You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damuwa da tunane tunane.


A falon su Hajiya Murja kuwa sun gama hallara kaf mutum uku ne kawai babu FA'IZA HASSANA DA HUSAINA bayan su kuwa tin daga kan Salisu har kan Jafar sun gama haɗuwa.

Abdul ne yace, "wai Hajiya meke faruwa ne aka neme mu haka??"

Fauzy tace, "ɗan kutumar uba dama kana can kana shaye shaye taya zaka gane me ake nufi?"

Yace, "ke wallahi ki kama kanki ko na sama ki yanzu"

Ta gasa masa harara gami da jan dogon tsaki.

Hajiya Saratu tace, "kunga ba wannan ne ya kawo mu nan ba kun gane?? muna neman hanyar da zamu ƙwaci ƴancin mu ne ta hanyar da zamu ci galaba akan DOGON YARO"

Dariya Sultan da Haisam sukayi kafin Sultan yace, "sai yanzu kuka farga da hakan kenan? ai ni tin tini nagama tsarina akansa, a komai nasa gaba shine me tarwatsani yaron nan dan haka yanzu shi na sako a gaba, ko yanzu ma nayi musu kutse na mayar da kuɗin da ya turawa Alhaji zuwa banki na kunga yau anyi haka gobe anyi yau da kullum dole Alhajin yagaji sai kuma naga matakin da ze ɗauka akansa"

Haisam yace, "wannan yaron indai baka yimasa kare kare ba ai zaka mutu da baƙin ciki, Hajiya ni dai banaso ku takuri kanku ku cigaba da naku aikin ku barmu muyi namu"


Bomboi yayi tsaki sannan yace, " ni tsohon nasa ma nakejin kamar na kashe wallahi, duk shine yake sangarta shi sai kace shi kaɗai ne ɗa wallahi da da yadda zanyi da tuni na ɓatar dashi"

Hajiya Murja ta rausaya sannan tace, "hee yaro kenan Dogon Yaro da ace shima me gajeren kwana ne kamar sauran ƴaƴanta da muka kashe da tini shima ba'a labarinsa, Allah ne kaɗai yasan abunda ya ɓoye a tareda yaron nan da har ya gagare mu wannan kaɗai idan na tuna yana bala'in tayar min da hankali"

Hajiya Saratu tace, "muna zaune ze tarwatsa mu ko a yanzu ya gaje komai bare ya kai lokacin da yakejin ya isa? ai abun baze mana kyau ba, dole mu tureshi kodan mu ji daɗin rayuwa"

Miƙewa Hawaz Yayi tareda cewa, "Sultan da Haisam fa sunai muku nuni da cewar karku damu dan haka ku barmu kawai ni nayi hanya ta"

Bomboi yace, "aikuwa zamu ƙare a haka wallahi haɗin kanmu shine mafi alfanu garemu a yanzu indai bamu haɗa kai ba babu yadda za'ai mufi ƙarfinsa shi mutum ɗaya ne amma yafi ƙarfin goma bare wasu ƴan tsirarin mutane, a shawarce mu haɗe kai wallahi"

Fauzy tace, "wannan gaskiya ce ba shakka idan bamu haɗe kai ba mu zamugani"

Hajiya Murja tace, "ai dalilin hakan ne yasa muka taraku, mu haɗe duk wanda yake son dukiyar ubansa yabamu haɗin kai"

Faisal yace, "kanmu a haɗe yake kuma zamu cigaba da hakan yanzu dai kowa yaji abunda aka faɗa dan haka mu watse tin kafin Alhaji ya shigo"

Da haka suka tashi kowa da irin mugun ƙudurinsa akan Jannarh.

Natiee tana zaune a falo tana kallo Jancy ya shigo yana sanɗa har ya wuce ta batareda ya lura da ita ba tace, "ina kaje???"

Ɗan firgita yayi ya zaro ido sannan ya juyo fuska a haɗe yace, "ina ruwanki??"

Ta kwashe da dariya sannan tace, "ga tsoro ga ban tsoro ai ni abun ne ya tashi kaina ka fita da sittirarka tsaf ka dawo da singileti da kamfai tsamo tsamo da kai ko suma kayi kyautar su?"


zama yayi kan kujera sannan yace, "eh meye amfanin su to? wani ne yace yana so shine nabashi kuma sai akai me? naki ne ko nawa?, marowaciya kawai ke in mutum ya biye muki bazeyi alkairi ba"

Ta taɓe baki tace, "ba nawa bane amma dai an bada maza da kayi karo da Yayyen ka ma cewa zasuyi daga gidan karuwai kake, kai dai garin bayarda abunka ga wasu wata rana ma har ranka zaka nema ka rasa"

A miskilance yace, "ranka kikace dama ba ranki ba dan haka ki rufen baki"

Tace, "naji ni dik ka isheni da magana kasa bana fahimtar ma abunda nake kalla "

Yatsine fuska yayi kafin ya ciro wayarsa ya turawa Zeety kira ba jimawa kuwa ta ɗauka.

miƙewa Natiee tayi tana zumɓura baki tace, "idan kun gama na dawo "

Dariya kawai yayi gami da ɗaga mata hannu.
Kai tsaye kicin ta nufa tafara taya Ummi aiki.

"Jannah yadawo ko?"
Ummi ta jefa mata tambaya.

Tace, "kinji motsin shi ne? ya wani zo ya addabeni"

Ummi tace, "aa kawai tinda naga kin tawo ɗungul ɗungul nasan da walakin"

Cigaba tayi da aikin murya ƙasa ƙasa tace, " shi kowane lokaci nashi na wannan jar yarinyar ne"


Ita dai Ummi murmushi kawai tayi.










*INDO CE.."*
[7/21, 10:25 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 6*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_












wurgi yayi da kwalbar turaren sannan ya ɗan gyara sumar kansa, Saɗaf saɗaf ya fito yana leƙe leƙe dan kar yayi katari da ƴar kanzagi cikin sa'a kuwa sai da ya gama ƙure falon yaje ƙarshe sannan yaji muryarta tana rera waƙa cikin harshen buzanci, tana zaune kan kujerar roba ta harɗe ƙafa.

Ido ya zuba mata cikin sarewa da fitar.
Dariyar Ummi ce ta katse masa tunanin sa, ya juya kanta cike da shagwaɓa yace, "Nan!! nifa abokaina ne suka gaiyace ni"

Ummi tace, "dama ai bance nice ko Natiee muka gaiyace ka ba kawai dai bama son kayi nesa damu ne"

Kafin yayi magana Natiee tace, "Ummi na? yau ina son fita siyayya ko Jancy na ze rakani??"

Ummi tace, "gaki ga shi, Jannah ka bata amsa"


Yace, "amma Ummi nafa gama shiryawa na tsara komai kawai shikenan sai suga banje ba? gaskiya yarinyar nan ta fiye jaraba"

Natiee tace, "zaka iya rantsewa zakaje wajen abokan ka ne??"

Ƙasa yayi da kai yana sosa ƙeya ya yace, "bana rantsuwa akan ƙarya kinji ko?"

Dariya sukayi kafin Ummi tace, "ya tabbata kenan ba da gaske kake ba?? shikenan ai Allah ya tsare"

Natiee tace, "hmm abokai abokai sai kace kaine ka ƙirƙiri abota a duniya, daga wannan yace Jannah yimin kaza sai wancan yace"

da sauri yace, "Nan kinji ko?? marowaciyar banza idan mutum ya biye mata baze taɓa yin abun arziki ba kalle ta dan Allah sai kishin tsiya ke dai ko matata ce ba lallai taimin wannan ƙididdigar ba"


Natiee tace, "to a jikinka ma meye na kishi? Babu wani abunda za a yiwa kishi a tareda kai"

Yace, "Ummi kina jinta tana neman maidani wani soloɓiyo kuma bayan bata ƙaunar ta ganni da masoyiya ta ƴar sa ido kawai sai na buge ki kar Allah ya haɗani ma da mata irin ki, da wata rana sai dai azo a tarar da gawa ta jarabarki ta kasheni"

Tayi dariya sannan tace, "insha Allahu wadda ta fini zaka aura wadda duk ma inda zakaje da ƙafar yawon nan naka tana tareda kai, dan ma Allah yasa kai ba mayen ƴan mata bane da abun baze maka kyau ba"

Tsaki yayi ya nufi hanyar fita yana cewa, "karki fito zauna masifa ki tarar bana nan"

Da sauri ta tashi ta mara masa baya tana cewa, "Ummi mun tafi"

Ummi ta murmusa gami da cewa, "Allah ya kiyaye ku kula dai kar kuyi wannan faɗan naku akan titi"

Kasancewar sauri yake yasa be lura ba sai jiyayi yayi karo da mutum sun bangaji juna,
da sauri yayi Baya yana zaro ido a tsorace .

Cikin tsawa Haisam yace, "kai dabban ina ne wai?? mara ɗa'a kai ko da yaushe baka ƙara hankali shashashan banza, da wane ƙwarin guiwar zaka bangaje ni? sai na tubirbiɗa ka a gurin nan, ita Aaminar bata koya maka girmama mutane ne??"

Ƙasa yayi da kai cikin sanyi yace, "kayi haƙuri, amma dan Allah ka dena zagin kimar mahaifiyata badan tana koyar dani girmama ku ba tabbas da yanzu ba wannan zancen ake ba"

Mari ya ɗaura masa cikin zafin rai ya shaƙe shi ya haɗa shi da bango ya matse shi da ƙarfi yana huci, sai da yaga yafara jigata sannan ya watsar dashi gefe yana cewa, "idan kaji zafi gobe karka kuma ɗaga min harshe idan yau iya shaƙe ka nayi gobe har sai ka mutu sannan zan jefar da kai mara amfani kawai"

Sai da ya wuce sannan Jancy ya miƙe ya kama hannun Natiee cikin ƙarfin hali yace, "kizo muje"

Cijewa tayi cikin kuka tace, "bazanje ba Jan ka koma cikin gida ka samu nutsuwa in anjima sai kaje gurin Zeety dan farin cikin da zata baka ni bazan iya baka ba"

Share ƙwallah yayi cikin rauni yace, "Natiee ba kina son zuwa ba? karki fasa saboda ni zan raka ki kuma yau bazanje ko ina ba tinda bakyaso na fita"

Jan hannunsa tayi zuwa ciki tana tafe tana kuka shima yana sharar ƙwalla.
Hajiya Saratu tayi dariya cike da farin ciki tace, "matsalar ja da manya kenan, Allah sarkin daɗi da ya tashi sai ya sako ka a ƙaramin su, tabbas da kaine babban su babu shakka da kaina zan kashe kaina saboda baƙin cikin ganinka baze barni rayuwa ba, karfa ka damu wannan fa kaɗan ne yadda kake ba zuciyar nan me kake ganin ze faru? ai yadda ka fito haka zaka koma bazaka taɓa cigaba ba, gashi kai akafi so sai dai kuma anfi ƙarfinka bawan su ma yafika daraja haka zaka ƙare a ƙarƙashin ikon su, idan ka shiga kace ina gaida tsohuwar ka"



Fincikarsa Natiee tayi suka shige ɓangaren su, shi dai binta kawai yake ƙafafunsa ne kawai suke jansa hankalinsa nutsuwarsa da tunanin sa duk basa jikinsa.

Kallo ɗaya Ummi tayi musu tayi ƙasa da kai sai da tayi da gaske sannan ta hana kukan da yake son kufce mata fitowa.

Zame hannunsa yayi yaja dogayen ƙafafunsa ya nufi ɗakinsa.
Natiee ta zauna kusa da Ummi cikin zafi da raɗaɗin da takeji tace, "Ummi kenan haka yayana ze kasance kamar mutum mara ƴanci?? shima fa ɗa ne a cikin gidan nan amma komai aka ɗebo sai a juye akansa? kenan baze taɓa samun nutsuwa ba? yanzu fa shi ba yaro bane yayi girman da yaci su dena wulaƙanta shi haka, ni nagaji Ummi idan shi baze iya ba ni zanyi tsayin daka dan ƙwatar masa ƴancinsa, zan iya jurar duk abunda za'aimin amma bazan juri a dinga cin zarafinsa ana tozarta shi ba dan shine ƙashin bayana shine jigo na shine wanda nake kalla naji daɗi shi tamkar magaji ne a gurin Abana dan haka tamkar uba nake ɗaukarsa, shi fa namiji ne amma sun maidashi kamar marainiyar mage Ummi me yayi musu?? me suke son maidashi a rayuwar nan? kullum sai dai suyi masa yayi kuka mu kenan bazamuyi farin ciki ba? kowane ɗa a gidan nan baya laifi sai Jan saboda shine ba mutum ba?, Ni kawai ki barni dan Allah Ummi nagaji sai dai ayi yadda za ai dani"

Taƙarasa maganar tana wani irin kuka me matuƙar girgiza me sauraronta.

Cikin dauriya Ummi ta danni zuciyarta sannan ta rungumo Natiee a jikinta, bayan ta goge hawaye tace, "Natiee bana son hana ku yin kuka amma yayi yawa, tabbas abunda suke yiwa Jan yaci yanzu su dena ƙwarai shi ba yaro bane amma a gurinsu har yanzu yaro ne, karfa ki manta shine autansu da ace ya girmi Jaafar koda da minti ɗaya? tabbas da ni da kaina zanyi tsara a tsakanin su dan na nema masa girmansa amma sai ya kasance shine ƙarami ni kuma ban kasance uwarda zata bari ƙani ya raina yayansa ba, idan kukai haƙuri komai ze wuce akwai lokacin da ze zo wanda ko sunyi masa ma baze damu ba, yanzun ma rashin gane hakan ne yasa kuke damun kanku"


shiru Natiee tayi tana sauke ajiyar zuciya, dama tasan shine ƙarshen zancen Ummi babu matakin da zata ɗauka wanda ya wuce hakan, bata ƙara magana ba har bacci ya saɓe ta,
Ummi ta kwantar da ita akan kujera sannan ta tashi.

Jancy duk ya rasa me yake masa daɗi yana so yayi kuka kashirɓan kamar yadda ya sabayi amma abun ya gagara, ƴan hawayen da suke zuba a idonsa ne kawai suke ɗan sassauta irin zafi da raɗaɗin da zuciyarsa takeyi,
Duk jinsa yake kamar ba'a nutse ba ga wasu zantuka marasa kan gado da tunaninsa yake bashi wanda kuma suke ƙoƙarin yin tasiri a zuciyarsa,
Tabbas Ummi takan gaya masa ya canja canjin kuma beyi mata daɗi ba, sam be ga canjin ba sai a wannan lokacin da yanaji yana gani yake irin wannan burkitaccen tunanin.

Yana cikin haka wayarsa tafara tsuwwa beyi niyar ɗagawa ba amma da ya tuna Zeety tana can tana jiransa sai ya ɗauka.

Cikin sanyi tace, "Jan? yau ma..."

Katse ta yayi da cewa, "kiyi haƙuri"


Murmushin tausayawa tayi sannan tace, "kai yakamata na bawa haƙuri dan kuwa nasan an ɓata maka rai ne"












*INDO CE..*
[7/24, 9:06 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 7*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_







jinjina kai yayi yace, "haka ne shiyasa ma yau bazan samu fita ko ina ba"

Tace, "Jan har yanzu kai kaɗai na sani sai yaushe zaka bani labarin ka?"

Murmusawa yayi sannan yace, "kamar bazan iya ba Zeety bana son fayyace abunda ya shafi ni da ƴan uwana"

tace, "kenan har yanzu ban kai matsayin da zaka ɗauke ni matsayin ɗaya daga cikin su ba? a gani na nima tamkar ƙanwa nake a gurinka dan mun zama ɗaya, kenan tunani na kuskure ne?"

yace, " karkice haka mana, na yarda zan gaya miki amma ba yanzu ba"

Tace, "har sai yaushe kenan?"

Yace, "bansani ba banida tabbacin lokacin amma ki shirya cikin kowane irin lokaci zan iya tsinkayar ki da labarin"

Murmushi tayi gami da cewa, "amma bana so ka cigaba da kasancewa cikin damuwa fa"

Yace, "karki damu tinda naji muryarki ai komai ya wuce"

cigaba sukayi da fira cikin nishaɗi da matuƙar so da ƙauna.

Zaune take kan kujerar roba ta kashingiɗa a jikin makarinta sai murmushi take wani daddaɗan tunani ne yake mata yawo dan haka har ta manta ma a inda take.

"Queeen!!?? Queeeen!!!!!"

Cikin wata ƴar siririyar murya yake kiran ta.
Zaro ido tayi akansa tareda cewa, "kai??? ta ina ka shigo nan???"

Sai da ya zauna sannan yace, "daga sama kawai sai gani a gaban Queen"

Harara ta maka masa sama da ƙasa sannan tace, "kai a suwa?"

Yace, "kinsan dai ni mutum ne ai ba aljani ba sannan kuma ba sata na shigo yi ba bare kice bazan shigo ta hanyar da kowa yake shigowa ba"

tace, "Naji amma ai da dalili"

Matsowa yayi kusa da ita ya sassauta muryarsa cikin salon me jan hankali yace, "matuƙar kina gidan? me ze sa ki tambayi dalilin bayan kece? saboda ke nazo ina fatan zaki bani damar ganawa dake"

Maida kallonta tayi zuwa gefe ta murguɗe baki sannan tace, "kenan? meyesa kake son shiga rayuwar wani ne?"

Gyara zama yayi tareda cewa, "yauwa anzo wajen tambaya kawai zanyi miki"

Tsira masa ido tayi alamun tana sauraron sa,
a marai-raice yace, "Zuhra meyesa kina mutunta kowa kina sakarwa kowa fuska amma banda Zaheer meyesa duk irin son da nake miki bazaki tausaya min ba?"

Sai da ta sauke ƴar ajiyar zuciya kafin tace, "Zaheer Zuhra sunan ma ko dacewa beyi ba, Zaheer! Zuhra ba taka bace ka gane??"

Cikin tattausar murya yace, "meyesa??"

Ta murmusa sannan tace, "saboda ta riga tayiwa kanta zaɓi kuma ta sadaukarda zuciyarta wa soyayya, ba sauran inda zan iya raɓa ka Zuhra ta Jannah ce ba Zaheer ba"

Yace, "menene abunda Dogon Yaro yake dashi wanda ni banidashi? shi namiji ne nima kuma haka ina ganin dama ɗaya garemu dani dashi kamata yayi ya kasance ba wani cikakken bambanci tsakanin mu"

cikin ɗaga murya tace, "aaaa!! wannan maganar taka ai sai tasa mutum ya faɗi da yaya zaka haɗa kanka dashi?? shi fa dogo ne kai kuma ga ka nan dai shi kuma mutum ne me hankali da nutsuwa ga aji ba kamar kai ba, idan kuwa haka ne?? kaga babu yadda za'ayi kuzo ɗaya dole akwai bambanci"

Ya kwashe da dariya tareda cewa, "shashashar yarinya, wai banda ƙuruciya ina dalilin ki na maƙalewa wanda baya sonki baya ƙaunar ma ganin ki? bana tunanin akwai ranar da ze saurare ki fa"

Tace, "Zaheeer!!! wannan kalaman naka ɗaci garesu, kuma bi'izinillah da ranka zaka ga ranar da zan auri Jancy kanaji kana gani"

Yace, "mahaukaciya"

Yana rufe baki tace, "mahaukaci"

Yace, "shashasha"
Tace, "shashasha"

Yace, "sokuwa mara wayo"

A ɗan tsawace tace, "soko mara yawo manaa!!!!, jarababbe ina cikin tunani na me daɗi da fa'ida kazo ka rushe shi ka dami mutane"

dariya yayi sannan yace, "kin raina ni sosai Zuhra amma ba komai wata rana bazakiyi ba, naji zan dena takura muki amma fa bazan dena sonki ba sannan kawai kibani dama na cigaba da nuna miki ƙauna kuma karkiyi mita akan ina sonki kin yarda?"

Tace, "nace aa, idan baka so nayi mita to karka wani nuna min ƙauna ka cigaba da sona ɗin wannan kai ta shafa kaima ka yarda??"

Lallausan murmushi yayi gami da cewa, "na amince tinda hakan ya kasance hukuncin da zuciyarki ta yanke min"

Murmusawa tayi sannan tace, "Zaheer kasan me yake damuna? Jan! na kusa dena ganinsa dan mun kusa kammala makarantar shikenan yayi min nisa fa"

Zaheer ya jinjina kai sannan yace, "shine damuwar? zanyi tunani kafin lokacin sai mu nemo mafita indai hakan yai miki"

Cikin farin ciki tace, "yauwa Zaheer ɗina da kana haka ai da banyi faɗa ba a duniya dan indai kaji bakina to kaine ka tunzura ni saboda rawar kanka"

Yace, "ba wai!! damuwar tamu ƙuruciya ce kawai take damun mu duka amma naji kuma na ɗauka laifi na ne "
..

Tace, "yauwa yanzu ka zama mutum da ka amsa laifinka"

Jancy
a kan hanyarsa ta dawowa daga wani ƙauye da Abansa ya saba zuwa duk sati domin bada tallafi ga mabuƙata, kasancewar baze samu zuwa ba yasa ya aikeshi,
tuƙin motar kawai yake amma hankalinsa baya tareda ita duk ya ta'allaƙa akan tunanin makomar rayuwarsa,
Kamar gilmin wani abu yagani ya gifta a gabansa ya wuce, gabansa yayi wata kyakkyawar faɗuwa har ƙasa,
Be ga komai ba sai dai kama da yagani da kuma bugawar da zuciyarsa tayi hakan yasa be sassauta gudun da yake ba dan kuwa burinsa a yanzu be wuce yaga Ummin sa da abar ƙaunar Natiee ba.

bayan yaƙara tafiya me nisa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment