You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake.'ya dafa
qafarsa zuciyarsa kamar zata buga yana fadin
afnan ko kaga fuskar wanda yaima salma
wannan mugunta?pls idan kaganshi zaka iya
ganeshi!?nayi alqawari ko dan gidan uban waye
sainaga bayanshi tinda ya cutarmin da
salma!kuka ne ya kubuce masa tare da cewa na
shiga uku shikenan an lalatama sister na
rayuwa.innalillahi wa inna ilaihirraju'un",momy
ta dubi aljh tace dashi inaso sadiya taje ta taya
yara zama kafin mu koma gida yanxuma nace
tabi Ahmad su tafi,aljh yace ba matsala,ta dubi
Ahmad tace yakamata kutafi dan dare yayi sosai
anbar yara a gida,tashi kawai sukayi suka fice
ba tareda sun CE komai ba.,momy ta biyo
bayansu sukai sallama ta wuce wajen
salma,.Habib yasake maida dubansa kan afnan
yana qoqarin sake yimishi magana,.sai gani
sukayi yana wani miqewa yana nadewa jikinsa
yasake dafewa kamar wuta gaba daya sukayo
kanshi kar kuso kuga rudewa wajen Abba da
ummanshi.Habib ma yadan tsorata da ganin
yadda yakeyi.,dan haka da sauri ya miqe yace
Abba bari akira Dr.dasauri yafice sai gashi tare
da Dr umma dukta rude gani take kamar dan
nata mutuwa zeyi.harta fara kuka,Dr yayi masa
wata allura sannan yace su samu towel da ruwa
su dinga jiqawa suna goge mishi jikinshi
ahankali zazzabin ze sauka,.sannan akula kar
ana yawan surutu akanshi,.dan jininsa ya hau
saisun kula Dr ya fice,nanfa hankali yaqara
tashi!!,Habib ficewa yayi abinsa ya nufi gun
salma,yana zuwa yaga momy tana sallah
yazauna bakin gadon ya tallabo salma tanata
bacci saidai jikin nata har yanxu da zafi,.addu'a
yafarayi cikin ransa ya allah ka nunamin Wanda
ya keta haddin yar uwata.lallai an cutar mai da
yar lelenshi,umma ta idar race dashi yakamata
kaxo katafi gida ko,ya kalleta momy kije gida
kawai ki huta zan zauna da ita.,momy so nake
da zarar ta farka ta kwatantamun fuskar wannan
azzalumin;.momy ta girgiza kai tace habibullahi
abinda yafaru yariga yafaru,kaje gida abinka
nizan kwana da ita kuma Dr yace da wuya ida
zata farka yau,kuma kota farka ba lallai ne ta
iya wata
magana me tsawo ba.dan haka katashi kawai
kaje gida abinka.,,haka momy ta matsa masa
yatashi yatafi badon ransa yaso ba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 11
==>Gari na wayewa sadiya ta kimtsa komai daya
kamata ta hada musu,.Ahmad yaxo yace idan
tashirya taxo suwuce shima zaije yaga yadda
suka kwana kafin ya wuce wajen aiki.sumayya
tasa kuka itama sai anje da ita taga
salma,.daqyar Ahmad ya lallabeta tareda
alqawarin anjima zai dawo ya kaisu idan anty
sadiya ta dawo sannan ta haqura,.suka kama
hanya sai asibity,suna shiga sukaga momy tsaye
akan salma suka qarasa da sauri,wai Ashe taga
tana motsi da qafarta ne shine duk ta rude wai
ko farkawa zatayi,.nan suka gaisa momy tace
suje su duba afnan rai abace sukaje badon sunso
ba,shima dai baccin yaketayi kamar
matacce,suka gaisa da umma sama sama Ahmed
yai sallama ya wuce abinsa,.sadiya taje ta
kawoma momynta abinci.sukaci sannan tatashi
taje ta duba salma ta dawo.,fitarta keda wuya
saiga Habib yaxo ya nufi qanwar tashi yna
tambayar momy ta farka kuwa,tace tadai dan
motsa yau da safennan,inaga da alamun
sauqi,likita yace babu wata damuwa zata tashi
cikin ikon Allah.yace ya afnan dinfa.tace shima
ba laipi kaje kadubashi mana.momy tayi tayi
yace shidai agaisheshi koyaje tinda ba magana
zai masa ba ai ba anfani,.ranar dai daqyar momy
tamatsa masa yatafi office yana maqale da
qanwarsa ko zaiga farkawanta amma shiru
hakadai yadaure ya wuce.,duk wannan abin da
ake inna bata sani ba.,aiko rufayda ta fakaici
idon sumayya ta salale sai gidan inna, tana zuwa
ta tadd inna a Palo taruga aguje ta fada jikin
inna tana haki,,inna tace yau naga arziki yannan
karyani zakiyi,daga ina kike haka kamar an
jefoki kodai kinyo tsokana ne aka biyoki.,tace a
a inna gudowa nayi sumayya bata sani ba nasan
zata iya biyoni shiyasa naketa gudu nasan
zataina nemana na barta ita kaidai.inna tace oh
kudai Baku rabo da shiririta.to ai yanxu zakiga
tabiyoki., ta dago kai a a inna ai bata isaba
tinda momy batanan kuma Khalid yana bacci
bazata fito tabarshi ba.,inna tace ina Maman
taku taje bayan jiya tabar nan!?rufy tace ai
tinjiya damuka koma gida bamuga anty salma
muna shiga dakinta mukaga jini a towel dinta
Ashe an yankata ne da bamanan shine momy ta
fita itama taqi dawowa aunty ne ma tatayamu
kwana shine....ai tuni inna ta hankadeta daga
jikinta takai mata duka ban gane an yankata ba
dan ubanki wani irin magana ne wannan ni zaki
kawoma shashanci.,rufy ta zumbura baki tace to
shine zaki dukeni ni gidama zan tafi abuna"inna
ta ruqota yanxu ina salman take?! Taqara turo
baki toba nace miki an yankata ba;,gaban inna
ya yanke ya fadi lallaima yarinyannan da gaske
take ko kuwa,.dan haka taqara jefo mata
tambaya! to ina mamanku tace ai tin jiya bata
dawo ba!,inna tasa salati innalillahi wa inna
ilaihirraju'un. Inna tayo waje tna qwalawa husna
kira!husna husna ta nufi sashensu,.momyn husna
ne tace ke bakyaji inna na kiranki husna tace ni
walh momy kinsan kiran inna yanzu haka ba
wani abin azo aji bane.,saiga inna tashigo
agigice ta miqa mata waya tace kirawomin
abubakar yanxu rafida tazo take cemin wai an
yanka salma wai mamansu ma bata kwana a
gida ba.,safiya tace wani irin an ynkata
kuma.husna ta kwashe da dariya tace umma kinji
ko yanxu shirmen rufy zaki kama,.inna tace
atafaf sai ankira mata abubakar.,husna ta kira ta
miqa mata, yana dauka inna bata bari sun gaisa
ba tace bukar
meyafaru da salma ne?!shiru yayi yana tunanin
waye yafadama ina abindake faruwa.tace kayi
shiru ina sauraronka kafadamun abinda yafaru
da salma.kame kame yafara inna..walh..inna
wayace miki.tsawa taimasa taredacewa zaka
fadamun kosaika rainamin wayau kodai salman
ta mutu ne da gaske.,yace a a inna bata mutuba
walh suna asibity tamaji sauqi inna ki kwantar
da hankalinki. Kuka inna tasa da salati shikenan
Ashe gaskiyane an kashe salma ba ason
fadamunne magana yake mata amma kojinsa
batayi duk. ya birkice gashi akan hanya yake
zaitafi asibity ba shiri ya jiyo yayo gidan Inna.,
husna da mamanta sunyi tsarko tsarko suna
kallon inna cike da mamaki.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 12
==>Zama tayi dirshan tana tafa hannuwa tana
cewa kungani ko yrinyar nan nasan haka nan
kawai bazatazo ta fada wannan maganar a
banza ba. Nasan ba hakanan ba akwai wani
abinda ake boyemin.,husna tace inna wani Abu
yafaru da salman ne?!tace gashi kuwa abubakar
yacemin suna asibity to da wuya idan salma tana
Raye., hjy safiyya tahau salati tace inna barida
asake kiranshi aji!;sai sukaji sallama abubakar
ne yashigo da sauri yayogun inna yana fadin
inna bata mutu ba tashi muje nakaiki ki ganta
.,tamiqe da saurinta tayo waje yabiyota
abaya,.husna tafito a guje tana fadin Abba nima
zanje kujirani Abba wai salman batada lapia ne?!
yace wai waye yaxo yafadama inna ne,.husna
tace rufy CE taxo tace mata wai an yanka
salma., murmushi kawai yayi yace allah ya
shirya jeki dakko hijabinki mutafi.,dasauri taje
da dakko suka fice akabar hjy safiyya a gida.,ita
kuwa rufy tuni ta sulale tai gida abinta., basu
tsaya ko inaba sai asibity.,suna shiga momy
saida ta tsorata da ganin inna amma ta dake
tace inna waye fada miki muna nan?!tace ban
sani ba an bari saita mutu sannan agayamun
ko.tace yi haquri inna walh tin jiya hankalinmu
be natsu bane,. Inna taqarasa gun salma tana
fadin oh
ni zuwaira meya samarmin salma ne!alhj kam
juyawa yayi yanufi gun afnan yana shiga yaga
dakin ba kowa mamaki ya kamashi yawo waje
sai suka hadu da hjy tafito daga toilet tayo
alwala.,yace ina afnan din?!tace ai yana ciki
baka shiga bane yace yanxu nashiga banga
kowaba tace wani irin bakaga kowa ba muje
nabarshifa yana bacci,suka shiga tare hjy taga
wayem tasaka salati tace alhj ina yanufa ne?!
sukayo
waje arude tai hanyan word dinda salma take
yace dawo karkije tare mukaxo da inna yanxu
kinazuwa hankali zai qara tashi murasa yadda
zamuyi da ita,.tace saida nace
ma sadiya tazo tazauna dashi amma ashe bata
xoba,.yace yanxu taho muje inyaso daga baya
saimu kirasu awaya mugaya musu abinda ke
faruwa. Da sauri sukai mota suna tafe suna duba
hanya, nan bangaren salma kuwa motsawa
tafarayi gaba daya sukayo kanta suna
tsatstsaye.Salma kuwa jitake kamar awani
duniyar take jikinta duk inda tai qoqarin juyawa
saitaji wani masifar ciwo kamar anyi mata
shegen duka., momy ta zauna tana fadin salma
salma sannu kinji!"ahankali
abubuwa suka fara dawo mata tafara tuno
abubuwanda suka faru tsakaninta da yaya afnan.
Tuni tafara shure shure da qafa tana fadin yaya
dan Allah kayi haquri bazan sake ba yaya
kataimakeni nace baxan sake ba yaya.,kasakeni
tuni momy ta tallabota ta rufe mata baki tana
mata addu'oi inna tace oh wani yayan take kira
ne momydai batace komai ba saida taga salma
tadaina shure shure sannan tasake mata
baki!"ahankali salma tabude idonta taqara
lumshewa dan tarasa ina tace gashi hankalinta
be gama dawowa jikinta ba., ta sake cewa yaya!
yayana!kazo ka ceceni dan gani take kamar har
yanxu a hannun afnan take.,momy tace salma
bude idonki mana kiganmu ga inna tazo dubaki
ga antynki sadiya ga sisternki husna kubude
idonki kinji ba abinda zai sameki!"jin maganar
su kawai take sama!sama kamar wani almara!.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 13
==>Tasake bude idonta tafara ganinsu dishi
dishi!.ta qara bude idonta sosai tana kalle kalle
dan batasan a ina take bama. Wajen yayi mata
wani kala ta kalli momynta tafara magana da
murya qasa qasa kamar haka"momy nan ina ne?!
momy tace asibity ne bakida lapia shine aka
kawoki,!tai shiru jim kadan tasake cewa momy
ina yaya Afnan!?momy tace yana nan
zuwa..zakici abinci?ta girgiza kai tafara kuka a
a momy dan allah kice masa karyaxo dan allah
momy walh kasheni zeyi.,momy tai saurin cewa
to kwantar da hankalinki zan gaya mishi dena
kuka kinji"inna ta bude baki tare da cewa kaji
wani shirme duk zafin ciwonne haka!inbada
zafin ciwo afnan dinne zai kasheki!ta kalli momy
tace Aisha anya kuwa yarinyar nan tana cikin
hankalinta? kijifa surutanda taketayi tinda ta
farka;momy tace inna zafin ciwo ne kawai zata
warware insha Allahu,.inna sai qara
shashshafata take itako tanata zare ido tana
kalle kalle sai lokacin ta kula da qarin ruwanda
ake mata.,sadiya da husna suka dubeta sukace
sannu ya jikin batace komaiba tafara qoqarin
tashi ta zaina nanfa taji qugunta yariqe gam ga
wani masifaffen ciwon jiki.,anty sqdiya tace ko
adagaki ne ta daga kai alamar eh., sadiyaa tazo
da sauri ta dagota ahankali,.amma Ina jitayi
bazata iya zama ba haka takoma ta kwanta;sai
hawaye suka fara gararowa afuskarta da sauri
anty sadiya tafara lallashinta tana goge mata ita
kuwa husna tsaye tayi tana kallon ikon allah
yadda taga salma lokaci guda ta rame manya
manyan idanunta sun qara bayyana fuskarta
yazama wani siriri lebenta ya bushe aranta tace
lallai wannan ciwo yabama sis dinta
wahala.,.alhaji abubakar kuwa haka suka dinga
Neman afnan ko zasu ganshi akan titi amma
babu shi babu labarinshi haka suka figi mota sai
gida.,suna shiga palo wazasu gani afnan ne
kwance ya daura hannuwansa akan qirjinsa ya
miqe qafa daya ya daga daya fuskarshi na kallon
sama!hawaye nata faman kwarara daga idonshi.,
sunyi tsarko tsarko suna kallonshi cikeda takaici
ta wani bangaren kuma sunyi hamdala da
ganinshi Abba yaqarasa yana fadin afnan
wannan wani irin rashin hankali ne zaka gudo
gida kazauna ciwo na cinka!hjy ta nemi waje
tazauna tare da cewa kaimadai kafada.,yaxo ya
kwanta ne yanata kuka kamar wani qaramin yaro
to dukanka akayi taja tsaki..mtsww tindazu
mukebin kwararo kwararo muna nemanka Ashe
kai gida ka nufo kabar yan iska acen KO., Abba
shikam harya karaya..yace haba kibarshi
hakanan mana bakya ganin halinda yake cikine.!
tace to mu kuma ai soyayi yajefamu atashin
hankalinda yafi haka.yanxu daya fadi ahanya
mota ta takeshi aimu yabari da baqin ciki., Abba
ya dafa kan afnan yace my son me kakema kuka
ko jikinne!?nan yaji jikin Afnan zafi kamar
garwashi. Yace kinji jikinshi kuwa tashi mu
koma asibity,.shigo dake kwance duk maganar
da suke be tankaba saida yaji ance yatashi
akoma asibity.,da Sauri yatashi ya zauna yana
cewa Abba dan allah kabarni walh naji sauqi
baxan koma ba,.Abba da umma sukace atafaf
saiya tashi sun koma bazasu zauna suna kallo
ciwo yakasheshi ba; fashewa yayi da kuka kamar
wani qaramin yaro walh Abba idan kuka mayar
dani mutuwa zanyi ni bazan koma ba,duk sai
sukaji ya kashe musu jiki. Alhaji yace abarshi
tinda bayaso zaije ya karbo masa magungunan
sallama nan hjy ta kira momyn salma take fada
mata afnan ya gudo gida,. Salma kuwa tananan
tana masu kuka ita akira mata yaya Habib da
yaya Ahmad suzo su kaita gida.,bashiri momy
tasa aka kirashi! saigashi yaxo kamar Wanda
yahawo jirgin sama.yana aikinshi a office daman
hanklinshi yana wajenta saikuma yaji kira"momy
dai tarasa yazatayi kar ahaifa danda ba ido!yaxo
dasauri ya dagota murya a shagwabe tace wash
yaya bayana ciwo da cikina yaya harda kaina
ciwo yake'.saiga hawaye sun sake kwararowa:
hankalinshi yatashi yace sorry sisterna waye
yatabamin kene!;pls zaki iya gane fuskarsa dia
kidaina kuka saina daukar miki fansa!;gayamin
kinji zaki iya ganeshi?,!kuka ta sakar masa tare
da cewa ba yaya bane.....
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 14
==>momy tai saurin cewa aina gayama yayan
naki karyaxo ba shikenan ba/Habib yai shiru
daga bisani yace momy wani yayan take
magana?tace uhm walh tinda tatashi taketa
shirme nima narasa mezan mata ma;salma kuwa
kallon maman nata kawai takeyi wai itace za ace
tana shirme/kodai basu San abinda yaya afnan
yai mata bane!;to amma idan basu saniba
meyasa tagansu a asibity?kodai daman sun tafi
sun barta ne dan yazo yai mata wannan Abu?!
duk acikin zuciyarta take wannan tunanin"ya
Habib ne ya katseta da cewa..qanwata kin
ganeni kuwa?ta daga mishi kai alamar eh"ya na
shirin jefo mata wata tambayar nan yakula
Ashefa inna tana dakin kuma ya tabbata batasan
halinda ake cikiba dan yasan baza a gaya mata
wannan mummunan labarin ba!shiru kawai yayi
ya dubi inna yace ke tsohuwa meran qarfe meya
kawoki nan?'ta turo baki tace abinda ya kawoka/
ai natsayane naga iyakar gudun
ruwanka tinda kashigo ko kallona bakayiba
balantana ka gaisheni kana nan gurin qanwarka
kaime qanwa ko"gaba daya sukasa dariya momy
kuwa taji dadi da aka cenja fira dan duk
hankalinta yatashi da irin tambayoyinda Habib
kema salma!hararanda
Habib yajefoma sadiya ne bashiri ta shanye
dariyarta sanadiyyar faduwar da gabanta yayi.
Tuni ta miqe tsaye takama hanya sumi sumi tai
waje momy tace ina zakije?tace
momy..zan.danje waje ne zafi ke damuna, momy
tace zafi kuma AC akunne yake fa. Qara
daburcewa tayi tace oh sanyi nakeso nace,momy
tace eyya to dawo abinki bari akashe nima
sanyin ya dameni.haka tadawo
tazauna jiki ba qwari/tana daga kai suka qara
hada ido da ya Habib yasake balla mata harara
bashiri ta miqe zumbur harsaida momy ta kalleta
sai cewa tayi momy zanje bayi ne yanxu zan
dawo'/inna tai karab tace kinsan bayin zakije
shine kikasa aka kashe mana AC dan gulma ko/
uhm kawai tace tafice abinda.momy tace inna
kenan sarkin son AC,.sadiya kam zuwa tayi ta
nemi guri tazauna akan wata farar kujera da aka
tanadesu dan masu zuwa ganin Dr! Ta jingina
kanta da bango hawaye suka ciko idanunta
aranta tace meyasa yaya
Habib yatsane ni?!wai yayshe ne zanyi abinda ze
burge ya Habib"itadai tanason yaya Habib amma
batasan laifinda tai mishi ba bayason
ganinta;tabbas tana matuqar qaunarshi amma
gashi tarasashi amatsayin mijin aurenta;hawaye
zafafa suka dinga bin kumatunta wai yaushene
zataga dariyar ya Habib?! Salma kuwa zamewa
tayi daga jikin yayan nata ta hade rai

===>BUTULCI KO SOSO!!!,? Part 15
==>yayi yayi inna kam tace ai dole saiya kaisu
gida itada jikar tata husna'momy ma tace yayi
haquri ya kqita sannan yawuce duk inda
zashi"hakanan ya haqura suna shirin fita saiga
Ahmad tare da sumayya sunxo aiko Habib yace
shikenan maza kazo kakai inna gida allah ya
ceceni. Yanxu office zan koma ana jirana kuma
tace saina kaita gida.maza kakaita saika
dawo.ko shiga beyiba yasashi yajuya sumayya
kam shigewa ciki tayi abinta., inna dai tace oho
dai koma menene.nidai akaini gida.,sadiya kam
tagama cin kukanta taje toilet ta wanke fuskarta
tace bari tadan leqa taga mamanta !tana bude
daki taga wayam tace umma kuma tafiya sukayi
an sallamesu ne amma bako sallama.ta juyo
dukda tanajin tsoro taje taga ya Habib amma
hakanan tadaure tace bari tashiga tagayama
momy.
Topa ana wata ga wata
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 16
==>Salma tsce yaya kayima Dr mgana mutafi
gida gobe yace to iyarigima zangaya masa!
ammafa sai in kinacin Abinci sosai;ta tabe tabi
tace yaya bakaga abincin danaci ba"yace nagani
amma ki qara"mudai zamu wuce saida sfe!
Momy tace Ku gaida gida suka fice abinsu, Abba
yace salma anji sauqi sosai momy tace aikuwa
alhmdlh!/yace to Allah ya kiyaye gaba kuma
allah ya tona asirin duk Wanda yai mata wannan
cutar ita kuma allah yasaka mata/momy da ya
Ahmad sukace Ameen summa Ameen! Yace toni
zanje nasami Dr arubutama afnan magungunan
daya dace tinda yaqi zaman asibityn kuma ga
ciwo nacinsa/
Momy tace oh haryanxu jikin ko",yace eh walh
yanacen zazzabi yaqi sauka saidai yaita
hawaye_momy tace to Allah yabashi lapia,
Ameen Abba yace yafice abinsa.Salma tanata
nazari cikin zuciyarta kome Abba yake nufi oho.,
to mema yasamu afnan din?! tambayar data kasa
bama kanta amsa kenan.wato bayan yakusa
kasheta shima ciwon yakamayi kenan! Wata qila
ma da hadin bakin su momy. To amma yaza ai
su momy suyi mata haka?!kuma meyasa idan
tanaso tayi maganarshi momy ke tattarewa!
gaskia akwai wani abu a qasa Ahmad ma yace
momy zantafi sister allah yabaki lapia sai yaga
ta fashe da kuka. Hankalinsu yatashi Ahmad
yace sister lapia yaqarasa yace wani abunne ke
miki ciwo?! cikin shagwaba da shashshekar kuka
tace yaya daman da gangan su momy suka gudu
suka barni yaya afnan yaxo yakusa
kasheni..taqara fashewa da kuka
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 17
==>Asuba nayi momy tatashi tai sallah nima
tatasheni nayi sallah ta hadamin tie me kauri
tabani nasha na qoshi 6 0 daidai Dr yashigo
dubani ya cimmani inashan tie yanataimin dariya
wai na warware haka yace to ya nakejin jikina
nace mishi komai normal babu sauran wani ciwo
nace mishi saidai banajin qarfi ajikina yace ba
damuwa ahankali zanji daidai. Dr yace anjima da
yamma zai sallamemu nan nafara murna nace
mezai hana a sallameni yanxu yace sbd
inada sauran allura yanxu zeyimin anjima zaimin
sai a sallamemu momy ma tanata murna yaimin
allura yafice abinsa. nan wani baccin yasake
kwasheni.
Wajen qarfe 8 0 saiga yaya Habib yaxo
muryanshi ne ma yatasheni daga baccin
danaketayi.sunata hira da momy ta fadamishi
cewa anjima za a sallamemu.
Ina tashi yaya Habib ya kalleni yace sister yau
sai gida ko. Nadanyi murmushi na CE yaya
yaushe kaxo? Yace tin daxu mana ke kinata
bacci gashi mun tasheki ko. Na girgiza kai nace
daman ngaji da baccin! Yace to nima yanxu zan
wuce office anjima sai Ahmad yaxo yamaidaku
gida idan nadawo daga office zanxo muyi
magana kinji!.nace to yaya saikaxo.
Yatashi yai sallama ya wuce abinsa. Momy
taqara hadamin tie me kauri nasha nasha magani
taje toilet tahadamin ruwan wanka tace nazo
taimin Niko nace ban yarda ba saidai inyi dakai
na. Tayi tayi haka ta haqura ta qyaleni. Naje nai
wanka na yadda takemin gashin haka nima na
daddage. Nayi inayi ina kuka idan natina yadda
yaya afnan yaimin abin yanamin ciwo arai.
Ina fitowa daga toilet momy ta gyara ko
ina.nazauna bakin gado nafara shafa mai saiga
aunty sadiya ta shigo tanata yimin dariya nima
inayi mata tace rigimammiya harkin warke ko
murmushi kawai nayi. suka gaisa da momy saika
yaya Ahmad shima ya shigo ashe tare suke. Aka
gaisa Momy nata tambayan dan autan NATA dan
tayi missing dinshi gashi asibityn basa bari ana
zuwa da yara da anxo mata da Khalid ta ganshi.
Sadiya taxomin da wata doguwar rigana tace na
cenja kaya daman wancen ta isheni momy tace
Aida tabarshi ma dan yau za a sallamemu sunyi
murna dajin hakan.momy tafadama yaya Ahmad
yadawo anjima yadaukemu .wayar momy tai qara
ta dauka tareda sallama Abba ne yakirata suka
gaisa ya tambayi jikina mum tace ta sauqi
anjima ma za'a sallamemu yace to alhmdllh
daman innace tace dole saina kirawo mata salma
taji muryarta yanxudai gata..yamiqama inna
waya suka gaisa tace abani.
Na karba nace hello inna tace me sunan mamana
yajikin naki?nace naji sauqi Inna Dr ma yace
anjima zai sallamemu inna yanxu aina fiki
qarfima
Tace rufaman baki kawai saiki kama ciwo yanxu
dakin tafi kinbarfa.
To zanxo gidan naku anjiman saikin fadamun
dalili.
Nai dariya nace shikenan inna saikinxo.namiqa
ma momy wayarta suka qarashe firansu sukai
sallama .
Ahmad yai murmushi yace inna iyayen rigima.
Yace amma momy yau dai kinsan dole yaya
Habib zaixo yatambayi salma yadda abinnan ya
kasance ko?! Tace tabbas kuwa nima tunaninda
naketayi kenan.amma
aiba wata matsala bane kawai cemishi zatayi ita
batasan fuskar wanda ya aikata mata
hakanba.yaya Ahmad furka a yamutse yace
momy wai meyasa kikeson a boye maganar nan
ne bayan abune me girma kuma kinsandai halin
Abba ada ma baibari afnan ya auri salma ba
bare yanxun dayake ganin an riga an dauke
mutuncinta kuma baisan cewa afnan din bane
toya abin zai kasance.
Momy tai wani taqaitaccen murmushi tace
Ahmad kenan kana manta wanene Habib ko to
duk wani tashin hankali zaixo da sauqi akan yaji
cewa afnan ne yataba mishi salma.dan haka
dolefa sai anyi haquri amma idan mun koma
gida akwai shawarar dana yanke insha allahu
komai zaidaidaita.
Ya Ahmed yace shikenan momy.
Nida aunty sadiya kuwa bamuce affan ba illa
dana sanya rigata na kishingida akan gado
inajinsu harsuka gama.Ahmad yace Toni
zanwuce sai anjiman zandawo nadaukeku.yafece
abinsa
Cen wajen yaya afnan kuwa daqyar umma
tamatsa mishi ya karya yasha magani sannan
yace zaixo yadubani umma tace ba inda zashi ai
yanxu nafishi lapia shida aka kusa kasheshi sbd
ni to ba inda zaije idanma zaixo din toyabari
yaqarajin sauqi.
Haka nan dai afnan ya haqura dukda ma dai
yana tunanin da wuya zai iya tunkarata da nufin
gaisuwan.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 18
==>Qarfe 6 0pm likita yaxo yaimin allura dan
harna fidda rai da sallama.
Saida naganshi sannan naji sanyi amma
saiyacemin wai yanxu yamma tayi sosai saidai
gobe aiko nafara shirin kuka shine yace ai wasa
yakemin ya bamu takardar sallama yanataimin
dariya wai baby salm akwai rigima.
Tsalle ne kawai banyi ba don murna dandai
bazan iya tsllen bane amma da sainayi dan
naqosa naganni a gida.aunty sadiya kam tin
wajen qarfe 4 tawuce gida yaya Ahmad ma yaxo
yaga ba a sallamemuba yawuce abinsa.
Dan haka nace momy kawo wayarki nakira yaya
yaxo ya daukemu tamiqomin na lalabo
number dinsa nakira yana dauka nace yaya kaxo
an sallamemu yadda nai maganar harsaida
yabashi dariya yace to ganinan zuwa Ku kimtsa
kafin na qaraso,
Momy tafara shirya duk wani Abu damukaxo
dashi.
Jim kadan saiga ya Ahmad na miqe da izzana da
danufin in ruga da gudu in riga momy shiga
motar amma sai akasin hakan dan jinayi baxan
iyaba tafiyarma da yaya aka qare dan banajin
wani qarfi ajikina.dan haka nabi ahankali.nace
momy nidai Ku sameni a mota ya Ahmad yace
meyasa kika fasa gudun nace sbd kar mutane
suyita kallona ne, yace kokuma bazaki iyaba ba
kedin kinajin kunyan gudu ne.
Nai murmushi na fice abuna.
Ahmad yataimaka ma momy suka kwaso komai
suka saka a both. Suka shigo mota muka kamo
hanyan gida. nikam gani nayi ko ina
yacenjamun.
Muna isa gida su rufy da sumeey sai murna suka
rugo da gudu suna oyoyo aunty tadawo. Khalid
ya rugo ya rungumemun qafafu saida mukai
kamar zamu fadi nidashi momy ta riqeshi tace
gafara cen zaka kayarmin da yarinya wato ni
inacen ina tunaninka amma kai ba tani kakeba
ko.ta auntynka kake.
Duk mukasa dariya gaba daya muka dunguma
sai Palo tindaga qofa nakejin gabana yana
faduwa muna shiga Palo qirjina
yai wani mugun bugawa take zufa ya ketomin
naji jikina yasaki idan ban nemi guri na zaunaba
zan iya faduwa sbd ina ganin wajenda afnan ya
danneni sai nakejin kamar yanxu abinke faruwa
sai kallon wajen nake zuciyata fal da baqin ciki
da qyar naja jiki dayan kujeran 3 setter na zauna
momy ta kalleni tace lapia naga kinyi wani iri!
Nace momy walh nagaji ne duk naji
banajin dadi kuma kamarma bacci nakeji kinsan
alluran nan tanasa bacci.tace eh gaskiya ne
yanxu kiyi sallama tukuna saikici Abinci kisha
magani saiki kwanta ko.
To kawai nace su rufy duksun kewayeni wannan
yace kaza wancen yace kaza. Aunty
sadiya ta hada mana komai na Abinci mukai
sallah mukaci Abinci nasha magani natashi nace
ni yanxu zanyi sllahn isha'i. Dan bacci nakeji
momy tce to Anty sadiya tatayani kwana inyaso
gobe saita wuce gida.daman mamanta nata kira
wai taqi dawowa kuma tasan afnan baida lapia
kotaxo ta gaisheshi.
Nidai ina sallah na sanya kayan baccina na
kwanta.inna taso taxo a Daren saidai babu me
kawota dan dole ta haqura.
Ya Habib koda yaxo ina bacci dan haka ya
bayyana momy buqatarsa nason in koma
wajenshi.
Momy kam tace batasan da wannan maganar ba
babu inda zani.yayi yayi momy takafe akan babu
inda zanje dan haka yace to shikenan amma
gaskiya zaisa mana bodyguard dan bazai yiwu
adinga abinmu agida ana zuwa ana lalata
rayuwarmu ba.
Shima dai daqyar momy tayarda dan saida
Ahmad yasa baki a maganar. Haka yatashi
yawuce jiki ba qwari domin kuwa shi yafison ya
tafi dani wajenshi. Gari na wayewa saiga inna
tareda husna tin duku duku dan mu bamu tashi
bacci bama su suka tashemu.
Muryar momy najiyo tana cewa inna kece da
sassafen nan sannu da zuwa. Ina tashi toilet
nashige nai wanka inna ta shigo dakin tana cewa
ina me sunan mama saigani nafito ina dariya
nace inna gani tace ah lllai sauqi yasamu nace
ai daman na gaya miki yanxu zan iya karawa
dake.
Tazauna bakin gado nida nazauna surutunmu
yatashi Anty sadiya tana tashi kuwa suka gaisa
Kicin tanufa tafara shirya mana kayan breakfast.
Inna tace ahada damu bamu karya ba idan mun
karya zamu wuce gidan bukar dan Jiya yake
gayamun Ashe afnan ma beji dadi ba zanje na
dubashi.saida qirjina yabuga data ambaceshi
nikam yanxu ina matuqar jin tsoron ya afnan.
Sadiya ta kammala komai muna cikin break
saiga ya Habib nan yasamu inna tanatamai
surutun bashida kirki baya xuwa ya gaisheta
nandai sukaita yan wasannin da suka saba. Suka
gaisa da momy bai samu damar magana dani ba
dai sbd ganin inna hakanan yawuce yace zai
dawo da yamma.muna gama break inna tace
husna taxo su wuce dan harmun shige daki nida
ita munata hira dan haka inna tace to idan an
gama meeting din afito mu wuce, momy tace
inna kujira Anty sadiya mana Ku wuce tare. Inna
tace bayan ko wanka batayi ba nibazan jirataba
Aunty sadiya kuwa daman bason tafiya yanxu
take ba.anma momy saida ta lallabi inna TAce
anty sadiya tai maza ta shirya. Dan haka
adaddafe tasamu ta shirya suka wuce
Suna isaa....
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 19
==>Suna isa suka cimma su abba da umma a
palo suna breakfast hjy ta miqe taqaraso da
Sauri tana inna sannu da zuwa kune da safe
haka Ku zauna.
Suka zauna kan kujera inna Abba da umma
sunata kwasan gaisuwa aunty sadiya tagaisheda
momynta da abbanta. Husna ma cikin kunya ta
dubi su umma da Abba tace ina
kwana.sukadanyi murmushi tareda cewa lapia
lau. Ya Maman naki?tace lapia lau. Inna tace ni
banga afnan dinba ina yashige ne. Hjy tai dariya
tace ai yana dakinshi nyi nayi ma yafito yaci
Abinci amma yaqi sai abbanshi yaje tukun danni
an rainani.inna tace toni barinje na ganshi
daganan inyi lallashi. Sukai dariya inna ta miqe
tace taso husna muje kinsan niba gane dakin
nashi nake ba sosai.
Akunyace husna ta miqe dukda dai itama
tanason ganinshi amma tanajin kunyan su Abba.
Haka suka kama hanya inatada inna sadiya kam
tashi tayi tashige dakinta. Sun shiga dakin
amma basuga kowa ba ga dakin duk ahargitse
alamun andan jima ba a gyarashi ba.
saidai sunji alamun watsa ruwa a toilet dan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment