You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kalmomin da
tafada masa abaya suka dinga dawo mata kamar
anyi recording dinsu. Tabbas ta fada masa wasu
kalmomi.
a gurin da take zaune. Kuma a irin wannan
yanayin na baqin ciki,.
Lokacinda take zubarda hawaye.
Zuciyarsu ke tsananin azabtuwa da son juna!.
take masa iqirarin cewa....Haba yayana walh
hannuwa na bazasu taba iya yin blocking dinka
ba.
Kayi hquri bazan iya aikatawa ba.
Kamar yadda bazan iya guje maka ba. Haka
baxan iya daina sauraronka ba. Idan kai zaka iya
yin blocking dina to ina me baka daman yin
hakan.
To amma kasani Kunnuwana bazasu taba gajiya
da sauraronka ba. Zuciyata bazata taba daina
azabtuwa da sonka ba.
Sannan a kullum zan kasance cikin baqin cikin
rabuwa dakai.
Idanuwana bazasu taba daina son ganinka ba
akoda yaushe. Alqawari ne na dauka bazan taba
auren wani namiji ba aduniya idan bakai ba.
Ashirye nake dana rayu dakai ako wani irin hali
ni bazan taba guje maka ba.
Ina qaunarka yayana qauna irinta har abada.!
Kayi haquri yayana walh bazan iyaba"hannuwana
bazasu iya blocking dinka ba.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 28
==>INNA..ki..taima..keni muryarta na rawa! Shi
kanshi afnan yai matuwar rudewa da furgita
tsoronshi daya karta fadi ta sume kamar yadda
tayi lokacinda yaje gidansu.
Dan haka yai miqe shima akidime yake fadin
SALMA!SALMA Dan Allah ki natsu ki natsu kinji
pls SALMA! Yana qara matsowa shima jikinshi
barin yakeyi,.
Haka take qara Ja da baya tana fadin INNA..kin
ganshin.. KO.. Daidai nan ta tokare da qofa tai
wani irin qara yayinda yaqaraso a guje ya ruqota
alokacinda take qoqarin kifawa. A daidai lokacin
daya ruqota taqara sakin wasu tagwayen ihu
gamida kuccewa ta fada cinyar inna ta
qanqameta sosai tana tsusa kanta a tsakankanin
Inna,!
Gaba daya mamaki ya hana inna cewa komai
ganin jikokin NATA sun afka wani irin yanayi na
rudu Wanda takasa fahimgarsu., batasan sanda
tafara fadin."LAPIA!LAPIA meyake faruwa ne!?
Salma kuwa qara qanqameta take tana fadin
Inna kaina ne kaina inna! Cikina..ke..inna ta
katseta da cewa meya samu kan naki?
Afnan yanajin haka be tsaya yayi wata wata ba
ya zari takalmarsa yabar gidan da saurinsa. Dan
yasan idan yazauna abin saiyafi haka.
Inna ta daqo tana qwala masa kira amma inaaa
dan talikin yayi nisa! Dawo wa tayi kan salma
taci gaba da cewa wai me kuke nufi ne
daganinsa kin fara kuka shi kuma ya gudu gudu.
Kin sakani cikin wasu wasi.
Wani irin sanyi salma taji aranta alokacinda ta
waigo ta tabbatar da cewa afnan baya palon.
Miqewa tayi batare da taceda inna komai ba ta
kwanta kan kujera domin har kanta ya fara ciki
ga wani zazzabi dayke niman kamata.
Inna tai juyin duniyar NaN akan salma tafada
mata gaskiya amma ta dake akan ita kanta ne
da cikinta kawai yake mata ciwo.! Haka ta gaji
ta rabu da ita tace ai idan tai tsami maji . idan
kuma Auren ne bakwaso ai
sai inji. Salma tai saurin tashi ta zauna gamida
cewa wani rin aure kuma.!
Inna ta galla mata harara tace irin na uwaki!
Dole takama bakinta tai cit! Tadan huta nawasu
yan daqiqu tatashi tace zata wuce. Domin ita
kam yau bataji dadin zuwanba ma. Daqyar
tasamu ta isa gida tana tangadi jiri take gani
sosai dan haka tana zuwa ta zube akan kujera
jikin nan NATA ya dafe yayi zafi rauu! wasu
zafafan hawaye ne keta sulalo mata. Momyce
tafito daga sashenta gaqaraso wajenta da Sauri
tana fadin salma lapia kuwa!meya sameki?!.
Tana kai hannu jikinta taji zafi rau!tace
subhanallah zazzabi kikeji haka kuma shine baki
gayamun ba"bari nakawo miki Abinci kici nakira
driver muje asibity.
Momy ta qwalama sumayya kira saigasu sun fito
dukkansu aguje suna dariya. Ganin salma a
kwance yasa sukai tsuru tsuru momy tace ma
sumayya maza kije ki zuboma auntynku abinci
batajin dadi ne. Ba musu ta wuce kicking sai
gata dauke da pleat din kuskus taxo ta dire ma
momy sannan taje firji ta dakko robar faro daya
ta kawo momy tace to tashi kici.!
Taqarayin wani narai narai da ido tace momy
cikina ciwo yake.
Momy tace kiyi haquri kici koda kadanne. Haka
tatashi momy tafara bta abaki. Bai wuce cokali
4 tayi ba kawai sai amai momy ta tallabota da
sauri haka ta dinga kwara amai duk jikinta yai
yaushi. Momy kam duk ta rude tasamu ta
kwantar da ita sannan tamiqe dasauri taje ta kira
habib tafada masa halinda suke ciki sannan taxo
tafara gyara wajen.!ba a dauki lokaci ba habib
ya turo da driver.
Aka kwashesu sai asibity. Suna zuwa aka
karbesu cikin kulawa kasancewar habib yayi
waya tun kafin su iso..Dr ya dubata sosai tareda
wasu yan tambayoyi itakam tadinga jera mashi
amsa. Tagaya mishi cewa takai 2weaks tana
fama da ciwon ciki kadan kadan. Sannan takanji
tashin zuciya lokaci lokaci ga yawan ciwan kai.
Dan hak Dr yasa aka debi jininta da fitsarinta
sannan yahada musu wasu yan magunguna dazai
taimaka mata yace suje gida tafara sha kafin su
dawo gobe a tabbatar da result din da aka
samu.! Momy bata kawo komai aranta
ba"sabanin ni da harna fara wani tunani! Kaji
iyayen katslandan
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 29
==>A dimauce momy ta miqe tana Innalillahi wa
inna ilaihirraju'un Dr karufamun Asiri jikinta ko
ina fari yake.
Yayinda ni da Dr muka saki baki da hanci da ido
duk muna kallonta.!
Mamakin Dr shine shin meyasa momy ta furgice
haka shin bata bataraba da qaruwanda suka
samu ne ko kuwa"
Mamakin salma kuwa shine.. Wani irin ciwo ne
juna biyu dahar momy ta furgice haka take
Neman faduwa.! A tsorace ta kalli Dr tana
qoqarin yimishi tambayar wani irin ciwo ne take
dauke dashi.!
Kafin ta kaiga cewa komai sai ganin momy
sukayi ta sulele aqasa sumammiya!.
A haukace salma tai kanta tana kwarma ihu tana
fadin Dr wani irin cutane nake dauke dashi har
baqin cikinshi yake Neman ya kashemin
mahaifiya"
Shima gaba daya yagama kidimewa yayo kan
momy yana fadin kawai nace mata ne kinada
ciki shine tashiga tashin hankali haka!? Ko
bakida Aure ne dai! Allah dai yasa
ba abun kunya kika daukoma iyayen naki ba.
Cikin wata irin murya salma ke cewa Dr cikin
baby nakedashi!? Yanxu baby ne acikina
taqarasa maganar tareda shafa cikin! Dr yace
qwarai kuwa kina dauke da juna biyu har na
tsawon wata uku babu yan kwanaki!" Ai kafin
yagama rufe bakinshi sai ganin salma yayi ta
kife a qasa da alamun itama suman tayi.!
Topa Dr yaqara rudewa matuqa da Sauri ya fice
yana kiran nurse kamar wani zararre.
Dan Danna akaxo aka kwashesu gaba daya aka
basu gado. Duk iya qoqarinda zasuyi akansu
sunyi Wajen 2 hours Amma basu farfado ba Dr
duk ya gama rudewa da al'amarinsu.
momy ce ma tadinga tafarfadowa tana sake
sumewa."dan Haka Dr ya kira Habib ya fada
masa abinda ke faruwa.
Karkuso kuga daburcewa wajen Habib dan shima
kadan yarage ya sume.
Dan Haka numfashinsa ke fita wani kan wani.
Baccin yayi ta maza da shima kwasarshi zq'ayi.
A kidime ya suri motarshi ya kama hanyar
asibityn yana rafka gudu kamar wanda ze tashi
sama.!
Allah ne dai ya kiyayeshi harya isa lapia. Yana
isa ya kira Dr. Dadauri yazo suka qarasa yanda
su momy suke daidai lokacin momy ta farfado
sukayi ido hudu da Habib kawai saita fashe ta
kuka.
Yaya Habib yaqarasa gabanta shima idonshi sun
kada sunyi jawur. Yace momy dan Allah ki
kwantar da hankalinki ki natsu kar hawan jininki
ya tashi. Pls momy komai ze wuce.
Murya a sarqe momy take magana tayaya
hankali na zai kwanta wannan balq'i ya afko
mana ta Ina zan samu kwanciyar hankali. Kawai
tasake fashewa da kuka shima kifa kanshi kawai
yayi yana zubda hawaye.
Saida sukayi mai isarsu sannan momy ta juyo
tace ina salman take!? A hankali ya dago da
idonsa jawur yace momy tana nan ita bata
farfado ba Drs sunacen suna qoqari akanta.
Gashi kema kinsa damuwa sosai aranki momy ta
wanne kikeso muji. Momy ki dauka wannan Abu
kawai hukunci ne daga Allah kuma babu yadda
muka iya saidai haquri mu rungumi qaddara.
Momy tafara qoqarin tashi yaji bazata iyaba
haka ta koma tana zubda wasu zafafan hawaye.
Nan Dr yaxo yafra duba momy. Jininta har ya
hau sosai akai mata allura tasamu bacci. Habib
yakira Ahmad yafada mishi abinda ke faruwa.
Tab! Haka ya tawo asibityn a fusace da nufin
komai ma zai faru to saidai yafaru dan yau saiya
fadama yaya Habib Wanda yaima salma fyade.
Cen bangaren su hjy safiyya kuwa gidan yacika
da murna domin yaune ranar da yaya Aliyu zai
dawo. An tanadar mishi girki kala kala. Husna
ma datake kwance batada lapia yau daida ta
gyagije sbd murnan dawowar yayan nata.
An tura driver yaje ya daukoshi a airport tare
suka wuce da husna akabar momy da inna A
gida. Basu wani Dade da zuwaba jirgin nasu ya
sauka. Ya kira wayar husnan tace yaya gamu
nan a waje nida driver kai muke jira .yace OK to
ganinan fitowa. Cen husna ta hangoshi yanata
faman waige waige itako sai washe baki take
tadaga waya ta kirawoshi yana dagawa tana
yaya gashinan INA kallonka yace to ai ni....
Kawai daiya hangota tanata dariya da saurinsa
ya karaso shima fuskarsa dauke da murmushi.
Tace ya ya Aliyu kaga yadda ka qara kyau kuwa
gaskiya garin nan ya karbeka.
Yasaki kyakkyawan murmushi Wanda yaqara
bayyana tsantsar kyawunsa gamida cewa yar
Autar mama kenan. ai ni naga duk kin cenja
munne gaba daya ma. Nida na barki yar qarama
kina 8years. Yanxu ko shekarunki nawa ma oho.
Ta murguda baki tareda rangaji dakai tace kai
yaya shrkarun nawa ne ma zaka manta KO.
Yai dariya yace to yar rigima wasa nake miki.
Amma ga dukkan alamu kinyi ciwo dan naga
kamar akwai rama a jikinki.
Tandan murmusa tace yaya kenan ya akai ka
gane. Yce ko Wanda be taba ganinki ba idan ya
ganki yanzu yasan kinyi ciwo. Tace gaskiyarka
ne yaya walh yanxu ma zuwanka ne yasa na
warware sbd murnar ganinka. Yace wayyo yar
Autar umma meyake damunki. Uhm kawai tace
labarin me tsawo ne yaya yanxu dai muje gida
ka huta
Suka qarasa mota suka shiga suka dau hanya.
Sun fara tafiya Amma gaba daya yakasa daure
Abinda yakeso ya tambaya dan Haka yace yar
Autar mama wai ina qawarki ne na dauka tare
ma zakuxo tarbana sai kikazo ke daya!.
Tadan jiyo ta kalleshi tareda cewa wa kenan!
Yadanyi farii da idonsa gamida cewa Salma
mana!. Tace oh kacemin Amarya! Dandanan
dariyarsa ta tsaya ya daure muska yana mata
wani irin kallon rashin fahimta cikin sassarqewar
murya Wanda bemasan yayi ba yace ban gane
Amarya ba!?.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 30
==>Husna tace Eh mana! Yaqara hade rai yace
Wato Aure akai mata ban sani ba.! Husna
tadanyi murmushi tace kai yaya maida wuqar ai
ba'a riga anyi bikinba ma daman ance saika
dawo!. Yadanji sanyi kadan aransa sannan ya
sake cewa to waima salman ne za'aima aure tun
yanxu! Wayema ya fada miki haka!? Tace kaidai
yaya kanada qosawa kabari idan munje gida
zakaji komai. Yace kinyi alqawari tace eh yayana
na kaina.! Haka yahaqura badan ranshi yaso ba
dan yaqosa yaji gaskiyar abinda husna tafada.
Ya qosa yaga ankai gida. Sun isa gida cikin
qoshin lapia murna kota ina. Inna kam bakinta
ko rufuwa bayayi. Ya Aliyu yaje yai wanka yaxo
dining amma duk cin abincin ya gagareshi inna
dasu momy da husna duk sun kewayeshi. Cikin
hikima yace Inna wai mamanki batasan zan
dawo bane?! Inna tace
oh Mamana Amarya ai rabona da ita tun ranarda
sukaxo nan da afnan sunataimin sakarci! Yana
qoqarin kai cokalin abinci bakinsa baisan
lokacin daya aje ba yana fadin Wani irin Amarya
kuma Inna! Tace kaidai ci abinci koma wani iri
ne ai zakaji. Gaba daya yaji ya qoshi dan haka
yamiqe tareda sakin wata yar tsaki mtsw..saiku
cinye abincinku ai.!
Gaba daya suka bishi da ido dan sun gaza
fahimtarsa. Momy tace A a inazakaje bakaci
abincinba yace nifa nama qoshi tin a jirgi. Tace
abincin jirgin wani abun kirkine! To dawo
kazauna ko zakayi amai ne saikaci abincin nan
bazamuyi wahalar banza ba. Murmushi kawai
yayi me kama da yaqe yakoma yazauna yacigaba
da tsakurar abincin. Ya kalli husna yace wai
meya samu wayar salma ne baya shiga! Tace
walh nima
bansani ba tinda tai ciwo ba'q samunta awaya
bansani ba ko wayar baya hannunta ne.! Oh tai
ciwo amma ko agayamun KO! Gaba daya sukasa
dariya sbd yadda yai maganar kamar wani
qaramin yaro! Inna tace kaji shirme banda
abinka idan an gaya maka zuwq zakayi. Yace
amma ai nakira waya nai mata sannu ko!
Anandai suka gama yan ciye ciyensu da firarsu
kowa yanufi makwancinsa domin dare ya tsala"
Wajensu momy kuwa Habib ne yadawo gida ya
kwashe su rufy yakaisu gidanshi.!fadila tayi tayi
yafada mata meke faruwa Amma yace mata
kawai momy ne batajin dadi; sannan yakoma
asibity cen suka kwana shida Ahmad. Yaya
Ahmad tinda yaje yaga halinda momy ke ciki
yakasa gayama Habib gaskiyar lamari dan gudun
qarya hurama abin wuta.! Momy tadan samu
sauqi dan qin zama tayima agunda aka ajeta
takoma gun salma saidai takasa daina kuka duk
in ta kalleta. Salma ta farka amma batasan inda
take ba har yanxu likitoci ne ke zarya akanta.
Sai fizge gizge take. Hakan yaqarasa jinin momy
ya hau sosai haka suka kwana ba barci.
Habib ne zaune akan darduma bayan ya idar
da sallah yayi jugum yana tunanin abinda Dr
yafada!.
Idan har kunason tayuwar yarinyar nan to mafita
daya CE! Kodai azubda cikin nan kokuma a nuna
mata cewar kuskure akayi wajen fadar
sakamakon!sannan kuje kucigaba da lallashinta
kuna nuna mata mahimmancin yarda da qaddara!
Sbd idan ba haka ba. duk ranarda ta fahimci da
gaske ne"zata iya shiga halinda yafi na yanxu.
Domin kuwa me ciki ba'asonta da damuwa
hawan jini zai iya kamata tun tana yar
qaramarta.
Dan Haka ko wanne daga cikin abinda kuka zaba
me hadarin gaske ne!
Wasu hawayen baqin ciki suka gangaro masa.
Aransa yace Tabbas dazaiga Wanda yaci
mutuncin qanwarshi da babu abinda zai hana
ya shaqeshi harsai ya mutu"
Wayarshi tai qara ta katseshi daga tunaninta ya
fada. Aliyu ya gani da numbernshi ta Nigeria ya
dauka da Sauri gamida yin sallama! Ya aliyu ya
gaisheshi cikin ladabi sannan yace yaya.. Hafin
yagama fadi ya Habib yace yaushe ga dawo ne
babu kodan sanarwa! Yadanyi murmushi gamida
cewa walh jiya nadawo aina dauka mama ta fada
muku zan dawo! Yace kai baka fada mana ba sai
ita" yace to babban yaya afwan yanxu dai ya
madam yasu momy! Y Habib yai shiru yama rasa
abinda zaice.! Daga bisani yace uhmm Aliyu
walh gamu nan ma A asibity salma da momy
duk basuda lapia!
Cikin tashin hankali yace subhanallah meya
samesu!?
Cikin rawar murya yaya Habib ke magana. Zan
gaya maka Amma gidanku babu Wanda yasani
Inna bata saniba momynku ba bata sani ba! Dan
Allah karka fadama kowa dan kasan inna zata
iya tada hankalinta hawan jininta yazo yatashi!
A rude ya Aliyu yaci gaba da cewa fadamun nayi
alqawari bazan fadamasu ba!
Ya Habib yacigaba da cewa fyade akaima salma
kusan wata uku dasuka wuce. Sanadiyyar barinta
da akayi ita kadai agida wani mugun yasamu
damar zuwa ya aikata lalata da ita! A wannan
lokacin salma tasha wahala sosai kwananta 3 a
asibity aka sallameta!
Shine yanxu akai gwaji akaga tana dauke da
ciki sanadiyyar haka ne Itada momy suke
kwance yanxu haka salma batasan yadda kanta
yake ba!"
Tinda aliyu yake bai taba shiga tashin hankali
irinna yau ba! Daga lokacinda yaji kalmar fyade
yayi tsananin gigicewa Wanda bai ma iya
fahimtar me Habib din yaci gaba da fadi ba"wani
irin juwa yafara dibarsa Allah yasa akan gadonsa
yake!
Shin wai mafarki ne yake! Ko kuwa gaske ne
abinda kunnuwansa ke jiyo masa!
Masoyiyarshi"abin qaunarshi" wacce yadade
yana tarairayar soyayyarta"
Wacce yarayu da tsananin qaunarta tun kafin
tasan kanta! Wacce yake burin tazamo uwar
yayansa"
Jinin jikinshi Salmat ita akaiwa fyade harma
tana dauke da ciki!?" innalillahi wa inna
ilaihirraju'un.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 31
==>Cikakken labari...! Alhaji Suleiman shine
Babban d'a awajen inna sai Alhaji Abdullahi
sannan Alhaji Abubakar Wanda a yanxu suke
kira da Abba! Haifaffun yar Kaduna ne. su uku
Allah yaba Inna kuma duk maza. Bayan rasuwar
mahaifinsu wato malam sani.
Inna ta koma wajen babban 'd'anta da zama
wato alhaji sulaiman.
Shine yacigaba da daukar nauyinsu" bayan
rasuwar malam sani da shekara1 Allah yadauki
rayuwar alhji sulaiman wajen tafiya tafiyan
neman halak da abinda zasuci a hanyar tafiyarsa
lagos ne yai Accident Allah yakarbi rayuwarsa!
Lokacin yanada matarshi daya hajiya Safiyya da
'ya'yansu biyu" wato Aliyu da husna. Tsakanin
aliyu da husna akwai tazara sosai dan harsun
fidda rai dasake samun haihuwa dan shima aliyu
sun jima basu sameshi ba!.cikin ikon Allah saiga
cikin husna anyi murna sosai!" Husna tanada
shekara 5 aduniya mahaifinsu yarasu. Daga nan
alhji abdullahi shiyacigaba da daukar nauyin
gidan harda dawainiyar makarantar Abubakar har
yakammala karatunsa'! alhj abdullahi yanada
matarshi me suna hjy Aisha wacce suke kira da
momy sunada yaransu hudu4 Habibullah Ahmad
salma sumayya! Habib shike gaba da aliyu Dan
yabashi wajen 6years sun taso tare jininsu ya
hadu sosai! Alhaji Abdullahi shiyaci gaba da
qoqari har Abubakar yasamu aiki" lokacin ne
yasamu matarshi mai suna zainab" cikin ikon
Allah tasamu ciki ta haifi santaleliyar yarinyarta
wacce aka rada ma suna sadiya!
Lokacin habib nada shekara 10 a duniya aliyu
kuma Nada shekara 4". Bayan 2years aka haifi
afnan aka sa mishi sunan mahaifinsu
aliyu!..wato Suleiman. Shine ake kiransa da
afnan.! Cikin ikon Allah habib kammala
secondary school dinshi aka turashi maleshia
acen yayi degree dinsa yadda yadawo amatsayin
Cikakken engineer.!
Lokacinda yadawo ne yayi daidai da lokacinda
sadiya ta kammala secondary school tanada
shekara 17" afnan kuma yana Ss1 shekaransa
15.
An haifi salma da husna yanda shekarau8
aduniya! Kwana 4 salma tabama husna domin a
jejjere aka haifesu" salma tun tana qaramarta
sun shaqu sosai da afnan idan yaxo gidansu
dagyar ake banbareta daga jikinsa!.
Yaya aliyu ne ma basu wani saba ba hasali ma
tsoronshi takeji danshi yanada fada kuma
bayason yawan rigima. Saidai yana masifar
tattalinta bayason yaga wani Abu dazai bata
mata rai"baya sati baixo yaganta ba tareda
tsarabar kayan ciye ciye,
Ranar wata Saturday Abba da dadynsu salma
suna zaune a palo yadda yakirashi domin
tattauna wani muhimmiyar magana.!
Dady ne ya dubi Abb yaci gaba da cewa..!.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 32
==>Ba komai yasa na kira ka ba illa wata
alfarma danake nema kuma nake ganin yadace
mu qara qulla danqon zumunci!
Ina nema ma Dan wajena Habibu auren yarka
sadiya domin na yaba da nutsuwarta kuma na
tambayi yaron nan yafitomin da wacce yakeso
Amma ya nunamun shi babu wacce yakeso
shiyasa nace toni zan duba mishi wacce tadace
kuma naga babu wacce tadace dashi kamar
sadiya. Dan haka ina nema mishi Aurenta idan
har babu Wanda takeso!
Murmushi kawai Abba yayi Wanda zamu iya
kiranta da yaqe gamida cewa Gaskiya yaya naji
dadin wannan maganar ai wannan basai kanemi
shawarata ba dan kuwa sadiya yarka CE kana da
damar zaba mata mijinda yadace da ita
ballantana kuma wannan yaro me hankali kuma
dan uwanta"
Ai kaima me bashi ne basai ka nemi shawarata
ba!
Dady yai murmushi cike da jin dadi yace a a
wannan ai haqqinka ne yazama dole na nemi
amincewarka kuma naji dadin yadda kakarbi
maganarnan yanxu saika sanarma iyalinka kuma
a tambayi sadiya idan ta amince.
Nima zan sanarda iyalina kaga idan komai ya
daidaita ma basai ankai abin da nisa ba"
yaqarasa maganar tareda qurama Abba ido!
Abba yadan sosa qeya yace gaskiyane yaya ai
dama ka yanke ranar Auren kawai tunda babu
wata matsala nidai daga gareni."
Dady yace a a baza'ai haka ba a duki kakkin
yarinya gwara anemi amincewarta dan Bazanso
arakura mata ba.
Abba yace shikenan yaya za'ayi yadda kace
amma nasanma babu wata matsala"
Nizan koma yaya duk yadda mukayi zakaji".
Dady yace to yayi kyau nagode sosai Allah yabar
zumunci.
Abba yace nikeda godiya yaya. Tareda miqewa
sukai sallama ya nufi gida zuciyarsa cike da
wasuwasi!
Lokacinda Abba yasanarma umma maganar tayi
farin ciki sosai haka ma bangaren su dady momy
tayi farin ciki matuqa kuma tabada goyon baya
Dari bisa dari!
Saidai kuma a bangaren gwaskayen babu komai
sai tarin damuwa Dan Kuwa habib hankalinshi
yayi matuqat tashi a lokacin da yaji za'a
hadashi da sadiya!
Danshi gani yake an rainashi da wannan yar
tsigigiyar yarinyarne za'a hadashi.
Saidai kuma haka nan ya daure ya amince da
zabin iyayensa batareda ya nuna qin
amincewarshi ba.
A bangaren sadiya ma haka.
Dan tayi kuka kamar ranta zai fita dan ita bawai
sonshi ne batayi ba Amma tana matuqar jin
tsoronshi dan bata cika ganin dariyarsa ba,
Tunaninta kawai ta yaya zata zauna da yaya
Habib!"
Ba'a jima ba aka tsayar da biki sati2 tunda aka
sa ranar bakin bata sashi a idonta ba sai
ana sauran kwana3 yazo shima a daddafe yake
tambayarta nawa take buqata Wanda zatai
hidima.
Tace mishi bata buqatar komai. Besake cemata
komai ba ya Ciro check din dubu dari biyar ya
miqa mata.!
Ta Amsa tareda dubawa ta ware ido gamida
cewa yaya ai wannan kudin sunyi yawa babu
abinda zanyi dasu!
Shiko gogan naka harya juya baya yana shirin
barin wajen yatsaya cak batareda ya juyo ya
kalleta ba. Sannan yace..!
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 33
==>Sannan yace idan kinyi Abinda zakiyi ki
zubar da sauran.!
Ya wuce abinsa yana qoqarin Ciro keys din mota
a aljihun wandonsa!
Yaqarasa cikin nutsuwa ya bude motarshi yacika
rigarsa da iska. Inda yabarta nan tsaye a Gardine
riqe da check din daya bata!
Wasu zafafan hawaye ne suka cika idonta fal!
Suna qoqarin gangarowa.
A zuciyarta tace yanxu A haka ne zamu zauna
toya zanyi kenan idan aka kaini gidanshi?!
Tasa mayafinta ta goge hawayenda suka wanke
mata fuska.
Sannan ta shige cikin gida cikeda tunani iri iri.
Ranar Saturday aka daura auren sadiya da habib
. yan uwa da abokan arziki an taru sai murna
ake! Kasancewar shine Wanda yafara yin Aure a
gidan.; shiko Habib ba wata gayya yayi ba dan
dayawa abokansa ma be sanar musu ba.
Dan shidai a tunaninsa wannan ba Aure yake ba
nan gaba dai zaiyi Aure.
Ankai amarya dakinta. Gida yayi kyau sosai ba
yabo ba fallasa.
4bedrooms ne akwai babbar Palo ga fadin tsakar
gida. Daga cen wani bangare kuma Swimming
poll ne da dan bukka wajen shan iska !.
Bayan biki da 1month Aliyu yafara shirin barin
qasar zai tafi qasar waje a cen zai kammala
karatunsa! Dady shiya dauka nauyin
komai"lokacin su salma da husna zasu shiga
Primary1. A lokacin da zai tafi ne ana gobe yaxo
gidan su salma yima momy sallama.
Yana Zaune a palo suna gaisawa da momy salma
tadawo daga school ta shigo da gudu da fada
jikin momy tana fadin wash momy nagaji INA
abincina"
Kafin momy tace wani abu muryar yaya aliyu taji
ya daka mata tsawa.. Ke bakyajin magana
karyata zakiyi ne!? Shiyasa nakeson Sumayya da
tafiki sanin yakamata. Da Sauri ta zame daga
jikin momy gamida juyowa ta bata rai ta dasa
mishi manya manyan idanuwanta masu kwantar
da zuciya. Ko qiftawa batayi. Tana turo baki.
Saida yadanyi murmushi acen cikin ransa!
tabbas yana tsananin son wannan kyakkyawar
yarinyar Allah dai yabashi ita yafada a cikin
zuciyarshi!. A zahiri kuwa qara hade rai yayi
gamida dubanta yace. Ke bakida kunya ni kike
murgudama baki ko?
Momy dai sai dariya take musu daman sun saba
wannan diramar . aiko yana tafiya ta fara
surutai.
Walh ni momy yaya Aliyun nan haushi yake bani
sai yaita ma mutane fada.
Da yaya afnan ne yaxo baya maun fada!
Momy tace to ai kece ba kyaji shiyasa yake miki
fada. Tace to kawai dan nahau jikinki shikenan
seyace in sauka.
Ni gara ma yatafi yaba mutane waje yaje Cen
taita musu fadan.
Momy tace tafi cen rufemun baki. Wato har ma
so kike yatafi ko. To bazai tafi dinba. Tashi
kibani waje marar kunya kawai ba yayanki bane.!
Wucewa tafi tana kumbura baki. Shiko yaya
Aliyu daga nan gidan ya Habib ya nufa .saidai
be sameshi ba dan Haka ya yanke shawarar
kiranshi a waya ko kuma ya tura mishi text dan
kuwa akwai muhimmiyar maganan dayakeso
yafada mishi.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 34
==>Haka kuwa akayi yana isa gida ya kirashi a
waya suka gaisa yace Babba yaya naje gidan ka
bansameka ba. Daman naje ne nai maka
sallama.
Nandai sukasha fira suna shirin yin sallama ne
ya aliyu yadan Sosa qeya yace yaya daman...
Sai kuma yafara uhm..uhm.. Daman.. Yaya
Habib yace mene ne kuma kaketa wani
uhm.uhm. kafadamun mana. Yadan fara kame
kame sannan yace daman.. Yaya..wata alfarma
nake nema.!
To fadamun mana mene ne inji ya Habib kenan!
Yaci gaba da magana yana sassarqewa kamar
wani marar gaskiya. Daman..yaya..so So... nake
ka kulamun..da salma.sosai. kafin nadawo pls!
Ya idasa maganar yana shafa qeyarsa!.
Yaya Habib ya fashe da dariyar da be shirya
yinta ba. Cikin dariya yaci gaba da cewa shine
kaketa wani inda inda kamar wani me
koyon magana!
Kawai dai kacemin kana ciki." To ka kwantar da
hankalinka kamar kayi baquwa ta mutu! Zan
kula maka da salma Kana dawowa zan baka
abunka!.
Sanda kansa qasa yayi kawai jikeda jin kunya
kamar yana gabanshi. Tabbas yaji dadin yadda
yayan nashi yayi saurin fahimtarshi.
Nan yaya Habib yaita tsokanarshi harsukai
sallama. Washe gari jirginsu ya daga.
Yatafi da tsananin farin ciki Dan yasan cewa a
yanxu salma tazama tashi duk sanda yadawo
Za'a aura mishi ita.
Bangaren Amarya sadiya kam zaman babu dadi
dan yaya Habib gasata yake kamar waina.
Kullum cikin kuka take Amma takasa gayama
kowa abunda ke faruwa!
Babban abunda yake qara qona mata rai idan ta
tuna shine.. Ranar Daren farkonta yadda Yaya
Habib yaxo mata a bushe babu ko dan kazar nan
da ake kawoma amare Babba abin baqin cikin
ma yadda yaxo bako kunya ya tumurmusheta yai
mata hawan qawara babu wani alamun tausayi
haka yai mata jage jage saida yaga bata
numfashi. Sannan washe gari ma haka yasake
yimata akan raunin jiya. Haka ya jera kwana7 be
daga mata qafaba HQ ya kumbura yai sasul
gashi batasan yadda zatayiba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 35
==>A kwanakin da salma tayi gidan aunty sadiya
ita kanta ta fahimci ba dadin yayan nata takeji
ba. Dan kuwa wata zubin a gabanta yake
balbaleta da fada kokuma tayi
abu ya gwasaleta.
Tun aunty sadiya tana boye mata har yakai abin
yawuce a boyeshi dan salma tagama fahimtar
komai.
Hakn yasa sadiiya tadena wani boye boye ta
kirata daki ta lallabata tace kota koma gida
karta sake tagayama wani cewa basa zaman
lapia da yaya habib.
Salma dai ranta baiso ba dan taso taje tabaiwa
momy labari. Kwanan ta 4 a gidan tace ita gida
zata koma ta gaji.
Aunty sadiya bata so hakan ba dan tana rage
mata damuwa sosai!
Haka taci gaba da zama cikin kadaici ta takura
da rashin samun kulawa wajen yaya Habib. Tana
shirye shirye komawa karatu dan ita dama harta
qosa tafara zuwa makaranta ko zata huta da
jarabar yaya Habib. Kawai saita fara laulayi.
Yaya Habib ne yakaita asibity akai treatment
dinta aka tabbatar mishi tana dauke da ciki
wata2.
Murna wajen yaya Habib ba'a magana" dan shi
Allah ya jarabceshi dason yara. Dahar yafara
tunanin ko juya ya auro sbd ya qosa yaga
jininsa!
Tun daga ranar ya Habib yafara tattalinta aiki
ma yahanata yi. Idan yaxo yaga tana wani abun
shizai karba yacigaba dayi ko kuma suyi tare.!
Ita kam harga Allah taji dadin wannan cikin dan
ya gyara zaman takewar Auren su. Itace har take
ganin dariyar yaya Habib. Ta kwanta jikinshi tayi
bacci yana tarairayarta tai amai ya wanke. Tai
mishi shawaba ya rarrasheta. Wannan abu yana
mata matuqar
dadi.! Dan ita harji take kamar ta zauna da
cikin" dan haka taita addu'a Allah yasa suci
gaba da kasancewa cikin farin ciki haka."dan a
yanxu ji take tana tsananin qaunar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment