You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ace ba kai bane babu wanda zaice inje gidan in amince inje dan ina tsoron gidan kamar yadda nake tsoron yarinyar chan.
Murmushi Barr Faruk yayi yace kaifa ka ji matsalar ka tsoro wani abu ne akace ke akwai acikin gidan?
Ni ban saniba ammah tunda har yarinyar tafito daga gidan ai dole yakasance abun tsoro, kabarni incigaba da lazumina kawai.

Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi dariya yake ma Barr Bilal akan tsoron shi da yayi yawa ahaka har suka isa sai ji yayi ya ja mota ya tsaya a gaban wani gida.
Kallon gidan Barr Faruk yayi yace wannan shine gidan?
Girgiza kai yayi yace ga gidan chan gaba.
Da mamaki Barr Faruk yake kallon dank'areren gidan da Barr Bilal yanuna mashi wanda a cikin layin babu gida me girmanshi da kyaunshi koda gidajen wajen suna da kyau sosai yace kana nufin wanchan shine gidan?
Murmushi yayi yace eh ai ba abun mamaki bane ga wanda yasan kud'in megidan nidai ina daga nan bazan k'ara matsawa ko ina ba sai kafita ka ida takawa.
Murmushi Barr Faruk yayi yace shikenan ba damuwa daman nima banaso ka isa har k'ofar gidan saboda na fad'a maka ba da sanin hukuma nazo ba banaso asan na zo kajirani bari inshiga infito.
Cikin sanyin jiki yace toh shikenan Allah yasa kafito lafiya ammah dai kadinga addu'a.


Baice mashi komai ba yawuce yatunkari gidan fitowa Barr Faruk yayi daga cikin motar rik'e da 'yar brief case d'in Faruk dan ya yi tunanin zai tafi da ita sai kuma yaga ba haka ba dan haka yatsaya yana kallonshi cikin ranshi yana mamakin rashin tsoron Barr Faruk.
Yana zuwa k'ofar gidan tsayawa yayi saida yaga babu kowa gaba da baya sannan yad'auko makullen nan yabud'e k'ofar yashiga k'aton fili ne yafara cin karo da shi duk ganyaye suna ta yawo a tsakiyar filin hango k'ofar da zata sadaka cikin gidan yayi yaga rufe take nan yataka ya isa yana zuwa yasa gudan key d'in yabud'e duk ya'nah ce da k'ura shiga yayi yana bin part parts d'in gidan da kallo yana tunanin wane part yakamata yashiga tunowa yayi da mafarkin da yayi d'akin da yagani tabbas kamar parlor ne koda babu kaya a cikinshi toh ammah wane parlorn daga ciki? Tsaye yayi yarasa wanda zai shiga ya yi kusan minti biyar tsaye a wajen shi kad'ai sai chan yafara tunanin labarin jawahir a k'arshen inda tatsaya mashi murmushi yayi yace babban parlor zan shiga cikin sauri yanufi wajen parlorn yana zuwa yatura k'ofar yajita a rufe makullen da suke hannunshi yasa zai bud'e ammah yak'i bud'uwa daga chan gefe yajiyo k'ara kamar ansa key anbud'e wani d'aki waiwayawa yayi baiga kowaba dan haka yaje yafara tura k'ofofin d'akunan saidai dukkansu a rufe suke ta k'arshence yana turawa yaji a bud'e ajiyar zuciya yasafke tare da kallon k'ofar d'akin tabbas k'ofar ce yagani acikin mafarkinshi ahankali yafurta Alhamdulillah!
Tura k'ofar d'akin yayi yashiga ya'na ce tafara yi mashi sallama a fuska yayi saurin cireta nan yaja yana bin d'akin da kallo k'ura ce sosai aciki kasancewar gidan ya dad'e babu kowa a cikinshi tsaye yayi yana tunanin ta ina zai fara neman Memory Card d'in da zai taimaka mashi wajen samun k'wak'warar shedar da yake nema kuma tabbas yana cikin d'akin, saidai baisan ta inda zai faraba bayan duk tulin k'urar dake cikin d'akin runtse idanunshi yayi yana ji kamar yajuya yakoma baya saidai tabbas yasan sai ya samo Mcard d'in sannan zai iya samun abinda yake nema.

Maganar jawahir ce ta cikin mafarki tafara dawo mashi lokacin da yaga ta jawoshi ta shigo da shi cikin gidan ta nuna mashi wani d'aki mai jan k'ofa tace kashiga nan a nan cikine kawai zaka iya samun memory d'in daga farkon d'akin zuwa tsakiyar d'akin kar kawuce nan zaka sameshi tana fad'in haka ta'bace.

Bud'e idanunshi yayi cike da k'warin gwiwa yaduk'a yafara lalube a cikin tulin k'urar dake k'asan dakin a nutse yake lalube daga yad'auko dutsi sai yad'auko wasu abubuwan ahaka har saida yazo tsakiyar d'akin har zai cigaba sai yatsaya ganin ya zo tsakiyar d'akin dan haka yacigaba da lalube sannan yaji ya ta6o wani d'an abu k'arami cikin sauri yadauko goge shi yashiga yi chan yayi murmushi tare da furta Alhamdulillah tabbas shine cikin sauri yamik'e tsaye kawai sai ji yayi k'ofa ta maida kanta ta rufe dak'arfi, juyawa yayi yakalli k'ofar daga bayanshi yaji wata plastic chair da tasha k'ura tana motsi nan ma yayi saurin juyawa ammah baiga kowa samanta ba sai gani yayi kamar anjata tazo dagudu ta wuce fit tagabanshi
A karo nafarko da yaji gabanshi ya fad'i ammah cikin dakewa yace wanene?
Fitilun dake cikin d'akin ne suka fara d'aukewa suna kawowa nan yayi saurin juyawa zaije wajen k'ofa sai gani yayi hasken d'akin ya d'auke koda da rana ne ammah wani irin duhu yabayyana har baya ganin abinda yake gabanshi Memory Card din yayi saurin zurawa acikin aljihunshi yad'auko wayarshi dan yahaska sai ji yayi anfizge wayar ta fad'i k'asa wata irin dariya yaji anfara cikin wani irin amon murya gabad'aya d'akin yana amsawa, nan yai saurin runtse idanunshi yafara karanta duk addu'ar da tazo a bakinshi.

Murya me k'arfi ce yaji tana tashi tana cewa baka isa kashiga gonata ba bazan ta'ba barinka ba idan har kafita da wannan abun da kad'auka ni na ajiye shi ni nake tsaronshi babu wanda ya isa yad'aukeshi batare da izini na ba.

Hannu yasa cikin sauri yatoshe kunnuwanshi da yakeji kamar dodon kunnenshi zaiyi zillo yafad'o saboda k'arfin muryar cigaba yayi da karanto addu'o'i daga bakinshi wata irin k'ara yadinga ji yai saurin bud'e idanunshi sai ganin wani k'aton dutsi yayi wanda yahaske d'akin ya yo saitin inda yake tsaye cikin sauri yamatsa gefe guda ta gefenshi dutsin yawuce yafad'i rijim a bayanshin nan k'ura tabaje d'akin, tari yafarayi yana son yashak'i numfashi ammah babu ta inda zai ji iska saboda k'urar da tacika a d'akin, duk ya fita hayyacinshi ammah duk da haka bai daina addu'ar da yakeyi ba chan yaji wata irin iska me k'arfi ta taso chan kuma sai yaji iskar ta lafa nan haske yabayyana a d'akin, d'aukar wayarshi yayi da take k'asa yayi saurin fitowa daga cikin d'akin yana tari jawo k'ofar yayi yarufe.


A chan 'bangaren Barrister Bilal dake tsaye waje jikin mota a tsorace yana jiran fitowar Barr Faruk nan yahango wani irin duhu ya bayyana a gidan kallon inda yake yayi yaga haske ammah cikin gidan duhu ne zufa ce tafara kwararo mashi tsoro duk yabayyana a fuskarshi k'afafuwanshi rawa suka fara briefcase din dayake rik'e da ita hannunshi yasaki, bakinshi yana rawa yafara karanta wa'innahu sulaimana wa innahu bismillahirrahmanur rahim ssaids fitsari yakusa yakubce mashi saboda tsoro tunani yayi yashiga mota yagudu kawai dan baya tunanin Barrister Faruk zai fito da rai bare ma yasamu nasarar d'auko abinda yakaishi cikin gidan yana cikin tunanin yaga hasken gidan ya dawo, bud'e motar yayi zai shiga sai ganin Barr Faruk yayi ya fito yana atishawa da tari jikinshi duk ya yi farin k'ura cikin sauri yanufi wajenshi yana isa yace lafiya Barrister ya akayi naganka haka?
Mik'a mashi key d'in yayi alamun yarufe gidan, amsa yayi yarufe sannan yarik'eshi suka nufi wajen mota yana mashi sannu yana cewa saida nace kar kashiga gidan nan ammah kashiga.
Dafe k'irjinshi yayi da yake mashi zafi ahankali yace kawuce da ni gidana.
Amsawa yayi da toh nan yakama hanyar gidan Barr Faruk.









_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_



*PAGE 8*


Suna isa gidanshi a tare suka shiga ciki Barr Faruk bai tsaya sauraren surutun da Bilal yakeyi mashi ba yawuce toilet yana shiga yamaida k'ofa yarufe nan yatsaya a bakin k'ofa yana tunanin abinda yafaru da shi tabbas a yanzu ya ida gasgata maganar Jawahir akan aljanar nan, ya dad'e tsaye kafin daga bisani yasamu yayi wanka yafito, shiryawa yayi cikin kayan shi da yake da su a gidan sannan yafito parlor yasamu Barr Bilal zaune yana shan lemu, yana ganinshi murmushi yayi yace Barrister yanzu har ka fito fes ba kamar lokacin da muka zo ba wai me yafaru da kai?

Zama yayi saman kujera yai shuru kamar bai ji abinda yace ba sai chan har Barr Bilal ya fitar da rai da samun amsar shi sai ji yayi ya ce babu komai kawai dai gidan ne ya yi k'ura sosai saisa kaga na fito duk k'ura jikina.
Barr Bilal ba dan ya yarda ba yace ammah Barrister na hango gidan ya yi duhu babu haske wallahi na tsorata sosai da guduwa zanyi.
Murmushi Barr Faruk yayi yace ni banga hakan ba kaga tashi muje masallaci gashichan anfara kiran sallar magrib.
Mik'ewa sukayi sukayo alwallah suka kama hanyar masallacin da yake a cikin anguwar.

Bayan sun dawo Barr Bilal yayi mashi sallama yakoma gida shi kuma Barr Faruk yayi zaman shi nan dan yasamu yayi aikinshi a nutse, bayan sallar isha'i kiran Dad yayi yace kar atsaya jiranshi bazai dawo gida ba zai kwana a gidan shi saboda akwai aikin da yake a yanzu Dad ya amsa mashi da toh tare da yi mashi addu'ar fatan nasara.


Wajen k'arfe goman dare d'auko laptop d'inshi yayi da yajona charge sannan yad'auko memory d'in yasaka a cikin wayarshi yana kunna wayar wata irin k'ara tayi me kama da tsawa dan har saida yatsorata.
Cikin recording yashiga yaga guda d'aya ne nan yakai hannu zai kunna kamar an fizgi wayar sai ganinta yayi ta k'wace daga hannunshi ta fad'i k'asa mik'ewar da yayi zai d'auko nan haske yad'auke gabad'aya gidan duhu yabayyana duk'awa yayi yafara laluben wayarshi har ya lalubota zai d'auka sai ji yayi anjata ta matsa, tsayawa yayi mamaki duk ya cikashi lokaci guda yaji k'arar bud'e k'ofar bedroom d'in kuma yaga hasken wayar ya kunnu ta d'an haska d'akin hannu yakai a karo na biyu zai d'auka sai gani yayi tawuce ta yi hanyar waje dagudu mik'ewa yayi yana cewa wanene yake ja min waya? Wai wanene?
Shuru yaji dan haka yabi wayar tashi ana cigaba da janta a k'asa shi kuma yana bi har saida sukazo daidai wani d'aki wanda babu komai a cikinshi suna zuwa k'ofa tabud'e ja yayi yatsaya cikin ranshi yana karanta addu'o'i dan lamarin ya fara bashi tsoro yana nan tsaye wayar tashige d'akin baiyi niyar shigaba yana tsaye a cikin bak'in duhun nan yajiyo ringing d'in wayar sai jin muryar Nasiba ta cikin wayar yayi tana cewa Hello Faruk ban ta'ba tunanin zaka iya rabuwa da ni ba Faruk ka san ina sonka dan Allah kadawo gareni,,, tana fad'in haka tafashe da kuka, cike da mamaki yace Nasiba kuma? Kirana tayi a wayar? Jin sautin kukanta yasa yayi saurin shiga d'akin yana shiga k'ofa tamaida kanta da k'arfi tarufe nan hasken wayar yad'auke d'akin yayi dund'um da duhu wata irin sautin murya yaji me kama da kukan hadari ta bushe da dariya duk d'akin ya amsa, Faruk nan fa gabanshi yafad'i ammah kokad'an bai nuna alamun tsoroba yana cigaba da addu'a a cikin zuciyarshi jin yadda ake cigaba da dariyar babu k'ak'k'autawa yasa cikin dakewa yad'aga murya yace wai wanene nan?
Bai rufe bakiba yaji anjawoshi da k'arfi anbuga kanshi da bango wani irin zogi yaji yai saurin sulalewa k'asa yazauna tare da rik'e kan da yakeji tamkar ya fashe, murya yafara jiyowa me k'arfi cikin gurnani ana cewa ka yi kuskure Faruk da har kashiga rayuwata na gargad'eka kar kafito da memory d'innan ammah saida kafito da shi, toh bazan ta'ba barinka ba yau d'in nan sai naga bayanka.
Sai a lokacin yafahimci kowacece tabbas aljanar nan ce ta gidansu jawahir bud'e baki yayi cikin juriya yace baki isa kiga bayana ba saidai ni inga naki bayan.
Sake bushewa tayi da dariya a karo na biyu sannan tace ka yi k'arya kaga bayana zan iya rabaka da ranka a duk lokacin da naso.
A harzuk'e yamik'e tsaye koda babu haske a d'akin cikin d'aga murya yace bazaki iya kasheni ba ammah ni zan iya rabaki da rayuwarki ta hanyar karanta maki ayoyin ubangiji, bai jira jin abinda zata ce ba yafara karanta wasu ayoyi daga cikin alk'ur'ani, wata irin k'ara tafara yi wadda taso tatada 'yar k'aramar girgizar k'asa a d'akin, saurin toshe kunnuwanshi yayi dan yasan k'arar zata iya yi mashi lahani a kunne sannan yana cigaba da addu'ar k'ofar d'akin ce tashiga bud'ewa da rufe kanta dak'arfi chan kuma sai yaji an daina k'arar d'akin ya d'auki tsit daidai lokacin hasken gidan yadawo, ajiyar zuciya yasafke tare da kallon wayarshi da take a k'asa tsakiyar d'akin, zuwa yayi yad'auka hannunshi d'aya yana dafe da kanshi yafita daga d'akin, dudduba saura d'akunan yayi yaji babu wata alama da aljanar za'ace ta shiga dan haka yakoma bedroom d'in duk wannan abun baisa yatsorata ba dan dama Faruk ba dai kafiya ba indai yasa kanshi yin abu babu abinda zai hanashi yana komawa yayi joining d'in wayar da laptop d'inshi yatura recording d'in acikin laptop d'in sannan yakunna wata irin k'ara yajiyo shuuuuu kamar iska dan haka yad'auko wayarshi yakunna karatun alk'ur'ani yasa volume sannan yad'auko earpeace yasaka yakunna recording d'in acikin laptop d'in...


Muryoyine yafara ji suna tashi a ciki hakan yasa yagane cewa cigaban inda tatsaya da rubutun tane acikin diary d'in:



*CIGABAN LABARI*

Jawahir cigaba da kallon Malamin tayi tana nishi inda shima yake kallonta kamar irin zakin nan da yake neman abinci ido rufe, ganin batada niyar shigowa yasa yad'ebo wani abu yawatsa mata wata irin k'ara tasaki tare da ida shigowa d'akin taja tatsaya a gaban malamin, Ummah jikinta rawa kawai yake tana jin kamar tasaki fitsari a nan inda take tsaye, Umar ko wani irin haushi da takaici suka cikashi lokaci guda yafara jin tsanarta cikin ranshi yana cewa tabbas a yanzu na ida gasgatarwa itace tarabani da d'an uwana, Abba ko zufa yafara yi shi kanshi ya tsorata dan bai ta'ba kawo ma ranshi itace take kisan ba.
Malamin kallon su Abba yayi yace kun ganta daman na fad'a maku fatalwa ce take cikin gidan nan.
Su duka sukace fatalwa kuma? Wannan ai jawahir ce kuma bata mutu ba.
Hannu yamik'a yana karanto wani abu me kama da yare sai gata ta tsugunna a gabanshi nan yadafa kanta yana cigaba da karatun nan tafara k'ara chan yasaki kanta yakalli su Abba yace tabbas akwai fatalwa a tare da yarinyar nan kuma itace take tsorata ku.
Umar mik'ewa yayi a fusace yace ba wai fatalwa kad'ai ba jawahir ce take amfani da damarta tana kisa itace takashe su Aliyu, zumbur Ummah tamik'e tace jawahir d'in takashe min d'a? Fashewa tayi da kuka tace akan wane dalili zatayi min haka me d'ana yatsare mata?
Mik'a mata hotunan hannunshi yayi yace gasu a wajenta nagansu tare da wannan wuk'ar kuma ina tunanin next target d'inta Abba ne.
Zuface tacigaba da kwararo ma Abba lokaci guda yajik'e sharkaf kamar wanda aka watsa ma ruwa saurin mik'ewa yayi ya amshi hotunan yana kallo tabbas hoton Aliyu ne da na Abokinshi kuma irin hotunan da aka dinga tsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu
Cikin wata irin firgitattar murya tabushe da dariya wadda tasa saida baki d'ayansu suka juya suka kalleta mik'ewa tsaye tanemi tayi nan malamin yasake watsa mata wani abu me kamar gari nan tafasa k'ara tare da komawa tazauna, a karo na biyu tasake yunk'urin mik'ewa yad'ebo abun zai watsa mata tayi saurin sa hannu takare nan wata irin iska tataso maganin yazube, yunk'urin d'ebo wani yayi nan tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye cikin sauri, muryarta ta rikid'e ta zama kamar irin kukan mafad'acin dokin nan bud'e baki tayi tafara magana wadda tasa gabad'aya d'akin ya amsa sunan Alhaji Mu'az takira sannan tacigaba da ce baikamata wannan yasa kashiga damuwa ba idan har zaka iya tunawa da abinda ka aikata ma d'an uwanka kaine kasa aka kasheshi sannan nima karabani da raina tabbas nasan wannan bokan ne yayi maku aiki akaina bazan ta'ba barin duk wanda yake da hannu ba akan mutuwata sai naga bayanshi, a yau d'innan zan rabaka da rayuwarka a gaban iyalanka kafara k'irga dak'ik'un mutuwarka daga yanzu.....bata rufe baki ba taji an shak'eta da wani abu me kama da igiya k'ara tasaki tana yunk'urin k'wacewa ammah takasa malamin ne yashak'eta da wani abu me kama da igiya na tsafi nan yashiga karanta wasu d'alasimai yana zagayeta kuka tafara yi ahankali chan kuma tafasa k'ara daganan bata sake cewa komai ba.

Abba jin kalamanta da yayi ba k'aramin tsorata yayi ba dan har fitsari yasaki bai saniba, ummah ko bata da banbanci da wanda yasuma dan d'if wuta tad'auke mata tun lokacin da taga jawahir ta taso kusan bata ma san abinda take cewa ba.

Umar ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba yace watau yarinyar nan gani take ma su Abba suka kashe mata mahaifi saisa take son raina ma mutane wayo har tana ik'irarin rabashi da rayuwarshi...


Muryar malamin suka ji yana cewa wannan ba wani abu bane tabbas a lokacin da aka saka mata laya a cikin baki anyi ganganci domin akusa da iccen suri aka saka saisa fatalwarta tatashi, kukwantar da hankalinku ni zan kamata yanzun nan in tafi da ita.
Abba saurin matsowa yayi wajen shi jikinshi yana rawa yace dan Allah malam kataimaka mana wallahi indai baka tafi da ita ba kasheni zatayi kamar yadda takashe abokaina zan baka ko nawa kakeso na yi maka alk'awali dan Allah kataimaka min.
Malam yace kar kadamu zanyi bakin k'ok'arina kakwantar da hankalinka dan ta riga ta zo hannu daga yanzu zata zama tarihi dan kun gama ganinta.
Umar kallon mahaifin nashi yayi yace Abba indai har kana da hannu akan mutuwar Abbu to baka kyauta ba, saurin juyowa yayi yakalleshi yace kai banza ne wanene yafad'a maka dagaske ne kawai dai so take taga ta kasheni saisa tayi wannan k'aryar ni bansan komai ba akan mutuwar d'an uwana, taya ma zan iya kashe shak'ik'ina bayan halarcin da yayi min a rayuwa idan har akace na kasheshi toh tabbas na zama butulu.
Cikin fushi yace toh shikenan saidai ni kuma ya zama dole inbi ran d'an uwana dan sai na d'auki *FANSAR RAI* kamar yadda takasheshi itama zan kasheta ban damu da aljannun k'aryarta ba!

Abba saurin girgiza kai yayi yace a'a Umar kar kayi haka kabar ma malam komai shi ya san yadda zaiyi da ita.

Malam zuwa yayi yabud'e jakkarshi yad'auko wata kwalba da wani abu cikin wata 'yar roba yanufo wajen da jawahir take a d'aure, bud'e idanunta tayi dakyar tana kallonsu a galabaice ahankali tabud'e baki tace me yasa zakuyi min haka, Abba nice dan Allah kukwance ni ummah, Abba murmushi yayi yace munafuka ai yau kema dole kimutu kamar yadda kikaso kikashe mu.
Ahankali tace kisa kuma? Da yaushe nace zan kasheku? Kallon umar tayi da yake ta huci tace yaya umar dan Allah kace susakeni kar sukasheni.

Tsanarta ce tagani k'arara a idanunshi ranshi a 'bace yace idan har su basu kasheki ba ni zan kasheki dan d'aukar ma d'an uwana fansa tabbas ke butulu ce jawahir duk halarcin da nayi maki a rayuwa baki ganiba.
Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar bai dace kace hakaba wannan ba shine butulci ba, shin laifi ne dan na d'auki fansar ran iyayena?
Tsawa yakwatsa mata yace ya isheki haka! wanene yakashe iyayen naki kina nufin Aliyu?

Juyawa tayi takalli malam da yaruntse idanunshi yadage yana ta karanto wasu d'alasimai a cikin wani abu me kamar mai cikin roba, wata irin razanannar k'ara tasaki nan kamanninta suka fara sauyawa k'iba tafara k'arawa lokaci guda sukaga ta rikid'e ta koma wani k'aton biri malam saurin bud'e idanunshi yayi kafin yayi yunk'urin yin wani abu tuni ta fisge igiyar tsafin da yad'aureta da ita wani irin tartsatsin wuta yatashi tasa hannu takare fuskarta.

Ummah saman kujera tayi saurin fad'awa tare da fasa k'ara tace mun shiga ukku wayyo jama'a kutaimaka min, Abba ko saurin ja da baya yayi yatsaya bayan Umar da yake rik'e sa wuk'a yana nunata alamun idan har ta iso zai caka mata, bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya sannan tace bazan ta'ba fasa abinda nayi niya ba.
'Debo maganin malam yayi dasauri zai watsa matayi tayi saurin gocewa ya sake d'ebowa a karo na biyu nan ma tagoce, zai sake d'ebowa tasa dogon hannunta tak'wa'be robar nan yazube.
Girgiza tayi tadawo siffar Khausar Ammin jawahir gashin nan nata ya mimmik'e saman iska juyawa tayi takalli Abba nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya yi saman iska, wuntsila wuntsila yafara yi da k'afafu saitin da fanka take wanawa tanufa da shi nan yafara ihu, cikin sauri malam yanufi wajen 'yar jakkarshi nan tayi saurin juyawa tanuna jakkar da yatsa sai ga hayak'i yana fita cikinta k'ara malam yasaki cikin sauri yad'auko jakkarshi da mamaki yake kallon khausar da tunda yake itace aljanar da tata'ba ja da shi ganin yadda hayak'i yake fita daga cikin jakkarshi yasa yayi layar zana ya'bace cikin sauri dan kar ta'ba mata tsafi.



Umar na ganin haka yayi sauri yanufi inda mahaifinshi yake kafin ya isa gashin khausar wani siriri guda ya shak'o wuyan Alhaji Mu'azu sai gashi a jikin fanka ta d'aureshi, ummah saurin mik'ewa tayi takoma bayan kujera ta'boye.

Umar saita khausar yayi da wuk'ar hannunshi cikin sauri yanufo inda take zai caka mata hannunta tanuna shi da shi sai ga wani irin haske ya fito yanufi wajenshi sakin wuk'ar hannunshi yayi yasa hannuwanshi duka biyun yashak'e wuyanshi karkata kanta tayi tana k'yalk'yala dariya nan shima yakarkata kanshi yana so yajanye hannunshi daga wuyanshi ammah ya kasa saboda tsananin mak'arar da tasa yayi, chan sai tayi wurgi da shi yafad'a k'asa yana nishi ummah da take tsaye bayan kujera tana kuka cikin sauri ta iso wajenshi tana zuwa tarik'eshi tana cigaba da kuka.


Khausar kallon Abba tayi da yake saman iska saitin fanka nan wani haske yafito daga idanunta sai ga gashinta ya sargafe akan fankar k'ara Abba yafara yi yana neman agaji, dariya tacigaba da k'yalk'yalawa tace mu'azu nice ajalinka kamar yadda karaba ni da mijina da rayuwarmu har kanaso kaga bayan 'yata a yau buri na zai cika zan kasheka kaima kamar yadda nakashe sauran mugayen abokanka dan haka dak'ik'un mutuwarka sun kusa cika, bud'e baki yayi a galabaice yana so yayi magana ammah ya kasa sai nishi da yakeyi sama sama duk jijiyoyin kanshi sun mik'e, idanuwanshi sunyo waje, ja tad'anyi da baya nan fanka tacigaba da juyawa da Abba yana ta wuntsila k'afafu saboda tsananin azaba har wuyanshi yakare ranshi yarabu da jikinshi.



Ummah ko tana zaune a gaban idanunta Abba yamutu kuka kawai takeyi tana kiran sunan Alhaji.
Faruk hankalinshi yana fara dawowa jikinshi ganin yadda tayi ma mahaifinshi yasa yasake yunk'urin mik'ewa dak'yar yajawo wuk'ar yanufi wajenta zai caka mata a karo na biyu, juyowa tayi tanuna shi da hannunta sai ga wani haske ya bayyana me kama da shocking yana shiga jikin umar nan yafara k'ara, murmushi tayi tace na so in k'yaleka ammah ka nema ma kanka mutuwa dan haka dole kaima kamutu, fad'uwa yayi k'asa yana tirje tirje

Ummah mik'ewa tayi dak'yar tana kuka tafara takowa muryarta tana shak'ewa tana kiran sunan umar chan sai tayanke jiki tafad'i k'asa.


Nuna Abba tayi da hannu sai gashi ya fad'o k'asa a mace, ja tayi da baya tare da tsagaitawa daga dariyar da take nan wani haske yafara fita daga jikinta sai ga suffar jawahir kamanninta ya dawo saurin bud'e idanunta tayi, akan Abba tasafkesu da yake kwance k'asa abinda yafaru ne yafara dawo mata a k'walwa har zata nufi inda Alhaji Mu'azu yake kamar ance tajuya tana waigawa sai ganin umar tayi kwance yana ta shure shure.

Cikin sauri ta isa wajenshi jikinta yana rawa ta tallabo kanshi tad'aura saman cinyarta

Please Login or Register in order to submit comment