You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"eh ba,ai
kunsha Dubai, zama ta g'yara, "amma d'uk fa kin
rame Pretty, hope lafiya? Kai ta k'ada mata tana
murmushi, "toh ko d'ai anzo gurin y'ar gida na?
Dariya tai,sai tai kasa da kai, tabbas Aunty A'i
mai Sonta ce, ba tajin zata iya boye mata
wannan. "Allah sa hakan ne pretty,pls ki ban
albishir. Kai ta daga mata tana d'an murmushin
kasa kasa. "Kai,dan Allah ki ban labarin ya y'an
gidan ki sukai da sukaji labari? K'allota tai, "kai
banjin wani ya sani ma bayan mama... Kai Aunty
A'in ta k'ada, "good,kun min d'ai d'ai, g'wara su
gani tashin farko,in yaso sai hawan ruwan mutum
ya hau muga inda zai mutu? Nan suka hau firar
yaushe gamo, yawanci kan matsalar gidan
mazajen nasu ne.. Sosai ta tayata murna har ba
tasan sanda ta ruka musu ba su ma. "Wallahi
Aunty A'i ina son naga kin haihu kema, d'uk da
ina ga kamar... Sai d'ai tai shiru. Murmushi Aunty
A'in tayi, kan tace "kina ga kamar bamu damu ba
koh? Kai ta k'ada, "ba haka ba. Sai ta g'yara
zama. "A da na damu sosai tunda na shekara
hudu, d'uk sosai ban damu wani chan ba,toh
g'wara nima akan maigidan, dan shi kam bai ma
fiya son yara ba, boko ta sha mishi kai da burin
tara kud'i, sam yaran basa a gabanshi. D'uk da
gaskiya ni ban ta6a samun mat'sala a gun dangin
shi ba, sai d'ai na damu daga baya sosai,dan ko
ba komai ina son ganin d'an kaina ko d'aya ne.
Ganin na mat'su ne yasa har da mukai wata
tafiya Umara mukaje muka ga likita, ni kam ban
da mat'sala, sai shi ne suke tunanin a gareshi
take a bangaren "hormones" nashi, wato
(Hormonal imbalance) sannan ga karancin shi
kanshi spm. (Low sperm counts). ''An d'aura shi
a magani, sannan da shawarwari, sai d'ai abin bai
ba. Muna da shekara shida muka sauya kasa
d'uk a dalilin na damun, sai likita ya bada
shawarar ai min "IN VITRO
FERTILIZATION" (IVF) wato a sanya k'wanshi da
nawa bayan "eggs" d'in yai fertilizing. Anyi
nasara, har ciki yakai wata 4 muka dawo gida,
sai d'ai ko wata ba mai ba na samu
"miscarriage". Sau uku ana k'wata haka,sai d'ai
duk basa zama,da haka na hakura na sanya ma
sarautar Allah ido. Sai na ma d'aina damun kaina
da abin,gashi yanzu muna zaman mu lafiya. Sai
dai ko in kad'aicin hakan ya ta6o ni wataran.
Sannan har yau ka'f cikin gidan ban tunanin sun
san haka ba in banda Mama. "Kawo iyanzu da
muke kok'arin cika shekara ashirin da aure.. Kai
Fure ta jinjina, tare da mata fatan alkairi. Bayan
tafi Fure ta zurfafa tunanin rayuwa. Cikinta
watan shi hudu kenan da sati biyu yau, sai yau ta
je gidan su Momy. Kamar kullum chan ta fara
nufa. Su Huwaila wacce ta aure ya mutu ana
parlour. Tun daga kasa har sama ta take
k'allonta. Doguwar Riga ne jikinta da babbar rigar
sanyi fara wacce ta boye asirin cikin. Kau da kai
tai,dan sosai tai k'yau, amma ganin kyashi su
kullum muninta suke gani. "Sannu Huwaila,ina ta
sallama ko baki ji ba? A wukance tace "eh. Sai
tai murmushi. "Ina Momy toh? Harara ta wat'sa
mata kan tace "tana kaina. Ita abin ma sai ya
bata dariya. Har ta juya zata fita sai ga nan
momyn ta fito. Har kasa ta gaida ta, da
mamakinta sai taga tana k'allonta ta amsa. Da ta
dago kai za taga ita momyn ke k'allo. Abincinta
ta mat'sar. Yau d'ai anyi mutunci, dan har ta fita
ba wanda ya tofa mata. Da sauri Momy ta k'alli
Huwaila, "ni fa kamar ciki nake tunanin yarinyar
nan take dashi, kai Huwailan ta k'ada, "haba d'ai
ciki Momy? Wannan katuwar riga kamar tana a
"swisszaland" ba dole ta mayarta mai ciki ba..
Kawai sai ta batar da Momy. Dariya Fure tai,
ganin hakkarta ta cimma ruwa, dan tanajin su
sarai. Dan ba wani sanyin azo muga ake ba a
gari. Mama sosai tai murnar ganinta, bare taga
jika har ya tasa. D'uk sai ta fara sinke kai da jin
kunyar Maman. Momy ke da girki, Abba yai
bangarenta don cin abinci. Wai sam ba tasan zai
dawo da rana ba tunda yau ba weekend ba. Zai
fara balbaleta tace ganan ai na gidan AAA, tuni
ya hau washe baki, "a toh zuba min, sai ku jira
y'ar aiki. D'auka tai suka tafi chan bangaren shi
da k'wandon. Wa'ina ce tasha miyar Egusi da
banda da jan nama. Tuni kamshin ya karad'e
parlourn Abban, shi kam bai jira ba yaje da
kanshi ya wanke hannu. Tuni ya fara kai gara.
Ita kam a kullum mamakin yadda ake ya6on
abincin Fure take,musamman Abba. "Maryam
miyar nan kar ta barki, za kiji haushi.. Sosai sai
had'iyar yawo take, amma isa ta hana ta ci
kamar kullum. Shikam Abba da ya gut'suro sai ya
mika mata, ta d'an y'atsine fuska kamar bata so.
Abba yace "ci d'ai. Daga bata d'aya sai ga
matarka ta t'soma hannu,d'uk loma d'aya sai ta
y'atsine fuska tuni sai gashi har tafi Abban ci.
Sai kam ya hau mata dariya kan ai wannan
"Master Chief ce a cooking. Haka ta d'au
ragowar ta kaima Huwaila, "gashi ku ci, kinga na
sai an wahalar da kai ba,tunda y'ar wahalar ta
kawo. Daga yau mun hutar da rose d'uk
weekend. Tuni k'wa kamar mai jira ta hau ci ita
da ya'yanta. Tun daga ranar su Momy ke cin
abincin Fure y'ar wahala. Sosai ta gama da y'an
gidan k'arfk'af da daddan abincinta. Sai ga nan
Momy na Allah-Allah weekend tayi, sannan
kullum cikin kushe abincin Rose mai aikinta take,
wanda a da gani take tafi d'uk y'an gidan iya
girki. By Feenat Ja'afar. 庐NWA.
9/29/16, 2:53 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 46_"Hand golf " ya sa
dan duba "CM" da mamaki ya k'allota, sai d'an
nishi take tana zufa,sosai yai mamaki,da sauri ya
fasa ruwan, ganin yaki, Waje yai gun AAAn, ina
zaton zata iya, InshaAllah,kuyi mata adu'a kawai.
Kai ya k'ada, "za mu iya shiga? Kai ya k'ada
shima likitan, "sosai, musamman kai, za ta fi
bukatar ka kusa. Maryam ya je bama abin
g'wajin da doctorn ya bashi,tuni ta sanar da
Umma da dasu Aisha. Tashi Umman tai kawai ta
shiga bayi ta d'auro alwala. Tara da wani abin,sai
ta zauna sallaya tana mai rokama y'ar tata sauki
da Nabiyur Rahmati. Komawar likita har Nurse
tai gunta, ganin yadda take ta ko'k'arin nishin
fitar D'a. Gaskiya likita yana jinjina mata,ganin
yadda ta dage sai ta haihu da kanta. Kawai sai
ya hau had'a abubuwan taimakon labor. Tana
t'saka da nishi sai ga nan AAA shida Maryam,
nurse tace ya shiga man ganin ya t'saye kawai
k'allon Furin yadda take nishi gumi na zuba
tamkar wacce ta had'iyi kunama. Kai ta daga
kamar ance k'alli kofa,suna had'a ido kamar zai
sau mata kuka.. Ido ta rufe,cikin masifa tace
"Fita.. Ka fita bana son ganin ka... Da sauri likita
da su Maryam suka jiyo,ganin AAAn ne sai abin
ya basu mamaki, cikin rawar murya AAAn yace
"Pretty ni ne fa... Da sauri ta bud'e ido, kawai sai
taji mugun haushi, "eh kai d'in.. Baki sake yake
k'allonta.. Ganin yaki fita ta juyo gefe, k'walin
"hand gulf'' ta d'au ta hulo mishi, cikin balbalin
masifa ta rufe ido tana sai ya fita... "Ya fita
kawai... Kawai sai ta farke da kuka... Cikin rawar
murya yace "yi hakuri, na fita, sannu, kiyi hakuri,
Allah sarki AAA. D'uk sai ya basu tausayi. Yana
fita ya goge k'walla, tabbas yasan ba karamin
wuya prettyn shi ke ci ba, tunda har zata iya
t'sanar ganinshi. Da sauri ya d'au waya yana
kiran Mama. "Ka k'wantar da hankalin ka,Muh'd
ya sanar ni, zata haihu lafiya.. Ka d'aure. Dak'yar
Maman ta d'ai d'ai ta shi. Sai d'ai Furi har goma
shiru ana ta fama. Tuni Maryam har ta fara
kuka. Abba karan nan ta kira, shima tuni ya taho
gida d'uk sai ya ji kamar bazai iya ci gaba da aiki
ba. Jin Maryam na kuka yasa ya d'au jarka ya
hau karanta mata d'uk wata adu'a ta saukin
haihuwa, "Umman su ko d'ai zaki je ne? Kai ta
k'ada, "bana tunani, sai ta share k'walla. "Sai d'ai
nasan d'uk inda Furera ta t'saya tana jin jiki..
Ganin tana hawaye yasa yai mamaki. "D'uk
yaran nan sun haihu lafiya Umman su, itama zata
haihu,in d'ai har tasha wannan adu'ar da yardar
Allah. Kai ta k'ada, "Allah yasa, amma haihuwar
Fure ba irin tasu bace... Komai ta sanar ma
Abban, nan yai ta mamaki, sai ya fita makotan
su, ak'wai dabino,ya samo danye fresh wanda
aka jijjige a take mai bauri. Yasa Umman dakeshi
cikin sauri, su basu rabo da zam-zam y'an Naira
dari, dashi ya had'a da ruwan tofin, ana haka Ada
ta shigo ajiye yara zata asibiti harda breakfast
d'in ta. Nan Abba ya bata sako, tare da ce mata
ta tabbatar tasha. G'wag'war maya ake da Fure
da likita kan bazata iya ba tana musun zata iya,
adu'a ce kawai fal bak'inta. Babu wanda ke a
K'wak'walwar ta sai Allah. Lokacin zuwan Ada
har Ummi ma tazo,tana zaune kusa da yayanta
wanda yake ta sallar "Dhuha" baji ba gani, in ya
hau "Sujjada" yakan jima yana rokar ma prettyn
shi sauki gurin Allah. Maryam ta kira, sai gata
tazo,idon nan ya k'ada, "Maryam ya akai? Kai ta
k'ada, "ina zaton ba D'a d'aya ne ga Ya Furera
ba, dan naji tun dazu likita na ambata mata
"Babies" kan bazata iya ba ita kad'ai. "Ba
komai,kiyi ko'k'arin ki bata wannan inji
Abba,InshaAllah zata iya tunda ansa Allah. Kai ta
k'ada, kan ta k'ar6a tai ciki. Sai d'ai fur likita
yace zata t'sayar mata da labor wai ya koma
baya,tace adu'a ce. "Zansha Doctor, adu'a ce, a
bani dan Allah.. Kai ya k'ada, dan shi yanzu
komai aka ce Allah kawai yinshi yake,dan yaga
Aya.... Cikin Rahmar Ubangi, ko minti goma batai
da sha ba taji wani nishi ya taho mata, da sauri
likita ya k'alleta kan ya d'akko abin ka'ri yai
mata. Baki Maryam ta toshe,take ta k'alli robar
dake a hannunta. Da ikon Allah ya zaro baby,sai
ga nan wani na biyo bayan d'aya. Tuni Furen tai
baya tana mai jan numfashi sama. Da gudu
maryam tai waje tana murnar taga yara biyu.
"Yaya Ahmad!..Ya Ahmad, yana d'urkushe yai
sujjada kusan minti biyu adu'a kawai yake ma
Fure. Ganin haka ta ruko hannun Ummi da Ada,
"wallahi twins ne, ta haihu naga... ''Assalamu
Alaikum warahtullah... Yai k'waya d'aya hagu da
dama. Cikin azama yace "Pretty fa? Sai ta zuba
mishi ido, dan sam ita bata ma kula da halin da
take ciki ba. Ganin ta zuba mishi ido yasa da
sauri yai hanyar kofar room d'in. Samu yayi likita
na fad'in zaki iya,ki kara nishi tana k'ada kai,
gaba d'aya numfashin ta sama yake. Ganan yana
ganin wani abu bak'i-bak'i likita na ko'k'arin fitar
shi. Da gudu yai kanta tare da kiranta, dusu-dusu
ta fara gani, tuni ta hau yunkuri kamar zatai
amai, da sauri likita ya jawo babyn da Allah ya
kara tunkudoshi. "Sir... Da sauri Nurse ta fara
nuna mishi Furen dake ko'k'arin d'auke numfashi
Ahmad na jijjiga ta. Cikin sauri ya bama d'ayar
Nurse d'in babyn kan yace "oh no! Cikin zafin
nama ya jona mata "Oxygen", tuni ta fara sama
da kirji tana jan numfashi, ko dusu-dusu ta d'aina
gani, cikin sauri ya zuke wata allura bai wata
wata ba ya chuka ta jikin cinyar Fure. Numfashi
mai k'arfi taja,wanda yai d'ai-d'ai da k'wala kiran
da AAA yai mata "PRETTY.......................... By
Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywa
9/29/16, 2:55 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 47_Ina Pretty ta lula,
Kanta yazo yana d'anna mata kirji yana k'allon
numfashin, sai d'ai ita ko gizau, tuni Ahmad ya
kafawa hannun likita ido ba ko kiftawa, ya ma
kasa kok'arin hanashi ko sashi,hawaye kawai ke
zubar masa, da sauri likita yace nurse ta nemo
mishi likita guda biyu,ya sanarta sunan su,kan su
zo ya kara mata wata allurar, ganin ba nasara
yasa Ahmad kawai ya zame gun yana kuka
kamar yaro, shi kenan shi, ya zama maraya. Kai
da g'wiwa ya hada yana rusar kuka, yayinda likita
yake ta aikin shi. Su Maryam da suka leko tuni
sukai waje suka had'a kai suna kukan Fure,dan
d'uk sun saddakar ta ma mutu. Wani numfashi
Fure taja mai k'arfi, a hankali ta fara mutsu-
mutsu d'ai-d'ai shigowar likita d'aya.
"Pharmacy".. Cikin murna likita ya kira shi, da
sauri ya daga jin tarin Furen,sai d'ayan likitan ya
cire mata Oxygen d'in. Da gudunshi ya karaso
yana kiranta, cikin hankali ta fara bud'e ido,komai
ya fara dawo mata. Akan AAA ta dire,wanda har
yanzun hawaye yake rike da hannunta a bak'inshi
yana d'an dariyar murna tare da shafa gashin
kanta, sai d'ai koh sannu ya kasa furta mata,a
hankali ya d'aura kanshi a kirjinta kamar wani
yaro. Cikin hankali ta d'aura hannunta a kanshi
tana hawaye da sigar lallashi, tasan da ta mutu,
da AAA shi zai fi kowa shiga a wani hali. Da
taimakon manyan likitocin suka had'u suka
temaki matar "pharmacy". Tuni su kuma Nurses
suna chan a d'akin taimakama yaran. Sai da
d'aya Nurse ta fita tace ma su Maryam toh su
d'aina kuka karamin suma tai... Sai da ya
tabbatar ta g'yaru da komai sannan yahau musu
godiya. Har aka gara ta d'akin hutu na
musamman suna a manne da hannun juna. Tuni
kuma aka hau buge-buge su Ada su su Ummi kan
Fure ta haifi y'an biyu, shikam suna a gado
d'aya. Sai ga nan yaran su an garo musu cikin
gadon yara. Wani ihu su Maryam suka buga da
suka ga uku, tamkar yara harda dan t'sallen
su,tuni suka bi Nurses d'in d'akin da Fure take
suna murna, kam suka ce musu banda hayaniya,
amma sun san ai ba abu ne mai wuya ba. Wai sai
a sannan ya ma tuna da yaran, tuni kowa ya d'au
d'aya, ummi tace "woow.. Adama tace "k'yau...
Yayinda Maryam tace "MashaAllah, kawai sai
nurses d'in suka sa dariya, dan ko su suna ta
yaba kyaun yaran, gasu da dan girman su, kan
suka had'a baki gun fad'in "Congratulations sir"
kai ya k'ada musu, kan yace "yau ak'wai k'yautar
magani a store. Na hannun Maryam suka ce
"wannan ne Hassan, ga nan Hussain, na hannun
Ummi kuma itace mace "Gambon su, kan suka
fita. Wajen gadon su Fure sukai da yaran, harara
ya kai musu cikin wasa, "ai munyi fad'a dasu,
kad'an ya rage na rasa Momman su ya k'wanto
kan Furen suna musu dariya har Furen, a hankali
ta lallashe shi kamar gaske. Ido kawai suka zuba
ma yaran da suka d'aura musu su. A hankali ya
k'allo Furiin, tambayarta yake shin tasan dasu?
Kai ta ka'rkace mishi tai kallar tausayi, ido kawai
ya zuba mata, Furii ta mishi komai.. Ga ta bashi
yara masu kamar shi, sai sumar(gashi)Furiin da
suka d'akko da d'an bak'in nan. Kan kace wani
abu sai ga nan y'an uwa sun fara diddikowa,
harda Mama ta wanke ido tazo ganin twins, sai
d'ai suna ganin uku sai su hau kabbara. Abba
cikin sauri yai d'akin Momy da har yanzu d'aya
saura bata bud'e d'aki ba tana bacci,wanda a
zahiri in ta dad'e takai goma,amma ranar Allah
ya k'wantar ta. Mut'seke ido take ta bud'e, ganin
Abban sai wage baki yake yasa tace "Alhaji
lafiya? Cike da murna yace "Maryam matar
Babana ce fa ta haifi y'an uku.. Cikin rashin
fahimta tace "waye hakan? Sai ta kai hannu kan
dank'wali tana warewa, "a wanake dashi bayan
Ahmad, Furera ce ta haifa ai..... Hannu kame a
kai Momy tai poster, jin Bud'e kofar gefe yasa ya
juya cikin murna, Huwaila ce, "Abba wa nake ji
kana haihu? Cikin murna yace "Sa'a matar
Ahmad, uku fa,ras, kuma da kanta... Waya aka
mishi sai yace "bari ga nan Ummi. Cikin zakuwa
yai waje yana amsa waya, baki sake suka bishi
da k'allo, Momy na furta "Furera kuma?... Cikin
kok'wanto. By Feenat Ja'afar. Feenat.mywapblo
9/29/16, 2:58 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/4, 10:09 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
48_"Kai Momy ina fa Abba bai ji da k'yau bane,
wane irin Haihuwa? Kuma y'an uku?.. Kai
"impossible".. K'allonta kawai Momy take, "tun
ba yau ba na fuskanci yarinyar nan tana da
ciki,amma fir kika karyata.. " no ba ma wannan
ba, saboda rashin mutuncin ya mot'sa musu,kinji
wai har akaita asibiti Ummi taje bamu sani ba?...
Tuni ta hau kumfar baki, kan zasu ga ba inda
zata toh.
"Wallahi Momy kar kije, tunda an nuna baki isa
ba kawai. Tuni ta hau zigata, kuma wai sai ta
hau buga ma su Rukayya da Aunty Jidda waya,
kowa ya ji sai ya na nata haihuwa kuma? Y'an
uku?.
Kamar k'wa yadda Momy tace d'in kin zuwa tai,
sai Huwaila ce taje ta ga k'wak'waf.
K'wanan su biyu yasa a sallame su, tare da
d'aukar Nurse mai zuwa duban su, dan sosai
jama'a sukai yawa.. Tun a asibiti Fure tasan tai
haihuwa, dan Abba mota biyu sukai zuwa ganin
yara shida Abokanshi, kowa yazo sai ya direma
Fure y'an banki.
