You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka
husna tace inna inaga yashiga wanka Ne ki
zauna kan wancen kujeran mirror din nikuma
indan gyara mishi dakin kafin yafito.yanadaga
toilet yajiyo murya Amman yarasa gane ko
waye.dan haka yaketa sauri yagama wankan.
husna kam tanata faman gyara ko ina saidata ta
kimtsa mishi tana cikin linke bargo sai gashi
yafito dagashi sai dan gajeran wando da farar
singlet gashi kwance a jikinshi kota ina.
Tsayawa yayi bakin koqar yana kallonta kamar
me shirin dukanta wani irin haushi yacikashi
aranshi yace kya gama haukanki danni walh ko
za'a kasheni ne bazan aureki ba saidai duk
abinda zai faru ya faru tinda ga inna ma yanxu
za'ayita ta qare. Yaqaraso bakin gadon ya
zauna.ya kalleta ido cikin ido ta Sauri tai qasa
da kanta batasan sanda ta saki bargon ba sbd
tsabar kunyan dataji. Tsigar cikinta duk suka
tashi. hannunta har karkarwa yake. Inna ta kalli
afnan tace wannan wanka naka kamar ana cenja
fata tin daxufa muke nan azaune.yai wani dan
malalacin murmushi yace to Inna wama yabaku
izinin shigomin daki duk kun hargiysamin daki.
Husna tai dukta tsargu dan tasan da ita yake
daqyar ta jawo jiki tadawo kusada inna
Inna tace oh abinda zakace kenan dan an gyara
maka dakin.to ai gobe ma rana ne. Husna tace
yaya ina kwana?ko kallonta beyi ba saida inna
tace bakajiba qanwarka tana gaisheka yace oh
lfy.tace ya jikin?ya harareta yace wai cemiki
akai banda lapia ne!?
Inna tace oh
Ashema lapia kake kasa muka taso tindaga gida
mukazo gaisheka to aiko kaizaka maidamu
gida.afnan yace inna ni daman inason ganinki
dan akwai magananda zamuyi
Tace to ina jinka.afnan ya kalli husna yace pls
abamu waje ko. Sumui sumui tafice tai palo su
momy sukace lfy harzaku wuce ne? husna tce a
a inna suna magana da yaya ne. Afnan ya dubi
inna yace inna dan allah ki taimakeni kisa Abba
ya auramin Salma. Walh ni salma nakeso ba
husna ba kuma salma tana sona kitaimaka kisa
baki Abba yabarni na aura salma walh inna
salma itace rayuwata yaqarasa maganar hawaye
kamar zasu zubo a idanunsa. Inna tai ajiyar
zuciya tace to afnan kasandai halin mahaifinka
ba'a iya kaudashi akan abinda yai niyya indai ba
wani ikon allah ba.
Amma zanyi maka qoqari afnan nima nafisonka
da Maman kasha kuruminka zanyima Baban
naka magana kaji ko
Afnan ya sauke numfashi ya dafa qafar inna
yace kai inna dakin gamamin komai walh.
Dan allah ki qoqarta dan walh idan ba'a
auramun salma ba akwai matsala inna.,
Tace to kaita addu'a idan Allah yasa matarka ne
saikaga anyi.
Yanxu bari naje nasamu Baban naku muyi
magana..
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 20
==>Afnan yai saurin cewa a a Inna ba yanxu ba
kobari saikin tafi gida saikisa akira miki shi
yazo kuyi maganan.tace to shikenan zan
kirashi.yanxu ya jikin naka?yace alhmdllh.
Inna tace to ai saikaxo kamaidamu gida ko tinda
kawarware. Yce to inna daman walh inaso nafita
su Abba sun boyeni agida sun hanani fita. Yanzu
bari nashirya na kaiki ammapa wancen qazamar
bazata shigarmin mota ba.inna tace wacece
qazamar afnan yace yar rakonki mana. Inna tace
lallaima yaron nan husna dince qazama to aiko
baka isaba saita shiga. Yai murmushi yanata
shirinshi.inna tamiqe tace ina jiranka a palo tayo
waje.shiko yahau shirye shirye yana gamawa
yayo palo duk suna zaune hardasu aunty sadiya
anata fira da Inna. Yana shigowa palon umma ta
dubeshi tace maza kaje dining ga abincinka cen
kuma kasha magani.
Inna tace kaisauri kagama kakaimu gida inaso
inyi bacci.,qarasawa yayi dining din yazauna
Abba ko yace haba inna ai bashida lapia kibari
idan zan wuce office saina saukeku.inna tace
shikenan ma kaizakafi lallabani dan wancen be
iya tuqi ba.yace to aini daman yanxu zan wuce
kutashi kawai muwuce.,
Suka tashi itada husna suka bishi abaya
Afnan kam jiyayi kamar ya hadiye ransa don
bacin rai da takaicin rashin fitanda beyi
ba.amma aranshi yace yau donene yafita kota
halin qaqa saiyaje yaga salmanshi.
Sadiya ta miqe zata wuce daki momy ta kirawo
sunanta tsayawa tayi ba tareda ta waigo
ba.momyn nata tace kinyima afnan din ya jiki
kuwa?!juyowa tayi tace oh sry fa ya jiki afnan?
Ji yayi wani dum kamar ta buga mishi dutsi
akai.yace da sauqi aunty amma be iya hada ido
da ita ba.ta juya abinta ta wuce dakinta.
Kadan ya iyacin abincin yasha magani sannan
unmansu tace nizan shiga inyi wanka kaima
yakamata kakoma daki ka kwanta. Dasauri yace
to umma.daman so yake tabar palon dan
yasamu ya fice.tawuce abinta
Shima yatashi yafice da saurinsa bema tsaya
daukar mota ba yanufi get dasauri me gadi
yataso yana gaisheshi tare da tambayanshi ya
jiki..dan ko ba a gaya maka ba dazarar ka kalli
afnan zaka tabbatarda yaji jiki dan yayi rama
sosai.afnan yana fita ya samu me adaidaita sahu
be sauka a ko inaba sai qofar gidansu
salma.uhm afnan kenan baya ko tunanin me
zaije ya tarar.
Said a ya isa ne yasauka ya biya me adaidaita
sahun sannan wani irin fargaba da tsoro ya fado
masa yarasa ma yazaiyi ya shiga gidan kuma
idan yashiga da wani ido zai kalli momy da
salma. Shin meye mafita juyawa zaiyi ko kuwa
dai Shiga zaiyi?!
Su momy kuwa tinda gari yawaye gidansu cikin
baqi yake yan uwa da abokan arxiki masu zuwa
gaisheda salma., suna zaune a palo momy da
salma sai Khalid sai hjy safiyya Maman husna
sai qawarta sameera sunata fira salma tadan
kashin gida akan kujera 2 setter Wanda yake
person din qofar palon. su rufy da sumayyakuwa
duk sun tafi school.
Salma ta dube baki zatayi magana muryar data
jiyo ana sallama ne ya datseta daga maganar da
take shirin yi.tareda tsantsar fargaban muryar
data ji.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 21
==>Momy ne ta amsa sallamar tare da cewa
wanene shigo mana.,afnan kam tsoro yahanashi
shigowa sai wani dan maqe maqe
yaketayi kamar mara gaskiya.koda yake daman
Mara gaskiyar

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 22
==>Momy ta juya da Sauri tafara buga qofar tana
fadin salma lapia.!ki bude qofar mana! Qara
lafewa tayi akan gadon momyn nata tana wani
irin kuka me tsuma zuciya.! Suna jiyo sautin
kukanta har palo. Momy ta juyo jiki a sanyaye ta
kalli afnan tace masa afnan kayi haquri tinda tai
ciwon nan abu kadan yake sata firgici nikaina
narasa gane kanta kwata kwata. Yanxu katashi
kaje gida kahuta dan kaima nasan bakajin dadin
jikinka kawai qoqari kayi kaxo gashi kuma
ansamu akasi yar uwantaka afirgice tace.
