You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka zo rabon ina ga nashi bawa wasu aka yi, "" hi Mrs Turaki jira ni na kai ki ai baki isa ki tafi ki bar ni ba, salon wani dodo ya kama min yar Chika ta!"" ""Chika?"" Na kara maimaitawa a raina nace. *Allah yasa ba wata kalmar batsa ba ce!* Domin shi duk abinda ya fito a bakinsa fada yake, sarkafe hannunmu yayi ya d'ago tare da sumbatar hannuna ya ce min. ""Muje ko? Chika na!"" A hankali nake binsa yana kallona yayi murmushi. ""Sai naji kamar mu yi ta tafiya haka, babu kowa a tsakaninmu. Babu wnada zai dame ne mu, babu tashin hankali."" Riko ni yayi na dawo gabanshi, ya hade goshinmu wuri guda. ""Ina ji a raina ni nafi kowa sa'a a wannan rayuwar duniya, ina kuma rokon Allah yasa kada nayi danasanin akanki har karshen rayuwata."" Hannunsa naji akan kuguna na bude idanuna. ""Ke hakkina ne fa, da zaran na taSa ki sai ki razana kamar wacce aka WoWWana mata wuta, ki sani Mijinki jarumi ne ahto ba zan yarda ina taSa ki, kina zabura kamar wacce aka saka mata lantarki ba."" Wayarshi ce tayi kara ya"

"Wauka yana faWin. ""Ok kuna airport kenan?"""

"Take na ga fuskarshi ta sauya, a hankali na kai hannuna kirjinsa ina Wan tab'awa, a hankali kamar"

"rarrashi. Zuba min idanun, ni kaina ina jin abinda ake fada tsaki yayi ya ce mishi."" As you wish!"" Rigima suke da Kakanshi akan ya zauna a part din iyayensa musamman na mahaifiyarsa shi kuma yace ba zai zauna ba, shine ake ta kai ruwa shi ya nace sai gidansa. Kallon kwayar idanuna yayi kafin ya ce min. ""Zaki iya zama a wancan jahannamar?"" Lumshe idanuna nayi kafin na bude akanshi. ""Duk inda ka kai ni zan zauna."" Bakinshi ya kai tare da sumbatar goshina, ""Muje su Auntynki sun tafi fa!"" Zare idanun nayi ina faWin, ""me yasa suka tafi?"" ""Ji gulma da kika samu Mijinki, kika manta da wasu aunty a can!"" ""Ni ba ruwana kai ne ai!"" ""Amma yarinyar nan kin ga girmana, lallai ma dole na shiga lamarin nan ayi mana Shari'a akan wannan sharrin da kika min."" Ya fada yana murmushi, har muka isa inda motar da xata mai mu airport an saka kome na mu, ya bude min na shiga sannan ya zagayo ya zauna a kusa dani. Rike hannuna yayi yana shafa lallen hannuna. ""Kin yi kyau! Amma. Jiya don wulakanci kika yi ta kuka har naji tsoron kada Mama ta ce an fasa tarewar da sai na ce kowa ya tafi mun gode anan zamu cigaba da"

"zama!"" Kifa kaina nayi ina dariya, ashe haka yake da surutu, an kira shi ya kai sau biyar karshe kashe"

"wayar yayi, ""idan suka gama bidiarsu dole na dauke ki mu tafi honeymoon!"" Murmushi nayi wato ina ga"

"ko Radio sai zuba yake min, har muka isa airport Win Uncle Auta yayi ta mishi fada akan bata lokaci da yayi ya ce musu. ""Ni fa bance a shirya wani biki ba, yawwa don da na san da wani bikin nan da na wuce honeymoon da matata ni bai dame ni ba, kowa ya zo ya kwashi gara yayi tafiyarsa ko Lunah!"" Ya tambaye ni yana kallon fuskana, kasa motsi nayi Ubaid. ""Amma kai dai daga dan iska sai kai, Allah yasa ka wuce bangon duniya ba honeymoon ba."" ""Tow ina ruwana, lunah kina jin yunwa na kawo miki wani abu?"" Wato shi dai haka Allah yayi shi da bala'in niman magana, har muka shiga jirgin a wurin zama ne fa ni zan zauna da su Aunty Hindatu da Goggo Alti, sai Ummanmu, suka janyo ni na zauna a wurinsu. ""tsayawa yayi ya ce musu, ku bani matata, ni na muku al™awarin zuwa aikin hajji in sha Allah, muna"

"sauka zan tafi da ita idan kafin a fara zan dawo muku da ita."""

"Kallonshi nayi kamar zan yi kuka na dauke kai, yadda yayi ta tsara su har suka bada hadin kai, na sha"

"mamaki. Kafin mu isa lagos ya shawo kansu, muna isa airport na lagos wata mota ta zo ta dauke shi da ni."

Ina kallon yan uwana cike mamaki su kansu lamarinsa kara basu mamaki. Duk jikina ya Wauki rawa.

"Haaka muka isa wani gidanshi a can victory Island, gidan yayi kyau, ya riko hannuna muka shiga avinda muka fara shi ne sallah, muna idarwa ya fita can sai gashi da abinci, kusan a tare muka ci yana bani ina kauda kai karshe ya janyo ni kamar yarinya karama haka yayi ta dura min, har na ji na koshi. Kafin ya riko hannuna zuwa parlour ya zaunar da ni akan kujeran parlourn, sannan ya fito ya zo ya zauna ya saka ni a gaba yayi ta kallona. Kafin ya kwantar da kanshi a cinyata, hannuna ya ja ya daura akan kirjinsa, tun yana min hira har barci yayi gaba da shi. Zama nayi ina kallonshi. A hankali nima na daura kaina kan kujeran na cigaba da nazarin rayuwa, kafin barci yayi gaba da ni. Wasa-wasa sai karfe shida saura muka farka, shi ya fara tashi ya zuba min idanu. Ji nayi an sumbaci hannuna, a hankali na ji dumin lips dinsa, bude ido nayi na kalle shi na ce mishi. ""Kin tashi?"" Gyada mishi kai nayi ya ce min. ""Sorry ko ni na tashe ki?"" Murmushi nayi na tashi zuwa dakin da muka cin abinci a cikin na shiga ban daki biyo ni yayi, zuba min idanu yayi da yatsu biyu ya nuna min abinda zai yi. Juyawa nayi zan fita ya riko hannuna na tsaya, ya gama yayi duk abinda Muslunci ya shara'anta sannan ya fito nima nayi nawa na fito na zo na samu yana jirana, a bayanshi na tsaya ya jamu sallah, bayan mun idar ya dauki Babban rigarshi ya ce min. ""Muje kin ji suna can suna ta Bala'i!"" Ya fada yana murmushi, gyara zaman mayafina nayi yana gamawa ya riko hannuna muka fita, har waje ashe dA mutane a gidan a harabar gidan na gansu suna taya shi murna."

"Motar ya bude min na shiga, sannan ya zagayo ya shiga yana zama muka bar gidan kafin mu isa har an kira Magariba, muna shiga can cikin gidan. Ya bude min na fita ya riko hannuna sai da ya ja min mayafina ya rufe min fuska, sannan ya rike ni gam, muka shiga tafiya kasancewar gidan ana ta hidima ga mutane sun taru, hotonmu da muka yi aka saka a wurin da za ayi taron, a hankali muke tafiya saboda tun da muka shigo gidan ake daukarmu hoto, lokacin da muka fito aka mana caa, sai da na ji bakiWaya kome ya tsaya min har cikin gidan muka shiga hannun shi rike da nawa, gam lokacin da zamu shiga yan matan family din sun fito, hannunsa ya kai kuguna, ya kara janyo ni jikinshi, kallonshi nayi murmushi yayi min da wani karamin murmushi, haka muka shiga cikin gidan ana rangad'a gud'a, kaina a sunkuye har gaban Kakarshi ta wurin Uba wato Daddah tare da Kakarshi ta wurin Uwa. GuWar da ake yasa ko ina na gidan ya amsa, riko mishi kunne wata babbar baturiya tayi tana mishi fada. ""Aunty Mom barci nake ji. Idan na ce"

"ku bari mu yi barci ba zaku yarda ba, amma gata Lunah bayan barci akwai wani abu da na.."" ture"

"keyarshi tayi tana faWin. ""Allah ya shirya ka wuce masjid;"" ta tura shi waje, daga nan ta riko hannuna ta"

"kara kawo ni gaban Mamarsu. ""Mum ga Lubnah!"" ""Labubu!"" Kaina a kasa ta rike hannuna, ta rasa bakin magana sai kuka, Daddah tsabar dad'i wani abun wuyarta na gwal ta cire ta saka min, ""tunda turaki ta kawo ka da sunan tana sonka, nasan bai yi zabin tumin dare ba."" Ba ta kara cire warwaronta, ta saka min a hannu. Yan uwan Mamanshi da suke zaune da kawayensu ba sai gashi anata zuba min kudi fa kyauta kamar ana hidima. Da yake an tura a kira su Aunty Hindatu, sai gasun nan, haka suka d'aga ni zuwa vangaren da xan zauna aka hada min ruwan wanka Aunty Zakiyah ta hada min kayan kamshi nayi wanka na gyara jikina na fito nayi sallah, sannan na gabatar da sallah da ya wuce min, sannan nayi isha domin za a yi min kwalliya, bayan na gama aka kawo min wani kaya irin na mutanen Ethiopia, haka saka min kayan tare da mayafinsa sannan aka gyara min gashina, ban ji dadin wannan kwlliyar ba. Ana cikin kwallyar ya shigo yana ganin gashin a bude ya ce bai san wannan zancen ba, hular da aka daura akan gashin ya kara fitar da ni, kasancewar Kakarshi Kirista ce har yanzu don haka kayan akwai Cross amma sai aka cire na kan hular, sannan muka fito bayan an gama shirin, su Aunty Zakiyah sun jima da barin"

gidan domin tas zai kunyata su.

Tunda aka ce zamu fito aka haska wani fitila da camera wanda suke can baya suna hango mu a

"majigi, sai suka huta da mikewa, flower girls dinmu Yaran Jasminah ne da Yaran mazan Uncle Auta, suka bude mana hanya muka cigaba da tafiya, Nusaiba yar Aunty Nuratu Kafaya ita ce da wasu yan Gym dinmu suka fito a bridesmaids, suka take mana baya a mazan da suka rufa mishi har da Ubaid. Haka"

muka isa wurin zaman muka zauna.

"Gashi an saka wakarsu ta can wanda suke yi da kafada, wasu daga cikin danginsu na can, sai wurin"

"yayi kyau. Haka akayi ta gabatarwa har aka gama kafin aka kira Ubaid ya bada labarin abokinsa, a hankali yake bada labari har ya gama sannan aka kira Nusaiba ta bada labarina, tun daga bude taron da Addu'a zuwa yadda take ba da labarina, kallon Aunty Zakiyah da ta d'aga min hannu nayi murmushi, bayan ta gama aka saka waka musamman namu na yan arewa, kafin aka saka wakarsu na Fulani. Kallona yake yana murmushi, bayan an fito da ni da shi. Aka yi ta zuba mana kuWi, daga shi har ni ba gwanayen rawa ba, haka muka tsaya musamman inda ya Wan saka hannunshi a kuguna da kuma rike hannunsa ina kallonshi. Wani abun da ya kara tashin hankalin a wurin masu adawa da aurenmu, musamman Badr ban ganta ba, na samu kyautar abin arzikin da abin duniya baa tashi ba sai karfe daya saura sannan aka raka su Aunty Hindatu zuwa gidan Ya Ado ango da yan uwansa, ni kuma aka wuce da ni bangaren fa aka gyara shi tas, aunty Innah har da cewa. ""Yanzu ba mamaki fitar nan har kin bashi hadin kai ko? Tow wallahi ba wani Woukin da zai yi akanki."" Tura baki nayi ina faWin. ""Wallahi ba abinda muka yi barci kawai yayi fa!"" Na fada ina jin haushi ko me na bashi ai hakkinsa ne, tun da muka dawo take fada, kamar nayi wani zunubi, bayan sun tafi Aunty Mom ta bani wasu abubuwan har da tarkacen mata irin na turawa, muna nan zaune da ita har suka dawo da yake har da Matar Ubaid da Uncle Auta, ana ta hira sama-sama, na lura matar Ubaid tana jin kanta ita wata shegiya ce, nima na nuna mata ni iyaka ce, suna shigowa kai tsaye wurina ya nufo ya cire min mayafin yana faWin.. ""zaki cutar fa fatarki da wannan uwar bargon wanda ko ita Momma bata isa yafa wannan abin ba."" Ya wurga da shi can kasa ya maza ya duba kafana da yake muna dawowa na goce da kafar, yana d'agawa yaga yayi ja. Rike baki yayi tare da dama a"

"kujeran ba juyawa Kanwar Uwarsa baya yana faWin. ""Yanzu kin san kafar tayi haka shi ne baki kira ni kin"

"d'aga min hankali ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wannan wacce irin masifa ce da tayi min asarar daren"

"amaarci."" Zuba mishi duka Kanwar Mamarsa tayi tana faWin.. ""kai dai baka da mutunci sai ka san yadda zaka yi da kafar."" Wallahi tsakaninsa da Allah ya kore kowa a gidan. Ya kuma nace sai ya cire gocewar."

""" Yanzu Lunah hakuri zaki yi na cire wannan abin domin wallahi ba zai hana ni sakat ba.""zare idanun nayi"

"na ce mishi."""" Ban isa ba wallahi ba zaka cire min masifa ba, ina zaman lafiya. "" Ai kuwa ya dauki wayarshi ya dokawa Kakanshi kira akan akan me zai shirya taron da na goce. Kafin wani lokaci tsofaffin nan sun iso gidan, ba sai gashi Uncle Auta ya dawo ba aka je a daren aka dauko me gyaran karaya, yayi tsalle ya tuma ya ce musu.. ""Malam gayan mun yadda ake cirewa amma ba zaka taba min matata ba!"" Sai da Uncle Auta ya ce mishi.. ""ka rungume ta domin idan kai ne waye zai rungume ta, haba don Allah."" Gyada kai yayi yana dawowa kusa da ni ya zauna, tare da rungume ni mutumin ya kama kafar ya latsa da"

kyau kafin ya ja wallahi ban san lokacin da na gantsara mishi cizo ba..........

"[12/17/2025, 7:29 PM] Maman Walid: 19"

"Shafa bayana tare da ce min. ""Shiiiiii!"" Sake fatar nayi tare da cewa. ""Don Allah ka ce ya bari na huta don"

"Allah ka gaya mishi ya bari na huta;"" ""Sake kafar ta huta!"" Ya fada yana bubuga bayana, ""sannu."" ""Boy dare yayi fa saura minti hamsin a kira sallah farko kai da matarka kun hana mu barci wallahi!"" ""Look at my eyes bari ya ja!"" Zare idanun nayi zan girgiza mishi kai, ya saka kaina a kafad'arshi, yana buga bayana, mutumin na jan kafar na fisge kaina zan yi ihu ya cilla min wani sweet a bakina na fashe da wani irin kuka. Tare da rungume shi. Kuka nake yana shafa kaina. Har aka gama jan kafar ina kuka, Daddah tayi ta min"

"sannu, anan barcin wahala yayi gaba da ni."

