You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kawai mu kuma shine namu ba abunsa ba dan haka bazamu sakar musu ba"

Natiee ta rausayar da kai sannan tace, "yanzu me zakiyi to Ummi?"

Tace, ba wannan ne ya kamata ba yanzu kije ki kira min shi dai-daita nutsuwar sa shine abunda ya dace dani"

tashi tayi ta kirashi ba jimawa suka dawo tare.
cikin sakin fuska Ummi tace, "Jannah yau bana jin daɗin jikina sosai kuma zan shiga kicin muje ka tayani aiki ko?, kodai baka da lafiya ne?"

Da sauri yace, "aa Nan lafiyata ƙalau kawai inaga dai zazzaɓi nakeyi"

Tace, "amma shine ka ƙi gaya min?"

ƙasa yayi da kai yana ɗan sosai ƙeya yace, "Ummi ai gani nayi ba wani babban abu bane bana so na tayar muku da hankali akansa"

Tace, "shikenan yana da kyau kasha magani, Natiee maza ki ɗakko masa maganin saura kai kuma ka ƙi sha, ni bari naje kicin ɗin idan kaji dama ina jiranka"

har ta ɗakko masa maganin yana nan zaune, sai da tace, "Jan gashi fa"
Sannan ya numfasa gami da lumshe ido yace, "Natiee zauna mana bana son ɗabi'ar nan taki ta miƙa min abu a tsaye"

Tace, "shikenan kayi haƙuri zan kula, karɓi kasha"

Karɓar yayi ya sha sannan ya ɗan kashingiɗa.
Natiee tace, "kenan? mu bamu da wani amfani a matsayin mu na ƴan uwanka? su ma iyayen ka kenan duk gara babu tind baka ɗauke su a komai ba"

Baki buɗe yake kallonta kafin yace, "Natiee wai a ina kika koyi kwainane da manyance haka?? wannan wace irin magana ce kamar nayi amai?"

Ta gyara zama sannan tace, "dole nayi manyance mana tinda har yau ka kasa gane ka girma, fisabilillah Jan haka alƙawari yace?? kana tareda mu amma baza ka iya gaya mana ko abu ɗaya da yake damunka ba sai dai kaita ramewa ta ciki ba wanda ya sani, Aunty Fa'iza da Yaya Hassana Da yaya Husaina da ni ƙanwarka ko mu kaɗai mun cancanta ka gaya mana wani sirrin na zuciyarka bare azo ga mahaifanka, da gaske fa bana jindaɗin abunda kakeyi Jan kayi nazari ka gani zaka gane ba dai-dai bane, idan ni ban fahimci komai ba Ummi mahaifiyarka ce kallo ɗaya zatayi maka ta gane kana da damuwa dan ita ta raine ka tin baka iya magana ba har kafara, kuma zata so sanin abunda ya dameka kuma ka ƙi gaya mata baka tunanin jefa ta cikin wani mugun hali??"

Dafe goshi yayi tareda cewa, "wayyo Allah!! Natiee maganganun nan sunyi tsauri da yawa basar kawai dan Allah"

Tace, "naƙi gaya min dalilinka na yin hakan"

Yace, "babu, kawai bana son tayar da hankalin ku ne"


Tace, "ohh kai ka mutu kenan mukuma muyi ta jimami??, to shikenan dai bar wannan zancen yanzu bani labarin Antin tawa Zeety"

Murmusawa yayi yace, "yau kuma kece da tambaya ta?"

Tace, "kwana biyu ne bamuyi ba shiyasa naji nayi kewarta"

Yace, "duk a kwanan nan ne bana cikin yanayi shiyasa ma kikaji bana zancenta"

tace, "Ayyah har na tausaya mata gaskiya tana sonka sosai"

Yace, "to ya ranki?"

Tace, "yana lafiya tashi muje gurin Ummi ni, ai tinda na ɗago zancen nan sai ka dameni kuma"

Dariya yayi tareda miƙewa suka nufi kicin ɗin.


Hajiya Murja
dariya tayi sosai kafin tace, "ai babban goro sai magogin ƙarfe Aamina gashi yanzu na sauya labarin ɓangaren naki da abu guda ɗaya, Haisam? baka ga ƙanin ku ya fita daga hayyacinsa ba?"

Yace, "ƙwarai Momi na gani kuma nayi mamaki"

hhhh tayi dariya sannan tace, "na firgita ƙwaƙwalwarsa hakan kuma kaɗan ne daga cikin mummunan shirina akansa, duk da irin dafa'in nasu nayi nasara cikin ƴan kwanakin nan na kauda duk wani farin cikin su, kuma zan ɗora daga inda na tsaya wasan be ƙare ba"

Haisam yace, "wato a waje kina nuna duk ɗaya ne ke da Hajiya Saratu amma a gefe kawai kanki kike wa gyaran hanya"

Tace, "duniyar haka ta zama Haisam dagani sai ƴaƴa na kawai ina amfani da ita ne dan ta temaka min ta wani ɓangaren har na cimma matsaya, yanzu na gane lagon DOGON YARO"


Alhaji ne zaune a falo shida Ummi suna cikin fira yace, "Aaminatu nayiwa ɗanki laifi fa"

Da mamaki tace, "menene ya faru?"

Yace, "da fari dai kafin shi yana da kyau ki tausasa zuciyarki dan kema abun ze taɓa ki, ina son yaje ƙasar waje ne dan ɗaukar matakin karatunsa acan baze dawo gida ba har sai na tabbatar ya girma yayi hankali "

katseshi tayi da cewa, "Alhaji meyesa??, idan yana tareda mu mukanji kamar muna ƙarƙashin wata garkuwa ne, idan ka fita fa daga ni sai Natiee mu kaɗai baka tunanin abunda ze same mu? Idan yana nan munajin daɗi inaga ace yayi nisa damu haka?"

"Kayi haƙuri bana son gardama maka amma bazan iya bari ya tafi ya bar mu ba"














*INDO CE..*

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment