You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

izini na ba,
Fateema, ko ta kanshi bata bi ba, burin ta kawai
ta bar gidan, mukullin Fure ta k'ar6a ta bud'e
mota, a baya ta sa jakar, sai gashi ya fito, "Fatee
ki saurare ni pls? Yanayi yana k'allon Fure kamar
mey nufin ta sa baki, ita kam Fateen ma sai ta
fara bata tsoro,don d'uk ta firgice mishi.
Shiga tai da zummar tada motar ya rike kofar
gam, "Fatima pls, kira take "ka cikan murfi mota,
ba kace naje ko'ina ba? Kai ya girgiza, "hakuri,
wallahi da wasa nake.. A tunzure tace "wasa? Da
sauri ya jijjiga kai, "eh, kiyi hakuri.. Wallahi ko na
kira su Abba? Da tai wani kukan kura da k'arfi
taja murfin motar, "Allah baka sa'a.
"Reverse" ta fara yana kiran sunanta, amma ina,
ga unguwa kamar ta mayu ba kowa layin, da
sauri ya shiga dan d'akko waya yasan Abba
kad'ai zai t'sayar mishi da Fatima.
By
Feenat Ja'afar.
庐NWA
9/29/16, 2:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 33_Sosai take kudu
dan ma kar ya cimmasu tai ta k'wane-k'wane,
sai da ta tabbatar da ta mishi nisa kan tai
"parking" achan gefen titi tana k'allon gabanta ba
koh kiftawa, haki take tana jawo numfashi
tamkar da kafa tai gudun. Fure ta k'allo ta "Kiyi
hakuri ki kori shedan sis Fatee... A "stirring"
motar ta d'aura kanta ta sau wani kuka mai
k'arfi, kawai sai Furen ta zuba mata ido dan ko
zata huce ta hakan. Sosai tai tana mai kara
t'sanar halin mutum. Sai da tai mai isarta kan ta
share, a sannan Fure ta fara ce mata komai yai
zafi maganinshi Allah, ta duba halin da take ciki
kar ta jama kanta matsala. Ita d'ai uffan bata ce
ba,sai ma hawaye dake k'waranya. Wayan ta taji
yana kida, a hankali ta sa hannu a jakar ta ciro,
"Abba" ta gani, tuni sai ta seta kanta kan ta
d'auka. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
sannan ya sanar mata kar ta fara dosar inda
suke tunda akan kishiya zata sa6i mijinta. Har ya
kashe in banda kuka ba abin da take, sai ta
share idon, kawai sai ta raya mata tai yola
dangin Ummanta kawai, Fure ta k'alla sai tace
tazo ta tuka. Ba musu sukai musanye, "kaini
tasha.. Kai ta k'ada mata ba musu, sai ta d'aura
kai a gefen kujera tana k'allon gefe hawaye na
t'silalowa. Kai ta daga ta k'alli Fure lokacin da
taji tana "Horn" sai Furen ta d'auke kai. Har suka
shiga gida bata k'allo ta ba. "Tasha nace ki kaini
fa.. Fita Furen tai had'e da bud'e baya ta ciro
kayan Fateen. Kawai sai ta bita taga iya gudun
ruwanta. A parlour ta sauke, a takaice ta karewa
ko'ina k'allo kan ta zauna, sai Furen taje "fridge"
ta d'akko mata sassanya ta tsiyaya a cup tare da
tsayawa a kanta ta bata. D'uk sai kuma ta fara
kunyar Furen,ba musu ta k'ar6a tak'wa shanye
tare da mikawa Fure,kara mata tai kan ta zauna,
tuni sai ta sau ajiyar zuciya. Kai shedan mugune,
nan da nan zai sa ka tafka tsiya zuwa anjima ka
dawo kamar ba kai kai ba. "Koh kud'in mota baki
taho dashi ba,hala zasu kai ki k'yauta? Sai a
sannan ta tuna da ba ko sisi d'uk ta zube mishi
t'siyarshi. Yanzu mui sallah,sai muci abinci,"I
know babyn mu yau ya jigata, dan yau Momyn
shi taji k'arfi... Dariya suka sa Fateen na goge
hawaye. Sallah sukai ta d'akko mata dan
"snacks" ta rage kan ta tafasa musu ko taliya ne.
Zama tai lokacin da take dumama miya tana
murmushi, "Ashe kin iya fad'a haka sis? Kai koni
na tsorata fa, kai ta k'ada. "Mutane ke koya
maka d'uk wani hali da ba naka ba. "Amma
wallahi da gaske na t'sani Salman, ko ganinshi
na t'sani yi, sam namiji bai da tabbas. Kai Furen
ta k'ada, "kiyi hakuri, komai mai wuce wa ne. Ki
zauna anan zuwa gobe AA ya dawo sai ya bamu
shawarar yi.. Da sauri ta k'allota, "namiji ne zai
bamu shawara? Da rashin fahimta Fure ta k'ada
kai, sai ta girgiza kai,"toh a gaskiya bazan zauna
ba, dan maza sun shani tuni na warke... Kiran
Salman ne ya shigo tana ji taki d'auka, dan "ring
tune'' nashi "special" ne. t'saki ta ja ta tashi ta
d'au wayar ta d'anna "reject" kamar ta cire
"buttun" d'in wayar. Ko ajiye ta batai ba ya kara
kira. Kawai sai ta kashe wayar gaba d'aya.
Shikam suna fita ya dawo d'aukar mukulli ya kira
Abban Fateen, suna gamawa sai ga nan kiran
likita, da mamakin shi ya ji yana mishi "congrats"
wai ya zama Baba.. Kamewa yai gu d'aya lokacin
da yace ma likita shi bai fahimta ba ya sanar shi.
Sai ga nan takardar asibitin ya d'auka da ta bari.
Kai ya dafe kai, har da k'wallarshi, wanda bai san
ta meye ba. Abu d'aya ya sani yaso Fatee har
yau d'in nan. Tuni ya bisu ko zai same su, shine
har tasha amma ba Fatee ba kalarta. Dak'yar
Fure ta shawo kanta ta zauna suka k'wana,
kusan k'wanan zaune sukai suna firar duniya, fir
taki ma k'unna waya bare a kira ta. Washegari
Fure da taryar AA ta tashi, sai d'ai Fatee na
tayata tana ta6e baki, dan gaba d'aya maza sun
sane mata t'saf. Ita dai Fure murmushi kawai
take binta da shi. By Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 28
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 34_Sai kusan magriba
AA ya shigo, a gajiye yake, lokacin suna a d'akin
baki ita da Fatee kan lalle ita sai ta tafi, suna
cikin gardamar taji dirin motar shi, sai ta fita tare
da kulle Fatee ta waje, sam bata so ta tafka
kuskure. Kamar ba kowa ta t'ar6e shi da fara'ar
ta, kamar kullum ya kimtsa kan yaci abinci, sai
kawai suka hau soyewar su ta ma manta da
Fatee. A zabure ta mike a cinyar shi a parlourn
tai d'akin baki da gudu, da sauri shima ya mike
yana "lafiya pretty? Tana bud'e ta tana zaune a
gefen gado ta k'wando mata harara. Sai ta kara
rufota kan ta kama hannun AAn sukai d'aki. A
nutse ta sanar shi komai harda hawayenta, sai
kai yake jinjina wa, lalle taga tasku, amma yafi
ganin lefin mijin. Parlour suka dawo ta kara bud'e
Fatee, kamar mey jira sai gata sanye da g'yale
da Jaka a hannu, "dan Allah karki t'sayarni, ki
barni na tafi nagode k'warai... Shiru tai ganin
Ahmad, sai yai mata k'warjini har batasan ta
gaida shi ba, hakuri ya fara bata kan tai hakuri
yanzu magriba tayi, zuwa gobe sai su san abin
yi, ba dan ta so ba ta hakura,kawai sai taga
girman shi. Ita kanta Fure ganin AAn sai taji tana
d'an dari dari dashi, dan kawai d'aurewa take,
amma ace gaba haka ya faru da ita wai... Hmm
sai Allah kawai. Fitowarshi a wanka kenan yaga
ta had'a tagumi, sai ya k'ada kai, tabbas yasan
maganar dazun ce. Yana k'allonta har ya gama
shiryawa ta lula duniyar tunanin dabi'ar maza da
mutanen duniya. Sai ya k'ada kai,a hankali ya
tako ya iso gabanta ya tsuguna. Ajiyar zuciya ta
saukar,kan ta d'an k'ak'alo murmushi, sai ya dafa
cinyarta, "I love you pretty... En banson ki sanya
shakku, ki cire tunanin komai a ranki, AAA naki
ne... bazai ta6a miki haka ba InshaAllah..
Hawaye ne ke ko'k'arin zubo mata, so take ta
gaskata shin gaske AAA nata ne? Sai kawai ta
sau su suka zubo, hannunta ya ruko,har yanzun
yana a tsugune, "Furii believe me, maza ba d'aya
ne ba... Tuni ya hau tsumata da dad'in
baki,Aiya,ita kam ta ziru t'saf, sai yasa hannu ya
sunkuyo da kanta da take murmushi hawaye na
k'waranya yasa ''lips" nashi yana tarar su. A
hankali ya dago ta suna k'allon cikin idon Juna,
tabbas ta aminta AAA na daban ne a sauran
maza, a hankali ta zamo itama tai yadda yayin
suna mai cigaba da karantar juna ta cikin ido, sai
ya tadasu t'saye tare da lafar da kanta a gun
zuciyar shi, a hankali tamkar wata baby yake dan
jujjuyawa kad'an kamar mai rawa,ita kam Fure
anyi luf..cikin nutsuwa ya kara karasa ta da
wakar da indai yai mata take jin a sama. Takanji
wani nishad'i, har ta manta da komai, sam in kaji
yana wakar ka zata shine mawakin, amma kawai
dan Furen shi baitin na "Nothing gonna change
my love 4 you.... Yake burge shi. T'saf acikin
daren ya ware Prettyn shi cikin sauki da lumana,
har ya lalla6ata tai bacci fuskarta d'auke da
murmushin son shi da jin dad'in baitikan, da yaso
yin shiru, sai ya ji tana ya cigaba. Murmushi yai,
Mata sai da lalla6a. Da safe suna kitchen yana
tayata had'a ''break" ta fito da dan gudunta, a
zaton ta ita kad'ai ce a kitchen, hannunta ta cire
a wuyan AAn taiyo gun Fateen da ta juya. "Sis
lafiya? Gaskiya a d'aina gudu da d'an mu.. kawai
sai taji ta ruko hannunta da murna ta d'aura kan
cikinta, "wallahi yau sai mot'si yake, cikin murna
Furen ta kara d'aura d'ayan hannun tana
murmushi, Allah sarki Fatee, fara'a take kamar
mey, shi d'ai Ahmad daga bak'in kofa yana ta
musu murmushi. Sai lokacin Fatee ta kula dashi,
a dan kunya ce ta gaida shi, sai ya amsa yana
ya Baby? Sai tai kasa da kai shi kuma ya shire
"apron" nashi yai waje. Kitchen d'in suka wuce
dan gama aiki, sai g'yada kai Fatee keyi ganin
yadda Fure ta zama "Chief ". Bayan sun gama
cin abinci ya shirya yace Fure ta kira Fateen. Sai
gasu sun fito sanye da Hijab. Sanarta yai ya ji
komai, sannan ta zauna anan zuwa yai ma su
Abban ta magana, ya d'ai lalla6a ta har ta yarda.
Cikin wayo yasa Fure tai mai "copying" numbern
mijin Fateen. Sosai take jin dad'in zama da ita
kamar sun saba a k'wana biyu. Iyanzu kam,ji take
Fure tamkar y'ar uwa ce a gunta. Cikin dabara
Fure tasa ta bud'e waya kan zasui "exchanging"
number. Tana bud'ewa "texts" d'in Salman na
shigowa, d'uk na ban hakuri ne zuwa wai ina
take? Tai mishi rai ta dawo, tabbas itace ma
had'in rayuwar shi, baki ta ta6e, "yau na gama
yarda da dad'in bak'in maza... Ji ni zai rai nawa
hankali? Wai mahad'in rayuwar shi? Fure tai
murmushi, kawai sai tai k'wafa ta hau goge su
tana mita. Ita d'ai Fure dariya take tana tai
hakuri. Shikam yana d'akin Fatee ya tasa "result"
yana k'allo, waya ake mishi kan yau za'a zo jeren
amarya, sai yai jim, "ba yau ba. Kawai sai ya
kashe waya. "Delivery report" ne ya fara shigo
mishi, da halamu kenan Fatee ta bud'e waya. Da
sauri ya fara dailing, da kamar bazata ta d'auka
ba, sai d'ai ta waske, ''ya akai? Cikin magiya ya
fara "Fatee, Fatima,Batool, haba Bintu na, dan
Allah ina kike? Kiyi hakuri pls... T'saki tai, "kaga
fa, ni wallahi wannan mayaudaran kalaman naka
bazasu min kom ba, ka ma d'aina tambayar ina
nake, dan wallahi bazan fad'a ba. " Haba
Batula,gaba d'aya kinsa na fita hayaci na, auren
ma d'uk ya ficen a ka, ga nan Umma ta tadan
nata akanki itama... Da sauri tace "kar ka maida
ni bi ta chan, ka zata fasa auren ka zai damen
ne?.. Kawai sai taja t'saki ta kashe. Fure tace "a
gaskiya yayi nadama fa man d'in nan.. Harara ta
dan sau mata, "ke fa na fuskanci bakisan halin
maza bane. Kai ta k'ada tana murmushi, sai ta
ajiye waya zata kama ruwa, tuni Fure ta sace
numbern Salman. Da yamma suna zaune suna
wainar filawa sai santi Fatee take, wani abu na
ciki, tunda taga positive Washegari ta t'siri
t'surfa. Fure sai dariya take mata, "haba mom
twins, Wa'ina ai sai Kano, kai ta g'yada tana
d'ang'walar y'aji, "haka ne kam, amma ke komai
naki ai "special" ne... T'sam Fure ta zuba mata
ido tana k'allon ta, ita kam sai zuba santi take,
"yajin ki ma na daban ne, a k'wana uku na koyi
abubuwa... "Lafiya wannan k'allo? Kai ta k'ada,
dan har ta Lula duniyar tunanin AAAn ta,tunda
tace koman ki "special" kawai shi ta tuno. By
Feenat Ja'afar.
Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 28
Feenat Ja'afar Novel's
"JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 35_Bud'e gate suka ji,
Fatee tace "d'an mikon g'yale na, hannu ta mika
kan ta yafa mata. Shi kad'ai ya shigo yana
murmushi, kai kasa Fatee tai mai sannu da
zuwa. Sai ya nuna wa Fure waje da hannu, kan
ya dawo kanshi,yana nufin ta d'akko mayafi, kai
ta g'yada, sai yai waje, ta d'akko ta tarar Fatee
zata shiga d'aki, tace "A'a. Mui zaman mu, zasu
zauna taji Ahmad na fad'in"bissmillah man, shigo
daga ciki. Juyawa Fatiman tai zata tafi d'aki, a
tunanin ta ko bako yayi, sai ta ji yace "bissmillah
Fatima, dawo kiyi zaman ki, tana juyo wa tai
ar'ba da Ango. Tuni ta k'ank'ance ido tare da rike
k'ugu, sai ya marairaice mata, kawai sai yaga ta
kara mishi ma k'yau dafari. "Mey ya kawo ka?..
Cikin marairaita ya matso, ''haba Fati ta, kamshin
masoyi ai baya buya koh AAA? Sudai dariya suke
musu. Harara ta sakar mishi, "kar ka yaudari
k'anka, dan ka d'auka ban sanka ba All... Shiru
tai ganin ya zube mata g'wiwa biyu a gabanta.
Sai ta k'allo su Fure, itama k'unne ta kama kan
tai hakuri. Sai ta d'auke kai, "tashi malam,bani
da matsayin nan, tashi, maza ka rufan asiri..
Ahmad ya k'allo, sai yai mishi da ido kan ya
cigaba da gashi. "A'a Batool, wallahi kin girmi
hakan, kinsan fa ina kaunar ki, believe me... Sai
yasa hannu a wuya halamar ya rant'se, tuni sai
ta fara hawaye, da zummar samun nasara ya
kara k'allon Ahmad, da halamun d'ai shi ya kit'sa
mishi komai. Sai Fure ta k'alleshi da tuhuma tana
k'anne ido d'aya, da sauri ya daga kafada
halamar ba ruwan shi. "A'a, g'wara ka auro mai
haihuwa,, kaga k'wanka kaima a duniya koh? Ni
kuma banni rai.. Kawai sai ta fashe da kuka. Da
sauri ya matso ta kara ja da baya.. " A'a Fatee,
gashi ai Allah ya bamu, kiyi hakuri nayi kuskure..
Sai ya k'allo Ahmad da ke girgiza kai halamar ya
k'wafsa, bai aune ba ya ji ta doko kofar. Bugo ya
fara akan ta bud'e dan Allah, tana kuka tace dan
ciki yazo ba dan ita ba, kuma ciki nata ne ya tafi
kawai. Yin duniya taki bud'ewa. Dak'yar yabar
gun Ahmad ya jashi suka fita, "gaskiya kai su6ul
d baka, sai da nace kar ka nuna mata kasan da
cikin nan, za ta d'auka shi ya kawo ka. Kai ya
dafe, "toh ya zanyi? Wallahi ni Fatiman ce d'uk
ta ban tsoro,sam bamu ta6a haka da ita ba.
Dak'yar yace ya dawo gobe kan sun shawo mishi
kanta. Sai bayan isha'i ta bud'e dan yunwar
cikinta. Fure na parlour, harara ta sau wa Furen,
kan ta zauna, "yi hakuri, ga nan abincin ki kici,
k'allota tai, "baga nan irin halin mazan da nake
fad'a ba, sarakan san kan tsiya, Allah ya kaimu
gobe da safe ku ga. Ita dai Fure murmushi kawai
take. Washegari bak'wai da rabi a gidan ta mishi,
Ahmad ya dawo a jogging ya tarar da mutum a
kofa. Sai ya jinjina kai,lalle Fatee ta kunno wuta.
Matar da ta gama shirin tafiya sai gata ta bingire
da bacci,har d'akin Ahmad yace ya bita, ganan
jaka ta had'a tai "ready". Gadon yaje ya zauna a
kusan ta cikin sand'a, tana t'saka da bacci taji
ana kamar shafa mata mara, da sauri ta bud'e
ido, tana ganin shi ta sau kara tun k'arfinta, da
sauri yasa hannu ya rufe mata baki,batai wata
wata ba ta gant'sara mishi cizon da ba shiri ya
cire hannun, "waya baka izinin shiga d'akin
jama'a? Cikin jin zafin hannu yace "ban sani ba
d'in,, kofa ta nuna, "toh fita, matsowa ya fara,
"ba inda zan fita fa, mai gidan yace in shiga.
Ganin yana kara matsowa yasa ta fara duben
abin duka,kasa ta s'akko da filo a hannu,"kar ka
matso nan, tsayawa yai, kan ya kara zubewa,
"toh kiyi hakuri, wallahi na tuba, harara ta sakar
mishi, "kai kasan wannan, ganin ta ki da lumana
shima ya fara fad'a, "dole ki koma, a tunzure tai
parlour tana "toh sai naga dolen, kawai sai yaja
mata jakar chan, "haba Fati.. Ganin su Ahmad
yasa yai shiru, "Dan Allah ku bata hakuri.
"Fatima kiyi hakuri, d'uk dan Adam yana da
hakan, amma ki duba yai nadama, Fure ta k'allo
wace ke magiya,"bai ba wallahi, Ahmad
yace"yayi man Fati, kawai sai ta sa musu
kuka,nan suka had'u suna bata hakuri,komai
sukace Salman sai yai kalar tausayi yace ''na
daina. Sai ga Fatee ta fara kukan shag'wa6a, su
Fure sukai d'aki suna leken su, tun in ya mat'so
tana ture shi har ya runkomota t'sam, sai kuma
yace mata yunwa yake ji, kai suka k'ada, "lalle
Fatee matsala, cewar Ahmad. K'allonshi Fure tai,
sai suka rufe d'aki suna dariya. A ranar suka
d'inke t'saf da Salman d'inta. Da zasu tafi suka
shige d'aki da Fure, dariya take mata kan ta
g'wara bawan Allah, "Hmm,bazaki gane ba, ni
nasan mey nasha a baya ai, sai d'ai wallahi har
na haihu ba mai gani na a dangin shi, amarya
yasan inda zai kaita ba a gida na ba. "Na haihu
kuwa, in kika cire Umma.. Toh ba d'an uban da
zai d'au d'ana wallahi, dariya Fure take, "a
assasauta d'ai, tace "za ki gani ai.
************************ Sadakin Maryam aka kai,
d'uk Wa'inar nan da ake toyawa sam Hassana
bata ji ba. Anan yayan su Ahmad ya fallasa
Momy taji wai K'anwar Fure aka kaiwa, nan ta
tada tsiya. Kan wallahi in dai za'a auro Maryam
toh Sai an auro Rukayya. Takanas Momy ta
Wanki K'afa har gidan Fure ta kare mata tass!
Wato wai so take ta gaje musu dangi da t'siya?
Toh tasan da saninta, indai har ta yarda auren
Muh'd ya faru da Maryam, toh wallahi itama
Rukayya sai ta shigo mata.. Da sauri Fure ta
rint'se ido hawaye ya zubo. Tab,ana wata ga
wata. Tunda har Momy ta rant'se toh k'wa tasan
Rukayya ta shigo ta gama... Hannu ta d'aura aka
hawaye na zubar mata, a hankali ta furta "wayyo
ni.. tama kasa koda ihu ne taji dad'i,kukan ma
sai hawaye, koh wata biyu ba ai da kashe "case"
d'in Fatee ba ga nata ya d'anno. By Feenat
Ja'afar. 庐NWA Feenat.mywapblog.co
9/29/16, 2:41 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
36_Tamkar mara lafiya haka tai lamo akan
kujera,har maigidan ya dawo, sam shima bai
shigo da walwala ba, sai d'ai yana ganin Furiin ya
rikice mata. Dan yanzun daga gidan yake Momy
ta sanar shi tazo, ga yaje gun Abba,Abba yace
tunda an nace abu kusan shekara nawa kawai ya
hakura ya aure tan, dama bai bi takan mama ba,
dan t'saf yasan abinda Momy tai agun ta ido ne.
"Pretty... Ido kawai ta zuba mishi, sai ya dago
ta,d'uk ta sau mishi jiki k'allo ne nata, tuni sai ya
tsorata, da k'arfi ya jijjiga kafad'unta "Furera... A
firgice ta k'alloshi,cikin sanyi tace "uhmm.. Suna
had'a ido ta barke mishi da kuka.
Juyin duniya Fure taki d'aina kuka, kawai sai ya
sa mata ido shima kamar zai sau kukan.
Jijjiga kafad'unta kawai yake halamar rarrashi
yana share mata hawayen,sai d'ai yana goge wa
wasu na zubowa, kawai sai ya d'auke ta tuni ta
damke ido tana cigaba yai d'akinshi da ita,
"bathroom" ya shiga,ya cika "bathtub" da ruwa,
sai ya bar kofar a bud'e, tana t'saka da kuka ta
jita cikin ruwa.
Da azama ta bud'e idon,ya k'ada yai jajjajir tana
k'allon shi, tuni shima ya fara ko'k'arin shiga ciki,
kawai sai ta kara jiniya tana dan bubbuga ruwan
da shura K'afa.
Shiru kake ji Fure, kuka ya kare. Shi kad'ai yasan
"week points" na prettyn shi, dan ka burkita mishi
ita da kanshi zai samo kanta, gashi yanzu harda
waka kamar ba ita ce dazun ba.
Shi kam yana a bak'in gado yana k'allon yadda ta
zubo da gashi ta gaba tana gogewa da "towel"
daure da wani, tare da wakar "mayafi na bargo
nah.. Sai murmushi yake.
Da hannu tasa tai baya da gashin fuskarta ta
baiyana,mutumin kawai ya zuba mata na mujiya.
"Towel" d'in ta hulla mishi a fuska, tuni ya shaki
kamshin "shampoon" jikin na "vatika" yana
lumshe ido,cire wa yai da zummar hulla mata ta
kawar da kai tana murmushi.
Bata aune ba taji ya janyo ta gaba d'aya suka
suka zube suna dariya.
"Wallahi ki tada musu hauka na fad'a miki, tuni
zance zaisha ban-ban, cewar Fatee da suke
waya.
"Hmm, sis Fatee bazan iya ba, in fa wani yaci
riba,wallahi wani duka zai ci, kar ki manta a
gidan su fa take? Babbar riba ta yanzu na samu
Maryam ta shiga gidan Hassana, wallahi ko
Rukayya tazo naci riba.
"Bari banja da ikon Allah ba, amma in dai kece
Furera Muh'd, Matar Ahmad AAA, wallahi
Rukayya sai d'ai gani da ido t'sakaninta da Mijin
ki.
Ki rubuta ki ajiye, bana ke zakiyi "wining" a
wannan "battle" d'in, InshaAllah daga wannan
karan kin zamarwa Momy ciwan ido,kin zama
k'arfen K'afa, InshaAllah ke da AAAn ki
TAKALMIN KAZA ne.
Ajiyar zuciya tai, sam ta ma sa a ranta Rukayya
fa ita ta shigo ta gama, amma bata isa ja da Sis
Fatima ba, yanzu sai ta hau mata.
"Amin toh, yanzu ma haka ina gida gun shirye-
shiryen bikin Maryam d'in, Fatee tace "ita
Maryam taji zancen? Kai ta k'ada mata, "mutum
d'aya yasan auren Maryam shine fansar zuwan
Kishiya ta ba...
"Sis wallahi ji nake kamar zuciya zata fashe in na
tuno AAA za'a d'aura mishi aure da RUKAYYA.
"Ina matukar son Mijina, shima yana sona, ance
ba'a "BA'A YABON DAN KUTURU" wai sai ya
girma da yat'sa.. "Believe me.. Na aminta da AA,
dan shi ya so ni a yadda nake, gashi yanzu ya
fiddo ni cikin jama'a.
"Sis Teema ya zanyi na rage kishi pls... Buh ki
d'aina k'wantar mun da hankalin kishiya bazata
zo ba, ki barni na zama "ready'' dan t'ar6ar ta.
Shiru Fateen tai, wallahi bata tara sani ga Allah
ba, amma a jikinta take jin tabbas auren nan ba
mai yuwa bane.
Sai dai ya ta iya, kawai sai ta hau lallashinta kan
tai hakuri tai ta adu'a in da alkairi toh.
Kamar Yarinya haka ta sau kuka a d'akin su
Maryam lokacin da suka kare wayar.
Hawaye Maryam ta goge, wacce tazo d'aki d'an
nuna wa Furen gadon da su Ada suka za6a
achan t'sakar gida.
Ba koh sallama ta shiga d'akin, da sauri Furen ta
hau goge hawayenta.
Zama tai tana k'allon fuskarta, sai Furen tai kasa
da kai kamar marar gaskiya.
"Ya Furera kishiya za'a miki amma ba wanda ya
sani? Kai ta dago tana k'ada mata, "toh mey
yasa zaki zabi ki muzgunawa kanki dan kawai jin
dad'in kanki da nawa? Kai Furen tai kasa dashi,
kawai sai Maryam d'in ta tashi tai waje, sai ta
d'aura bayanta.
"Umma! Umma!!.. Cikin shesshekar kuka take
k'wala mata kira, tana zuwa ta wat'sar da hoton
gadon kasa, d'ai-d'ai Fure ta taho,
"Lafiyar ki kuke kuka?
Kawai sai Maryam d'in ta k'ada kai da takaici,
"ku zama sheda toh Umma, na fasa auren nan
wall... Da sauri Fure ta rufe mata baki tana
girgiza kai.
Ture hannun tayi tana hararar Furen, "bari kiji
Fure, wallahi nafi k'arfin ai "playing" wannan
"game" d'in dani daga ke har har dangin Muh'd
d'in..
Fad'i take ita kam sam bazata d'au wannan ba,
tun wuri yazo ya debi sadakin shi ya ware, ita
za'a rai nawa hankali?
"Mai suka maida ki? Sakaryar da baki san abinda
kike ba ko mai?
da har za'a fanshi aure na da kishiyar ki? Kai ta
k'ada tare da rike k'ugu.
Da taga suna bata hakuri ma tai waje, ba ita ta
dawo ba sai da taji kiran Muh'd yana sanarta
yazo.
Ba jima wa ta karaso, wankin babban bargo ta
rufe ido tai mishi, sannan ta jaddada mishi ba ita
ba auren shi, dan sunfi k'arfin cin zarafi.
Gaba d'aya yai mutuwar t'saye jin masifar
Maryam, har ta shige gida kamin ya farga fara
t'sayarta.
Wasa-wasa d'ai Maryam ko waya ta d'aina amsa
nashi, ga a gidan kullum kuka, barin ma da taji
irin cin kashin da dangin ke ma Fure, mamakinta
d'aya "wai shin ina masifar Fure tayi? Ina
wayonta?
D'uk da tana matukar son Muh'd amma mutuncin
y'an gidan su yafi k'arfin komai a gunta.
Sai d'ai shi Abba yace sam bai san zance ba,
tunda taki fad'a mishi dalilinta na fasa auren
k'anin mijin Fure.
Tanan kawai suka samu cikas.
Biki saura sati uku, in kaga Fure d'uk zabge,
amma k'arfin halinta yasa sai mai kula zai gane.
Yauma tana gida, Umma sai tausarta take kan ta
cire damuwa, tabar wa Allah komai, Maryam ta
k'alla wace tun ranar ta d'auke mata kai, sai tai
murmushi.
"Maryam.. Banza ta mata, d'uk da tabar abinda
take. Bata damu ba ta kara cewa
"Maryam tun ranar chan naso son kisan k'in
auren ki da Muh'd tamkar kin bawa Momy damar
cin galabar mu ne, dan dama so take a fasa naki,
wanda nai imani baza'a a fasa na Ahmad.
"Maryam.. Kiyi hakuri kibi zuciyar ki, ni ki bar
nawa gurin Allah, ki sani fasa auren ki, bazai
sauya zani gun Momy ba. Matsowa tai ta dafa
hannunta,d'uk Umma na k'allon su.
"Maryam, kai ta dago tana hawaye, sai ta share
mata.
"Ki min alkawarin sauke gammon nak'in nan da
kika d'aura, ki duba so,da kuma kaunar da bawan
Allah nan yake miki, da naso auren ramako dake,
ashe kana taka Allah na tashi, kar ki bawa Abba
kunya, ki manta dani, ki fuskanci Moh'd, ina
rokon ki...
Dago wa tai ta k'alli Umma, sai Umman ta tashi
ta basu gu, sai ta jijjiga wa Furen kai.
"InshaAllah, amma fa ki sani, wallahi d'uk dan
uban ni da ya nemi takani zan murje mutum.. Kai
ta k'ada mata, "wannan ban hanaki ba, ba kuma
zan fara hanaki ba.
Da wannan ta samu suka d'inke da Muh'd d'in,
aka cigaba da hidimar biki a gidan guda biyu.
Dan sam ko kusa Ahmad bai ko mot'si, asalima
Fure ke tambayar shi wataran kan abinda yake
shirya wa, banza yake mata.
Ita kam bangaren Momy koh a jikin su, d'an ko
ita ta isa yiwa Rukayya lefe, yayinda a bangaren
Mama tasa wa kowa ido, daga Ahmad d'in har
Muh'd,dan ba mai ne manta cikin harkar kara
auren shi.
Ku tambayen ina labarin Hassana man?..Lol.
Hassana d'ai sai ana saura sati wata d'aya biki
kan taji labari, akanzo har gida ana tambayar ta
da gaske mijinta wai zai aure?
Wataran harda shewa zata bada amsar A'a,
Yayanshi ne zai kara aure dan matar ba ta
haihuwa.
A ranar Momy ce ta tare ta da zancen ba koh
rufi, haka ta dawo gida ta hauka cewa Muh'd,
yayi lallabin duniya taki, a fafur sai ya fasa, sai
d'ai a ranar da tasan wa zai auro mata tattare ta
bar gidan.
Sai dawo wa yai yaga gida a bud'e tayi gidan su,
hakan ya

Please Login or Register in order to submit comment