You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zama kamar zautacce a wancan zamanin ga rashin kwanciyar hankali daga cikin gidansa ga neman abinda za a ci.

Lokacin muna da shekara takwas a duniya. Ni da Hadiza tare muka tashi cikin ikon Allah suka sake samun ciki a lokaci daya. Abin ya had'ewa Mama laulayi da ciwonta da yake tashi a sa'i da lokaci don dai ma Gwaggwo da

Babanmu a tsaye suke akanta duk inda suka ji magani mussaman na hausa suna ko'karin saya mata. Kuma idan an

jarraba ana dacewa. Sai dai idan kwana ya kare babu yadda za a yi. Mamanmu ciwonta ya tashi da zafin gaske ga ciki na wata biyar a jikinta.

Suna zuwa asibiti aka bata gado lokacin ma ba ta gane wanda yake kanta.

"Kwana biyu 'yan gidansu suka zo, domin duk abinda yake faruwa babu wanda ya sani a cikinsu. Gwaggo ganin yadda abin ya yi tsanani ya sanya ta sanar dasu. Wani d'anuwan Dada da yake da rufin asiri ya bada umarnin a d'auketa a kaita babban asibiti zai biya kudin da duk abinda aka buk'ata. Babu rabon shan wahala da asara rai ya yi halinsa a lokacin da ake yin cuku-cukun. Mamanmu ta rasu da cikin a jikinta a daran alhamis aka kaita Juma'a da safe."

Alokacin da kuruciya ban fahimci mutuwa ba. Ni dai kawai na daina ganinta idan na tambayi Gwaggo sai tace mini ai ta tafi saudiya.

"Da aka share makoki Dada ta bukaci da Baba ya ba ta ni, tunda ni ce karama. Ummansu Hadiza ta ce a bar mata ni din za ta had'a ta ri'ke mu tare 'yarta idan an d'auke ni Hadiza ba za ta ji dadi ba."

Ganin yadda ta nuna damuwarta akan hakan ya sanya Babanmu ya ce Dada ta yi hakuri ta d'auki anti Yagana idan ya so ni sa'i da lokaci sai a dinga kaini garin muna gaisawa.

Haka kuwa akayi suka tafi da anti Yagana tana kuka Ina kuka haka muka rabu. Gwaggo ta rungume ni tana cewa na yi hakuri za a dinga kaini lokaci zuwa lokaci.

***

Na koma hannun Ummansu Hadiza gabad'aya. Da farko kamar abin arziki sai daga tafiya ta mika tukkuna ta fara nuna fifiko da bambamci a tsakanina da yaranta Hadiza da Fati wadda ta haifeta bayan rasuwar Mamanmu. 'Kiri'kri take nuna komai. Ina kallo zata sayawa yaranta wanduna da 'yan kunnaye da kayan kwalliya ni ba zata saya mini ba. Sai dai na je gidan Gwaggo idan ta lura babu d'an kunne a kunnena sai ta saya mini ko ta cire na kunnanta ta sa mini. Wasu lukutan ma haka zata dafa ruwan zafi ta wankeni da wandon jikina wanda sai ya fi wata d'aya ban cire ba. Gwaggo itace take saya mini wanduna da kayan kwalliya sannan itace take tsefe mini kai ta ba ni kudin kitso na shiga nan makotansu a yi mini.

"Da Ummansu Hadiza ta lura da Hakan sai ta hana ni zuwa gidan gabad'aya. Idan mun taso daga makarantar allo Hadiza zata shige ta kwanta ni kuwa zan yi shara da wanke-wanke sannan na je wurin Babamu na kar'bo kudin cefene na je na yi. Tun ban kai shekara goma sha biyu ba na ke yi mana girki. Nasha k'onewa a hannu da k'afa wasu lokotan idan na nuna mata sai ta yi mini banza, sai ta ga dama za ta ce mini sannu. Haka nake warkewa. Kayan makarantarmu na boko ni nake wanke mana. Wani sa'in ma idan Ina wanki Ummansu Hadiza za ta de'bo 'yan k'ananun kayan tagwayen da take goyo Hassana da Usaina ta watso mini tace na wanke musu."

"Ba ni da lokacin kaina kullum idan naje makaranta na dinga gyangyad'i kenan, domin wasu lukutan ma da daddare har aikena take yi wurin masu awo da kantina idan tana buk'atar wani abu."

Watarana mun dawo daga makarantar boko ni da Hadiza nuna tafiya sai ga Yaya Aminu akan Kekensa. Na dinga

washe baki ya tsaya a gabanmu Yana murmushi. Hadiza ta murguda bakinta ta bar wurin bata gaishe shi ba. Ni kuwa muka gaisa sosai Yana yi mini wasa kamar yadda ya saba a lokacin da yake tambayata me yasa na daina zuwa gidansu ban rufe masa ba na sanar dashi Ummansu Hadiza ce ta hana ni.

Ya rarrasheni sosai yana fad'in ki cigaba da ha'kuri dadin abin ma ke macace aure za a yi miki watarana sai labari. Ya d'auko dari biyu ya ba ni.

Ina shiga gida Ummansu Hadiza ta rufe ni da fada wai na tsaya shiririta bayan na san akwai abinda zan yi. Na ce

"mata mun gaisa da Yaya Aminu ne shiyasa ban shigo da wuri ba. Hadiza tana daga cikin d'aki na ji tana cewa wannan cangal din ai dan'iska ne, ki cigaba da tsayuwa dashi zai lalata ki."

"Raina ya b'aci sosai. amma sai na share ta ban ce komai ba, itama Ummantasu bata kwa'beta ba. Na cire kayan makarantar jikina domin yin abinda yake gabana."

Sa'i da lokaci Yaya Aminu ya kan ba ni dari biyu a duk lokacin da muka had'u. Ni kuma zan kar'ba da murna da farinciki domin wannan dari biyu da yake ba ni tana taimaka mini sosai a makaranta idan ana birek don ma wani sa'in Sahura tana zuwa da abinci sai mu ci tare ina rage yunwa mutuka. Su Hadiza Ummansu tana basu hamsin hamsin kullum. Ni ce dai bata bawa. To ashe tana lure da ni idan an fito birek din ina sayan Aya da gyada. Sai ta je ta gayawa Ummansu ita kuma ta titsiyeni tana tuhumata wai maza nake bi suke ba ni kudi suna tabbatani.

Na dinga kuka ina gaya mata ba haka ba ne. Yaya Aminu ne yake ba ni dari biyu wasu lukutan. Ta dinga fad'in to shi ma ai d'an iskan ne garjejen tuzuru dashi yana zaune shekara arba'in babu aure ai dole sha'awa ta yi masa yawa ya

dinga tare yaran mutane Yana tattabe su. Na ce wallahi babu abinda yake yi mini Umma ki aika a kira Sahura ma ki

tambayeta ni ba na kula maza.

Hadiza ta dinga fad'in itama Sahurar ai halinku daya haka take kashe kudi a makaranta.

"Da Babanmu ya dawo ta gaya masa. Ya yi mini fad'a sosai, amma shi bai zarge ni ba. Sai da Baba Sule ya zo"

"Ummansu Hadiza ta gaya masa. Ya dinga zagina Yana zagin Mamanmu har sai da ya dake ni da igiyar da muke shanya, yana fad'in ba zan gurb'ata musu zuri'a ba."

"Ummansu Hadiza kamar wadda ta yi mini farraku da dangin Mamana ko an kai ni garin ba na dogon zango nake Sanya rigima sai na dawo Koda anti Yagana ta yi haihuwar fari ma da muka je da Gwaggo ta ce zata barni a can din na kwana biyu 'yan'uwa su gan ni. Kuka nasa sosai kan cewa ba zan zauna ba, kafata kafarta. Haka Dada za ta yi ta fad'a ta gaji ta ha'kura domin ba na iya sakewa dasu na dai fi son cikin wahalar kamar yadda Dada take fadi a koyaushe."

Sai zuciyata ta sake 'ke'kashewa na ji a raina babu wanda ya isa ya raba ni da alhalin Gwaggwo domin sune suka

tallafi Mamana a lokacin da bata da kowa yanzu kuma suna tallafata. Duk da basu had'a ji'bi da Mamanmu ba 'kawance ne kawai da zaman gari d'aya ya had'a su da Dada amma kusan koyaushe na dubi gwaggo sai na ga kamar dangin Mamana nake tare dasu gabad'aya. kuma ina zuwa gidanta Muna gaisawa sa'i da lokaci amma ban ta'ba bari Hadiza ta farga da hakan ba.

Sahura k'awata ce sosai a bayan gidanmu gidansu yake. Ajinmu daya da ita a boko da allo haka zalika ma makarantar

dare ajinmu daya da ita. Gidansu babane Babansu Yana da rufin asiri daidai gwargwado. Ya rasu ya dan bar musu d'an abin hannu kuma yana da akid'ar boko sannan akwai had'in kai a gidan zumunci bai lalace ba. Nan nake zuwa na huta a wasu lukutan na yi ta kuka tana tausata ina gaya mata ina so ko diploma ma ne na yi domin na samu aikin da zan dogara da kaina. Ita kuma ta yi mini alkawari za ta gayawa Baban yayansu a yi mana kokari a tare idan jarrabawarmu ta fito.

"Muka ta so a gidanmu 'yan mata mu hud'u. Hadiza ce babbar cikinmu sai ni, sai Fati wadda aka haifeta bayan"

"rasuwar Mamanmu, sai kuma tagwayen da ta yi. Daga su ba ta sake haihuwa ba. Sai da Babanmu ya auro Ummansu Saminu mai suna Sakina. Tana zuwa ta fara da maza ta gwaye Hassan din ya rasu kwana biyu da haihuwarsu."

Tsabar yadda nake wahala a gidanmu ya sanya na tsunbure jikina ya tsuke. Shekaruna suka 'buya. Sai ya zamana har

su Hassana sun fi ni kyawun gani da 'kira ta 'yan matanci. Dama ba a zancen Hadiza da Fati tunda a lokacin Uwarsu a tsaye take a kansu da kayan ado da kwaliyya. Gasu da jiki ruguzaza irin nata. Babban burinta a lokacin miji ya fito ta yi musu aure gabad'aya. Ba ta damu ni da halin da nake ciki ba. Duk sai da suka riga ni fara al'ada. Na dinga nuku-nuku ranar da na fara na b'uya ina kuka. Da 'kyar na gyara kaina. Na bi duk matakan da ake koya mana a makarantar dare. Sai dai wandunana biyu ne kacal gashi ba ni da audiga ina dai ganin su Hadiza da ita suna amfani ni kuma sai na yagi dankwalina na kasa shi biyu nake kunzugu dashi. Su yi tayi mini dariya Usaina ce ma daga cikinsu ta mu ta zo daya itace a 'boye take d'auko mini audigar a cikintata ta kawo mini.

Anti Sakina wato Ummansu Saminu itace daidai da Ummansu Hadiza domin dama ita a shirye ta shigo gidanmu.

"Kuma tunda ta ga ta fara da maza a gidan ta gyara zamanta. Itama Ummansu Hadizan tunda ta lura da cewa 'yar bana bakwai ce ta shafawa kanta lafiya. A wasu lukutan tana yi magana idan ta ga son zuciyar da ake yi a gidan. Ta dinga fad'a tana cewa su yaranki shafaffu ne da mai ne da ba za su yi aiki ba. Wannan ba gata ki ke nuna musu ba Murja aure za ki yi musu ba kuma ki san inda zaki kai su ba. Ita wannan din ki kewa gata. Wahala dai mai shigewa ce, kuma shi da ba a yi masa mugunta domin ba kasan ranar da zai yi maka ba."

Makamantan maganganun take yi mata a duk lokacin da ta su ta had'o su a gidan. Ni dai ba na cewa komai sai dai na yi musu shiru su yi su gama. Na dai ajiye a raina cewa watarana sai labari.

Daf da za mu yi saukar al'kur'ani a makarantar allonmu wani Alhaji Halilu mai kudi da mata biyu ya fito fagatatan

"Yana son auran Hadiza wata uku kacal yake so a sanya a d'aura auran Babanmu ya ce bai shirya ba domin bai ajiye komai ba. Mutumin ya ce gidansa akwai duk abinda ake buk'ata ba sai an wahalar da kai ba. Babanmu ya ce za a yi bincike tukkuna ya jira shi. Baba Sule ya yi tsalle ya shiga sha'anin bai bari an tsananta bincike ba ya ce tunda yarinyar tana so a maganata ta 'kare. Kuma dai yanzu a sha'anin aure kawai a binciki aljihun mutum, idan zai iya ri'ke"

iyali ai an yi barka. Balle ya ji labarin mutumin da rufin asirinsa harkar motoci yake yi. Babanmu Ya ja bakinsa ya yi

shiru bai sake magana ba. Baba Sule shi ya yi ruwa da tsaki ya kar'bi kudin auran dubu dari masu danko irin na da.

"Gari ya d'auka an kawo kudin auran Hadiza dubu dari. Makaranta ma a ajinmu zancen ake yi, ai Hadiza aure za ta yi"

kuma mai kudi ne wanda za ta aura.

"Hadiza da Ummansu sun samu abinda suke so. Sai ta fara jiji da kai gabad'aya ma ta daina zuwa makaranta daga ta bokon har ta allon. A lokacin ajinmu uku a boko za mu yi jarrabawar shiga aji hud'u. Allo kuma duk da ba kokari ne da ita ba amma tana cikin 'yan sauka. Ko da ta daina zuwa malamin ajinmu ya tambayeni dalili na ce wallahi ban sani ba. Ya samu Baba da maganar yana gaya masa ya kamata ta cigaba da zuwa domin a hada saukar da ita idan ya so ranar d'aurin auranta sai a bata allonta. Da ya samu Ummansu da maganar sai ta ce tunda aure za a yi mata bai yiwuwa a hada gudu da susar duwawu, auran shine yake da a hakku. Karatun kuma ko Yaya ne ta samu ya isheta. Shima Babanmu bai damu ba ya rabu dasu."

Bikin Hadiza ya hade da hidimar saukarmu. Hidima ta yi wa Babanmu yawa ta ciyar da 'yan biki da sauran

abubuwa. Bai biya mini kudin allo da ankon saukar ba. Gabad'aya abinda kowa ya biya dubu goma sha bakwai gashi kullum idan na je makarantar sai an yi mini magana na kawo.

dana sake tuna masa maganar a lokacin suna tare da Baba Sule suna shirya yadda d'aurin aure zai wakana. Baba Sule ya buga mini tsawa kan cewa na tashi na basu wuri. Shi kuma Babanmu bai ce mini komai ba.

Na kwana da tunani da fargabar tunda na san idan ban bada kudin ba wata'kila za a iya cire sunana. Washe gari na

shirya da wuri na fita gidansu Sahura na nufa aron wayar babarsu na yi bayan mun gaisa. Muka shiga d'aki ni da Sahura duk na fad'a mata yadda akayi. Sai ta kara k'arfafa mini guiwa akan na sanar da dangin Mamana ko za su taimaka mini.

"Lambar anti Yagana ce da ni a kaina. Na kira ta ba tare da ja'inja ba ta d'auki muryata muka gaisa. Na gaya mata halin da nake ciki. Ta ce tana nan tafe a cikin satin amma kafin nan zata turo mini abinda yake hannunta na fara biya kafin tazo, tace babu wanda za a gayawa daga cikin dangin Mamanmu abin kunya ne."

To ashe a ranar ma Yaya Aminu ya je ya biya mini ya samu labari ne a bakin Hamusu 'kaninsa tunda ajinmu daya dashi kuma tare zamu yi saukar ya san ina daga cikin wad'anda ba su biya ba.

Ya zo har gidanmu Yana gaya mini ya biya mini don haka na kwantar da hankalina. Amma bai fad'a mini keken da yake hawa ya sayar ba.

"Da anti Yagana ta zo na fad'a mata. Ta yi ta godiya ta ce na ajiye kudin da ta turo mini a acct din Mamansu Sahura idan ina buk'atar wani abu sai na kar'ba. A daran muka je gidan Gwaggwo domin yin godiya. Ita kuma ta dinga yi mana fad'a tana cewa ai duk yiwa kai ne, kuma duk wanda ya yi wa al'kur'ani hidima a gidan duniya to babu shakka a lahira shi ma zai yi hidima dashi."

*1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank. Mutanan nijar dala dari katin Airtel.*

*07084653262*

"[11/21, 9:33 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*"

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE *

*M.W.A.*

*TALLAH!*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi"

masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana

"sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN

1GB @550

2GB @950

3GB @1450

4GB @1550

5GB @1700

CHECK CODE *323*4# VALIDITY 30DAYS CHAT@08112392177 CALL @08037026306

8037026306 fatima musa ibrahim opay

*@Arewa books*

*Bintuumarabbale.*

*free pege*

*12*

"Duk sabgogin bikin Hadiza ba ta sanya ni a ciki ba. Ina dai kallo ita da 'yan'uwanta da suka fito ciki d'aya suna ta kai kawo amma ni ban san komai ba. Har 'kawayenta na waje da ire-iren yaran 'yan uwan Ummansu sun fi ni mutunci. Sai na zama kamar bare a gidan su kadai suke yin shige da ficensu. Ta inda Allah Ya taimakeni ma hidimar saukata ta d'auke mini hankali, amma dai duk da haka abin ya yi mini ciwo, haka zalika ma ya yi wa anti Yagana, don sai da ta gaza ha'kuri ta yi mini maganar. Na ce haka suke yi mini dama ba tun yau ba, suna had'e mini kai da b'oye mini abinda ya shafe su."

"Ranta ya baci sosai, ta ce sai ta samu Baba da maganar, na ce kawai ta bari yin hakan zai haddasa rikici domin cewa za a yi ta zo na kwashe 'karya da gaskiya na gaya mata. Ko kuma wasu su canza mata manufa a ce tana yin hassada ne domin ba ni ba ce zan yi aure ba."

Haka ni da ita muka zama ware a cikin gidan. Dama a d'akin Anti Sakina ta sauka. Da yake ta iya zaman duniya ta rik'eta da kyau ta janyeta tunda dama ba wani shiri suke yi da Ummansu Hadizan ba. Aka yi hidimar biki da sauka lafiya kowa ya kar'bi sakamakonsa. Ni da allo da kyauttuka na mussaman. Ita kuma Hadiza aka kaita gidan mijinta mai wadata da abin hannu Allahu Halilu.

Anti Yagana bayan hidimar da kwana biyu ta tattara kayanta ta tafi da takaicin abubuwan da suka faru a sha'anin da ya gabata.

"Ni kuma na cigaba da rayuwata da 'yan'uwana da muka rage mu uku a d'aki daya. Sai ya zamana raini ya shiga tsakanina dasu. Usaina ce kawai take girmamani, amma da bana kai zuciyata nesa da kullum sai mun yi fad'a, kuma babu yadda za a yi a ba ni gaskiya kasancewar ni ce babba a cikinsu."

"Ganin haka ya sanya na je na samu Maman bokola wata mata ce a bakin titin gidanmu take da shagunan d'inki. asalinta 'yar ghana ce ta zo ta kama haya a kusa da gidansu Sahura. To duk yawanci 'yan gidansu ita suke bawa d'inki, ni ma ta ta'ba yi mini sau d'aya amma kyauta ta yi mini, dalilin Sahura muke gaisawa idan na je gidansu. Da ban sameta a shago ba na je gida na sameta na ce don Allah zan dinga zuwa ina koyon d'inki idan na iya sai ta daukeni aiki ko kalmasa na dinga yi mata."

Sahura ta dinga yi mini dariya tana fad'in ai ita ba za ta iya d'inki ba saboda wahalarsa. Ni kuma na ce ina da naci

akan abinda raina yake so. Maman bokola ba ta da ganin 'kyashi ta amince mini tace amma ba shago zan dinga zuwa ba gida zan sameta duk ranar asabar da lahadi da safe take zaman yanka sai na zo na kalla. Ta yi mini alkawari kuwa daga na iya d'inkin za ta d'aukeni aiki.

"Ban yi kasa a guiwa ba na samu Babanmu na gaya masa. Ya ce babu damuwa amma lallai na sanar da Uwata yana nufin Ummansu Hadiza. Na gaya mata yadda muka yi tace tunda ubanki ya barki yawon gantali da sunan koyon d'inki ni menene nawa a ciki, Allah Ya bada sa'a. Abinda tace mini kenan"

"hakan bai karya mini guiwa ba, kuma na dinga tunani akan lafuzanta bini-bini sai ta jefe ni da mummunar magana mussaman wadda ta danganci maza. Ni Kuma ba kulasu nake yi ba, asali ma a unguwar ba a taba cewa ana sona ba, yaranta ne kullum cikin zance da samari, amma ni babu wanda ya ta'ba zuwa wurina."

Duk ranar asabar da lahadi da wuri nake zuwa gidan Maman bokola watarana ma ni nake yi mata shara da wanke- wanke kafin mu zauna ta fara gudanar da aikinta ni kuma ina ta nazari.

Hakan bai d'auke mini hankali na mance da haddar da nake yi ba. Karatun boko na ma ina kokari sosai domin duk abinda na sanya 'kulafuci akansa ba na yi masa rikon sakainar kashi tunda yayansu Sahura ya yi mana al'kawarin shige mana gaba wurin samun diploma na ajiye a raina sai na ga abinda ya turewa buzu nadi.

'Bangaran Gwaggwo ma tana yi mini alheri sosai. Hakan nan Yaya Aminu wannan d'ari biyun da tun ina 'karama ya

kafa mini adashinta yana ba ni a duk lokacin da za mu had'u.

"Tafiya ta mi'ka a cikin sha'anin auran Hadiza matsaltsalu suka fara kunno kai. Ashe da manufar da ya aureta,"

"yana so ya mori kuruciyarta ne ba don ya haihu da ita ba. Matansa biyu na gida sun haifa masa yaran da ya 'kayyadewa rayuwarsa. Daga zarar ta samu ciki sai ya zubar dashi. Wannan shi ya fara kawo musu matsala wadda tun tana nuku-nuku har dai ta zo gida ta fad'a tana kuka, duk garin jikin nan babu ta rame saboda fargaba. Ta ji labari an ce yawan zubar da ciki ya janyo cancer da raunanar mahaifa, kuma dai zahiri itama tana so ta haihu. Suka dinga fa'di tashi a boye. Ummansu na yawon gidan malamai domin nemo mata taimako a juyo da hankalinsa. Amma a banza, idan ta yo yajin ta dawo gida baya zuwa biko da 'kafafunta take komawa dakinta."

"Babanmu kuma ya ce ba zai iya ba, dama can sune suke son auran, idan ba zata iya zama ba ta nemi saki. Ko ta sanar da Baba Sule waliyyanta. Shi kuwa Baba Sule da ya ga lamarin ya kwa'be ya dinga zamewa yana fad'in

Please Login or Register in order to submit comment