You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wad'anda nake ajiyewa suka fita tare da Yusi din. Can wurin anti Maimuna suka nufa cikin nishadi."

"Da yamma likis ina kwance gajiya ta kayar da ni, ina ta lissafin abubuwan da zan saya dangane da bud'e shagunan dinkin da zanyi. Anti Maimuna ta shigo a kid'ime tana kiran sunana."

"Na tashi zaune cikin tashin hankali don na d'auka mutuwa aka yi, ko maigidan na mu ne ya samu matsala. Ta ce."" Yarinyar nan Ihsan akayi wa fyad'e."""

"Gabana ya buga da karfin gaske na ce."" Kada dai ki ce mini yar nan makota da take shigowa wasa wurin yara."" Ta ce."" Itafa, yanzu nan yara suka shigo suna fad'a."""

"Na dinga nanata Innalillahi ina fad'in"" Yarinya 'yar shekara bakwai, me za a samu a tare da ita, amma ya kamata ayi binkice akan wanda ya aikata wannan mummunan lamari."""

"Anti Maimuna za ta yi magana kenan. Uwar yarinyar ta shigo tana kuka da yarinyar a hannunta tana cewa."" Ai tace Yusi ne kullum yake cire mata wando."""

"Cike da d'imuwa na ce."" Yusi kuma? baiwar Allah wace irin magana ce wannan? Yusi me ya sani da har zai aikata haka."""

"Anti Jamila da shigowarta kenan ta bude baki tana cewa."" Ai ba a shedar d'an yau, yo shekararsa sha d'aya fa, ai daf yake da balaga, yaron da aka haifa yau ma gabansa yana tashi balle saurayin da yayi wannan shekaru."""

"Na mi'ke tsaye da sauri ina fad'in."" Karya kike yi munafuka yarona ba zai ta'ba aikata haka ba, a dai binkita a cikin"

"yaranku."""

"Uwar yarinyar tana kuka take fad'in."" Wallahi ba zan yarda ba fa."""

"Na dubeta tare da cewa."" Kada Allah Ya sa ki yarda din, ki yi duk abinda za ki yi."" Ta juya ta fita a fusace."

Jamila ta bi bayanta tana kara zugata.

"Na zube a kasan wurin cikin tashin hankali. Anti Maimuna ta dafa kafad'ata tana cewa."" Amina a bi komai a hankali, tabbas na sheda Yusi ba zai yi wannan sakarcin ba. Dole dai a tsananta da bincike. A cikin gidan nan fa akayi can koridon da yake bayan dakina."

"Na dubeta hawaye na ko'karin kwace mini na ce."" Anti Maimuna lamarin nan ba na zama ba ne, ba yadda za a yi na yi lako-lako a d'orawa yaron nan abinda bai aikata ba."""

"Ta ce."" Ni ma ban ce ki yadda ba, amma dai abi a hankali."" Ban ce mata komai ba har ta fita."

Kamalu ya shigo yana nishi kafafun wandonsa duk a tattare. Sai gumi yake yi.

"Na dube shi zan yi magana ya katse ni Yana fad'in."" Kokawa muka yi da su Turmuzi da Shahid Yayan Ihisan din, sun kama Yusi suna ta duka, sun d'auko almakashi wai zasu yanke masa wurin fitsari."""

"Cikin kad'uwa da d'imuwa na ce."" Ina Yusi din, don sai a lokacin ma na tuna da cewa ban ga gilmawarsa ba tunda lamarin ya fasu. Kafin yayi magana Salima ta shigo tana kuka."

"""Anti 'Yan-sanda ne a waje suka ri'ke Yusi gashi can a hannunsu. Suna neman Babanmu. yanzu Mamanmu ta kira shi a waya ya ce gashinan zuwa."

Hijabina nasa da sauri na kama hanyar fita yaran suka rufo mini baya.

Kofar gidan ta cika da mutane yara da manya. ga Yusi a hannun daya daga cikin jami'in yana kuka. Yayin da wasu ke ta tambayar abinda yake faruwa.

"Na iske wurin da yarona yake kai tsaye na ce."" Sake shi domin ba shine ya aikata abinda ake zargi ba."""

"Jami'in ya ce."" Ai magana ta kare tunda yarinya ta ce shine yake cire mata wando idan suna wasa, kuma kowa ya tabbatar da cewa shi din abokin wasanta ne, ke kin san haka, sannan iyayen yarinyar ma sun sani."""

"Wani zazzafan hawaye ya kwaranyo mini na ce."" Wallahi ba shi ba ne, yaron ma guda nawa yake da zai aikata hakan, ku dai kara binkice, maraya ne, Allah ne gatansa, ni ce gatansa."""

"Ya ce."" Ai marayun sun fi iyashege, saboda haka ba zamu sake shi ba sai mun gama gudanar da bincike."""

"Yusi ya rike gefan hijabina yana kuka, yana cewa."" Mama wai me na yi?"" Shi bai ma san akan me aka ri'ke shi ba."" Jami'in ya fizgeshi hannunsa daga jikina ya kwada masa mari mai tsanani!"

"""Tambaya kake yi me ka yi ko? za ka ci ubanka idan muka je station."" Murya Kamalu na ji da k'arfi yana ce wa."" Kai ma ubanka, shegu mugwaye sai Allah Ya saka masa."" Sai kuka ya k'wace masa."

"Wurin ya cika da hayaniya! wasu na fad'in."" Dama ai yaron bashi da kunya, dan iska b'arawo ne shima, wasu kuma sai jajantawa suke yi. Yayin da wani jami'i daga cikinsu ya yi kukan kura zai cafko shi. Ganin haka ya sanya ya fafara da gudu ya yi gabas!"

"kaina na ya dinga bugawa kamar ana kwala mini guduma! Na dinga jin Hajijiya da kyar anti Maimuna ta zo ta janye ni daga wurin, rashin makama yasa na bi bayanta zuwa cikin gida tana rarrashinta tare da cewa na kwantar da hankalina inshallah gaskiya zata bayyana."

"Na zube kasa cikin sanyi jiki na ce."" Anti Maimuna ya zan yi ne?"" Ta ce."" Addu'a za ki yi itace magani."""

"Da karfin gaske na furta."" Inna lillahi wa'ina ilaihi raji'un!"""

Tunda na dingi nanata Innalillahi na ji sauki yana saukar mini. Can kira ya shigo wayata dake uwardaki. Kafin na yi wani yun'kuri Salima ta shiga d'akin ta dauko mini da sauri ta ba ni. Hamusu ne ya kira. Na daga don ban yi mamaki ba tunda zan ce irin wannan sai ka tsince shi a wurin da baka ta'ba tsammani ba.

"Cikin damuwa yake tambayata labarin da ya samu gaskiya ne. Na ce."" Kai wanene yake gaya maka?"" Kai tsaye ya ce."" Kamalu ne."" Na girgiza kai, ashe yaron can ya nufa lokacin da ya yi wa 'yansanda rashin kunya. Na ce."" Haka dai iyayen yarinyar suke zargi Hamusu Amma a duniyar nan me Yusi ya sani da zai yi haka."""

"Ya ce."" Wane police station suka tafi dashi?"""

"""Ka bari kawai ba sai ka je ba, Babansu Salima Yana can, in sha Allahu abun ba zai yi tsanani ba gaskiya zata bayyana."

"Kada ka gayawa Gwaggwo."""

"""Ba zan gaya mata ba in sha Allahu Amma anti Amina ki bari na je don Allah, kada duniya ta zage mu, wannan sharri"

"ne?"""

"Na goge hawayen dake zuba a kumatuna na ce."" Hamusu muddin aka binkita lamarin ba Babu gaskiya bisa zargin da suke yi wa yarona wallahi sai na d'aukaka kara ba zan yadda ba."""

"""Da damuwa mai yawa a tare dashi ya ce."" Mu ma ba zamu yadda ba anti Amina, kawai ki gaya mini station din, zan"

"je a yi komai a gabana."""

"Na ce."" Ka bari zan kira ka zuwa an jima, don a halin yanzu ni ma ban san station ba, amma na gaya maka maigidan"

"Yana can zamu yi waya idan an jima."""

"Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefana. Na kalli anti Maimuna tare da furta."" Ba zan yadda ba wallahi sai na d'auki"

"mataki akan wannan sharrin da aka yi mini."""

"Shiru ta yi ba tace komai ba, gabad'aya duk jikinta ya yi sanyi, yanayinta sai ya nuna kamar akwai abinda ke damunta"

"ko take 'boyewa, shine dalilin da yasa take ta cewa da ni na yi hakuri na bar maganar. Ni Kuma ba ta san yadda nake ji a cikin raina ba."

Muna zaune ni da ita da yara cikin alhini maigidan ya shigo da Yusi a hannunsa. Gabad'aya muka zuba masa ido. Ni

"dai ganin yarona kalau, ya sanya na dinga godewa Allah, Amma yanayin mijin na mu shi ya fi d'aukar hankalina. Ya zauna kan kujera kamar mara laka. Ya dubi yaran tare da basu umarnin fita, Salima da yan'uwanta suka fice gabad'aya, Yusi din ma ya bi bayansu."

"Anti Maimuna ta ce."" Da alama an samu maslaha sai dai yadda na ganka a sa'bule kamar akwai matsala."""

"Ya ce."" Matsala babba ma kuwa."" Sai ruwan hawaye ya ciko kwarmin idonsa. Na ce."" An gano wanda ya aikata kenan?"""

"Kai tsaye Ya ce."" Turmuzi ne!"""

"Gabad'aya muka shiga gigita! hawayen da ya ciko kwarmin idonsa ya zuba a kumatunsa. Ya nisa kafin ya yakice kuttun takaicin da yake sasakarsa ya ce."" Yaron nan Yusi bashi alhaki kuma dukan da jami'an nan suka yi masa sai Allah Ya saka masa, abinda ya faru shine; Wato rud'u da firgice da kuma tsoratarwa ya sanya yarinyar nan fad'in Yusi ne yake cire mata wando. Amma a zahiri Turmuzi ne, tun farkon fara shigowarta wasa gidan nan yake janta bayan korodo yana cire mata wando ya bata alawa. Mahaifin yarinyar shi ya yi mata wayo da daburu ya lallabata kan ta gaya masa wanene tana kuka tace Turmuzi ne ya ce duk wanda ta gayawa sai ya kasheta. Ya kunna mata wani film yana nuna mata irin kisan da zai yi mata da wuka."

"A ranar da ya cire mata wandon ya danneta."" Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! sai kawai ya fashe da kuka yana girgiza kansa, tabbacin abin yana susar zuciyarsa."

"""Yaushe Turmuzi ya lalace haka, yaushe ya balaga da zai iya haikewa yarinyar mutane. Shekara sha hudu me ya sani, a cikin gidana, ni ban kasance mazinaci ba, Allah kada ka jarrabe ni."""

"Babban mutum Yana kuka tukuru!"""

"Gabad'aya jikinmu ya yi sanyi. Kudirin da yi na d'aukar fansa akan haka na janye ganin irin gigitar da ya shiga. Anti Maimuna ta ce."" Yanzu a wace matsayar aka tsaya?"""

"Yasa hankice ya share fuskarsa."" Maganar ta mutu, mahaifin yarinyar ya janye karar da ya yi. Yanzu sun kaita asibiti an duba wurin raunin kad'an ne, yarinyar ta yi bayani bayan gabansa da yake sa mata har hannu yana sa mata a wurin."""

Na sunkuyar da kaina k'asa kawai sai wasu hawaye masu rad'adi suka goce mini suka dinga fafara gudu a kumatuna. Yaushe rabon da na yi kuka irin wannan har na manta. Ba komai ne yake daga mini hankali ba yadda tarbiyar yaran k'ananu take nema ta gurbace. Wai kamar Turmuzi shekara sha hudu shine da aikata wannan lamari.

"Sai na ji anti Maimuna tana fad'in."" Ban yi mamaki ba, dalili wayar da take hannun yaron babu abinda ba zata janyo ba. Tuntuni na gayawa Jamila cewa ta kwace wayar bata da amfani tunda ba aikin karatu yake yi da ita kallace kallace yake yi da, ya yaudareta ne kawai ya ce ta siya masa zata dinga taimaka masa bangaran karatunsa. A gabana akayi hakan, kuma ta saya masa. Na tabbata idan ka bincike wayar ba za a rasa fina finan banza ba, domin wasu lokotun idan ya shigo wurina Yana kallo baya barin kowa ya zo wurin da yake. Ya kan rage murya ko ya sanya airpix a kunnansa."""

"Fad'a sosai ya shiga yi, domin shi duk abinda ake yi bai san yaron yana da waya ba, uwar bata gaya masa ba a"

"lokacin da zata saya masa sai lefin ma yake ko'karin shafar anti Maimuna. Ana haka Jamila ta shigo. Ganinmu a hargitse ya sanya ta dan yi sanyi tana fad'in."" Yanzu nan na ga yaron nan Yusi nace ashe an samu maslaha sun ba dashi kenan."""

"Lokacin da take maganar hankalinta yana kan maigidan. Aikuwa tana rufe baki ya fara bata amsa, ya warwarewa mata zare da a bawa, har da barazanar saki muddin ta cigaba da yin abu ba tare da saninsa ba, domin ya tabbata wayar ta taka muhimiyar rawa wurin lalacewar yaron."

"Bata yarda ba don kuka ta fashe dashi tana fad'in an yi wa yaronta 'kage, wallahi ba zata yarda ba sai ta d'auki mataki. Ya kuwace sai dai ta d'auka a gidan ubanta domin idan tace zata yi wani yun'kuri na fitar da maganar sai ya sake ta."

Jin haka yasa ta fita tana kuka. Ya tashi ya bi bayanta. Can muka dinga jin hayaniya a wurinta da kururuwar Turmuzi Gabad'aya muka nufi wurin. Ya samu narkeken itace yana dukansa dashi. Duk ya fasa masa hanci. Wahala ta sanya yaron fad'in shine ya aikata amma ba zai kara ba. Da kyar na kwace itacen hannunsa ita kuma anti Maimuna ta rirri'ke shi. Lokacin ne Jamilar ta dadi a wurin tana wani irin abu wanda ya tabbatar mana da cewa aljanune suka buge ta. Maigidan bai tsaya ba ya kama hanya ya fice da wayar da ya kar'ba a hannun yaron. Ni da anti Maimuna muka tsaya a kanta da tofi da addu'a har suka saketa bacci ya d'auketa.

"Lokacin da muka fito na kalli Anti Maimuna cikin sanyin jiki na ce."" Dama anti Jamila tana da aljan u?"

"Ta ce."" Tana dasu amma ba koyaushe suke tashi ba, sun fi zuwa yayin murna ko bakinciki idan ta haihu ma haka suke tashi akai akai har sai an yi suna."""

"Na girgiza kai ina mamaki, tabbas hakan zata iya faruwa idan aka yi duba da yanayin halayyarta. A hargitse take koyaushe kuma bata da yarda gata da mugun izza da girman kan tsiya."

Sai bayan sallar isha'i tukkuna hankalina ya daidaita.

"Yusi ya shigo ya zauna kusa dani jikinsa duk a sa'bule. Na dube shi a tsanake na ce."" Ka je massalacin ko?"""

"Ya daga kansa alamun ""E, sai ya ce."" Mama ina Yayana yake? yanzu ina fitowa daga massalaci na ji wasu suna cewa 'yansanda sun kama shi saboda ya zage su."""

"Na ce."" Yana can gidan Gwaggwo k'arya suke yi yanzu nan zan kira Hamusu a waya ya kawo shi gida."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin jikinsa. Na dau'ki wayata da sauri number Hamusu na nema. Ya daga muka gaisa Yana tambayata ya ake ciki.

"Na ce."" Hamusu komai ya zo da sau'ki ga Yusi a gabana tun d'azu suka ba dashi saboda gaskiya ta bayyana kanta."" Ajiyar zuciya ya sauke yana godewa Allah kafin ya cigaba da cewa."" Yanzu dai an kama wanda ya aikata ko?"" Na ce."" E, ana kan binkice dai."""

"Ba na so na fad'a masa yaron gidan nan ne, yin hakan kamar tozarta maigidan ne, kuma na ji dadi sosai da tsayuwar da ya yi akan sha'anin har gaskiya ta bayyana."

"Na ce."" Don Allah tunda kana da abin hawa ka kawo mini Kamalu akan babur d'inka kada ka bari ya taho da kansa,"

"dama akwai maganar da nake so mu tattauna dangane da bud'e shagunan da zan yi."""

"Ya ce."" A a, Kamalu ai baya nan, tun lokacin da ya zo ya gaya mini abinda yake faruwa ban sake ganinsa ba, bai dawo gidan ba ne?"""

"Cikin faduwar gaba na ce."" Bai dawo ba wallahi, amma don Allah yi maza ka duba gidanmu ko yana can."" Da sauri ya kashe wayar."

"Yusi ya dube ni."" Mama ya akayi, ina yayan nawa?"""

"Cike da fargaba na ce."" Yana can gidanmu, yanzu Kawunku zai je ya d'auko shi."""

Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu. Ina nan zaune ina sakawa da kwancewa. Hamusu ya kira ni yana tabbatar mini da cewa Kamalu baya can gidanmu.

"Na ce."" Ka ga Saminu a gidan kuma?"""

"Ya ce."" Kwarai kuwa shine ma ya tabbatar mini da cewa baya nan, don koda sallah bai je musu ziyara ba."

"Jikina ya shika, sai fargaba ta yi mini sallama, da ban kawo komai ba a zuciyata, amma yanzu babu irin tunanin da ba na yi. Na ce."" Hamusu bari na yi magana da maigidana yanzu zan kira ka zuwa an jima."

"Na kashe wayar da sauri na tashi na fita zuwa d'akin maigidan tunda ba girkina ba ne, Yusi ya biyo bayana da sauri yana kuka. "

*Gudun aure 1k on talgram via 0542382124. Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari katin Airtel a kankare a

tura mini shaida ta wannan lambar*

*07084653262*

*TALLAH*



*DA MAGANI A GONAR YARO!!*

*08089965176*

*07084653262*

"*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*"

*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*

*07084653262 ko*

*08089965176*

*SIYAN NAGARI!!!!!!*

"*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* [11/29, 12:50 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!!*"

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE *

*M.W.A.*

*@arewabooks*

*Bintuumarabbale*

*Last free peges*

*20*

Abinci yake ci a lokacin dana shiga d'akin yana tare da anti Maimuna da alama maganar dai suke kara tattaunawa domin cikin alhini na same su. Shigowarmu d'akin ni da Yusi ya sanya suka bi mu da kallo bakidaya

"Na ce."" Yanzu nan Hamusu ya ke gaya mini Kamalu baya can wurinsu. Tun fa da lamarin nan ya faru ya bar unguwar ni wallahi na d'auka Yana can gidan kakarsu ashe Yana gayawa kanin uban ya fita ba a sake ganinsa ba, duk inda ya kamata a duba mini Hamusu ya duba ba a ganshi ba."""

Hawaye ya zubo a kumatuna na sanya hannu na goge gabad'aya jikina Yayi sanyi sai nake ganin kamar akwai abinda yake shirin faruwa da yaron.

Anti Maimuna ta shiga kwantar mini da hankali. Shi Kuma maigidan ya tsame hannunsa daga abincin ya d'auki wayarsa muna zaune ya kira station domin tambayarsu tunda ya ji labarin rashin kunyar da yaron Ya yi. Gabad'aya mun yi tunanin ko sun kama shi.

Suka tabbatar masa da cewa baya hannunsu. Hankalina ya sake tashi. Gidajen redio uku ya kira ya bada cigiyarsa duk ya Basu bayanai akansa. Sannan ya waiwayo gareni ya shiga yi mini nasiha da kawo mini misalai na kaddarori na rayuwa.

"A wannan dare na yaba masa kwarai da gaske dashi da anti Maimuna sun yi mini kara, sai kusan sha biyu da rabi"

tukkuna na yi musu sallama na koma wurina jikina duk Yayi tubus. Yusi kuwa ya ci kuka ya koshi sai ajiyar zuciya yake yi.

Yadda na ga rana haka naga dare.

Ina idar da sallar asubahi na kira Hamusu domin tambayarsa ko ya samu wani labari akan yaron. Ya ce mini babu wani labari shima tun jiyan yake zaga gidajen masu unguwani. Da station da suke area ko an kai shi can.

zuciyata ta dinga raya mini munanan abubuwa Ina ta tunanin ko wane hali yake ciki a yanzu. Fatana dai ace yana hannu nagari.

Kwana uku babu wani labari babu Kamalu babu dalilinsa. A lokacin na gama gigicewa. Komai na rayuwata ya tsaya

cak! Na kira anti Yagana na sanar mata da halin da nake ciki. Sannan na bawa Ya Falmata ha'kuri domin halin da nake ciki ba zai barni yin komai ba.

Tsangayu uku na bada sadaka domin a yi mini ro'kon Allah akan lamarin Allah Ya bayyana mini yarona ko da rai ko a mace.

"Sahura zuwanta biyu ta ce mini muje gidan wani malami da rigar Kamalu zai yi aiki akai idan ma yana raye zai gaya mana, idan kuma baya raye nan ma zai gaya mana."

"Na ce ba zan iya zuwa ba, tunda na sanya a yi mini ro'kon Allah shikkenan. Zuwa lokacin na saduda burina ko gawarsa ce na ga ni."

****

"A ranar da Kamalu ya cika sati da 'bata Hamusu ya kira ni a waya da rana gatse gatse. Ina d'agawa ya ce."" Anti an samu labarin Kamalu sai dai lamarin ba dadin ji wallahi."""

"Na ce."" Hamusu gaya mini idan mutuwa ya yi duk inda yake zamuje a ba ni gawarsa ko zan rasa komai."""

"Ya ce."" Yana nan a raye sai dai yana hannun hukuma tare da wasu matasan Yara 'yan nan gaba damu, wata'kila ma zaki san gidan Alhaji mato."""

"Na ce."" Na san gidan Hamusu mai ya had'a Kamalu da yaran gidan nan Kuma?"""

"Ya ce."" Neman mafaka ya yi dasu, ashe bayan ya zo ya gaya mini abinda ya faru, sai ya hadu da daya daga cikinsu yake gaya masa zai kwana a gidansu. Da ya tambaye shi dalili sai ya ce 'yansanda ya zaga shi kuma Yana jin tsoron komawa gida a kamshi."

"Shine da yaron mai suna Kamsusi ya bashi mafaka. A kuma washe garin ranar ya gudu dashi legos. Suka shiga wani kamfani sukayi sata aka kuma cafke su har da Kamalu. Inda nake jin dad'i kamfanin da suka shiga yana daya daga cikin mallakar Alhaji Tajo, muna sa ran yaran za su samu sassauci."

"Na ce."" To Hamusu yanzu ya kake ganin za a yi? kana ganin zasu ba mu yaron nan cikin sau'ki idan an yi duba da irin yaran da suka ja shi, hukuma ba zata aminta da korafinmu ba, dole tunda tare suka aikata barnar a hukunta su."

"Ya ce."" Ai Kamalu shine k'arami a cikinsu. Bai balaga ba har yanzu shekara sha hud'u, za a samu rangwami. Sauran"

"kuwa duk sun haura ashirin. kwai dai hankalina yana tashi ne idan na tuna ta'adacin da yaran suka jima suna yi. Dama an ce hukuma neman su take ruwa a jallo, tunda basu jima da cinna wuta a wani a shago ba bayan sun kwashi kudi masu yawan gaske."

"Jiki a mace na ce."" Hamusu duk yadda Allah Ya yi daidai ne. Zan yi magana da maigidana yanzu zuwa an jima"

"abinda muka tattauna zan sanar da kai in sha Allahu rabbi."""

"Ya ce."" To shikkenan anti ni ma ta nan din zan cigaba da bincike akan lamarin in sha Allahu za mu sau'ki."""

Muna gama waya da Hamsu na kira maigidan na gaya masa. Sai ya ce ai ya samu labari don har gidajen jaridu sun

buga da kafafen da zumunta. Shi ma a fece book ya gani. Ya kwantar mini da hankali kafin ya dawo har ya na fad'in lamarin zai zo da sauki tunda mamallakin kamfanin mutumin kirki ne.

Tun kafin Azimi rabona da sa data a wayata saboda ba ni ma da sukunin shiga media kallace kallace dalilin ayyukan da suke gabana.

Ashe lamarin har ya yi girman da gidajen jaridu ke watsa labarin. Ko da yake mutumin babba ne a kasar hakan ba zai zama abin mamaki ba tunda motsi kad'an zai yi media zata d'auka balle wani abu da ya shafe shi. Yanzu kenan hotonan Kamalu suna can suna yawo a duniya kowa yana fad'in albarkacin bakinsa.

"Da yamma Sahura ta kira ni a waya tana jajanta mini. Itama dai a fecebook din ta gani, maganar dai guda daya ce na"

"kwantar da hankalina

Please Login or Register in order to submit comment