A gidan ma haka, jama'a sosai, kusan kullum
Aunty A'i na nan gidan kusa da yara, Fatee na
jan nata tsohon cikin, shi yasa d'uk tai lum,
amma d'uk da haka tana a hanya kullum,
Hassana an zo, dak'yar aka d'anne zuciya ganin
ikon Allah, sam AAA baida k'arya, amma akan
yaran shi ya tada ta, d'uk wani kaya na ban
sha'awa yara sun sha su, an k'awata d'akin su
g'wanin ban sha'awa.
Yara sunci Hassain,Hussein, da Hasna(pretty),t
uni tun a asibiti yai ma yaranshi huduba, sam ba
sunan kowa, dan kowa yazo yana son mai suna,
Hasna kam wai ta mishi k'yau, shi yasa ya sa
mata shi, dan ta chanchanci zama pretty 2 wai.
Har sukai k'wana 5 ba Momy ba Aunty Jidda bare
Rukayya, d'uk rashin shiga jama'a na kishiyar
Rukayya amma tazo gidan Fure a karo na farko.
"Anya mutanan nan zasu ga Annabi Ya Furera?
Ace tunda haihu, ba wacce ta leko dubaki cikin
Momy da Aunty Babba? Murmushi tai kan ta
k'alli Maryam d'in, "mey kike so toh nace? Tunda
kinsan yadda nake gunsu.. Baki ta ta6e Maryam
d'in, Aisha tace "ki barsu ke d'ai Fure, kar ki fara
komai, aciki har hudubar hanasu su Hasna da
ake miki..
Murmushi tai ta k'ada kai, ita kad'ai tasan mey
zatai.
"Ba wanda zan hana yara,asalima nai alkawarin
d'uk wacce ba tazo ba zan kai mata har gida ta
goya.
Karamin t'saki Maryam tai, "wallahi ba mahalukin
da ya isa na haihu bai min barka ba na kai mishi
D'a, wallahi ko zai mutu. Tab, karshen kyyaya
kenan wannan... Shiru tai lokacin da Aisha ke
zungurarta, su Momy ne t'saye bak'in kofa ita da
su Aunty Jidda.
"Momy shi yasa nace miki bazan zo gidan nan
ba kika tilasa min, sam na ki jinin had'uwata da
shegiyar yarinyar nan.. Ta nuno Maryam.
Ciki momyn ta shigo, tana mai harar kowa na
parlourn, kasa Fure ta s'akko cikin girmamawa,
ita kam Maryam baki ta ta6e, tare da dan
gunguni ciki ciki.
"In bata nuna haka ba ina za kusan y'ar gidan
mai waldar mashin ce ita... Da sauri Fure ta
dago, Rukayya ce, tuni taji zuciyarta na tafasa,
ga nan Huwaila, ga Aunty Jidda, ga kuma Momy.
Wani murmushi tai, kan a hankali ta girgiza kai,
Lalle Allah a yau ya ara mata ranar da ta jima
tana neman zuwanta, ranar da har sallar t'sakar
dare tai dan zuwanta.
"Mtsww.. "Alhamdulillah, a ko ina zan bugi kirji
sannan nai alfari, "of course, ita ce sana'ar uban
mu, amma kamun nan sai ki fad'an sana'ar taki
uban...
"Maryam... Cikin t'sawa Fure ta kat'seta, "ki
kama kanki, baki ta ta6e, Cikin fusata Rukayya ta
mike, ''karya na fad'a, iyalan t'siya da t'siya, an
zo aci aziki ai dole a haiho y'an uku, kinga ko ba
komai an mamaye gida.
Ido Maryam ta rint'se, a rufen tace "Ya Fure ba
miyi dake zaki t'sayar ni a batun nan ba fa,
saboda haka wallahi sai na furta.
Ido ta bud'e, har da mat'sowa kusan Rukky, su
Momy da Aunty Jidda ido ne kawai nasu, dan
sosai sun yi mamakin fitsare idon Maryam, wai a
gaban su take wannan rashin mutuncin?
"Sana'a ba chacha bace, ba kuma satar kud'i
bace a Ak'watin gwamnati, a jerin barayin
g'wamnati dole uban ki ya fito ciki, ga chacha
kamar ibada, ga neman mata kamar d'an taure,
ga....
Mari Fure ta sakar mata, cikin t'sabar fusata ta
fara mata fad'a, "wa ya fad'a miki wannan abin?
Rike da kunci Maryam tace "sana'ar ubanta na
fad'a, ko ke ba k'ya kishin naki uban?....
"A'a ki barta, ki barta ta kai Aya, tanan zamu san
lalle an gaji t'siya da talauci, bak'in ciki take da
dukiyar uba na, kuma wallahi yafi Ubanku Malam
Muhamm...
"Rukayya....cikin t'sawa Fure ta kat'seta, kan ta
nuno ta da hannun cikin t'sananin fushi da
"ki iya bak'in ki, ya zama ranar karshe da zaki
kara wannan kuskuran na ambatan sunan
mahaifin mu ciki. Kiyi komai, amma wallahi ki
t'sallake wannan, ba zan d'auka ba... Ta karasa
tana mai kawar da kai gefe,
Ba wanda ba k'alleta ba lokacin da tai t'sawar,
yayinda su Ahmad suka karaso bak'in kofar
parlourn suka t'saya gefe.
Harara Aunty Jidda ta k'wada mata, "dallah rufe
mana baki a gun, ji ta, har wani abin tunkaho ne
ga alfari ga d'an waldar, an fad'a muku ya'yan
mai walda, matsiyata kawai... Ido Fure ta rint'se,
kan ta dago ido ta sauke su kan Aunty Jidda.
"A fad'an komai, amma uban mu daraja ne
gareshi matuka a gun mu, a gaskiya yau hakurina
zai kare akan hakan, kai ta girgiza, "dan Allah
sam bazan d'auka ba, sam Allah.
Sai ta sa bayan hannunta ta goge y'ar k'wallar
da zata ta fad'o mata.
"Momy kina jinsu ba kiyi magana ba? Sunci sun
koshi wai har ita wannan tana da baki? Yaushe
kika samu y'ancin kai dan kin tashi a JUYA?
Shine har zaki wani hau fallin fararo budurci
bayan haihuwa?... Cikin sauri Maryam tace
"Dallah rufe mana baki, ki bari y'an gidan masu
y'ancin magana suyi, dan yanzu sunan JUYA ya
koma naki... Tunda gado ta zame muku sai ki
haiho...
Kanta suka yiwo ita da Huwaila, tuni Maryam
taci damara,Fure na ganin haka ta shiga t'sakiya,
yayin da Ahmad suke kuts'o kai dan jin abin na
yawa,
"d'uk wanda ya ta6a ta wallahi zan zage muci
uwa a gidan nan dashi... Ido ta rufe tare da
sauya musu kama "hakuri ba hauka ne ba, kar ku
kaini bango Wallahi.
"Kuma ki sani haihuwar ba gado bace, dan da
tuni yaya Babba(Aunty Jidda) ta gada, ba gado
bace, wallahi da tuni nima na gada, ba gado
bace, dan da tuni kowa a duniya ya gadeta, dan
ba dan uban da aka ta6a ruwan shi daga sama
ya fad'o, kowa uwa ce t haiho Shi a duniya.
By
Feenat Ja'afar.
[5/4, 11:53 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA"
漏 Feenat Ja'afar.
49_ If you feel so high? Then Stay away.. Or
else.. K'yam suka t'saya, baki sake suke k'allon
Fure tai turanci,
"Wa? Da wacce ta isa ta dake ni ne ina k'allo? Ai
wallahi da mutum ya debi hakoranshi a kasa, na
rantse.
"Toh ba anan ba, sai d'ai ku tafi gidan uban ku
yau, ku tattare ku kara mai, aje inda aka fi
k'wari.
Baki Maryam ta ta6e tana since damara, yayinda
da Fure ta rint'se ido.
"A gaskiya bazan iya fita ba izinin mijina ba, kiyi
hakuri Aunty Jidda... Cikin fusata ta tashi tana
huci,
"Are you challenging me?.. Murmushi Furen tai,
kan ta girgiza kai,
"No,am not, sai Aunty Jiddan tai murmushin
mugunta, sai dai kan tai magana Fure ta karasa
da "Amma "If it comes to that... Sai ta juya
bayanta tare da rint'se ido.
"Then i challenge you"....
Su kam su Ahmad jin abin na yawa yasa sukai
cikin parlourn.
Aunty Jidda tace
"Eyeee... Lalle kin koshi Fure... Uban waye
gatanku a garin nan? Da sauri tace "Allah, da
kuma...
Marin da Momy ta sau mata mai mot'si ne yasa
ta kasa karasa wa tare da yin baya zata fad'i taji
an rukota da Hannu da yawa.
Sanye yake cikin farar "suite" da "purple" d'in
y'ar ciki, sosai yai k'yau, da ganinshi Naira ta
zauna mishi, ganan fatar nan tai k'yau... "Ya
Suleiman, cikata Ahmad d'in yai,dan Ya Suleiman
yafi rukota, da gudu maryam ma tai yo wajen shi,
kwai sai suka ruk'unk'umeshi tare da sakar mishi
kuka. Hannu yasa d'uk ya zagaye kafad'un su,
har wani ka'rkarwa jikinshi yake,tuni ran y'an
maza ya tashi.
Cikin Azama zai gun Momy Fure ta rike shi, kai
take girgiza mishi hawaye na zuba,ganan kukan
dan Maryam ya karad'e parlourn, kawai sai ya
rint'se ido, tare da cije le6e.
"Muje, kan na aikata kuskure Maryam, Furera
d'akko shiga ki fito. Kai ta sunkuyar, kan ta dago
su kan Ahmad, wanda idonshi rintse bazaka gane
halin da yake ciki ba.
"Ahmad, ka ban izinin fita dan Allah.
Ido a rint'sen yace "ki bi umarnin su Momy, ki je
gida Furera, kije...
Kawai ya juya ya fice a parlourn cikin sauri.
Ido ta rint'se, wato taje? Kawai sai ta k'ada kai.
"Sai ai gaba ya sallama ki, Huwaila tace "kuma a
bar mana yara.. Harara Maryam ta sakar mata,
"ko baku fad'a ba, dan mu kad'ai aka kawo
mu,babu su cikin garar auran mu.
"Ku barsu Fure,ku saman a mota. Wajen Hasna
Fure tai, tana a k'wance ta fara ko'k'arin goyata
Rukayya tazo, "bakiji ki bar mana yara ba aka
ce? Tana jin tana ko'k'arin d'auke ta ta dago a
tunzure ta sau mata mari, "uwar kice tai min
nakudar da zan bar muku yara na? Eh? Toh naga
wanda zai t'sayarni in ya haifu.
Jan Rukayyan Aunty Jidda tai, "ku k'yale su suje,
mey za kici da yaran bare a huce a kanki?
Ko ta kansu basu kara yi ba su Ada sukai waje
da sauran, fure ta d'akko hijab, yayinda d'an
gidan Maryam ke t'sala kukan ta d'auke shi,
t'sawa ta daka mishi, "ai ba inda zaka bini
yaro,tuni ta yakice shi tai waje,kasa yai yana
bori da kara jiniyar kukan shi.
A bak'in gate Fure ta dago tana k'allon Ahmad
dake cikin motarshi a k'ulle, da sauri ta d'auke
kai ganin zai k'allota ta shige mota.
By
Feenat Ja'afar.
庐NWA.
9/29/16, 2:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 50_Suna ko'k'arin jan
mota sai ga nan Muh'd yai sauri fita a tashi yazo,
t'sayawa ya Suleiman yai tare da K'awar da
kanshi, tuni Maryam ta k'ank'ance ido, kofar ya
bud'e, "Ya Suleiman ka'r kai haka, "Maryam ka'r
ki tafi, dan Allah Aunty Furera kuyi hakuri, yanzu
AAA ya kira ni, mey yai zafi haka?... "Ka shiga
daga ciki zasu kora maka bayani, sannan tafiya
kam nayi na gama, wallahi ka ma biyo ni da
takkadda ta.. Murfin motar ta ja, tuni Fure ta sau
kuka lokacin da Ya Suleiman ya ja mota, shi kam
Muh'd ya ma kasa komai. Da sauri ya juya jin an
dafa kafad'arshi, AAA ne idonshi yai jajir, "ka
shiga ka d'akko yaron ka ciki yana kuka, ka'r ka
kula kowa,kawai ka fito mu tafi, kai ya k'ada
mishi. Rukayya

Please Login or Register in order to submit comment