Katashi ka lallaba kaje gida kaji! Hannu yasa
a aljuhu ya ciro handkerchiefs ya goge
hawayenda ke fuskarshi sannan ya miqi yace to
momy barin koma Allah yabata lapia jiyawanda
yayi ne ya kula Ashe ma basu kadaine a palon
ba hjy safiyya da sameera sunyi jigum jigum sai
kallon ikon Allah suke. Afnan ya sauri yakoma
ya zauna sai yanxu yatuna Ashe be gaisheda
kowa ba! Sannan ya sanda kanshi qasa yace
momy na manta bamu gaisaba ina yini. Tace
lapia qalau yajinka ya sadiya da gajiya. Yace
lapia lau sannan ya juya yagaisheda hjy safiyya
suka gaisa da sameera yai musu sallama ya
tashi yafice cikeda jimamin abinda ya faru! ,
yana fita momy ta juyo ta cigabada kiran salma
dan ta bude qofa amma shiru taqi budewa. Da
Sauri momy ta nufi dakin salma ta dakko spare
key din yakaye wajen salman taxo ta bude qofar
tashiga. Su hjy da sameera duk suka biyo
bayanta., salma na qwance ta kifa kanta a pillow
momy ta zauna kusa da ita ta janyota jikinta taji
jikin tana yadau zafi sosai tace subhanAllah
salma zazzabin kuma dawowa yayi itakam ta
runtse idonta kamar wata me barci.hjy safiyya ne
tace nifa wannan Abu ya dauremin kai.ana cikin
firq lapia kawai yarinya daga ganin mutum saita
firgice kamar taga mutuwa?!momy tace kedai
ganemin hanyan nima narasa gane kanta amma
inaga kawai zafin tsiwonnan ne har yanxu be
saketa ba. Momy ta dubi sameera tace dan Allah
sameera taimaka ki miqomin place dincen da
Kofi na hada mata tie,.sameera tace to momy
bari zan hada mata dandanan aka hada mata tie
daqyar momy tasamu ta bata sannan tabata
magani bacci ya kwaaheta. Nan su hjy sukaima
momy sallama kowa ya watse ,zuwa cen saiga
su rufy driver ya dakkosu daga school! Suna
zuwa sukai dakin salma momy ta dakatar dasu
da cewa kar Wanda yasake yashiga batajin dadi
tasamu bacci kuma zakuje kutasheta. Haka suka
tsaya duk basuji dadi ba sudai kwanan nan duk
gidan be musu dadi abokiyar firansu ba
lapia..suka nufi dakinsu suka cire uniform dinsu
sumayya tashiga kitchen ta debo musu
Abinci suka baje suka kama ci.,
Afnan kam daqyar ya iya kaiwa gida yashiga
palonsu yana dangadi kamar Wanda
yasha ya bugu.yana buga qofar palo yai sa'a
kuwa aunty sadiya tana zaune tana kallo tataso
tabude batace mishi qala ba ya wuce sashensa
yana zuwa yafada kan gado kamar Wanda
akaiwa duka! Umma tafito daga daki tace ma
aunty sadiyA wai har yanxu yaronnan bedawo ba
kuma anata kiranshi yaqi dagawa. Anty sadiya
tace umma yanxu yashigo daman yanzu zanza
nafada miki yadawo.
Umma batace komaiba tanufi sashensa ranta a
bace.
Tana zuwa ta fada dakinshi yai saurin juyowa
danganin Wanda yashigo tazaun ta dubeshi rai
ahade tace ina kaje baka iya gayamun zaka FIta
ba?inace ma wai ba abbanku yace karkaje ko
inaba!?
Afnan yace to umma yanxu shikenan ni bazan
fitaba saidai naita zama agida kamar mace
yaqarasa maganarashi ashagwabe.harsaida
yabama Umma tausayi tace to ai kozaka fitan
saika bari kaqara samun sauqi ko!yanxu dai bari
akawo maka
abinci kaci kasha magani.
Tamiqe tai kicking ta kamo masa abinci daqyar
tasamu yaci haka taita lallashisa kamar qaramin
yaro. Ranar dai haka ya yini daga tunani sai
kuka rayuwa ta juya masa baya.
Misalin qarfe 6:30mp saiga yaya Habib yaxo
yasamu salma tanata bacci nan yai sallah
sukaita fira da momy rufy da Khalid duk sun
baibayeshi sunatamai surutu. Sumayya kuwa
tana gefen momy. Sai ganin salma sukai ta
shigo dakin sumui sumui ta nemi waje ta zauna
akan kafet dinda Habib ke zaune ta lafe jikin
kafadarshi kamar me shirin yin kuka. Ya kalleta
cikeda kulawa yace sister lapia kuwa waya
tabamin ke duk naganki wani iri ne!? Tai wani
irin gajeran murmushi Wanda zamu iya kiranshi
da yaqe tace yaya ba komai.
Yace haba sister kifadamun gaskia mana! kinsan
banason naga kina damuwa naso na daukeki ki
koma gurina momy ta hana amma ba komai
yanxu haka nasamar muku bodyguard gobe insha
allahu zai fara zuwa dan haka ki kwantar da
hankalinki insha allahu babu abinda zaisake
zuwa ya cutarda rayuwarki ki natsu ki manta da
komai kinji my dia sister kinga kunkusa fara
exams dan haka ki maida hankali akan karatunki
Allah shizai saka miki kuma shizai tona asirin
duk wani me nufin cutar mana dake kinji KO!,
Runtse idonta kawai tayi sbd hawayenda ke
qoqarin gangaro mata bata iya cedashi qala ba.
