You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *????PRINCE SAPWAN????*


*STORY AND WRITTEN BY MARYAM YUSUF (UMMU JUWAIRIYYAH) AND SALMEERT (AUTAR MAMA, ƳAR LELEN ROYAL STAR)*


*Yanda muka fara littafin nan Ranar 20 May 2022, ALLAH ka bamu ikon gamashi lafiya*


*Wannan littafin ƙirƙiraren Labarine ba muyishi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan ya yi dai-dai da tsari ko halin gidanku ko Masarautarku to ayi mana Afuwa ba da sani bane.*


*Ba mu yarda wani ko wata ya chanja mana tsari ko yanayin littafinan muba.*

*Wannan littafin na kuɗine #200 kachal, ki biya ki sha karatun ki hankali kwance*



*??ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION??*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍????✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / ??????
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER?? ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*

*Bismillahi rahmanir rahim*.



*PAGE 1&2*



""""""""""""""""""""Cike Makil International Airport na garin Katsina yake ,dan ko masaka tsinke babu.


Dogarai ne birjik da alama dai ko wani Ɗan sarki ne zaiyi tafiya sukazo rakiya ko kuma sukazo taryarsa.


5minutes da shigata airport din naji dirar mikiyar jirgi , ganin duk Dogaran sunyi gurin jirgin ne yasa muma muka bi bayansu dan baza'a barmu a baya ba.


kusan 1 hour da dirar jirgin kafin wani haɗaɗe kuma kyakyawan Saurayi kamar balarabe ya fito cikin tafiyar izza da ƙasaita, cikin shigarshi ta Yaran Sarakai masu ji da kuɗi da ilimi haɗi da saurauta, dan kallo daya zakayi masa kasan shi jinin Sarautane gaba da baya.


dan ko yanayin tafiyar da yake cikin kasaita da nuna isa, cikin yanga ya fara tafiya, yana lumshe ido alamar Iskar gurin tana yi mishi daɗin shaƙa.


Dogarai ne suka fara taka masa suna mai kwasan gaisuwa, ko kallo basu ishe shi ba da alama dai akwai shi da jin kai, dan ko alamar suna gurin baya nunawa.


tafiya kaɗan ya ƙarasa gurin wasu lumtsuma-lumtsuman motoci na alfarma, bayan motar na kalla, inda anan ne naga an rubuta Yarima Sapwan 1, wani Dogari ne yazo da sauri ya bude mishi motar shiga ya yi.


sauran ma duk shi-shiga suka yi, motar shi ce a tsakiya sai huɗu gaba huɗu baya sai tashi ta tara wadda take tsakiya wanda duk an rubuta musu Yarima 1, wato Yarima Sapwan wanda mudai a iya yanzu mun gane cewa sunan shi kennan Yarima Sapwan.




****************



"Fulani yau fa wannan Yaron zai dawo, da Alama dai duk abinda muka shirya ya lallace", ya fada yana zama kan kushin din dakin, fuskarshi da tsananin ɓacin rai.



"menene na wannan ɓacin ran, ai ka kwantar da hankalinka a wannan dawowar zan halakar dashi a doron ƙasa domin , babu wanda zai gaji Sarautar masarautar Katsina sai Yarima Faiq", wata mata ta fada , wadda take cikin shiga ta Alfarma ta matan Sarki.



Wani mugun kallo ya jefeta dashi, kafin ya saki wani munafiƙin murmushi da bazaka iya fassara ko na menene, ba.




******************


Abincicika ne kala-kala shirye akan wani ƙayattacen dinning na Alfarma, sosai part din ya haɗu da za'a iya kiranshi da Aljannar duniya dan tsabar haɗuwarshi, ko ina ka duba cikin part din kayayyakin Sarauta ne na Alfarma, wata hamshaƙiyar matace tsakiyar parlourn cikin shiga ta kece raini .



**************


wani hamshakin gidan sarauta na cikin garin Katsina naga motocin Yarima Sap 1, sun shiga, sosai gidan sarautar ya haɗu da ko ina idan ka duba bayine da Dogarai birjik, ta ko ina kowa yana harkokin gabansa, direct motocin gaban fada suka tsaya sai da ya shari kusan 10 minutes kafin ya fito daga motar, bakin kofar fadan ya nufa, wani Dogari cikin masu tsaron kofar fada , ya yi saurin shiga fada dan sanar da Mai martaba isowar Yarima , sauran dogaran ne suka zube kasa suna kwasar gaisuwa.



Mai martaba ne, ya bashi Umarnin shigowa hakan yasa da sauri dogarin ya yi waje, domin isar da sakon Mai martaba.



ko jiran fadar sakon Mai martabar bai yiba ya shige ciki, yana yamutsa fuska.


tuni Mai martaba ya Sallami kowa dan zai gana da gudan jininshi, ko da ya shiga fadar kwalam babu kowa sai Mai martaba dake zauna kan kujerar mulki ta alfarma, wadda kana ganin yarda take walali kasan Akwai zinari a jikinta.

sosai kayan cikin fadar suka tafi dani domin komai na ciki na gargajiya ne, kusa da Mai martaba ya matsa .


da murmushi Abbun nashi ya kamo hannushi yana rungume shi , ɗuƙar da kanshi kasa ya yi, kafin yace.


"Sannu Abbuna An yini lafiya, na sameku lafiya?" ya fada yana yamutsa fuska kamar baya sonyi magana.



girgiza kanshi ya yi, kafin ya Ansa masa da "Alhamdulillah ya karatun?" jijjiga kai ya yi alamar Lafiya qlau.



murmushi ya yi, dan yasan wannan halin nashi na body language bazai iya barin shiba, sosai ya ringa janshi da fira amma amsar shi daga "uhmm, sai umuhmm", gashi shikuma na fiskanci yana bala'in son suyi fira.




gajiya ya yi, da irin amsar da yake bashi hakan yasa, ya ja hannunshi, ta cikin part din ya bude wata kofa, wani kayattacen parlour kofar ta sadasu dashi, shi kuwa Prince Sap, bin Mahaifin nashi kawai yakeyi a baya, dan gaba daya jikinshi ya yi wani irin mugun week.





*******************



"ba Ɗan ba har Uwar so nakeyi na kaudasu daga cikin duniyar na, domin a halin yanzu su kaɗai ne ciwon kaina, dan ni ba Sarautar ce a gaba na ba, Karfin fada aji shi nakeso" wata mata ta fada fuska a murtuƙe babu alamar rahama.



"to yanzu Kilishi ya za'ayi kinga dai yanzu abubuwa sunason dagulewa", ya fada a ruɗe.



wani murmushi ta saki wanda direct za'a iya kiranshi da na mugunta.



wata iriyar juyowa tayi, kafin tace "Na tsane ta, bana kaunar duk wani abu wanda ya fito daga jikin ta kuma ya zama dole daga ita har munafukin d'an na ta su ziyarce lahira nan kusa bada jimawa ba, ta fada ba tareda ta ji shakkar komai ba,



"Toh yanzu miye abun yi?", ya fada yana zazzare idanu.



"karka damu Waziri, ka barmin komai a hannuna kaidai tashi ka tafi", Kilishi ta fada tana zama ragwajaɓ kan kujera.



jiki a sanyaye, ya tashi ya fita , bin bayanshi tayi da murmushi kafin ta tashi ta fara Safa da Marwa .



*****************



parlourn ne babba wanda da gani kasan na Sarki ne, zaunar dashi ya yi, kafin ya zauna kusa dashi, hamshaƙiyar matar ɗazun ce ta shigo ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi mai nuna tsaninanin farin cikin da take ciki.




murmushi shima naga ya saki, sosai Mai martaba ya riƙe baki yana cewa,"watakan Uwarka kawai kakeyiwa dariya ni bandani", ya fada yana dan dukan kafadarshi.



Dariya Gimbiya Khadija tayi tana zama kusa da su, tana zama ya kwantar da kanshi kan kafaɗarta, haɗa ido suka yi da Mai martaba murnushi suka saki a tare kafin su daura hannayensu a kanshi su haɗa baki garin cewa ,"Allah ya yi, maka Albarka", lumshe idanunshi ya yi, yajin sanyi cikin ranshi.


Kuyagin gidan ne, suka fara shshigowa da kololin Abinci iri-iri daga part daban-daban wai a bawa Prince ,shi kuwa da yasan Halin tsarin masarautar da yawan magautansa a cikin gidan shi yasa tunda ya taso baya cin abincin kowa sai na Mahaifiyar da kuma Nene Mahaifiyar Abbunshi domin su kada ya yarda dasu a Masarautar, domin ta ko ina hari ake kawo masa, shiyasa ko yana son ci Maamah dinshi ke hanashi domin ita tasan ko mai ke faruwa a cikin Masarautar nason ganin bayan Prince Sap.



************


"ke! Sapna dan Ubanki zoki karasamin wannan wanke-wanke dan ba ciwo ba ko mutuwa kike kina dawowa Wallahi saikin karasashi , dan duk cikin Gidan nan babu Baiwan wannan sallamamiyar Uwar taki mai bakar kafa , gayyar masu bakin jini, da shegen naci, tunda kika zo gidan nan, gaba daya arzikinmu ya rushe, komi ya lallace mana, Yoh inama dalilin Auren gayyar tsiya irinku",ta fada tana daga tsuman da suka daura a kofar ɗakinsu a matsayin labule.


kwance take kasa tana ta muɗuɗuƙa da bulkayi kamar tarwaɗa sai wata mata fara tar dake kusa da ita tana yi mata sannu.

"Haba Aunty Tabawa kiyi hakuri ni bari in tashi inyi miki", matar ta fada tana yinkurin tashi.

da sauri wata ƴar Yarinya tace ", Ummie barshi na tashi na karasa ai tama kusa gamawa saura kaɗan", ta fada tana zama kan kujerar da aka ijiye a gurin.

da sauri Gwaggotabawa Tarawa finciki hannu Yarinyar tana cewa,"zan mugun saɓa miki Abasiyya , ke nasa?, ita nasa kuma ko zata mutu tana cikin yinshi sai ta yishi", ta fada tana tura Abasiyya ɗakinta.


Ummie ce ta tashi zata fito waje ta cigaba da wanke-waken riƙe hannunta akayi da mamaki ta juyo dan ganin waye, ban sadda bakinmu ni da Oummu Juju ya hade gurin furta Fatabaraqallahu Ahssanunqaliqin, Yarinya ce da baza ta wuce 15 to 16 years ba tsaye, fara mai dara-daran idanu wanda kallo daya zaka yimusu kasan cewa, fararene tar saidai dan sirkin ja dake cikinsu wadda da ka gani kasan Wahalar ciwone ya maidasu haka, bakinta dan karami wanda yake dauke da siraran lips pink colour sai sheƙi suke, ga siririn hancinta wanda ya yi dai-dai da face nata, jikinta dan dai-dai ita bamai ƙibaba ita ba siririya ba dai-dai misali dai, sai diri mai daukar hankali, komai dai yaji a jikinta Masha Allah.

"Ummie barshi bari na cigaba nama kusa gamawa fah", ta fada tana sakarwa mahaifiyar murmushi wanda da ka ganshi zakasan na karfin haline.


"zaki iya kuwa?, ki bari na karasa", ta fada da a alamar tausayawa akan fuskarta.

"zan iya mana Ummie kalli na samu sauki fa", ta fada tana..........

*muje zuwa.......*


*ZAKU IYA TURO DA KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN.* ??


*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK*


*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN*.??




*IDAN KUN TURO TO KU TURO MANA DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*??

*07033371851*



*KO KUMU WANNAN NUMBER DIN ??*






*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE ??‍♀️??‍♀️TARE DA SAHIBAR ROYAL STAR??*

??PRINCE SAPWAN??

*STORY AND WRITTING BY SALMEERT (AUTAR MAMA , ƳAR LELEN ROYAL STAR) AND MARYAM YUSUF (OMMU JUWAIRIYYA)*



*YARDA MUKA FARA LITTAFINAN RANAR 20 MAY 2022, ALLAH KA BAMU IKON GAMASHI LAFIYA*




*WANNAN LITTAFIN ƘIƘIRAREN LABARINE BA MUYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA, IDAN YA YI DAI-DAI DA TSARIN GIDANKU KO MASARAUTARKU TO* *ANYI MANA AFUWA BADA SANI BANE*


*BA MU YARDA WANI KO WATA YA CHANJA MANA TSARI KO YANAYIN LITTAFINAN BA*


*WANNAN LITTAFIN NA KUƊINE #200 NE KACHAL KUƊINSHI, KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE*


*??ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION??*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍????✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / ??????
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER?? ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*



Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki????
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,??‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas??
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai??
Sleeping dress, kananan kaya na gayu??kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari????domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya??08101521252
nagode kwarai da gaske????

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.


PAGE 3&4

"""""""""""""""""""Tana nuna jikinta, "To Allah ya yi miki Albarka Insha Allah sai kin zama gatanmu baki daya", ta fada tana maida hawayen idonta.


Sapna kuwa dauke kanta tayi, bata nuna tama ganiba, a hankali ta nufi gurin wanke-wanken tana dafe ciki tare da ciza lips alamar tana jin ciwon har cikin kwakwalwar kanta, A hankali take wanke-wanke, ball taji anyo da wani kwano har saida ya bugar mata kafa wani irin azaba ce ta ratsa har cikin tsakiyar kanta.


ko dagowa batayi ba dan tasan ko waye zai iya yin haka, ba ko Sallama ta shigo gidan tana fito kamar ƴar arnaku buta ta dauko toilet ta shige da waka abakinta babu ko Addu'ah girgiza kai Sapna tayi tareda cigaba da yin wanke-wanken ta,



"Ke bakar annoba, kiyi maza ki gama wanke-wanken nan ki zo ki haza murhu don ban ga uban wanda zai dafa miki abinci ba" cewar Inna tana maka mata harara, ita dai Sapna kanzil ba ta ce ba, kawai ta cigaba da yin wanke-wanken ta, Malam kuwa abun duniya ya ishe shi,




Yana son yayi magana amma yana gudun yace wani abu Inna ta hau shi da zagi domin kuwa sarai sanin halin matar tashi da yayi zata iya zabga mishi ashar ko agaban waye, Ummi shiru tayi bata iya ce komai ba amma maganar gaskiya ba kadan take tausaya ma Sapna ba, a kullum adduar ta guda shine Allah ya kawo mata miji na gari tayi aure ta huta abun ta,




Sapna bata wani jima ba ta kammala wanke-wanke, nan take ta shiga kazantaciyar kitchen nasu ta hada wuta yanda Inna ta umurce ta, tana yi tana zubda hawayen bakin ciki, don ba kadan take jin jiki ba, ga aikin da Inna ta sake saka ta, ita sam batada mutumci a idon yan gidan ba mai kaunar ta in ka cire Ummi wani lokacin Malam na dan son ya nuna mata kula amma kuma sai ya kasa, ita dai bata san miye dalili ba, amma ai in da sab'o yaci ace ta saba,




Adduar ta a koda yaushe shine Allah ya bayyanar da mahaifiyar ta, domin kuwa Ummi tasha bata labarin cewa Umman ta bata mutu ba, kawai dai basu san in da ta nufa bane, domin kuwa Ummi bata taba gaya mata cewa Umman ta haukacwa tayi ba,




**************
"Jakadiya kiyi yanda nace ki aikata, wallahi idan kika bani kunya zaman ki ya kawo karshe a cikin fadar nan", cewar Fulani tana makawa Jakadiya harara, "Ranki ya dade duk yanda kika ce ayi hakan ma za'a yi Uwar'gida sarautar mata, Allah ya ja da zamanin ki,



"Ya isa karki cika ni da surutu" Fulani ta dakatar da ita tareda nuna mata hannu alamar ta fita, ba tareda bata lokaci ba ta fita tana mai kimtsa abubuwa da dama aran ta,



"Yau kinmanin kwana uku kenan amma har yanzu babu alamar ciwo tattare da dan iskan yaro nan hanya kuwa Jakadiya ta aiwatar da abunda na umurce ta tayi cewar Fulani ta na kallon Waziri,




A dan rude Waziri ya fara magana "Fulani me kike nufi, Jakadiya kika bawa magani ta sakawa Yarima Sapwan a abinci lalle kin yi wauta, kar ki sake ki kara bata, kuma yanzu ki san yanda kikai kika nuna mata wannan magani ba wai na cutarwa ne ko wani abu ba, saboda gudun asirin mu ya tonu,




Kii tuna, jakadiya tana tareda Gimbiya Khadija komai ma zata iya gaya mata, "A'a Waziri kwantar da hankalin ka, ai na riga da na mata kashedi in har ta yarda ta gaya ma wani toh zata ziyarce lahira ne, domin kuwa a ranar bazata kara koda minti daya bane a duniya,




"Hmmm toh shikenan naji zancen ki, amma ki kula sosai, ki bari mu bi ahankali sai mu kashe Dan banza ba tareda ya bamu ciwon kai ba, cewar Waziri, Fulani wani Irin murmurshi tayi wanda ita kadai tasan ma'anar sa, bata sake kallon Waziri ba belle yayi tunanin zata yi magana,




****************
Kwance yake saman tafkeken gadon sa, wanda gaba dai ya tafi da tunani na, da alama dai itama Yar lelen royal gadon ya tafi da tunanin ta, domin kuwa gado ne mai kyau ya hadu iya haduwa, ya salam na iya furta ba tareda nace komai ba, Prince Sapwan sai danne-danne yake a laptop dinsa da alama dai wani aiki mai muhimmanci yake, domin kuwa gaba dai ya tattara hankalinsa kan laptop din,




Gani nayi ya dafa kirjin sa, yana son yin magana amma ya kasa furta komai, daga nan kuma bai sake sanin inda hankalin sa yake ba,



Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta na fadin "Yarima kayiwa Allah ka mun magana, me yake damun ka ne, me kaci, ka gaya min don Allah ta fada ya yinda ta sake fashe da wani irin kuka mai cin rai, sosai jikin mai martaba yayi sanyi nan take ya shiga rarrashin ta, shi kan sa ji yake kamar ya dinga kurma ihu, domin kuwa a gaskiya ya tsorota da wannan yanayi na d'an nasa addu'o'i ya shiga tofa masa tareda karanto ayatul kursiyu,




Wayan sa ne ta shiga ruri nan take ya daga tareda cewa "Doctor ka shigo, doctor shigowa yayi tareda gaishe da Mai martaba, sarki ko amsa masa bai yi ba "don Allah ka gaya min me yake damun Yarima, Doctor ka ga ya min gaskiya idan ma matsalar babba ne kawai sai na fita dashi kasar waje, Sarki ya fada a sanyaye,



Kalo daya zakayiwa Price Sapwan ka shaida komai bazai iya yiwa kansa ba a halin yanzu domin kuwa kwance yake kamar mattace amma idon shi bude, komai baya iya wa kansa tunda safe da abun ya faru dashi, Gimbiya Khadija kuwa taci kuka har ta godewa ALLAH,



"Dube-dube likita ya shiga yi wa Prince Sap nan take ya juya ya kalle Sarki tareda cewa, "mai martaba kayi hakuri don Allah bisaga maganar da zan fada domin kuwa Yarima Sapwan yayi lossing din kwakwalwarsa a halin yanzu ba abunda zai iya tuna, kuma ba abunda zai iya yiwa kan sa,




Ai bai ida zancen sa ba Gimbiya ta fashe da kuka mai taba zuciyar mai saurare, sosai ta shiga rera kuka tana jin tausayin dan nata, nan take sauran matan gida suka fara shigowa daya bayan daya, ai kuwa nan take ko ina ya dau zancen rashin lafiyar Prince Sap, kowa ya girgiza ba kadan ba, ya yinda murna wajen Fulani da Kilishi ba'a ko magana, amma fa a boye,




Mamaki Fulani ta shiga yi ita dai bata san ta masa komai ba, amma tunda tasan daman ba ita kadai ce ke bakin cikin sa ba, shiyasa nan take ta bawa kan ta amsar cewa aikin Kilishi ne,




Magani kala-kala babu wanda Sarki baiyyi ba, kasashen waje kuwa ba inda ba'a kai Prince Sap ba, amma ko alamar chanji babu ciwo kullum sai gaba yake tayi, kusan wata biyar kenan da rashin lafiyar Sapwan, babu in da masu je, Gimbiya kuwa yanzu tama daina kuka ta barwa Allah komai,


*******************
Da sauri ta fito daga cikin rubaben dakin nata, sanadiyar wani irin aman da take ji, tuwon da taci jiya duk ya bata mata ciki, ni dai sai kallon ta nake tayi domin kuwa yarinyar kyakyawa ce ajin farko, sai da Yar lelen royal ta taboni tana cewa Oum Juju zaki chinye diyar mutane?? ai kuwa nayi maza na kauda idona daga kallon ta,




Inna ce ta fito tana kururuwa tana cewa "Innahu min Sulaimana wa innahu Bismillahi Rahmani Raheem, me nake gani haka, Sapna ba dai ciki ne dake ba"



Sapna a rude ta d'ago tareda fashewa da kuka tana fadin "Wallahi ni ba ciki ne dani ba kar ki min sharri, Inna bude baki tayi tana mamakin Sapna, domin kuwa koda wasa Sapna bata taba gardama da ita ba, amma ga shi nan yau tayi,




Ummi ce ta fito daga cikin dakin tana fadin "Yoo kuma sharrin da zaki mata kenan, domin kuwa taji duk abunda ke wakana a tsakanin su, Inna don Allah kiyi hakuri ki shafa mata lafiya, kin dai san tun jiya bata jin dadi, Inna bata ce da Ummi komai ba fashe wani mugun harara da ta watsa mata,



"Sannu Sapna, Allah ya sawwake" cewar Ummi tana mai kara jin tausayin Sapna, "Yauwa" Sapna ta fada da kyar, Ummi wanke mata fuska tayi tareda gyara mata jikin ta, suka koma daki, ko minti biyar basu yi ba Inna ta kwala mata kira,




"Ke shegeya ki fito ki fa dora sanwa, don dai bazai yu ba na dafa abinci kuma kiyi zaune-zaune ki ci ba, uban ki ma yaci, saboda haka wlh ko mutuwa zakiyi sai kin dafa abinci, "Haba don Allah Inna ki bari ni nazo na dafa" cewar Ummi ya yinda ta yaye labulen dakin tareda cewa, "kin ga dai tun jiya bata jin dadi don Allah ki shafa mata lafiya mana,



"Kin ga Ummi ki fita a idona na rufe, ko kuma in saba miki wallahi ni ban haife yar da zata dunga mun wa'azi ba tana takura min kinyi kadan, baki isa ba wallahi, dakin Sapna ta nufa tareda cewa "ke kuma bakar munafuka ki fito nace ko kuma mahaukaciya uwar ki ce zata zo ta dafa muna abinci,




Tun daga cikin daki Ummi ta dinga jiyo sautin kukan Sapna, domin kuwa duk sanda Inna ta kira Umman ta da mahaukaciya toh fa ranar Sapna wuni take tana disgar kuka, sosai yarinyar ta dinga bata tausayi, Ummi zata shiga dakin ta kenan, budar bakin Inna sai cewa tayi,




"Wallahi ki kaje kika rarrashe ta, toh ban yafe nono na da kika sha ba, shashashar banza kawai wace bata san ciwon kan ta ba, Ummi dai shiru tayi tana kallon Inna daga bisani tace "Inna kiyi hakuri me yayi zafi haka,




**************
"Gimbiya ta abin so awaje na, kin san dai ina son ki sosai fiyeda tunanin ki, kuma nasan kina min biyyaya, bakya yin jayyaya dani, toh yau ma ina son ki min biyyaya, ki saurare ni da kyau" "Toh shikenan Mai martaba Allah ya kara sawon kwana ina sauraren ka" "Allah shi miki albarka, Khadija ina son nayi Yarima aure,




Gimbiya tsoro ne bayyane karara akan kyakyawar fuskar ta, kuka take shirin yi, mai martaba ya dakatar da ita tareda girgiza mata kai alamar a'a kar tayi kuka, "Don Allah kayi hakuri ba wai saba wa umurnin ka zan yi ba, amma don Allah ka bari har sai Yarima ya ji sauki ya kuma zaba wa kan shi matar da yake so, amma a halin yanzu babu matar da zata so zama dashi sai don kudin mu da kuma mulkin ka, "mai martaba kayi min rai ka fahimce nufi na don Allah, Gimbiya Khadija ta fada ya yinda ta fashe da kuka mai cin rai,





Sosai take bawa mai martaba tausayi, domin yasan Khadija mace ce mai ilimi da sanin yakamata sam abun wani bai dame ta ba, rarrashin ta ya shiga yi tareda nuna mata amfanin auren da zai yiwa dan nasu,




nan fa ta kara nuna masa, ai ita zata iya kula dashi, nan mai martaba ya dinga nuna mata, ai wasu abubuwan bai kamata tana masa ba, wani abu bazata iya masa ba sai dai matar shi, nan dai ya dinga bata baki har ta amince, "toh amma Mai martaba wace ce matar tashi" ,ta fada tana kallon cikin idanunshi.




"ki kwantar da hankalinki idan lokaci ya yi, zaki san ko wacece", ya fada yana dauke idanunshi daga cikin nata.


"yadai kamata da nasan ko wacece sirikar tawa ko rowarta akeyimin", ta fada da murmushi kan fuskarta.



"ki kwantar da hankalinki kinsan dai bazan taɓa zaɓawa ɗana abinda zai cutar dashiba", ya fada yana dan dafa kafadarta.



****************


Sapna ce ta fito murhu ta fada, kafin ta daura gangarememiyar tukunyarsu lamba 10 kafin ta tashi, ta dauki niƙan su ta , kai a achan ta tsaya har aka niƙo musu kafin ta dawo, rariya ta dauka ta fara tankaɗen dawar da takai niƙa, kafin ta gama har ruwan ya taso, hakan yasa ta talga.


tana cikin aikine Baba ya shigo, dafa kanta ya yi yace, "Allah ya yi, miki Albarka Allah yasa ki zama wani abu a rayuwa", ya fada yana maida hawayenshi.



"to Ahmadu , su kuma nawan da baka sa musu Albarkar sai sun zama wani abun", ta fada tana jifarsu da harara, shidai bai ce komai ba, ɗakinshi ya shige.


da sauri Inna tabishi tana cewa ", to kawo abinda ka samo ka wani wuce daki zugui-zugui sai kace wani na Allah", ta fada tana dalla mishi harara.



da sauri ya fiddo kuɗin ya miƙa mata, "Kai! Ahmadu karka rainamin wayau kace wannanne kaɗai kuɗin", ta fada tana huci kamar ita ta nemo kuɗin.



"Wallahi Tabawa iya kun kuɗin da nasamo kenan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment