You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar daga sama yaga wani maciji baƙi siɗik murtukeke ya sako kai kan titin ya doshi ɗaya tsallaken da alamun tsallakawa yake son yi.

wani mugun burki ya sha wanda yasa motar ta ɗanyi tsalle tayarta da ta haɗu da kwalta ta bada wani farin hayaƙi sannan ta tsaya,
Rintse ido yayi da ƙarfi tareda furta "Hasbunallahu'wani'imalwakil"


Har ya buɗe idanunsa yaƙara ɗora su akan titin Macijin be gama tsallakawa ba gashi dai kansa ya wuce amma gangar jikin bata ƙare ba bare a ga ƙarshen sa,
Sosai Jan yaƙara firgicewa dan kuwa ko a tatsuniya be taɓa jin labarin macijin da ya kai wannan tsawo ba.

Juyawar da kansa yafarayi ne yasa ya ƙara rintse idon yana buɗewa kuma yaga ko ƙurarsa babu,
Lokaci guda kuma wata muguwar kasala da tsinkewa ta saukar masa kamar an zare masa laka jikinsa yayi wani bala'in sanyi tin daga tsakiyar kai har ɗan yatsan ƙafa ga wani mugun rauni da zuciyarsa tayi.
yakasa ko motsin kirki sai wasu zafafan hawaye da suke sintiri akan fuskarsa,
Duk da wannan yanayin da ya faɗa be fasa addu'o'i yana neman temakon Allah ba, har ya fitar da rai da komawa gida sai kuma yaji ƙwari ƙwari a jikinsa cikin sauri kuwa ya sake ɗora motar kan hanya jiki na rawa fatansa kawai ya ganshi a gida koma yaga ya shigo cikin mutane dan kuwa titin ba kowa kamar anyi shara.


Yana cikin tafiyar yaƙara ganin maciji kalar golden ya faɗo akan glass ɗin motar har sai da yayi tsawa yai ratsa ratsa, Jancy kuwa besan lokacin da ya juya motar ba saboda kiɗima da gigita yayi cikin jeji da ita saura ƙiris yayi karo da wata bishi Allah ya tsare motar ta tsaya.


Ko buɗe ido ya kasayi ga wata zuffa me zafi da take keto masa jikinsa sai ɓari yake, kawai ya saduda ya miƙa wuya jiran irin ɗanyen hukuncin da macijin ze yanke masa kawai yakeyi.














*INDO CE..*
[7/25, 12:45 PM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 8*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_







Zuhra gyara kwanciya tayi tareda cewa, "
Zahra idan kin gama shirmen naki sai kiyi shiru nidai bacci zanyi"

Zahra tace, "da ranar nan??"

Zuhra tace, "kinga surutun naki ne fa ya hanani bacci kimin shiru"

taɓe baki tayi sannan ta fice daga ɗakin.
Zuhra kuwa bayan ta gama lissafin dokin ranon bacci yayi gaba da ita.

A firgice ta farka ta dire daga kan gado tayi waje tana ƙwalawa Zaheer kira, suna falo shi da Zahra da Momu suna hira ta iso a gigice kai tsaye wajen Zaheer ta nufa tana cewa, "Zaheer Jancy bashida lafiya dan Allah kazo ka kaini wajen shi so suke su kashe shi kayi sauri ka tashi"

da mamaki yace, "bangane ba fa Dogon Yaro ba lafiya to ke tayaya kika sani? kuma ni banida lambarsa kawai ruɗani ne ma irin naki amma mutumin da bakisan a duniyar da yake ba"

cikin son gazgata gaskiyarta tace, "da gaske nake ina cikin bacci naganshi yana ta kuka ka kiramin Alamee ka tambayeshi yana ina wallahi baya lafiya ka temake ni Zaheer"

Momu tace, "ikon Allah waye wanda take magana akansa ne Zaheer??"

Zaheer ya ɗanyi ƙasa da kai sannan yace, "abokin karatun ta ne"

Momu ta jinjina kai sannan tace, "tinda hakane ka kira kaji ɗin ai yana da kyau hakan"

Waya ya cira ya kira Alamee cikin sa'a kuwa ya ɗauka tareda cewa, "aboki yane??"

Zaheer yace, "kasan ƙanwata ai Zuhra itace ta rikice min wai Jancy ba lafiya yana ina ne??"

Cikin kaɗuwa Alamee yace, "kut to ai baya gida yaje wani ƙauye yau kuma yanzu yaci ace ya dawo gaskiya dan yace baze jima ba tinda ba tareda Alhaji suka tafi ba, bari na nemeshi naji"


Zaheer yace, "yauwa nagode"

Alamee yana kashewa ya kira wayar Jancy har sai da ta katse sau uku be ɗauka ba dan haka ya kira Sufyan yana ɗauka yace, "Sufee Jan be dawo gida ba ko?"

Yace, "eh da ya dawo ai ze sanar damu"

Alamee yace, "ai kuwa ba lafiya ya kamata mu bi sahun sa maza ka fito mu haɗu kuma ka sanarwa su Zuhair da sauran abokan mu"

Sufee yace, "shikenan yanzu zan fito kawai ka tawo sai mu haɗu ko?"


Yace, "ina zuwa"

Cikin sauri ya shiga cikin gida ya ɗakko mukullin mota ya ɗau hanya.

Jancy kuwa yana jin ƙarar wayar amma yakasa ɗauka yadda yake zaune idan ba zuffa ba ba abunda yakeyi sai jikinsa da yake karkarwa yana kallon macijin ya silale yayi ƙasa ya cigaba da tafiya, ya daɗe a cikin wannan halin kafin ya samu ya janyo wayar ba tareda ya duba me kiran ba ya ɗaga ya kara a kunne.

a kiɗime Sufee yace, "kana ina Jancy muna ta nemanka amma shiru"

a wahalce yace, "Sufee ina wata hanya banyi nisa sosai da futowa daga ƙauyen ba kuma bazan iya dawowa gida da kaina ba kuzo yanzu dan Allah"

Sufee yace, "muna kan hanya karka damu zamu zo amma karkayi wani wajen mu neme ka mu rasa ka tsaya anan ba abunda ze sameka da yardar Allah"

Kai ya gyaɗa tareda cewa, "to"

har suka iso beyi wani yunƙuri ba dan a matuƙar tsorace yake gani yake yana fita daga motar ze ƙarayin mugun katari da macijin a hakan ma be yarda tafiyar yayi ba.

Basu tsaya nemam ba'asi ba kawai suka maidashi ɗaya motar suka rufe waccan, sannan suka kama hanyar komawa gida, har suka dawo be ce musu ƙala ba, kai tsaye gidan su Alamee suka wuce dan sun san baya ƙaunar abunda ze ɗaga hankalin mahaifiyarsa.

Sai da yayi wanka ya huta ya dawo hayyacin sa sannan suka maidashi gida.

A falo ya tarar da Ummi da Natiee yana yin sallama duk suka bishi da ido Ummi ce kawai ta amsa sallamar tashi Natiee kuwa kallon tuhuma kawai take jefa masa.

Murmushin ƙarfin hali ya saki gami da zama a gefen Ummi yace, "sannu da gida Nan"

Tace, "yauwa amma baka da lafiya me yafaru ne?? ba Aba ne ya aike ba?"

Ya gyaɗa kai sannan yace, "hakane Ummina yanzu na dawo duk a gajiye nake wallahi"

Yaƙarasa maganar tareda yin miƙa, yaƙara da cewa, "ke Natiee yau me kukai mana ne? wai ma baki iya gaida mutane ba? kawo min ruwan bunu do Allah"

Tashi tayi tareda cewa, "ba dai kace bazaka dani ba gashi nan ka dawo a gajiye ai, sannu dai ba dan halinka ba ya hanya?"

Yace, "lafiya lau ba'a zo nema na ba?"

Natiee tace, "to za'a fasa ne?? kayi shiru da zancen su kawai ka huta ze fi"

Ummi dai kallonsu kawai take haka kawai takeji kamar ba dai-dai Jannah yake ba amma tasan ko zata mutu dan tambayarsa baze gaya mata gaskiya ba amsar dai itace ba komai"

ko alamun wani abu ya faru be nuna musu ba har dare yayi suka rabu da nufin ya tafi bacci, yaso yin baccin amma abun ya faskara da ya rufe ido macijin nan guda biyu su yake gani sai ya firgita, tin yana ɗaukar abun da wasa yaga har ya girmama ya kasa baccin gashi yanajin sa da ya rintsa sai yayi muguwar firgita gashi dare yayi sosai, tashi yayi ya ɗauki filonsa ya nufi ɗakin Ummi tana zaune tana lazumi da alamu ta gama nafila ne da sallama ya shiga ya zauna a kusa da ita ya ɗora kansa kan kafaɗarta.


Sai da ta kammala addu'ar ta shafa sannan tace, "Jannah meke damuwarka??"

Yace, "Ummi nakasa bacci"

Tace, "meyesa?"

Yace, "bansani ba nima kawai firgita nake"


Tace, "bakayi addu'a bane?"

Yace, "nayi amma ban dena ba kuma inajin baccin amma nakasayi"

yayi maganar cikin rauni kamar ze fashe da kuka.
Jinjina kai tayi tace, "ka cigaba da addu'ar tashi ka kwanta "

Tashi yayi ya koma kan gadonta ya kwanta ita kuma ta zauna kusa dashi ta tayar masa da kai da cinyarta sannan ta shiga binsa da nata addu'ar tanayi tana shafa kansa,
A hankali nutsuwa tafara saukar masa yafara numfashi cikin kwanciyar hankali zuwa wani lokaci bacci yayi gaba dashi.

Ido ta zuba masa a zuciyarta tace, "lallai akwai abunda yafaru da Jannah yau ɗinnan kuma ya zama dole na sani dan na ɗauki matakin da ya dace"











*INDO CE..*
[7/27, 12:50 PM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 9*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





Sai da Aba yazo tashin shi su tafi masallaci ya tarar baya nan kai tsaye sashin Ummi ya nufa dan yasan baze wuce can ba yana zuwa ya tarar dashi yana ta shaƙar bacci, "lafiya? kuwa" itace tambayar da yafara jefawa Ummi.

Cikin sanyi tace, "nima tambayar da nayi masa kenan yayin da na ganshi sai dai kasan be zama lallai na samu gamsashahiyar amsa ba, amma banajin lafiya yake yace firgita yake amma be sanar min da abunda yake tsorata shi ba"

Ya ɗan numfasa sannan yace, "shikenan Allah ze mana tsari da koma mene tsashe shi muje mu gabatar da sallah"

koda gari ya waye ma babu irin tambayar da Alhaji da Ummi basuyi masa ba amma ba amsa.

a wunin ranar ko fita beyi ba gaba ɗaya babu wani ƙwari a tattare dashi.
Ummi ce ta kalli Natiee cike da damuwa tace, "zurfin cikin ɗan uwanki yayi yawa Natiee, jiya da daddare beyi baccin kirki ba ya dinga firgita kuma nasan dole akwai dalili amma yaƙi sanar dani baki lura da dawowar sa jiya ba? nasan baya cikin yanayi me daɗi sai dai shi baya cika amsa tambaya koda yasan abu amsar sa ɗaya ce ba komai, amma nasan ke ze iya gaya miki dan haka ki tambayar min shi, na ƙwallafa rai akan son sanin abunda yake damunsa"


Natiee tace, "Ayyah Ummi shiyasa naji jikinsa zafi rau tin jiya da ya dawo ashe bashida lafiya, Allah ya sauwaƙe ni kuwa zan tambaye shi sai dai nima ɗin sai yaga dama yake gaya min abunda yake ransa"

Ummi tace, "amin, eh amma dai ba kamar mu ba ai"

tashi Natiee tayi tana cewa, "bari naje gurinsa tin kafin ya fita"

Yana zaune kan kujera ya rufe fuskarsa da tafikan hannunsa duka biyun har ta ƙarasa inda yake be san tazo ba sai da ta dafa kafaɗar sa sannan ya ɗago idanunsa da suka sauya kamanni ya zuba akanta.

Cikin tattausar murya tace, "Yayana baka da lafiya ko??"

Kauda kai yayi gefe sannan yace, "zauna do Allah bana son ganin ki a tsaye kina samin ciwon kai"

Murmusawa tayi sannan ta zauna ta zuba masa ido tana binsa da kallon tuhuma, suna haɗa ido ya kauda nasa tareda girgiza kai a fizge yace, "bana son kallon nan Natiee"

Tace, "to na dena matsoraci yanzu faɗa min me yake damunka? anya kuwa yau ka ci abincin da muka baka ma kuwa??"

Ya gyaɗa kai alamar "eh" sai da ya furzar da wata zazzafar iska sannan yace, "Natiee dan Allah"

Da sauri tace, " dan Allah me kake son cewa?"

Ya ɗanyi ƙaramin tsaki sannan ya cigaba da bata labarin abunda yafaru dashi a hanya yanayi yana rintse ido yana cije leɓe.

Kasa motsawa Natiee tayi saboda mamaki da Al ajabi duk ilahirin jikinta yayi sanyi zuciyarta ce kawai take bugawa da gudun gaske.

Dariya yayi tareda lumshe ido yace, "kenan??"

Cikin rawar baki tace, "kenan me Jan??"

Yace, "aa bafa wani abu bane kawai ina son cewa kenan da kece lokacin kawai mutuwa zakiyi saboda tsoro, na zata na fiki tsoro fa Natiee ashe ba haka bane"

Fashewa tayi da kuka tana cewa, "baka fini tsoro ba Jan tayaya ma? kaine garkuwata idan ina tareda kai banida wani haufi tayaya zaka fini tsoro kuma?"

Shafar kwantacciyar sumar kansa yayi yana dariya har fararen haƙoransa suka baiyana sai da yayi me isar sa sannan yace, "ba abun kuka bane Natiee gaskiya kin bada mata, kiyi shiru do Allah dan wallahi dariya kukan naki yabani"

Tashi tayi tareda cewa, "tafiya ta zanyi idan na gama kukan nawa sai kazo ka neme ni ko na dawo da kaina amma wallahi sai nayi, yanzu da ace ya kashe ka fa?"

ya ɗan ɗage kafaɗa alamar bata shafe shi ba, yace, "shikenan na mutu muradin ƴan uwana ya cika kinga an wuce gurin, damuwa ta a ciki kawai halin da iyaye na da ƙanwata zasu faɗa shine abunda ze dameni, nasan ko Abana a cikin yayye na ba kowane yake masa kallon uba ba duk ba ƙaunarsa suke ba abun duniya kawai shine suka sa a gaba, ina tsoron ranar da zasu juyar da akalar zalumcin su kan mahaifina"

Da gudu ta fice tana ƙara fashewa da kuka, ya murmusa gami da cewa, "Natiee kenan a dole dai sai kinyi kukan nan"

Zuhra kwance take kan kujera tayi lif a cikin bargo sai rawar sanyi take, Momu ce ta tsaya akanta tana cewa, "Queen? zazzaɓin nan duk akan wannan yaron ne wai?"

Tattaɓe baki tayi tana shirin fashewa da kuka tace, "Idan da ya mutu fa shikenan na dena ganin shi"

Tattausan murmushi Momu tayi ta zauna a kusaa da ita cikin sigar girma da manyance tace, "idan kika ga mutum ya mutu to ba ya mutu ne kawai dan a dena ganinsa ba kawai Allah yayi shi ba me tsawon rai bane bazamu rayu tareda shi ba, ba ya dawo gida lafiya ba? ki kwantar da hankalin ki babu abunda ze faru sai ikon Allah"

Gyaɗa kai tayi sannan tace, "to kicewa Zaheer ya kaini gidan su na dubo shi"

da sauri Zaheer yace, "Queen kinada hankali kuwa?? kinsan adadin sashin da zaki wuce kafin ki isa gareshi? haka kawai kisa ayi masa sharrin da har ya koma ga Allah baze manta ba to gaskiya ba dani za'ai wannan ba"


juyawa tayi ta gyara kwanciya taƙara tattakewa a cikin bargon sai zumɓuro baki take.

Natiee sai da tagama kukan sannan ta zaiyanawa Ummi abunda ya faru kamar yadda ya gaya mata.

Nazari sosai Ummi tayi kafin tace, "maza nema min wayar Ariee kice ya haɗani da Baffi"

Cikin sa'a kuwa tana kira ta sameshi, bayan sun gaisa Ummi tace, "Baffi meye haɗin Jannah da macijin iska?? kuma har yake neman hallakashi??"



















*INDO CE..*
[7/28, 10:09 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*




NA INDO CE..




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*


Na kuɗi ne😂
300 kacal

FREE PAGE


*shafi na 10*






_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





Baffi ya ɗanyi nazari kafin yace, "ba komai bane macijin na gidan su ne ina nufin a gidan nan akai masa aikin, ba nufin kashe shi akai ba kawai anyi ne dan a firgitar dashi kuma sunyi nasara a yanzu haka sun jefa ruɗani da kokonto a tattare dashi, kiyi ƙoƙarin mantar dashi wannan labarin idan ba haka ba zasu cimma abunda suke muradi na zautar dashi"

Ta jinjina kai sannan tace, "zanyi hakan Baffi nagode matuƙa"

Daga haka ta yanke kiran sulluɓar da wayar tayi zuwa ƙasa ta zuba tugumi cikin sanyin jiki gami da damuwa"

Natiee tace, "kinji ko Ummi? na rasa me mukai musu suka tsane mu mahaifi ɗaya ne yayi silar zuwan mu duniya amma sun jajirce wajen ballagazar da rayuwar mu a matsayin su na yayyen mu nakasa gane meye ribar su da yin hakan"

Ummi tace, "Natiee da na fitar da rai daga duk wata ƙauna ta tsakanin mu da Aban amma yanzu na gane babban rashin adalci ne mu kaɗaita kanmu mu barshi, da nayi tunanin saboda shi ake mana haka amma yanzu na gane dan dukiyarsa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment