You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa gaisuwarsu, suka rinqa zubo masa kirari har ya shige. A Babban falon ya samesu bayan Laure ta zuba musu abinci da ta dafa musu ire ire daban sai wanda suka zaba. Imam na kwance a kujera yana zane a white sheet while Imran yana kallon Tv. Shigarsa Imran ya juyo yace "Papa barka da dare" yana murmushi ya qarasa tareda zama a kujera, Imam ya miqe zaune suka gaishesa ya amsa, again sai ya qara kai hannu ya dauki sheet dinda Imam din ke zane a cikinsa yana kallo a tsanake, yaso ya gane building din amma sai kansa ya kulle, sai ya kalli Imam din yace "What's this?" Imam ya dan matso suna kallo a tare sai ya kai yatsa yana nuna gurbin da bai gama sketching ba, yace "This has to go from here to the top" ya sake nuna wani gurbin "And from there, it goes straight to the outer layers of..." bai qarasa ba Papan ya sake kallonsa yace "Ina nufin building din Imam, Ina zan san outer or inner layers" ya qarasa maganan yana murmushi, sai Imam yayi murmushin shima sannan yace "It's JPMorgan Chase Tower" Papa ya dan hade girarsa in confusion da fari, sai can yace "Houston??" Imam ya gyada kai tareda kai hannunsa ya juya zaman sheet din a hannun Papa dan a kaikaice ya riqe ta shiyasa bai gane ba, aikuwa nan Papa yadan ware ido bayan ya fahimci zanen, sai ya sake juyawa ya kalli Imam din da mamaki, yace "Taya kas..." "How do you know it?" sai lokacin Imran yace "Papa you took us there, remember?" ya gyada kai yana sake kallon zanen. Har gobe baya jin zai daina mamakin abubuwan da Imam ke zanawa, it's just raw talent da Allah ya bawa yaron tun baije ko Ina a rayuwa ba. Sai ya sake cewa "But who taught you this?" Imam ya girgiza kai sannan yace "I just did it" shiru Papan yayi baice komai ba yana kallon d'an nasa. Anan part din yaci abinci tare dasu sannan ya tafi.

Har yazo kwanciya baiji shigowar Momma ba sai kawai ya tafi sashen nata. Yana shiga hadimanta suka fice duk suka bashi guri ya qarasa har bakin dakinta tareda tura kofar, amma sai ya jita a datse. Ahankali ya kwankwasa shima shiru bata amsa ba. Haka ya hakura ya nufi dakin da Fadwa take, nan ma Habiba ta fice ta bashi guri ya qarasa ciki, tana kwance acikin crib dinta amma batayi bacci ba dan ga feedernta nan akan wani stool Habiban ta ajiye alamun bata dade da bata madaran ba. A hankali ya sunkuya ya daukota sannan ya zauna a resting sofa dake dakin yana dan mata wasa da yatsansa a kumatunta tana kallonsa. Quri yayi yana kallonta cikin tausayawa, yarinyar abun tausayi ce, so vulnerable a hannunsa. Hamma tayi sai yakai hannu ya kare bakin nata da haka kuma idanunta suka fara lumshewa alamun bacci, sai ya danyi murmushi na sanin yawan baccinta. Madadin kuka sai yarinyar ta zamo me yawan bacci akai akai, maida ita yayi cikin crib dinta sannan ya lullubeta, saida ya mata addu'o'i sannan ya fice. Bai koma dakin Momman ba ya wuce bangarensa.
Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay

Shaidar biya 08134692758



MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa



Chapter 11


Free page

Har garin Allah ya waye Momma bata rintsa ba, wani irin zafi da nauyi ta rinqa ji a zuciyarta kamar ana diga mata wuta. Babu abunda ke mata dadi a wannan lokacin, kuka kuwa ta yisa har ta gaji, ta kuma tsinewa jinjirar da duk ahalinta da suka ja mata wannan fitinar a gidan aurenta. Ita babu abunda yafi ci mata ranta irin wai akan yar tsintuwa za'a mata kishiya, akan yarinyar da ba'a san asalinta bama balle susan wacece ita. Indai haka ne toh tana jin har duniya ta nade babu ranar da zatazo Fadwa da abunda ya shafeta, bazata taba manta baqin cikin data qunsa ta dalilinta ba. Tun gari bai gama wayewa ba ta danna kira a Aina'u, a bugu na uku ta dauki kiran sai ta fashe da kuka me cin rai, hankalin Aina'un a tashe tace "Subhanallahi, Binta meya faru?" Momma bata bar kukan ba tace "Adda in nace banason yarinyar nan ko a gaba kar kowa ya kamani da laifi. Wallahi na tsani komai game da ita, ji nake kamar in kasheta in huta" da sauri Aina'u tace "Innalillahi, meya haka wai. Kanki daya kuwa, ki nutsu ki fadamin meya faru?" Cikin gunjin kuka tace "Wai akanta Abdulaziz yake ikirarin qaromin abokiyar zama, kishiya fa Adda, kuma wai akan yar tsintuwa" ta qarasa maganan wani kukan na zuwa mata da karfi. Shiru Aina'u tayi dan wannan batu ya daketa sosai itama, amma cikin dakewa tace "Binta kowa da irin kaddararsa a rayuwa, taki tazo a hakane sai ki zamo me karba ki godewa Allah, bawai kuma Ina bin bayan Abdulaziz bane, haqiqa dan kyautawa bai kyauta ba. Hakan da yayi kuma sake tabarbare lamuran yayi, duk da kema kinada naki kamashon kusan kashi saba'in acikin alamarin nan, na fada miki ki danne komai ki riqe yarinyar nan, ta hakan ne zaku samu maslaha tunda kin fahimci yanason yarinyar sosai, da ta hakan ne zaki qara janyo mijinki a jiki amma kikayi biris da maganata Binta, kika nuna ke kin isa kiyi yanda kike so babu mai tanqwaraki, Kinga irin kofar da kika bude yanzu ko, kinga irin matsalan da nake guje miki ko? Yanzu wa gari ya waya?" Momma ta share hawayenta cikin qunan zuci tace "Nida Yarana mun zamo abun banza agurinsa kenan? Kinason kicemin yar tsintuwar ta fimu a gurinsa kenan?" Aina'u tace "Ko daya, ni nasan bata fiku a gurinsa ba, amma laifinki anan shine. Tunda kikaga a karo na farko Abdulaziz bai bi ra'ayinki akan yarinyar nan ba sai ki sauqo ki karbeta, da shine zaman lafiyan naku, amma kika nuna naki taurin kan. Ta Ina kikaji ance Maza suna son macen da kullum tanason nuna ra'ayin ta ne abun fifiko akan nasu, Namiji ba'a masa haka duk sanyinsa Binta, amma baki fahimceni ba, sai da nace miki kota salon kissa ki karbi yarinyar da yanzu wata maganar mukeyi" Momma tayi shiru tana dafa kanta, ji take komai na duniyar ya fita kanta a wannan lokacin, wani kukan ne yana qara zuwa mata, sai kawai ta sakeshi a hankali wannan karon, shiru Aina'u tayi tana sauraron ta, dan itama bawai bataji zafin lamarin bane, amma tasani Binta tana aure a gidan sarauta ne kuma ko ba yanzu ba, there are high chances sai Mijinta ya qaro mata abokan zama, amma cewar ta dalilin Fadwan ne kwata kwata yasa itama taji ta fara qin yarinyar a zuciya. Tunda yarinyar ta shigo picture din abubuwa suke ta lalacewa a gidan auren qanwar tata.
Hakuri ta hau bawa Momman, ta qara da fadin "Kiyi hakuri, kuma a yanzu ma lokaci bai qure ba. Ki samesa kuyi magana ta fahimta, mijinki yanada sanyin hali ta wani wajen. Nasan ko yau kika karbi yarinyar zai ajiye wannan batun agefe. Try that Binta, in sha Allah komai zai wuce" sai sannan Momma tace "Bazai taba wucewa ba, wannan baqin cikin da nake ji ayanzu bazai taba wucewa ba wallahi" Aina'u ta sake cewa "I said try that Binta, I'll be traveling later. It's a morning flight, 10 o'clock" Momma tace "Yau ne tafiyar?" tace "Eh in sha Allah, we decided Bristol was okay" tace "Allah ya sauqeki lafiya Adda, sai nan da two months din kenan?" Aina'u ta dan ja numfashi "I wish I'll be there for you, amma in sha Allah zan rinqa kira, ni dai dan Allah ki sauqo da kanki kibi lamarin nan ta hankali. Sannan ki kama bakinki, ba kowacce magana zaki rinqa fadi ba yanzu, nasan halinki in kina cikin bacin rai, akan gab'a mijinki yake yanzu komai zai iya faruwa. Ki sauqo ku fahimci juna, sannan banda wannan banzan dabi'ar taki na rufe daki. Kun dawo cikin jama'a ne yanzu. Ki bashi girman sa sosai. Mutumin nan is in line for the next ruler of that Emirate Binta, yanda kike mu'amalantarsa kwata kwata bai dace ba. A Gidan mulki respect yana zuwa fiye da komai, kin taso cikinsa amma sai in kasa gane ta inda halinki ya banbanta" shiru Momma tayi tareda dago kai ta kalli kofar ta data rufe tun jiyan, sai Aina'un ta cigaba da magana "I'll call you in muka isa" tace "Toh Adda Allah ya kaiku lafiya" ta amsa da Amin sukayi sallama.

Saida Momma ta ajiye wayan kuma taji abubuwan na dawo mata da daddaya, maganganun da Papan ya fada mata suna amsa kuwwa a kanta da daddaya, ta duqar da kanta tareda dafawa da hannunta duka biyu. Tananan zaune aka kwankwasa kofan nata, shiru tayi da farko sai taji Laure tace "Ranki shi dade kiyi hakuri ki bude" sai kuma kukan Khadija ya karade dakin, da dan hanzari Momma ta yaye duvet dinta ta sauqa daga gadon ta nufi crib din da Khadijan ke kwance, a hankali ta dauke ta sannan ta nufi kofan ta bude. Da Jidda ta fara cin karo an shiryata cikin blouse dinta na yara me kyau a jikinta tana tsaye a bakin kofa ta fara kuka itama. sai ta miqa mata spare hannunta alamun ta iso gareta, da sauri yarinyar ta taho gurinta, sai ta nufi makeken gadonta hannuwanta riqe dasu. Zaman ta bakin gadon sai da ta fara feeding Khadijan sannan ta riqo Jiddan a jikinta tanajin sonsu na shiga lungu da saqon zuciyarta. Sun fi minti biyar a haka sannan Laure tayi sallama. Momman ta dago kai tareda bata izinin shigowa, nan ta shigo ta gaisheta cikin girmamawa, ta gyada mata kai tana maida hankalinta kan Khadija, fita Laure tayi bata dade ba ta kawo mata breakfast dinta in different dishes har kala uku, ta jera mata su a kan ottoman din dake tsakiyan babban dakin sannan ta sake fita. Batafi 30 minutes da fita ba su Imam suka shigo dakin suma, kasancewar weekend suna gida ranar. Ganinsu yasa Momma ta musu murmushi tace "My boys, kun tashi kuma?" dan ta quduri niyyan bazata sake fushi da 'ya'yanta ba akan wani dalilin bacin ran da mahaifinsu zai saka mata. Ganin fara'arta yasa su Imran suka iso wajenta da murmushi suna gaisheta, tana kallonsu ta amsa sai ta kai hannu ta shafa kan kowannensu aranta tana karanto musu addu'a. Ita sai yanzu take ganin kuskurenta na dora fushinta ga 'ya'yanta, to me sukayi su?. Hira suka fara mata Imran harda kwanciya da miqewa a gadonta duk tana kallonsu. Tana gama feeding Khadijan sai Imam ya miqo hannu zai karbeta, a nutse ta dago ta daga jikinta tace "Oya! go to your big brother" tana murmushi ta miqa masa ita ya riqeta yana kallonta, bayan shudewan sakanni kuma ahankali tace "Imam" sai ya dago kai yana kallonta, sannan ta kalli Imran ta kira sunansa shima, sai duk suka bata hankalinsu suna saurarenta, tace "These are your sisters, kunji? Bakuda wasu qannen sai su biyun nan, Inason ko me zakuyi ku jasu a jiki kunji" Imran ne ya fara amsawa da "Toh" while Imam yayi shiru yana kallon uwar tasu, sai ta cigaba da maganan "Duk inda za'a je a dawo bakuda kamar qannenku biyun nan, ku hada kanku kunji" Kafin su amsa Papa yayi sallama a bakin kofan, Jidda ta tafi da gudunta tana kiran sunansa. A nutse ya shigo dakin yana kallonsu da murmushi a fuskarsa, saida ya zauna a dayan bangaren gadon sannan Momman ta gaishesa, ya amsa yana kallonta sai kuma ya miqa hannunsa gurin Imam ya basa Khadija. Sai da Papa ya jira yaran suka fita ya miqe tareda dawowa kusa da Momma har sannan hannunsa riqe da Khadijahn, a nutse yace "Meyasa kike son rufemin kofa ne Fatima?, banason sabuwar dabi'ar nan taki" bata kallesa ba tace "Ai na bude, yanzu ma ai ba a kulle ka samota ba" sai ya kawar da zancen da fadin "Inason zuwa Abuja gobe, and maybe it'll take me one week or so" rass Momma taji zuciyarta ta tsinke tuna yanzu yanada wata a waje da har maganar aure ta fara shiga tsakaninsu, sai ta dago ta kallesa tace "Ka bani yarinyar a qarqashin kulawata zan riqeta" dan stiff yayi yana kallonta, ta sake cewa "Naji zan riqeta a gurina, sai mu bar zancen auren naka" nan ma bai amsa ba ya dauke kansa, ganin haka tace "Dama akanta zaka qaro min abokiyar zaman kuma yanzu na yarda zan riqetan. Shikenan ai ko?" sai sannan ya dan dubeta yace "A'a... Kiyi hakuri jiyan ma nayi kuskure wajen yin maganar cikin bacin rai, amma tun asali inada niyyan qarin auren ko ba dan zuwan Fadwa ba. I'm sorry i made you think it's because of her" ya juyo gaba daya, ahankali ya nusar da murya "I'm sorry Fatima" cikin bacin rai Momman tace "Wallahi saboda ita ne, ai babu abunda zaka fadamin in yarda dakai yanzu Abdulaziz" sai ya juya ya kwantar da Khadija da tayi bacci akan gadon sannan yace "In Allah ya kaimu gobe zan tafi, akwai abunda kukeda buqata?" muryarta na rawa tace "Gurinta zakaje ko, baka dade da dawowa ba amma har zaka koma, in ba gurin ta ba Ina zakaje?" cikin gajiyawa yace "Gurin aiki na zanje Fatima, I'm the leader in this family co-operation, and basically! They need me there everytime to analyze most of the work. Sannan ita wadda kike fadin zanje gurinta ba'a Abuja take ba, A Maiduguri take. Ina Abuja Ina Maiduguri?. Sannan wannan magana taje gaban iyayena, sun kuma bani ammana akan hakan. Yanzu maganarki kike so in bi kenan ko me?" Kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, nan ya hau lallabinta amma bata fasa ba, daga qarshe tace "Dan Allah ka fita, banason ganinka. Kaje can ka qaro mata dubu ma Abdulaziz, ka auri duk matan duniyar nan sai ka gutsittsira Yar tsintuwar taka ka raba musu kowa ta riqe nata sashen". Da bacin rai Papa ya bar dakin a wannan karon ma.


Paid book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya 08134692758




From the writer of KUNCIN ZUCI...And now



MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa


Chapter 12

Last Free Page

Bayan tafiyar Papa da kwana biyu, Maimuna ta kira Momma. "Anti Binta kiyi hakuri, alamarin dai beyi dadi ba. Yarinyar kamar wanda aka jefemu da ita, daga wannan sai wannan" Momma tace "Ni dai haka kuma za'a ganni a barni, ana zaton mutuwa zanyi dan ya fara neman wani auren kome?" Maimuna tace "Kai Anti Binta, ni ai kinsan duk abunda ya shafeki kamar ni ya shafa. Muma ba dadin wannan lamari mukeji ba. Kuma naji zafin wannan maganar auren nima. Amma kuma kema kinyi sanyi sosai akai Anti" tace "Kamar ya nayi sanyi akai" Maimuna ta danyi qasa da murya "Yar sarkin Borno fa yake nema yanzu haka, shekaran jiya ma Baban Sajida ya fadamin suna shirin zuwa da manya neman auren, Mai martaba yayi reaching out to Masarautar, kuma ga dukkan alamu ana daf da shirin basa auren" Wani irin buguwa zuciyar Momma tayi, 'Yar sarkin borno' bama common mace za'a kawo mata cikin gidan ba, Yar wata Masarautar me qarfi. Gumi ne ya yanko mata batasan lokacin da ta miqe daga zaunen da take akan kujera ba, tace "Yaushe za suje?" Maimuna tace "kamar dai yace cikin satin da zamu shigan nan dan basaso adau lokaci. Anti ki fitar da yarinyar nan daga gidanki, zamanta ba alkhairi bane kwata kwata. Tun ba'a je ko Ina ba kinga abunda ta fara jawowa, wallahi ni kwata kwata ma banason yarinyar nima" jikin Momma na rawa tace "Bari zan kiraki Maman Sajida" da haka ta kashe wayan. Kira ta dannawa Madina har ya katse bata dauka ba, ta sake bugawa a na biyun ta dauka tareda sallama, Momma bata ma tsaya amsa sallaman ba tace "Madina kishiya za'a min dai saboda yar tsintuwarcan" ta qarasa maganan muryarta na rawa, Sai Madina tace "Hasbunallahu, Adda kishiya akanta kuma. Toh saboda me?" tace "Saboda zai kawo mai kula masa da yarsa da kyau. Madina wai ni yau Abdulaziz yake nunawa duniya wata tsintacciya ta fini a gurinsa, wai ni ya tozarta saboda yarinyar da shima kansa baisan asalinta ba. Shikenan yanzu kam sai maqiyana su zuba ruwa a qasa su sha son ransu dan dadi" Madina tace "Wallahi tallahi bazata sabu ba, Yar Ina ce?" cikin rawar murya Momma tace "Yar Shettiman Borno" sai da Madina tayi shiru na wasu daqiqu tukunna, can tace "Me Adda Aina'u tace? Kin fada mata?" Tace "Na fada mata tace in karbi kaddarata, inyi hakuri" a zafafe Madina tace "Shi hakurin mun bi kansa mun taka da kafarmu. Wallahi baza kiyi hakuri ba Adda, bazata sabu ba, bamuga ta zama ba. Yar sarkin Borno fa!" "Kuma fa ki tuna wannan karon choice dinsa ce, shi ya ganta yake son aurenta, in baki manta ba zan tuna miki Adda. Auren hadi aka muku da juna" Kukan da Momma take riqewan ne ya kubuce mata, tana yinsa tace "Amma Abdulaziz yana Sona" Madina tace "Nasan hakan Adda, amma dole ki tashi tsaye wannan karon, dan yana sonki ai ba zama zakiyi ki tankwashe kafarki ba, ni mijina na biyun nan da zan aura Kinsan fafutukar da nayi akansa ne?" Momma ta danyi shiru tana digesting maganar na dan wasu sakanni sannan tace "Madina bazan je gurin malami ba, Wallahi akan tatsitsiyar yarinyar nan bazan je gurin malami b..." Madina ta katseta  "Ai ita wannan zan baki shawaran yanda zakiyi da ita, ita ai qaramar alhaki ce. Akan wadda za'a kawo miki zaki dau mataki. Mutanen Maiduguri yawancin su basa zama hakanan Adda, wasunsu guma guman 'yan bin malamai ne, ba ga qawayena nan muna ta fafutukar tare ba. In baki sani ba wanda yamin aiki akan mijin nan nawa har can Maidugurin na bisa ya gama min komai, Wallahi ba'a zama hakanan Adda. Itama da shirinta zata shigo miki kinaji kina gani kin zama 'yar kallo a wajen Babban jidda" cikin firgici Momma tace "Na shiga uku na ni Fatima!! Madina nidai ko jifana akayi da yarinyar nan ne? Kamar wadda tazo ganin bayana. Daga wannan sai wannan duk a dalilin 'yar tsintuwaaa" Madina tace "Toh kin ma san yadda zakiyi a samu maslaha....kawai ki hallaka yarinyar sai muga ta inda za'a bullo da auren, ai me renon ta za'a auro miki ko? To ki kashe ta kowa ma ya huta Adda" Dif Momma tayi shiru tukunna, maganar na samun waje a kwakwalwarta, Madina ta sake cewa "Kiyi tunani ki gani Adda, wallahi in ba haka ba kin rinqa qunsan bakin ciki ta dalilinta, ai wasu haka Allah yayisu, da ibtila'i suke yawo a jikinsu, wannan mafari ma kenan tun tana wata biyu a duniya, Ina ga ta girma?" sai sannan Momma tayi magana cikin wani irin sanyin jiki "Kina ga hakan ne mafita Madina?" da sauri ta amsa da "Tabbas. Adda ki dau mataki yanzu kafin gaba kizo kina danasani" "Zaman yarinyar nan a gidanku ba alheri acikinsa. Uwarta ma ta jefar da ita ko ta mutu ko tayi rai balle ke. Masifa ce mai zaman kanta inkin ga hakan" har sannan Momma jikinta bai dawo daidai ba, sai kawai tace "Bari zanyi shawara, zan kiraki zuwa gobe" tace "Toh Adda. In kuma bazaki iya ba ai kinada amintacciyar hadimarki. In bakyayi da Habiba yanzu ai akwai Laure, wannan idonta a bude suke zata iyayin komai dan kudi" Momma ta sake cewa "Zan dai kirakin" da haka sukayi sallama ta kashe wayan cikin sanyin jiki. Tunani ta fada wanda batasan lokacin da Lauren ta shigo falonta na biyun tana sanar da ita tayi baqi a falon farko ba, firgit ta dago kai tana kallon Lauren, sai ta sake cewa "Kinyi baqi ranki shi dade suna Babban Falo" ta gyada kai kawai batace komai ba.

Da wannan maganar Momma ta kwana arai tana tishi akan tishi. Ita dai tasan batason yarinyar ko na misqala zarratan, amma kuma anya kisan beyi tsauri ba kuwa. What if Abdulaziz ya gane, what if asirinta ya tonu kowa ya gane ita ta kashe yarinyar? tasan Abdulaziz bazai taba yafe mata ba. Toh amma inta bar yarinyar tun yanzu ga abunda ta jawo mata, then what if nan da wasu shekaru in ta girma, wani irin masifa zata rinqa janyo mata? What if Abdulaziz ya fifitata akan su Jidda da Khadija, kai har dasu Imam ma. Inaaaa abunda bazata taba zuba ido ta gani ba kenan, 'ya'yanta sune gaba akan komai a gidan nan, 'yan asali, tsatson mulki gaba da baya. Da wannan shedan ya kanainaye zuciyar Momma a wannan daren. Takai ta kawo ma babu abunda take hasaso wa sai jana'izar Fadwa da za'a yi nan da kwanaki qalilan.

Washegari haka ta tashi da wannan tunanin. Da wata Hadimarta mai suna Yalli ta zo yi mata hidima sai tace "Kice da Laure Ina buqatar ganinta" ta amsa da "Toh ranki shi dade" da haka ta miqe daga tsugunnen da take sannan ta fice.
Bata dade da fita ba Laure ta shigo falon, bayan ta gaisheta cikin girmamawa sai Momman ta miqe ta nufi dakinta tareda fadin "Biyoni". A kan resting sofan dakinta ta zauna sannan ta umurci Lauren da ta rufe kofa, da hanzarinta tayi abunda aka sata sannan ta zauna a qasan carpet tana sunkuyar da kai. Saida Momma ta nausa sannan cikin nutsuwa tace "Magana nakeson muyi, amma Inason ya kasance daga ni sai ke, kuma har duniya ta nade banason jin na ukun mu a cikin wannan maganar" cikin hanzari Laure tace "Allah ya qara miki girma, wane ni...har in mutu baza kiji ba, wannan alqawarine" Momma ta gyada kai cikin amincewa, dan ba tun yau suke tare da Laure ba, ta mata sani tun da kuma tana ji ajikinta bazata bata matsala ba, sai taji Lauren tace "Amma kafin nan ranki shi dade Inason ki amincemin in leqo ko Ina, dan tabbatar da babu na ukun a boye" tace "Na amince" nan Laure ta miqe tareda leqa manyan windunan dake dakin ta tabbatar babu alamu kowa a gurin sannan ta jasu ta rufe gaba daya, da haka ta dawo ta zauna tana maida dukkan hankalinta kan uwar dakin nasu. Saida ta Jira Momma tace mata akan Fadwa ne batun sannan tace "Ranki shi dade. Nidai tun dawowar ku na qissima abubuwa dayawa game da yarinyar nan. Shegu irin su ba sa kawo alkhairi a duk gidan da suka shiga daman" Momma ta gyada kai cikin gamsuwa tace "Inason mu hada kai wajen kai qarshen yarinyar kowa ya huta, ko nawa kikeso zan biyaki in har aikin ya tafi daidai" cikin  gamsuwa Laure tace "Ko baki biyani ba zan iya miki wannan aikin, kuma hakan shine daidai ranki shi dade. Ai qaramar alhakice, ba wahala zeyi ba. Ta hakan ne hankalin mai girma Yarima zai dawo jikinsa. Yara irinsu ba abun riqo bane. Hakan da zamuyi taimako ne" Mamma ta sake gyada kai tace "Kije sai na nemeki, kuma kinji dai abunda na fada miki ko? Kar na uku ya shigo cikin maganar nan dan ke zan sako a gaba" da sauri tace "Nayi rantsuwa kuma nayi alkawari ranki shi dade, babu mai ji har tashin qiyama" da wannan ta fice daga dakin tabar Momma a zaune tana qissima abubuwa a rai.

Washegari Momma taje sashen Uwah dan gaisheta kamar yadda ta saba. Laure na riqe da Khadijah tana biye da ita a baya suka yi sallama a babban falon. Basu samu kowa anan ba sai suka zauna zaman jiran fitowarta. Hadimarta laraba ce ta isa ciki dan sanar da ita isowarsu, Jim kadan Uwah ta fito daga dayan falon nata tare da wasu mata guda biyu wanda daga gani mutum zai shaida 'yan'uwanta ne. A ladabce Momma ta gaisheta tana sunkuyar da kai, ta amsa a tsanake kamar ko da yaushe. Saida Momma ta gaisa da sauran matan sannan daya daga cikin su tace da Laure ta miqo musu Khadija su ganta. Suna riqe da itan sai Uwah ta miqa hannu zata karbeta su Momma suka jiyo kukan jinjira daga can falon da

Please Login or Register in order to submit comment