Haka suka watse a gidan kowa yana tausaya min. Cak na ji kamar ina yawo a iska na bude idanu me

"cike da barci na kalle shi, murmushi yayi min sannan ya ce min. ""Yi barcinki, my chest is your special bed, don haka rufe idanunki."" Ya fada yana tafiya a hankali har dakinshi, ya kwantar da ni a hankali, ajiyar zuciya na sauke ya shiga ban daki yayi wanka da alwala sannan ya fito, ya ja min bargo yayi sallah. Kafin ya kwanta. Sai da yayi sallah nafilla kafin ya Wan kishingida, yana addu'a gyangyadi yana fisgar shi ya Wan kwanta. Ai kuwa barci ya dauke shi, sai jin shigar sallah yayi da sauri ya shiga yayi alwala ta nufi masallaci, bai fito ba sai da garin ya fara haske. A hanya ya hadu da Kawunsa da Mijin Goggonsa kallo daya ya musu ya shiga shafa gemunsa cikin murmushi irin na tantiran yan duniya, ya d'aga musu gira irin tow ya nima haka nake, don iskanci goya hannu yayi a baya ya cigaba da tafiya yana murmushi. Tabbas yana shiga musi hanci da kudundune. Yasan su ne suka shirya aka dawo da shi gidan don haka sai ya fitine su da rashin kunya da rashin mutunci yadda da kafarsu, zasu zo su ce ya bar musu gidan. Duk yadda aka tsara ya sani amma yafi son su fuskanci guilty din tare da shi, yadda suka yi amfani da damarsu. Sai da ya isa"

kofar gidansa ya fara wani iyayi irin na zumudin sabon ango.

"Ai ko da ya shiga cikin gidan, dakinsa ya wuce ya samu tana barci abin ya burge shi, amma ya zauna a"

"bakin gadon yana wani murmushi yana jin wani irin dad'i da nutsuwa. Kayi mafarkin kai Gwauro ne ba karamin masifa ba ce, shafa kaina yayi sau biyu na bude idanuna. Da suke cike da barci a hankali ya ce min. ""Good Morning Queen!"" Murmushi nayi na tashi zaune kafin na ce mishi. ""Kayi hakuri ban yi sallah ba."" Na dauko a hankali na daura kafar a kasa, sai naji babu zafin sosai zan mike naji ya janyo ni, sumbatar goshina yayi yana faWin. ""Kin yi kyau!"" Murmushi nayi na kara mikewa, ya dawo da ni na zauna ina kallonshi. ""Lokaci yana kurewa!"" ""Ok muje na raka ko!"". Ya fada na mike a hankali, zai dauke ni na ce mishi. ""Don haka ka yi hakuri wallahi xan tafi da kaina."" Murmushi yayi ya ce min. ""Nayiwa Mama al™awarin kula da autarta!"" Haka ya dauke ni har ban daki. ""Ni dai ka fita xan iya kome da kaina."" ""Tow!"" Ya fita ni kuwa nayi wanka da alwala a gurguje, na fito nayi sallah. Ina idarwa ya shigo da mug na tea, mika min daya yayi ya ajiye na shi ta fita can sai ga shi da Pjym riga da wando ya mika min."" Kwanta muyi barci!"" Kallon kayan nayi sai kuma na amsa na nufi ban daki na saka, ina fitowa ya zubawa kofar ban dakin idanun kuri, kunya ce ta rufe ni na saka hannu bibbiyu na rufe fuskana. Tasowa yayi ya balle gaban"

"rigar yana murmushi ya ce min ""haka nake son ganinki!"" Ya janyo ni zuwa bakin gadon ya zaunar da ni."

"Yana sonta yana kaunarta amma baya son ta ga kamar don jikinta, baya son ta ga kamar bai da hakuri"

"akanta. Ko dama can yana kwadayinta ne. Zama ya kara yi ya daura kafa daya akan Waya, ya janyo ni jikinshi. Haka yasa na daura kaina a kafad'arshi. Murmushi yayi. ""Na jima ina addu'ar wannan ranar, yau ni ne Matata ta daura kanta a kafadana! Alhamdulillahi alakulli halin."" Ya furta yana murmushi, ina gama sha ya amshi kofin ya fita da shi, can ya dawo ya kashe wutar dakin, sannan ya zo ya riko hannuna muka kwanta. Janyo ni yayi kan pillow shi, ya kuma ja bargo ya rufe mu, ya ce min. ""Ki yi barci domin nima barci zan yi!"" Daga haka na sauke ajiyar zuciya, ""ki yi barci hankalinki kwance domin kina tare da Mijinki ne."" Gyara kwanciya zan yi ya gyara min tare da daura kaina a kirjinsa. ""This is your place, wurin naki ne ke Waya!"" A hankali ya cigaba da shafa bayana, tun ina jin wani irin yanayi har barci yayi gaba da ni, sosai wunin ranar muka yi barci, da alamu kowa ma yasan cewa muna hutuwa, karfe daya na rana muka tashi saboda yadda ake buga kofar gidan daga waje, sake lumshe idanuna nayi na bude a hankali, zame jikina nayi daga nashi na nufi ban daki fitsari nayi sannan na wuce waje bayan na saka doguwar hijab har kasa, bude kofar nayi yan matan nan ne, na zuba musu idanu. Ban ce musu kalla ba, sai jin shi nayi ya rungume ni ta baya.""uban me kuka zo yi?"" Hannunsa ya sakalo shi ta kan cikina. Daura nawa hannun nayi akan nashi. ""Maybe sun zo ganin wuri ne, su shigo mana!"" Na fada ina juyawa cikin gidan. ""Before na je na dawo na ga wata Yarinya sai na mata rashin mutunci."" Ya fada tare da banke kofar, ai kuwa bamm kofar tayi kara. Wato shi dai kome na shi daban ne. Kitchen na nufa ya biyo ni, cire hijab din yayi yana faWin. ""Yanzu da zance mu yi wanka!"" Rufe mishi baki nayi da hannuna ya shiga sumbatar hannun na kwace ina faWin. ""Me yasa baka jin nauyi ne?"" Kallon sama yayi kafin ya kalli gefe da gefe yana niman wani abu can ya ce min. ""Nauyin wa zanji? Naki?"" Ya nuna ni da yatsa sai kuma ya janyo ni yana faWin. ""Gaya min yadda ake jin kunya sai na fara akanki?"" Na jima ban ga tantiri irin wannan mutumin ba. ""Ina wayata take ne ma? Na ji su Aunty Innah zasu shigo ne?"" ""Eh kai zasu shigo da karfe biyar na yamma."" Sake baki nayi na ce mishi. ""Au kasan da haka daman?"" Na tambaye shi, jingina yayi da wall din kitchen din, yana faWin. ""Eh kai na sani hala sai kuma ki yi kuka?"" Ya fada yana jan hannuna zuwa waje dakin da"

"nake tsammanin shine nawa ya kai ni, ya ce min."" Ki yi wanka ga Ni nan zuwa."""

"Ban daki na wuce nayi wanka da alwala, sannan na fito ina daure da towel, shigowa yayi sai kuma ya"

"juya ganin nima na diririce, ai kuwa yana fita na yi maza na saka kayana, sannan na fito na same shi yana tsaye, murmushi yayi min ya ce. ""Muje mu yi sallah."" Haka na bishi har dakinsa, muka yi sallah. A lokacin yunwa ya dame ni. Riko hannuna yayi muka bar gidan bayan na koma dakin na gyara fuskana, hannuna cikin nashi muka isa har gidan kakanshi, tun da muka shiga ake min sannu har na samu wuri na zauna ina gaishe su, abinci aka kawo mana na ji yana ta fulatanci, ai kuwa Daddah ta rufe shi da fada aka shiga kawo min abinci, kafin wani lokaci an cika min gabana da abin karyawa. ""Kayi hakuri Turaki bata jin magana ashe haka ya barka da yunwa har yanzu."" Murmushi nayi ina kallonshi, hada min abin karyawa yayi ya mika min tea din na fara sha, da zafi na ajiye mishi ina hura bakina. Dauka yayi yana d'aga min har yayi huce na dauka na fara sha ina murmushi. ""Sha Chika!"" Haka na karya shima ya ci kaWan, kusan sai da naci na bar mishi sannan ya ci. Ganin yadda na zaSi wasu abubuwan wasu kuma na bari ya sake murmushi yana faWin "" kina loss weight ko?"" Ci yayi yana faWin ""cigaba da rage kiba, kin ga ni na ci Abinda kika bari ina laifi."" Haka muka gama sannan aka kwashe ya riko hannuna muka tafi dakin da Kakarshi ta wurin Uwa take, ina shiga ta rungume ni tana faWin. ""Labubu kin ji sauki kenan?"" Gyada mata kai nayi ya ce mata. ""Granny meye matsalarki da ni yanzu bayan na yi aure kina min kallon banza ko kishi kike ne don nake na yi ba?"" ""Allah ya rufa min asiri."" Ta fada tana buga mishi sanda ya kauce yana dariya sannan ya fita ya barmu a dakin, mun sha hira da ita kafin ta ke gaya min ""an jima zamu koma gida ma yaushe zaki zo mana!"" Murmushi nayi na ce mata ""Sai ya kawo ni!"" Haka muka yi ta hira jife-jife har na tayata hada kayanta, ta dauko kudi me yawa ta bani, nayi ta Godiya. Shigowa yayi ya ce mata. ""Ki fito gashi an zo Waukarki!"" Ai kuwa na rakota zuwa waje, a lokacin suke gaisawa da sauran mutanen gidan, haka ya rakata har wurin motar ta kira ni. A hankali na isa wurinta na tsaya, riko hannuna tayi ta saka min abu a cikin hannuna. "" Ki kula da Mijinki da kyau, ki kuma kula da kanki."" Ta rike hannuna alamar tana bani abu me muhimmanci, sannan ta sake hannuna yazo gefena ya rufe mata kofa yana faWin. ""Granny yarinyar nan ta kwace min ke!"" Murmushi tayi tana faWin. ""Ka taimake ni ka rike musu yar mutane!"" ""In sha Allah!"" Ya fada, bayan ya ja hannuna baya, suka tashi motar suka bar gidan, yana d'aga musu hannu. Sannan ya mai da ni can parlourn Alhaji ELYakub Kumo, muka zauna a rough carpet din parlourn, mika min wani album yana faWin. ""Wannan hoton zuriarki ne!"" Amsa Yayi ya mika min, a hankali na fara bude shafi zuwa shafi. Hoton Babanshi ne na farko ya matso kusa da ni. ""Wannan shine Papa!"" Juyawa nayi ina kallonshi. ""Kuna kama!"" Bakin shi na ji a kan hancina. ""Sosai kai!"" Ya fada bayan ya sumbaci hanci. Sosai ya matso kusa da ni, kamar zai boye ni a jikinsa. Wani hoto na bude, hoton"

"Mamanshi ce. "" Mammy ko?"" "" Ya aka yi kika san Mammy nake kiranta?"" Ya fada yana sumbatar kuncina. "" Bari mana Chairman yana nan fa?"" ""Tuni ua gudu parlourn wurin Matarshi."" Da mamaki na kalli wurin da yake babu alamar shi. Gira ya d'aga min. ""Ai na gaya miki, ni lamarina mai karfi ne!"" Tura baki nayi, yayi maza ya rike bakin da yatsarsa guda biyu. ""I like this lips!"" Ya fada yana sakewa. ""Kika kara tura min baki sai na ciza!"" Hoton bikinsu ba buWe. ""Lokacin ina zero kafin na zama plus.""

Please Login or Register in order to submit comment