You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, haka yasa nayi shiru ina sauraren Mama. Har ta gama min bayani sannan muka yi sallama, bayan isha da ya dawo ina kwance a dakina ya leko zai fita da gaggawar. ""Zaka tafi wurin Adaa?"" Cak ya tsaya yana kallona. ""Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya."" Shigowa Yayi min a zauna zai dauki yar nayi maza na kwace Y'ata. ""Me yasa kike min haka? Ni ma fa y'ata ce, sai ki hana ni daukarta idan na zauna bakya kula ni gaya min me nayi miki da zafi?"" Hawaye ne ya zubo min na ce mishi. ""Ka damu ne da mu? Ai dmuwarka yana kan Adaa."" ""Ki tsaya mu yi maganar gaskiya."" ""Wani irin maganar gaskiya bayan na samu jan bakinta a cikin kayanka, na biyu na ga sakonta yadda ka mata a daren da kuke tare na ga layin jan bakinta a jikin rigarka, sannan ta zo gidan nan ita da Matar Kaduna tsohuwar Step mother dinka me ya rage da ban gaya maka ba? Akwai ko babu? Duk abinda na gani shima ba hujja ba ne? Zaka iya amfani da ita amma ka sani ni da kai Y'a mace muka haifa ka rufa min asiri kada a lalata min y'a wallahi ban tab'a zina. "" Ya dauke ni da mari wanda ya janyo nayi shiru tare"

"da rike fuskana. ""Marina ka yi?"" Na tambaye shi, ina kallonshi hawaye na zuba min daga idanuna. ""Na"

"cancanci kyautar mari daga gare ka?"""

"Kura min idanun yayi idanunsa sun yi jajjur, tashi yayi ya bar gidan bakiWaya na sha kuka, kamar ya"

"bana son na kira Ya Ado domin zan d'aga mishi hankali a daren na sayi ticket na Jos, kamar ya san abinda nake shiryawa, da safe sai gashi tare da Kakanshi, suka shigo na gaishe su. Na koma dakin na dauko musu yar da na gama shiryata na mikawa Kakar ita, sannan na koma dakin na cigaba da hada kayana na fito da su waje, na ajiye. "" Y'ata ina zagi da wannan kayan?"" ""Baffa gidanmu zan tafi"" shiru yayi kafin ya"

"ce min. ""Gaya min me suka miki shi da su?"" Ai kuwa na fara kuka, na rasa yadda zan mishi bayanin"

"wulakancin da yake, ganin har lokacin kukan ya ki karewa Ya ce mishi. ""Allah sai ya bi mata hakkinta,"

"domin ka zalunce ta sosai."" Yadda yake mishi fada ba nan yake fita ba, har da cewa. ""Ban da ita wacece zata zauna da kai tsakaninta da Allah ba tare da ta tuna cewa kai wani ne, tayi maka alfarmar zama da kai har da haifa maka zinariya me yasa zaka wulakantata?"" ""Datti rashin kunya take min wallahi ban mare ta don bana sonta ba, ranar ta kira ni manemin mata jiya kuma tana ™o™arin kirana da maxinaci kawai don ta samu wani abu da tabbatar mata muna tare Adaa!"" ""Ban rabaka da yarinyar nan ba?"" ""Amma Datti!"" ""And so what? Abubuwan da kake yi yasa take zarginka, ai nima ba yau na ce ka rabu da ita ba nayi karya? Bari ka ji idan ka sake ta bar nan ta je har gidan dan uwanta ko iyayenta wallahi ba zan je biko ba. Kuma ba zan tab'a shiga lamarinka ba, ba ruwana da kai, wallahi xan gayawa Kakarka. "" ""Datti don Allah kayi hakuri!"" "" Ita zaka bawa hakuri domin ita ka cutar matarka ta rufin asiri babu wanda ta kaiwa kukan kayi mata laifi bs kasan ana jiran a ga ta kuma kuka akanka ba ne a ce damar ba sonta kake ba."" Sai naji bawan Allah nan ya biya ni, cikin shashekar kuka na kara kai min kukan na ce mishi."" Baffa Mommy Zeenatu ta ce matu™ar tana raye sai ta aura mishi Adaa ni ba auren ne bana so ba, a zo a raba da Y'ata, ni na yafe mishi duk abinda yayi min Daada mutumin kirki ne, kawai ya je yaji auren shi ni ban damu ba kuma ban yi bakin ciki ba, abubuwan da yake yi kada wata rana a cutar min da ita tunda har gidanta yana zuwa da sunan soyayya duk anan suka gaya min. Kayi hakuri Alhaji amma lokaci yayi da dole na hakura da zama da shi."" "" Ita Zeenatu ta ce miki zai auri yarinyar ko? "" ""Eh tace akwai baiko da Mahaifiyarshi ta tabbatar za a yi aurenshi. Allah ya basu zaman lafiya gara na tafi wurin Iyayena sun fi kaunata ba xan zauna bakin ciki ya kashe ni ba tunda ta gaya min cewa budurwanshi ce tun fil azal tun Haihuwar Nana take gaya min bani da mazauni a cikin KUMO FAMILY, tunda na.fara da y'a mace, ni ina son abuna ganin haka yasa take tunanin gara ta haura mishi adaa saboda na haifi y'ace Mace Allah sarki ina son abina koda shi baya so kuma naga lamarin maganarta gaskiya ce domin ya sake min kula da yarinyar duk ya koma nawa wanda a baya tare muke kome Innalillahi wainnalihir rajoun ina jin zuciyata kamar zata buga."" Kafin wani lokaci na tashi karamar bom ai daga shi har kakanshi hankalinsu ya tashi haka ya, kai kakan gida ya dawo yayi ta rarrashina da gaya min cewa babu wata mace after ni, daga"

"karshe dai wannan abinda ya janyo rikicin aka janye ya min al™awarin ya fita sabgar yarinyar,"

A can Family house Winsu kuwa Alhaji ELYakub Kumo ya tara su yana tambayar su meye matsalarsu da

"Auren Turaki, domin ya fahimci ba turaki ne basu so ba, shine kawai suke yiwa kafar angulu. A gaya musu rayuwarsa suke bukata ko me? Ya kara cewa. "" Nayi ™o™arin na muku adalci, amma Zeenatu kin saka kafa kin shure kun zata tsoronki nake ji da na kyale ki? Ba tsoronki nake ji ba, Yara mata biyu kika"

"haifa mana bai saka mun miki gori ba ina ruwanki da rayuwar Matar Turaki da ita yanzu ta fara haihuwar? Ki jira idan ta kara yin mata macen sai ki ce ta gaje ki, da mace da namiji duk muna so, Mudansir ka gayawa matarka idan haihuwar maza banza ne me yasa ke baki yi ba? Ke ni da Dadda mun mijinki ya"

kara aure? Ina ga kin zo lokacin da dole ki fahimci kowani mutum da wanda Allah ya ke sakawa ya

"tsayawa Mudansir ka tafi Kumo akwai jikar Kawunka Alhaji Umaru ka aurota na musu magana yarinya ce shekarunta ashirin da daya, tana jami'a idan ta shigo Allah ya bata Yara maza sai mu ga yadda zaki yi."""

""" In sha Allah Baffa an gama zan je na dubata?"" Wani irin dukar kirjinta tayi tana faWin."" Sai kayi Auren"

"Baban Mimih?"" "" Ai ba yau na gaya miki, ki fita harkan iyalin Turaki, ban san me yasa kike son tashin hankali da rashin son zaman lafiya, tunda ni s matsayina na Mijinki baki ji maganata ba. Ina ga idan mahaifina saka ni ai dole nayi tunda bani da kamarshi, kuma ban isa ya gaya min na ki ji ba, don haka ki"

"je ki yi yadda kike so, Baffa in sha Allah zan je ka ganta."""

"Shima dama kamar ta ishe shi, hanyar hukuntata yake nuna, ai kuwa yan uwansa suka goya mishi"

"baya, hauka tuburan tayi tana faWin. Wallahi babu wnada ya isa ya mata kishiya. Ba wanda ya bi ta kanta kuwa."

***

"Alhamdulillahi da muka shimfida zaman lafiya s gidanmu, bakiWaya ya tattara kome ya ajiye a gefe. Ya"

"saka ni da yarshi a gaba yana bani wani irin kulawa, da ga na gaya mishi period Wina ya dawo ya ce shi ba ruwansa idan na kara samun ciki yana so ko Yara dubu ne. Jin haka yasa na fara kaucewa tsarin domin kuwa ina lissafin kwanaki da Ovulation dina, a lokacin kwanakin ina kiyayyewa. Kuma Alhamdulillahi sai"

gamu har kusan wata shida lafiya lau.

"Sai a lokacin ya shirya mana zuwa gida, gashi yarinyar tabarkallah, ta Gombe muka isa, murna kamar"

"Sarah da mamarsu dauke mu,. Kwananmu biyar anan naji labarin Auren Jasminah da Kawunsu. Nayi murna ai kuwa ka kirata ina ta tsokanarta. Tayi dariya anan Kano suka hadu da mijin. Yana da mata biyu ita ce ta uku, wani ikon Allah bai taSa haihuwa ba sai tarin albarka da Allah yayiwa rayuwarsa sannan"

yana rike da Yaran riko a gidansa kamar nashi.

Kawunsu kuwa ina komawa Bauchi na samu labarin a bakin Daada ya gaya min ai sai na kwantar da

"hankalina, gidanmu can dutsen tanshi muka sauka. Yarinyar da muna isa aka dauke ta, basu dawo da ita ba sai La'asar likis, na sha kulawa wurin Mama da Yadiko, da nake bata labarin abinda ya faru mamaki take tayi tana jinjina al'amarin. Kafin muka samu natsuwa da Isha muka wuce gidanmu da aka gyara shi, anan muka kwana washi gari Ya Sani ya kawo mana abin karyawan daga gidansa, nan yake gaya min"

kamfanin Turaki na nan Bauchi shine yake kula da shi......

"[1/12, 1:52 PM] Maman Walid: Ba zan iya cewa dukkanin halayen turaki nawa akwai na banza ba, amma"

"zan iya bada labarin shi din mutumin kirki ne mai adalci, shi din Gwarzo ne jajjirtaccen jarumi ne, da yake tsaye akan gidansa. Bai yarda ni d yarshi mun yi kukan wani abu ba, alakulli halin yana tsaye har kan yan uwana. Danginsa ma suna matu™ar son ya zauna a tare su, satin mu biyu s Bauchi muka wuce Abuja inda Taj yake muka yi sati daya, sannan muka wuce wurin Dangin Mahaifiyarshi. A can muka fara azumi sannan muka dawo gida. Gida lokacin watan yarinyar tara, aka yi sallah anan Lagos muka yi, sannan aka"

"yi bikin Alhaji Mudansir Kumo da yar danginsu mai suna Barakatu, yarinyar Fulani kyakyawar gaske."

Haka muka kasance s hidimar duk inda aka ganmu haka ake rige-rigen daukar Yarinayr da take

"kafad'arshi, wani ikon Allah dafa Hajiya Zeenatu da yarta Kowa jikinsa yayi sanyi, bayan bikin turaki ya"

"biya min aikin hajji na tafi, lafiya lau na fara aikin hajji, sai dai kuma wani abun mamaki ranar arfa na fara"

"wani irin zazzaSi me zafi. Haka dai nayi aikin hajjin. A daddafe, har muka dawo gida, tunda a airport asibiti ya wuce da ni, sai da aka kara min ruwa da allurai na samu kaina. Ina bude idanuna muka yi ido huWu da Yar Daada, sai dariya take min ya ce min. ""Congratulations love kin sake daukar wasu yaran Turaki gaskiya ni jarumi ne, Mammy bata cika shekara ba, gashi nan kin kara daukar Yarana a womb dinki."" Kura mishi idanun nayi ban san lokacin da na fashe da kuka ba, ""yanzu kai wannan abin burgewa ne?"" ""Eh kai wallahi abin burgewa ne fa."" Duk yadda naso na gaya mishi yadda za a Wauki lamarin nuna min yayi shi bai ga wani abin muni ba, haka na kyale shi ba don na so ba, amma wannan karon na san nayi ciki don sau hudu ana min karin ruwa, sai da cikin ya cika wata biyar a lokacin Nana tana da shekara daya da kusan rabi, sannan na samu kaina. A lokacin aka yi bikin Almustaph babban dan Aunty Innah, haka na tafi gida da ciki a lokacin duk wanda ya hanni da cikin sai ya san ina da ciki domin yayi wani girma. Sannan duk tsawon lokacin nan anyi scanning har sau biyu daya ne kuma yaki nuna Gender. Haka nayi ta fama da shi, ai kuwa su Mama da Yadiko suka ta min fada akan me zan zo kada ka kara zuwa ko ina sai na haihu. Kusan anyi bikin ina kwance. Sai da na shafe sati kafin na wuce Jos, kwana Waya nayi a"

"gidan Aunty Raliya, muka wuce lagos."

"Tunda na dawo Alhamdulillahi, kulawar da nake samu a wurinshi ya wuce yadda nake tunani, haka"

"muka yi ta lallabawa har na shiga wata tara, anan aka ce ba zan iya haihuwa da kaina ba. Dole ya saka hannu aka za ayi min CS'. Ya kira Mama ya gaya mata, aiki za ayi min ko zata zo ne, kwanaki uku a tsakanin sai gata tazo, kafin aka min aikin. Wani ikon Allah yara uku maza biyu mace daya ita ce kusa karama a cikinsu, haka aka fito dasu Mama tayi ta mamaki. Kafin na farka danginsa sun cika asibitin, sai murna da godiyar Allah da suke ta yi. Lokacin da na farka da surutu sai kuma kirga da nake yi, kafin wani"

lokaci ™arfin maganin ya sake ni.

"Alhamdulillahi a cikin kwanaki biyar na samu kaina, a kwanaki na bakwai aka sallame ni, yan uwa da"

"dangi da abokan arziki sai fatan alkhairi ake mana, duk wanda ya ga Yaran sai a ce Turaki ya fini ™arfi, domin yaran sak da sak suka yi da shi, sati na biyu aka yi suna shima walima kawai aka yi Mazan Haris sunan Abbanshi. Hassan ya ci. Husaini ya ci sunan Kakanshi Hassan Ajmal. Husaini Amjad, gambon kuwa aka saka mata sunan Mama,kiranta da Anum, Mama ta zauna da ni har muka cika kwanaki arba'in, a wannan lokacin kan sai da aka dauko min me reno. Mama bata kyale ni ba sai ta min biki ciki da wajena,"

"sannan ta bar gidan. Inda muka buWe shafin kauna ni da shi, kamar zamu cinye kanmu."

Wannan karon yarana suna samun kulawa dukkanmu uku haka matar Alhaji Mudansir ta haifi

"danta namiji, aka saka mishi sunan Alhaji ELYakub, suna kiranshi da Dady. Wannan abin da ya faru yasa kowa ya shiga hankalinsa. Hajiya Zeenatu bata da wani katabus, yarta Mimi da kyar aka yi aurenta koda"

yake wani gaye ta kawo wai tana so garin bincike aka samu dan safarar miyagun kwayoyi ne. Haka yasa

aka fasa auren sai wani shima ba laifi amma dai ya fi wancan kusan irinta ne.

"Rayuwa ta bani abubuwa dayawa, a lokacin da ban zata ba, a lokacin da naso abubuwan ban samu ba,"

yau dai gashi ni ce cikin Alkhairi da kwanciyar hankali.

***

Bayan shekaru biyar ..

Hafiz kuwa jinya ya sha kamar zai mutu don zai da ya kwanta a bayara can asibitin kutare da masu tarin

"fuka, anan ta sha jinya Jalilah da aka kashe auren guduwa tayi ta shiga bariki. Aka nime ta aka rasa, wannan abin yayiwa Goggo talatuwa ciwo, a cikin wannan yanayin Allah yayiwa Goggo Alti rasuwa, lokacin Yarana suna da shekaru uku, Nana taka da shekaru hudu da rabi, haka muka zo har Jama'are kowa ya ganni sai ya tambaya anya nice kuwa, murmushin gaske nake gani a fuskar dangina da yan uwana da suka tsaya min, mun hadu da Hafiz ganin yadda Ajmal yake tsalle a jikin Abba Amjad yana jikin Ya Umar da Nana a gefen Ya Ado, Anum a cinyar Ya Tahir abin sai ya sake shi jin kamar na shi ne Yaran, haka ya bar cikin mutane ya koma can bayan gidan yana kuka, domin idan da xai bada labari tow duk wnada ya gayawa Ya auri Lubnah ™aryata shi za ayi, yau gata da Yaranta da Mijinta, da yau ace sun haifi"

Wa da ita da yanzu ana alakanta shi da ita amma yanzu sai zai ace tsoho.

"Ko wancan watan yaji labarin yadda Karima tayi mummunar hatsari tana can asibitin Mahaukata, yaran"

da kuwa an kwashe su ba a san inda aka kai su ba.

"Kwanan mu goma sai ga Turaki a Bauchi, yazo yayi ta mita wa Mama da Yadiko. ""Fisabiilillahi yaushe"

"Lubnah zata girma ne? Sati daya na bata amma ta kara kwana uku, nasan yanzu kusan har magana sun yi da Hafiz yayi ta nunawa mutane ita as tsohuwar Matarshi."""

"""Kai ai baka da matsala sai na kishi, idan bai nunawa jama'a ita tsohuwar matarsa da yayi wasa ya rasa ta,"

"ai kai abun alfahari ne ace yau ga matar da ya rasa saboda sakarcinsa."" Inji Yadiko sai kuma ya shafa kai yana murmushi. ""Kuma fa haka ne fa!"" Haka ya gama musu iyayi, sannan ya bar gidan ya tawo gida. Na gama abincin dare, ina wanka ya shigo har ban dakin."

"Zan iya cewa zane ni yayi amma zanewar kauna, haka muka fito cike da kaunar juna. Sai da muka yi"

"sallah isha sannan muka fito parlourn muka ci abinci da yaran, sannan muka yi hira na shiga da Yaran cikin dakinsu na kwantar da mazan gado daya matan gado Waya. Sannan nayi musu addu'a."

"Kafin na dawo dakin ibada wato dakin mijina, yana ganina ya kashe aikin da yake ya tashi ya kashe"

wutar dakin sannan ya muka bude wutar kaunar da take rura zukatarmu.

Washi gari.

A group naje jin Hafiz an tura shi asibitin ™wa™walwa na jahar Kano wato saboda halin da yake ciki da

"ake tsammanin hauka ce, ni da kaina nace damuwa ce, domin domin ita kadaice zata zarar da shi, haka, dayawa cewa suke hakkina ne y kama shi, don haka ya kare da hauka."

Satinmu uku muka wuce da Yara Lagos. Don ma yaran nan gidan Ya Ado suke tafiya hutu ko can KUMO

"FAMILY. Hankalin zuriar KUMO ya kwanta. Ita kuwa Falilah matar Ubaid an ce wai asirin da tayi kokarin yi min ne ya koma kanta ko ma Yaya ne Allah ya kyauta. Matar Uncle Auta muna shiri da ita. Domin ko lokacin bikin yarta Dada haka muka tsaya a matsayin kawayenta ni da Amaryan Ubaid, ai kuwa sai muka"

hade kanmu yadda kansu yake haka.

"Yarinyar daga Lagos muka kaita abuja, aka sha biki wata shida a tsakanin aka yi bikin Taj. Shekara biyu"

"da auren Dada aka yi bikin Yar Ya ado a Bauchi a lokacin ina goyon mai sunan Ya Ado, wanda muke kiranshi Annur."

Ana gama bikin mijina ya sako ni gaba muka dawo Lagos. Wato idan Turaki yana bina a Sannu ji nake

"I'm melting domin ni kaWai nasan gajiyar da nake samu a tare da Mijina, ni daya nasan waye shi. Ina son mijina ina kaunar Mijina kuma nasan shima yana sona Sosai. Dirin motar shi naji na fito ya shigo, isa gabanshi nayi na amshi jakarshi. Ina murmushi nace mishi. ""Barka da dawowa ya hanya ya aiki?"" Jan kumatuna yayi yana faWin.. ""Alhamdulillahi na same ki lafiya ina Yaran suke?"" Murmushi nayi na yi nace mishi. ""Naa tana gidan Ya Ado, Amjad yana gidan Taj, Anum da Ajmal suna can wurin Dadda dani sai auta ne a gida, janyo ni yayi yana faWin. "" Ke dai ki ji tsoron Allah ki daina kiran Auta domin wallahi akwai shida na zuwa na gaya miki goman nan dai sai kin dire min su! "" Murguda mishi baki nayi nace mishi.."" tunda a ruwan sha ne ai sai ka dura min. "" Na shige dakin biyo ni yayi yana faWin. "" 'Aa ba a ruwa ake sha ba, amma bari na gaya miki yadda ake shan shi."" Ya fada yana rungume ni ta baya na fasa ihu karami"

cikin jan hankali.

"Alhamdulillahi anan zan tsaya da labarin Lubnah. Da yake cike da alakar Zuci soyayya da rikita rikita, Na"

"gode sosai da wa'danda suka biyo ni a labarin nan, Ubangiji ya kara hada mu a wani labarin mai sunan......... Fatan alkhairi son so Fisabiilillahi......"


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment