You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yaran, fatan na sameku lafiya."""

"Ta amsa a sake tana cewa."" Lafiya Lou ki ka same mu, yanzu nan dama Babansu da ya shigo yake gaya mini za ki zo mu gaisa."""

"Wani d'an matashin yaro da tun zamana a wurin na ji ana kiransa da Turmuzi Ya ce."" Mama itace amaryar Babanmu ne?"""

"Ta ce."" E, ita ce"" Shiru ya yi bai ce komai ba, sai kuma can ya tashi ya fita da sauri. Sauran yaran kuma suka cigaba da sha'aninsu babu wanda ya gaisheni a cikinsu."

"Na cika da mamaki sosai, kuma ita Anti Maimuna haka sunanta yake ba ta tsawatar musu ba."

"Minti kusan goma ina zaune muna dan ta'ba hira. Na lura tana da sakin fuska, kuma dai a haka kamar babu wani kulli a zuciyarta. Tana gaya mini yadda tsare-tsaren gidan yake. Sai dai yadda na fahimta tana da son jiki da kazanta a jikinta da falonta na lura da hakan, tafin 'kafafunta duk sun yi daud'a. Kuma kayan bacci ne a jikinta masu ruwan haske,"

"Amma sun dafe, gashi dai safiya ce, amma kusancina da ita hancina yana ta sha'ko mini warin hammatarta, dukda hallita ne, amma dai akwai kazanta a sha'aninta, tunda mutum ya san yana da ki'bar da za ta ajiye masa gumi sai ya bi matakan gyarawa."

"Shigowa ta yi babu sallama tana cewa."" Tun d'azu Turmuzi ya je yana gaya mini ga amarya nan a sashenki, anti Maimuna ai sai ki ce na zo ni ma a zauna da ni, a kalla fa kun fi minti ashirin a tare, ni ba fa na son haka."""

"Cikin kausasa harshe take yin maganar. Ita kuma sai ta fara dariya tana cewa."" Yanzu nan nake cewa Salima ta zo ta rakata wurinki ku gaisa, ai na yi tsammanin bacci ki ke yi ne."""

"Ta zauna tana d'an kallona kafin ta ce."" Ba bacci nake yi ba, kuma da ki ke cewa Salima ta rakota wurina makauniya ce ita, ai babu wanda ya yi mata jagora ta shigo wurinki, haka Turmuzi ya gaya mini."

"Anti Sakina ta ce."" Ke fa matsalata dake Jamila gajan ha'kuri wallahi, wannan ba a bin damuwa ba ne fa."""

"""Gajan ha'kuri kamar yaya Anti Maimuna, gaskiya na fada fa, kin san ni komai a bud'e nake yinsa."""

"Na ce.""Haba baiwar Allah, kya bari mu gaisa ko? Ai zan shigo har wurin naki dama bisa bin umarin maigidan, ina"

"fata dai na sameku lafiya."""

"""Lafiyarmu lau wallahi, ya hidima fatan an tashi taro lafiya."""

"""Alhamdulillahi, na shigo cikinku da kyakykyawar zuciya, ina fatan zaku karbe ni hannu biyu."" Ta ce."" In sha Allahu rabbi."""

"Falon ya yi shiru. Yaran duk sun zubo mana Ido. Sai na dube su a tsanake na ce.' Babu wanda ya gaishe ni a cikinku, kuma duk ku gaya mini sunayenku."" Da yar dariya na yi maganar."

"Sai suka fara rige-rigen gaisheni, kowa yana ko'karin gaya mini sunansa. Na dubu Anti Maimuna da fad'in."" Salima ce"

"babbarsu ko?"" Ta ce."" E, itace gata nan sai tsawon kafar tsiya."" Na ce."" Ai girman 'ya mace ba shi da wahala, daga zarar ka fara da mace sai girma ya kamaka."""

"Ta yi dariya tana cewa."" Wallahi hakane. """

"Anti Jamila tasha kunu bata tofa mana ba. Ni Kuma ina sane ban sanya maganata da ita ba, saboda karon farko na fahimci bata da hankali, sannan yadda take nuna gadara akan Uwargidan, tana gaya mata magana kausasa bayan ko banza ta girme mata, to ni ba zan d'auka ba, duk cikinmu babu yaro, ba na tsammanin itama ta ba ni wasu shekaru da yawa. Shiyasa tun bayan gaisuwar da muka yi da ita, ban 'kara tanka mata ba, daga karshe ma sai na tashi na yi musu sallama na koma wurina da tunanin yanayin zamantakewar da suke gudanarwa mara kangado."

"Ciki da falo ne wadatattu, kuma kayan katakon da ya zuba mini masu kyau ne da tsada da manyan labuleye. Harda"

tibi irin ta bango. Na yaba masa sosai domin d'akin nawa ya yi kyau k'warai ko na wata budurwar albarka. Matsalar dai kawai babu bandaki a d'akin duk suna can waje. Dakinsa ne kawai dashi. Kicin din ma na had'aka ne. Amma gidan akwai yalwa irin gini ne na wadata babu takura. Har da wurin saukar baki a cikin gidan

"Na d'an gyara abinda bai yi mini, na ware kwanukan da zan zuba a kwando, da fulasai, da duk abinda zan nema domin ba na tunanin zan kwashi kayana na kai kicin din gabad'aya, domin fitar da na yi d'azu, na hasashi akwai gyara sosai a tare dasu, gidan gabad'aya babu tsafta har kicin din, kudaje sai bi suke yi, ban sani ba ko suna da mai aiki oho. Na zauna ina hutuwa amma gabad'aya hankalina na kan yaran, mussaman Yusi jiya ya sharbi kuka lokacin da za mu taho sai wayo aka yi masa aka fita dashi daga gidan."

"Gwaggo wayarta ta lalace sai na nemi ta Hamusu dukda ba ni da tabbacin Yana gidan, amma dai ai garin yanzu ya waye."

"Muka gaisa Yana 'yar dariya yake cewa.""Amina Anya yau kin yi bacci arziki kuwa, na san hanalinki Yana kan yaran nan."""

"Ni ma cikin barkwanci na ce."" Ban yi ba gaskiya, ai shiyasa ma na gaza ha'kuri na ce bari na kira ka, na ji ya suka kwana."""

"Ya ce."" Suna nan lafiya lau, ga Yusi nan ya warware Yana ta wasansa. Shi kuma Kamalu gashi nan, Yana zubawa"

"Gwaggo ruwa."""

"Na ce."" To fara ba ni Gwaggon mu gaisa tukkuna."""

"Ya mika mata watar. Na ce."" Gwaggo ina kwana, Kun tashi lafiya?""."

"Cike da kulawa ta amsa tana cewa."" Ya kwanan bakunta Kuma."" Na ce."" Alhamdulillahi Gwaggo. Sai ta dora da cewa"

"."" Ai ana ta fad'in nagartar abokanan zamanki, an ce kansu a had'e yake ba su ta'ba fad'a ba, kema ki bi su a yadda ki ka gansu domin samun daidaito. Ubangiji Allah Ya sanya alheri."""

"Na ce."" Amin Ya Allah, ai kam babu lefi, akwai fahimta a tsakaninsu, in sha Allahu zan zauna dasu lafiya."" Ta ce.'""To Allah Ya kad'e fitina."""

"Hamusu Ya kar'bi wayar yana fad'in."" Fita zan yi anti Amina, ga Yusi ku gaisa, idan na dawo da yamma zan kira ki sai ku gaisa da Kamalu, don ya fita yanzu, na ce miki dama Yana zubawa Gwaggo ruwa, yau me ruwanta ne bai kawo mata ba."""

"Na ce."" To shikkenan bawa Yusi wayar."" Ya mika masa da zumud'i a tare dashi Yana dariya yake cewa."" Mama shine jiya ku ka yi mini wayo kuka gudu ko?"""

"Na sauke ajiyar zuciya a nutse na ce."" Babu gaisuwa sai korafi ko Yusi."" ""Yi hakuri Mama, ina kwana ya kuke?"""

"""Na ce."" Ina lafiya lau, zaka zauna a hannun Gwaggo ko?"" ""Um-um!"" Ya furta da sauri."""

"Na yi dariya tare da cewa."" Shikkenan zan zo na d'aukeku sati mai zuwa in sha Allahu."" Farincikinsa Ya tsananta ya"

"ce."" To daga yau zan fara lissafi Mama."" Na yi dariya tare da cewa."" Ba wa Baba Hamusu wayar zan yi magana dashi."""

"Yana kar'ba na ce."" Don Allah da yamma idan babu takurawa kai da Usaini ku kawo mini kekunan d'inkina mana,"

"akwai sauran kayan jama'a a hannuna. Maigidan Ya ce na ajiye aiki Hamusu, shiyasa gabad'aya yanzu hankalina ya karkarta wurin ganin na kafu anan din. Dukda na san da yawa wad'anda za su biyo nan din, amma ina so nan din ma a san ni akan sana'ata."""

"Ya ce.""Anti Amina dadina dake akwai himma, kina da zuciya da neman na kanki, Allah Ya dafa miki, in sha Allahu kuma daga na dawo daga kasuwa zan je can gidan naku na samu Usainin."""

"Na ce."" Shi ma na gaya masa Ya na jiranka."" Ya ce."" To shikkenan za mu zo in sha Allahu."""

Muka yi sallama na kashe wayar na ajiye. Ina sake nazarin yadda al'amurana za su kasance a sabuwar rayuwar da na

tsinci kaina a cikinta.

To cikin kwana uku kacal na fahimci yadda al'amuran suke gudana a gidan Alhaji Muntari. A kwai kusakurai masu

"girma da suka riga suka yi karfi a yanzu wanda idan an ce za a gyara su za a samu matsala babba, tunda tun fil'azal a haka suka gina gidan da kuma mijin nasu."

"Alhaji Muntari rayuwarsa yake gudanarwa irin ta bahaushe zalla, karin abin kuma iyakacinsa sakandire bai yi zurfin karatun boko ba, na addinin ma akwai matsala domin Yana tafka kusakurai a sha'aninsa, kuma yadda na lura dashi ba mutum ne mai so a yi masa gyara ba. Irin mutana nan ne da duk abinda suka yi daidai ne. Tun ranar da ya fara auratayya da ni, na fuskance dhi. Idan mun kammala yana kallona zan shiga bandakin da yake cikin dakinsa na tsarkake jikina, amma sai dai na fito na same shi Yana bacci tare da najasar a jikinsa. Abin takaici kuma da ban haushi baya tashi sallar asubahi. Har sai gari ya yi haske tukkuna zai yi sallah."

"Sun samu bambamci da Yaya Aminu ta wannan gefan, domin shi Abbansu Yusi akwai ibada. Ta inda dabi'arsu ta zo daya wurin mayatar yin jima'i, duk dare lokacin Yaya Aminu sai ya kwanta da ni, shiyasa da Allah Ya had'a ni da wannan din ban damu ba, tunda jikina ya riga ya saba da Hakan."

"Alhaji Muntari d'an sharholiya, aji dad'in duniya kawai. Addini bai dame shi ka'in da na'in ba. Ya yi ado da kwalliya ya ci abinci, sannan ya kwanta da mace, wannan shine abinda ya fi bawa muhimmanci. Gidansa babu yunwa da abinci, Yana kuma ko'karin tsarewa kowa mutumcinta. Sai dai 'keta da matan gidan suka sanya a zukatunsu. Abinci d'anye dai gashinan a store. To duk wadda take da girki idan zai fita zai bata dubu biyu kudin kayan miya kawai da markade, tunda Yana Aiko da nama ko kaji daga kasuwa."

"Ranar da na kar'bi girki, gabad'aya dubu biyun na karar da ita na yi komai a wadatace kamar yadda suke yi ba. Koda na dibi na maigidan da wanda zan ci sai na bar musu tukunyar domin ban san ya za a yi na raba.Na kira anti Maimuna ganin tana da sau'kin fahimta, na ce ta raba a hankali sai na koya."

"Sai suka fara hayaniya. Anti Jamila na fad'in."" Akan me, za ki kwashe miyar duk ki juye a kwanukan yaranki, haba anti Maimuna, akwai son zuciya fa."""

"Na yi shiru ina kallonsu da mamakin irin fitsarar da Jamila ke yi wa Anti Maimuna, ita kuma duk sai ta diririce,"

"hannunta Yana kyarma tana raba abincin take cewa"" Kowa za a zuba masa, Jamila ki kwantar da hankalinki."""

"Ta kalleni tana cewa."" Ke ma ai da ki ka yi girkin ke ya cancanta ki raba abincinki, tunda dai kin san gidan iyali ki ka shigo, mijinki ya gaya miki komai, to ba sai ki k'arasa ladanki ba."""

"Uffan ban ce mata ba, na danne zuciyata da take shirin danna mata zagi."

"Anti Maimuna ta ce."" Jamila, wai me ki ke nufi ne, na gaji fa da wannan iyashegen da ki ke yi mini, ki dinga yi mini tsawa, tunda Amina ta zo gidan nan, ki ke neman fitina, ina lefi don ta yi abincin ta ce mu raba, ai yaran mu ne gabad'aya. Kuma idan ta ce za ta yi rabon ba ta san ya za ta yi ba, komai sai a hankali. Amma kin zo kina ta yi mini rashin kunya, me ki ke nufi ne?"""

"""To, ai gani na yi, kin fito da son zuciyarki 'karara, idan ke za ki yi miyar ai ba za ki saki jiki ki yi kamar wannan ba,"

"kuma duk kin d'ibe kina zubawa a kwanukan yaranki, waccan ma da ki ka zuba a robar rufaida yogurt ta wacece?"""

"Cikin bacin rai na ce."" Wai ke don Allah menene haka? Ba fa girma da mutunci ba ne, ya za a yi mata tana iyakacin"

"k'okarinta a gida, kina yi mata abinda ki ke so, ga yaranta suna jinki, idan kuma watarana suka yi miki fitsara fa, don Allah ki daina haka anti Jamila, mu yi hakuri dukanmu."""

"""Kin ga, don Allah Ya isa, lefin ai na ki ne, me yasa ba za ki raba abincin da hannunki ba, ai mai iyali ki ka aure dole ki"

"yi, ni ma kafin na ajiye nawa sai da na yi wannan bautar, ba zan yadda da sigar munafurci ba, shine za ki kira ta ki ce ta zo ta raba akan me?"""

"Na ce.'' Babu dole Hajiya, ina lefin ma girkin da na yi, kuma ni dai ki dubi tsabar idona da kyau ki ga ni, ba zan"

"lamunci wannan daga wurinki ba, ban shigo domin tashin hankali ba, amma idan kin ce ayi to a shirye nake, haba ina dalili, mata tunda na zo gidan nan ki ke ta hayaniya, ko kin d'auka hakan zai sanya na ji tsoronki ne."""

"""To kada Allah Ya sa ki yi din mana, munafuka kawai, wallahi muddin ki ka ce ba za ki zauna lafiya da mu ba, ke ce a"

"wahale, kuma maigidan zai dawo sai na gaya masa abubuwan da kuka fara yi mini. Ni ban iya rayuwar munafurci ba, kome za a yi to a fito fili a yi shi a gaban kowa."""

"Na ce."" Idan Ya dawo ki sanya shi ya sallame ni, tunda ke ki ka sanya shi ya aure ni. Kuma wallahi ki daina kira na"

"munafuka idan ba haka ba, ni duka nake yi ban iya cacar baki, jikinki ne zai gaya miki."""

"Turzumi babban yaronta ya ce."" Aikuwa wallahi sai na kwala miki dutse' na fasa miki kai idan ki ka daketa."" Yaran gabad'aya suka kwashe da dariya. wadda hakan ya kara kona mini rai!"

"Anti Maimuna ta buga musu tsawa suka yi shiru, ta ce."" Kowa ya d'auki abincinsa ya isa haka."" Suna fara hayaniyar d'aukar abincin. Na bar wurin raina a kuntacce wannan wane irin gidane ......"

*1k on talgram via 0542382124. Binta Umar gtbank*

*07084653262*

"[11/25, 10:29 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*"

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE *

*M.W.A*

*TALLAH!*

"*Gidan 'kawa ne da kece raini, abin ma sai wanda ya yi joning da su, nan zai kashe kwarkwartar idonsa ga sau'kin farashi!*"

"  Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki  wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha. "

"  Shigo duniyar da kyau da jin daWi suka haWu  daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ™arin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi"

https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t

https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t

*@Arewa book's*

*Bintuumarabbale*

*Free pege*

*16*

"Ta ina zan yi sake na samu ciki har na haihu a irin wannan gida na alhaji Muntari. Lallai dole na yi takatsantsan, domin tashin farko na lura gidan ba irin wurin da za ka saki jiki ka haihu ba ne, dalilin rashin saiti, da gurguwar rayuwar da iyalinsa suka kafu akai. Wannan marayan da Allah ya jarabce ni dashi ya ishe ni. Ina ro'kon"

"Ubangiji ya ba ni ikon kula dashi tare da d'an'uwansa da kuma tarbiyarsu. Dole kuma koda yarana sun dawo gidan, na sanya ido kwarai a rayuwar da za su gudanar sabili da rashin gamsuwa da tarbiyar yaran gidan. lamarin dai sai da kawai mu ce Allah Ya magance mana."

"A daran ranan na fara had'iyar maganin hana d'aukar ciki. Dama na yi guzurin abina, zahirin gaskiya ba zan iya"

haihuwa dashi a irin wannan yanayin da shi kansa bai san menene rayuwa ba.

"Muka cigaba da tafiya a haka. Anti Maimuna macece mai sau'kin hali, kuma mara son hayaniya, yayin da ita Jamila ta kasance bagidajiya mara fahimta. Ko da yake babu mamaki idan an samu hakan daga wurinta domin a can karkara ya aurota wani kauye a karamar hukumar bichi, shiyasa komai nata take gudanar dashi cikin gidadanci, da kuma zargi. Gabad'aya jininmu bai hadu ba, tunda na fahimci halinta, sai nake takatsantsan, ban ta'ba yadda mun yi rigima ba, duk takalar da za ta yi mini, ba na nuna na san ta na yi. Sabgar gabana nake yi. Idan ba ranar girkina ba ma, ba na fitowa, ina ta sana'ata."

"Sai dai kuma zamansu a Kamalu a gidan yana nema ya zama d'an zani, domin ko kwana uku ba su yi da dawowa ba, matsaltsalu suka fara kunno kai. Yusi yaro ne mai son jama'a, ba shi da wahalar sabo, kullum Yana cikin yaran gidan su yi ta wasa. Amma ba a k'arewa lafiya sai ya shigo mini yana kuka, Turzumi ya dake shi. Idan na tambaye shi dalili sai ya ce babu komai, kawai dukansa ya yi. Sai dai kawai na rarrashe shi amma abin yana damuna mutuka."

"Kamalu ya yi ta kumbure-kumbure, yana jin haushi. Na hana shi motsi, domin dama tunda suka dawo gidan na zaunar dashi a gabana yana taimaka mini da wasu abubuwan na sana'ata"

"Ba ni da matsala da maigidan, domin kamar yadda ya fad'a tunda yaran suka dawo hannunsa yake iyakacin bakin kokarinsa. Ya kammala musu komai na makarantar boko da Islamiyya wadda yaransa suke zuwa. Satin da za mu shiga za a koma makaranta gabad'aya. Matsalata yadda Turmuzi ke cin zalin Yusi. Wanda na tabbatar da cewa ba zai yi masa lefin da zai kai hannun jikinsa ba, face dai cin zali da ganin gidansu ne. Sai kuma rashin kwa'ba daga wurin uwarsa."

"Yau zai dake shi. Amma hakan ba zai hana shi komawa cikinsu gobe ba. Kullum dai sai ya je cikinsu, sai kuma ya"

dawo mini yana kuka.

"Ban ta'ba yun'kurin d'aukar mataki ba. Na d'auke kaina kawai, amma zahiri ba na jin dad'in hakan."

Watarana ya shigo yana gursheken kuka wanda ya fi na koyaushe. Saman goshinsa ya kumbura har ya yi 'kululu! Na kama shi da sauri ina mulmula masa tare da tambayarsa.

"Ya ce."" Mama Turmuzi ne ya buga mini kai a bango."" Na ce."" Me ka yi masa yau kuma?"""

""" Ban yi masa komai ba mama, ball ya bugo shine don na mayar masa. Ya kama ni da duka Mamansu tana kallonsa."" Kamalu da yake sanya mini zif a jakkunkunan da nake yi na sayarwa. yana huci Ya ce """

"Wallahi mama ba zan yarda ba dubi fa ki ga yadda ya lun'kuma masa goshi, na rantse da Allah sai na rama masa."" Ya tashi da mugun sauri ya kama hanya fita. Na dinga 'kwala masa kira bai juyo ba."

Na yun'kura na tashi da saurin gaske na bi bayansa.

Sai kawai na same su a farfajiyar gidan suna dambe. Kamalu har ya kaishi kasa yana saman ruwan cikinsa yana ta dukan bakinsa. Kusan gabad'aya muka isa wurin da uwarsa da sauran yaran gidan.

"ihu! ta kurma ganin jini a bakin yaronta gashi a kwance a kasa yana kuka. Ta yi kukan kura ta janyo Kamulu. Na je na fizge shi daga hannunta. Sai ta hau d'ura masa ashariya tana fad'in "" Kashe mini shi za ka yi a gidan ubansa, wannan wane irin samun wuri ne, agola da zage k'wanji akan d'an gida. Na rantse da Allah ba zan yarda ba."""

"Anti Maimuna ta ce."" To, wai me ya had'a su ne, Jamila, ba fa a shiga fad'an yarana, a bi komai a hankali."""

"Na ce."" Ka da ki yarda Jamila, don Allah ki yi duk abinda za ki yi, wato ke yaranki ba su lefi ko? Kin taba tuhumar dalilin da ya sanya Turmuzi yake dukan Yusi kullum, na san kin sani. Ki dubi goshinsa ki gani, a wurinki akayi kuma kuna kallo ya buga kansa da bango, ba ki mulmula masa ba. Yanzu kuma ko kunya ba ki ji ba kin zo kina kumfar baki, ki yi abinda za ki yi, ai ba tsoronki nake ji ba."""

"Aikuwa zan yi wallahi, ba za ki kawo mana alakakai cikin gida ba, shi yaron naki ai ba mu muka janyo shi ba, rashin"

"zuciyarsa ne yake kawo shi wurina, ban ga dalilin da zai sanya ki kawo mana masifa cikin gida ba, dama an ce yaron nan mugu ne, sannan kuma 'barawo ne, duk mun samu labarin haka. Wallahi tallahi sai sun bar gidan."""

"Gabad'aya wurin ya yi tsit! domin Kalmar 'barawo da ta kira Kamalu ta girgiza kowa, har yaran. Anti Maimuna ta ce."" Wace irin magana ce wannan Jamila, shin ke kin san me ki ka haifa, kada fa ki yi wa kaddarar wani dariya, tunda haihuwa ki ke, kuma kowa da k'uruciyarsa."""

"Na ce."" Rabu da ita Anti Maimuna jahilace ai, bagidajiya mutuniyar kauye. Don kin kira yarona 'barawo ba zai dame ni ba, tunda kema kin haifa, kuma sai dai idan ke ce za ki bar gidan, amma Kamalu da Yusi zama daram, tunda ba na ubanki ba ne."""

"Wannan maganar tawa ta harzukata har sai da kwalla ta ciko a idonta. Muryata na rawa take cewa."" An ce masa"

"'barawon, ai ba karya aka yi ba, ko za ki musanta ne, sau nawa ana kulleshi a Police station? Wallahi za ki ga matsayina a gidan nan na rantse da Allah sai kin yi dana sanin kirana da jahila, 'yar iska mai suffar karuwai."""

"Na ce."" Na ji dai, ni na je makaranta, kuma ba 'yar kauye ba ce ni, ina da ilimi, sannan ba 'kazama ba ce."""

"Ta goge 'kwallar da ta d'igo a kumatunta. Ta tashi yaronta da yake kwance yana kuka ta ri'ke hannunsa suka kama hanyar barin wurin. Na dube ta tare da furta."" Ina jiran matakin da za ki d'auka. Jahila bagidajiya kawai."""

"Tunda na lura ba ta so a kira ta da hakan, ni Kuma na ri'ke. Sai ta yi wani kukan kura za ta kawo mini cakuma. Anti Maimuna ta shiga tsakani."

"Ta dinga d'ura mini ashariya sai ka ce bamagujiya. Na ce."" Kin ga aikin jahilicin naki ko, a gaban ya ra ki ke wannan tumasamcin, ni ba zan yi kokawa dake ba saboda na je makaranta."

"Anti Maimuna fad'i take don Allah Amina ki yi shiru, wallahi mu ba mu taba fad'a ba, da dadi babu dadi muna zaune lafiya."""

"Na ce."" To ni ba sakarai ba ce, anti Maimuna ba zan zauna wannan bagidajiyar tana juya ni ba, ita din banza, ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ba ita ta ajiye ni a gidan ba, wallahi daidai nake da ita, mu zuba shege ka fasa."""

"Ganin babu sassauci a tare da ni ya sanya ta juya wurinta tana rarrashinta. Ta tura ta wurinta tana bata ha'kuri. Yaransu suka dinga ihu suna kiran Kamalu da 'barawo hooo! 'barawo ne."""

"Yusi ya fashe da kuka ya ruga da gudu ya shige wurina. Shi kuwa Kamalu Yana tsaye durmin danya babu alamun firgici, ko nadamar abinda ya aikata. Kuma ihun da yaran suke yi masa bai sanya zuciyarsa ta yi rauni ba."

"Na ja hannunsa muka bar wurin zuciyata na 'kuna, duk abinda yake faruwa a gidan, ban tana gaya masa ba, yau kam idan ya dawo zan zayyane masa, ba zan iya ba wallahi."

"A ranar dama girkin anti Maimuna ne, na yi ta Allah-Allah gari ya waye ya shigo domin da b'acin ran abin na kwana a"

raina.

"Ko da ya shigo da safe sama-sama muka gaisa gabad'aya na kasa sakar masa fuska. Ga yaran su ma duk sun damu ganin yanayina sun takure kansu wuri d'aya. Hakan ya kara dasa mini kunci tare da dakacen auran gabad'aya, domin da na tabbatar da cewa bai fi karfin gidansa ba wallahi ba zan aure shi ba."

Yanayi na shi ya

Please Login or Register in order to submit comment