zan bada itan, addu'ana daya kar Allah yasa ta fada mugun hannun ko kuma ta taso cikin Christianity, Qasar nan ba ruwansu da wannan in suka tashi bada yaro, Allah ya dubeta duk inda take" a sanyaye Ladan ya amsa da Amin sannan suka koma wani batun daban.

Da wannan tunanin ya koma gida, amma abun mamaki yana dosar gidan nasa ya samu motoci biyu a fake a daidai bakin gate. A kallo na farko ya gane daya data kasance ta police daya kuma bazai shaida ta waye ba, duk yanda yakai ga taurin zuciya sai da yaji hantarsa ta kada, tunaninsa a wannan lokacin kodai neighbors dinsu sunsan me yake faruwa toh?. Da haka yayi parking a gefensu yana fitowa sai daya daga cikin polisawan ya qaraso garesa suka gaisa ya qara da "Sir, we need to have a few words with you" shima yace "Let's go inside then" da haka ya musu jagora zuwa cikin gidan suka shiga tare yana gaba.
A falo ya tadda Momma zaune kusada wata middle age woman wacce ke riqe da folders a hannunta tana nazarin bayanin da Momman ke mata, ta gefe dasu kuma Habiba ce tsaye riqe da Fadwan a hannunta ga twins tsaye a gefenta suma, sai bayan su Papan sun zazzauna matar ta kallesa ta fara magana cikin harshen turanci kamar haka "Matarka ta kira office dinmu akan yarinyar da aka ajiye muku jiya, shine muka zo saboda akwai buqatar zamu riqe yarinyar a hannun mu Mr. Kargi" sai police daya ya karbi maganan shima "Amma kafin nan munada buqatar muje station kayi cike cike, mun duba cameras na street dinku mun tabbatar ajiyeta akayi amma dole sai mun tafi dakai dan buqatar bayani daga bakinka" jiki a sanyaye Papa ya juya yana kallon Momma da taqi kallon idonsa, duk yanda yakai ga danne bacin ransa saida hakan ya bayyana akan fuskarsa, sai matar can din ta sake cewa "Ka fahimcemu Mr Kargi, bamu zo da tashin hankali ba aikin mu muka zo yi, yara irin wa'innan daman aikinmu ne na tabbatar da sun samu kulawan da suke buqata" nan Papa ya gyada kai ahankali, a turance yace "I understand...Miss??" tayi saurin cewa "Eva..It's Eva Hollaway, from Texas Department of Family and Protective services" ya gyada kai "Okay, Miss Eva..I understand" da haka suka mimmiqe sai ta juya tayi godiya a Momma da ta kirasun, a nutse ta amsa da "Thank you Miss Eva" Papa na kallonta, Har suka fice kuma taqi kallonshi sai sunkuyar da kai take tana wani ciccin magani.

Papa bai dauki wani dogon lokaci a station din ba ya gama cike ciken da ake buqata daga garesa, amma da aka nanu masa clip na record din matar da ta ajiye jinjirar sai da ya qame a zaune dan mamakin ganin motar da ta fito daga cikinta, kansa ne ya kulle ganin babu wani alamun talauci a tattare da matar duk da yanda ta rufe fuskarta, hasali ma irin motar da yake hawa tazo da ita sannan daga yanayin kayan da ya gani jikin yarinyar tun farkon ganinsa da ita ya shaida cewan duk inda ta fito babu talauci a ahalin. Anan suka sanar dashi plate numbern motan matar was not registered kwata kwata duk iya tracing din da sukayi, ya gyada kai cikin fahimta yana jin wani tausayin jinjirar na sake shigansa a wannan lokacin amma haka ya danne komai har ya gama abun suke buqata daga garesa a station din.
Kasancewan maghrib ta masa a nan din sai bai je social service office din ba, sukayi agreement da miss Eva dake tare dasu a station akan zai dawo washegarin ranan.

Fitowa sukayi a tare da ita tana riqe da Fadwan sannan ta nufi motan ta ta sakata suka tafi da ita yana kallonsu wanda hakan ba qaramin karya zuciyar sa ya sake yi ba. Ga tsananin bacin ran abunda matarsa ta masa wanda har sannan yana jin dacin rashin ganin mutuncinsa da batayi ba tayi abu gaban kanta batare da shawararsa ba, haka ya hadiye komai ya nemi taxin da zata kaisa gida. Da ya isa gidan yana bude falon Momma ta dago kai tana kallonsa sai ya dauke kansa ya nufi dakinsu dan yayi sallah, saida ya zo wucewa ta gabanta ta fara kokarin miqewa da kyar dan Habiba da twins basa falon, tana kallonsa tace "Baban Jidda i had to do what is safe for us, this is the only way and you're not making any effort to do so" sai ya juyo a nutse yace "Kinji nace wani abu ne?" tayi shiru tana kallonsa batace komai ba, ya juya tareda nufan dakin yana danne duk wani abunda ke taso masa a zuciya. Har suka zo kwanciya Papa baice mata qala game da abunda tayin ba, itama ganin haka sai taqi kulasa aganinta duk inda aka samu kwana biyu komai zai wuce, zasu dawo yanda suke a baya dan sanin da tayiwa mijin nata mai hakuri ne da kuma rashin riqe abu arai...Saidai abunda bata sani ba shine wannan karon tayi kuskure, ta kuma tura shi har zuwa maqurar da ya dau damarar nuna mata matsayinta na macen dake qarqashinsa.

The following day beyi qasa a gwiwa ba ya tafi office dinsu Eva da safe. Da isarsa ya fara neman izinin yaga Fadwan amma suka qi barinsa acewarsu hakan "It's not allowed" sai aka kaisa office din shugaban sashen a inda shima shugaban yayi kiran na qasa dashi a qaramin meeting room wanda a nan Papa ya sake musu bayanin duk abunda ya farun, bayan sun gama paperwork sai ya nemi magana da over roll shugaban nasu a office dinsa. Sanin co-operation companyn su Papan ba boyayye bane a Houston yasa shugaban bashi girman sa har da kawo masa ruwa amma bai sha ba, ya gyara zama tareda dan matsar da glass cup din gefe yace "What are the necessary requirements that I'll need to fulfill before adopting this child legally?".
Sai shugaban me suna Carl yace masa abune me sauqi tunda duk wani qualities din da ake nema na wanda zeyi adopting yaro shi Papan ya cikesu, kawai za'a bi legal paperwork ne for court approval amma kuma akwai abu guda daya, sai da consent din both married couple din which means sai lallai da amincewar ita Momman sannan za'a basu yarinyar, Jan aiki.
A farkon satin da ya fara going through process din ko bin ta kan Momman beyi ba ganin yanda ta manta da batun ma ta cigaba da rayuwar ta cikin kwanciyar hankali a gidan, duk yanda hankalin twins yake kan Fadwan more especially Imam haka ya danne in sun tambayesa inda take sai yace musu "Tananan lafiya". Habiba ma taji zafin uwargijiyar tata amma babu yanda ta iya balle tayi magana, haka ta cigaba da abunda ya kawota gidan tana ganin yanda Momman ta kama sabgoginta kamar ba uwa ba. Papa na iya kokarinsa na danne komai dukda tana ganin coldness dinsa lokaci lokaci dan abune da ya quduri niyya a ransa na sai ya bata mamaki akan abunda tayin. Zata sha mamakinsa matuqa.

A wani dare ya yanke shawaran kiran mahaifin sa dan sanar dashi duk da yasan ko bai fada masa ba abunda yake shirin yi din daidai ne. A lokacin da ya gama isar da bayanin nasa ta waya, sai Dattijon ya nutsar da muryarsa gurin cewa "Abu ne mai kyau hakan, kuma Allah zai muku jagora matuqar niyyarku akan yarinyar tsaftatacciya ce" yace "In sha Allah. Nagode, Allah ya qara girma" sai mahaifin nasa ya sake cewa "Mai dakin taka ce zata riqeta?" Ya amsa da "Muna shawara akan wannan din tukunna" sai yace "Yayi, Allah yayi albarka" ya amsa da Amin yanajin nauyin abun da yake shirin yi din na sauqa daga zuciyar sa.

Sati biyun da suka biyo baya ya cigaba da cukucukun adoption din tareda Eva kuma zuwa sannan suna barinsa yaga Fadwan in yaje office din nasu, atarin lokuta in aka kawo masa ita sai yaji kamar ya tafi gida da ita a lokacin, wani irin iko na ubangiji sai ya saka masa so da tausayin yarinyar matuqa aransa, da ita yake kwana arai most days saboda tunanin yanda batada kowa da kuma gata a wannan lokacin sai inda aka miqata. Da akazo batun lallai ana buqatan consent din Momma sai yayi confiding da Eva akan halin da yake ciki da me dakin nasa, itama taji ba dadi sosai amma cikin qarfafa gwiwa tace "Mr Kargi, Ina ganin soyayyar yarinyar nan a idanunka da kuma actions dinka, wanda hakan ya nuna min cewa Fadwa is safe with you, zata samu dukkannin gatan da muke fatan duk yaron da muka bada shi ya samu, abun da zakayi yanzu shine ka nemo qwararren lawyer da zai shige maka gaba akan hakan, Ina tabbatar maka da in process din ya tafi daidai ba sai matarka tayi signing komai ba zaka tafi gida da 'yarka" ta qarasa tana murmushin bashi qwarin gwiwa, godiya ya mata sosai yana jin dadin shawaran nata sannan ya bar office din. Da wannan Papa yayi wining case din a kotu a ranan Thursday, 15th of November. A yayinda qwararren lawyernsa da ya shige masa gaba ya jajirce sosai dan ba qaramin kudi ya zubar akan case din ba duk dan saboda suyi winning case din...And right there agaban su Ladan da sauran jama'an dake zaune cikin kotun Alkalin ya qaddamar da cewar Fadwa ta zama 'yarsa halak malak.

Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758


MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa ✍️


Chapter 05

Free page


Bayan kwana biyu da gama zamansu na kotu sai department of child services din suka yi masa duk wasu cike cike na takardu da yake buqata akan Fadwan wanda bayan nan har asibiti sai da suka kaita tare dashi akayi mata duk wasu gwaje gwajen da ya kamata kuma Alhamdulillah sai results dinta suka fito "Disease free", ba qaramin dadi Papa ya ji ba more especially da ya ga genotype dinta was excellent. Da fari su Eva sun nemi zabinsa na canja mata sunanta in yanada buqatan hakan amma bai amince ba. Sai da akazo cike mata surname ya nemi su cire Kargi daga cikin sunanta su saka mata "Fadwa A. Abdulfatah" akan wasu dalilai nasa da bai bayyana musu ba, har Ladan dake zaune a gefensa sai da ya kallesa a wannan lokacin amma baice komai ba.

A kwana na uku.
Yana riqe da ita suka fito daga social service office din Eva na biye dasu, sai da suka qarasa ga motarsa sannan ya juyo ya fara godiya a Eva, tana murmushi tace "This child is lucky to have you, Mr Kargi" yayi murmushi "Thank you once again Miss Eva" da haka ya bude motan sai Ladan ya nemi yi masa rakiya sanin me zai tarar a gidan nasa, girgiza kai yayi yace masa "Ba damuwa, zan kiraka" ya qarasa maganan yana saka Fadwa acikin baby stroller da yayi attaching da car seat dinsa wanda takanas ya siyo guda biyu, daya nata dayan kuma na upcoming babyn da za'a haifa masa.
Bai dauki lokaci ba ya isa gidan sannan ya zagaya ya sake daukanta a hankali yana murmushi ganin yanda ko motsin tashi batayi daga baccinta. A compound din ya tadda su Imran na wasa da bingirar ruwa, Imran din na gudu Imam na biye dashi yana jiqashi suna dariya, ganin Papa da Baby hannu yasa suka nufesa da saurinsu, Imran yace "Papa, ka dawo mana da Fadwa?" ya gyada kai yana murmushi "She's back, as your sister" Imam yayi murmushi yafara kokarin karbanta sai Papan ya basa ita ya dora ta a kafadansa har da dan jijjagata kadan duk Papan na kallonsa, da haka kuma sannan suka shiga cikin gidan. Basu samu Momman a falon ba sai Habiba da take ta goge goge, tana ganinsa ta tsugunna suka gaisa sannan yace "Karbi yarinyar nan a mata wanka, akwai madaranta ko sai an siyo?" da sauri ta kalli hannun Imam ta kasa amsawa saida Papa ya sake maimaita maganan sannan ta amsa da "Eh ranka shi dade, akwai" da haka ta karbi Fadwan jiki a sanyaye tana hasko rikicin da za'a kwasa da uwardakinta.
Maganarta Dutse....Momma na zaune a bakin mirror'n ta Papa ya shigo dakin, ta juyo ta kallesa sau daya ta dauke kai dalilin har sannan suna 'yar sama sama da juna, amma ga mamakinta sai taga ya zauna a bakin gadonta yayi patting gefensa yace "Zo ki zauna zamuyi magana" asannu ta tashi sannan ta qaraso kusada shi din ta zauna. Saida suka dauki wasu mintuna sannan cikin nutsuwa ya fara jefa mata tambaya "Fatima, Inason ki fadamin ko da akwai abunda na rageki dashi a iya zamanmu?" sai ta kallesa tana hade fuska tace "Meya kawo wannan maganan kuma?" yace "Inason ki bani amsata" ta girgiza kai tana kawar da fuskanta, ya sake cewa "Akwai ta inda na sabo a zamanmu? ko ta furuci..ko kuma ta yanda nake mu'amalantarki da yasa kike yawan daukana ba'a komai ba" nan kuma ta dan ware ido tace "Ni yaushe na dauke ka ba ba'a komai ba?" "In akan maganan 'yar tsintuwar can ce yasa kake fadan hakan ai nayi abunda ya dace ne" cike da bacin rai yace "Kina nufin kin fini sanin abunda ya dace kenan Fatima?, ace Ina mijinki amma kullum maganata ce zata zamo abun tsallakewarki, abun takawarki yanda kika ga dama, a kullum ke sai kinyi qoqarin defying dina a duk abunda zance kenan" a zafafe itama tace "Ya Ina matarka zakace sai kayi forcing dina akan abunda banaso. Tun kawowar yarinyar nan gidan nan nace maka ka fitar da ita kaqi to ya kake so in maka in ban kira an fitar min da ita daga gidana ba" Papa baisan lokacin da ya miqe ba yana munata da yatsa yace "Baki isa ba Fatima, baki isa ki juyani yanda kika ga dama ba in kyaleki. Bamu

Please Login or Register in order to submit comment