You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Matarshi suka kawo min ziyara, a bakinsa nake jin labarin business Trip din da yayi, haka na bawa kaina hakuri na shanye na cigaba da hakuri. Sai da ya shafe sati uku cib ranar na shiga gidan Uncle Auta. Na samu wani labarin wai ashe an d'ago da maganar aurenshi da badr,"

akan idanuna suke fadar zata shigo ta kwace mijinta.

"Haka na fita na tafi gida, na kira Hindatu ina kuka, na gaya mata duk abinda yake faruwa. Nace mata. """

"Ni zan koma gidan Ya Ado ba ni da sa'a da aure!"" Fada tayi min sosai sannan Aunty Hindatu ta shiga bude min sirrin zama yar bariki a gidan miji, sai nayi ta jin kunyar kuma maganar Allah gaskiya ta gaya min, haka muka yi sallama da ita, da safe Uncle Auta ya kawo min cefane, na yi girki don daga ganin haka nasan yana hanya, haka na shiga nayi aiki wurin sha biyu ya shigo gidan, kallo daya nayi mishi, na wuce na rufe kofar gidan na dauke key na saka a kitchen, sannan na gama abin da nake na shiga ban daki nayi wanka, wurin karfe daya da rabi na fito na daure da towel. Shigowa yayi na kalle shi fuskarshi a haWe ga"

"alamu yayi ya ce min. ""Key nake bukata!"" ""Babu inda zaka sai ka gaya min me kake nufi da ni?"""

"""Bani da lokacin magana bani key?"" Ya nuna min hannu, gyara zaman towel din nayi na dauko baby oil"

"dina na cigaba da shafawa a hankali cikin wani salon jan hankali. Yaki kallona, ne saboda baya son ya dauko amma kamar an ce ya d'ago kai idanunsa suka yi farin gani......"

"[12/19/2025, 9:58 AM] Maman Walid: 22"

"Da wani irin sauri ya dauke kai yana.. ""Kin ga saura minti uku a shiga sallah ba ni!"" Yana kallon yadda na"

"mike, ""Ya Ilahi."" Ya furta a hankali, ya rasa me yake mishi dad'i. Turare na dauka nayi ta shafawa har aka shiga sallah, sannan na wuce na daki doguwar riga da abin sallah na shimfida mana na ce. ""Zo ka jamu sallah, tunda na masallaci ya kwace maka!"" Yadda nayi maganar a sanyayye tare da wata Ja'iran murya yasa shi, shiga gaban sallah. Haka ya jamu, amma zuciyarshi kamar ta fito don azabar karfin turaren nan"

dakyar yayi addu'a ya fita a dakin murmushi nayi ina bin shi da idanun. Oh dai.

"Bayan na idar da addu'a, na nufi kofar dakinsa na buga, shiru yayi ya ki amsa min. Na kara buga kofar"

"ina kiranshi. ""Malammmmmmm!"" Haka nayi ta bugawa har ya gaji ya buWe, murmushi nayi mishi. ""Food"

"is ready!"" Kallona yayi yana mamakin. ""Ba zan ci ba!"" Riko hannunshi nayi nace mishi. ""Wallahi nan ne"

"kan nace na zai yiwu ba, oya muje!"" Na ja hannunsa, ina faWin. ""Oya muje ka ci abinci, ba zai yiwu a bani amanarka azo a ga wani abu ya same ka, na shiga uku ba."" Na ja mishi kujera ya zauna sannan na shiga zuba mishi abinci kome daidai cikinsa. Sannan na ajiye mishi na saka cokali. ""Ke yanzu baki ji kunyar kayan jikinki ba?"" Kallon kaina nayi dress ne irin na yan makaranta, skirt da riga, ko gwiwa basu kai ba nace mishi. ""Ina zan ji kunya tunda gidan mijina ne!"" Na fada ina murmushi, tabbas yayi kewar abincinta,"

amma kuma fushin da yake da ita har yau ba daina jin zafi ba.

"Sai da ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha kafin ya mike. ""Yawwa Goodluck;"" na ce mishi"

"sannan ya wuce abin dariya a fusace yayi tafiyarsa. Haka na gyara table din na kai kome kitchen, sannan na wuce dakina. Ina waya da Mama muka gaisa sosai har da Yadiko. Kafin muka yi sallama.. ina zaune wani idea ya fado min wata rigarshi na dauka na saka, yau ko da karfi sai mun shirya wallahi na gaji. Ni ko labarin Hafiz ban kara ji ba, ina zaune ina karanta wasikar jaki ya shigo ya shirya zai fita ya ce min."""

"Bani key zan je KUMO FAMILY MANSION!"""

"""Sai gobe yau lokacina Better go to your room, babu inda zaka na gaya maka."" Daga haka na cigaba da"

wasa da kafana.

Sake baki yayi yana kallon yadda take mishi tsirfa kala-kala. Abin ya bashi mamaki. Haka ya koma dakinsa

"can naji ana buga min kofar gida kofar na je na tsaya ya zuba min idanu ganin Hijab har kasa na ce. ""Waye?"" ""Uncle Auta ne "" aka bani amsa. ""Ai sannu me kake bukata?"" ""Wurin Turaki na zo!"" ""Ayya sai dai gobe amma yau turaki nawa ne ni Waya."" ""Ki yi hakuri ki bani aronsa."" ""Ina ka je kawai da ya tafi har tsawon sati uku ka tambaye ni ya gama amarci ko bai gama ba, amma haka na zuba mishi idanun don haka sai ya biya kwanakin da yayi baya tare da ni wuce wurin Maman Daddah kafin na kira ta na gaya mata kun fara niman sabin yan mata!"" ""Tow haka abin ya koma!"" Ya juya yana faWin haka juyawa nayi na kalle shi yana rike da hularshi. Cike da mamaki yake bina da kallo. ""Kayi lokacinka yanzu nawa ne!"" Na"

wuce dakina.

"Fitowa yayi da sauri daga ban daki, jin yadda aka shiga sallah, ya sa shi kara nufar kofa a zafaffe domin"

"yana tsoron kada ta kara sashi rasa sallah Asr kamar yadda ya rasa ta Dhur, sai dai kash kicibs suka yi da ita cikin hargitsetsan yanayi da yake kara karayar mishi da wasu kwarin gwiwa da yake da shi, kin kallonta yayi domin haka na iya Dragging dinsa into wani part da bai shiryawa ba, cikin makirin muryanta da rabonsa da ya ji muryan kusan sati uku kenan, ta ce mishi. ""Malammmmmmmmm!"" Jin wani abu yayi ya tsaya a tsakiyar kansa ban da ita da tasan tasirin da muryanta yake da shi, da ba zata tab'a kiranshi da wannan yanayin ba, hade rai yayi ya cigaba da tafiya don baya son ya kara kallonta ba tare da ya nufi masallaci ba, ada idan aka ce mishi mata dangin shaidan ne baya tab'a amincewa, dawowarta gida yau a karo na biyu ya amince ita din tafi kowa sanin hanyar da zata kashe shi, kafin ya gama tunani"

"ta kara cewa. ""Malammmmmmmm yunwa nake ji!"" Raka'a na biyu da aka kai ya saka shi dafe goshinsa"

"tare da watsa mata harara, ai kuwa ta shiga buga kafarta. ""Shi kenan kamar yadda ta min dazun ta kara"

"yanzu dole nayi sallah a gida "" ya rasa yadda zai yi da ita tare suka ci abinci amma yanzu tana kara mishi wani abu wai yunwa take ji. Zuba mata idanun yayi ya juya zai tafi, na bi bayansa har dakin ya shimfida abin sallah, nima na fito naje nayi alwala na dawo dakin na samu ya fara bin bayanshi nayi muka yi sallah tare. ""Yunwa nake ji!"" Na fada a hankali ina matsawa kusa da shi. ""Malammmmmmm!"" Juyowa yayi ya"

"rufe min bakina. ""Naji!"""

"Tashi nayi a hankali zan fita daga cikin dakin ya ce min. Na yarda so halitta ce, ya ratsa zuciyata,"

"amma ba zan jure abinda ya faru ba , ki min bayani Lulu... ina sauraronki ya aka yi Hafiz ya zo gidan nan?"""

"Murmushi nayi tare da zuwa na zauna a gabanshi, hannuna na kai gaban rigarshi na shiga balle bottom"

"din. Bai hana ni ba sai ma kallona yake. ""You like it?"" Gyada kai nayi a hankali ya cire rigar tarin kwanji da tsokoki suka bayana. Daga nan labarin ya sauya, wasu abubuwan dai sirrin Turaki ne da ni, domin na fahimci wata rayuwar daban take da lissafin mai karatu, shi bako ne a bangaren, yayinda ni yar gari na kasancewa wacce take rayuwa a wani bangare na garin, kamar yadda ake cewa mata suna suka tara haka ma mazan suna suka tara, a daren nan namiji gwarzon mijina, y goge min hadda bakiWaya ya bude kaina ya zuba min nashi iya nashi shi dayansa. Ya daura ni a lissafinsa wanda iya ni kaWai ya daurawa, akwai rana mai matu™ar daraja irin wannan ranar? Akwai wata rayuwa mai dadi irin wannan rayuwar?"

Mutumin nan ya wanke min duk wani abinda nake ji ko nake gani. Mutumin nan ya dasa min so da

kaunarshi tare da bu™atarshi a kodayaushe.

"Sai bayan kome ya lafa ya kara rungume, yana shafa bayana kamar za a kwace mishi ni! ""Thank you"

"Lunah!"" Kwantar da kaina nayi a kirjinsa, ina jin wani irin yanayi yana ratsa tsakaninmu. Mun fi awa a makale da juna, kafin ya tashi ya haWa mana ruwan wanka, kin shiga mu yi nayi amma haka ya tilasta min na shiga muka yi wankar muka fito. Kunyarshi kuma sai ya cika ni, riga da wandonsa ya dauko min na saka, ya gyara gadon ina kallonshi. Bayan ya gama ya janyo ni jikinshi muka kara kwanciya, kanshi ya daura a kirjina, na rungume shi. Furfura kanshi na kai hannuna ina tsige su ya ce min.. ""Kin ga furfura ko? lokacin da na ganki ina talatin da wani abu, yau gani ina bawa arba'in baya, tunda kika amince kika aure ni, zan gaya miki, ina da lafiyar da zan jiyar dake farin ciki a ranan da muka kasance! kawai ki kaunace ni ki bar jin kunyana domin ni bani da kunyar!"" Tabbas bai da kunya, amma sai na tsinci kaina da kasa"

magana na cigaba da wasa da gashin kanshi. Ina murmushi da jin wani farin ciki a raina ya ce min.

"""Ki ce min wani abu? ina jiran kalmanki ko da ta a'a ce."" Murmushi nayi ya d'ago kai yana kallona, wani"

"irin tartsatsin kauna nake hangowa a cikin idanunsa. He like me, sama da yadda nake tsammani."

"Chakulkuli ya fara min nayi ta kaucewa, daga karshe yayi nasarar daukata ya daura ni akan kafarshi yana"

"faWin. ""Shi yaren soyayya ba ruwansa da yare ko kabila, ba ruwanshi da jinsi mace ko namiji, shi wata halitta ce da take wanzuwa cikin zukatan masoya imma mutane imma wasu halittun na daban, ya kike"

"fahimci haka? Ni na fahimci haka ne lokacin da na hadu da ke."""

"Akwai wani irin dad'i da nutswa idan ka ji namiji yana fitar da abinda yake ransa. ""Ina sonka Malam,"

"sai dai ina tsoron kada ka juya min baya, ina tsoron kada ina murnan na rabu da Hafiz!"" Rufe min baki yayi yana girgixa min kai. ""Allah ya min tsari na zama kamar Hafiz Allah ya rufa min asiri na zama irin Hafiz, Ubangiji ya hanani ranar da zan zama kamar Hafiz. Kai Allah ya nuna min mutuwata sama da ranar da zan ga na zalunci matar da nake aure ba."" Kifa kaina nayi a goshinsa na ce mishi. ""Na gode!"". "" Me yasa kike godiya! "" "" Ai kai mutumin kirki ne kuma me cika alkawari ne, shi yasa nake maka godiya domin"

"zaka cika alkawarin da ka Wauka. """

"Haka kawai na zauna ayi min sakiyar da ba ruwa, mijina yana sona nima ina son mijina, akan me zan"

"bar wani ya shiga tsakaninmu, a ranar duk a gida yayi salollin, wurin karfe tara aka buga gidan ya kalle ni, murmushi nayi na nufi kitchen na dauko key na mika mishi. Ya je ya bude Kofar. "" Ka fito daga prison kenan?"". Murmushi yayi sannan ya amshi ledar kafin ya kara magana ya banko kofar, Uncle Auta ya ce mishi."" Ni ka wulakanta?"". "" Sorry Uncle!"" Wato mu fa sai yau muke cin kazar amarci, muka ci muka yi"

"nak, sannan muka baje a parlourn muna hira da kallon wani film."

"Daren ranar dai dayawa zasu so jin labarin amma kuma, ai lamarin Babba ne fa. Domin ni kaina sai da"

"naji kamar na gudu mutumin nan wayo ne da shi, amma kuma duk abinda zai yi tausayi yake ba ni domin ya jima bai yi auren ba, ni kuma sai na mishi uziri, sai da muka kwashe sati daya cib sannan ya fara zuwa office shima din dakyar na lallaba shi, har da cewa Uncle Auta da Ubaid zasu mishi dariya ya ce musu sai ya rama min kwanakin da baya nan, riko shi nayi nace mishi. "" Wato bazani kayi kana gaya musu sai yanzu muke amarci! "" "" Ai ke kika gaya musu! "" Zare idanun nayi na ce mishi."" When?"" "" Kin manta kenan. "" Yana tuna mun ranar na ji kunya ta kama ni da gudu zan fita ya riko hannuna. "" Ban da gudu don Allah!"" Kaina na daura a kirjinsa ina murmushi. ""Kin yi kyau kullum kara kyau kike min!"" Ya fada min wata katuwa magana a kunnena, kunya ta sa na kifa kaina ina faWin. ""Yaushe zaka fara jin kunya?"" ""Hala ranar da tsufa ya cimma ni!"" Girgiza kai nayi na raka shi har wajen sannan ya shiga mota ta bar gidan nima na dawo parlourn, tunda na dawo na shiga aikina, karfe uku saura na wuce lokacin na kusan gama hada sobo, da yake yace zai zo da baki tuwan shinkafa miyar Egusi nayi, ina ta aiki na ji an buga gidan na zata shi ne ina zuwa na bude Matar Uncle Auta da Ubaid sai wasu mata biyu da yan mata uku. Murmushi nayi na ce musu.."" Barkanku da zuwa ku shigo!"" Na wuce kitchen na kawo musu ruwa. Na juya zan tafi na ji daya tana faWin. ""Dazun na ga posting din wata arewa dairy wai Yan Bauchi suna da rowa, basu iya baka kyauta daga ruwa sai ruwa."" Murmushi nayi na wuce kitchen, na hado musu snacks da nayi na karban baki na fito musu da shi, sai lokacin juna suke. Na koma na hada abinci a kula guda, sannan na kawo musu na ce musu. ""Don Allah ku yi serve kanku, bari na sauya kaya."" Na koma dakina na watsa ruwa na sauya kayan jikina, ina kasa kunnena ko zanji dirin motarshi, amma ina sai ji nayi yana gaisawa da matan, kafin ya shigo dakin.. ""ina ta son na maka oyoyo!"" Zungure min goshi yayi yana faWin. ""Kin san dai da baki zan zo!"" Na dauko wata hijab dina har kasa na daura akan riga da zanin da yake jikina. ""Kina kyau da riga da zani."" Haka ya riko hannuna ya ce min. ""Waye dai taya ni shiryawa?"" ""Muje na gaishe su sai na raka ka, ka sauya kayan ko?"" Haka muka yi na fito na gaishe su, sannan na cewa Matar Uncle Auta"

"da Ubaid. ""Kuci abinci!"" Na raka shi dakinsa, ya watsa ruwa ina tsaye na fito mishi da wasu kananun kaya,"

"ya saka sannan ya saka turare na riko hannunshi,. Muka fito a lokacin da su Uncle Auta da Ubaid suka"

"shigo gidan, ashe matan biyun nan mazajensu ne da Yaransu, haka mazan suka koma dinner table, su kuma matan suka zauna a parlourn na koma kitchen na yi ta fito da kayan abinci, shi kuma yana karba idan na kawo sai ya sumbaci hannuna, ko ya ce min. ""Sannu da ™o™ari!"" Ina kawowa zai sumbaci goshina. ""Allah ya miki sakayya da gidan Aljanna!"" ""Amarya ko Falisha zata taya ki ne?"" Inji daya matar. ""A'a mu yan Bauchi, mun iya aiki da kanmu ko Malam?"" Gyada min kai yayi bayan mun gama na wuce kitchen, sai gashi ya biyo ni da abincinsa. Ajiye min abincin yayi. Ya saba muci tare don haka na wanke hannu ya zauna a kan wani kujeran kitchen din nima haka, muka shiga ci tare. ""Wani abu ya faru ne?"" Ya tambaye ni bayan na tura mishi loma. ""A'a babu abinda ya faru!"" ""Akwai mana baby gaya min."" Murmushi nayi"

"nace mishi. ""Zance ne irin namu na mata."" Gyada min kai yayi yana kallon yadda nayi ta tura mishi abinci, sai da muka gama ya wanke hannu ya taya ni wanke kwanon, muka fito ina cewa. ""Dauko tissue please!"

""" Wurin cin abincin ya nufa Uncle Auta ya ce masa. "" Sai ka gaya mana matarka ce ta baka abinci a baki!"""

"""Kai dai da baka iya romantic ba, a barwa newly couples kayansu!"" Ya tawo lokacin har na shigo parlourn,"

"yana zuwa ya mika min. Na amsa tare da goge mishi ina faWin.. ""Malam gashin baki da kasumbar nan suna bukatar gyara fa."" Na faWa kasa kasa. ""Tow idan suka tafi ba sai ki gaya min ba, ai tun jiya nake bin ki, amma kika share ni."""

"""Ok bari mu sallami baki!"" Na fada ya koma wurin mazan. ""Duk wannan soyayyar kafin a haihu ne"

"idan aka haihu shi kenan sai ya zama tarihi."" Murmushi matar Uncle Auta tayi ta ce mata . ""Da don haihuwa ne, da tuni ya tara goma na yara. Kauna ce dai da bata tsufa ba, sannan bana jin idan zasu cika gidan nan da Yara zai fasa wannan halin shi ba bafulatani ziryan bane kuma ba bahaushe ba ne da mace"

na fara haihuwa zai zuba mata yaran ta ji dasu shi ruwa biyu ne.......

"[12/19/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 23"

"""Mu kanmu mun yarda ™abilar uwarsa tayi tasiri akanshi. Yadda ya iya jiranta ta dawo gare shi."" Sai duk"

"suka yi shiru, kasancewarta Babba a tsakaninmu sannan muna bata girmanta daidai gwargwado."

"Tun da fadi haka bata kara magana ba, sai ta yi shiru,sai dai na fahimci wani abu a nan shine matar"

"Ubaid kamar ban mata ba, da farko na zata matar Uncle Auta ne take min kallon gani gani amma daga bayan zuwan waWanan matan sai ja lura da yadda Matar Ubaid take bina da idanu. Bayan tafiyarsu na gyara parlourn na tattara wanke-wanke, ya rungume ni ta baya yana me taya ni wanke -wanke. ""Maza biyu da suka zo nan Alhaji Ahmed da Alhaji Mohammed, abokan kasuwancin Papa ne, Alhaji Mohammed yana Cotonou da iyalinsa, shi kuma Alhaji Ahmed yana abuja, tagwaye ne su."" Gyada kai nayi na juya ina fuskarshi. ""Su ma wadancan tsalla tsalla yan mata da suka zo da su dama an shirya proposal ne ban sani ba?"" ""Ni waye ya gaya miki an shirya haka?"" ""Amma ai a bakinsu naji ana cewa yana Bauchi na da rowa!"" ""Wallahi ni ban fadi haka ba sai dai ko su."" Dan dagalgala nayi tare da sumbatar goshinsa ya saka hannu ya dauke ni cak, na sumbaci goshin sannan ya sauke ni na ce mishi. ""Ina ga sai na fara saka maka"

"abu domin na lura family dinka basu da buri da ya wuce su ga an yi min karin wata mace!""na juya na na"

"zabga mishi mintsini. "" Na gaya maka wannan shine kashedina da kai wata mace sai na fille maka kai!"" """

"Tow ranki shi dade!"" Haka ya fada yana dariya, a tare muka gama wanke kayan muka gyara kitchen din tas sannan ya riko hannuna zuwa parlourn nan ma muka gyara wannan na fito na samu yana jirana."

"Bude min hannu nayi na shiga da sauri ina sauke ajiyar zuciya. ""Ina sonka dayawa!"" "" Ok bani labarin"

"ranar kika fara sona!"" Biye mishi nayi muka yi ta hira shi kuma ya zuba min idanun ina bashi labari ina dariya ko ina farin ciki."

"Haka muka gina kanmu, kuma muka gina rayuwarmu. Zan iya cewa tunda na fahimci tarin alkhairin da"

"yake tattare da mijina, tafiya ta kama shi ina hada mishi kaya ya zauna yana goge kanshi ya ce min. "" Ko zaki raka ni ne?"" "" Ka manta ina son zuwa gidan Ya Ado ne?"" Shiru yayi kafin ya ce min. "" Zaki iya min alfarman na dawo sai mu tafi tare?"" Kallonshi nayi sai nace mishi. "" Allah ya dawo da kai lafiya."" Na fada ina murmushi, bana son ta ha kamar raina bai so ba, haka na shirya mishi kayansa, har na taimaka mishi ya sa kaya amma ina son zuwa na ga yan uwana, amma yadda ya nuna baya ra'ayi na share ban kuma magana ba. Bayan na gama shirya shi ya ce min. ""Me zan saya miki?"" ""Kome ma ina so!"" Daga haka muka fito ya shiga motar, bayan tafiyarshi ne nayi baki duk da ya hana su zuwa amma Amma saboda masifa sai sun zo. Na musu iso suka shigo parlourn. Na kawo musu abinda ya dace sannan muka kara gaisawa na ga sai dariya suke yan matan idan suka kalle ni, sanin zasu iya saka ni a damuwa yasa na"

barsu na wuce dakina. Kiran Aunty Zakiyah ta shigo ta ce min zasu zo in sha Allah gobe ita da Yaranta.

Nayi murna sosai nace su zo da niyyar kwana yaran tunda basu gari. Ina gamawa na fito parlourn. Matar

"Uncle Auta ce ta shigo tana faWin.""ku wasu irin jakuna ne? Ku wasu irin jahilai ne? Kun dauka tafiyar da"

"yayi Da badr wani abin arziki ne, shegu yan marasa kunya da mutunci."" Tayi musu tas, ""wai don Mijinki yayi tafiya Da badr shine zasu mai da shi babban al'amari."""

"""Sune da wahala na yarda da Mijina sannan ni ba mahaukaciya ba ce bana saka karfi akan kome idan ya"

"ce zai kara aure yayi wallahi bani da case da shi sai dai duk wacce zata aure shi ni ce na bude shi a leda babu Macen da zata gaya min waye shi."" Tunda na fadi haka na ga sun yi wani firgita. Murmushi nayi na ce musu. ""Ni saka kishi ne, ba ji kishi ba ce. Turaki da yana da buri da ra'ayin tara mata hala da nazo a ta hudu, idan kun iya ku kama kanku idan baku iya ba, ku cigaba ni bani da energy da zan yi fada akan namiji domin mijina mijin mace daya ce, idan kuka ga kaddaran wata mace ta ratsa to in sha Allah rabo ce ta kira ta, daga yau kada na ™ara ganin kafar kowacce yar iska s gidana idan ba haka ba, between ni da lu xa a damu matsala."" "" Ai ki kyale su sai na gayawa Turakin!"" "" Akan me zaki gaya mishi, sun yi na farko yayi musu fada na biyu ya dake su da yake jakuna ne, na uku na shiga cikin lamarin, kun zo ku hada mu fada tow ta Allah ba taku ba, wallahi kun yi karya ku shirya da kyau domin Allah ya bada sai dai ku yi Hakuri sai na kona fuskar yarinya idan ta kara shigo min gida idan kuna ganin wasa ne Allah ya dawo da"

"ku gidana zaku gane baku da hankali!"" Yadda na musu tass suka fita kamar munafukai."

"Wannan yasa na samu sauki amma na dan shiga rud'ani da naji labarin yana tare da Badriyyah, har"

"dare bai kira ni ba haka na kwanta zuciyata babu dad'i, gaskiya kishi masifa ce haka nayi ta juyi har sha biyu na dare, karshe na tashi nayi sallah nafilla ina addu'a na fara jin barci haka yasa na tattara na koma"

"gado. Kafin barci yayi gaba da ni, karfe shida na safe kiransa ne ya tashe ni don kiran sallah asuba ban ji"

"ba, haka na tashi ina mai amsa mishi bayan mun gaisa nace mishi."" Ya hanya?"" Ya amsa min da "" lafiya lau!"" "" Nayi ta jiran kiranka jiya amma baka kira ba!"" Na fada a shagwab'e. "" Kin san Allah kada ki d'aga min hankali, kin san yadda na bar garin nan!"" Tab'e baki nayi na ce mishi.""Sallah zan yi!"" Na katse kiran, haka kawai sai shaidan yana min wata huxubar tsiya, haka nayi sallah na yi azkar ya kara kirana. Dauka nayi ya ce min. ""Please muyi video call;"" kashe kiran nayi na bude datana. Na shiga imo shi ya sauke min apps din Wai yafi sau™in kiran idan baka kasar. Can kuwa sai ga kiranshi. Dauka nayi ina kallonshi. Haka kawai nake jin haushinsa. ""Yan mata nayi miki laifi ne?"" Murmushi nayi na ce mishi. ""Ba kome."" Sai yayi ta kallona. ""Da gaske ban miki kome ba?"" Girgiza kai nayi, buga kofar dakin aka yi, na ji yana cewa. ""Waye?"" Abinda na ji kenan. ""Hamma nice badr ban dakina ruwan ya tsaya ne!"" Kallona yayi na dauke kai. ""Tafiyar har da ita zata ga likita ne."" ""Ban tambaye ka ba!"" Na gaya mishi. ""Ki tsaya!"" ""Ni kitchen zan shiga ina da baki!"" Na fada ina mai mikewa zan kashe wayar ya ce min. ""Ki tsaya."" ""Me kake bukata? Ina ga ai na sallame ka sannan ita wacce take magana ai lokacinka take bukata."" Na

Please Login or Register in order to submit comment