You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya kisa.
Da mamaki yake kallonshi yace kai yanzu har ka yadda da ta yi kisan.
Kallonshi yayi yace a'a me zai hana in k'i yadda bayan mutanen da takashe hatta lauyoyinta ma bata barsuba saida takashesu mun fa dad'e muna fafatawa akan wannan shari'ar kusan wata goma kenan, na tabbata dan baka ta'ba zuwaba kaga shara'ar da kaima abun sai ya baka mamaki ai gobe nasan dole ayanke mata hukuncin kisa saboda batada lauyan da zai tsaya mata inma akwai to tabbas babu abinda zai iya yi.

Murmushi Barr Faruk yayi cike da jin dad'i dan yasan tabbas Barr MB baisan shine lauyan da zai tsaya mata ba, gyara zama yayi cike da jin dad'in bayanin da yake kora mashi yace ammah Barrister taya akayi ita yarinyar tabi manyan mutanen takashe su kuma har suka iya tsayawa?
Dariya Barr MB yayi yace toh nima dai abinda ban saniba kenan dan nidai anbiya ni kud'in aiki ankuma fad'a min itace tayi kisan tadinga binsu d'aya bayan d'aya tana kashewa kuma abinda zai baka mamaki daga danginta sai abokan mahaifinta takashe.

Barr Faruk idanu yazuba mashi yana kallonshi yace toh wanene yashigar da k'arar?

Shuru yayi sai chan yace mutane ukku ne kuma duk abokan mahaifinta ne d'aya daga cikinsu ya je gidan yatarar da ta yi kisa nan take gargad'inshi da shima yashirya tana nan zuwa gareshi shine yakira police aka kamata bayan ya koma gida daga nan yashigar da k'ara a kotu

Jinjina kai Barr Faruk yayi yace saidai har yanzu ban gamsu da hakan ba.
Murmushi Barr MB yayi a karo na biyu yace koma menene ni ban damuba tunda an lale min kud'ina yanzu jira nike agama shara'ar a ida cika min kud'ina.

Girgiza kai Barr Faruk yayi yace ammah hakan ba daidai bane.

Barr MB har ya bud'e baki zaiyi magana kome yatuno sai kuma yafasa yace ina saurarenka minene yake tafe da kai kayi min Kiran gaugawa haka.
'Dan yatsina fuska Barr Faruk yayi yace daman zuwa nayi mugaisa dan kwana dayawa rabon da muhad'u tunda nabar aiki a court d'inku.
Barr MB ba dan ya yardaba yace toh shikenan Nagode kasan yanayin aikin ne namu sai ahankali.
Hakane Allah ubangiji yataimaka mana.
Ya Amsa da Ameen nan sukayi sallama yafita daga motar shikuma yaja motarshi yatafi

Yana isa gida bai lura da su Dad da suke parlour zaune ba har zai haura saman step sai jin muryar Dad yayi ya ce Shalele.
Tsayawa yayi tare da juyawa yadawo yana murmushi yazauna yace Dad ashe kuna nan ban lura da ku ba.
Momcy ce tace taya zaka lura da mu ka shigo wani a birkice da kai.
Sosa k'eya yayi yace wallahi momcy gajiya ce nayi.
Uhm daman inba gajiya ba minene acikin aikin lauya aini da ka bi ta tawa da bakayi aikinba.
Daddy yace a'a Nuratu kidaina wannan maganar dan bata daceba albarka kawai yakamata musa mashi acikin aikinshi dan yana bakin k'ok'arin shi kuma ni abun alfahari na ne inga d'ana ya kasance jajirtacce.
Momcy cikn sanyin jiki tace hakane Alhaji.
Daddy yace yauwa,,sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yasunkuyar da kanshi k'asa yace Son daman akan maganar sa ranar aurenka da Nasiba wata nawa kakeso asa?
'Dago kai yayi yakalleshi cike da jin dad'i yace Daddy ranar aurenmu za'a tsaida?
Murmushi Daddy yayi yace Eh haka nake buri Son dan yanzu auren ne yadace da kai tunda ka samu aiki sannan shi Alhaji Sufyan shi yakirani waya yace mufito atsaida ranar aurenku.
Sunkuyar da kai yayi cike da jin kunya yace Daddy duk lokacin da kuka tsaida ya yi min.
Momcy tace shegen gora ji yadda ya marairaice kamar duka ammah tunda yace haka kawai Alhaji asa shekara guda.
Saurin d'agowa yayi yace shekara kuma momcy?
Momcy da Daddy ko me zasuyi inba dariya ba, Faruk mik'ewa yayi cikin sauri yabar wajen.

Koda yashiga part d'inshi sosai yanuna farin cikin shi akan ranar aurensu da za'a tsaida nan yakira Nasiba yafad'a mata itama tayi ta murna.

Suna gama wayar tashi yayi yashiga wanka yana cikin wankan yaji kamar giftawar mutum ta wajen toilet din saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba dan haka yad'auko towel yad'aura yafito yadudduba ba kowa cikin d'akin dan shi daman ya san dakanshi yarufe k'ofar da key nan yakoma ya ida wankanshi yafito yashirya yasafko parlorn k'asa yayi lunch d'inshi sannan yakoma part d'inshi yakashe wayoyinshi dan yasamu yayi aikinshi cikin nutsuwa.

File d'in jawahir da aka bashi yad'auko yasake dubawa tare da duba bayanan da yatattara akanta daga k'arshe yabud'e laptop d'inshi yacigaba da bincike sallah ce kawai take tadashi daga inda yake har k'arfe sha biyun dare yayi bai san tayiba yana nan yana aiki, momcy ma da taga bai fitoba saidai takawo mashi dinner d'inshi a nan d'aki.

Har wajen k'arfe d'aya yana nan yana aiki, hamma da yafara ne yasa ya ayyana a ranshi zai tashi yaje yakwanta ahankali yafara jiyo taku a chan k'asan bene kamar ana hawa step k'arar takalma masu tsini ana k'was k'was, shuru yayi yana saurare sai jin k'arar yake ta k'i k'arewa daga karshe yaji kamar anyo wajen d'akinshi cike da rashin tsoro yamik'e yaje yabud'e k'ofa sai ji yayi tsit k'arar ta daina lek'awa yayi baiga kowaba dan haka yamaida d'akin yarufe yazo yakashe laptop d'inshi yashige bedroom alwallah yayi yai sallah raka'a biyu sannan yahaye saman gadonshi saida yatofe jikinshi da addu'a sannan yakwanta bai dad'e da kwanciya ba bacci yakwashe shi.


Washe gari wajen k'arfe tara yagama shirinshi dan da k'arfe goma za'a fara gabatar da shara'a sama sama yayi breakfast nan iyayenshi sukayi mashi addu'ar samun nasara sannan yatafi lokacin da ya isa kotu ta cika makil Alk'ali kawai ake jira ya iso daga chan gaba yaje wajen da Barr Bilal yakama mashi yazauna nan suka gaisa da sauran lauyoyin suna a haka alk'ali ya iso nan kowa yamik'e tsaye har saida yaje yazauna sannan su ma suka koma suka zauna.
Me karanta k'ara ne yatashi yafara yin sallama sannan yace a yau 2 ga watan marich wanda yai daidai da 6 ga watan rajab... Shara'ar farko da zamu fara gabatarwa itace shara'ar indo wadda ake zargi da kashe d'an kishirta dan haka kotu tana buk'atar indo tabayyana a gabanta, wata mata ce tafito idanuwanta kumbure saboda tsananin kuka me gabatar da k'ara juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace indo.
D'ago kai Alk'ali yayi yakalli wadda aka kira da indo sannan yasadda kai yayi yan rubuce rubuce yace kotu tanaso indo tabayyana mata yadda akayi takashe d'an kishiryata......

Haka aka gama shara'ar indo aka yanke mata hukuncin da yadace nan aka sake kiran wata shara'ar wani da yake zargin abokinshi da shigowa gidanshi cikin dare yayi mashi sata, and'auki lokaci ana tattaunawa kowa lauyanshi yana k'ok'arin kareshi inda daga k'arshe aka gane makwabcinshi ne yashiga yayi mashi satar.


Ana gama yanke hukunci nan me gabatar da k'ara yamik'e yace sai shara'a ta gaba wadda itace ta k'arshe a yau itace shara'ar Jawahir wadda ake zargi da kisan mutane bakwai, wadda iyalan mamatan suka shigar da k'ara wata goma da suka wuce.
Alk'ali d'ago kai yayi yace kotu tana buk'atar ganin wadda ake k'ara.
Me karanto k'ara ne yasake maimaita abinda Alk'ali yace.
Ma'aikatan gidan yari ne mata biyu suka tafo suna janye da ita har wajen da aka tanadar mata dan tatsaya.
Me karanto k'ara yace ga jawahir wadda ake k'ara nan ta bayyana.
Alk'ali yace kotu tana buk'atar ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara.
Barr MB ne yamik'e yace Assaalamu Alaikum nine Barr Mahamud Bello lauyan da yake tsaya ma masu k'ara.
Jinjina kai Alk'ali yayi yaduk'a yayi yan rubuce rubuce nan Barr MB yazauna, me karanto k'ara yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara idan akwai.
Shuru kotu tayi ana jira aga wane me kasada ne wanda yagaji da rayuwarshi yatsaya ma jawahir.
Jawahir da take tsaye duk'ar da kanta tayi idanuwanta sun cika taf da k'wallah.
Barr Bilal ne yad'an ta6o Barr Faruk da yafad'a duniyar tunani daidai lokacin da aka sake maimaita ana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara, ahankali yamik'e tsaye yayi sallama yace nine Barr Faruk Sani Maishadda lauyan da yake kare wadda ake k'ara, gabad'aya kotun d'auka tayi da surutu, jawahir dakyar ta iya d'aga kai takalleshi lokacin shima ita yake kallo ko kad'an bataso hakaba taso ace ya bari anyanke mata hukunci,
'yan sanda ne suka shiga nutsar da mutanen da suke kallon shara'a, Barr MB da mamaki yake kallonshi yai mashi irin kallon nan na haka kayi min?
Alk'ali jinjina kai yayi nan Barr Faruk yakoma yazauna.

Alk'ali d'agowa yayi yace kotu ta ba lauyoyi dama idan da mai kwakkwarar shaida yatashi yagabatar da ita inkuma wadda ake tuhuma tana da abinda zata kare kanta akan tuhumar da akeyi mata na kisan kai akaro na hud'u da akayi zaman kotu toh bismillah
Shuru jawahir tayi still dai kanta yana sunkuye a k'asa.
Mai karanta k'ara ne yasake karanta abinda Alk'ali yace nan tayi shuru .
Mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama inma Jawahir wasu yan tambayoyi.
Alk'ali yace kotu ta baka dama.
Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yataka ya isa inda jawahir take tsaye yace Malama jawahir shin ko zaki iya sanar da kotu dalilinki na kashe wad'annan bayin Allahn da kikayi?
D'ago kai tayi takalleshi da Idanuwanta da sukayi jajir tana so tabud'e baki tayi magana ammah ta kasa bakin nata taji kamar anrike mata shi.
K'ara maimaita mata tambayar yayi ammah shuru saidai kallonshi da takeyi.
Murmushi yayi yace idan wannan tambayar batada amsa toh ga tambaya ta biyu a lokacin da Alhaji Tanimu yashigo yasameki kinyi kisa kinyi mashi barazanar zaki kasheshi shima haka ne ko ba hakaba?
Still dai shuru jawahir tayi saidai hawayen da suke gangaro mata.
Murmushin mugunta yayi yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a yakamata kotu tagaugauta yanke ma jawahir kisa daidai da laifinta da tayi na kisa saboda batada amsar da zata iya badawa a wannan tambayoyin da nayi mata yakamata kotu tayadda da cewa jawahir itace wadda tayi kisa tayi amfani da mark ajikin hotunan wad'anda takashe, d'auko hotunan yayi yamik'a aka mik'a ma Alk'ali.
Duba hotunan Alk'ali yayi nan Barr MB yacigaba da cewa tabbas Jawahir ta shek'a wad'annan bayin Allahn lahira batare da ansan dalilinta na aikata hakan ba wanda daga k'arshe tahad'a da lauyoyin da suka kasance suna nema sukare ta.
Jawahir runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawaye suka gangaro mata.
Barr Faruk ne yai saurin mik'ewa tsaye yace ya me girma me shara'a ya kamata kotu tagargadi Barr Mahmud Bello akan munanan maganganun da yake jifar wadda ake k'ara da su.
Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta amshi k'orafinka dan haka kai barrister kagyara kalamanta.
Dan rissinawa Barr MB yayi yace nagode ya me girma me shara'a ina Neman afuwa
Sannan yajuya yakalli jawahir yace ko zaki iya kare kanki akan wannan laifin?
Shuru jawahir tayi tana mecigaba da kallonshi.
Juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tagaugauta yanke ma Jawahir hukunci dan batada amsar da zata iya kare kanta da ita.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace ina da ja ya me girma me shara'a ina so kotu taban dama zan d'anyi wasu tambayoyi ga iyalan mamata.
'Yan rubuce rubuce yayi sannan yad'ago yace kotu ta baka dama.
'Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yafito yatsaya nan Barr MB yakoma yazauna cike da jin haushi dan ba haka yasoba.
Me karanta k'ara ne yamik'e yace kotu tanason ganin iyalan masu k'ara sugurfana a gabanta.
Daga chan cikin jama'ar da suke zaune kallon shara'a wasu mutane goma suka fito sukazo gaba wajen da aka tanadar suka tsaya, matsowa Barr Faruk yayi kusa da su yace ku ne iyalan wad'anda suka rasu?
Dukansu d'aga kai sukayi alamun Eh.
Murmushi yayi yace ko zaku iya ma kotu bayani akan mutuwar mamatan shin akwai wanda yaga lokacin da jawahir tazo gidan takashe su?
Kame Kame suka fara suka rasa tayadda zasuyi bayani .
Barr Faruk sake jefo masu tambaya yayi yace munaso kuyi mana bayani yadda akayi kukasan itace tayi kisan nan ma sukayi shuru suna kallon gefe d'aya juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tawanke jawahir daga laifin da ake zarginta da shi dan babu wanda zai iya bada shedar cewa Jawahir ce tayi kisan, saurin mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata kotu tasa Barr Faruk yagyara kalamanshi dan yana nema yazargi wani na daban bayan kuma kowa ya san itace tayi kisan tun daga mark d'in da ke jikin wad'anda aka kashe.
Jinjina kai Alk'ali yayi, Barr Faruk juyawa yayi yace ina neman afuwa ya me girma me shara'a saidai ni ina ganin har yanzu basu bada kwakkwarar shaida da tanuna jawahir ce tayi kisan ba,
Alk'ali yace miye hujjarka na cewa haka?
Barr Faruk yace saboda ko lokacin da su Barr muhsin suka rasu and'aura zargi akan wannan baiwar Allahn alhali lokacin tana nan gidan yari ana tsaronta taya zata fita har tayi kisa tadawo.
Barr MB a fusace yace ammah ai kowa yasan itace tayi.
Juyawa Barr Faruk yayi wajenshi yace shin a matsayinka na lauyan masu k'ara tunda su sunkasa yin magana munaso kafad'a mana a lokacin da jawahir tashiga gidajen mamatan ance wasu da dare takashesu shin ta wace hanya tashiga gidan alhali gidan rufe yake ko su basu rufe gidajen su?
Juyawa Barr MB yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tambayoyin Barr Faruk sunyi ma masu shigar da k'ara tsauri saisa suka kasa bashi amsa sannan jawahir ana zarginta da yin layar zana ta wannan hanyar ne take zuwa tayi kisan, ya me girma me shara'a yakamata kotu taduba bayanina da yadda akayi jawahir takasa kare kanta a lokacin da nayi mata tambaya.
Alk'ali duk'awa yayi yai yan rubuce rubuce yad'ago yakalli jawahir yace shin ko zaki iya kare kanki akan tuhumar da akeyi maki?

Barr Faruk kallon jawahir yayi da take ta hawaye ta kasa cewa komai kowa ya zuba mata idanu yana jiran tayi magana chan dai tagirgiza kai, Barr Faruk maida kallonshi yayi ga Alk'ali yace ya megirma me shara'a muna nema kotu tataimaka mana tad'age k'arar nan zuwa zama na gaba domin akwai binciken da muke wanda bamu idaba a matsayina na lauyan wadda ake k'ara kuma saboda k'arancin lokacin zuwana bai sa nasamu na ida bincike na ba ina neman wannan alfarmar kotu taduba min.
Murmushin nasara Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata kotu tayi watsi da wannan alfarmar da barristern wadda ake k'ara yanema domin baida wata kwakkwarar shaida da zai iya kare wadda ake k'ara da ita, munaso kotu ta gaggauta yanke ma wadda ake k'ara hukuncin da yadace da ita.
Shuru Kotun tayi har saida alk'ali yagama rubuce rubucenshi yad'ago yace barrister Faruk kotu ta amshi uzurinka a matsayin lauyan wadda ake k'ara wanda bai dad'eba da tsaya mata dan haka kotu ta baka dama kaje kakawo mata kwakkwaran shaidar da kace ba ita tayi kisan ba, zamu d'age wannan k'arar zuwa 2 ga wata nagaba watau wata d'aya me zuwa insha Allahu shi muke fata yakasance zama na k'arshe,,,,yana fad'in haka yabubbuga table.
Barr Faruk wani irin dad'i yaji a ranshi dan yasan wannan hanyar kawai zaibi yaku6utar da jawahir saboda baida hujjar da zai iya kareta, inda shikuma Barr MB yaji kamar yabuge kowa saboda haushi.

Jawahir fashewa tayi da kuka dan ba haka tasoba haka matan suka riketa suka tafi da ita prison.

Haka aka tashi Shari'a masu murna sunayi masu bak'in ciki suna yi.


_*Free page*_


_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_


_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_






_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/11, 21:25] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]



*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*


*PAGE NINE*

Barr MB suna fita yanufi wajen Barr Faruk da yake shirin shiga motarshi yana zuwa murmushi yayi yace Barrister kenan wane tsotsai yakaika tsaya ma Jawahir ina ce ko ka gaji da rayuwarka ne saisa?.
Shima murmushin yayi yace kusan haka dan daman ita mutuwa akowane lokaci zuwa takeyi.
Tab'e baki yayi yace hakane daman ashe kaine lauyanta shine kazo kabugi ta cikina kaji sirrina?
Cikin rashin damuwa yace wannan ai ba wani abu bane tunda duk cikin aikinmu ne.
"Na san da haka saidai kai na san bakasan komai ba akan case d'in jawahir dan haka Kataimaka ma kanka kajanye daga tsaya mata".
Kar kadamu barrister kai shaida ne bana bayan k'arya akowane lokaci bayan gaskiya nakebi dan haka kai zan ba shawara kajanye kar kad'aure ma k'arya gindi inma kud'i aka baka kamaida masu abinsu.
Barr MB Katseshi yayi yace kai kana ganin kaine akan gaskiya nima haka nake gani dan haka muhad'e kawai wata me kamawa idan Allah ya sa rayuwarka ta kai.
Dariya Barr Faruk yayi yace toh Allah yakaimu nan yabud'e motarshi yashiga yabar Barr MB duk haushi ya cikashi.

Barr Faruk yana komawa gida wanka yayi yashirya yafita parlour dan yayi lunch momcy ce tafito tana fara'a tace Son har andawo?
Zama yayi saman cushion cike da nuna gajiya yace Eh Momcy.
Itama zama tayi gefenshi cikin nuna tausayawarta tace sannu son da alama ka gaji dayawa ina fata dai anyi nasara?
Murmushi yayi yafad'a ma momcy yadda akayi,,,ta tausaya ma jawahir sosai koda bai fad'a mata ainahin abinda akayiba ya 6oye mata dan kar tatada hankalinta tanuna bata yadda ba yasa yace mata kawai zarginta akeyi da laifin kisa kuma baya tunanin ita tayi saboda yarinya ce k'arama.
Addu'a tayi akan Allah yataimaka yaku6utar da ita idan har batada laifi aciki.
Ya amsa mata da Ameen.
Fitowar Daddy ne yasa suka gaisa shima yayi mashi sannu da dawowa sannan suka d'unguma zuwa dining area dan suyi lunch, suna cikin yi Dad yakalleshi yace Son gobe fa za'ayi baikonka da Nasiba.
Murmushi yayi me nuna jin dad'i yace toh Daddy na gode sosai, wata nawa za'a tsaida bikkin?
Shuru Daddy yayi sai chan yace ina tunanin bazai wuce wata ukku ba dan Dad d'inta ya ce bayaso aja lokaci dayawa kuma mu ma bamuda matsala mun gama shirinmu tunda hatta gida kana da shi.
Momcy tace hakane Alhaji nima kaina bansan aja lokaci dayawa saisa nanuna farin cikina da akace baza'a fi wata ukku ba.
Faruk yana jinsu saidai yayi murmushi yacigaba da cin dinner d'inshi.


Bayan sallar la'asar yana dawowa daga masallaci ko gida bai shigaba yashiga motarshi yabar gidan yakama hanyar prison.

Jawahir tunda aka maidata a cikin d'an kurkukun d'akinta bajewa tayi a k'asa tana wani irin kuka me cike da k'ara, duk tacika wajen da kuka wasu ma'aikatan gidan ne sukazo da manyan bulalai suka sameta nan suka kwatsa mata tsawa sukace tayi masu shuru dakyar ta iya danne kukan nata saidai hawaye da take idanuwanta duk suka k'ank'ance maida idanuwanta tayi tarufe bata sake bud'e suba saida Barr Faruk yazo batare da ta bud'e idanunba tana jin abud'e k'ofar anshigo cikin muryar kuka tace bance maka kar ka kuskura kashiga acikin wannan maganar ba? Sau nawa nafad'a maka mutuwata tafi rayuwata amfani, Miyasa bazaka ji maganar da mutane suke fad'a ba akaina, dakyar tabud'e idanunta tace barina in rayuwa a doron k'asa tamkar kashe d'an maciji ne ba'a sare kanshiba, shawara zan baka kabi maganar da sauran mutane suka fada maka karabu da ni gudun kar matsalata ta shafeka.
Matsowa yayi kusa da ita cikin sanyin jiki yace jawahir ban damuba kowace irin matsala tasameni dan ni na riga da nasa ma raina ina da burin taimakonki komai zan iya yi dan ganin kin fita daga gidan nan saboda zama nan baidace dakeba.
Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tace Barrister Kaine kake ganin haka ammah ni rayuwata a cikin d'akin nan ta fiye min kwanciyar hankali akan bala'in da nake ciki wanda barina gidan nan zai iya shafar kowa.
Cike da mamaki Barr Faruk yace wane irin bala'i ne kike ciki haka? Shin ko zani iya saninshi?
Tashi tayi zaune tace saninshi zai iya sa kaima yashafeka bazan gaji da fad'a makaba kanisantar da kanka daga gareni.
Jawahir nayi maki alk'awalin zan taimaka maki da dukkan k'arfina.
'Dan guntun murmushi tayi tare da janye kanta gefe.
Barr Faruk yace nasan ba lallai ne kiyarda daniba dan kina min kallon kamar halayyata iri d'aya ce da tasu barrister muhsin saidai ni ba haka nakeba kiyarda da ni.
Girgiza kai tayi tace ba na ji akwai wanda zan iya yarda da shi a wannan lokacin har zuwa k'arshen rayuwata.
Jawahir ya kamata kifahimceni banzo da niyar cuta agarekiba kitaimaka kiban had'in kai dan inwanke ki daga zargin da duniya takeyi maki.
Wani irin kallo tayi mashi tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargi ne?
Koma minene Jawahir ina da burin taimaka ma rayuwarki,
shuru tayi na d'an lokaci kamar tana nazarin wani abu sai chan tayi murmushi tare da goge hawayenta kamar ba ita bace tagama kuka tace shikenan tunda ka ce zaka taimaka min saidai duk matsalar da kashiga kar kayi kuka da kowa sai kanka.
Cikin nuna rashin damuwa yace na amince da haka, dan haka inaso kiban tarihin rayuwarki.
Mik'ewa tayi tsaye tana tafiya dakyar har ta isa wajen yar k'aramar tagar da take yawan tsayawa wajenta,,ganin kamar bataji abinda yaceba yasa Barr Faruk yasake maimaita mata.
'Dan guntun murmushi tayi batare da ta juyoba tace na amince zan fad'a maka tarihin rayuwata ammah ba anan ba saidai idan zaka fitar da ni daga kurkukun nan muje wani waje dan Indai a nan ne na tabbata zamu shiga matsala daga ni har kai dan matsalata zata iya shafarka, bazata ta'ba barinkaba.
Shuru Barr Faruk yayi kamar yana nazarin maganarta sai chan yace wace irin matsala zata shafeni?
Kowace irin matsala zata iya shafarka Indai har kanason jin tarihina saidai kayi yadda nace maka.
Ajiyar zuciya yasafke yace shikenan Jawahir zan kwatanta hakan zanje in nemi amincewar shugaban gidan nan in ya amince sai mu fita muje wani wajen zuwa gobe.

Baya baya tafara ja lokaci guda muryarta tafara rawa tace kayi gaugawan barin wajen nan yanzu.
Da mamaki yake kallonta yace saboda me?
Juyowa tayi fuskarta cike da tashin hankali cikin d'aga murya tace na ce kabar wajen nan katashi kafita!
Ganin yadda lokaci guda tabirkice yasa yamik'e yawuce yafita cike da mamaki, bayanshi Jawahir tabi cikin sauri tajanyo k'ofar tarufe tare da ja da baya ahankali taje chan wajen kusurwar d'akin tatsaya jikinta gaba d'aya rawa yake nan tayi saurin zama tare da dunk'ule jikinta waje guda tadafe kanta da dukkan hannuwanta.
Barr Faruk yana tsaye yana kallonta ta 'yan hudojin k'ofar yana jiyo sautin kukanta ahankali da magana wadda bazaice ga abinda take cewaba chan kuma sai yaji ta shuru.

Ji yayi kamar yashiga d'akin dan yagane ma idanunshi abinda yake faruwa da ita sai kuma yafasa yawuce suka tafi.

Yana fita direct office d'in shugaban gidan yarin yawuce yana zuwa yashiga lokacin wasu files ne hannun Alhaji mahadi yana dubawa yana ganinshi Murmushi yayi yace ya dai abokina har ka gama?
kujera faruk yaja yazauna yace abokina dan Allah wata alfarma nazo nema a wajenka.
Alhaji Mahadi yace haba alfarma kuma? Ina jinka
Numfasa yayi yace Jawahir nakeso ataimaka a ara min ita zuwa gobe zan fita da ita saboda zan d'auko wani bayani ne wanda itace zata taimaka min wajen d'aukoshi a matsayina na lauyanta.
Zaro ido mahadi yayi yace fita fa kace zakayi da ita daga gidan yarin nan?
Cikin nuna rashin damuwa yace Eh kuma insha Allahu da nagama abinda zanyi zan maidota.
Girgiza kai mahadi yayi yace kayi hak'uri Barrister gaskiya hakan bazai yuwuba kafita da ita dan tana cikin tsaro me tsanani fita da ita laifi ne a k'a'idar aikin nan ba'a

Please Login or Register in order to submit comment