You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_








Sai da Aba ya tabbatar ya ƙoshi sannan shima ya ci, bayan sun kammala Aba yace, "Yaro ina fatan dai ba wani abun?"

Yace, "Abana bana rabo da ƙorafi wallahi fita nakesonyi kuma waccan farar yarinyar ta hanani "

Aba yace, "wa kenan ba dai Fauziya ba?"

Da sauri Ummi tace, "wace fa idan ba karkatacciyar kuka ba? tayi ma bacci ita idan zaka fita ka fita idan kuma bakai niya ba to, ko gurin wa ma zakaje a daren nan oho"

yayi ƴar dariya sannan yace, "Nan!! ina namiji idan ban fita ƙarfe taran dare ba waye ze fita?, Aba bar zancen kawai bazan fitan bane saboda nayi mata alƙawari kuma banason saɓawa"

Aba ya murmusa cike da farin ciki yace, "masha Allah ina matuƙar farin ciki da jin daɗin irin kulawa da ƙaunar da kake bawa ƙanwarka Harma da yayyen ka guda uku wanda sune suka kasance fansar sauran ƴan uwan naku a gurina, inada tabbacin ko bana raye zaka iya kulamin dasu indai da ranka da lafiyar ka, ina ƙara jaddada fatan alkairi na gareku baki ɗaya Allah ya yi muku jagora a duk lamuran ku"

Cikin jin daɗin addu'ar ya amsa da "amin Abana abun alfahari na, insha Allah bazaka mutu kabarni ba zamu rayu tare"


Aba yayi murmushin manyance ba tareda yayi magana ba .
cikin harshen buzanci Ummi tace, "Jannah! kaje ka kwanta dan Allah gobe litinin fa zaka tashi da wuri"

beyi musu ba ya tashi rungume Aba yayi yace, "Allah ya tasheka da rai da lafiya Abana"

Aba ya shafa kansa gami da cewa, "Amin Allah ya amsa tareda kai Yaron kirki"

Yana murmushi ya koma wajen Ummi itama rungumeta yayi yace, "Ummina karki manta kimin addu'a"

Tace, "Jan bazan manta ba"

Dariya yayi sannan ya nufi hanyar sashinsa yana tafe yana waiwayen su.


Ummi sai da ta tabbatar ya tafi sannan tabawa kukan da yake cinta damar fitowa.
Aba ya dawo kusa da ita ya zauna cikin tausayawa yace, "Aaminatu? meyesa zakiyi kuka? ni kuma yaya zanyi kenan idan ke da kika kasance ƙwarin guiwata kikayi kuka??"


Share hawayen ta shigayi tareda ƙoƙarin tsagaita kukan.
Janyota yayi zuwa jikinsa yayi mata masauki cikin sanyi yace, "Aamina kin jure kinyi haƙurin zama dani har lokacin nan, lokacin da mukejin ranar kukan mu ta wuce Allah ya azirta mu da ɗa kamar MUFTAHUL'''JANNAH amma ki zubda hawaye? meye ya ragewa rayuwar mu wanda ya wuce mu godewa Allah da ya bamu su? shine ya bamu kuma yasan halin da suke ciki kuma dukan mu muna gareshi ne duk abunda ya faru dani dake dashi dasu duka ma duk Allah yana sane kuma yasan me gaskiya yasan mara gaskiya koda ba a gidan duniya ba wata rana zakiga lokacin da Allah zeyi mana SAKAYYA (Littafin Gimbeeya) akan duk wanda ya zalumce mu, ƙwarara masa zuciya yakamata mu dinga yi ba mu raunana masa ita ba, dan Allah Aaminatu"


Shiru tayi tana sauraren sa har ya kammala sannan tace, "a koda yaushe idan da ɗan adam zeyi nazari? tabbas da ze gane lokacinsa kaɗan ne lokacin farin cikinsa ƙalilan ne, jiya ta wuce ɗazu ta wuce ko anjima bamu san ya zata kasance mana ba bare kuma gobe wannan sai Allah, kuma muna manta cewa mutuwa rigar kowa ce idan baka mutu ba to za'a mutuwar maka, za'a mutu a barka ko kuma ka mutu kabari bakasan halin da kabar baya ba, ina tunanin goben mu da ƴaƴan mu tabbas zuciyata tana gaya min akwai babban ƙalu bale da ɗanmu ze fuskanta a rayuwar sa ta gaba bayan na baya da ya fusjanta koma nace yake ka fuskanta kaga kuwa ni kuka ya kama idan kayi nazarin kalamai na zaka fahimci hakan"

Aba ya numfasa sannan yace, "wannan gaskiya ne Allah yasa mu dace ya iya mana akan duk abunda bazamu iya ba "

Jancy.
har ya gama ƙalular sa da tunane tunane ya kwanta bakinsa ɗauke da addu'o'i yana shirin bacci yayi awon gaba dashi yaji wayarsa tana ƙara , kamar baze ɗauka ba tsoro da shakka yasa shi ɗaukar dan dole cikin sanyi ya kara a kunne tareda yin sallama.

A ɗaya ɓangaren Fahad yace, "kai Dogo zo kaimin wankin ƙananun kaya dallah,

kamar zeyi kuka yace, "nafa kwanta har nafara bacci ka bari sai gobe"

Cikin isa da gadara yace, "yanze nake so kuma idan kanajin ka kai kace ba zakai ba"

share ƙwalla yayi gami da cewa, "ina zuwa amma kana ina?"

Yace, "kayan suna sashin Hajiya Murja kuma kazo sashin mu kayi wankin banaso kasa a injin wanki kuma"


"to" kawai yace sannan ya tashi ya nufi sashin Hajiya Murja yana tafiya yana sharar ƙwalla, raɓewa yayi ta hanyar da yasan bazeyi karo da Aba ko Ummi ba.

Sallama yayi a falon babu wanda ya amsa har sai da yayi sau uku sannan Fauzi tace, "gafara dallah kazo ka cikawa mutane kunne da sallama kamar wani maroƙi ubanme zakai anan??"

Ƙasa yayi da kai sannan yace, "Yaya Fahad ne yace inzo inyi masa wanki"

Tace, "sai dai kaje ɓangaren su dan bayanan bazaka shigo ba"

Hajiya Murja ta murmusa a ƙasaice tace, "barshi ya shigo Fauzi me ze iya ɗauka koma me ze iyayi?? zo ka wuce ka ɗauka sai ka shiga sashin nasu yana ciki"

Cikin sanyin jiki ya shiga yana tafiya a hankali cikin tsoron yayi takun da ba dai-dai ba ya faɗa ruwa.

Jaafar da yake zaune yana danne dannen waya ba tareda ya kalleshi ba yace, "kai maza ka kawo min 30k idan ka koma"

Cikin ƙarfin hali yace, "saboda me?? me zakai dasu??"

Yayi ƴar dariya sannan ya cigaba da danna waya.
har ze wuce ya dakatar dashi da cewa, "dakata!!"


Tsayawar yayi yana sauraron abunda ze ce, sai da ya gama danne dannen sannan yace, "shagali zanje nayi nida budurwa ta kai harma da abokaina bani 50k kawai ina jiranka gobe kafin ka tafi makaranta zan karɓa kuma idan ka bari tsohonka ya hana sai na saɓa maka kamanni"

da " to" kawai ya amsa dan baze iya yin jayayya dashi ba musamman anan da ya shigo tsakiyar su, wucewa yayi inda Fahad ya kwatanta masa ya ɗauki kayan sannan ya wuce sashin Hajiya Saratu.

Haka sukai ta ciccira shi har 12:00am sannan suka barshi ya koma sashin su lokacin bacci ya gama cin galabarsa.

Washegari da ƙyar ya tashi saboda bacci me nauyin da ya danneshi, sai da yayi addu'a sannan ya tashi ya nufi ɗakin wanka shower ya sakarwa kansa ruwan yafara dukansa yana ratsa shi a sannu a sannu ajiyar zuciya ya sauke gami da lumshe ido sannan ya shiga shafa sumar kansa ya a yamutsa ta, tunanin mafarkin da yayi a daren ne yake ta yimasa yawo aka ya rasa ina abun ya dosa ko kuma yake son zuwa amma yasan mafarkin ba shawai ɗin mafarki bane me hujja ne, ya rasa meyesa baya taɓayin mafarki me daɗi sai dai mummunan mafarki kullum, yana ganin abubuwa da yawa wanda ya kasa fahimta kuma baya son sanarwa wani irin munanan mafarkan dan yana matuƙar gujewa damuwar su.


ya daɗe yana tunane tunane kafin yayi wankan ya fito ya kintsa, lokacin da ya fito tini Natiee ta gama shiri dan kuwa tana tsoron barazanarsa idan ya rigata shiryawa ƙarshe ma baze bari tayi shiri me kyau ba.

Sai da ya tanadi kuɗin da ze bawa Jaafar sannan ya samu ƙwarin guiwar fita a wajen motarsa ya tarar da Jaafar ɗin yana jiran fitowarsa kuɗin kawai ya bashi ya shige mota dan bayason hayaniya bare tashin hankali duk abunda ze zamo matsala ba ƙaunarsa yake ba.


Zaune take a gaban madubi tana ƙarewa kanta kallo fara ce sol kyakkyawa sahun farko ƴar duma duma hannu tasa ta kwashe gashinta da ya bazu har kan fuskarta tayi baya dashi ta cigaba da kallon fuskart, Masha Allah, tana da ƴan saffa saffan idanu ba manya ba ba ƙanana ba farare sol sai ƙwayar idon da tayi sirki da brown color sai dogon hancinta irin wanda ake kira hanci har baka ɗan bakinta ɗan madai-dai-ci.

Cikin shauni tayi ƴar kwalliya mara yawa daga kwalli sai manbaki sai hoda.

Zahra ce ta shigo tana kiranta, ta amsa sannan ta cigaba da cewa, "na rasa ma da yaya zanje makaranta yau Zahra bani shawara mana"

Zahra tace, "kai Queen gaskiya Allah ya fiddake dai kawai, amma wannan kwalliyar duk akan wanda ko kallonki ma ba lallai yayi ba bare ya gani, Shawarar da zan baki kawai ki dena kwalliyar ma"

tace, "wallahi bazan dena ba son gaskiya nakewa Jan dan haka zan juri ko me zeyi min na rashin mutunci wata rana sai labari idan na mutu sai dai ace ai da Zuhra ta So Jancy sosai, to irin wannan tarihin nakeson kafawa a rayuwata"

Zahra tace, "banajin wata rana ma Jan ze kalle ki a matsayin mace, kinfiye zaƙewa da yawa ki tsaya iya matsayin ki tinda ya riga ya nuna miki iyakar ki"

Tace, "dena wannan maganar Zahra, banida iya tsakanina da Jancy babu wani layi da ze shata wanda ze shiga tsakani na dashi sonshi ba? to Yanzu na fara"

Zahra tace, "to naji amma ya zakiyi da masoyiyar sa da ya mutu akanta"


Zuhra tace, "Zeety!!!!!!............"








*INDO CE..*
[7/18, 9:03 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..

Marubuciyar Sirrin Ƙeta A jini Ɗaya Tajmahaal paid book Ib ɗan wanka Rintsin So tareda Sihirin ƙauna da Dogon Yaro


*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 4*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_







bazan iya cewa, "itace katanga tsakanina da Jancy ba dan na lura akwai rashin jito tsakanina dashi kawai ita ɗin tana matsayinta na wadda yake so ni kuma ina sonshi dan haka babu ruwa na da ita kawai bana yanke ƙauna da sa rai akansa"


Zahra ta jinjina kai tace, "Allah ya bada sa'a nidai ki tashi mu tafi kar kisa mu makara dan ke ba asara ce dake ba ni zaki cuta"

murmushi tayi ta tashi ta ƙarasa shirin a gurguje.

Idanunsa a lumshe ya kwantar da kai jikin makarin kujerar motar duk hankalinsa ya lula duniyar tunani.
Natiee ta cewa direba, " yau ba sai ka ɗauki wannan matar ba kawai ka wuce"

Ba tareda ya buɗe idon ba yace, "Natiee wai meye abunda tai miki ne?? jiya kin hanani ganinta yau kuma kar a ɗauketa to akanki zata zauna??"

kallonsa tayi sama da ƙasa sannan ta taɓe baki ta basar.
murmushi kawai yayi batareda yayi magana ba.

Direba yace, "hajiya za'a dakko ta ko kuwa?"

tace, "eh kayi sauri dan Allah"
...

Suna isa gidan su Zeety suka tarar ta gama shirinta su kawai take jira dan haka babu ɓata lkaci suka cigaba da tafiya.

Tin a parking space sukayi katari da juna, tana ganinsa tayi saurin komawa ta laɓe a jikin mota,
Shi kuwa yama manta da ita a duniya tafiyarsa kawai yake yana tunanin abunda ya dameahi.
Zuhra kuwa tsoro ne ya lulluɓe ta da sauri ta ɗage hijab ɗinta rufe fuska dashi hakan ya bawa jikinta damar fitowa saboda hijab ɗin ba wani babba bane.

Dogon Yaro kuwa ɗaga idon da zeyi ya sauke su akanta duk da besan ko wacece ba amma abun ya bashi haushi sosai sai da yazo saitin ta sannan ya saki wani dogon tsaki wanda yasa hantar cikinta juyi.

A kiɗime tace, "kayi haƙuri wallahi banaso ka ganni ne nasan idan ka ganni ranka ɓaci zeyi"


Cakk ya tsaya ya dena tafiyar yayi jimm sannan ya juyo ya kasheta da rikitattun idanunsa, da sauri tayi ƙasa da kai jikinta har tsuma yake.

Ɗan tsaki yayi sannan yace, "ke bugaggiyar ina ce da zaki ɗage sittirar ki ki rufe fuska? halama kinfara hauka kuma? ai tinda na ga wannan shirmen nasan baya wuce ke buzur"

Cike da shakka tace, "kayi haƙuri dan Allah"

kallon baki kai ba ya watsa mata sannan ya cigaba da tafiya cikin takunsa na ingarman namiji, da ido ta rakashi tareda tunanin ranar da zata dena tsoronsa gashi yaro amma zubin matasan da suka bawa 29 zuwa 30 baya gashi da kwarjini kamar wani babba.
Murmushi ta saki bayan ya ɓacewa ganinta ita hakan da ta faru ma daɗi tayi mata dan wani lokacin sai tazo a bati ta koma a sadaka ba tareda ya ko kalli inda take ba duk da irin alayen da take masa.

Hajiya Saratu ce tsaye sai kai kawo take a falon cike da damuwa.
Hajiya Murja tayi sallama ba tareda ta jira an amsa ba ta nemi guri ta zauna,
Ganin Hajiya Saratu tarasa zaune tarasa tsaye yasa tace, "meke faruwa ne?"

dama jiran wanda ze ɓula mata take dan haka tayi saurin cewa, "meye ma baze faru ba Hajiya Murja? kullum yaron nan barazana yakewa rayuwata ina cike da tsoron lokacin da ze ida girma wallahi"

Tsamm tayi tana tunani zuciyarta ce ta buga da sauri ta kalli Hajiya Saratu tace, "wannan haka yake tabbas idan ya girma akan wannan tafarkin komai ya rushe mana"

Hajiya Saratu tace, "yanzu meye mafita dan gaskiya nafiki jin tsoronsa kinga wani irin kallon tsana da yake min kuwa? bazan lamunta ba gaskiya, gashi duk asirin da za'ai baya taɓa shi lallai Aamina ta haifa min ƙaddarata"

Hajiya Murja tace, "ya kamata kuwa mu ɗauki mataki dan yanzu ne yake tashen balaga wannan yaƙin ba namu ne mu kaɗai ba samun ƴaƴan mu zamuyi mu tattauna dasu yanzu sune yara sabon jini zasu fimu sanin makwanta dan haka zamu haɗa duk tuggu da zamu ga bayansa, ni baƙin cikina ma irin muguwar ƙaunar da Alhji yake nuna masa burina kawai na rabashi da uban nasa sai naga meye kuma ze rage masa dashi da uwar tashi, sai dai asiri ko tsafi ma baze musu ba, amma ina tunanin sharrin da baze fita ba zamu laɗɗafa masa wanda Alhji da kansa ze tsaneshi"

Farin ciki ne ya ziyarci Hajiya Saratu dariya gami da shewa tayi kafin tace, "shiyasa ina dake banada fargaba wannan yayi haka yakamata muyi tin farko amma bamuyi ba, yanzu ya kamata a buga wannan wasan kuwa wallahi.

Fauzy da ke gefe tace, "wallahi na tsani yaron nan ɗan iska kuma idon mutane gaba ɗaya akansa yake basa ta mu sai shi shi kaɗai ake ɗauka a matsayin ɗan Alhji ina baƙin cikin wannan wallahi"

Hajiya Saratu tace, "kwantar da hankaln ki yarinya ai tazo ƙarshe, maza ki sanarwa ƴan uwanki duk su hallara akwai tattaunawa"

Tace, "to"

Aba yana dawowa ya ɗauki wayarsa ya koma sashin sa ya samu guri ya kwanta akan kafet.

Cikin kulawa Aba yace, "YARO!!! idanunsa a lumshe batareda ya buɗe su ba yace, "Abana"

Aba yace, "baka gaya min meke faruwa a fannin kasuwancin mu ba"

tashi yayi ya zauna sannan yace, "Abana komai Alhamdulillahi yana tafiya dai-dai yadda ya kamata, ka duba Asusunka ɗazu na tura maka kuɗi"

Aba yace, "Masha Allah jajirtaccen Yaro bari na duba"

wayarsa ya ɗauka ya shiga dubawa ya bincika tsaff sannan ya kalli Jan a nutse yace, "ka tabbatar ka tura??"

Jancy yace, "ƙwarai kuwa Abana"

Aba ya sake yin nazari kafin yace, "zasu kai kimanin nawa?"

Cikin tsitstsinkewar magana Jancy yace, "Abana?? kar dai kace min baka gansu ba"
....

Aba yace, "eh hakane bangansu ba kodai ka samu kuskure ne wajen turawar?"


Yace, "aa Aba banyi ba gaskiya sai dai in wani ne yayi kutse cikin lamarin"

Hajiya Murja da take tsaye tana jinsu batareda sun san ta shigo ba tace, "madallah ɗannan lallai kanada ƙarfin hali ai kowa yaji yasan inda kuɗin sukayi waye yasan sirrin ku da zeyi muku kutse sai dai in kaine ka kutsa su a Aljihu ai kashe kuɗin da kake ma yayi yawa ina zaka same su in baka taɓa na wani??"

Alhji yace, "ya isa haka, banason fitina da tashin hankali ni ban haifi ɓarawo ba, ɗana ba haka yake ba sai dai in naki ɗan ba wannan ba, bansan ma menene ya kawo ki ba, ki wuce ki bamu guri keda bakyason zaman lafiya"

Tayi dariya sannan tace, "eh lallai yau naji kan Aba da ɗansa Allah ya sittira, gaskiya bakaji daɗi ba Dogon Yaro kai da tsohonka yana sonka yana baka kuɗin nan meyesa se kai masa sata?? wannan ai abun kaico ne sata bata dace da kai ba kaida ake nunawa ƙauna duk da dai dama irinku ɗin kunfi lalacewa, naji ance har ƴan mata gareka to ni dai Allah ya kiyaye min tawa karka lalatan ita tinda ka zama haka"

Tsawa Aba ya doka mata badan ta kai matsayar maganarta ba tayi waje ba shiri amma ko iya haka taji daɗi ko babu komai tasanya tsoro da ƙunci a zuciyar Jancy.

Cikin tashin hankali da razani Jancy yace, "wallahi Abana ni ba ɓarawo bane kuma ni ba lalatacce bane bansan ya akai ba amma ni ban taɓa kuɗinnan ba, kayi min komai dan haka banga dalilin da ze sa na zalumce ka ba Abana wallahi ba ni bane"






Comment and share saboda Allah.



*INDO CE..*
[7/18, 9:03 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 5*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




Aba yace, "hmm Jannah nasani sarai dan dai bakasan wacece wannan ba da bakai tunanin zan yarda da abunda ta faɗa ba, ka kwantar da hankalin ka mu fauwala wa Allah kawai karka shiga damuwa akansu"

Rausayar da kai kawai yayi ba tareda ya iya yin magana ba.
Jiki ba ƙwari ya tafi ya kwanta cike da tarin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment