You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan gado yana ta kalle kallen inda zai mata maSoya a cikin Wakin da yake jakar irin wacce ake goyawar nan ce mai kamar ta ΄an makaranta bai ankara ba sai ya ji ana faWin an sanya bom a unguwa ya kusa tashi hakan ya"

"sanya ya ruWe wani tashin hankali ya ziyarce shi, matar ma hankalinta ne ya tashi dama bata"

"da Wa ko Waya tun da suka yi aure bata samu rabo ba wannan dalilin ne ma ya sanya yake mata wula™anci shi ne zai yi aure, tana shirin tashi tsaye domin guduwa ta tsira sai ji ta yi an kinkime ta an saSa ta a baya, mamaki al'ajabi ne ya baibaye ta dan ta san dai mijinta ko karen hauka ne ya cije shi ba zai taimaka mata va sai dai ta yi ta kanta amma kuma ga shi har da Waukanta ya saSa ta a baya hakan ya sanya ta fara godewa Allah a kan ko canji ne ya samu na lokaci guda yake son su tsira a tare don a nata zaton ta Wauka guduwa zai yi ita ma ta yi ta kanta amma sai ta ji ya warce ta ya saSa a baya ko nauyinta bai ji ba shi da ko a irin soyayyar nan ta ma'aurata bai taSa Waukanta ba amma yau ga shi dalili mai sa a le™a jikin sirika ya Waga ta cancaras ya goye a barsa. A Sangaren miji kuwa bai san cewa matarsa ce ya goya ba da yake a kusa a ita ya ajiye jakar kuWin a kan gado jin an ambaci tashin bom a lokaci ™an™ani a ruWe da kuWinsa da kuma gudun kar ya mutu wani ya auri amaryar da ya ci burin aure wacce ya tafi ™auyensu saboda ita ya siyar da kadararsa ta shanu dan su yi aure. Duk a tunaninsa jakar ce ya goya ba matarsa ba dan yadda matar ta ma™al™ale sai ya Waukan hannuwan jakar ne ya ma™ala, ita kuma matar ganin ya goye ta sai tausayi irin na mata ya sanya wani son sa da ™aunarsa ya ratsa ta ta mi™a hannu ta Waukar masa jakar ta a haka ya bazamo daga cikin gida ni™i-ni™e goye da matar da yake ma tana da jiki sosai hakan ya sanya yake gudun tin™is-tin™is ko takalmi babu ga shi daga shi sai singileti yana fitowa ya ga inda jama'a suke dirfafa sai gudu ake mata wasu Wauke da yara sai kuka Wiya suke ganin abin da basu taSa gani ba shi ma a haka ya bi ayari tamkar ΄an gudun hijira"

sai tada ™ura ake a layin sai ka ce masu gudu a sahara.

"Wani gida da yake kallon gidan da mijin nan ya fito goye da matarsa, ita kuma matar gidan tana wanke -wanke ta ji ana cewa bom zai tashi kowa ya yi ta kansa, tsabar rikicewa kwandon wanke-wanken ta Wauka ta kifa a kanta a tunaninta hijabinta ne a haka ta taho tana gudu kai a kife da ™aton kwandon zuba kwanukan wanke-wanke tana fitowa ta bi bayan mijin nan da yake goye da matarsa, ta cikin tular kwandon take kallon yadda yake zandama gudu ko ™a™™autawa babu shi ne abin da yake bata darita duk kuwa da halin da ake ciki na tashin hankali. Dan kowa a unguwar ya san mijin matar bashi da mutuncin ba ya ganin kan uwar kowa da gashi amma dai ita kanta ta san wuya ce in ji tsula ta sanya shi goyon matarsa kallon su take tana gudu kwandon yana kangal-kangal amma da yake bata ma san abin da ta kifo a kan nata ba da sai ta"

yi wa kanta dariya.

"Kowa ya bazamo har da masu himilin kayan wanki a ™ulle a zannuwa dan gudun kar su yi asarar kaya sai su kinkima su Wora a kai suke zabga gudu, wata mata ta fito Wauke da randar ™asa"

wacce ake zuba ruwa yake sanyi ita kaWai tana gudu tana faWin

"""Gwara na rasa komai a akan na rasa randar nan saboda sanyinta ™afata ™afar randata"" Ta ficr fuuuu. Jabiru ya take wa wasu miji da mata makafi baya da suka fito daga wani gida kowa ri™e da sandarsa amma a hakan mijin yana dafe da kafaWar matar a haka suka fito, Jabiru da shegantaka ganin suna sauri basa gudu duj da kaancewar su makafi amma bai tausaya musu"

ba ya buWe baki ya ce

"""Ya fara ™ara bom jama'a ya kusa tashi kowa ya ™ara ™aimi wajen gudu kuna dai ganin an ce a film Win turawa wasu sai sun kusa tsira idan bom ya tashi sai ka ga ya tashi da su bayan taku kaWan ne za su ™ara yi su tsira"" Wannan jawabi nasa ya sanya makahon nan Wauke hannunsa daga kafaWar matarsa ya daina dogara sandar ita kanta sandar sai ya mata hawan doki yadda yara"

suke yi ya shiga zabgar gudu. Matar tasa ma gudun take tana kiran

"""Malam kana ta ina?"" Amma Malam ba ya ma jin ta dan ya daWe da bada tazara a tsakaninsa da ita yana can gaba yana biye da wata mata mai siyar da taliya da manja ta gama tace taliyar kenan sanarwar ta sauka a kunnuwanta haka ta Woro robar taliyar haWe da kaskon manjan tana zabgar gudu abinta. Jabiru shi ne a ™arshe sai kwasar dariya yake yana ta mamakin gudun mutuwar da jama'a suke ya tabbatar da a ce za su san ™arya yake sai sun sumar da shi in ma sanadin dukan da za su taru su masa basu kashe sa ba, bare kuma in suka san ta'asar da ya aikata wa ³an karota suka biyo su shi da kakarsa ya tabbatar sai sun kai shi hannun ΄an"

karotan sun dam™a shi i ma mai za a masa na hukunci a masa.

"""Dan wula™anci Barira maimakon ta kinkimo tukunyar tuwon nan shi ne ta kamo hannun ΄a΄an suka gudu ita ce kaza uwar ΄a΄a, ta bar tukunyar a gida sai an je wurin yada zango yara suke kukan yunwa hallaw ga Badamasi uban nemo abinci sai in ™ara tafiya neman abin da za su ci bayan ana cikin halin tsoro ai kamata ya yi duk inda mutum zai je ya tafi da guzuri gudun ko ta kwana"" Jabiru ya ji wata muryar mutum a bayansa yana gudu yana faWa tamkar zai ari baki wai a kan matarsa Barira bata Wakko tukunyar tuwo ba. Waiwaya wa ya yi ya ga mutumin wani Wan lukuti Wauke da wata tukunya lamba uku jikinta duk miyar kuka da ludan Waukan tuwon ma a cikin tukunyar da alama Wumame ne a ciki tukunyar duk ba™in tukunya a jiki duk ya goga a jikin"

farin yadinsa amma bai damu ba shi kawai ta tuwon yake dan kar ya tafi nemo wani.

"""Haka kawai a zamanin Tinubun nan yadda masara da hatsi suke tsada kai hatta maggin miya tsadar da ya yi bai taSa yin irinsa ba amma dan rashin tausayi tana ganin ba ita ta nemo ba ta gudo ta bar Wumamen a gida bom ya tashi a unguwar tukunyar ta yi ™urmus a can inda muka je kuma a saka ni salati da salallami na nemo wani abin da yara zasu ci"" Ya faWa yana yi yana Wan"

gudu.

"""Hmmm! Kai ba tsuntsu mai wayo ba to ai tsuntsu mai wayon ma ta dabara ake kama shi, in dai tukunya ce da kan ka za ka jefar da ita yanzu nemowar da ka ™i dai sai ka sake nemowa tun da kai Allah ya Worawa nemowar ba matarka ba da ta kwashi ΄a΄an ma ai ta yi ™o™ari dan wauta irin taka da kuma ™iwiya sai a bar Wan mutun a Wakko tukunyar tuwo?"" Jabiru ya faWa a ransa yana Wan"

rage gudun da yake sai da mutumin nan ya wuce shi ya bashi ΄ar tazara ya wangame baki ya ce

"""Jama'a a ™ara wuta dai a ™ara mai wajen gudu ga wani ™ara can daga nesa haya™i yana tasowa da alama Waya daga cikin bom Win ya tashi"" Kowa da yake ta kansa yake babu wanda ya samu damar waiwayowa bare ya ga da gaske haya™in ne yake tashi ko kuma su lura cewar basu ji"

wani ™aran tashin bom ba duk sai suka danganta hakan da rashin nutsuwar da suke ciki.

Mutumin nan mijin Barira wanda yake Wauke da tukunyar tuwon Wumame jin gudu sosai yana

neman gagararsa sai ya yi wurgi da tukunyar tuwon ya fara she™a gudun a ransa yana cewa.

"""Haba sai yanzu na ji ina gudu sosai ashe dai tukunyar nan ce take hana ni rawar gaban hantsi"" Jabiru kan dariya sai da ya kasa gudun ma ya dakata sai da dariyar ta tsagaita sannan ya daure ya ci gaba yana zuwa inda mutumin ya yi wurgi da tukunyar sai ya ga tukunyar da ban, murfin da ban ludan ma ya yi nasa wuri sai tuwon da yake ta masifa a kansa ashe ba wani tuwon kirki bane duka guda huWu ne wato yankan Wumamen huWu wanda bai fi ma yaran su cinye lokaci"

guda basu ™oshi ba tun da yankan ma ™anana ne.

Sai da ya tabbatar jama'ar unguwar nan su yi nisa ya dawo wani shago da mai shi ya bazama ya bari a buWe ya Wauki cincin da lemo a frige mai sanyi ya ci ya yi hani'an ya kwashi wani cincin

Win ya zuba a aljihu da lemo roba Waya ya ce

"""Oh ni ko ina Iya Ansai ta buya ita kuma na san dai yanzu yadda kawo ya bazama babu wani mai bada labari idan an tambaya wato idan ΄an karota sun zo sun ce basu ga wasu masu napep sun shigo unguwar ba, kin ga babu mai cewa ya ga wani saurayi ko wata tsohuwa ta zo da alamar rashin gaskiya a tare da ita ko ma ΄a unguwar su ce basu yarda da su ba bare har a shiga bincin a unguwar a gano inda muka Soye adaidaitar mu yanzu dai cincin da lemo ba sata na yi ba wale-wale aka yi fa su ba adana ba"" Ya faWa a ransa yana kallon shagon tare da"

fashewa da dariya a fili ya ce

"""Kaico ni Jabiru jikan Iya Ansai yanzu da gari banza na zo na ce ko alewar naira biyar a bani a shagon nan sadaka sai an kai rana za a bani in ma ba a mini korar kare ba, amma sai ga shi an bar shagon a buWe na shiga ciki ina wada™a har da shan lemo da cincin kai Allah dai ya biya"" Ya faWa yana fitowa daga shagon ya samu wani kango ya buya cike da tsoron abin da ya faru jiya a kango da su da mutanen Soye amma haka ya daure ya zauna a ciki sai da magriba ya fito domin"

zuwa ya samu kakarsa su san na yi.

"""Amma kuwa wannan an yi Wan iskan saurayi to mene ne rubarsa da ya yi hakan? A she dai ™arya yake babu wani bom haka kawai ya bazama mutane da yara kowa yake gudun famfala™i, hatta jama'an tsaro da aka sanar da su suka kasa zuwa unguwar kowa yana tsoron ya zo abu ya ritsa da shi"" Cewar wasu samari da suke tsaye a layin da Jabiru ya baza su ya zo wucewa"

yaji ana ta batun abin da ya faru.

"""Wannan an yi ja'irin yaro haka kawai ya tafa ha kulan jama'a ina barci na ji matata tana tashina a kiWime cikin gagan barcin nan na suri sandata muka fito ko gama warewa ban yi ba, kai da abu ya yi abu sai gani na hau saman sandar tamkar wani ™aramin yaro wato ina dokin kara irin"

"na yara da sandar bara ta"" Cewar makahon nan da suke magana da wani mutum."

"""Yo Malam Abashe ba har gwara kai ba ni fa nan na saSi matata a bayan nan nawa wallahi duk"

"tunanina jakar kuWina ce ta goya wai ashe ita ce kuma sabo da rashin tausayi da imani irin nata sai ta yi lifet a bayana nake zabga gudu da su tumemiyar mace a bayana ga tana Wauke da jaka duk ni kaWai, wallahi bayan nan nawa kamar na Wauki buhun dusa biyar haka nake jin yana ciwo ko ina amsawa yake, kawai dan takaici sai da muka je inda aka yada zangon nan zan sakko jakata sai na ji tana min sannu goWai-goWai ta sakko ni mamaki da al'ajabi ya hana ni maganaa nan na tabbatar cewa tsoro da firgita babu abin da ba ya sakawa kalli bayana fa, Allah sa kar ya"

"yi kanta"" Ya faWa yana juya masa bayansa."

"""Yo da wane idon zan gani, haba dai sai ka ce wanda ya goyi ra™uma ko goWiya? Tabarakallah yo ai ka samu lada ga ladan tseratar da iyalinka ga ladan goyo"" Malam makaho ya faWa yana ΄ar dariya. Takaici ne ya hana shi magana wai ya samu lada, haka Jabiru ya zo sumi-sumi ya fice ta gabansu babu wanda ya lura da shi dan ko ina ma sai hayaniya suke tun da a ransu basu taSa saka cewa wanda ya yi abin zai iya dawowa unguwar ba ma, tun fa sun gano ™arya ya shirga musu tun da dai ko haya™in toyin ™one shara babu bare wani haya™in tashin bom. Iya ma ganin duhun magriba ta saWaWo ta buWe ™ofar gidan ta fito dan tun da Malam ya shige gidan nan ko ™wa™™waran motsi bata ji ba bare ta sanya rai za su fito ta tabbatar yau ko sallah sai dai su harhaWa. Wajen napep Win ta nufa tana ta addu'ar Allah sa Jabiru bai yi wauta sun kama shi ba ko su tafi da napep Win nasu baki Waya. Dan haka tana dosar wajen sai ta ga napep Win yana nan yadda suka bar shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta lallaSa ta shige bayan adaidaitar"

ta zauna sai da ya zauna a fili ta ce

"""Ni ΄ar nan ina zan gano Jabiru?"""

"""Gani"" Cewar Jabiru da yake zaune a mazaunin direba sai dai ya sunkuya shi ya sa Iya bata lura da shi ba da ta shigo, da farko sai da ta tsorata i dai jin muryarsa sai ta ji wani sanyi da daWi, haka suka yace buhun suka ka bar wajen tare da bin kwaltar suka koma ta inda suka biyo dan in suka lulu™a Jabiru ba zai gane hanyar gida ba, dan haka suka sadda™ar suna addu'ar Allah ya sanya saSani da su da ΄an karota a haka suka samu Allah ya taimake su suka koma gida. Nan Jabiru ya bata cincin da lemo tana sha suna hira suna dariya kowa yana bada labarin"

abubuwan da suka faru Iya kan dariya har da runtsirawa.

"""Gaskiya Jaburu ka cika jikana aradu"" Ta faWa tana ™ara yin dariyar sai da ta cinye cincin da lemon"

suka yi sallah kowa ya watsa ruwa.

"""Oh ni Ansai yau ma haka muka ™are gallafirin mu babu cinikin ko kwabo sai mai da muka she™e"

"sai dai tun da mun kuSuta daga hannun mutanen can ai shikenan"" Ta faWa a zuciyarta lokacin da ta kwanta bacci."

*³AN KAROTA*

Tun da suka bi bayan su Iya haka suka sha walgigi amma basu ga ko mai kama da su ba dama Allah bai sa ko lambar jikin napep Win sun gani ba bare har su samu wata hujja wajen

neman su ga shi kuma basu gan su da idanunsu ba shi kansa wanda suka kaWe Win da ya

farfaWo bai gane komai ba dan sai ya zama kamar wani zautacce ce ma dakyar dai ya dawo

daidai.

09013181851

"[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ³AN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep)"

NA

MAMAN AFRAH

Akwai youtube chanel Win da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta

hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.

"Waya zaSin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA"

RUBUTA SHIRME

kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaWai za ki gwangwaje da karatu.

"a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki"

iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE

"Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ³AR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA,"

"KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA."

09013181851

Page13



Washe gari ko da Iya ta shirya Jabiru sai cewa ya yi jikinsa duk ciwo yake na gudun da ya

sha yi jiya dan haka yau sai dai su huta.

"""Qur'ani baka isa ba Jaburu wanda ya fito nema ina shi ina hutu abin ma ya zama rashin hankali wallahi, haka kawai ka san bashi na ciwo muka taho birnin nan dan ganin na cika maka burinka amma maimakon ka zage dantse ka nema sai ka ce wai jikinka yana ciwo ni ma ai in gudun ne na yi ko dan ni jikin ™arfe gare ni ba na tsoka ba"" Cewar Iya tana tsaye ri™e da tsantsa shi kuma"

yana kwance ya yi Wai-Wai a kan gado.

"""Ni dai ban ce ba amma dai ai kya bari mu huta ko yau da gobe ne jibi sai mu fita m..."

"""Wallahi ka yi tsalala kamar shayi ana zaune ™alaw har za mu kwana biyu bamu fita nema ba kamar wasu wanda aka yi wa baki wato kai gaka Wan daWi gida ka samu kuntsumemiyar katifa a gado in aka barka sai ka wuni kana baccin asara, to ka tashi fita babu fashi"" Ta faWa tana Waka"

masa duka a ™wabri da sauri ya tashi yana kumbura baki ya fito haka ya yi alwala ya yi sallarsa.

"""Wai nan sallah ce aka yi gari ya waye rangararai ai wannan sallar ™adangari ce ai su ne suke"

"Waga kai da hantsi"" Ta faWa tana taSe baki."

"""Wai ya za a yi da abinci ne Iya?"""

"""Ban sani ba wato kai ka fi so muke ™wamushe Wan kuWin hannun namu da Allah ya sanya yaron nan Šan har™alla ya bamu sai mun kashe mu zo mu tsugunna bayan kasuwar arincaSar har yau"

"bamu san ta ina take ci ba, ko ficika bamu yi ba wata™ila ma yau sai an saka mata mai"""

"""Haba Iya ci ai ya zama dole kin san dai ciki manta kyautar jiya gare shi, ki siya mana ko waina"

"ce in mun fita """

"To na ji, amma garin masara zan auno yau ake tu™a tuwo ina dalili ina Wan mafari zan ke cacar"

"kuWi ni ba gwabnati ba"" Ta faWa tana shigewa bayi ta yi wanka ta fito."

"Tun da ta shirya take fama fa Jabiru a kan ya yi wanka amma ya ™i, haka ya Wauki mai ya lallafka sai she™i yake tamkar an zuwar da man gyaWa kwalba guda a kansa. Haka suka fita ta kulle gidan tana ta mitar zai ke kashe musu kasuwa in ba ya wanka saboda za a ke ji yana warin dauWa. Bayan sun ci waina da ™osai a wajen wata mata da take soyawa suka tafi suka"

ringa bilayi

"Gidan mai suka je suka sha mai na dubu Waya, Iya tana ta faman mita a kan kuWin da ta bayar amma Jabiru ya yi kunnen uwar shegu da ita haka ta gaji da mitar ta yi shiru. Ranar ma haka suka wuni amma babu fasinjan da suka samu ga suna Wan tsoro duk inda za su kutsa saboda kar a je ΄an karota su gano su, ganin dai babu ciniki gudun shanyewar mai a banza sai Iya ta ce su samu inuwa su zauna ai rabon mutum ba ya wuce shi indai suna da rabo to fasinja zai zo har inda suke. Har la'asar babu wanda ya Waga musu hannu ga shi tun wainar safe basu ci komai"

ba sallah ma a wajen Iya ta yi Jabiru ne ya je masallacin unguwar ya yi sallah ya Wakko mata

"ruwan ita ma ta yi. Suna zaune a cikin napep Win bacci ya yi awongaba da Iya ta jingina sai sakin munshari take. Jabiru da yake zaune kansa sunkuye kamar an ce ta Wago kai ya hango wata budurwa tsaleliya ΄ar duma duma, tana tafiya hannun nan a ma™ale tamkar lauje sai wani hura hanci take. Tun da ya kafe ta da ido daga nesa har ta zo gifta adaidaitan bai Wauke idanunsa ba ™urrr yake kallonta ko ™iftawa ba ya yi, ita kuwa tana ankare da shi amma sai ta yi"

kamar ma ba a yi ruwansa a wajen ba.

"""Malam tafiya za ka yi ne?"" Ta masa tambayar a yangance tana farfara idanu Jabiru da shegen son mata ya ga matar birni a take ya fara kaWa kai kamar ™adangare dan da ta yi magana sai ya ji tamkar an watsa masa ruwa mai ™an™ara, domin abu ne ya haWe masa goma da ashirin ga daWin"

sautin ta ga kuma abinka da ba a saban ba yau sun samu fasinja.

"""Ko ba tafiya za ka yi bane?"" Ta jefa masa tambayar lokacin da ta Wan dawo da baya har tana"

Wan wani karkata kai gefe. Wannan karon har wata in ina ya ji ta same shi.

"""Eh, eh, eh tafiya zan yi"""

"""Ohk "" Ta ce tana ™o™arin shiga bayan, Jabiru kan kallonta sai da ™eyarsa ta amsa saboda ™o™arin waiwaye ba komai yake birge shi ba sai yadda bakinta ya sha jambaki da lips stick sai she™i yake. Tana shiga babu wani dogon tunanin tambayarta inda zai kai ta sai kawai ya saka mukulli ta tashi adaidaitar ga shi babu wata nutsuwa a tare da shi duk ya susuce dan shi a take sai ya ji ya kamu da son budurwar i dai yadda ya ga yanayinta ya san ko a ™afa aka Waura mata shi sai ta"

kunce ta jefar.

"Riiii ya warce adaidaitar ya yi wata uwar kwanar da ta sanya Iya da take bacci ™afarta Waya a waje Waya a ciki jin za ta wuntsulo cikin bacci ta ji hakan sai ta Wauka ma ko faWa ne ya tashi tsakanin fulani da hausawa a ™auyen su wani ya hankaWa ta dan ita a cikin bacci take kuma ta ma manta cewar a Kano suke, yanzu ba a ™auye ba bare har ta tuno zaune take a cikin adaidaita sahu. Jabiru da yake ta Allah, Allah ya nuna ™warewarsa wajen tu™i kar budurwar ta ce ta fasa hawa ta sauka ga shi yana jin shau™in ganinta duk ™amshin turarenta ya buWaWe napep Win, kwata- kwata ya ma manta da wata Iya tana bacci bare har ya tashe ta ta gyara zamanta duk kuwa da tana sakin munshari, ita kuma budurwar ko da ta shiga tana Wan danna waya bata ma lura da Iya ba bare har ta yi la'akari da munsharinta, Iya da buWe idanunta kanta ya sauka a saman napep Win kawai sai ta gane bacci take dan ta tuna a inda take, da sauri ta maido ™afarta tana rafka"

salati ta rirri™e napep Win da hannu biyu.

"""Lahaula wala ™uwwata illah billah, Jaburu amma yau na ™ara tabbatar da cewa albasa bata yi halin ruwa ba, idan ubanka Umaru ne ya mini wannan ™an™anci dama ai na san a rina an saci zanen mahaukaciya, wato kai ga mai arincaSa ko abin nema ya samu, ni Ansai gamu ga Allah Sarawo a hannun mata"" Cewar Iya da ta takarkare tana faWa cike da faWa ganin kamar tana"

magana da bango.

"""Wai dan matar ubanka wacce bai aura ba Jaburu ba magana nake maka ba, ji yadda ka sha"

"wata uwar kwana sai ka ce za ka karya kan arincaSar? Kana ganin ™afata a waje amma ko ka ce in tashi in mayar da ™afar ciki son ka guntule mini ™afa in dawo yawo da sanda to ahir Winka wallahi ko so kake ka kashe ni ka ci gadon arincaSar da kuWinta ma bamu biya ba kai da ba wani ™wa... Bata ™arasa ba Jabiru da sai yanzu ma ya lura da masifar da take faman masa ya ji tana neman masa Saran-Saramar cewar bai ™ware a tu™in ba ta sanya ΄ar fasinjar da suka samu su rasa kuma shi ba rasa ta Win ne damuwarsa ba shi bai gaji da ganinta ba. Signa yake mata a kan ta yi shiru kar ta ji™a musu aiki,

Please Login or Register in order to submit comment