You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ya dawo da ita hayyacinta data dawo nutsuwarta zata nemi mijinta"""

"Addu'o'i ya rinqayi Mata tare da kiran kakan Hamdan ya qurfana gabansa yace  kace da yarka ta gargadi danta ya qyale yarinyar nan ta rayu cikin salama idan yaqi to zamusa manyan sarakuna su batar dashi munyi Masa iyaka da matar wani"" Jinjina Kai yayi ya juya ya fice malamin ya dubi Alh Barau yace  kayi tafiyarka zaa shigar da ita gda ayi Mata magani nan da kwana uku ku dawo ku dauketa hakanan akaci gaba da kula da lfyrta ba ita ta farka ba sai a"

rana ta ukun da asuba tana tashi tayi salati ta fara waige waige.

"Numfashi Mal na Allah yayi ta juyo da sauri ta sauke idonta akansa shima ita take kallo yace  barka da dawowa duniyar mutane"" idanta na kansa tace  ina mijina waye Kai"" murmushi yayi yace  mijinki yananan ni me magani ne Ina fatan kin warke"""

Shiru tayi tana kallonsa ya dauki waya ya Kira Alh Barau suka gais a ya sanar dashi mara lfyrsu ta sukayi murna sosai sannan ya qara neman alfarmar zata zauna anan kafin komai ya daidaita kasancewa mahaifiyar Safwan ta hau tsini ta cake akan Babu yanda zaayi danta ya zauna da karuwa bayan ta gama lalata matashi sannan ta zauna da ita matsayin suruka ita bazata iyaba duk yanda Alh Barau yaso fahimtar da ita jihadi zasuyi su ceto yarinyar daga sake fadawa hallaka abin ya fрskara dole sai qyaleta yayi yaci gaba da shiryawa dannasa inda zai zauna da iyalinsa suji dadin rayuwarsu salin alin.

Haukan nata yaga yayi yawa dole ya shirya ya tafi garinsu ya sanar da manyanta abinda yake faruwa mahaifinta wato kakan Safwan yayo tattaki yazo ya tausheta tare da nuna Mata fa'idar hakan dole hakanan ta hqr tayi musu fatan alkhairi sati biyu Harmdan tayi a gdan malamin yana kula da ita sosai tare da yimata nasihohi masu ratsa jiki da suka sanya jikinta yin sanyi zuwa yanzu duk wani rudu da qyaleВn duniya sun fita a ranta tayi murna sosai da Mal na Allah yake fada Mata ai sun zubar da cikin jikinta sannan sunyi Mata katanga da duk wani aljani da yakeson shiga rayuwarta ranar da ta cika sati biyu ne Rukky ta kawo Mata ziyara saboda suna

chart sosai sunyi murnar ganin juna sosai suka rungume juna suna kukan murna Rukky tace.

" Na shiga dimuwa da tashin hankalin rashinki Harmdan Babu inda ban duba ba kuma bansa an dubamin ba Amma Babu wani lbr sau uku Ina zuwa su Safwan a qarshe babarsa tace shima ta dauki sama da shekara guda Bata gansa ba ance ganin qarshe tare akayi muku ya daukeki wai zai komar dake KD, daganan sai nayi tunanin zuwa gurin Mahmood Ina zuwa naga gidan a kulle na tambayi me gadin gdan yake cemin ai shi kansa baisan meye ya faru ba yasan dai ogansa shi kadai ya shiga gda daren da abun zai faru da safe ya saba tashinsa da asuba yaje tashinsa kawai yaji ya lancaba qafarsa a cikin wani abu a parlour ya kunna fitila kawai sai yaga ruwa aqasan kamar amai yana daga kansa yaga megidan nasa a ratayi jikin panka shine ya fita ya nemo dauki aka kawo masa suka Kira jami'an tsaro aka sauko dashi akayi bincike aka gano shine ya rataye kansa aka rinqa Allah wadarai dashi a qasar Nan"""

"Kuka Harmdan takeyi sosai tana shassheqa tace  bashine ya kashe kansa ba wlh Hamdan ne ya kasheshi ... "" Saurin rufe Mata baki tayi tace  to kiyi Shiru don kuwa ya kashe mutane da yawa shima Honorable ya karci qasa a dakin hotel tare da wata karuwa yaje ya kasheshi itama karuwar ya kasheta sannan ya kashe Xeecup itama a qasan gadar tamburawa aka tsinci gawarta ta dige ta zagwanye a cikin tabo ke in taqaice Miki baa ganeta ba saita hanyar takardun dake cikin Jakarta national ID card da master card dinta sannan shima producer irin mutuwar Mahmood yayi ke duk wani mutum da nasan ya taba mu'amala dake babushi a"

"duniyar nan ciki harda Safwan bawan Allah da kika lalatashi kika jawa iyayensa asara"""

Kuka ta Kuma rushewa dashi tana cewa  aa Bai mutuba yadai so kasheshi haqansa bai cimma ruwa ba daga bene hawa na biyu ya jefoshi akace saboda kawai baban Safwan ya shige gaba an daura mana aure shima Kuma a qoqarin nemawa kansa mafita ne inada cikin Hamdan a jikina Safwan ya sanar dashi amma yaqi yarda wannan dalilin yasa ya shige gaba wajen daura

mana aure sabida haka ya jefoshi daga bene amma cikin hikimar Ubangiji karaya daya yasamu yanzu haka bansan inda yake ba Amma Mal na Allah yace very soon zai dawo

"[1/31, 4:53 PM] Real Oum Hairan: =ифо *_Zaman!_*=ифо"

*_Period_*

*_39-40_*

Ajiyar zuciya sukayi tare daidai lkcn da sukaji anyi sallama hamdan ta miqe da sauri tayo waje suka zubawa juna ido cike da shauqin qauna da tausayin juna tana share hawaye saboda ganin hannunsa daya karye shima itan yake kallo zuciyarsa yanajin wani sanyi yana kwarara na ganin masoyiyar tasa cikin aminci nufosa tayi da gudu ta fada jikinsa suka rungume juna suna sauke

numfashi.

"Dagota yayi ya saqalota da Hannunsa mara lfy ya dora habarsa saman kanta yaja fasali yace  inasonki Harmdan"" rungumeshi ya qarayi tana sauke ajiyar zuciya suka shiga dakin nata itadai Rukky tafiya tayi saboda ta lura qawar tata tayi nisa sun jima suna kallon juna kafin yayi Mata murmushi yace  mom tanaso tayi taron biki Amma na hanata yanzu haka da ita muke suna tare"

"da Mal na Allah a soron baqi tace yau a gidanki zaki kwana"""

"Zaro ido tayi shima ya zaro sukayi dariya a tare yace  nasha wahala Amma na dace masoyin gsky shine bakajin komai don ka sadaukar da komai akansa"" sunkuyar da kanta tayi ya sakeyin murmushi yana Shirin yin mgn Suka shigo da sauri Harmdan tayi qasa da kanta sukayi dariya tare Mom ta kamo hannunta tace  dole kyaji kunyata Mana kin sacemin da shekaru kusan biyu"

Koda yake ya riga ya wucce yanzu sabuwar rayuwa zamu tunkara sai a yawaita Istigfari

"Kuka ta saka ta shige jikin Mom Mom ta rinqa lallashinta hardai tayi shiru suka miqe suka tafi ko a gdansu Safwan bangare guda aka ware Mata ita da mijinta saboda Mal na Allah yace kada a nisantata da mutane Junnul ashiq nacine dasu idan aka kebanceta zai it's dawowa ya gallebesu haka kuwa akayi ko da sukaje Mom Hana akaita bangarenta tayi Saida tayi sati biyu a bangarenta tana gyarasu su uku Kubra da Bushira sai Hamdan gyara mara algus Safwan kuwa yana jinyar hanunsa cikin sati biyun yaji sauqi sosai idan yaga dugu dugu saiya zagayo gurin matar tasa Amma Babu fuska dole haka yake hqr ranar juma'a aka fara bikin Rukky itace babbar qawarta bikin Yaya uku Alh Barau yakeyi Bushira Kubrah da Safwan komai iri daya yayi mawa Harmdan da yayansa Kuma ya hada Mata lefe kamar yanda aka kawowa yayansa ranar kamu da yamma saiga dangin mahaifinta daga gana har yanzu ba musulmi bane Amma sun waye sosai suka qullo kudade masu kauri suka bawa Mom akan ayi Mata kayan daki musamman qanwar mahaifinta Mom taso taqi karba Amma suka dage haka ta karba tabasu masauki akayi biki dasu ranar lahadi akakai amare gidajensu kowacce aka barota da halinta wannan dare anyi kwanan soyayya Safwan ba daga qafa kwana biyu baqi suka gama watsewa gidan ya rage daga mom sai Harmdan Mom tana ganin wani salo na rashin kunya gurin Safwan, wata biyu da tariyar ta fara rashin lfy gwajin farko aka gano cikine wayyoh murna gurin"

Safwan da iyayensa har Dad a zuwa dubata.

Watanni sukayita tafiya tana rainon cikinta lkcn haihuwa ta sullubo yaranta biyu duka mata akasha suna yara sukaci sunansu Fadima da Zainab watansu hudu ta fara fuskantar yanayi kafin ta ankara anyi Mata barna suna zuwa asibiti akace sabon cikine wata daya ta nuna bataso Mom ta rinqayi Mata nasiha harda ta hqr hakanan shima ta haifeshi namiji Mukhtar shima

shekararsa days tayi masa qani a shekara uku dai sukayi yara hudu Allah kenan me kyauta da

"qari wahalar da tasha a haihuwar Mahmood ne yasa Mom nema Mata tazarar gargajiya sukaci gaba da rayuwarsu da yaransu hudu gwanin sha'awa,"

Rukky kuwa itama Allah ya tarfawa garinta nono abokin Safwan Jabir shine ya aureta Suma

suna zamansu lfy cikin so da qaunar juna soyayya me qarfi tana gudana tsakanin masoyan inda rayuwa taketa albarka komai ya wucce kamar komai Bai faruba.

_Alhmdllh Nan na kawo qarshen wannan lbr daya wahalar dani dafatan zakuyimin afuwa na jina Shiru da kuka rinqayi insha Allah bazan sake daukan lbrn da zai bani Kashi haka

ba _

_Sai Allah ya hadamu a *_BATURE_* _idan naga dama Kuma na kirashi da *_AURENA DASHI_* *_(Ahlil kitab)_*

_Ke muku fatan alkhairi_

*_Ummuh Hairan_*


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment