You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katse kiran, ba zan kara shiga damuwa akan wani namiji ba, haka yayi ta kirana amma naki dauka asalima kashe wayar nayi na shiga aikin gidana baji ba gani, kusan da yake raina a b'ace yake aiki kawai nake har da su wnki a washing machine, bayab na gama na koma dakina na kwanta ina da miya a frij. Shi na fitar idan suka zo sai na"

dafa shinkafa da dodo.

"Wurin karfe sha biyu Uncle Auta ya zo da Matarshi, Ni abin sai ya dame ni. "" Ni fa ba fushi nayi ba,"

"amma shi yana ganin kamar nayi fushi ne? Lallai fa ita ai yar uwarsa ce, sannan ko babu kome akwai aure a tsakaninsu akan me xan bawa kaina wahala kan namiji, ni zama da kishiya ba bako bane a wurina, idan zai kara aure wallahi ni ban isa na hana ba, shi yake ganin haka babban tashin hankali ne, na taso naga gidanmu mata biyu ne haka yasa na sakawa raina duk inda aure ya kai ni tow akwai wata ko na samu"

"wasu, amma wallahi ni ban ji kome ba!"""

"""Ok me yasa kika kashe wayarki?"" Murmushi nayi na ce mishi. ""Nasan halinsa yanxu zai ta ™o™arin sai ya"

"gamsar da ni akan yana da gaskiya, bayan ni nasan yana da gaskiya. Idan ya cika son sai ya min bayani zan iya jin behind the scenes yana yin wani abu ne, shi namiji ne ya kamata ya tsaya akan kafarshi. Ba laifi ba ne ya gaya min gaskiya amma bana son a kan kaina na yiwa Mijina kallon wanda ya kasa."" "" Na gamsu da maganarki amma ki kunna wayarki wallahi zai iya hana iyayenmu zaman lafiya sai ya saka su"

"zo na gaya miki gaskiya idan kin yarda. """

"Kunna wayar nayi sai ga kiran ina dauka ya ce mishi. "" Yanzu nake shirin kiran Datti da Daddah! "" "" Da"

"kuwa baka kyauta."" Nan muka shiga hira su Uncle Auta suka bar gidan, muna gama wayar na kashe, sai ga kiran Aunty Zakiyah, wai suna kofar gida na zo an hana su shigowa, haka na fita na shigo dasu, muka zube a parlourn, muka yi ta hira a dauko musu abinci suka ci, sannan muka yi sallah La'asar bayan nan ya kira ya ce."" Ya nake jin muryan Yara sun iso ne?"" Nace mishi eh , daga nan suka yi sallah, zan iya cewa daga nan muka shirya dai dare Ya Ado ya zo ya dauke su, ya bar mun Takwaran Mama,har da uniform"

dinta na makaranta.

"Na ji dadi haka na cigaba da kula da gidan, sai dai duk lokacin da muke waya sai naji muryan Badr, kusan"

"kamar da gangan yake zama kusa da ita. Kawai sai na sakawa raina matu™ar zan ji muryanta zan kashe wayar. Shima kuma ya gane idan zai yi waya da ni, sai dai ya bar inda take. Ya ce min ganin likita take amma da na bude data na ga hotonsu ana ta sakawa a status. Ba karamin ™o™ari nayi da na danne zuciyata, na zuba mishi idanu. Har ya dawo cikin ikon Allah ranar juma'a, suka zo gidana ta nuna min ta fita da mijina, dauke kai nayi kamar ban san me yake mun zafi ba, amma na san yadda nake ji. Tunda na tarbe shi ban kara bin ta kanshi ba, sai dare na rufe kofana. Tunda ya kaita bai dawo ba sai sha biyu saura da ya dawo ya samu kofata a buWe. Yayi bugun duniyar nan nayi kamar ban ji ba, washi gari ban fito ba sai karfe tara, na wuce kitchen yana parlourn yana karyawa. Nayi kamar ban ganshi ba. Wallahi ba zan iya hakuri akan wannan ba, domin yadda tayi ta min iskanci tana kallona tana dariya. Yafi kome yi min zafi. Ina tsaye ina fitar fa abincin jiya da bai ci ba, ya bar min na zuba musu ruwa, shigowa yayi ya ce min. ""Jiya ni daya na kwana!"" Shiru nayi domin abinda yake bakina idan na fada sai ya kusan suma, haka yasa na ciza bakina sai da ya fashe. Sake bakin nayi a hankali na wuce na hado kayan tea na daura a tunkaya.. ""Lubabatu nayi wani abu ne?"" Murmusa mishi nayi ina faWin. ""Me ya faru?"" Na tambaye shi. ""Amma naga kamar kina wani abu da ban saba gani ba ne."" ""Ok ba mamaki kai kake ganin haka;"" na fada a takaice ina nufar inda tukwane suke, na wanke na juye miyar na dumama. Sannan na wuce na dauki plat da cokali na jera abincin da kome da kome, sannan na nufi hanyar waje ya amshi tiren na koma na juye ruwan zafin, na nufi parlourn na zauna a hankali na fara ci. Da cokali Waya. ""Ina cokalina?"" Kallonshi nayi sannan na ce mishi. ""Wannan abincin ba zai ishe mu ba;"" ""kamar ya? Naga abincina na ne na jiya."" ""Ai ya koma na kowa da kowa!"" Na fara ci a hankali fir na hana shi. ""Wai meye matsalarki ne?"" ""Kai ne?!"" Na bashi amsa, ""kai ne matsalata idan ina da wata matsala kai ne. Idan zaka auri Badriyyah lafiya lau, amma kawo min ita ko zuwa ka zauna sai sha biyun dare wallahi ba zan yarda ba, kashe nayi maka yasa na rufe kofar gobe ka kara dawowa min gidan rufe shi zanyi.;"" na mike xan tafi ya dawo da ni"

"na zauna yana murmushi, ""kishi haka lunah........"

"[12/21/2025, 3:54 PM] Maman Walid: 24"

"Ya fahimci raina a fusace yake kuma a kufule nake, sai ya fara cin abincin har ya cinye yana murmushi. """

"Babu wata mace da zata shigo min! "" "" Waye ya sani ita fa virgin ce ni kuma fa?"" Rike bakina yayi yana faWin."

"""Ba ruwana da Virgin ko rashinsa, ke nake so ba budurcinki ba, ke nake so ba fuskarki ba, ke naso ba"

"wani abu ba, soyayyarki halitta ce daga Allah, zan so ki zan kaunace ki zan kuma kare ki, sannan zan hana ki kuka, zan saka ki murmushi da farin ciki, hannuna kawai zaki rike na cika wannan al™awarin da na miki"" kura mishi idanu nayi a hankali naji hawaye na zuba min zuciyana ya karaya, tsoron kada shima ya min halin Hafiz na fara kuka wiwi karshe na bar mishi parlourn zuwa dakina ina kuka. Shigowa dakin yayi ya same ni ina zaune sai kuka nake, durkusawa yayi a gabana. ""Tsoron me kike ji?"" Girgiza kai nayi ina shashekar kuka. "" Yar uwarka ce, ni kuma bare, akwai lokacin da Alakar zuci baya tasiri sama da dangantaka. Idan ba zaka zauna da ni ba ka gaya min na tafi ka ji, don Allah kayi hakuri ka ce min na tafi wallahi."" Wato wani irin rungume ni da yayi tare da buga bayana. ""Shiiiiii"" yayi ta fada min sannan ya janye ni a jikinshi yana share min hawaye. Murmushi yayi yana faWin. ""Kin yi kyau, ina ganin mace tana kuka bata kyay amma ke kuka kyau yake miki? Ji wannan hancin don Allah!"" Wato ba iya rarrashi ya iya"

"ba, hatta dauko wani abun da zai mantar da ni fushin da nake yi sai da ya raba ni da fushin, sannan ya"

"janyo hannuna muka fita parlourn, wani abu da na fahimta tun kwanakin da muka yi na sati Waya a"

"gidan, Malamina ba mutu me yawan shan ruwa bane, idan ka ga ya sha ruwa to bukatar haka ce ya taso mishi, kuma idan dai sha ruwan yana sha dayawan gaske ne yadda idan ja shiga hannunsa bana marmarin sake fadawa hannunsa, domin duk sauran kwanakin da yayi da ya dawo daga tafiya bai wani damu da ya fanshe su ba. Wannan abin sai ya tsaya min a rai na daura mishi ayar tambaya. Me yasa bai"

damu da ya bukace ni ba.

"Domin ban san cewa haka tashi halayyar yake ba, ranar haka muka kwana duk da ina son ya"

"bukatar shi amma sai na lura kamar shi yafi bukatar hutu, don gefena can ya je ya kwanta. Kuma yana kwanciya sai barci. Ban iya barci ba daren nan haka nayi shi ina juyi domin na sha abubuwa wai irin miji zai dawo nan na gyara jikina. Sai dai kash babu abinda ya faru, tashi nayi a hankali na wuce dakina."

"Kusan kwana nayi ina juyi da naga abin ba zai kare ba, na tashi zuwa ban daki nayi alwala na fito, na"

"gabatar da sallah nafilla, har dai da na fara jin barci na koma gado na kwanta."

"Da asuba da ya farka ya ga bana dakin, sai da yayi wanka sannan ya shirya ya tafi masallaci, bai dawo ba"

"sai da gari ya fara haske. A lokacin da ya shigo ya same ni akan abin sallah, ina azkar zama yayi na ga fuskarshi kamar akwai damuwa da gajiya ya kalle ni. Na shafa addu'a, na gaishe shi bai amsa ba, ni kuwa na share na tashi na fara nad'e abin sallah. Ina tsaye naji ya rungume ni ta baya yana faWin.. ""Matar Turaki, jiya sai da kika saka ni barci sannan kika gudu wai me nayi ne?"" A hankali na janye daga rikon da yayi min na wuce inda nake ajiye abin sallah na ajiye sannan na cire hijab dina, na nad'e shi sannan na"

"koma gadon na kwanta, kafin na ce mishi. ""Ka je ka kwanta ka huta gajiya akwai gajiya a tare da kai."""

"Murmushi yayi ya biyo ni gadon yana faWin. ""Ai a wurinki zan huce gajiyar Matar Turaki tana fushi da"

"Turaki na shiga uku na!"" Ban kula shi ba, haka ya haura gadon daga nan kuma sai da ya tabbatar da fushin da nake ya kare duk wani rigimar da nake ji ya tafi kamar kura akan iska, muka dulmiya juna cikin duniyar kaunar juna. Daga ranar bai kara yayi tafiya ya dawo ya nuna min ya gaji yayi ta barci ba, yana dawowa zai huce gajiyarshi da ni, ni kaina lokacin zamana da Hafiz nasan ba haka nake ba, amma a yanzu na zama wata yar iska irin dai matar da basu gajiya da tattaunawa cikin dare nan, kuma ai maganar gaskiya ni bazawara ce, ta wannan wurin ai ina da hadda har da tartil taya ga katon mutum a gidana za a ce nayi hakuri da shi, ko shi ba mutum ba ne. A bangaren family Winsu ba karamin uzurawa suka yi akan ya auri Badriyyah ba. Shi kuma da yake dan duniya ne ya ce ba zai aure ta ba, ko yanka"

namar shi ake ana gasawa ba zai aure ta ba.

Badriyyah tana da wanda yake sonta amma bakar jaraba ta hana kanta hango haka.

**

Hafiz

"Tun baya da Turaki ya mishi shegen duka, ya bar Lagos ya dawo ya shirya da kyau, sai dai Me yana isowa"

"Jama'are, ya samu labarin Karima ta zo ta kwashe Yaranta, wani abin tashin hankalin Yaran da yake ta"

"zargin na shine ta ce a gaya masa Yaran ba nashi ba ne, Yaran da ta haifa na tsohon saurayin ta ne,"

"sannan kada ya ce zai nime ta domin ba zai same ta ba. Kusan hauka ne Hafiz ne bai yi ba domin sai da aka daura shi a gadon asibiti, daga karshe aka tura su asibitin Bauchi domin abin kamar zai saka shi hauka, kafin aka shawo kan matsalar, tun da ya dawo hayacinsa ya tuna ya kashewa Lubnah bata mahaifarta bayan shine baya haihuwa, ya wulakanta Lubnah akan Yaran kai duk abinda yayi na mugunta sai gashi yana dawo mishi, haka zai zauna yayi ta kuka. Domin yasan yanzu kan Lubnah ta mishi nisa,Ita kanta Jalilah da ta fahimci Hafiz din da ta sani ba shi ne yanzu, sai ta fara niman hanyar da zata rabu da shi, ranar wata Alhamis bayan isha yana zaune ya zubawa tv idanu. Ta zo ta zauna da takarda da biro ta mika mishi. ""Ina son ka sake ni, domin kaima kasan naka haihu ana aure don a hayayyafa ne kai kuwa baka da wannan damar."" Murmushi yayi sannan ya ce mata.""lokacin da nake tare da Lubnah kina daga cikin mutanen da suka yi ta zuga ni na rabu da ita? Na kara mata kishiya, nayi yadda nake so amma yau an wayi gari don bana haihuwa ki ce zaki rabu da ni? Ina soyayyar da kike min Wanda yasa kika gagara zama da mazankina baya? Yanzu bani da amfani zaki guje ni. Ai ba zan iya rabuwa da ke ba domin sai na"

"fanshe sadakina sai na rabu da ke."""

"""A'a Hafiz ni bance ka rabu da Lubnah ba!"" Murmushi yayi ya bai kara magana ba, yana kallonta tare"

"da nazarin abinda zai mata yadda zasu yi balance. Haka ta bar parlourn yayi ta nazarin, ya rasa Lubnah har abada, ya sani kashedin da Mijinta ya mata kaWai ya razana shi amma ya zai yi? Yana son Lubnah ko wani hali yana son ya rabata da kwanciyar hankalin gidanta. Yana son ta fuskanci halin da yake ciki, amma yasan ko me zai yi ba zata tab'a dawowa gare shi ba. Amma kuma yana da hanyar da zai dawo da"

ita gare shi ko bata dawo ba itama ta fuskanci yadda yake ji.

"(Labarin Hafiz ko ba zance muku kai tsaye gaskiya ba ne, amma kuma akwai maza ire-irensu da suke"

"ganin idan basu sami yadda suke so ba, gara ayi ragas kowa ya rasa, sannan idan suka ga mace ta samu"

"nasara a Rayuwarta bayan rabuwa da su, sai su fara jin ciwo da bakin ciki burinsu su ga ta wulakanta. Allah yasa mu dace!) Amma kafin ya zo ga Lubnah sai ya fara ta kan Jalilah."

**

Allah ya gani ta kowani fuska Ni da mijina muna samun zaman lafiya. Sai dai kuma yadda wasu

"abubuwan suke faruwa da barazanar da nake fuskanta yasa na gayawa Mama, murmushi tayi tana faWin. ""Ai ko na kwantar da hankalina, miji mata hudu ne shi, ba xai yiwu ki ce ba zai kara aure ba, idan kika ga haka shine maslaha ki kwantar da hankalinki, idan kuma kika fara fuskantar matsala ki min magana nazo na dauke ki."" Sai na samu nutsuwa ko ba kome Mahaifyata tana tare da ni, ko sun yi magana da ita ne naga ya dan damu da zuba mishi idanu da nayi, har ya kai ni gidan Ya Ado na wuni sannan ya dawo da ni"

gida.

"Sannan wani abu da na kara fahimta, mutum ne da ba zai yiwu ya boye maka kome ba, amma dan"

"zaman da nayi da shi sai na hango mutane biyu da suke tare da shi, kusan kamar shine yake kulawa da su."

"Akwai wani abu da na kara yarda cewa mutum ne shi mai matu™ar kishi, hana Ubaidullah shigowa"

"gidansa. Haka idan ka ga Uncle Auta a cikin gidan nan, tow abu me muhimmanci ne ko tare suke,"

"tsakaninsa da Ubaidullah parlourn baki ni kuwa bana tab'a shiga domin kai tsaye ya gaya min, Ubaid da Uncle Auta, suna da tsalle shi kuma yana da kishi, idan ya wuce gaisuwa don Allah bai yarda na sake da su ba. Sannan idan baya gari duk abinda zasu kawo min iya waje zasu tsaya su bada a kawo min cikin"

gidan. Wannan yasa ko gidajensu ban cika zuwa mazan nan ba.

"A watan da muka cika wata uku da aure ne, wata makociyar mu ta haihu. Suka gaya min da yake yar"

"arewa ce. Matar Uncle Auta ta gaya min ta waya, yana dawowa daga Office bayan ya ci abinci na gaya mishi. Murmushi yayi ya ce min. ""Ok sai kin dawo!"" ""Na gode sosai! Ai sai gobe zamu shiga gidan!"" ""Tow Allah ya kai mu!"" ""Amin Ya Allah!"" Bayan ya gama cin abinci muka dawo parlourn ina jikinshi aka buga kofar gidan, kallon juna muka yi ya mike ya fita can sai gashi da Matar Ubaid, Maman Nihla. Zama tayi na tashi na kawo mata ruwa na ajiye mata. Sannan na koma dakina. Ban san me ya faru ba amma yadda take kuka da mishi bayani da fulatancin yasa na fahimci rigima ce. Kwanciya nayi na cigaba da abinda nake yi da nake da Aunty Hindatu. Muryan Ubaid na ji sama-sama, fada kamar zasu daku. Har sai da na fita don na ji maganar da hausa Mr Turaki yana faWin. ""Ai gaskiya ne akan me xan barka ka shigo min gida, bayan nasan waye kai, na san halinka matarka baka tsaya a kanta ba, baka Musulmi baka Kirista, me kake son cimma? Idan ba rashin mutunci da rashin arziki ba."" Fitowa nayi suka juyawa zuwa gare ni. Allah yasa da hijab har kasa, ""Me kika fito yi?"" Ya daka min tsawa, juyawa nayi na koma dakin. ""Ai na gaya maka ni matata sirrina ce, har abada ba zaka tab'a samun damar kare mata kallo na, kayi focus din matsalarka. Idan ka rungume matarka zaka fahimci nimar da Allah ya maka, ita Lubnah da kake cewa matarka tayi koyi da ita ka manta yadda muka yi da kai ne? Don Allah kada ka lalata min aurena domin ni"

"ban shiga rayuwar gidajenku ba."""

"Da haka na fahimci idan matar shi tayi mishi wani abu yake huce haushinsa akanta bata iya kome ba,"

"ga Lubnah nan tana yin abinda ya dace a gidanta, dama ba shiri muke da ita ba, ashe Mijinta ya kara a abubuwan da zai kara dagula lissafin kome. Kawai sai naji zuciyata bata min dad'i ba......"

"[12/23/2025, 12:47 PM] Maman Walid: 25"

"Don haka suka gama rigimarsu, ya shigo zai min masifa na saka mishi kuka. Ganin yadda nake kukan da"

"gaske sai ya rungume ni yana shafa baya har nayi shiru. ""Dayawan mutanen da suke kusa da ni idanunsu akanki yake ni kuma kishi ne da ni kamar na cire zuciyata na fitar da shi waje. Ina sonki dayawa don da na kasa boye shi, sorry idan nayi kuskure ki yi hakuri kin ji!"" A hankali na janye kaina daga jikinshi, zuwa"

"yanzu na fara jin tausayinsa be mess with everyone domin ni. ""Kin yi shiru?"""

"""Tsoro nake ji, tsoron kada kishi ya cigaba da ruguza zamanmu!"" Na faWa ina shashekar kuka."

"Murmusa min yayi tare da rike hannuna, ya ce min. ""Tabbas ina kishinki, ina kishin wasu mazan su kalle ki. Ina kishin idan na tuna duk tarin ni'imar da Allah ya miki kafin ni wani ya fara WanWanawa ina ji kamar na mutu, a duk lokacin da na tuna Hafiz ya fara samun kusanci da ke kafin ni sai na ji ban cancanci haka daga kowacce fuska. Look ina da zafin kishi wallahi ina ji kamar ni Waya Allah ya halitta da kishinki."" Ya d'ago kai yana kallona idanunsa sun jajjur murmushin karfin hali yayi kafin ya ce min. ""Ina da kishi"

"sosai!."""

"A hankali na janye a jikinshi, na cigaba da kuka, zama yayi a kusa da ni yana faWin. ""Amma ba ina bin"

"abinda zuciyata, ta saka ni ba ne,. Kawai abu daya na san ina yi shi ne kaurace miki, dole na ke saka kaina"

"a tare da ke, nayi ™o™arin danne haka amma ina."""

"Aure wata uku zuwa hudu yau Turaki yake gaya min yana kishina, kishin da yake yasa shi kaurace"

"min? Kallon kasa nayi ta yi ina jin kamar zuciyata zata buga. A hankali na matsa daga kusa da shi na koma can gefe. Nayi shiru na rasa me zan yi na huce idan nace ya sake ni ma ba zai sake ni ba. Don haka nayi shiru ban kara magana ba, sai dai shi a lissafinshi ai ya fada min abinda yake ranshi ne, don na daina jin zafinsa, ni kuwa sai nake ganin gara mu rabu kowa ya kama gabanshi. Idan ba haka ba, a banza zan ta"

cuta da sunan kishin da yake ji da shi.

"Duk yadda yaso ya rarrashe ni, zan ture hannunsa ina murmushi. "" Na fahimce ka ai! "" Daga haka na"

"datse duk wani abin da yake tsakaninmu, daren ranar ban shiga dakinshi ba da ya zo yana tambayar ko abinda ya fada ne ya saka ni ware kaina daga gare shi na girgixa kai nace mishi, ga ""period nake bana son Magana!"" Kuma nayi dace period din ya zo, don na samu sauki na bar shi, haka yayi hakuri ya koma dakinsa, na kyale shi ya zauna shi Waya. Washi gari, ban tashi nayi abin karyawa da wuri ba, ina tashi na hada mishi tea da bread da egg, na koma na kwanta. Lokacin da ya shigo dakin ina juyin ciwon ciki, ""ko za mu tafi asibiti ne?"" Girgiza mishi nayi tare da cewa. ""Ba damuwa ka je ai ba kome."" Haka ya bar gidan da kyar shima sai da ya makara. Wurin karfe biyu na gama abincin dare da na rana, don ya ce zai zo duba ni. Haka na gama kome nayi wanka, da ya tashi zuwa sai gashi tare da Airah. Yadda take wasu abubuwan yasa na kai zuciya nesa. Murmusa mata kawai nake, har ya ci abincin ya kalle ni cikin kulawa ya ce min.. ""Ya jikin naki?"" Murmushi nayi kawai na cigaba da cin apple. ""Da sauki ko?"" Lumshe idanuna nayi ina gyad'a mishi kai. ""Allah ya baki lafiya."" Tura mishi sako aka yi ta wayar ya duba, tare yanayinsa ya sauya. Ya kalle ni da kyau sai ya cire hannunsa a cikin abincin yana faWin. ""Na koshi!"" Ya fada yana ture plat din, murmushi nayi na tashi na hada juye wanda ya ci na gyara wurin, ya ce min.""mu koma!"" ""Allah ya kiyayye hanya!"" Na shige kitchen a bisa ka'ida raka shi nake, amma na barshi ya fita shi kanshi sai da ya juyo ya kalle ni, sannan ya bar gidan. Sai da na shiga kitchen hawaye yayi ta zubo min. Haka na sha kuka"

"na ban gayawa kowa ba, shima kuma ban san dalilinsa nayi haka ba,"

"Wurin karfe hudu da rabi, na fita gidan Uncle Auta, muka tafi gidan barka a can muka hadu da Matar"

"Ubaid, kamar yadda ta yi kamar bata ganni ba, haka nayi kamar ban santa ba, na cigaba da danna wayar ita kanta mai jegon da yake kawarta ce da kyar ta amsa min, ban yi karambanin a bani yaro ba, daga kan cinyar Matar Uncle Auta na kalle shi, daga nan na cigaba da uzurina. Ba zaka fahimci yadda abin yake ba, kusan kowa a gidan sai na fahimci kamar baya maraba da ni, har muka fita daga cikin gida, bayan mun dauko hanya ne matar Uncle Auta take tambayata. ""Wani abu ya haWa ki da Maman Nihla ce?"" Girgiza kai nayi ina kallon kasa. Na d'ago na ce mata. ""A'a."" ""Tow shi kenan!"" Daga haka muka isa gidanta na zauna kadan sannan na wuce gida, ina shiga na same shi yana aiki, ""sannu da dawowa!"" Ya ce min, murmushi nayi na yi nace mishi. ""Yawwa!"" Na wuce dakina na barshi a parlourn yana aiki, kiran sallah"

"Magariba yasa shi lekowa ya samu ina tattara wasu takardun, zuba min idanu yayi kafin ya ce min. ""Me"

"zaki yi da su?"" Murmushi nayi mishi, na ce mishi. ""Ina shiri ne in case."" Daga haka na cigaba da aikina. Kai"

"wasa wasa sai da muka shafe sati uku zuwa wata guda hala har ya manta ya gaya min bakar magana, tafiya ta kama shi Russia, mutumin nan na zata zai ce min na shirya mu tafi amma ya wani hada kayansa yayi gaba, ni kuwa na hada nawa kayan na wuce Bauchi don tsabar masifa mota na bi, balle har ya bincika ya ji labarin inda naje, zuwa yanzu watanmu hudu da sati biyu, a cikin watannin nan bai wuce a"

"kirga hada shimfidar da muka yi, haka na shanye duk wani b'acin rai."

"Kwana biyu me kyau muka yi a hanya, muka iso Bauchi kafafuna sun kumbura. Sai da na wuta"

"sannan na dauki keke napap, zuwa gidana da yake G. R. A. Ya samu me kula da gidan yana waje, na isa cikin farin ciki ya amshi jakata yana tambayar ya hanya? Na ce Alhamdulillahi, na shiga bayan ya bude min, sannan na shiga cikin gidan. Kasancewar isowar safiya ce mika mishi atm nayi na ce mishi. ""Don Allah ayi min cefane, sannan ka haWa min da dankalin turawa, kome dai ka kawo min and ina niman"

"alfarma kada wani ya tambaye ka, nazo kace na zo don Allah!"" ""In sha Allah Hajiya."""

"Daga haka na wuce cikin gidan na shiga aiki, nayi wanka na gabatar da

Please Login or Register in order to submit comment