You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana faWin ""Good gurl kada ki kara zuwa ni kika sayawa mutunci. Da gudun tsiya ya bar"

"unguwar ko tunawa da ya yi hatsari baya yi. Lokacin da ya isa gidan damuwarsa biyu ya tirke Taj domin ya ga abinda yayi mata daga window yana daga cikin dalilan da yasa ya mata haka, na biyu abinda ta kawo mishi. Lokacin da ya isa kai tsaye inda ta ajiye mishi leda bag din ya nufa, yadda ya je ya ga babu shi babu dalilinsa ya kwalawa Airah kira tare da tambayarta. Da sauri ta ce mishi.."" yanzu Badr ta wurga a wancan gwandon sharan. "" Wani irin zare idanu yayi kafin ya ce mata. "" Ko Ubanta da Uwarta basu isa na ajiye abu su sauya min wuri ba, ke ubanki ne ya ce ki sauya mishi zama daga inda yake? "" Da sauri ta nufi inda ta jefa ta ciro tana faWin."" Kayi hakuri hamma."" Kamar zata yi kuka ya ce mata. ""Oya je ki wanke ki kawo min, abin Lubnah ko a kashi aka saka zan wanke na ci!"" Mahaifiyar Badr ta ce masa. ""Allah yasa na asiri ake baka ba."" ""Ni nake bata kudin da zata kaiwa bokonta domin wallahi ya iya aiki. Domin ta"

"mallake ni."""

"""Allah yasa ba wani abu take wankewa take baka ba ."" ""Ai yanzu nake son gaya miki ko shi ta bani nake"

"sha, ba matsalar babban matsalata shine yadda ba ayi mana aure nayi da kaina naji abinda masu mata suke ji, idan suna....."

(Dan iska )

"[12/13/2025, 7:26 PM] Maman Walid: 13"

"Watsa mishi ruwa Ubaid yayi domin kaf a duniya babu kunya cikin lamarinsa, ya kauce ruwan ya watsu a"

"gefenshi. ""Kai wani irin mutum ne da bai san ido ba?"" Ubaid ya tambaye shi, ""ido? Sun aka ace maka sun san idon ne? Matar da nake so zasu gayawa Magana sai nayi shiru saboda ina son su so ta? Kai ji idan suka ce basu sonta ni ina sonta. Zan iya rayuwa da iya ita ba tare da nayi nadama ba, zan kuma iya datse alaka da kowa domin ita, gaya min wani abu nake bukata? Yau suna tare da ni ne domin abinda nake da shi ita kuma tana guduna ne saboda su. Idan da yau babu su babu abinda nake da shi tabbas rayuwata"

"sai tafi haka citta."""

"""Me yasa kake karawa matsalar nan fetur ne?"" ""Saboda na gaya maka su din basu gaba, idan babu su iya"

"Mujitafa gare ni su basu da abinda zasu ba ni, idan aka ce iya kai ne babu abinda zai saka na kalle su. Su gode ma da nake kula su oya su bar min gida!"""

"""Amma kasan dole matarka ta shiga cikinsu?"" Ya fada yana kallon shi ya kara da cewa. "" Dole Matarka"

"tasan su din naka ne? "" ""I fuck su nawa ne, kai dalla su fita min ina da kake magana anan basu ne suka turawa Matarka hotonka da Lunah ba? Ko an gaya maka basu ne suka tura min hotonka da Lunah ba, kai ma kana manta da bala'in mutanen nan su fita kafin na kira Dattijo ya min waje da su."" Jin haka yasa bakiWaya suka mike tare da barin parlourn musamman yadda ya kara da cewa."" Damuwarku na auri Yaranku idan suka samu ciki da ni na zama next victim to ba da ni ba! Da naci guba a hannunku gara na"

"mutu a tsaye. Sai kace an taSa soyayya ko auren dole kun bi kun dame ni. """

"Suna fita Ubaid ya mishi magana ya d'aga mishi hannu yayi ya ce mishi."" Tsaf kafi kowa sanin waye ni"

"Please je ka wurin matarka kada ka dame ni! "" Shima ya samu nashi kason, ba musu ya bar gidan, ya kara wanke fruit din da kanshi sannan ya zauna ya fara ci kusan abinda ya ci kenan, fitowar Airah da take jin kome ya watsa mata harara ya ce mata."" Ki tattara abinda kika dafa ki je na gode."" A rud'e ta ce mishi."" Sir me na aikata? "" Wani haWe rai yayi sosai ya ce mata. "" Taya xan yi bakuwa tazo gidan nan amma ki ganta ki basar da ita kin san how she meant to me? Da zaki ganta ki share ta don ni na share ta? Daga yau kada ki kara zuwa gidan nan, wannan shine zuwanki na karshe sannan ji gayawa mutanen da suka turo ki ita din rayuwata ce. "" Yadda ya mata tas ya kore ta, abin ya bata mamaki domin kuwa yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake bala'in ashe basu shiri Yes tasan basu shiri amma kuma meye na jin haushin"

kowa?

"Labarin nan har kunnen Alhaji ELYakub, murmushi yayi yana faWin. ""Shi kuma irin nashi borin kenan, a"

"kyale shi yayi yadda yake so ai matarsa ce idan ya gama fushi da kishin zai sauko a saka ranar da ya dace."" ""Baffa me kake nufi?"" ""Eh abinda nake nufi kenan;"" ya tashi ya bar parlourn."

*

"Karfe tara na dare Taj ya shigo gidan, yana parlourn abinda Uncle Auta da Nurse tana wanke ciwon,"

"kallon Taj yayi ya dauke kai kamar bai ganshi. ""Good evening Sir?"" Banza yayiwa Taj Uncle Auta ya amsa"

"mishi, tsayawa yayi a can gefe nurse din ta gama ya sauke rigarshi ya kishingida yana jin zafi da shigar"

"maganin. ""Sir!"" Bai iya karasawa ba saboda yadda ya buWe ido akanshi. Zubewa a kasa Taj yayi ya dawo gabansa. ""Kayi hakuri wallahi kuskure ne, wallahi ban san cewa ita din taka ce ba."" "" Wai mai ya faru ne?"" Murmushi yayi ya ce mishi.""Tashi ka tafi!"" Ya cigaba da kallon tv, Uncle Auta ya kara mishi tambayar me ya faru, amma yayi shiru can ya kara cewa."" Wai kai meye matsalarka ne da kowa kake son samun matsala ne?"" are ayaba yayi ya gutsara yana kallon tv, "" naji irin rashin kunyar da kayiwa su"

"Khaulatu."""

""" Taya zan yi kunya arba'in da wani abu idan na ji kunya kai zaka bani auren Dadah karama? Kai ko kai"

"ka min rashin mutunci zan rama daidai gwargwado, kowa ya ji yadda ake ji."" Daga haka ya cigaba da cinye abin da ta kawo mishi. ""Tow shi Taj fa?"" ""Kama shi nayi yana rike hannun Matar Turaki!"" Daga haka na cigaba da abinda yake sai kuma Uncle Auta yayi shiru wato maganar gaskiya shine zai matuar wahala"

"zaka samu sune suka mishi laifi, shi kuma kamar mace wurin gasa bakar magana."

"""Dazun mun yi magana akan lamarin, ina ga kamar su a bangarensu akwai babban challenge da dole"

"ta bangarenka ne za a samu masalaha. ""Shiru yayi kafin ya ce mishi. ""Gaskiya bana ganin akwai wata mafita, zan duba in sha Allah."""

***

"A few weeks later na ji gara na koma Bauchi na gaji da lagos, har saka wayata nake a gaba ko zai kira ni,"

"amma mutumin nan na rasa inda ya saka ni, abin da nayi nasan nayi kuskure amma taya zai manta da ni bayan nasan cewa mutumin nan yana kokari tow ya zanyi da danginsa? Sune. Daukar wayar nayi ina kallon sunansa wato Masifaffen da na saka sunanshi. Wani bude kofar dakina aka yi da wani karfi ban san lokacin da na danna kiran ba. Wayar na cillar tare da kallon kofar dakin. ""Kika ce zaki koma Bauchi?"" Bakina yana rawa na ce mishi. ""Eh Ya."" ""Aikin fa?"" ""Yace kada ka kara zuwa!"" ""Ke wacce irin mutum ce bai shegen taurin kai?"" ""Ya Ado ba fa!"" ""Amma kece kika ce zaki ajiye aikin? Ya Ado ya kake so nayi?"

"BakiWaya an hade min kai a office din kamar wacce nayi wata zunubi, wacce take kula ni itama ta daina kula ni. Ya Ado ina son aikina ina son na, amma kullum turo min sakon barazana ake akanshi. Na rasa yadda zan hatta wurin aikin ina ganin yadda ake bina idan ban ajiye aikin ba ya zan yi? Ni kaina bana son nayi haka don za'a ce saboda abinda ya mana zan yi butulci amma ka fahimci wani abu bana son saboda"

"ni ya samu matsala da kowa zan koma Bauchi."""

"""Hafiz ya can yana jiranki amma kin sani ko? Kuma Baban Jama'are yana bibiyar Abba akan ki koma"

"gidan Hafiz, ki sani ba zan shawarar gidan Hafiz ba, amma ki bude baki ki cewa CEO ya turo domin shine irin mijin da kike bukata. "" "" A ce na aure shi saboda abin duniyarsa ka fahimta mana! Allah yanzu"" "" wannan yarinyar Allah ya san dalilin da yayo ki a yanzu baki shiga cikin arnan farko ba, wurin taurin kai. Da ba karamin wahala za'a sha dake ba, shi Mr Bilal din ya ce ba zai iya kare ki ba ne?"" Tura baki nayi na ce mishi."" Ya ce maka yana sona ne? Ina korata yake a jikinshi gara na koma Bauchi na huta! Ko ban"

"koma gidan Hafiz ba aure zan yi."" Na manta da wani zancen wayar ya Ado ya zuba min idanu ya ce min."""

"Yanzu kina nufin zaki koma gidan Hafiz kenan?"". "" Ya Ado mugun da ka sani."" Tass naji saukar hannunsa"

"a fuskana, ban san yadda akayi ya tawo gabana jikinshi yana rawa ya ce min. "" Har fata kike ki koma wancan kazamin rayuwar? Burinki shine ki wulakanta Mama da ta gama kunce zaninta a kasuwa ko mr Turaki bai ce yana sonki ba, wallahi kin ji na rantse da Allah na bashi ke, idan kin so ki shiga bariki aure babu fashi domin ba ma zaki koma Bauchi satin nan zan daura auren na ga uban da ya isa dakatar da ni, bari ki ji sadaka zan bashi ke. Yar iska mara kunya!"" Cin mutuncina Ya Ado yayi min, kiranshi yayi a waya ya ce ya shirya nan da sati biyu. Ai kuwa na fashe da kuka har da ihu, na kira Mama ko zata goya min baya amma ta ci mutuncina tare da cewa, idan da na san wutar da ake hurawa a Bauchi da ba zan fara"

"kiranta ba, tayi ta sakawa Ya Ado albarka."

"Ai ban san lokacin da na fara rashin lafiyar karya ba, Ya Ado ya ce ko mutuwa nayi sai an daura auren"

"naje gidan shi ayi min jana'iza. Kwana biyu da faruwan lamarin ba sai ga Uncle Auta da sadaki ba, shi kuma Ya Ado yace a kai Bauchi, lokacin da suka isa Bauchi Ya Umar da Ya Tahir suka amsa, tare da Alhaji Sa'idu. Domin har da baki daga Gombe babban hidima aka yi, lokacin da labarin ya isa Jama'are an kawo sadakina, sai hankalin kowa ya tashi. Immediately sai ga Ya Hafiz a lagos, duk da Ya Ado ya hana shi shiga gidan amma yadda ya haukace sai da naji kamar nayi mishi wani kuskure mai girma domin kuka yake wiwi yana rokon ko za a kashe shi ne ya yarda fatanshi ya mutu ina tare da shi, akwai wani abu da na kasa rabuwa da shi a tsakanina da Ya Hafiz shine tausayi, ina tausayinsa wanda na fahimci cewa har yau zuciyata tana tunawa da shi, sai dai da ba tuna da tarin laifuffukanshi a tare da ni, sai na ga bai"

"cancanci nayi wasa da rayuwata ba, amma kuma shi Mr T zai zauna da ni bana haihuwa ne?"

"A rana na biyu da yake zuwa gidan na fita, wanda sai da nayi danasanin fitar da nayi. Domin kuwa"

"lokacin da na fita na same shi yana tsaye ya zuba min idanun Ya Hafiz da na sani Wan gayu ne na fitar hankali amma wannan na gabana kamar wanda aka kamo shi daga cirani, gashi ya yamutse kamar wanda aka biyo bashin masifa, kallonshi nayi na tuna yadda yake min dariya a baya. ""Me kake bukata?"" ""Ki yi hakuri!"" Shiru nayi ina kallon kasa ashe akwai ranar da Ya Hafiz zai bani hakuri? Ashe akwai ranar da zai zo ya ce min nayi hakuri? Na zata shi mutum ne me ra'ayin kansa ba a saka shi ba ya ji kuma baya gani. ""Amma kasan na amshi sadakin wani ko?"" Tsayuwar motar Mr Turaki a gaba damu ya kashe ya fito, ya tsaya yana kallonmu. ""Ya Hafiz kayi hakuri ka rabu da mu, ban san me ciwon kai ba sai da na haWu da shi, ban san yadda zuciya take ji ba sai da na same shi a rayuwata, nasan kuruciya tasa na amshi"

"soyayyarka amma shi zaman jirana yayi har wannan lokacin, ina jin wani abu a kanshi."""

"""Karya kike yi, wallahi karya ce bakya sonshi kudinsa kike so don ya biya muku bashi."" Ya cigaba da zage -"

"zage. ""Wuce ki shiga cikin gidan."" A hankali na juya ina kallonshi, hawayen dake ta danne shi ya sauko da gudu, na saka bayan hannu na goge. """

"A wancan ranar da ya tsaya a gabana, rawan kai da rashin sanin ciwon kai yasa naki kulawa da tarin"

"Alkhairinsa, amma a yau da yake gabana sai nake ganin kamar banbanci sabon rayuwar da yake bibiyata da shi ba, nayi laifi amma haka ba yana nufin daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki ba ne, wancan da ya tsaya min a wancan rayuwar kama yake da gardi irin almajirai da aka Wauki nauyinsu. Madadin yau"

"wanda yake gabana, CEO ne guda mai cike da kammala da nutsuwa, ba kamar wancan na baya mai"

yawan murmushi da fara a ba. A yadda nake kallonshi tsaf zan buga kirji nace shi din masoyina ne amma

"kalaman Ya Hafiz da ya fada ya saka ni jin wani irin abu ya tsaya min. "" Kana ta murna ka kai sadaki shi sadaki ba aure ba ne, kuma idan har a Bauchi za a daura auren in sha Allah ta haramta maka. Domin kuwa ni ne mijinta a duniya ni ne a lahira!"" "" Ya Hafiz wannan rayuwata ce, me yasa sai ka lalata min rayuwata ? Me na maka kake son saka ni a damuwa? Na zata duk tarin alkhairin iyayena da suka maka sai ka tozatani?"" Murmushi yayi alamar ya samu nasara ya a kaina sai ya juya kan Mr Turaki ya ce mishi. ""Ka sani baya haihuwa, domin!"" ""Waye ya gaya maka kowa yake bukatar Haihuwar? Ni ita nake so, ba"

"wani abu ba, idan don wani abu nake bukata baka isa ka aure ta a farko ba, ka. Ji na gaya maka kul!"""

"""Wallahi baka isa ba! Lulu ki dawo gare ni hatta Arzikin Abba yana tare da aurenmu tunda muka rabu"

"masifa suke ta faruwa baki gane ba ne? "" Cikin wani irin baki ciki. Na juya zan fita suka fara fada kamar zasu kashe kansu."

"Kasa magana nayi ina kallon maza biyu a gabana, na rasa yadda zan yi da rayuwata. Ban gama nazarin"

"abinda zan fa musu ba, sautin muryan Ya Hafiz ya daki dodon kunnena. ""Ke ce silar farin cikin iyayenmu, ki dawo aurenmu domin kaf duniya babu namijin da ya isa ya zauna dake, don ni nafi dacewa da ke."

"Luluna ki sani babu wani namijin da zai so ki sama da yadda na so ki!"""

"Sautin murmushin CEO na ji yana mai kallon agogon hannunsa ya ce min. ""Think wisely, ba zan raba"

"ki da Ex Winki ba. Amma ki sani ten years ba ten months ba ne, ba kuma ten weeks, ba ten days ba ne ba"

"kuma ten hours ba ne. Ba kuma ten minutes ba ne, na ajiye kome dominki duk lokacin da kika shirya ina nan ina dakonki."""

Sai na shiga rud'ani CEO ko Ya Hafiz waye zan komawa...........

"[12/14/2025, 9:16 PM] Maman Walid: 14"

"Ji nayi kaina yana wani irin juyawa, da karfi na ce musu. "" Ya isa nace ya isa haka. Ka je ka amshi"

"sadakinka kai kuma na kara ganinka sai na kashe kaina sai ka auri gawata."" Na juya cikin gidan da sauri"

"don na gaji da maganarsu. Muryan Hafiz ya kara tsayar da ni. ""Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!"""

"""Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure, don abu kazan kazanka ubanka!"" Inji Ya Ado da ya fito."

""" Kuma wannan da yake gabanka shi ne Mijinta. Aure kake cewa ba zata yi ba? Kai ne zaka hana auren,"

"kambu tow Bismillah macuci azzalumi mara imani. Ina ga sai an shiga tsakaninka da Lubnah tunda abinda kake nufi kenan katon dakiki jahili."""

"Tas Ya Ado ya wanke Hafiz sannan ya bawa Mr Turaki hakuri. Tun daga nan na kara shiga damuwa,"

"lokaci zuwa lokaci ina ganin sakon kudi da kati da kuma data, tow me zanyi da shi? Ni ire-iren waWannan abin basu wani burge ni. Amma haka na share na cigaba da harkan gabana, Ya Hafiz ma bai daina kirana ba tare da barazana, har na rasa yadda zan yi da raina, a gefe kuwa Mr Turaki ya zuba min idanun bai kara bin ta kaina ba, sai dai abinda na fahimta shi irin mutanen nan ne masu iya dafa mutum da ruwan sanyi ba faWa ba zagi amma wallahi gara yayi min hargowa irin na Hafiz amma ina ko da wasa bai ara bin ta kaina ba, har ranar da na bar lagos, sai da na isa gida na huta na ji yana ta waya da Mama da Yadiko, zuwa yanzu na fahimci yadda Turaki ya samu fada a gidanmu, yadda ka san su kwanta ya bi ta"

"kansu, Mama kuwa tasa ni tayi a gaba tana min gyaran jiki da jike jike take min, tare da dauke min huta."

"Ban san inda ta hadu da wata yar maradi, matar nan har gida take zuwa ta min gyaran jiki. Ko waje"

"bana fita saboda gyara da kulawa. Sai abin Yadiko nake jin an saka auren wata guda, tab'e baki nayi kamar wacce ta ga kashi na ce mata. ""Kuna ta wani damuwa bayan shi ba sona yake ba!"" Na fada ina tura baki, rike baki Yadiko tayi ya ce min. ""Inji waye? Waye ya gaya miki baya sonki? Ko kafin ki zo sai da ya zo kwanansa daya ya koma ko garinsu bai je ba, a tsohon dakin Sani ya sauka. Mijin da kika samu ba karamin mutumin kirki ba ne, har wurin danginmu sai da ya zaga ya gaishe su. Ke ki godewa Allah."" Tura baki nayi na ce mata. ""Ba wani sona yake ba kawai ganin haka kike kawai."" ""Soyayyar ta daki hancin kaniyarki, baya sonki kuma haka za ayi auren idan kin shiga ko sha piya-piya ki mutu ja'ira kawai."" Inji"

"Mama tana mai sake labulen, tana mita akan Yadiko take biya min nake iskanci kala kala."

A daren Hafiz yazo gidan yayi ta kuka yanzu zai cika baki zuwa anjima zai koma yayi ta bada hakuri.

"Zuwansa na uku kenan, babu wnada yake kula shi. Ganin haka Yadiko ta fito ta ce mishi."" Amma kasan haramun ne nima a cikin nima?"" "" Yadiko ina son Matata, aka raba ni da ita."" "" Uwarka ta rabaka da ita! Ita ta kawo khulu'i amma bata kai kotu ba, uwarka da yan uwanka suka kai kotu, don mune marasa zuciya sai mu dauke ta mu dawo maka da ita, sakarai kenan ai Lubabatu ta wuce lisafinka abinda baka zata ba ne ya same ka, tunda baka so ta samu miji irin wanda take tare da shi, sai ga shi bata cutar da kai ba, ta samu mijin kere sa'a shine bari ka lallabo kazo da wata fitinar da zata janyo a dakatar da auren"

"ko?"""

"""Ai kuwa ko Hasiya da ifritai take yawo bata isa ba wallahi, lokacin da ka rabu da ita ai cewa kayi mata a"

"gari kamar jamfa a jos, ina zaka kai kayan wanki, da Allah ya tashi sakayya sai gashi ita da kake mata kallon ba zata samu mijin da bai kai ba, sai gashi Allah ya bata wanda baka isa ka tsaya a gefensa ka ce ka tab'a auren Lubnah ba, kai ko a lahira ka ga Lubnah ka ce kasanta sai Allah yayi mana hisabi, fita kafin na watsa maka ruwan zafi dan iska mara mutunci idan na. Ganka kamar na ga mutuwata haka nake ji."

"Yanzu ka kawo kara ta auri wanda ya fika saboda bakin ciki sa mugunta. """

"Kusan abinda Mama ta fada gaskiya ne, yanzu Ya Hafiz ya dawo ne don yaga xan auri wnada ya fishi,"

"da ace baya ne ko a jikinshi tunda yasan wanda zan aura bai kai shi ba, amma a cikin lokaci kalilan yaji"

"labarin wnada zan aure haka yasa yake jin kyashi da hassada, yana niman hanyar da zai bata kome kowa"

"ya rasa. Wannan abin ya d'aga mishi hankali. Shi yasa yake ta wannan koke -koken Mama kuwa ta rantse ya sake zuwa sai ta mishi babu dad'i, ya kullaci auren nan a ransa kuma duk inda ya zane, zai lalata auren"

nan sai yayi.

Hafiz

"Tunda ya bar gidan yake kiran Hajiya amma bai same ta ba, ya kirata yafi sau uku. Amma bai same haka"

"ya koma gefen titi ya kira Nana, ta dauka. "" Ina Hajiya?"" "" Bata nan"" ta bashi amsa, "" Nana ya zanyi? Ba zan iya barin Lubnah ta auri wancan mutumin ba, idan ta aure shi wallahi ko na fada na taSa aurenta karyata ni za ayi. Na gayawa mara mutunci cewa har hauka tayi ya ce shi ma mahaukaci ne zasu zauna cikin kauna da soyayyar mahaukata. Nana kamar xan mutu don Allah ki gaya min yadda zan yi?"" Ya tambaye , har da kuka kamar yaro. Shiru tayi ta ce mishi. ""Ni dai ina kyale su, ka kyale musu rayuwarsu, rayuwata ma ta ishe ni ina cikin tashin hankali ba zan iya tsayawa ka kara cutar da Lubnah ba, domin duk sharrin da Hajiya ta tura mata gashi nan akan nawa Yaran, mijina ya sako ni a gaba ni ba sakakkiya ba ni ba mai aure ba, sannan kai kanka kana cikin arzikin Lubnah ne tunda har yau babu wnada ya ce ka bashi key Win motar da ake tukawa ashe kuwa dole ka barsu su rayu cikin kaunar juna, idan kuwa ka dage sai"

"ka raba su, wallahi karshe rabon da yake tsakaninsu ya kashe ka."""

"Sai yau yake wani irin danasanin hana Lubnah haihuwa yasan yadda Uwa take akan Yaranta, ba zata"

"tab'a hakura da Yaranta, ta auri wani namiji ba, yau gashi yana ji yana gani wani zai dauke mishi Lubnah, yau da yana da Yara da ita wallahi ko da iya Yaran zai saka dole ta dawo, kuma ya daura daga inda yatsaya. Amma bai san wani abu yasa ya ki hada jini da ita ba, a yanzu idan kalle ta sai yaji kamar bai taSa mu'amala da wata mace bayan ita ba, sai ga ita Waya ce zata iya daukar laluranshi, ita Waya ce zata so shi zata iya hakuri da shi, wani shegen kishi ne ya kama shi ya kira Hajiya sai lokacin ta dauka tana faWin. ""Lafiya dai?"" ""Hajiya so nake a nakasa min mijin da Lubnah zata aure tun kwanaki nake gaya miki a yi abinda zai hana auren, kamar yadda aka binne zancen bashin nan amma kin ki yin kome!"" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce mishi. ""Hmmmm Yaron nan da zai auri Lubnah Kakaninsa akanshi suke, suna tsaye akanshi yadda baka zata ba, ita kanta Lubnah Uwarta tana tsaye a kanta babu yadda za ayi wani abu na sihiri ko tsafi ya same su, domin suna cikin kariyar Allah. Sannan idan aka matsa mutum zai iya fuskantar gagarumin lamarin wanda mutuwa ce.."" shiru yayi duk da wannan bala'in tsoronshi da"

"mutuwa a fili take, duk abinda za'a kawo mutuwa a cikinshi yana gudu."

""" Hajiya a nakasa shi ya koma ba namiji ba!"" Ya fada yana kallon titi. ""Baka gane bane? Ba fa abinda za a"

"iya mishi domin Yaron jikinshi a tsare yake itama Lubabatu babu wani abunda zai iya zama a jiknta, da kamar da ne zaka iya amfani da yadda za a zuba mata abincin da zata ci, in sha Allah za a dace amma a yanzu ko me ka bata ba zata tab'a karba ba."" ""Hajiya a hada a kayan gudunmawar da zaku basu, na"

"hakura amma wallahi sai ta fito saboda matsala. """

""" Ka shirya mutuwa?"" Ta fada mishi cikin kosawa da maganarshi, "" sannan ka sani irin wannan aikin ba"

"karamin kudi yake ciki ba, idan ka shirya sai ka turo kuWin aiki da na yanka,

Please Login or Register in order to submit comment