Momy tai ajiyar zuciya tace ai inaga exam
dinnan ma da wuya idan zata iya har yanxu
jikinta be wani qwari ba gashi kuma batason cin
abinci.
Ya Habib yace to kingani ko sister keda kiketa
murna zaki shiga ss3 amma bazaki dage kidinga
cin Abinci kisamu lapia ba. Yanxu yaushe ne
exam din naku?! Sai lokacin ne ta iya bude baki
tai magana tace ranar Monday ne"yace to kinga
ashema jibi ne lallai kuwa idan kika tsaya sanya
za a tafi abarki idan kuwa kin dage dakun gama
exam zan cenja miki makaranta zan maidaki
Turkish kuma zan samar miki driver dazai dinga
kaiki yana dawo dake. Da sauri tamiqe daga
jikinsa tana murmushi harta manta da
damuwarda take ciki tace momy ina abinci
nah!?.kafin momy tace wani abu Sumy tai tsalam
tace to yaya ni kuma pa?"tareda turo baki kamar
alade ya hangi kashi....! x
===>BUTULCI KO SO!!!? Part 23
==>Gaba dayansu suka kwashe da dariya salma
ta dubeta tace kedai kishi kike to saidai ki mutu
dan yarinya bazanyi makaranta daya dake ba.
Yaya Habib yace to duk ya isa haka kema idan
har kika dage sosai zan kaiki duk mkarantar da
kikeso kinji yar autan mama! Ta tabe baki cikin
shagwaba tace yaya nima Turkish din nakeso
asani"kafin tagama rufe baki salma tace aiko
baki isaba walh yaya saidai asamar mata
wani".ya dubesu yace to duk Ku kwantar da
hankalinku kowa za'a sashi a inda yadace
banason rikici kunji"rufy
tace Dady muma axenja mana! Murmushi yayi
yace wato abin naku yazama qasa kenan ko;to
duk an fasa tinda abin hakane kowa ya zauna a
inda yake!.ya dubi salma ya daga maya gira
alamun karta damu sannan yace kije kici abinci
kisha magani kinji ko.ni yanxu zan wuce
gida"yasa hannu a aljuhu ya ciro kudi ya
miqama kowa nashi sannan yaba momy nata
Wanda itama batasan ko nawa bane sannan
yatashi yai musu sallama ya wuce.
Salma tatashi tai dakinta taje tai sallah sannan
ta tashi tawuce dining taga an shirya komai
kowa yaci iya cinsa.!aranta tace lallaima anraina
komai saida akaci aka rage me makon atasheni
duk an barmin kwantai"
Haka nan dai ta tuttura tinda tanajin yunwa
kuma ga abinda yayanta yace mata. Tana
gamawa momy tazo tabata magani tasha sannan
tace bari taje tai wanka ta kwanta.
Tashiga toilet ta watso ruwa sanna ta nemi wani
riga da wandonta na bacci tasa ta haye gado.
Sai lokacin tunanin wayarta ta fado mata. To
inama ta jefa wayar?! Saita tuna Ashe fa
lokacinda tatashi daga bacci taga bataga su
sumayyaba wayarta ta janyo ta kunna data ta
hau WhatsApp tana cikin chatin taji jikinta duk
babu dadi sbd tagama period kuma batai wanka
ba dan haka tace bari taje tai wanka Wanda
shine sanadin fadawanta hannun afnan. Kuma
tindaga nan batasake ganin wayar nata ba.itadai
tasan akan gado ta ajiye to kowaye yadaukar
mata waya oho!? Tambayar da takasa samun
amsarta kenan. Dan haka ta diro daga kan gadon
ta nufi dakin momy tana zuwa kafin tace wani
abu sumayya tace dama kin koma dan yau bazan
kwana a dakinki ba"tsaki kawai salma tayi tace
angaya miki ke nazo kira to dakixo da karkixo
duk daya yarinya! Sannan ta kalli momy tace
momy wayanafa waya daukarmin.? Tai murmushi
tace sai yanxu aka tuna da wayar kenan"to aiko
nima bansan inda take ba.
Ta marairaice tace haba momy pls ina aka
kaimin walh nayi missing frnd dina kuma data
na a kunne yake za aitamin magana pls momy
kibani.
Momy tace to aini ban dauka wayarki ba. Amma
ki tambayi auntynki sadiya dan naji tace tagani
kuma ta adana miki.amma bansan yadda ta
ajeba saidai kibari saitaxo.,
Tab!tai shiru tana yan waige waige saita hango
wayar momynta akan wardrobe da Sauri ta
dauka tahau lalubo numbern Anty sadiya"
Momy tace mezakiyi.?
Tace zan kiratne mana inji yadda ta ajemin.,
Momy tace ohh lallai kura tayi lapia.
Tana kira kuwa taci sa'a tana kusa. Tce hello
aunty ina yini' Lapia tafadi tana dariya tare
dacewa lallai qanwata lapia yasamu"salma
tadanyi dariya tare da cewa Anty daman zan
tambayeki ne ko kinga wayana! Tace aiko
lokacinda na kwana dakinki na ganta kasan
pillow kuma na dauka nasa cikin handbag dina
da safe na manta ban baki ba sbd tafiyar danayi
ba shiri su inna na jirana shiyasa na manta ban
baki ba kuma na taho dashi gida. Amma daman
ina shirin gobe zanxo naqara dubaki saina taho
miki dashi.,
Salma bataji dadi ba Amma saitace shikenan
Anty saikinxo din"sukai sallama ta kashe ta dubi
momy tace toni zanje na kwanta.,momy tace
sumayya maza kitashi kibita kuje Ku kwanta
sumayya ta turo baki zatai magana momy tace
ba magana nake miki ba'haka nan tatashi badan
taso ba salma kam hartayi gaba tare da cewa
dolenki dakixo

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 24
==>Asuba nayi hjy taxo ta bugama Abba qofa ya
bude tace alhj kayi sallah kuwa. Yace eh nayi
shigo daman inason magana dake. Taqaraso
suka zauna bakin gado,
Sannan ta gaisheshi.
Abba ya dubeta yace hjy jiya kinsan Inna takirani
tace eh.
Yace to bayan naje shine inna take gayamun wai
lokaci yayi dazan hada yaran nan Afnan da
salma aure.
Bayn na nuna mata qin amincewan hakan inna
tasa kuka da sauran maganganu wanda
bakai ba tushe tatayarmin da hankali intaqaice
miki zance bandawo gida ba harsaida nai mata
alqawarin hadasu aure.
Yaci gaba da cewa
To kuma kinsan wannan lamari bamai yiwuwa
bane shiyasa tindaga jiya hankalina atashe yake
narasa mafita.
Da nayanke shawarar fada mata abinda yafaru da
salma! To amma nayi tunanin halinda inna zata
qara saka kanta aciki shiyasa nace bari dai
ngaya miki yanxu mene ne mafita!?
Hjy tai ajiyar zuciya daga bisani ta dubi Abba
tareda cewa.
Toh nidai alhj dazakaji shawarata anawa tunanin
wannan ai abin farin ciki ne kuma rufama juna
asirine.
Yanxu idan akace salma wani bare zata Aura
kaga dole ne sai an fada mishi abunda yafaru da
ita kuma wannan kamar cin zarafine da kuma
tonan silili.
Idan ba tayi dace da miji me sonta bane yadinga
mata gori kenan., akan abinda itama bada
sonranta bane tsautsayine kawai ya hau kanta.
To Amma yanxu kaga afnan shi yasan abinda
yafaru da ita kuma har yanxu yana sonta
ahakan.
To alhj kaga zaifi mana rufin asiri sai ayi tuwo
na maina kenan.
Ammapa ni anawa tunanin kenan.
Wani irin kallon rashin fahimta alhj yake mata.
Yace wato ke har yanxu kina nan akan bakanki
kenan.
Yaci gaba da cewa
Daman nasan abinda zakice kenan.sbd daman
cen abinda kikeso kenan.
To Amma idan da kinson wannan hadin yanxu
yakamata ki cenja ra'ayi sbd bakisan qatonda
yai mata fyade ba.
Yanada cutar qanjamau ko bayidashi.
Wannan duk be dameki ba. Ke baruwanki da
lafiyar danki.
To idanke kina ganin wannan hadin me yiwuwane
gwara ma ki cenja tunani.
Ke ko tunanin yadda aka wulaqanta miki yarinya
ba kyayi.
To kisani bazan taba bari a kashemin yaro ba.
Shi kadai Allah ya bani na miji kuma nabari azo
a goga mishi cuta.
Towai shiyace miki ma har yanxu yana sonta.
Ai shidinma ba mahaukaci bane.
Juya kanshi yayi yai wani dan gajeran tsaki...
Mtsw...tare da cewa keda akace kibada shawara
kinxo kina wani fadin abinda bazai yiwuba.
Sadda kanta tayi qasa tace Allah ya huci
zuciyarka..Amma alhj ai shawaran na bada
bawai nace ayi dole bane.
Kuma kace kayima inna alqawari akan zaka aura
mishi salma.
Sannan na tabbata afnan shiyasamu inna yace
tai maka magana domin Jiya bayan fitanka
shima yafita.
Na tabbata hakanan inna bazata taso da wannan
maganarba saida izinin afnan.
Kaga kenan har yanxu yanason salma!.
Taci gaba da cewa.
Ni nasan daman soyayyarsu da salma bazai iya
gudunta akan wannan abun daya sameta
ba.
Kuma ya burgeni.
Sannan Wannan shine lokacinda yakamata ya
nuna mata shi masoyin gaskiya ne.
Kuma zai iya kasancewa tare da ita a kowani
hali.
Yanxu sai kayi tunani.
Danka dai yanason salma!
Kai kuma kayima Inna alqawarin hadasu aure!
Sannan wannan abun alfaharine agaremu.
Kuma rufin asirin zuri'armu ne.
Sai kaje kayi tunani ni iyakan abunda zan iya
fada kenan.
Amma ka gafarceni idan na bata maka rai.
Gaba daya jikin Abba yai sanyi da irin
maganganun umma.
Saidai har yanxu yanajin bazai iya bari Afnan ya
auri salma ba"
To amma ya zaiyi da inna!?yakasa samun
wannan amsar.dan haka ya dubi umma yace
shikenan na gode! Ni yanxu zanshiga wanka ayi
qoqari agama hada break kafin na fito.
Umma tamiqe tace to alhj saika fito.
Bata zame ko inaba sai kicking nan taga aunty
sadiya tanata hada abincin break.
Ta gaisheda momyn nata sannan tace umma ai
nashiga dakinki zan gisheki ban ganki ba.nace
ko kina dakin Abba ne shine kawai nataho
kicking nakama aiki dan yau inaso ne naje
gidansu salma.
Umma tace eyya aiko yakamata kije kidubata
kam,
Nima yau naso tambayan Abbanku zuwan .to
amma banga fuska bane dan yau ranshi abace
yake kuma hankalinshi a tashe yake.
Jiya inna tatayar masa da hankali.
Aunty sadiya ta ware ido tace topa wani abun yai
mata ne!?
Umma ta yamutsa Fuska tace kinsan dai halin
abban naku.
Wai tataso mishi da maganar auren salma da
afnan ne wai dole saiya hadasu Aure.
Shine ya nuna mata beyarda ba. Shine ta dinga
mishi kuka hankalinshi yatashi har saida yai
mata alqawarin hadasu aure.
Shine yau yatashi da bacin rai wai yaza'ai ya
aura mishi yarinyarda aikaima fyade be sani ba
kota kamu da wata cutar.
To shiyasama nakasa tambayarshi nabari saiya
huce.
Gaban anty sadiya saida yai wani mugun
bugawa.
Amma ta wani bngaren kuma taji dadin wannan
maganar.
Dan kuwa shiyafi kowa dacewa da aurenta. Bai
cuceta a banza ba.
Dan haka tace tohpa yanxu momy yaza'ayi
kenan"
Tace oho nidai nabashi shawara idan yaji
shikenan.
Aunty sadiya tace to umma Alllah yazaba abinda
yafi alkairi!
Tace Ameen dai.
Yi Sauri kigama kimtsawa dan yanxu zai fito
yayi break ya fita.
Umma ta fito tazo palo tadan kashin gid'a akan
kujera.
Abba kam yana gama kimtsawa beyi wani
jinkiriba ya nufo palo anty sadiya tana tsaye
tana shirya abinci akan dining ta duqa ta
gaisheshi ciki ciki ya amsa da ganinsa kasan
yana cikin damuwa.
Yace sadiya maza kije ki kirawomin afnan yataso
yanxu inason magana dashi.
Tace to abba.
Ta nufi sashen Afnan tafara buga qofa. Shima
lokacin ne yasamu dan bacci ya kwasheshi,
kamar a mafarki yaji ana buga qofa. Ahankali ya
bude ido yana sauraron ko Zaiji an qara.
Yaji anci gaba da bugawa.
Daqyar ya iya tashi jikinsa ko ina ciwo yake
haka yaqaraso bakin qofar ya bude.
Aunty sadiya yagani ta jefo mai wani harara
shiko yace ina kwana.
Bata amsa ba tace Abba na nemanka yanxu
kuma.
Ta juya abinta bata saurari me zaice ba.
Tana zuwa tace Abba yana zuwa.
Abba na zaune akan dining umma ta zuba mishi
abinci Amma ba abinda ya iya ci.
Saiga Afnan ya fito jiki a sanyaye yaxo ya zauna
akan Capet
Ya dubesu yace umma ina kwana.
Tace lapia lau ya jiki.?
Yace da sauqi.
Sannan yace abba ina kwana.
Wani irin kallo yajefo masa me cike da alamun
tambayoyi!.ba tare da ya amsa gaisuwanba.
Cikin zafin murya yace AFNAN..!
Firgicinda yayi saida qwaqwalwarshi da ruwan
jikinshi duk suka dena aiki.
Tsoro da fargaba suka ziyarci zuciyarsa.!
Muryarshi na kyarma yace Na'am Abba.
Abba yasake jefo masa wani hararan daga bisani
yace.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 25
==>Afnan kabani kunya. Ban taba tunanin zaka
watsamin qasa a ido ba.
Wai harkayi girmanda zakaje kahadani da inna
akan salma ko?.to kasamu yadda kakeso. Domin
kuwa tayi abinda kasakata.
Kuma zan Aura maka salma!
Amma kasani duk abinda yafaru dakai kai kaja
ma kanka tinda kai bakasan ciwon kanka ba.
Baka kishin abinda akaima yar uwanka .
Dan haka zan Aura maka salma!kuma babu saki
atsakaninku har abada.
Sannan nacire hannuna akanka kaje kai duk
abinda kaga dama.
Afnan kansa na qasa ya dago kannshi ahankali
idonsa sunyi jawur ya kalli Abba kabinsa na
karkarwa yace Abba..walh..ni...kafin yaqarasa
tuni Abba ya daka mishi tsawa..get out
kabacemin da gani. Banason ganika agabana.
Agigice ya miqe kamar zai kifa sbd Sauri.
Umma ne ta kira sunan Afnan"tsayawa yayi cak!
batare da ya waygo ba. Sannan taci gaba da
cewa haba alhj dan Allah ka sassauta mishi
mana., baka ganin shima ba lapia ne dashi ba.
Abba bece mata komai ba ya miqe yadauki
jakarsa da keys din mota yai waje fuuuu!
Batareda yaci komai da aka Zuba mishi ba.
Ganin Abba ya fice afnan ya juyo ahankali ya iso
dining din yadda umma ke zaune yaja kujera ya
zauna idanuwanshi cike fam da qwalla.
Umma ta dubeshi tace Haba afnan kakwantar da
hankalinka kariga kasan halin babanku.
Fushi yayi kuma zai huce nan bana jimawa ba.
Kuma ni ina bayanka 100 bisa 100. Naji dadin
abinda ka yanke na taimakon yar uwanka.
Kuma karka sake kace zaka kalli abinda akaima
naka yar uwan domin kasamu hanyan
musgunama salma.
Dan kuwa ita babu laifinta aciki.
Inamai farin ciki da wannan lamari domin rufin
aairinmu ne gaba daya.
Dan haka ka kwantar da hankalinka ka qyale
alhj.
Yanxu dai kaci Abinci kasha magani kaga sai
rama kakeyi duk kabi ka lalace.
Nan dai taita lallashinsa har saida yaci ya qoshi.
Daman shi babban damuwarshi shine abba yaqi
amincewa.
Amma tunda sai ya amince komai zai faru me
sauqi ne.
Suna cikin firansu. Saiga aunty sadiya tafito ta
fesa kwalliya tayi masifar kyau.
Doguwar riga tasa na atanfa ya zauna daram
ajikinta taqaraso gunsu cikin takunta irin na
qasaita. Sannan taja kujera ta zauna gamida
janyo kulan Abinci tana qoqarin zubawa tace
umma Abba harya fita ne.
Ta gefen ido kuwa wata irin harara ta dinga
aikawa afnan din.umma tace eh yanxu yafita ko
break dinma beyi ba.
tace to umma nima na shirya yanzu zanci abinci
ne na wuce.
Umma tace to idan kinje dai kice ina gaisheda
me jiki kuma insha Allahu nima gobe ina nan
zuwa dubata. Afnan zai kawoni shima daganan
ya dubata.
Saida suka kalli juna aunty sadiya da afnan.
Sannan yai qasa da kanshi cike da kunya da
fargaban abinda Umma tafada. Sadiya taci gaba
da cewa toh umma zasuji insha allahu,.
Afnan ya miqe yace to aunty ki gaisheta.
Tai kamar batajishi ba. Yakama hanya yai
dakinsa. Aunty sadiya ma tatashi taje daki ta
dakko jakarta da takalminta Wanda sukai
macing da kayan gamida sa hijjab dinta taima
momy sallama ta fice.
Salma kuwa yau tatashi ta qarfinta domin
tanajin qarfi ajikinta sosai. Sauqi dai yasamu da
izinin Allah. Kwalliya kuma yadawo sabo!!.Tsaye
take gaban mirror tana taje gashinta yadda ta
sakeshi abaya, gamida dakko wani siririn hula
Wanda macing color ne da kayan datasa
tsakiyarshi a bude yake. Ta gaban hulan kuma
an rubuta (love is life!) Riga da sket ne ajikinta
Wanda yaya Habib yayo mata tsaraba daga
Dubai. Sunyi matukar amsar jikinta.
Tayi masifar kyau Wanda ba'a magana.
Ta sanya wannan hular gamida fito da gashin ta
tsakiyar hulan.
Ta qara duba mirror sannan tasaki wani
murmushi Wanda yasake bayyana tsantsar
kyawunta gamida lumshe ido domin it a kanta ta
burge kanta.
Palo tayo tana tafiyarta a nutse tana isowa palo
kafin takaga zama tajiyo sallamar aunty sadiya
nan tatsaya cak! Aunty sadiya tana shigowa ta
aika mata da wani irin qayataccen murmushi tuni
Anty sadiya ta ware idanu gamida fadin. Woww!!!
Sister irin wannan kyau haka ai saikisa inyi
rangaji in fadi aqasa. Taqara sakin mata
murmushi sannan ta ruga ta rungumeta tana
fadin kai aunty ai kinfini hadewa.
Taqara dubanta tace kai!!waneni da had a kaina
da matar manya. Wannan ai dole kidinga furgita
maza irin wannan kyau haka"Ammapa kar karki
ya fashe kidauka wai kinfini kyaune. Kin wani
zabga jan baki kamar yar hayin kogi. Gaba daya
suka kwashe da dariya.
Salma tace to aunty ni duk ba wannan ba ina
wayana!toce kwantarda hankalinki gata a jaka.
Ta karbi jakar tana kokuwan budewa. Saiga
momy tafito tana dariya tace kudai bakwa rabo
da barkwanci Indai kuka hadu.
Dariya kawai sukayi salma ta ciro wayarta tayo
daki tafada kan gado aunty sadiya kuwa nanta
baje suna gaisawa da momy. Tin kafi tacire
wayar a key take ganin saqonni daban daban
messages miss call WhatsApp.!dan haka tarasa
ina zata fara dubawa. Saita yanke shawarar bari
tafara shiga whatsapp tana shiga saqonwa zata
fara gani..uhmn..saida gabanta yafadi dan jitayi
kamar yana kusa da itane zai kamata. Afnan ne
yai mata sqo har gashi biyu..hannunta na rawa
ta danna ta shiga ga abinda saqon farko ke
dauke dashi...Amincin
Allah shi tabbata agareki yake yar uwata kuma
abar begena a kullum. Na kirawayarki baki
pecking ba bansani ba ko kina bacci ne.
Daman ba komai bane inaso na fada miki ne
daman zanxo anjima in kawo muku ziyara
kigaya momy kuma ki shiryamun kayan dadi
kinji my dear sister!! Lallai fa afnan an shirya
maka kayan dadi irin Wanda baka zata ba kuma
kaci ka qoshi..!! x
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 26
==>Da wani dogon tsuka. Mtswwwwwww!!!.gami
da cewa...!Allah shi kyauta in Auri mugu! Ai ko
maza zasu qare aduniya bazan taba aurenka ba
sbd na tsaneka tsana mafi girma.!mugu kawai"!
Tana turawa tai blocking dinsa.
Amma mezai biyo baya!?
Tunanin baya ne ya fado mata!

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment