You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace idan zaka iya zamu had'u a chan Rahama Restuarent.
Toh shikenan nan da rabin awa zaka sameni a chan.
Batare da ya amsaba yakashe wayar.

Tsaki Alhaji Mansur yayi yace yaron nan ya cika jin kan tsiya shi gani yake kamar shi wanine ammah bakomai zan safke mashi girman kan nan nashi bari inje inshirya intafi duk yadda mukayi da shi zaka ji.



Suna gama wayar yatashi yashiga wanka yashirya yafita.

Yana isa Rahama Restuarent babu mutane sosai a ciki yaja kujera yazauna nan yabada umurni akawo mashi coffee yana cikin sha ne Alhaji Mansur ya iso yafara ware idanu yana tunanin inda zai zauna kafin Faruk ya iso da mamakinshi sai hangoshi yayi zaune, murmushi yayi sannan yanufi wajen yaja kujera yazauna yace ashe har ka iso.
Batare da ya kalleshiba yace Eh, me kake buk'ata akawo maka?
Yatsina fuska yayi yace bana buk'atar komai.
Batare da ya ce komai ba yacigaba da shan cofee d'inshi, Alhaji mansur hannu yasa a aljihu yazaro cheque ya ajiye mashi a gabanshi yana murmushi yace gashi
Batare da ya kalli cheque d'inba yace menene wannan?
'Yar dariya yayi sannan yace abokan rayuwa ne mana kakalla kagani.
Kallon cheque d'in yayi yai murmushi sannan yacigaba da shan coffeen shi.

Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ya yi nasara yace wannan gabad'aya na mallaka maka su kaje kacire inma basu ishekaba kayi min magana ink'ara maka wasu.
Sai a lokacin ya ajiye coffeen yad'auko cheque d'in yaduba murmushi yayi yace 5billions, me kakeso inyi maka ne?

Bushewa Alhaji Mansur yayi da dariya yace dakyau haka akeso kud'i masu canza kowa, gyara zamanshi yayi yace yauwa ka yi tambaya mekyau abu d'aya nakeso kayi shine kajanye daga case d'in yarinyar chan, idan har kayi haka ni kuma zan k'ara maka linkin wad'annan kud'in.
Jinjina kai Faruk yayi yana murmushi yace wannan ne daman dalilin kiran da kayi min.
Eh shine kaga sai mutaru murufa ma juna asiri kai kaci dukiya ita kuma akasheta, kai kowane lokaci ma kaji kana son kud'i kakirani ni kuma zan aiko maka da su batare da 'bata lokaci ba.
K'ara duba cheque d'in yayi gaba da baya sannan yayageshi yawurga mashi.
Baki Alhaji Mansur yasaki yana kallonshi cike da mamaki yace kai kana da hankali kuwa? Ka san abinda ka aikata?

Mik'ewa yayi tsaye lokaci guda fara'ar da take fuskarshi tagushe cikin d'aga murya yace ni ko nasan abinda na aikata dan ni ba irin sakarkarun lauyoyin da ake siya bane, idan har kanaso kaga 'bacin raina toh kace zaka siyeni da kud'i, ka kalli kanka kai ba abun kunya bane kakalli kamata kace zaka siyeni da kud'i? Ko ka mance wannan Barr Faruk Sani Maishadda ne lauyan gaskiya?
K'ut Alhaji Mansur yahad'iye wani wahalallen yawu duk idanu suka raina fata dan bai d'auka zai ga haka daga wajen Faruk ba.
Girgiza kai yayi yace bazaka ta'ba samun hakan daga gareniba dan ni aikina gaskiya nake karewa bana d'aure ma k'arya gindi dan haka kawai kasaurari nan da kwana biyar zamanmu a kotu, yana fad'in haka yajuya a fusace zai tafi sai jin muryar Alhaji Mansur yayi ya ce Faruk kar ka aikata wannan kuskuren dama ce guda d'aya nabaka kaje kayi tunani cikin kwana biyu idan har baka canza tunaninka ba toh komai zai iya faruwa.
Ja yayi yatsaya har yagama sauraren maganar tashi sannan yawuce yayi tafiyarshi.
Buga teburin Alhaji Mansur yayi tare da furta shiittt!! sannan yamik'e ranshi a 'bace yatafi...



*BAYAN KWANA BIYU*

Daddyn Faruk ne zaune a parlornshi hannunshi rik'e da Jarida yana dubawa inda gefenshi matarshi ce zaune tana dannar waya, wayarshi da take gefenshi ce tafara ruri nan yad'auko ganin number ce ba suna yasa yace ko wanene yake kirana da wannan number d'in?
Hajiya Nuratu murmushi tayi tace kad'aga kaji ko wanene Alhaji.
Bai musaba yayi picking tare da yin sallama.
Wata irin murya yaji wadda babu alamun mutunci a cikinta akace ina fata ina magana da Alhaji Sani Maishadda?
Kallon Haj Nuratu yayi da itama take kallonshi sannan yace Eh shine da wa nake magana?
Sanin da wanda kake magana ba dole bane dan ba shine dalilin da yasa nakiraka ba saidai ina so kabud'e kunnuwanka kasaurareni dakyau, kaja ma d'anka kunne yafita daga harkarmu inko ba haka ba zaya gane cewa ya ta'bo tsuliyar dodo dan zamu farauci rayuwarshi.
A kid'ime Dad yamik'e tsaye cike da tashin hankali yace Hello ina ji dan Allah me d'an nawa yayi maku?
Bushewa akayi da dariya sannan akace bakaga komai ba daga cikin tashin hankali indai har bai zare hannuwanshi daga case d'in Jawahir ba dan indai har yace zai cigaba da kareta zamu kasheshi.
Dad ida rud'ewa yayi cikin rawar murya yace dan Allah kuyi hak'uri kar kukashe shi wallahi shi kad'ai namallaka na yi maku alk'awali zai janye.

Kar ma yajanye mudai mun fad'a maku kugargad'eshi dan yaron nan naku ya cika taurin kai saidai ba irinmu ake ma taurin kai ba dan zamu iya rabashi da rayuwarshi....ana fad'in haka aka tsinke kiran, Daddy nan yafara cewa hello hello ammah yaji shuru sai lokacin yagane cewa ankashe wayar, wurgi yayi da wayarshi saman kujerar tashin hankali k'arara yabayyana, Hajiya Nuratu da take tsaye gefenshi itama hankalinta a tashe ganin yadda mijin nata hankalinshi yatashi sosai tace Alhaji lafiya me yafaru.
Alhaji Sani da yafara kwarara zufa kallonta yayi sannan yakoma yazauna nan itama tazauna gefenshi tace dan Allah kayi min bayani menene yafaru.
Girgiza kai yayi yace Nuratu muna cikin matsala dan anfara farautar rayuwar Faruk akan aikinshi.
Saurin dafe k'irji tayi cike da tashin hankali tace me? Rayuwar d'ana ake farauta? Me yatsare masu?
Ajiyar zuciya Dad yasafke sannan yace akan wai case d'in Jawahir sukace idan har bai janyeba sai sun kasheshi.
Fashewa da kuka Haj Nuratu tayi tace na shiga ukku d'an nawa zasu kashe? Inko har hakana ya zama dole ya ajiye aikin nan gabad'aya dan wallahi inason d'ana banason inrabu da shi.
Cikin sanyin jiki Alhaji Sani yace wannan dolene Hajiya mik'o min wayata yanzu inkirashi.
Mik'ewa tayi cikin sauri tad'auko mashi wayarshi tamik'a mashi tana cigaba da kuka cike da tashin hankali gabanta yana dukan ukku ukku akan kalmar kisa da aka furta za'a yi ma tilon d'anta.....







_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 17*

....Lalubo number d'in Faruk Daddy yayi yakira ammah har tatsinke ba'ayi picking ba, dan haka yasake kira, saida yayi mashi 5 missed bai d'aga ba, lokacin Faruk yana gidan kaso wajen Jawahir ya bar wayarshi a cikin mota dan bai shiga da ita yanzu saboda a tsarin dokar gidan ba'a bari ashiga da waya shine ma ake d'aga mawa yana shiga da ita saboda kusancinshi da shugaban gidan saisa.


Kallon Jawahir yayi da tunda yazo take zaune ta yi shuru jikinta ya yi sanyi sosai yace wai jawahir me yake faruwa da ke ne haka na d'auka abin farin cikine tunda kwanaki ukku kawai suka rage mana.
Girgiza kai tayi tare da yin d'an guntun murmushi sannan tace Barrister bazaka fahimta bane ina tsoron halin su Alhaji Mansur su d'in mugaye ne sannan ina bak'in cikin abinda yafaru da kai da budurwarka duk a kaina.
Murmushi yayi yace indan wannan ne kikwantar da hankalinki insha Allahu babu matsala sannan maganar Nasiba kibarta kawai na san fushi take da ni ammah da sannu zata safko dan muna son junanmu sosai.
Gefe d'aya takalla tana murmushi ahankali tace Yaya Umar d'ina sai kuma tafashe da kuka.
Hankalin Faruk tashi yayi yace Jawahir lafiya kukan me kikeyi haka?
Girgiza kai tayi tace nima ban saniba saidai kawai ina son Yaya Umar tabbas Ammi ta cutar da rayuwata taya zan iya yafe mata wannan laifin da tayi min na rabani da rabin rayuwata? Shin ita batasan mecece soyayya ba? Shin ta mance yanayin da tashiga a lokacin da tarasa Abbuna?,,, mik'ewa tayi tsaye cikin muryar kuka tace na san bata mance hakan ba kawai dai ta yi amfani da son zuciyartane wajen rabani da masoyina.
Mik'ewa shima yayi yace Jawahir kidaina tuna abinda yawuce.
Taya zan daina tunawa bayan ta dasa min ciwon da bazai ta'ba warkewa a cikin zuciyataba, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen fuskarta sannan tajuyo takalleshi tana murmushi tace ka ga katashi katafi azahar ta yi.
Kallon agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace hakane bari intafi ammah bazan dawoba yau.
Murmushi tayi tace ba damuwa Barrister hakan ma nagode a kowane lokaci ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwarka, musamman akan jajircewarka a lokacin da kuka had'u da Alhaji Mansur ba kowane za'a ba wad'annan mak'udan kud'in ya iya barinsu ba.
Da mamaki yake kallonta yace ya akayi kikasan hakan?
Murmusai tayi a karo na biyu sannan tace wannan ba abun mamaki bane, yanzu dai katafi kar karasa jam'i.
Jinjina kai yayi sannan yawuce yatafi.

A nan cikin masallacin gidan kaso yayi sallah sannan yashiga motarshi bayan ya fita daga gidan ne yad'auko wayarshi sai ganin 5 missed call yayi yana dubawa yaga Dad ne mamaki yakamashi yace lafiya kuwa Dad yayi min wannan missed call? Dialing d'in number d'in Dad yayi, lokacin Dad yana tsaye yana kaiwa da kawowa hankalinshi a tashe yana add'ua Allah yasa ba wani abu yasamu d'an nashiba itako Mom zaune take tana fitar da sautin kuka ahankali adaidai lokacin wayarshi da take hannunshi tafara ringing, jikinshi yana rawa yaduba sai ganin Faruk yayi ajiyar zuciya yasafke sannan yad'auka ko sallama baiyi ba yace Faruk kana ina?
Daga chan 'bangaren yace ganinan a mota Dad zan dawo gida lafiya dai ko?
Muryar mom yajiyo tana cewa kace mashi yayi sauri yadawo gida yanzun nan, nan Dad yafad'a mashi.
Amsawa yayi da toh duk sai jikinshi yaji ya yi sanyi ganin hankalin iyayenshi yadda yatashi dan haka yagane akwai dai wani abu, duk da yanaso yawuce gida saidai kuma yaji ya fiso yafara yin abinda zaiyi kafin yaje gida dan haka ya yalalubo wata number yakira yana gama wayar yak'ara ma motarshi gudu cikin k'ank'anin lokaci ya isa inda zaije.


Baifi minti sha biyar ba yafito yatafi gida yana isa a parlor yasamesu cirko cirko suna ta kaiwa da kawowa ja yayi yatsaya yace Dad Mom lafiya naganku haka?
Mom ce tayi saurin isowa wajenshi tare da fashewa da kuka, nan hankalinshi yatashi yace me yafaru Mom?
Muryar Dad d'inshi yajiyo yana cewa dole katambayi me yafaru Faruk ka ja and'aga mana hankali toh wallahi bazamu iyaba ya zama dole ka ajiye aikin nan naka.
Cikin rashin fahimtar abinda yafaru yace Dad me yasa? Me yafaru da har zakayi wannan furucin?
Jinjina kai yayi yace Faruk komai ma ya faru akan aikin nan ake barazana da rayuwarka har ake kiranmu waya ana gargad'inmu idan har baka janye daga wani case ba za'a kasheka.

Murmushi yayi yace haba Dad wai dan wannan ne kukwantar da hankalinku babu abinda zasuyi min kawai dai sun fad'a ne dan sutsorata ku.

Mom ce tadaka mashi tsawar da bata ta'ba yi mashi irinta ba tace kai shashashan ina ne? Ina kata'ba jin anyi irin wannan? toh wallahi baka isaba Faruk ya zama dole ka ajiye aikin nan akan wani banzan case ka rasa matar da zaka aura ka 'bata da surukinka sannan kuma a yanzu wasu suna barazana da rayuwarka ai ba dole sai ka yi aikinba.

Girgiza kai yayi yace a'a Mom dan Allah kar kuyi min haka.
Muryar Dad ce takatseshi yace Faruk bamu shirya kwana zaune ba ka san dai bamuda wani d'a bayanka dan haka ya zama dole ka ajiye aikin nan gabad'aya dan gudun had'arin da yake cikinshi.

Gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace na shiga ukku menene yake faruwa da ni? Su wanene suka kira iyayena, tabbas nasan bai wuce mutane biyu,,, matsawa yayi wajen mahaifin nashi yace dan Allah Dad kuyi hak'uri kar kurabani da aikina wallahi sunyi hakane kawai dan injanye daga case d'in jawahir suna so sutauye mata hak'k'inta kuma janyewata daidai yake da rasa rayuwarta gashi na yi mata alk'awalin zan taimaketa kukwantar da hankalinku babu abinda zai faru da ni ina akan gaskiyata ubangiji yana tare da ni basu isa suyi min abinda Allah baiyi min ba su d'in azzalumai ne barinsu a doron k'asa daidai yake da cigaba da yad'uwar zaluncin su sannan.....wani irin gigitaccen mari Dad yad'aukeshi da shi wanda yasa saida yai saurin ja da baya tare da dafe kuncinshi yana kallon mahaifin nashi.
Mom ce tace ka min daidai Alhaji.
Cikin fad'a Dad yace kai wane irin shashasha ne wanda baisan abinda yakeba watau mu zakayi ma wa'azi ko? Toh bari kaji indai har mune iyayenka ya zama dole ka ajiye aikin nan yau yau d'innan.
Inkuma ba haka ba saidai yaza'ba ko mu ko aikin,,, cewar mom cikin 'bacin rai.

Runtse idanunshi yayi da suka kad'a sukayi jajir sannan yasulale yazauna k'asa dirshen ahankali yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, sannan yabud'e idanunshi yasafkesu akan iyayenshi muryarshi tana rawa yace Dad dan Allah kuyi hak'uri kutaimaka min kunsan girman alk'awali....mom ce takatseshi tace wallahi Faruk kasake magana sai na k'ara maka wani marin, aikine mun hana shi kuma idan har kai ka isa da mu kaje kayi yadda kakeso,,, tana fad'in haka tawuce a harzuk'e tabar wajen.
Dad ma bayanta yabi suka bar Faruk nan zaune dirshen a k'asa, duka hannunshi yasa yadafe kanshi yace wannan wace irin *K'ADDARA CE* menene yake shirin faruwa da ni? Me yasa su Alhaji Mansur basubar abun a tsakaninmu ba saida suka saka iyayena a ciki? Ya jawahir zataji idan har taji labarin na janye?
Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mashi yace Mom Dad meyasa kuka kasa fahimtata?
Wayarshi ce tafara ringing yashare kamar bazai d'agaba sai kuma yad'auko yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi dan haka yayi picking cikin 'bacin rai.
Dariya ce tafara tashi sannan akace ya kaji salon namu Barrister? Ina fatan dai a yanzu ka janye gudun kar wani abu yasameka dan nasan iyayenka bazasu ta'ba jure ma rashinka ba.

Murmushi yayi cike da takaici sannan yace hakan bazai ta'ba sawa injanyeba ina nan akan bakana, tabbas a yanzu na tabbatar ku d'in matsorata ne da har kukeson janyewata, ba jarumta bace ace kun biyo ta 'bangaren iyayena nine nan daidai da ku dani yakamata kukara.

Daga chan 'bangaren akace kana nufin bazaka janyeba kenan?
Eh ina nan aka bankana sai na kunyataku a idanun duniya idan har ina da numfashi kowa sai ya san ku d'in azzalumai ne.

Dakyau Barrister kai d'in ka cika taurin kai ammah dasannu zamu saitaka muzuba mugani.
Tsaki yaja sannan yakashe wayar ranshi duk a 'bace, wajen yayi zaune dirshen yana tunanin ina ma ace iyayenshi zasu fahimceshi ammah yanayin da yagansu ya san bazasu ta'ba fahimtarshi ba musamman Dad da yake kaifi d'aya, yana nan zaune yana neman mafita aka fara kiran sallar la'asar Dad yafito yawuce masallaci ko kalllon inda yake baiyi ba dan haka shima yatashi cikin sanyin jiki yanufi part d'inshi cikin sauri yawatsa ruwa sannan yad'auro alwallah yana fitowa yasaka kaya yad'auki wayarshi cikin sauri yanufi masallaci dan har antada sallah a lokacin.

Saida yarasa raka'a biyu, bayan ya gama sallah zaune yayi a masallacin duk yana jinshi wani iri saidai yana kallon hakan akan abinda yafaru tsakaninshi da iyayenshi, saida yaga za'a fara sharar masallaci wajen k'arfe hud'u da rabi sannan yafito cikin sanyin jiki yataka yanufi gida, yana cikin tafiya sai ganin wata jeep yayi ta faka a gabanshi anbud'e k'ofar baya ko kallonta baiyiba yawuce zai tafi sai ji yayi ance dan Allah malam muna da tambaya.
Juyowar da zaiyi nan aka watsa mashi wani farin abu a fuska, runtse idanunshi yayi nan yanemi yaruga suka jawoshi da k'arfin tsiya suka saka a mota daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba.




Ahankali yafara bud'e idanunshi yana maidawa yalumshe, jijjagashi da akayine yasa yabud'e idanunshi nan yafara ganin mutanen da suke tsaye bibiyu, runtsewa yayi yasake bud'ewa sai ganinshi yayi cikin wani d'aki tsakiyar wasu mutane su biyar kowanensu d'auke da makami, yunk'urin tashi yayi sai a lokacin yajishi d'aure tamau, kallon kujerar da yake zaune samanta yayi ta roba and'aure mashi hannuwa da k'afafuwa, abinda yafaru da shine yafad'o mashi a rai yakalli mutanen da suke zagaye da shi dukkansu babu wanda fuskarshi take da kalar imani, d'aga murya yayi yace suwanene ku? Meyasa kuka kawoni nan?
Su duka shuru sukayi suna kallonshi.
Ganin haka yasa yakwatsa masu tsawa yace bakuji ina tambayarku nace wanene yakawoni nan wajen? Ko ku kurmaye ne?
Daidai lokacin aka bud'e k'ofa aka shigo da mamaki yake kallon wanda yashigo ahankali yace Alhaji Mansur?
Murmushi yayi yace tabbas nine barrister ashe ka farka ai tun jiya muke nan tare da kai kana ta bacci lallai da alama baccin ya yi maka dad'i.
Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi yace kana nufin tun jiya nake nan wajen?
Dariya Alhaji Mansur yayi yace sosai ma ai ba abun mamaki bane.
Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Alhaji Mansur me yasa ka aikata min haka, ashe daman kaine kasa aka d'auko ni?
Kujerar da take kallon inda Faruk yake zaune yajawo yazauna sannan yace toh ya ka iya tunda taurin kanka ne yaja maka, kaga yanzu cikin ruwan sanyi na satoka yanzu kana nan tare da mu jibi bazamu shiga kotu da kaiba.

Shuru Faruk yayi yana tunanin halin da iyayenshi zasu shiga idan suka nemeshi basu ganshiba, cikin karaya yace Alhaji Mansur hakan da kayi bai dace ba domin ina akan aikina ne ba wai ina yin hakan dan in tozartaku ba.
Bushewa da dariya yayi yace ashe zakayi saurin karaya haka ban yi zaton haka ba saidai ka makaro Faruk, tunda har nagargad'eka baka jiba toh a nan zaka cigaba da rayuwarka da mutanena.

'Dagowa Faruk yayi yakalli mutanen d'aya bayan d'aya sannan yayi murmushi yace ban damu da duk abinda zakayi min ba Alhaji Mansur tunda ina akan gaskiyata sannan ko da ba ni ba ita yarinyar bazata ta'ba barinku ba sai ta kasheku kamar yadda takashe sauran abokan naku dasannu ku ma zaku bak'unci lahira,
Mik'ewa yayi a fusace yawanka mashi mari.
Saurin runtse idanunshi yayi saboda wani irin zafi da yaji ya ziyarci kuncinshi, d'agowa yayi yakalli Alhaji Mansur cike da mamaki bakinshi yamutu yakasa cemashi komai.
Nunashi da yatsa Alhaji Mansur yayi yace kasan abinda bakinka yake fad'a domin ni d'innan ba kanwar lasa bane na tabbata har yanzu baka ida sanin wanene ni ba, ba kowa bane zai takani yazauna lafiya.
Murmushi Faruk yayi yace wannan marin da kayi min bashi ne kad'auka karubuta ka ajiye wannan.
Alhaji Mansur har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayarshi da take hannunshi tafara ringing dubawa yayi sannan yai picking basu ji abinda ake ce mashi ba saidai sukaji yana cewa Eh gashinan ya farka ai yanzu bamuda damuwa abokina kakwantar da hankalinka yana nan wajen a nan zai ci gaba da zama har sai lokacin da yasaduda yadawo hanya inko ba haka ba saidai yakasance tare da mu, dariya yafara kyalkyatawa sai kuma chan yace toh shikenan sai anjima sai mun had'e ai na d'auka zakazo kaga mutumin namu duk wannan jin kan nashi babu shi atare da shi yau, ai kabarshi ina nan da kai sai ya safke girman kan nan nashi,,, suna saurarenshi yagama wayar sannan yakalli Faruk yace toh Barrister daga yanzu ka ga gidanka nan a nan zaka cigaba da rayuwa babu kai babu fita,, sannan ku kuma yanuna wad'annan k'attin biyar yace kucigaba da kula da shi ban yadda ko tsakar gida abarshi yafito ba hatta toilet gashinan cikin d'aki.
Gabad'aya sukace angama oga.
Murmushi yayi sannan yawuce yafita.
Da idanu Barrister Faruk yabishi yana jin wani irin k'unci a cikin ranshi ba komai yad'aga mashi hankaliba sai iyayenshi da baisan halin da suke ciki ba, muryar d'aya daga cikin k'attin yaji wanda da alama shine ogansu ya ce ku zauna nan da shi bari inje indawo.
Amsawa sukayi da toh nan suka wuce suka zauna suna kallon Faruk nan yajingine kanshi a jikin kujerar tare da runtse idanunshi.



A chan 'bangaren iyayen Faruk ganin har dare bai dawoba kuma ga motocinshi duk suna gida dan haka suka fara tunanin ina yaje ko abokinshi yazo suka fita a mota, hankalinsu bai ida tashiba saida dare yayi baidawoba har k'arfe sha biyun dare sannan suka kira wayarshi suka ji ta akashe, atak'aice dai haka suka kwana rabi a zaune ammah bai dawoba.


Wasa wasa washe gari har azuhur bai dawoba dan haka Dad yadinga kiran abokan Faruk da yasani yana tambayarsu sukace basu ganshiba, nan hankalinsu ya ida tashi sukayi tunanin ko mutanen nan suka saceshi, Momcy kuka tadinga yi sosai akan rashin ganin d'an nata haka tashiga mota tadinga zuwa gidajen da tasan yana d'an zuwa ammah babu labarinshi.


Har dare haka suka ci nemanshi ammah babu 'bar'bashinshi ba su ba hatta duk wanda yake kusa da su saida yashiga tashin hankali akan rashin ganin Barrister inda daga k'arshe aka kai cigiyarshi gidajen television da na redio.



Nasiba suna zaune ita da iyayenta a parlor suna kallon news inda ita hankalinta yake akan waya tana chart a nan ne iyayenta sukaga hoton Barr Faruk an dallo ana cigiyarshi, jin sunan wanda ake cigiyane yasa tayi saurin d'ago kai tamaida kallonta ga TV gabanta wani irin mummanan fad'uwa yayi tace na shiga ukku Daddy Mummy kuduba min wallahi Faruk ne ake cigiya me yafaru da shi?.
Murmushi Alhaji Sufyan yayi yace tabbas wannan Faruk ne ikon Allah ko ya akayi haka, yanzu haka wajen iya yin shi ne yayi ma wad'anda suka kasa hak'uri suka d'aukeshi ko kuma wannan yarinyar takasheshi.
Hajiya Maijidda rik'e baki tayi tace na shiga ukku yanzu Faruk d'inne ya'bata tun shekaran jiya?
Nasiba da tayi mutuwar zaune hankalinta ya tashi sosai kasa cema iyayen nata komai tayi tana ta kallon hotunanshi da ake dallawa a TV ana cigiya chan sai ga hawaye sun fara fita nan tasa ma iyayenta kuka.
Su dukansu kallonta sukayi cike da mamaki sukace ke kuma kukan me kikeyi?
Cikin kuka tace Daddy Faruk d'ina ba'a ganshi ba ya 'bace .
Daddynka fusata yayi yadaka mata tsawa yace ke bana son shashancin banza ai ba ubanki bane ya'bace da zaki ma mutane kuka kuma yaushe Faruk d'in yazama naki wannan azzalumin maci amana, inma banda abinki miye abun tada hankali kan 'bacewar wanchan butulun?
Cikin sheshek'ar kuka tace wallahi Daddy Faruk ba mugu bane mutumin kirkine bana son wani abu yasameshi dan Allah muje nemanshi.

Mummynta ce takai hannu tabuge mata maki tace ke dai shashasha ce miye abun tada hankali ga 'bacewar wanda yaso yatozarta mahaifinki yanzu haka rashin mutuncin yayi ma wasu sukaji basu iya hak'uri,

K'ara sautin kukanta tayi tana jin wani irin haushi akan maganar da iyayenta suke marar dad'i akan Faruk dan ita ta san har yanzu tana jinshi a ranta.


Mahaifinta ne yace kibarta kawai Hajiya sai tayi ta yi tunda ita batasan ciwon kanta ba bata kishina duk cin zarafin da yake mana bata gani ni wallahi dad'i ma naji yanzu ai iyayenshi zasu gane abinda muke fad'a masu akan abubuwan da d'an nasu yakeyi tunda su basu iya hanasu.

Mik'ewa Nasiba tayi cikin sauri tajuya tafita daga parlorn tana cigaba da kuka.

Mummynta ce tace oh ni yau naga ikon Allah watau Alhaji yarinyar chan dai da alama bata hak'ura da yaron chan ba.

Cikin 'bacin rai yace kibarta ko kukan jini zatayi bazata ta'ba auren Faruk ba ko da ace yana nan bare ma baya nan dan bazan ta'ba ba irinshi auren d'iyataba.

Shuru Mummyn Nasiba tayi dan ita babu abinda tatsana sama da 'bacin ran d'iyartata dan ma ba hali da ta je ta lallasheta.


Nasiba kuka tadinga yi kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa wani irin tausayin Faruk ne taji ya d'arsu a zuciyarta, wayarta tad'auko takira numbers d'inshi dukansu a kashe nan tacigaba da rusa kuka daga k'arshe tatashi tad'auko mayafinta tazari key d'in motarta tabi ta k'ofar baya taficce batare da sanin iyayenta ba.

Tuk'i take ammah kuka takeyi ahaka har ta isa gidansu Faruk, tana isa ko tsayawa rufe motar batayi ba tashiga gidan da gudu, duk mutane ne zazzaune anyi cirko cirko kowa yana jimamin 'bacewarshi tsawon kwana biyu, a parlor tasamu Mom zaune tana ta matsar

Please Login or Register in order to submit comment