You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi damar cigaba da shirin auren shi
cikin nutsuwa da aminci, bai ma kara bi takanta
ba.
************************
Ana saura k'wana d'aya aure har gida Momy tazo
ta chake shi harda kukanta kan wai ya mayarta
mahaukaciya, ita kad'ai take kid'anta a auren.
Tuni yai shiru, Fure dake kitchen d'akko ruwa
tana jin yana fad'in "nifa Momy kar a kaini bango
nai ba d'ai d'ai ba, dan wallahi bazan auri
Rukayya b... Mari ta sauke mishi, tuni Fure da
akai akan idonta tasau "tambulan" din lemon ya
fashe tana k'allon Momy.
Haka ta taka ta durkushe gaban Momyn da
g'wiwa biyu wacce ke kukan dan ba ita wai ta
haife shi ba, amma ai wai ita taci kashinshi har
ya zama mutum
"dan Allah Momy kiyi hakuri, dole zai bi umarnin
ki, zai auri Rukayya, dole ne wannan.
Tun fitar Momy ya kasa ko mot'si daga inda
yake, cikin d'auriya Furen ta fara lallashin shi da
kalamai masu sanyaya rai, kan Momy kam Mama
ce, dole yabi umarninta, kodan ta fita zargin ba
sa hannunta a kin aurenshi ba, dan Allah, kuma
domin ta... Har kuka tai mishi, shi d'ai kala bai
ce ba.
A t'saye yake gaban madubi kamar kullum tana
shirya shi, sai d'ai yau shirin na daban ne, dan
wai shirin d'aurin auren kishiyarta take mishi.
D'uk inda tai K'allonta yake, sam tun jiya har yau
baida walwala, sai yaga ma kamar shi kad'ai
yake kin auren, dan har wani wasa ta d'au abun.
Turare take fesa mishi, kamar kullum taja baya
tana yaba mishi k'yaun da yayi, sai d'ai wannan
karan ci kanki bai ce mata ba, d'uk yadda tai
haka yake binta da ido.
Muryar y'an gidan Angwayen ne a parlour kan
wai sunzo tafiya dashi.
Takalmin shi sabo da jiya tasa Muh'd ya siyo
mata "half cover" takai gaban shi zata sa mishi,
cikin zafin nama ya dagota cikin masifa, cikin
t'sawa yace "Mey kika d'au abin ne? Wasa?
K'arfa ki mayarni yaro... Gaba d'aya ya burkice
mata.
Murmushi ta k'ak'alo na dole, tare da d'an zame
hannunshi tana fad'in, "relax", sai ta sa hannu
kan maballin wuyar rigarshi, har yanzun yana
mat'se da ita, "yau fa ba ranar fad'a bane Dear,
muje ana jiran ka a parlour.
Hankad'a ta yai kan gado,cikin fusata ya bud'e
kofar ya doko mata ita.
Da sauri ta tashi tasa sakata.
Tuni ta zame kasa ta cire d'aurin dank'walin data
sha, ihu zata kurma ta tuno basui nisa ba.
"Wayyo! Shi kad'ai ta iya furtawa,kan tai ko'k'arin
tashi, tuni ta fara ganin jiri,ba shiri ta koma ta
zauna, sosai tai k'arfin halin kin nuna damuwar
ta gaban Ahmad, da rarrafe ta hau gado, tuni
wani irin kuka mai matukar daci yazo mata...
"Shikenan ita, ta faru ta kare mata.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 2:47 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 37_Batta da mai
lallashinta kusa,saboda haka sai da tai mai isarta
tukun ta samu nutsuwa. A hankali ta daga kanta
zuwa ga agogon dake manne a d'akin na hutansu
suna k'allon juna. Sai tai lamo tare da kura ma
agogon ido,(10:50am), tasan d'uk inda suke
yanzu an d'aura na Maryam da Muh'd k'arfe
goma, kenan saura minti goma a d'aura na
mijinta? A hankali ta yunkura ta tashi,sai ta
furzar da iskar bak'inta ta k'ada kai, kaya ta hau
cire wa, d'uk k'walliyar ta goge da kuka. Bandaki
taje,cikin sauri tai wanka ta fito ta hau shiri,
sosai tai k'walliya kamar ma ita ce amaryar, sai
ta bud'e "wardrobe" d'inta cikin kayan da ta
tanada a fitar bikin ta hau zabi. Akan wata
dakakkiyar shadda ta t'saya fara ce,tasha zubi
da zare "Orange" da "blue" "gown". D'inkin yasha
"stones work" mai k'yau da t'sada, Kai ta kama
tattare achan kasan keyarta kan ta kamashi da
"ribbon" ya had'u waje d'aya a bayanta. Cikin
nutsuwa ta zira rigar kan ta t'saya gaban madubi
rike da dank'wali, ta baya ta d'auroshi, yadda
gashin zai shiga ya fito ta t'sakiyar d'aurin. Nan
da nan komai ya ji, sarka da "bangles'' had'e da
zobuna sun hau. Turare ta fara feshi, had'e da
murmushi lokacin da ta k'alli kanta a madubi.
K'warai ance in kana da k'yau, wai ka kara da
wanka, ita d'ai Pretty tanaji da d'an k'yaun nan
nata wajen kara k'wask'wareshi ta dawo mai
k'yau. D'akin ta g'yara kan ta fito parlour ta
kunna "burner", dirin mota taji, a hankali taji
gabanta ya fara fad'uwa, kila har an d'aura an
dawo... Da k'yar ta iya seta kanta ta had'iye
kukanta. Har tai hanyar d'aki taji Fatee na
k'wada sallama. Da fara'a ta juyo tana amsa
mata. Baki Fateen ta rike, "inye, ka ga uwar gida
a gidan AAA.. Kingan ki kuwa? Fuska ta K'awar
tana murmushin k'arfin hali. Fatee ta karaso
dak'yar tana tura ciki. "Allah ya kawo AAA
yanzun, na tabbatar za kisha k'arin angwanci,
kai! Ke ko a jikin ki koh? K'allon Fateen take,
tamkar ta sau kukan bak'in ciki haka take ji, wai
ko a jikinta? "Ki bari ka'r na huce tawa haukar
akanki da cikin ki.. Dariya kawai ta hau mata
tamkar taga shasha, kawai sai ta zuba mata ido,
ji take kamar ta rufeta da duka. Sai ta juya kanta
chan gefe kuka na shirin zubo mata, "wato ke da
zaki taushi zuciyata, ke kike min dariya ma...
Cikin dariyar keta Fateen tace "no,sorry, sorry,...
Sai d'ai fa taki t'sagaita dariyar, harda k'walla,
Fure na shirin fashewa da kuka ta t'sinkayi Fatee
na fad'in "Angon Furera... Da sauri ta rint'se ido,
gabanta ya cigaba da d'ukan tara-tara. Sai da ta
tabbatar ta had'iye kukanta tukun ta juyo had'e
da k'ak'alo musu murmushin dole. Shi da Salman
ne, sai d'ai kamar su ma dariyar suke,gogan na
ganin ta juyo ya g'imtse fuska, kawai sai taji
wani rauni yazo mata. Tun yanzu har ya fara
washe baki ni kuma yana had'en rai? K'wafa tai
a ranta, da gaske ne kam Namiji ba d'an goyo
bane ba. Ji fa yadda ya bar gida yana cin magani
amma daga d'aura aure har ya ware,ita kad'ai ya
dake wa. "Sannun ku da dawo wa, murmushi
Salman yai, kan yace "kinga taso mu tafi kan
wannan ''nuclear bom'' d'in ya tashi damu Batool.
Harara ta dan sau musu kan ta d'auke kai, sai
dai ko ita taga bala'in d'auriyar ta. Tashi Fateen
tai tana dafa cinyoyin ta, har yanzun dariya take
a ciki ciki, "toh K'awa, sai munzo d'anna kirji
anjima. Yake tai mata, suna dariya suka fuce ita
da mijin. Fure fa ta cika tai bamm! Kiris take jira
ta fashe da kuka. Kan maigidan ta dawo, kawai
sai taga yai d'aki ya barta, sam ba fara'a a
fuskarshi. Kai ta k'ada, sai ga nan wasu hawaye
masu d'umi sun zubo. "Wato ni AA zai manna
ma? Dak'yar ta iya tashi tai d'akin cikin goge
fuska, tana k'allon kiran Aisha da Adama taki
d'auka, gani take yau kowa ya t'saneta, sai d'ai
kana k'allonta kasan tai kuka. Jingina tai a jikin
kofar tana k'allon yadda ya t'saya a gaban
madubi yana kunce "link" d'in hannunshi. K'allo
d'aya ya mata ya d'auke kai zuwa ga abinda ya
ke, d'uk sai ta kara jin ta samu karaya. D'uk ta
marairaice fuska. Karasa wa tai gun da yake kai
a kasa taki duban shi, d'ayan hannun ta ruko
tana tayashi cire wa,ido ya zuba ma fuskarta
yana dan kunshe dariya ganin yadda ta
marairaice. Jin burbushin kunshe dariya yasa ta
d'an dago tana k'allon shi, suna had'a ido ya
kasa jurewa,dariya yake irin ta ketar nan, kawai
sai taga an ma mayarta mahaukaciya, cikin fushi
ta y'ar6ar da hannun da ta rike ta ta turo baki
tana shirin sakar kuka. Maimakon ya t'sagaita
dariyar tashi kawai sai nunata da hannu harda
rike ciki, tuni k'wa sai kuka ya k'wace mata, bai
nufa ba kawai ya ji tana k'wada mishi pillow ta
ko'ina ko zata huce takaicinta. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.co
9/29/16, 2:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 38_Karewa yake,yana
mai cigaba da dariyar, ganin ba gajiya zatai ba
yasa ya fara ko'k'arin kar6ewa ya rukota, tun
tana tirjewa har tai lumm yana jijjiga ta tare
fad'in sorry,sorry. Dak'yar ya samu tai shiru sai
ajiyar zuciya take. Kanta ya dago, sai ta rint'se
ido d'uk k'walliya ta baci, sai ya sa hannu yana
goge mata hawayen sannan ya cigaba da jijjigata
da mata kirarin da ke sa ta nutsuwa. Luff,kake
ji,ba ko shesshekar, sai yai murmushi, shi kad'ai
yasan lagon Prettyn shi. "Pretty"... Ido rufe ta
dan mot'sa, sai yai murmushi, "you know.. "My
destiny is taking me where my love is. "Kin riga
da kin tare ko'ina nawa Furii..har ma ban iya
k'allon wasu mata a mat'sayin sun isa balle su
kamoki,cos I can see only one thing..hear one
thing..and think about one thing... That you
pretty.. Ido ta bud'e, sai ga nan hawaye ya
zubo,k'allon cikin idon shin take,so take ta gano
akasin zancen shin,amma ta kasa.. Ko haka ya
barta tasan yai mata lallashi da son shi, sai d'ai
kan ta farga taji dan hayaniya a kusan k'unnenta,
kamar kuma na d'aurin aure a waya yai
"recording". Sai ta mat'se ido,dan jin maroki na
fad'in sadaki kamin yace "na auren Rukayya da
Nasir.... Da azama ta bud'e ido tana k'allon shi,
gira ya daga mata yana murmushi.. Da sauri ta
karbi wayan ta kara taro wa, abu d'aya ta kara ji,
sai ta k'alloshi wai kuma ta hau kukan dad'i.
******"""" MU D'ANNA BAYa.. Tun bayan fitar
AAA da ang'waye dan halartar d'aurin aure suka
sauka gida inda za'a taru a tafi nasu Muh'd. Gida
ya shiga,"direct" yai d'akin Mama, ganan y'an
biki wasu a "parlour", su Ummi yaga,ya tambaye
ta Mama, sai tace tana bangaren Abba, sam
itama haushin za ai ma y'ar d'akinta kishiya take.
Da sallama ya t'saya bak'in kofa, daga ciki Abba
ya bashi izinin shiga, suna a parlour Mama na
had'a mishi "tea" d'uk yai wani iri, ji yake sam
bai zatan samu nasara ba. Bayan ya gaida su yai
shiru, Abba ya K'allonshi, "Har kun iso? Kai ya
k'ada, kan ya dago kai, da sauri Abba ya ajiye
kofin shayin, "Subhanallah, Abba na, kuka fa? Ido
Mama ta zuba mishi, kawai sai ya goge yana
kara zubo da wasu, tashi Abban yai, dan a duniya
ya t'sani ganin ran kowa ya baci a yaran shi bare
Ahmad t'dokarshi. "Haba Baba na.. Maza da
kuka? Fad'an wa ya ta6a min kai? Mama ya
k'alla, da mamaki itama take K'allonshi, kawai
sai yace shi baison auren nan, sam baison
Rukayya... "Abba yaushe akai auren namu da har
za'a kosa na kara aure dan bata haihu ba, nan
yai ta mishi, kan tana chan wai ya barta sai bori
take ta rufe kanta a d'aki tana kuka. T'sam
Abban yayi, sai yace Mama ta miko mishi
wayarshi. Momy ya kira, cikin k'ank'anin lokaci
tazo. Ganin Ahmad durkushe yasa tasan da wata
a kasa. Waje ta samu ta zauna, sai Abba ya
sanarta abinda Ahmad yace, tuni ta hau 90, kan
aure ba fashi, wallahi tunda har yau d'aurin aure,
yau ya nuna mata bata isa ba, yau harda Mama
ta balbale, tuni ta bawa Abban haushi, "t'saya kiji
Maryam, ki cire son rai, yaron nan kar mui mishi
dole, in aure yake bida zai ne in lokaci yayi, sam
ban zata ba had'in zumunci kike son kulawa ba,
kiyi hakuri, suma zasu haihu ne, amma a bar
auren nan... Kuka Momy ta sau, yau wai an nuna
mata karshenta, sannan an nuna mata ba ita ta
haifi Ahmad ba.. Shidai gogan yai kasa da kai,
fatan shi komai ta fanjama fanjam, yai lallashi
daga baya. "Momyn su kiyi hakuri, sam abin bai
ba, ranar aure kace ka fasa... ''Rufan baki, ai da
saninki a haka, kuma dad'inta na haifa, aure yau
za'a d'aura da d'aya a wanda na isa... Sallamar
Alhaji Nasir ce ta kat'se ta, "lafiya kuwa Abba?
Hayaniya har t'sakar gida fa... "Yauwa Nasir,
shigo, cewar Momy,shi d'ai Abba da ido kawai
yake binta, "Momy kuka? Mey toh yai zafi haka?
"Komai nace kawai kace toh Nasir,, hawaye ta
goge, "ina son ka auri Rukayya, ka fanshen bak'in
cikin da ake son dasa min akan Ahmad.. Da
mamaki ya k'allo su Abba, suma shi suke k'allo,
"haba Momy, aure fa? Ni? Kai za... "Ban san
musu Nasir,in dai ba kana son ku hallakani bane..
Kawai sai Momy ta hau haki.. Asma ta mot'sa,
da sauri suka rukota, Nasir dama ya sani yake
bai shigo ba t'saut'sayi ya fad'a masa.. Haka
yanaji yana gani ya yarda dan Momy na fad'in in
wai bai yarda ba wallahi zata mutu...Lol Ko su
Rukayya basu san zance ba sai da aka d'auro
suka ji, dan chan gidan su akaje. Bori ta hau
yiwa Momy kan ya za'a ta mata haka? Tana
k'wance asmar ta d'an saketa take bata hakuri.
Fur Rukayya tace batasan wannan ba, mey zatai
da tsoho, dan farin gidan, tuni ta tattare tai gidan
su tana kuka. ********************** Da sauri
Fure ta ruk'unk'umo abinta tana kukan murna, sai
kara kakank'ameshi take har tana shirin fad'arsu
kasa sai sukai kan mai laushi. Karan nan bai
hanata ba, dan yasan na murna ne, sai ma yahau
tsokanarta da fad'in, "haba uwar gida, yau fa ba
ranar kuka bace... Dariya ta hau yi kuma kuka
kuka. Sai ya zame dank'walin tare da mirgina ta
kasa suka zuba ma juna ido, mey zata ce da
abun nan? Lalle Allah bai had'a maka zafi biyu,
gashi an so a muzguna mata Allah bai yarda ba,
sai ta hau matso hawaye. Kanshi ya d'aura a
kafad'arta yana goge hawayen, sai ta hau kuma
sunne kai cikin kunya. "Sosai bayan na fita zuwa
kawai zanyi na auri Rukayya tunda naga ni kad'ai
nake k'ida na, sai d'ai ina fita na t'saya a bak'in
kofa, ina ji kika sa key kika zube, wai kuma harda
kuka, kinyi dauriya fa, ko irin y'ar haukar k'aryar
nan da mata suke ke baki ba.. Hakan ya nunan
ta ciki yana cinki, kawai sai nai jahadi na tunkari
yakin dake a gaba na... Kat'se shi tai ta hanyar
d'aura "lips" nata cikin magand'ar sa tana jin
kamar da haka zata biya shi. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 30
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 39_Lokaci sosai suka
d'auka, kan a hankali ta fara ko'k'arin zame
kanta ido rufe,shima nashi haka, "thanks" shine
abinda ta furta, sai ya ware ido cikin nata, lalle
yau ya biya ta ba kad'an ba. Tuni kuma ya hau
tsukanarta tana dariya.. A mota suke,yau shi ma
zai kaita gidan bikin, hannunshi d'aya na nata
kawai ta juyo tana ta aika mishi murmushi yana
k'ada kai. Lalle kishi masifa ce, sannan batasan
haka son AAA ya kai ba cikin ranta sai yau da
ake neman a k'ak'aba mishi auren dole. Hannu
yasa yai tagumi yana k'allonta da murmushin
yadda ta zuba mishi na mujiya. Kawai sai taje ta
lafe tana d'an mishi dariyar kauna,t'sam ya
rukota yana sauke ajiyar zuciya. Yau d'aya ya
kara tabbatar da son da Pretty ke mishi. Dak'yar
ta dago tare da d'aukar wayanta, hannu ta daga
mishi, tare da fad'in ''Bye... Sai taji yai shiru yana
k'allonta kawai. Ta kara fad'in "hello", a hankali
yace "I love you.. Kai ta k'ada tana murmushi,
sai ta k'arkata kai da fad'in "I know... Cikin
shag'waba, bak'inshi ya nuno mata, ba gardama
ma ta nashi mai zafin, tare da fad'in "bye" ta suri
jakarta zuwa waje, dan tasan in ta biye mishi a
motar nan zasui ta zama. Zagawa tai ta
bangaren da yake, ta daga mishi hannu, kai ya
leko, "Remember that...Nothing gonna change
my love 4 you... Sai ta k'ada mishi ido tare da
d'aura jaka a kafad'arta.. Tace "really? Kai ya
k'ada, tare da jero Nothing..Nothing... Hannu
tasa a bak'inta tare da d'an wata munafukar
dariya, sai ta manna wa hannunta "long kiss''
Muahhh... ta nuno shi da hannun "love you... Da
farin ciki suka rabe, har sai da ya kule kan ta
k'ada kai ta shiga gidan su Umma. Da gudunta ta
karasa tana kiran su Adda da Aisha. Tuni suka
fara mata barka,reshe ya juye wai da mujiya.
Fatee ce ta kira ta, kan itama gata a hanya
bayan azahar, tana ta mata dariyar keta kan wai
d ansha da ita, ai ta fad'a mata taji a jikinta
auren nan babu shi, itade murmushi take kawai,
amma tasan da k'yar ta t'sallaka rijiya da baya.
Sai dai kuma ta tushe k'unnenta a gun su Momy.
Lafiya aka gama biki, sosai sun ma Maryam
bajinta har ta ninka Fure, kayan kitchen guda
Fure ta d'au nauyi, Ga nan AAA ya ma su Umma
gudunmawar kayan abinci da drinks, dan fur suka
ki k'ar6ar kud'inshi, Abba d'ai ya zama d'an k'allo
da Umma. Aisha Bedsheets, Ya Suleiman kam an
kafu sosai, d'uk kayan parlour shi yai,sosai ya
ka'r mata nera, kamar kullum yau ma kawu ya
d'au nauyin gado, ganin haka yasa ya sai mata
babba mai t'sada da k'yau. Koh y'ar gidan wani
mai kud'in karshenta kenan. Amarci sukaci ba
k'arya a gidan Hassana, yanzun ne Muh'd yasan
yai auren so da tararaya, sai yanzu yasan sirrin
dake cikin auren y'ar masu karamin k'arfi da
suka rena. A gun Momy kuwa, kowa ta d'aina
kula shi dan a ganinta an mata babban
wulakanci. Kullum sai Ahmad yazo gabanta
neman gafara, yau d'ai har da d'an guntun
hawayenshi dak'yar ya shawo kan Momyn. Ta
bangaren Rukky kuwa tuni babanta yace bazata
zauna mishi gida da aure kanta ba, su Momy su
ne iyayen ta,dole haka tanaji aka yayimeta aka
kaita gidan Nasir. Hassana na gida, fur Muh'd
yaki zuwa biko, yace ai ba shi yace ta fita
ba,zata iya dawo a d'uk lokacin da taso, ganin ba
sarki sai Allah yasa ana wata da bikinsu ta
tattaro ta dawo,sai d'ai ganin Maryam a gidan ba
karamin bala'i ta tayar ba, a fafur sai d'ai ya
sauya mata gida. Shikam yace amarya tace had'i
take bida. Komai yi suke a gaban Hassana,haka
zai ta biye wa Maryam suna guje guje a parlour
akan abu kad'an. Hassana sai a ta6e
baki,"mahaukata kawai.. Sam Maryam bata bin ta
kanta, sai d'ai da taga zata shiga gonarta zata
taka mata birki. Sunan Huwaila ake yau, wannan
ce rana tafarko tun bayan auren su Maryam da
Fure suka had'u da Familyn gu d'aya. Murmushi
kawai take, jin ana chakarta kamar kullum,ga
rashin auren Rukayya ya dad'u,tasan batta bak'in
komai. Muryar Hassana tafi ta kowa tashi a
d'akin maijegon. D'ai-d'ai su Maryam da Ummi na
shigowa suka t'sinkayi Hassana na fad'in "bar
mat'siyaci, nima ana chan anga guri ana ta
6arkan hauka, cewar Hassana. Da sauri Maryam
d'in ta karasa d'akin, sai da taje d'ai-d'ai kan
Hassana tukun ta k'alli Fure,"sha kurumin ki
sister, sai tai gefen Hassana da hannunta tukun
tace "dan tuni t'siya ta kare kan t'sohon nan na
gida mai kud'in LUKUD'I ... Wanda da iyalanshi
su ci k'wada K'adangarun BARIKI suci... "Sannan
t'siya ta kare ga uban yana da kud'in, amma in
ya dire buhu masara, daga ranar ba sauyin abinci
har sai ta kare. Sai ta k'allo Hassana, "toh indai
kikazo nan, toh k'wa t'siya ta kare a gun ubale...
A tunzure Hassana ta mike, zatai kanta, da sauri
Maryam d'in taja baya tana k'allon Hassanan
kamar taga kashi, ilahirin d'akin sun zubawa
Maryam ido suna k'allo baki sake, ''ni fa t'siya ta
da y'ar gidana akuyanci, yanzu sai fa kice zakiyi
dambe dani? A kuma cikin taron jama'a.. "Toh
wallahi ki iya bak'inki... Chan ta mat'sa kusa da
Ummi ta zauna, tai banza da Hassana wacce ke
nad'e tabarmar kunya cikin jama'a. Har dariya
Aunty A'i yau tayi, lalle wai "GABA DA GANTA...
Tun zuwanta gidan Maryam d'in ta tarar da
fad'an su da Hassana tasan za'a buga da
Maryam. Yayinda maijego ta ta6e baki, badan ta
kanta take ba yau da ta takawa Maryam burki.
D'uk da tabbas batai ma Hassana sharri ba, dan
fa sai da ta ciwo maganin zama da ita ka'f kan
ta yarda a had'a su zama tare, tai alkawarin d'uk
d'an uban da baiji kunyar taka mata y'ar uwa ba,
toh itama bazata ji kunyar take shi ba. Ita kam
Fure kasa tai da kai tana murmushi, tabbas
tasan wataran KARE na yawo, KURA na yawo
tasan dole za'a a had'u. Batajin da wanda
Maryam zata dagawa K'afa a ka'f Familyn su
Huwaila. Lalle kam,dole ta zama y'ar k'allo, dan
k'wa badai ita ta takawa Maryam burki ba sam.
Fatee ta haihu babyn ta mace, da zumudi ta
gama abinda zata kai mata tai gidan, dan ta ce
an sallame su. "Drama" taje ta tarar, wanda
sosai taci dariya. Fatee na band'aki taji sallamar
y'an gidan su Salman, da sauri ta wat'sa jin sun
shigo d'akin da ake shirya baby. Cike da murna
suka zauna a gama su k'ar6i baby. Da d'aurin
kirji ta fito, nad'e da towel a kanta, d'ai-d'ai za'a
basu Baby da sauri ta karaso ta shiga t'sakani,
"Wa? Ai wallahi na rant'se ba shegen da acikin
ku zai d'au y'ar JUYA.. "Dallah mat'sa min daga
nan, ta warce y'arta ta d'ane gado tana bala'i.
Gaba d'aya sun kasa cewa uffan, Fure da tazo
ganin ikon Allah yasa ta ma kasa sallama, Ashe
da gaske FATEE take da tace ba mai d'aukar
y'arta acikin k'annen Salman sai d'aya? "Ido ko
kunya babu wai kunzo ganin Y'a? Toh g'wara ku
d'au fagon wani gu ku barmin gida, tuni wasu
suka fusata, har sun manta, ana haka y'ar k'anin
Baban su tazo da y'an gidan, jin yadda Fatee ke
ma dangin mijin wankin babban bargo yasa taja
tai shiru, aikwa sai da ta wanke ta tas! Kan d'uk
taji sanyi. Zuciya sukai suka fita suna ta jika y'ar
tasha.. "Eh zan jika...aje d'ai, gaiyar na aiya.
Salman sai da yazo bada hakuri,yana dari dari,
ganin yadda take cika, ba shiri yai shiru. Suna
zuwa suka sanar da Umman su Salman d'in, da
mamakin su sai su ka ga tai dariya. Sosai Fatee
ta burgeta, sai ta k'allo su, "kuna nufin kunji
haushi? Kai suka k'ada mata, sai tai murmushi,
"da zaku san adadin shekarun da na d'auka kan
na haife ku da baku kara kiran wata JUYA wai
dan bata haihu ba, na zuba muku ido ne, dan
nasan dole wataran zaku d'au darasi. Kowa
k'allon kowa yake, su d'ai tun ba yau ba suna
mamakin yadda Umman su ta t'sufa kuma wai
ya Salman ne d'anta na fari. By Feenat Ja'afar.
庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:49 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 40_Rayuwar tana tafiya
ma Fure cikin godiyar Allah, domin a kullum ta
Allah tana matukar samun cigaba a rayuwa. Bata
da tawaya ta ko'ina ta bangaren jin dad'i ko
zamanta da mijintan, sai d'ai har yanzun Allah bai
nufi samun ciki ba, a kullum batta kalmar fad'i
ga Allah da ya fice "ALHAMDULILLAH" domin ya
bata d'ukkan farin cikin rayuwa... Tawaya ta
rashin D'a, bazata tai ma Allah butulci
ba..InshaAlllah, Abadan. Ga wani karin farin cikin
budi da ya same ta,AAAn ta ya bud'e mata
"Restaurant" nata na kanta. Jere suke, anyi
rubutu cikin "bord" d'aya da symbols.. "AAA
pharmacy & stores Ltd. Yayin da nata dake
makotanshi yasa mata "Mr's AAA Restaurants"
tamkar tag'waye abin g'wanin ban sha'awa. Toh
mey zata ce da Allah? Sai Godiya. Ajiyar zuciya
ta sau, lokacin da ta kara g'yara mak'wancinta
tana mai zuba ma AAAn ido wanda ke murza mai
a gaban "mirror" yana mai dan k'allonta. A zahiri
shi take k'allo, amma sam hankalinta yayi kan
dumbin Alkairin mijinta gare ta. A hankali ya tako
zuwa gefenta ya zauna, tai kur'i da ido ba ko
kiftawa. Ido ya zuba mata, ba t'sammani sai ga
nan siririn hawaye ya zubo bisa kuncinta. Hannu
taji a fuska ana goge hawayen, cikin nutsuwa ta
waiwayo da duban ta gare shi, murmushi yai
mata, kan cikin zancen karatun kurma ya tada
kai halamar mey ne ne? Murmushi tai,kan ta
k'ada kai halamar babu, sai ta matso tare da
d'aura kanta kan kafafunshi tana k'allon
fuskarshi,sai ya kai hannu yana mai tattare
gashin da ya bazar mata, sai ta ruko hannun tare
da rint'se su cikin nata tana k'allon shi. D'ayan
hannun takai fuskanshi tare da murmushi tana
shafo ta,shikam murmushi yake mata,cikin
sanyin murya ta hau mishi godiya bisa ga
k'yautatawar shi gare ta.... "Life is really not
worth living without you! You make me feel so
special and complete! I can鈥檛 find words to
utter,but I just want to say 鈥淭hank you and I love
you much more Dear... JazakALLAH. Ajiyar
zuciya ya sau, tare da k'ada cikin da jin dad'in
kalamanta, cikin salon shi dake sata taji tamkar
ita d'in "Queen" ce a "Universe"... Tuni ta sa
mishi ido kawai tana k'allo,ganin d'uk yadda tai
taga tafi AAA iya lafazin a fagen kaunar shi,sai
d'ai ina,tuni ya mata nisa. Dariyar suke,lokacin da
ya bud'e mata''bott" tana d'aukan k'wandon
abinci,sam bazaka ce su ne suka shekara 4 da
aure a tare ba, sun fi kama da irin sab'bin auren
nan dake ji da junan su. Mika mishi d'aya tayi,
kamar kullum ta d'au na Momy. Chan ta fara
yada zango kamar kullum, suna "parlour" ta tarar
Huwaila na kuka tana fad'in ta gama aure.. Suna
jin sallamarta sukai shiru, waje ta samu, sai ga
nan Rukayya ta fito a kitchen da abu a hannu,
kamar kullum cikin girmamawa ta gaida Momy,
sai da ta k'au da kai tukun ta amsa da "lafiya,
kan Aunty Jidda tazo, ita kam harara ma ta sakar
mata, su kam sauran ba wanda ya tanka ta, shiru
kake ji ba mai cewa uffan. Takan rasa a rayuwa
mey ta t'sarewa bayin Allahn nan, sam yadda
suka ki jininta ko Maryam da bata barinsu basu
t'saneta haka ba. "Mtsww.... T'saki Rukkay
taja,kan ta samu gefen Aunty Jidda ta zauna.
"Gaba d'aya anyiwa mutum dabaibayi duk an
hanashi rawar gaban hant'si. Ta karasa tana
y'atsine fuska, murmushi ta mata,kan tai kasa da
kai, Aunty Jidda tace "wai ni ba naji an bud'e
Restaurant da zummar nata ba? Hala tun yanzu
ya fara raba gado tunda ba D'a bare kwai? Baki
Momy ta ta6e, "shi fa ya sani, ni ina ruwana, su
had'u su talautashi ma shi ya sani. Kasa tai da
kai kawai tana jin su, tana jin Rukky ta amshe..
"hmm, matsiyaci kuke ji,ai bai iya samun gu ba,
sam yadda zaki san abin nan da agumau yadda
yaya ke rawar kai akanta, wallahi shi yasa bazan
ta6a harka da mat'siyacin mutum ba, sam.
K'allonta take, sosai nata sai ido, Fure lalle Allah
ya yarfa wa zuciyar ki hakuri, dama Maryam na
gun. Tamkar masu huce haushin mijin Huwaila a
kanta haka kowa ke mata, sai d'ai wai harda
Huwailan a zaginta? Abinda da mamaki, indai har
zata kirata da haka. Ita d'ai murmushi ne kawai a
fuskarta, sai ta janyo "basket" d'in abincin ta
mika gaban Momy tace ta tafi, ba wanda ya
tanka,sai ma t'saki da Rukayya taja mata. Sai da
ta t'saya a gefen "corridorn'' ta goge hawaye kan
ta karasa gun Mama. Anan

Please Login or Register in order to submit comment