You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya d'auke ni mai nauyin gaske anan na bingire ba tare dana hau katifar dake shimfide a gefe ba. Wajan sha

biyu da rabi anti Yagana ta tashe ni. Wai na hau katifa kada jikina ya yi ciwo. Sama sama nake jinta na ja jikina na hau katifar na kwanta ta kashe fitilar d'akin ta fita. Gefin asuba na tashi na zauna gabad'aya dan'kon baccin ya saki idona. Gabana ya dinga bugawa. Wani mafarki na yi mara kyau wai ga mutane a kofar gidanmu a tsaye anata hayaniya. Wani Yana cewa a tafi a nemo Kamalun duk inda ya shiga.

na sauka daga kan katifar na nufi bandakin da yake cikin d'akin cikin sanyi jiki da kiran Innalillahi wa'ina ilaihi! Ban kwanta da abin a Raina ba ballantana na ce. Gabad'aya sai hankalina ya yi gida don mafarkin ya tsorata ni sosai.

"Muna karyawa da Anti Yagana na ce."" Jira nake Babanmu ya tashi daga bacci anti yau za mu tafi tunda an daura aure, na bar din'kunan mutane wallahi, ga Kamalu, kin san abin sai a hankali."""

"Ta ce."" Malama kya bari dai sai gobe wace irin tafiya ce wannan da gaggawa haka, Shi ma Babanmu haka yace sai"

"gobe sai ku tafi a nutse, jiya ai mun jima dashi da daddare muna hira."

Kiran waya ya katse maganar da zan yi. Ina dubawa na ga Usaini. Gabana ya buga. Hannuna na rawa nasa a

kunnena.

"Ya ce."" Anti Amina an tashi lafiya? Yau za ku dawo ko?"""

"Na ce."" Lafiya Lou, wata'kila yau ko gobe, ina fatan dai lafiya, ina Kamalu ka bashi wayar mu gaisa."" Ya yi shiru bai ce komai ba."""

"Cikin mi'kawa Allah lamarin na ce."" Usaini tunda na ga Kiranka na tabbatar da matsala, ka fad'a mini kawai, abinda ba sabon abu ba ne, me ya faru?"""

"A sanyaye ya ce."" Anti abin ne babu dadi wallahi, da har na ce kada a gaya miki. Ummansu Hadiza ta ce a fad'a miki kawai, ki san abinda yake faruwa."""

"Na daga kai ina kallon Baba lokacin yana ko'karin shigowa. Na ce."" Usaini gaya mini don Allah, ba na son kwane"

"kwane Kamalun mutuwa ya yi ne?"""

"Ya ce."" A a, da asuba ne da aka tashe su shi da Saminu domin su yi sallah, bayan sun fito daga massalaci sai suka je tu'ka-tu'kar kofar gidan Alhaji Lawan. Suka kwashe jarkokin mutane har da sababbi sun kai goma suka had'a da zungureriyar kurar ruwar wani dan garuwa. Suka nufi cikin kasuwa, su uku Saminu Kamalu da kuma Shamsu 'kanin Bashir abokina. To Allah dai Ya rufa asiri ba su sayar ba, Malam Maharazu na bayan gidanmu ya shiga kasuwar da wuri shine ya gansu a gurin masu sayarwa ana ta ciniki, to da yake akwai police station ana gane sato wa suka yi, gabad'aya su ukun aka kama su suna can a cell a kulle."""

"Ajiyar zuciya na sauke na ce."" To Usaini Allah Ya kyauta, idan hali ya yi za mu iya dawowa yau, idan kuma hakan bai samu ba sai gobe idan Allah ya nufa ."""

"Ya ce."" Shikkenan anti Amina, amma don Allah ki kwantar da hankalinki, na sanki da sanya damuwa a cikin rai, kin ga ba ke kad'ai ba ce, wallahi ba ki ga yadda Ummanmu take kuka ba yanzu ta yadda da cewar Saminu shine shugabaa cikinsu."""

"Na ce."" To, zan danne Usaini, ba zan sanya damuwa ba, na gode kawai zan kira ka idan an jima, yanzu ya mu"

"tattauna da Babanmu."""

"Na kashe wayar na dube su. Gabad'aya hankalinsu Yana kaina, ba sai na yi musu karin bayani ba sun ji komai tunda"

handsfree na sanya wayar rad'au duk sun ji komai.

"Anti Yagana ta fashe da kuka tana fad'in."" Wannan wace irin masifa ce, yaran nan suke nema su janyo mana, jarkokin ruwa uban me za su yi da kudin idan sun sayar, Yara k'ananu dasu."""

"Na bita da kallo ban ce komai ba, domin a lokacin ma ni kaina kullewa ya yi na rasa tunanin me zan yi, na san dai tun"

lokacin da Usaini ya fara yi mini bayanin abinda yake faruwa wani abu mai nauyi ya tokare mini a wuya.

"Babanmu ya dubeta Yana fad'in."" Ai ba sabon abu ba ne Yagana ke yanzu ki ka ji shine dalili. Ki daina yi musu kuka, yi musu addu'a kawai, Allah Ya tsayar musu iya nan, kuruciya ce kowa da irin tasa."""

"Tana goge hawaye wasu na sake zubowa. Gabad'aya ta rikice sai Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un take yi. Ya dube ni yana cewa."" Tashi ki shirya mu tafi a samu a fito da su, zaman cell din ma wata masifar ce, bari na fita na yi sallama da jama'a."""

Ya tashi ya fita da saurin gaske.

"Na dubi anti Yagana da kanta yake a sunkuye hawaye na zuba tana sharewa na ce."" Ashe ba ni kad'ai ba ce mai saurin kuka."""

"Ta kalle ni, na yi murmushin da babu nishadi a cikinsa. Na tashi kafafuna na rawa na shiga d'aki na fara had'a kayana. Cikin zuciyata ina ta kiran sunan makagina da ya kawo mini d'auki"

***

Tafiya ce muka yi ta a gigice cikin rashin kintsi shiyasa ba kowa muka yi wa sallama ba. Allah Ya nufa muka samu mota mai kyau da rashin tsaye tsaye. La'asar sakaliya muka sauka a tasha nan kasuwar kwari.

"Na kira Usaini domin jin karin bayani. Ya ce mini ai har yànzu yaran suna can cell a rufe domin jama'ar unguwa sun ce sai an shiga kotu an hukuntasu tunda an jima ana sace musu kayan ruwa."""

"Na ce."" Kai kana ina yanzu, ko kana shago ne?"""

"Ya ce."" E, ina shago anti kin san Babanmu da zaku tafi ni ya barwa dan mukkuli, idan an samu aiki na yi, nake basu kudin abinci, yanzu haka ma akwai aikin mutane a hannuna."""

"Na ce."" To yi zamanka tunda kana da aiki, amma ka samu wani ka turo shi muna nan tashar kwari, ya zo ya d'auki kayan nan zan bashi kudin mota."""

"Ya ce."" To yanzu kuwa anti."" Na kashe wayar. Na dubi Babanmu da yake tsaye a jikin wata tumba ta wutar lantarki,"

"tausayi ya ba ni kwarai, haka dai na daure na yi masa bayani duk yadda muka yi."

"Ya ce."" Ai dama da wuya jama'ar unguwar nan su ha'kura, kin san babu had'in kai, idan matsala ta faru a"

"maimakon a had'u a kashe wutar sai a samu wasu a gefe suna rurata. Yaran nan kowa yana dasu sai addua."" Na ce."" Baba tafi gida ka huta, ni zan wuce station din, in sha Allahu abin ba zai yi girma ba."""

"Ya ce."" A'a, ba zan bari ki je ke kadai ba, mu je tare Amina, idan da namiji abin zai fi yin kyau."" A sanyaye na ce."" To shikkenan Allah Ya taikaita, su kuma Ubangiji Allah Ya shirya mana su."" ya amsa da ""Amin Ya Allahu "

*1k on talgram*

*0542382124. Binta Umar gtbank*

*07084653262*

"[11/19, 9:07 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*"

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE *

*M.W.A*

*Marubuciyar*

*Yar bangar siyasa*

*Ba'aboren namiji*

*Madadi*

*Ga irinta nan*

*Goje*

*Babban yaro*

*Sadauki Omar*

*Nida Yaya sadam*

*Da sauransu..!*

*TALLAH!*

'Yan uwa

"Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,"

duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su

Sandal flakes Hawee Gabgab Halut

Dorot Coconut chips Dufr(farce) Black khumra

Brown khumra White khumra Oil perfumes da Body sprays

"Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku."

Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka Call/WhatsApp

07037489958

"Location:Gonan Ganye,zaria Kaduna state"

Nationwide Delivery

*Free pege*

*10*

*@Arewa books*

*Bintuumarabbale*

Lokacin da muka isa station din yaran suna cikin cell a rufe. Wani d'an-sanda ya ce maza a sayo musu abinci domin tunda aka rufe su da asubahin babu wani abu a cikinsu.

Na fito da dubu d'aya na ba wa wani 'karamin ma'aikaci daga cikinsu ya je ya sayo musu abinci da ruwa ya shiga ya kai musu.

"wanda case din yake hannunsa ya yi mana bayanin duk yadda suka yi da mutanan unguwarmu. Shi ma ya so maganar ta mutu ganin yaran kananu ne amma wasu daga ciki suka ce ba su yarda ba, kamar dai yadda Usaini ya fad'a suna cewa an jima ana yi musu sace-sace a cikin unguwar."

Babanmu ya ce bari ya je ya samu mai unguwa zai dawo yanzu. Ya tashi ya fita da saurin gaske. Ina zaune ina kallo ana ta shigowa da masu lefi har da mata daga cikinsu akwai wadda na kusa zubarwa da hawaye budurwa ce duka bata wuce shekara sha shida ba take sace-sace. Matar da suke zaune a gidanta haya tana sana'a idan ta fita unguwa yarinyar sai ta shiga d'akinta ta k'asan 'kofa da yake akwai rara ta sace mata kud'i sai yau da dubunta ta cika ta kamata. Da aka tambayeta tana kuka tace Mamanta ce take turata ta d'auko kudin sai su sayi abinci. Koda aka tambayi uwar ba ta yi jayayya ba tace hakane.

Ita kuma matar da suke zaune a gidan nata tana ta rantsuwa wallahi sai ta yi 'kararsu a kotu tunda duk abinda take yi musu basa gani sai sun cutar da ita.

"Dubu hamsin da biyu ta d'auke mata Allah Ya sa ba su ci da yawa ba. Aka lissafa dubu hud'u suka ci, na zaro a jakata na bata. Na ce. "" Don girman Allah ki dubi maraicin yarinyar nan ki rufa mata asiri, kada ki fitar da maganar nan, wanda ya suturta wani Allah zai suturta shi. Dan kuskure ta yi, haka nan mahaifiyarta amma ki yi hakuri, idan ya so sai ki tashe su daga gidanki, Amma dai maganar nan ta mutu anan."""

"Ta yi shiru sai huci take yi. Uwar da d'iyarta Kuma sai kuka suke yi. Na ce."" Ke kuwa baiwar Allah ba kya jin tsoron ranar da Ubangiji zai tuhumeki akan abinda ya baki kiwo. Kada fa ki manta yarinyar nan amana ce a wurinki ki bar"

"ganin ke ki ka haife ta, tana da hakki a kanki, haka zalika ma Allah Yana da hakki a kanki, me yasa za ki dinga tura ta"

"tana yi sata, ki lalata mata rayuwa. Ba zaku nemi taimako ba? Ke me yasa ba kya yi sai ita, ki ji tsoron Allah, kuma ki yi nadama akan abinda ki ka aikata."""

"Ta share hawayen da yake gudana a fuskarta tana fad'in."" In sha Allahu zan kiyaye wallahi rashin yadda zamuyi ne ya sanya shaidan ya ribaci zuciyata, amma na yi alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba."

"Na ce."" To Ubangiji Allah Ya yafe mana gabad'aya, Allah Kuma ya shirya mana."

Jami'in ya gama rubuce rubucensa ya tura su wurin d.p.o domin ya sake yi musu sulhu. Ina nan zaune suka shiga suka fito. Muka yi sallama suka fita.

"Jin shiru Babanmu bai dawo ba ya sanya hankalina ya tashi. Don ba na k'aunar yaran nan su kwana a wurin nan, ina"

"so a samu maslaha. Na kira Usaini a waya domin jin Ina aka kwana nan yake tabbatar mini da cewa suna nan tafe gabad'aya har da mai unguwa."""

Na kashe wayar zuciyata gabad'aya babu dadi.

Koda suka so station din zama aka yi sosai a office din D.P.O aka fito da yaran gabad'aya sun firgice yini daya da suka

yi a rufe. Har da yar rama a tattare dasu. Gefan idon Kamalu ya dan tasa kamar duka kamar kuma alamun kuka. Kallo daya na yi musu na kawai kawar da kaina. Da 'kyar aka samu sasanci. Amma dukda haka d'angaruwar nan sai da aka biya shi kud'in taya da wili acewarsa ba a haka ya ajiye kurar ruwansa ba.

"Kudin beli dubu talatin. Suka buk'ata Kowanne dubu goma gabad'aya kudin hannuna basu wuce dubu sha uku ba. Babu yadda za a yi na yi belin mutum biyu na bar dayan. Tare suke shashancinsu, bayan haka ma iyayensa ba su da wani karfi ta abinda za su ci suke yi. Na bada abinda ya rage a hannuna na fita na ciro sauran na na cika musu sannan suka ba mu yaran muka kama hanyar gida lokacin tara saura na dare."

Lokacin da za mu shiga gidan ne na lura da dinginshin da Kamalu yake yi shi da Saminu sai ra'be-ra'be suke yi suna bin bango.

Usaini kuwa sai talle musu keya yake yi. A haka muka shiga gidan duk suna tsaye cirko cirko. Na bude d'akin na shiga na zauna 'kafafuna har yanzu ba su daina rawa ba.

Tun ina jin hayaniyarsu har na daina ji tabbacin kowa ya watse ya kama abinda yake gabansa. Na tashi na le'ka

"tsakargidan ta tagar dakina. Sai na gansu su biyu a zaune a tsakargidan su kad'ai. Shi Kamalun Yana ra'kube a kuskurwa ya rungume gwiwarsa. Yusi din yana gurfane a gabansa Yana kuka. Na daure zuciyata sosai na ce."" Kai Yusi kukan me kake yi ku taso daga nan ma."""

"Ya kalleni da sauri yana cewa."" Mama don Allah ki yi hakuri kada ki dake shi, jikinsa da ciwo da kafarsa ta kumbura, ya ce ba zai sake yi ba."""

"Na ce."" Ai ba zan dake shi ba, ku taso ku dawo d'aki."""

"Ya riko hannunsa yana cewa."" Yaya ta so mu je, ta ce ba zata dake ba."" Ya dago kansa ya kalleni. Na ce."" Ta so ku shigo ba zan dake ba."" Sai hawaye shaaa! suka fara zubowa daga idonsa. Na d'auke kaina da saurin gaske na bar jikin tagar."

Rigijib haka na zube kan tabarmar duk ko'karin da nake yi wurin danne masifaffan kukan dake ta damuna kasawa na yi. Ya kufce da karfin gaske na sanya hannu na toshe bakina. Na silale na kwanta ina kukan haikan tare da tunanin ranar da Allah zai yaye mini k'uncin dana ciki tunda ga kuruciya.

MAFARI

Malàm Salisu mai hula shine mahaifinmu. Mutum ne mai ha'kuri da sanyin hali. Uwa uba kuma mara son hayaniya

domin da wahala wata hatsaniya ta tashi a cikin unguwarmu ka ji sunansa a ciki. Ya kan kokari wurin ganin ya kama girma da mutumcinsa. Yadda ake fad'a tun yana k'arami ya tashi da zuciyar neman na kansa . Dalilin da ya sanya ma kenan ya fara fatauci zuwa gari gari kai huluna. Sai da Iya mahaifiyarsu ta nuna rashin yardarta da hakan tukkuna ya ha'kura. amma dukda hakan fataucin ya janyo masa alherin arzikin had'uwa da uwargidansa wato Mamanmu kenan mai suna Saratu. Asali Maiduguri kowa ya san gari ne da ake sana'ar huluna irin daban daban. A nan garin Allah Ya had'a shi da Mamanmu a kasuwa ta je sayayya kusa da shagon da yake zama ya gudanar da sana'arsa. Ba a ja dogon lokaci ba da suka aminta da junansu soyayya ta kullu sai iyaye suka shiga cikin lamarin aka gudanar da bincike ta kowane bangare babu wata matsala waliyan Babanmu suke shige gaba har garin borno aka dauro aure.

Babanmu bashi da matsalar wurin zama tunda mahaifinsu su uku kacal ya haifa kuma kafin rasuwarsa sai da ya

bawa kowa wurin zama. A gidansa da yake unguwar kabuga cikin kwaryar birnin Kano Mamanmu ta tare da komai na al'adarsu. Sun yi farinciki sosai a lokacin da suka ga wurin zamanta ya yi kusanci da gidan aminiyar Dada wato mahaifiyarta. Suka dinga godewa Allah da ya sanya akwai wadda za su barwa amanarta a garin.

To Gwaggo maihaifiyarsu Yaya Aminu itace ta zama uwardakin Mamanmu kuma uwa a gare ta.

Mamanmu ta jima bata haihu ba. Hankalin Babanmu ya tashi don ganin yadda 'kaninsa Sule daga yin auransa har

"ya haihu. Kun san dai zama irin na Malam bahaushe. Babanmu ya fara wasu dabi'u. Ya canza gabad'aya. Gashi dai bashi da wani karfi kullum da 'kyar suke kai labari amma a hakan ya fara fafutukar kara auran wata bazawara. Ashe a lokacin Mamanmu tana da ciki ba ta sani ba, Shima bai sani ba. Tsabar tashin hankalin da take ciki ya gigitata ta kasa gane halin da take ciki. Ita macece mai bala'in kishi. Dalilin da ya sanya ma kenan ta figale ta lalace koyaushe ita da mijinta babu zaman lafiya. Shi kuma a lokacin idonsa ya rufe da son haihuwa."

Sai ta tattara kayanta ta gudu gidan Gwaggo da kudirin ba zata koma ba ta gama auran gabad'aya. Ita ba zata zauna

da kishiya ba. Gwaggo ta dinga rarrashinta Amma fafur ta ce ba zata koma ba.

Shi kuma Babanmu kamar sammatace a lokacin baya ganin kowa da mutunci sai Ummansu Hadiza. Domin Iya

mahaifiyarsa ma ta rasa gane kansa. Ta je gidan Gwaggwo akan Mamanmu ta koma dakinta. Gwaggo ta ce idan mijin yana buk'atar cigaba da zama da ita ya zo a samu sasanci.

"Ashe Baba Sule ne yake zuga shi akan kada ya je ya rabu ma da auran Mamanmu gabad'aya tana da farar kafa ba zai ta'ba cigaba ba. Auran Murja wato Ummansu Hadiza shine alheri a tare dashi tunda yayar matarsa ce, kuma gidansu akwai arziki na dukiya da kuma na haihuwa."

Babanmu ya yarda da maganar d'an'uwansa. Ya jingine Mamanmu a gidan Gwaggwo ita ba mai aure ba ita ba mara aure ba.

Lokacin da Gwaggo take yun'kurin sanar da su Dada halin da ake ciki a lokacin Mamanmu ta dinga wani irin ciwon kafa babu tafiya sai rarrafe.

Gwaggo ta aika aka sanar da Babanmu halin da ake ciki. Ya ki zuwa tunda a lokacin ma har an d'aura aure ya tare da matarsa a daya daga d'akunan dake cikin gidan.

"Gwaggo ba miji ne da ita ba, ya rasu shekaru kusan biyar kuma ya bar mata marayu hud'u itace take d'awainiya dasu a lokacin inda Allah Ya rufa asiri tana 'Yan sana'oi na hannu a lokacin shiyasa asirinta yake a rufe. Haka ta yi ta jigila da Mamanmu asibiti akayi gwaje-gwaje likita ya tabbatar da ciki na wata shida kuma har ya juya shine sakamakon ciwon kafafun da take yi."

Ba a mamaki da ikon Allah amma lamarin ya bawa kowa mamaki. Gwaggo ta sanya aka kira babamu a karo na biyu yaki zuwa. Sai ta shirya ta nufi shagonsa anan ta same shi da maganar ta kuma nuna masa sakamakon a rubuce.

Ya tsorota sosai kuma ya yi mamaki da ikon Allah jikinsa ya mutu ya gaza had'a ido da Gwaggo ya dinga kame-kame Yana ko'karin kare kansa. Gwaggo ta ce to tunda haihuwa ce matsalar sai ka zo ka d'auki matarka ka kuma ji tsoron Allah ka yi adalci da ni da kai duka amana aka ba mu. Ta kamo hanyar gida ta bar shi da alhini.

Baba Sule ya so ya zuga shi domin ya firje ya'ki amincewa da cikin akan ba nasa ba ne. Babanmu ya ki yarda da shawararsa saboda shi yafi kowa sanin yadda ya sami matarsa.

To ashe haihuwar ra'kuma daga babamu ne. Domin itama Ummansu Hadiza duk da take bazawara kuma ta haihu a

"wani wuri ba daga shigowarta ta haihu ba sai da Mamanmu ta haifi anti Yagana da shekara biyar tukkuna Ummansu Hadiza ta samu cikin d'anta na fari, kuma cikin ikon Allah da ya ta haife shi kwana biyu Allah Ya kar'bi abinsa. Ta dinga kuka tana cewa Mamanmu ce ta 'kona shi da ruwan zafi tunda a lokacin da ya rasu Mamanmu ba ta jima da yi masa wanka ba."

Dama zaman doya da manja suke yi. Mamanmu tana dannewa ne a matsayinta na Uwargida. Kada ace ita ce bata

k'aunar zaman lafiya. Amma dai duk da haka watarana idan Ummansu Hadiza ta kai ta bango fitowa take yi su yi ta cacar baki. Tana da ha'kuri a wasu lukutan. Amma ba ta son raini. Shiyasa anti Yagana take fad'in halinmu daya da ita na rashin san wargi.

Kusan lokaci daya aka samu cikinmu ni da Hadiza a yadda Ummansu Hadizan take ba mu labari tare suka dinga

laulayi har Allah ya kawo lokacin haihuwar tazarata da Hadiza ta kwana tara ce. Ita aka riga haihuwa sai ni. A lokacin

ita an yi mata hakika da tinkiya katuwa. Ni kuwa Babanmu ya ce bashi da kudi sai dai Mamamu tayi ha'kuri tunda ya

yi mata na fari.

"Mamanmu ta dinga kuka tana fad'in ba ta yarda ba ai 'yar sunna ce, yadda aka yankawa kishiyarta tinkiya itama sai an yanka mata. Shi kuma ya ce Ai ba dole ba ne, shi dai ya rad'awa 'yarsa suna Amina. Kamar yadda ya rad'awa 'yarsa Hadiza."

Can gidansu Mamanmu da suka ji labari abin bai yi musu dadi ba ko kad'an. Da yake Dada tana kiwon akoyiyi sai tasa aka yanka guda daya. Aka soye tsaf da zasu zo duba ni suka kawo mata da sauran abin buk'ata.

"Dukda haka abin bai saki Mamanmu ba, domin bambamci ko a kayan barka sai da Babanmu ya nuna na Hadiza sun fi yawa ni kuma nawa kad'an. Da ta yi magana ya ce ai ita ya yi mata ba fari."

Wannan abin ya dinga haddasa rikici a gidan. Babanmu daga ya d'auko hanyar gyara idan ya gane kuskuransa sai Baba Sule ya rusa. Ya d'ora shi a wata hanya ta daban

*1k on talgram via 0542382124..Binta Umar gtbank*

*07084653262*

"[11/20, 1:17 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!*"

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE *

*M.W.A*

*TALLAH!*

Albishirinku mata 'Yan gayu yan gwalisa kuyi maza kugar zayo shagon (Aysha/Addah beauty saloon and spa).

"Shin kintaba zuwa ingancaccen saloon din Aysha/Addah, idan baki taba zuwa ba kiyi maza kar a barki a baya domin sun qware a wajen aikinsu Wanda suke services dinsu cikin sauki tare da annasuwa"

Suna wanke kai(wash and set) suna wanke qafa(pedicure)

And sunayin steaming iri iri suna saida (supplements)suna kitso dama duk wani abu daku so Wanda akewa mace ta amsa sunanta mace yar qwalisa

"Address dinsu nanan a Federal low-cost opposite open University gombe state Ko kuma ku tuntune mu a wannan number kamar haka,"

08037925676

Or 08167764242

Whatsapp ko kuma Call we r available 24/7..

*@Arewa books*

*Bintuumarabbale.*

*free pege*

*11*

Sanyin halin Babanmu shine ya sanya Baba Sule yake yi masa kutse a cikin duk al'amuransa . Kwata-kwata Allah bai had'a jininsa da Mamanmu ba tunda ta zo gidan gaisuwar kirki ba ta had'a su ba. A wasu lukutan ma sai ya zo ya yi abubuwansa ya fita bai kulata ba kuma tana a matsayin matarsa d'an'uwansa ciki daya sai dai ita take ture komai ta gaishe shi. Idan kuma 'yan miskilancin suna kusa da ita kuma sai ta share shi har ya gama abinda ya kawo shi gidan ya tafi yana habaice habaice sai ka ce wani mace.

"To irin wad'annan matsaltsalun su Mamanmu ta dinga ajiyewa a ranta har ya haddasa mata ciwon zuciya wanda shi ya zama ajalinta duka ba a ankara ba, ta dinga ciwo a tsaitsaye har sai da ta fara kumburi tukkuna Baba ya farga suka nufi asibiti likita ya tabbatar da cewa zuciyarta ce ta ta'bu. Gwaggo ta shiga rudu sosài don har Mamanmu ta ma ta fita dauriya, ita ta dinga tausarta. A lokacin shi ma babamu ya tsorota sosai ya mayar da hankali wurin nemo mata magani na gida dana asibiti. Ya nemi alfarmar gwaggo akan kada ta sanar da gidansu halin da ake ciki."

Kulawar da take dan samu dalilin ciwon sai Ummansu Hadiza ta sanya kishi a ciki. Itama koyaushe sai ta kirkiri ciwo ta kwanta tace bata da lafiya. Haka babamu

Please Login or Register in order to submit comment